Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 4
fito nema domin idan baku manta ba a baya an gaya mana cewa ba zai taimakemu ba face ya jarraba gaskiyarmu, amanarmu da jin kanmu. Gashi gaba dayanmu nan mun wulakantashi Lushaira ce kadai ta taimakeshi. To yanzu bamu da wani zabi da ya wuce mu yi abu biyu. Abu na farko shi ne, dole ne mu tura wasu daga cikinmu su bazama izuwa neman wannan Almajiri a cikin wannan daji. Zamu za6i mutum takwas ne bibbiyu su watsu gabas da yamma, mu kuma ZAmu rabasu shiga cikin wannan kauye mu zauna tsawon kwana bakwai muna jiran dawowar wakilan namu. da suka tafi neman jarumi Imran. Ina son kowannenmu ya kiyaye dokokin da wannan Almajiri ya kafa mana cewar kada mu ci ko mu sha wani abu a cikin wannan kauye, kuma ba zamu zauna a ko ina ba face a cilkin kasuwar kauyen. Sannan zamu kasance a tare koda yaushe. Hakika ba karamar sa'a muka yi ba har da muka fara haduwa da jarumi Imran tun a farkon wannan tafiya tamu. Sai dai kuma mun yi rathin sa'a da muka kasa haye jarrabawarsa ta farko. Lallai ne mü yi hattara nan gaba idan muka sake saduwa da shi". Koda gama wannan jawabi sai Suzaila ta waro mutum takwas daga cikin tawagar ta sallamesu suka nausa izuwa cikin jeji domin neman jarumi Imran, sannan ta jagoranci sauran abokan tafiyar suka durfafi wannan kauye da ke gabansu. Lushaura ce ta jera da Suzaila a 6angaren damanta, shi kuwa Hasnalu na daf da Lushaira. Ana fara tafiyar ne Hasnalu da Suzaila suka hada idanu. Bisa mamaki sai Hasnalu ya ga Lushaira tayi masa wani dan guntun murmushi. Nan takẻ yaji wani irin farin ciki ya lullu6eshi tamkar an bashi sarautar duniya. A dai-dai wannan lokaci ne kurna zuciyarsa ta buga da karfi, ya tsorata ainun sakamakon ganin zubar hawaye a idanun gimbiya Suzaila. Ashe Lushaira ma ta ga zubar wannan hawaye na Suzaila don haka sai ta dubeta cikin tsananin damuwa ta ce, "Ya ke kawata ina dalilin zubar wannan hawaye a idanunki?" Koda jin wannan tarnbaya sai Suzaila ta yi murmushi ta ce, "Ya ke kawata ki yi sani cewa ba komai ne ya sani zubar da wannan hawaye ba face tsananin SO da begen jarumi Imran. Hakika na yi matukar takaici bisa rashin ganewa cewar shi ne wanan Aimajiri da muka hadu da shi muka wulakantashi. Burina shi ne mu sake haduwa da shi lallai a sannan ne zan nuna masa irin tsantsar kaunar da nake yi masa koda kuwa ba zai amince ba ya biya mana bukatarmu". Koda Suzaila tazo nan a zancenta sai yarima Hasnalu yji wani irin bakin ciki ya yi katutu a cikin zuciyarsa yaji ya tsani jarumi Imran inda ace ma ya. san shi ne wannan Almajiri da tuni ya kasheshi don kada ya hanashi mallakar Suzaila. A can karkashin zuciyarsa kuma sai yaji yana mai cewa, "To idan ma ka kashe jarumi Imran a banza ne tunda babu yadda za a yi Suzaila ta soka face ka yyi gagarumar bajinta ta jarumtaka wacce tafi ta ta. Ai kuwa tunda baka kasancc jarumi ba babu yadda za a yi haka ta faru, ashe kuwa Suzaila tayi maka nisan da har abada ba za ka iya mallakarta ba." Koda Hasnalu yazo nan ả tunaninsa sai shima hawayen bakin ciki ya zubo masa. Ashe Suzaila ta lura da sa'adda wannan hawaye ya zubowa Hasnalu, nan take a karon farko taji tausayinsa ya kamata, amma da ta tuna cewa bai kasance jarumi ba sai taji ya fita daga ranta gaba daya, kuma ta daina jin tausayinta. Nan dai tawagar ta ci gaba da tafiya. Ai kuwa suna shiga cikin wannan kauye sai suka ga jama'a maza da mata, yara da manya masu siye da siyarwa sukayyo caa! A kansu suna kawo musu tallan kayan ciye-ciye da na shaye-shaye iri-iri masu ban sha'awa. Har wasu daga cikin jama'ar su Suzaila suka fara kokarin yin siyayyar sai Suzaila ta daka musu tsawa suka shiga taitayinsu. Tsawar da Suzaila tayi nema ta sa mutanen garin suka firgice suka ja da baya suka zuba masa idanu kawai. AA Misau ke Magana Kawai sai suka ci gaba da tafiya a cikin garin ba tare cda sanin inda suka dosa ba. Suzaila tayi ta raba idanu, kawai so take ta ga nutumin da za ta iya aminta da shi ta tambayeshi inda kasuwa take. Daga can kuma sai ta ce a cikin zuciyarsa, at bai kamatsa ba mna in yarda da kowa ba a cikin garin nan tunda Aimajiri ya yi mana kashedi. Ai kasuwa bata buya duk inda take nia za mu ganta. Haka dai suka ci galba da tafiya har Allah Ya sa suka hango kasuwàr garin Cikin farin ciki suka durfafo hanyar kasuwar. Da isarsu tsakiyar kasuwar suka ja tunga suka tsaya. Suna tsayawa sai wani dogon mutum ma'abocin kwarjini sanye da alkyalɔba da farin gernu ya taho garesu fuskarsa cike da annuri ya ce, "Lale marhaban da manyan baki." Kawai sai ya kamawa gimbiya Suzaila dokinta ta sauka. Suzaila ta dubi mutumin ta ce, "Wane ne kai?" Dattijon ta ce, "Sunana RUBIYAN IBINI ALBASI ni ne Sarkin kasuwa". Koda jin haka sai fuskar Suzaila ta fadada da murmushi ta ce, "Muna da bukatar gida a cikin kasuwar nan wanda zai isheni na zauna ni da dukkan jama'ata har tsawon kwana bakwai". Rubiyan ya ce, "An gama ranki ya dade, ábinda za ki biya shi ne, dinare dari biyu da hamsin". Ba tarc da Süzaila ta ce uffan ba sai ta dubi daya daga cikin kuyanginta. Nan take kuyangar ta kwance wata jaka da ke rataye a kafadarta ta đebo dinare mnai yawa a ciki sannan ta kirgi dinare đari biyu da hamsin ta mikawa Sarkin kasuwa Rubiyan. Hannunsa na kyarma ya karbi kudin domin a zatonsa ba za a biya ba saboda ya tsuga kudin. Tabbas ya ninka kudin ne gida uku saboda baya son su biya su zauna saboda wani boyayyen sirri amma kumna sai ya ga tsadar ba ta dami su Suzaila ba. Nan take ya gane cewa lallai wadannan baki sun kasan ce mn ashahuran masu arziki ko kuma Sarakai amma dai sun fi kama da Sarakuna ma saboda ganin irin yanayin shigarsu. Nan dai Rubiyan ya yiwa Suzaila da tawagarta jagora izuwa wani tafkcken gida a cikin kasuwar. Da Zuwansu kofar gidan kowa ya sauko daga kan dokinsa. Rubiyan yasa mukulli ya bude katuwar kofar gidan kowa ya ja dokinsa ya shige cikin gidan. Gida ne mai girma da fadi kuma an yi masa tsari irin na gidan sarauta, akwai bangaren garkar dawakai kuma akwai wani dan lambu mai cike da furanni kala-kala abin sha'awa. A kallah đakunan gidan sun kai guda goma sha biyu. Daki na karshe shi ne wanda ya fi sauran gaba đaya girma da kawatuwa har da 'yar karamar fada a cikinsa. Bayan Suzaila ta shiga cikin ko ina a cikin gidan ta gama nazarinsa sai ta dubi Suzaila da Hasnalu ta ce, "Ku ne za ku zaun a cikin wannan daki wanda ya fi gima da kyau ni kuam zan zauna a wancan dakin da ke makoftaka da naku." Cikin mamaki Lushaira ta dubi Suzaila ta ce, "Haba ya ke yata ya ya kina matsayin shugabar wannan tafiya amma za ki bamu dakin da yafi naki komai." Koda jin haka sai gimbiya Suzaila tayi murmushi ta ce, "Akwai dalilin da ya sa nayi hakan amma ba za ku san dalilin ba sai anan gaba idan har mun sake saduwa da wanda muka fito nema," Gama fadin hakan ke da wuya sai Suzaila ta rarraba sauran jama'ar izuwa dakunansu yadda babu wanda zai takura, Hatta Bayi da Kuyangi sai da kowa ya sami inda zai kwanta cikin wadata. Bayan an gama wannan shiri ne Sarki Kasuwa Rubiyan ya dubi gimbiya Suzaila ya ce, "Ranki ya Dade yanzu saura maganar abincin da za ku ci a tsawon kwanaki bakwan da za ku yi ả wannan kauye namu Har ruwan shanku da kayan marmari idan kuka biya dinare dari da ashirin Zan wadata ku dasu". Koda jin haka sai Suzaiia ta yi murmushi ta ce, "Ai bama bukatar komai na ci ke na sha daga garela: saboda mun taho da isasshen guzirinmu. Na sallarneka kaiya tafiyarka". Cikin sayin jiki Rubiyan ya juya ya fita da ga gidan gaba daya. Tafiyarsa Leda wuya sai yarima HASNALU ya dubi Suzaila ya ce "Ni kam ban yarda da wannan mutum ba domin Akwai alamun rashin gaskiya akan fuskarsa. Suzaila ta gyada kai tace Nima naga haka amma dai ko me suke nufinmu to muna shirye da su." Tana gama fadin hakan ta juya ta shige cikin wata dakin ta bar Lusihaira da hasasnalu a tsaye suna masu binta da kallo a lokacin da kuyangjn Suzaila suka bita a baya duu! Domin su yi ma ta hidima. Su kuwa nasu kuyargin na tsaye a gefe daya suna sauraron umarmi Wannan shi ne abinda ya faru ga su gimbiya Suzaila bayan sun sadu da jarumi imran kenran ba tare da sun shaida shi ba kuma ya subuce musu AL'AMARIN Sarkin kasuwa Rubiyan kuwa, lcikacin da ya bar wannin gida inda ya kai su giimbiya Suzaila bai zume ko ina ba sai a gidan Sarkin garin nasu wani kesurgurmin matsafi kuma azzaluni wanda ya zamo abin tsoro ga kowa a kauyen. Shi dai wannan Sarki ana kiransa da suna LABARAZU IBINI KAURAM. Sarki Labarazu yana bautawa wani katon dodo ne wanda kullum sai an yanka masa mace budurwa da namiiji saurayi yasha jininsu don haka ne idan baki suka shigo garin ake lullubesu da tallan kayan ciye -ciye da na shaye-shaiye. Da zarar mutum ya kuskura ya ci ko ya sha wani abu da aka siyar masa nan take zai 6ingire kasa a kama barci, sai dai ya farka ya tsinci kansa a cikin wani katon kogon dutse a cilkin keji. A cikin wannan dutse ne dodon da Sarki Labarazu ke bautawa yake. ldan kuwa aka wayi gari babu mutanen da za a yankawa dodon to fa sai a tafi farautarsu a cikin sauran Garuruwan da ke makotaka idan acan din ma ba a samo ba, to fa dole ne a davvo gida a kamo masu tsautsayi! Hhhhh Nima Gudun Kar A kamo dani Zan dakata Anan saimun Hadu a littafi na shidA SHIN SU GIMBIYA SUZAILA ZA SU TSIRA DAGA TARKON WANNAN MATSAFIN SARKI? YAUSHE ZA SU KUMA SADUWA DA JARUMI IMRAN SHIN JARUMI IMARAN ZAI AMINCE YA BIYA MUSU BKATARSU? INA LABARIN IARUMI MAI KAION BUSA A MUTU, WATO MURAISU DA SU DA MAIHAIFIYARSA A CIKIN DAJIN KIRZUFA MENE NE MATSAYIN SOYAYYAR HASNALU DA GIMBIYA SUZAILA SHHIN JARUMI IMRANA ZAI SOYAYYAR GIMBIYA SUZALA? Mu hadu a ittain BUSA A MUTU kashi na shida dan jin ci gaban wannan kasaitaccen Yabäri Daga Mai debe muku kewa a kullum a ko yaushe Abdulaziz Sani M Gini Nikuma AA Misau ke Magana Domin Samun ire iren wadannan litattafai zaku iya Samun mu a WhatsApp group dinmu ta hanyar danna wannan rubutun dake kasa 👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4