Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels BUSA A MUTU Littafi Na Biyar (5) Part A Na Abdulaziz Sani M Gini AA Misau ke Magana Barkanmu da wannan lokacin Dafatan Muna lafiya Ina Ma'abotA son cigaban littafin Rijiya Gaba Dubu to Albishirinku ranar Asabar Zamu dora daga inda aka tsaya Insha Allah Marubucin yaci gaba da cewa.... LOKACIN da Sarkii Jamal wanda ke nulkin binin yazo karshe a bayaninsa bisa shawarar da za abi domin a ga karsher jarumi maí kahon BUSA A MUTU sai geha dayan Saraakunan da ke cikin dakin taron suka yi tsuruu-tsuru suka kama kallon junansu. Duk wanda ka kalla sai ka ga aiarmua tsananin Tsoro a cikin fuskarsa. tsawon yan dakiku ba a sami wanda ya kara ce wa komai ba. Daga can sai Sarkı Imras yai gyaraa murya ya ce, Ya ku yan uwana- Sarakai, ku y sani cewa nayı iyakar bincikena a cikin hallarar tsafi domin gano hanyar dà zamu iya magance wannan matsala. Mafitar da na samo tana da tsananin wuya kuma na jarrabata ma amma abu ya faskara. Ina so ku sani cewa shi ilimin tsafi :kogine mai Tsnanin zurfin da bashi da karshe saboda haka ga wata sabuwar shawarar da zan bamu Wannan shawara ita ce, mu tara gaba dayan bokayennu su dukufa aikin bincike a tare Tsawon kwana bakwai ma'ana su hada KARFI DA KARFE wajen aikin binciken, idan aka yi hakan tabbas za a gano wata hanya ta biyu wacce za ta fiye mana sauki Koda Sarki Imsar yazo nan a zancensa sai fiye da rabin sarakai da ke cikin fadar suka kamu da matukar farin ciki, sauran kuwa sai hankalinsu ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe. Musamman ma-Sarki Huraisu wanda tunda aka fara magana bai ce uffan ba, amma ya sunkui da kansa kas yana tunani. Nan take dakin ya sake hargitsewa da hayaniya gami da musu da kace-nace tsakanin 6angaren da suka gamsu da shawarar Sarki Imras da wWadanda basu gamsu ba. Ana cikin wannan hayaniya ne kawai aka ga wani bakon boka ya shigo cikin fadar. Shi dai wannan boka ya yi shiga ne irin ta mutanen kasar Hindu kuma kallo daya za ka yi masa ka san cewa jinin Hindu ne. Ya kasance tsoho tukuf mai shekarun da lallai sun haura dari, kuma gaba dayan gashin da ke jikinsa fari ne sol. Gemunsa dogo ne ya zuba har kasan cibiyarsa. Gashin bakinsa kuma murtukeke ne ya cika fuskarsa. Launin kayan jikin nasa koraye ne shatar kuma yana dogara wata koriyar sanda. Koda Sarakunan suka yi arba da wannan bakon boka sai kowa ya cika da tsananin mamaki da suka ga wani irin farin haske da ke tashi a jikin musamman bokan tamkar bai kasance mutum ba. Da shigowar bokan cikin dakin taron sai komai na dakin ya sauya launi ya koma kore kuma dakin ya haskake gaba daya yadda ko allura ce ta fadi sai an ganta. Hatta iskar da ke kadawa a cikin dakin wacce ke shigowa ta cikin tagogi da kofofí saida ta sauya yanayi ya zamana cewa gaba dayar dakin ya dauki wani ifin sanyi madaidaici mai dankaren dadi. Take kowa ya firgita da ganin wannan boka hatta Sarki Imsar kuwa wanda yake ganin ya kai wani babban matsayi a harkar bokanci. Cikin tsananin girmamawa dukkanin Sarakunan suka mike tsaye don girmama bakon bokan kuma suka dare aka samar masa da hanya ya wuce ta tsakiyarsu. Tun kafin ya karaso inda karagar mulkin take Sarki Huraisu ya mike tsaye daga kan karagarsa ya koma gefe daya yana mai yiwa bokan nuni da ya zauna alkan karagar tasa. Koda ganin haka sai bakon bokan ya dubi Sarki Huraisu ya yi murmushi ya ce, "Ya kai mai birnin Lairuf ai babu mai zama akan wannan karaga taka face wanda ke da gadonta. Na gode bisa wannan girmamawa da ka bani". Koda gama fadin hakan sai bokan ya koma gefe daya kusa da Sarki Huraisu ya tsaya sannan ya fuskanci gaba dayan sarakunan da ke cikin dakin ya ce, "YA Sarakunan wannan nahiya ku yi sani cewa ni sunan a BOKA KIRISHNA BIN URAD. A halin yanzu duk fadin duniya babu wani boka mai yawan shekaruna da yawan sirrikan tsafina kuma ina zaune ne a cikin wani kogo da ke can bayan birnin Hindu wanda ake kira KOGON HAREMA. Shekafata dari da sittin da uku a cikin wannan kogo, kuma a cikinsa uwata ta haifeni. Ina fadowa duniya mahaifiyar tawa ta mutu. Aljanu ne suka reneni har na girma. Tsawon shekaru dari da sittin din nan ban taba fitowa ba daga cikin kogon Harema ba sai yau kuma idanuna kawai na rufe, ina budewa na tsinci kaina a gaban wannan daki da kuke wannan taro. Ku yi sani cewa duk halin da kuke ciki bisa fargabar mutuwar ya'yayenku duk na sani kuma idan ba a dauki matakin gaggawa ba wannan masifa sai ta yadu ko ina a cunya ia žamo sanadin da gaha dayan ya'yayen sarakan duniya za su rasa rayuwarsu. Ni kaina asalina d'an Sarki ne don haka wannan masifa sai ta shafeni. Yanzu haka na zo mana da mafita ne guda daya wacce ita ce kadai hanyar da zamu bi mu tserar da duniya daga cikin wannan mummunan tashin hankali ". Koda boka Kirishna yazo nan a jawabinsa sai gaba dayan Sarakunan suka kamu da tsananin farinciki kuma kowa ya nutsu aka yi tsit tamkar mutuwa ta gifta aka zubawa boka Kirishna idanu domin aji bayanin da zai yi a kan wannan mafita da yazo da ita, musamman Sarki Imras da Sarki Huraisu. Boka Kirishna yai gyaran, murya sannan ya ce, "Ya ku wadannan Sarakai ku yi sani cewa'a halin yanzu duk duniya babu wani mahaluki da zai iya yi mana maganin wannan masifa face wani jarumi guda daya wanda ya kasance ma'abo cin addinin Musuiunci ana kiransa da suna IMRAN IBN HÚZEIR. Jarumi Imran ya kasance kyakkyawan saurayi kuma mai matukar jarumtaka ta gaban kwatance anan kuma yana da launin fata na wankan tarwada, ma'ana shi ba fari bane, kuma ba baki bane kumay na da tsawo dai-dai misali gami da kaurin jiki. Mutum ne shi wanda baya zama a waje daya kuma rayuwarsa gaba daya a cikin daji take fiye da shekaru goma sha biyu da suka shude. Bai ta6a cin nama ba ko wani abinci.dabam wanda bai kasance dan itaciya ba ko ganye. Kullum dare da rana a cikin farauta yake gami da bautar Ubangijinsa. Baya farauto kananan dabbobin daji sai manya kuma a shekara sau uku kacal yake shiga cikin gari daga lokacin zafi sai lokacin sanyi sai kuma lokacin damina. Bai damu da komai na jin dadin duniya ba. Baya sa sutura mai kyau, baya cin abinci mai dadi, kuma baya kwanciya akan shimfida mai taushi. Babu abinda ya tsana sama da zalunci sannan kuma baya taimakon mutum face ya jarrabashi ya tabbatar da cewa yana da abubuwa uku. Abu na farko shi ne, dole ne ya tabbatar da cewa mutum yana da gaskiya, amana da jin kai. Babbar matsalarmu anan ita ce bamu san a inda jaurmi Inran yake ba a halin yanzu bare muje my riskeshi tunda ya kasance matafiyi wanda baya žama a waje daya. Na yi iya bincikena na kasa gano inda yake a yanzu saboda shi tsafi baya tasiri a kansa. Shi ac kadai wanda zai iya shiga cikin dajin Kirzufa ya kamo Muraisu kuma ya fito a raye." Sa'adda boka Kirishna yazo dai-dai nan a zancensa sai kankalin kowa ya dugunzuma aka yi shiru ana tunani da zullumi. Daga can sai Sarki Huraisu ya dago kai ya dubi boka Kirishna cikin tsananin mamaki ya ce, "To yanzu ta ya ya ke nan za mu ga jarumi Imran har mu nemi taimakonsa alhalin bamu san inda zamu je mu ganshi ba. Sannan kuma abu ne mawuyaci mu iya kiyaye jarrabawar da zai yi mana?" Koda jin wannan batu sai boka Kirishna yai ajiyar zuciya sannan ya ce, "Akwai hanyar da za a bi a tafi farautar jarumi. Hanyar ita ce kowanne Sarki da yake nan ya yi tunani a cikin mutanensa ya zabo mutane hudu wadanda ya yarda da jarumtakarsu da AA Misau ke Magana kuma gaskiyarsu dole ne ya zamana cewa akwai mace guda daya a cikinsu. Bayan kowanne Sarki ya kawo mutane hudu sai a hada mutanen duka a, sake rabasu izuwa kaso hudu. Kason farko su nufi gabas su shiga duniya farautar. jarumi Imran, kaso na biyu su nufi yamma, kaso na uku su yi kudu, su kuma kaso na hudu su nufi arewa. Babu shakka kafin shekara ta zagayo sai daya daga cikin wadannan rukuni hudu sun hadu da jarumi Imran sun gabatar masa da bukatarmu. Idan har suka ci jarrabawarsa lallai zai taimaka mana ya fitar damu daga cikin wannan mummunan tashin hankali. Wannan shi ne iyakar taimakon da ni boka Kirishna zan iya yi à matsayina na bokan da babu kamarsa a doron kasa. Sauran aiki kuma ya rage a garcku yaku wadannan sarakuna. Wannan shi ne furucina na karshe a gareku kumna ba za ku sake. ganina ba ko jin muryata sai bayan na samí nasara bisa abinda za a tafi nema. Koda gama wannan jawabi sai boka Kirishna ya bace bat daga cikin dakin taron tamkar bai taba Wanzuvwa ba. Al'amarin daya kara dugunzuma hankalin sarakan ke nan kuma suka kamu da tsananin al'ajabin duk abubuwan da boka Kirishna ya zaiyanc. Sai da aka sami lokaci mai dan tsawo dayansu bai ce uffan ba daga can sai Sarki Huraisu ya koma kan karagar maulki ya zauna ya kawo gwauron numfashı ya ajiye kuma ya dubi gaba dayan surakunan da ke cikin fadar ya ce, '"Ya ku yan uwana srrakei ku yi sani cewa yau D na dada tabbatar da karin maganar nan wacce masu iya magana ke cewa; "Komai nisan gari akwai wani gari a gabansa" Ban taba zaton cewa a halin yanzu akwai wani boka mai đaraja ba wanda yafi su Sarki Imras karfin sihirin tsafi ba sai yanzu. Shawarar da zan bamu ita ce, lallai mu yi amfani da wannan umarni wanda boka Kirishna ya yi mana. Yanzu na sallami kowa ku je ku zauna ku yi tunanin mutum hudun da za ku zabo daga cikin mutancnku wadanda za su yi wannan gagarumar taliya domin bamu da wani zabi wanda yafi mu yi hakan." Koda Sarki Huraisu yazo nana zancensa sai gaba đayan Sarakunan jikinsu ya yi sanyi suka kasa cewa komai kuma suka kasa mikewa tsaye domin su tafi. Daga can sai Sarki Jamal ibini Ihisar ya numfasa va dubi Sarki Huraisu cikin nutsuwa ya ce, "Ya kai wannan'Sarki mai daraja ka yi sani cewa shekara guda fa ba kwanaki kadanbane. Shin baka zaton cewa kafin mu ga jarumni Imran gaba dayanmu zanmu iya rasa dukkanin 'ya'yayenmu? Ka ga ke nan idan hakan za ta iya faruwa tafiya neman jarumi Imran bata da wani amfani.." Kafin Sarki Huraisu ya baiwa Sarki Jamal amsa sai Sarki Imras yai sauri ya tari numfashinsa ya ce, "Ai koda mun rasa 'ya'yanmu gaba Gaya dole ne muyi iya kokarimu wajen dakatar da wennan masifa tunda bamu san saadda karshenta zai zo ba ko don saboda mu tsirar da iyalannu da jama'armu daga cikin tashin hankali da fargabar da suke ciki". Dajin haka sai gaba dayan sarakunan suka kama hayaniva kowa na fadin cewa, "Ya amince da wannan shawara ta Sarki Imras." Nn take fadar ta watse aka bar Sarki Imnras da Sarki Hurainu su biyu rrak a zaune cikin tagumi da Tunani Sai da suka shafe kusan dakika dari da ashirin a zaune dayansu bai ce uflan ba sannan yai ajiyar zuciya ya dubi Sarki Huraisu y. ce, "Hakika gaba da gabanta aljani ya take wuta. Ya kai bokina yanzu ashe akwai Goyayyen mashahurin boka a duniya kamar Kirishna amma bak sani ba? To wai shin ma mene ne dalilin da ya hana boka Kirishna neman wannan silin sibirin gashi da ke jikin Sarki furaisu dan vvana tunda yana da karfin sihiin da kai baka da shi" Kodajin wannan batu sai Sarki Imras yai ajiya numfashi ya ce "Ya kai abokina ka yi sani cewa kamar yadda kaima ka yi mamakin wannan al'amari haka inma na yi, to amma ni yanzu tashin hankalin da muke ciki yasa ma ban damu da batunsa ba. Ina mai sanar da kai cewa ina matukar son dana yarima Hasnalu fiye da komai a wannan duniya, da dai mutuwa ta daukeshi gwara ni ta fara daukata". Sa'adda Sarki Huraisu yaji wannan batu sai ya cika. da tsananin mamaki ya ce, "Ya kai abokina ai ya'yanka guda biyu ne me yasa ban ji kayi batun 'yarsa Lushaira ba?" Koda jin haka sai fuskar Sarki Imras ta sauya yanayi izuwa tsananin fishi ya ce, "Ai kaima ka san cewa har abada ba zan taba son Lushaira ba musamman da kamanninta suka zo iri daya sak da na yar uwata Husnaila. Har abada ba zan taba kaunarta ba musamman idan na tuno da iin tsantsar kiyayyar da ta nuna mini ta guje ta bi Sarki Muraisu izuwa cikin dajin Kirzufa har ta aureshi suka haife mana jaraba a yanzu. Ina tabbatar maka da cewa inda zan sami ikon ganin Husnaila a fili yanzu nan da nan take zan sareta da hannuna." Koda jin wannan batu sai Sarki Huraisu yaja dogon numfashi ya ce, "Ya kai abokina ka yi sani cewa kai bacin rai ne ya saka duk kake wannan batu amma ina so ka gane cewa ni fa na fika shiga cikin tsananin tashin hankali. Abu na farko shi ne, a halin yanzu 'yata gimbiya Husnaila ba ta san yadda aka yi na sami wannan mulki AA Misau ke Magana ba duk ranar da ta sani na san za ta tsaneni ne ta kawar da 'duk kaunár da ke tsakanina da Ita Abu na biyu kuma shine duk ranar da wannan yaro ya gama busa kahon busa a imutu to babu inda zai dürfafa fa cẻ nan birnina domin yazó ya kasheni ya karbi mulkin mahaifinsa. Bani dawanda zai iya kareni face Suzaila, idan ta ji abinda ke tsakahina da mahaifinsa kuwa ba za ta taimakeni ba taje ta ciro wannan gashin sihiri da ke wajenkaa cikin kwalba a ajiye ta bani ba. Wai shin ma har yanzu kaima baka sami damar ciro gashin bane? Ina fatan dai ka yiwa wannan Kwalba cikkaken adani Lokacin da Imras yaji wannan tambaya sail ya takarkane ya bushe da dariyar mugunta sannan ya hade faska ya dubi Sarki Huraisu ya ce, "Shin ka ta6a ganin wanda ya yi wasa da rayuwarsa? To ka sani cowa na dauki wannan gashin sihiri tarnkarishi ne ruhina a cikin wannan abu. yadda nake bashí tsaro da kulawa, bana bảiwa raina da: lafiyata Waishin kaima na tarmbaycka mana, me yasa har yanzu baka labartawa gimbiya Husnaila labarin wannan gashin sihiri bạ da ke wajena domin taje ta fiddo maka shi ta ceci rayuwarka tunda bokaye. sun gaya maka cewa ita ce kadai za ta iya ciro gashin?" Koda jin wannan tambaya sai shima Sarki Huraisu ya kyalkyale da dariya tarmkar babu wani abu da yake damunsa a rayuwa. Lokaci guda kuma ya hade fuskarsa ya ce, "lHaba ya kai abokina shịn ka manta ne cewa ni da kai KAR TA SAN KAR. Ana sani cewa yadda nake mutuwar Son wannan gašhin sihiri domin na cika babban burina nà duniya kaima kake sonsa don haka bazaka ta6a yarda ba na mallakeshi. Abu na biyu kuma ai idan na nunawa 'yata Husnaila muhimmancin wannan gashin sihiri zan jefata cikin tunani da wasi-wasi wanda zai sa ta tayi bincike har ta gano sirin da na boye ma ta tsawon "shekaru. Ni yanzu abinda nake so da kai shi ne, mu ajiye maganar gashin sihiri a gefe guda mu tunkaru wannan babbar masifa da kegabanmu". Kafin Sarki Huraisu ya gama rufe bakinsa tuni karar kahon BUSAA MUTU ta cika birnin gaba daya. Al'amarin da ya haddasa girgizar kasa, nan take Sarki Huraisu da Sarki Imras suka zube kasa suna masu yin rub da ciki cikin tsananin razana da đimaucewa. Gaba daya birnin sai da ya hautsine, gidaje suka rinka rushewa. Gaba daya birnin sai da ya hautsine, gidaje suka rinka rushewa suna zubewa A kasa Ba a sami nutsuwa da kwanciyar hankali ba sai bayan shudawar sa'a guda da faruwar al'anmarin Asanman ne wani Sarki bokansa da ya baro can wacce ya tafi ya barta a Kwance ya sami sako daga birnin cewar babbar 'yarsa wance babu Iafiya ta mutu Wani tsutsun tsefi ne ya kavo wannan sako a rubuce a ci'kin wasika. Kode Sarki Raukib ya karanta Wannan wasika sai ya fashe da matsanancin kuka na bakin ciki Nan take ya kama kiran sunan 'yarsa yana begonta kuma yana ihu áa guje-guje tamkar nahaukaci sahon shiga. Koda sauran Sarakunan suka ga halin da Sarki Raukib ya shiga sai duk suka kamu da tsananin Tausayinsa wasu suka tayashi kukan bakin ciki, wasu kuwa sai tai ka ga kawai idanunsa Sun kada sun yi jawur saboda fishi da takaici. Koda aka fahimci. cewar idan aka kyale Sarki yaci gaba da wannn kuka da sambatu zai iya haukacewa sai aka yi sauri aka kamashi aka shigar da shi cikin gidan gidan sarautar aka kaishi har cikin masaukin a aka bashi giya mai dadi da banju ya sha.... Zan dakata A saikuma wani lokaci idan Allah ya kaimu Dafatan Kuna lafiya AA Misau ke Magana Domin shiga WhatsApp group dinmu danna blue din rubutun nan Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QBUSA A MUTU Littafi Na Biyar (5) Part B Na Abdulaziz Sani M Gino AA Misau Ke Magana Ina yima Daukacin jama ar wannan gida barka da wannan lokaci tare da fatan Alkhairi YA YI TATIL, NAN TAKE BARCI MAI NAUYI YA SACESHI BAI SAni . AL'AMARIN yarima Hasnalu kuwa, tun bayan ganawar da ya yi da gimbiya Husnaila a cikin lambu ta kafa masa sharadi na cewar sai yaje dajin Kirzufa ya kamo yaro mai kahon busa a mutu ya zo da shi sannan za ta karbi soyayyarsa- sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi a duniya duk da cewa ya yi alkawari a cikin zuciyarsa cewar ya yarda ya rasa rayuwarsa a kokarin cika wannan buri. Cikin shigar yaki yarima Hasnalu ya shiga gidan sarautar bangaren da aka bashi masauki. Duk inda ya wuce sai ya ga dakarun gidan suna risinawa suna gaisheshi cikin girmamawa saboda matsayinsa. Haka dai ya ci gaba da tafiya har ya isa cikin dakin da aka bashi. Koda ya tura kofar ya shiga ya yi arba da wanda ke ciki sai ya cika da tsananin mamaki. Ba wata bace zaune a cikin dakin face 'yar uwarsa gimbiya Lushaira. Hasnalu ya tura kofar ta rufe sannan ya dubi Lushaira ya ce, "Ya ke 'yar uwata mene ne ya kawoki nan dakina har kika zauna ina jiran dawowata?" Koda jin wannan tambaya sai Lushaira ta dubi Hasnalu a cikin alamun tausayawa ta mike tsaye ta kama hannunsa ta zaunar da shi suka fuskanci juna Sannan ta dubeshi cikin nutsuwa ta ce, "Ya kai dan uwana ka yi sani cewa duk abinda ya dancka ai nima ya dameni. Ka gafarceni na yi maka laifi domin dđazu sa'adda ka tafi lambu domin ka gana da gimbiya Husnaila na bika a baya baka sani bã, kuma na labe na saurari duk irin hirar da kuka yi inda a karshe ta kafa maka sharadin sai ka yi gagarumar jarumtaka wacce tafi wadda tayi kuma ka shiga dajin Kirzufa ka karno mai kahon BUSA A MUTU sannan za ta aurcka. Ina mai tabbatar maka da cewa duk wuya duk rintsi sai ka ci wannan jarrabawa da ta baka kuna sai ka cika burinka ka mallaketa". Koda jin wannan batu sai yarima Hasnalu ya cika da mamaki ya ce, Haba ya ke 'yar uwata kada ki zama 'yar abi yarima a sha kida mana. Ni kaina da na kudurce a zuciyata da zahiri cewar zan iya cika wannan sharadi ai na san cewa abu ne wanda ba zai taba yiyuwa ba, kawai dai na gwammace na rasa rayuwata da dai na dawo gida ba tare da na cika ka'idar da masoyiyata ta gindaya mini ba. Ina so ki sani cewa na kamu da tsananin son gimbiya Husnaila irin son da in ban mallaketa ba bakin ciki ne zai zamo ajalina". Koda hasnalu yazo nan a Zancensa sai idanunsa suka ciko da kwallah har hawaye ya zubo masa. Al'amarin da ya sa zuciyar Lushaita ta karaya kenan Ta sake kamuwa da tsananin tausayinsa ta rungumeshi a loakcin da itama hawaye ya fara sartu akan kyawawan kumatunta ta ce, "Ka kwantar da hankalinka ya kai dan uwaná na yí malka alkawarin zan taimakeka ta kowanne hali har burinka ya cika." Koda jin wannan batu sai yarima Hasnalu ya janye jikinsa daga cikin na ta suka sake fuskantar juna sannan ya share hawaycnsa ya ce, "Haba ya yar uwata ta ya ya zan iya cika wannan buri nawa alhalin ban kasance jarumi ba?" Lushaira ta ce, Ai ba jarumtaka ba ce take baiwa mutum komai ba. Akwai sa'a da rabo a rayuwa wadanda za su iya kai mutum matsayin da bai taba tsammani ba. Ni na san hanyar da zan bi na taimakeka ka cika sharadin da gimbiya Husnaila ta gindaya maka. Abinda nake bukata da kai kawai shi ne, ka kara hakuri domin komai yana da lokacinsa sannan kuma ina son ka yi kokari ka sarrafa zuciyarka akan yawan begen gimbiya Husnaila. Ma'ana ka tursasa zuciyar taka ta danne soyayyar don gudun kada ciwon So ya jefaka a cikin mugun hali" Koda gama fadin hakan sai gimbiya Luzaila ta mike tsaye ta fice daga cikin daki gabadaya Hasnalu na zaune yana mai binta da kallo cikin tsananin Mamakin yadda za ta iya tainakosa har ya mallaki gimbiya Husnaila wanda shi a ganınsa inda duniya zata taru tayi masa agaji ba za a iya cika wannan buri ba AL'AMARIN gimbiya sulaiza kuwa, bayan ta rabu da yarima Hasnalu sai ta wuce kai tsaye izuwa Turakar mahaifiyarta Sabirat. Tana siiga cikin turakar ta iske Sarki Huraioa tare da Sabsrat a zaUne suna tatfauun wa. Kallo daya ta yi musu ta fuskanci cewar suna cikin matukar damuwa domin akan fuskokinsu ta ga damuwar karara. Suzaila ta karasa gabansu da sauri sannan ta zauna a gefe daya tana mai fuskantarsu ta dubi Sarkı Huraisu cilkin damuwa ta ce, "Ya kai Abbana wacce irin shawar a kuka yanke yanzu kai da sauran Sarakuna bisa wannaa matsala da kc gabanmu?" Koda jin wannan batu sai Sarki Huraisu ya yi ajiyar zuciya sanann ya kwashe labarin duk abinda ya faru a faia ya zaiyane sna ta har da batun bakon boka Kirishna kuma mafitar da ya kawo Koda jin wannan batu sai gimbiya Süzaila ta cika da tsananin murna ta ce, "Ya kai Abbana ka yi sani cewa iin wannan dama nake nema a rayuwata wacce zan yi gagarumar tafiya ta yin abin al'ajabi wanda in na yi shi zan bar abin tarihi wanda ba za a taba mantawa da shi ba har bayan raina. Ba zan yabi kaina bả tunda an ce yabon kai jahilci amma kai kanka ka san cewa nacancanta ka zabeni a cikin mutum hudu da za ka ware a cikin mutanenka wadanda za su yi wannan tafiya tunda ina da jarumtaka, ina da amana dai-dai gwargwado haka kuma ina da tausayi da kamanta gaskiya." Lokacin da Suzaila ta zo nan a zancenta sai hankalin Sarki Huraisu ya dugunzuma ainun ya dubi Suzaila cikin tsananin damuwa ya.ce, "Ya ke 'yata kin sani cewa ke kadai gareni a duniya don haka bana son ki yi nisa da ni kuma bana son rayuwarki ta shiga cikin hadari. Kin ga kuwa wannan tafiya da za a yi itace tafiya mafi hadari da za ki yi a rayuwarka domin jarumtakarki ba za ta ceci rayuwarki ba tunda karshen tafiyar za a durfafi dajin Kirzufa ne bay an kun sadu da jarumi Imran ya aminta da ku ya yi muku jagora." Suzaila ta kyalkyale da dariya ta ce, "Ya kai Abbana ka yi sani cewa a rayuwata yanzu babu mahalukin da yake burgeni sama da jaurmi. Yanzu da naji labarin wannan sadauki mai suna Imran kuma na ji

Chapter 1 of 4