Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
musu bayanin sallama sai gimbiya Suzaila ta rugo gareshi suka rungume juna a lokacin da hawaye ke zubo ma ta ta ce, "Ka gafarceni ya kai Abbana ka yi sani cewa ban ta ba nisanta da kai ba sai wannan lokaci kuma ba don ina so kana so zamnu rabu ba sai domin wannan tafiya ta zama wajibi tunda ita ce ruhin ceton rayuwar dukkanin jama'ar da ke wannan nahiya tamu." Sarki Huraisu ya numfasa a lokacin da shima hawaye ya zubo masa ya ce, "Tabbas magan arka gaskiya ce, shin yanzu kin yi sallama da mahai fiyarki?" Suzaila ta ce, "Na yi sallama da ita amma yanzu haka ma tana nan a can kofar fadar nan a tsaye tana jiran ta ga fitowarmu" A can 6angaren Sarki Imras kuwa, bayan an sallami matafiyan sun fara kokarin fita daga cikin fadar sai Sarki Imras ya kwalawa yarima Husnalu kira shi kadai ba tAre da ya kirawo gimbiya Lushaira ba.... Nima kuma rashin jin ya kirani yasa zan dakata anan saikuma wani lokaci AA Misau ke magana Dafatan kuna nan cikin koshin lafiya Domin shiga whtsap group dinmu ga link nan a kasa 👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QBUSA A MUTU Littafi Na Biyar (5) Part D Na Abdulaziz Sani M Gini AA Misau ke Magana Barkanmu Da wannan lokaci dafatan kuna lafiya ya ku Jama'ar wannann gida ina muku fatan Alkhairi A lokacin Liushaira na tsaye daf da Hasnalu. Koda Hasnalu yaji Sarki bai kira 'yar uwarsa ba sai shi kadai sai kawai ya kamo hannun Lushaira ya ja ta da gudu suka nufi inda Sarki Imras ke tsaye Hasnalu ya yi hal:an ne don kada mutane su gano cewa akwai wata matsala tsakanin gimbiya Lushaira da mabaifinta. itama Lushaira sai ta tafi ga Sarki Imras cikin tsananin farin ciki suka rungumeshi gaba daya. Koda Sarki Imras ya ji Lushaira a jikinsa sai ransa ya baci, duk maganganun da yake son ya gayawa Hasnalu sai ya fasa. Haka dai ya yi musu bankwana ba a yadda yake so ba kuma ya rakosu har kofar fada. Anan ne su gimbiya Suzaila suka riski sauran abckan tafiyarsu a tsaitsaye bisa Rakumà da Dawakai kuma ga guzuri mai yawan gaske a tanada akan Rakumai kuma kowanne Basarake da Kuyanginsa guda goma sanye da tufafi mai launin tutar birninsu suma duk suna bisu kan Rakuna. Ba tare da bata lokaci ba aka hau kan dawakai sannan aka kama hanya aka fice daga cikin birnin Lairuf. Sarki Imras da Sarki Huraisu na Lsaye a kofar gidan sarautar suna hangen 'ya'yayensu har sai da suka 6ace musu da gani sannan Sarki Imras yai ajiyar zuciya ya dubi Sarki Huraisu ya ce, "Ya kai abokina ka yi sani cewa wannan ita ce damarmu ta biyun karshe wacce zamu iya ganin bayan makiyanmu amma idan har su gimbiya Suzaila basu hadu da sadauki Imran ba ya basu hadin kai anje dajin Kirzufa an kashe 'yar uwata Husnaila da danta Muraisu to muna cikin GABA TSINI, BAYA SIYAKI." Koda jin wannan batu sai Sarki Huraisu ya numfasa ya ce, "Hakika na yarda da wannan bayani naka to amma kai yanzu me ka gani a cikin bincikenka bisa wannan tafiya amma kuma na ga wani mummunan tashin hankali wanda zai biyo bayan nasarar da aka samu. Babu kokarin da ban yi ba akan na gano kowanne irin tashin hankaline amma na kasa. Abin da ya sa ban damu ba shi ne, koma wane irin tashin hankali ne in dai mun kawar da Muraisu da Husnaila ai mai sauki ne tunda fargabarsa ba ta kai tasu ba a garemu, " Koda jin haka sai Sarki Huraisu ya bushe da dariyar farin ciki sannan ya ce, "Hakika ka zo da magana mafi kyau da kwanciyar hankali a gareni. Yanzu zamu zuba ido daga nan zuwa tsawon shekara guda mu ga abinda zai biyo baya. Wai shin ina son na tambayeka, mcne ne dalilin da ya sa ka tura 'ya'yanka duk su biyun izuwa wannan tafiya mnai hadarin gaske alhalin su kadai gareka? Baka tsoron ka rasasu gaba daya?" Lokacin da Sarki Imras yaji wannan tambaya sai ya yi murmushi ya ce, "Dalilin da ya sa ka bar yarka gimbiya Suzaila ta yi wannan tafiya shi ne yasa nima na bar 'ya'yana suka tafi saboda bana son su gano wani babban sirri da ke boye a karkashin rayuwata. Yanzu wane irin hukunci ya kamata mu yankewa Sarki Jamal bisa laifin munafuntarmu gami da hada kai da sauran sarakai don gudanar da abinda suka ga dama ba tare da saninmu ba?" Sarki Huraisu ya numfasa kuma ya dubi Sarki Imras ido da ido ya ce, "Abokina ka sani cewa a nahiyar nan gaba daya mun fi dukkan sarakunan nan karfin mnulki, arziki da daukaka, saboda haka bai kamata ace wasu Sarakai suna kawo mana matsala ba a cikin harkokinmu. Ina mai tabbatar maka da cewa koda bayan mun kawar da wannan matsala wace ta addabemu Sarki Jamal ba zai daina yi mana zagon kasa ba saboda haka kamata ya yi mu kawar da shi daga kan doron kasa gaba daya , kuma mu shiga kasar tasa na Zabi wanda muke so ya ci gaba da tafiyar da mu." Koda jin wannan batu sai Sarki imras ya hushe da dariyar mugunta ya ce, "Da kyau abokina ka cika abokin tafiya domin hazakarka da tunaninka duk iri daya ne da nawa. Wannan shi ne abında ya firu a birnin Lairuf bayan an zabi Dakarun da za su tafi neman jarumi Imran sadaukin da aka tabbalar da cewa shi kadai ne zai zai shiga dajin Kirzufa ya kamo yaro mai kahon BUSA A MUTU ko kuma ya kashe shi domin a huta da fergabar mutuwar 'ya'yan Sarakai. AL'AMARIN Su gimtya Suzaila kuwa, lokecin da suka yi dan nisa ga barin cikin birnin Lairuf sai suka rabu izuwa kaso hudu, wato runduna hudu, kowacce runduna akwai shugabanta amma bisa akasi sai ya zamana cewa yarima Hasnalu da 'yar uwarsa duk suna cikin rundunar gimbiya Suwzaila. Ba wai wani ne ya raba ayarin gaba daya ba da hanunsa, kacici-kacici aka yi, duk rundunar da mutum ya fada a lokacin da ake kacici-kacicin kawai shi ke nan babu canji. AA Misau ke magana Hakika gimbiya Suzaika tayi matukar bakin Ciki da ya zamana cewa su yarimaHasnalu sun fado cikin rundunarta amma da yake babu yadda za ta yi sai ta hakura. Nan take rundunar su Suzaila ta nufi yammaci, sauran rundunonin kuma suka kasu gida uku, gabas, kudu da arewa . Sai da su gimbiya Suzaila suka shafe yini guda suna tafiya basu yada zango ba, sai dai shan ruwa da cin abinci ne kadai ke tsayar da su. Duk tsawon wannan tafiya duk sa'adda Suzaila ta waigo baya sai ta ga Hasnalu ya kura ma ta idanu yana murmushi, al'amarin da ya fusatata ke nan ainun ta ji ma ta tsaneshi gaba daya a rayuwarta kuma ta kudurce a ranta cewar komai daren-dadewa sai ta taka masa birki kuma ta cire masa soyayyarta daga cikin zuciyarsa. Daf da magariba ne suka iso bakin wata korama. Kawai sai gimbiya Suzaila ta bayar. da umarnin a tsaya a wajena yada zango. Cikin tsananin farin ciki kowa ya sauko daga kan abin hawansa aka daure dawakai da rakuma suma aka basu abinci da ruwan sha, sannan aka shiga kafa tantuna. Gimbiya Husnaila na ta tantin dabam, tare da kuyanginta suna yi ma ta hidima. Haka ma yarima Hasnalu shima nasa tantin dabam kamar yadda gimbiya Suzaila ma ta shiga cikin na ta tantin kuyanginta suka yi ma ta wanka, sannan ta kwanta akan shimfida mai taushi tana hutawa. A dai-dai wannan lokaci ne ta fara gyan-gyadı saboda 'yar gajiyar da ke jikinta. Daga can kuma sai barci ya saccta gaba daya. Faruwar hakan ke da wuya sai ga gimbiya Lushaira ta shigo cikin tantin. Koda ganinta sai gaba dayan kuyangin na Suzaila suka risina a gareta suka kwashi gaisuwa. A dai-dai wannan lokaci ne gimbiya Suzaila ta fara sumbatun mafarki. Koda jin haka sai Lushaira ta dubi kuyangin gaba dayansu ta yi musu inkiya da su fice daga cikin Tantin. Lushaira ta je daf da gimbiya Suzaila ta zauna kuma ta kura ma ta idanu tana mai sauraron sumbatun da take yi. Kawai sai taji tana ta jero kalmomin soyayya ga wani jarumin saurayi har take siffanta kyawunsa. A cikin siffantashi ne Lushaira ta gane cewa ba kowa bane wannan saurayi face sadauki Imran wanda suka fito farautarsa. Koda fahimtar haka sai hankalin Lushaira ya dugunzuma ainun, take tausayin dan uwanta Hasnalu ya turuketa saboda ta gane cewa SON MASO WANI yake yi, wato KOSHIN WAHALA. Abinda ya daure ma ta kai shi he, ya ya Suzaila za ta fara soyàyya da muturnin da ba ta ta6a ganinsa a'zahiri ba? Kamar an ce da Suzaila tashi sai ta farka a firgice tana mai kiran sunan sadauki Imran a fili karara. Koda ta bude idanủnta ta ga gimbiya Lushaira zauhe a gabanta tana yi ma ta murmushi sai kunya ta kamata sannah ta dubi ko ina a cikin tantin ta ga babu ko mace daya daga cikin kuyanginta sai ta dubi Lushaira cikin mamaki ta ce, "Ina kuyangina suke, kuma nene ne ya kawoki nan cikin tantina?" Sa'adda Lushaira taji wadannah tambayoyi sai ta 'sake yin mufmushi ga Suzaila ta ce, "Ya ke waninan yar Sarki jarumar jarumai ki yi sani cewa ba komai ne ya kawoni nan cikin tántinki ba sai domin BA Remi wata alfarnma guda daya a wajenki. Dangane da kuyanginki kuwa ni ce na sallamesu gabi dayansu saboda na shigo na iskeki kina sumbatu na soyayya a cikin mafarkin na ki, kuma abin kụnya ne kuyanginki su rinka jin ki kina yin hakan". Koda jin wannan batu sai Suzaila ta kamu da tsananin kunyar Lushaira ta sunkui da kanta kas kuma hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa, abinda ke ma ta dadi. Daga can sai ta dago kante ohankali s ta dubi Lushaira ta ce, "Wane irin sambatu kika ji ALina yi a cikin barcina?"e asvot r s as Lushaira ta ce, "Na ji kina anbaton sunan 6 sadauki Imran kuma kina ta zaiyana masa kalrno in Hisoyayya tarmkar kun shafe shekar: a tare, kuina kamar baki da warni masoyi wanda ya fishi a. doron 8t aves Ya ke Suzaila kina nufin ke nan: kin kamu da 8 tsananin son sadauki Imran tun gabannin ki ganshi a zahiri? Kada ki 6oye mini komai tunda ciwon ya mace na mace ne?"" st ấees n siie Kodajin wannan bata sai jikin gimbiya Suzaila ya yi sanyi ta dubi Lushaira a cikin nutsuwa ta ce, a "Ya ke kawata ki yi sani cewa tun daga ranar da na fara jin labarin sadauki Imran na ji na kamu da tsananin sonsa da begensa saboda ni a rayuwata ina son jarumin da ya fini jaruntaka saboda shi kadai ne mutumin da zai iya burgeni nà amsn tas Haka kuma ina son mutumin da ya.fini kyau, kuma ina son mutumin da zai iya yin abinda ni ba bazan iya ba"'. Koda jin wannan batu sai gimbiya Lushaira tayi murmushi ta ce, "Ban ga laifinki ba domin ni na son AA Misau ke magana mutum mai ra'ayin kansa, kuma mại magana daya. Amma ina son na baki wata shawara guda daya. Shawarar kuwa ita ce, idan za ki so mutum kawai ki soshi don son da zuciyarki ke yi masa da kuma gamsuwa da shi a ranki, amma ba don kyansa ko jarumtakarsa ba, saboda shi kyau yana iya disashewa sakamakon tsufa ko sauyin rayuwa. Haka kuma jaruntaka tana yankewa sakamakon tsufa ko larura. Alfarmar da na' zo nema a wajenki kuwa ita ce, ina son kada ki kyahaci dan uwana Hasnalu a cikin wannan tafiya kuma, kada ki wulakantashi saboda ni na san cewa ya kamụ da tsananin kaunarki, idan kika juya masa baya z ki iya jefa rayuwarsa cikin mummunan hali. A takaice dai abinda nake rokonki anan shi ne, koda dai ba za ki nuna masa so ba, kuma ba ża ki karbi soyayyarsa ba to kada ki wulakantashi. Lallai ina mutuwar son dan uwana Hasnalu fiye da yadda ma nake son kaina, idan kika gur6ata rayuwarsa har abada ba zan iya yafe miki ba, Da wannan furuci nakc yi miki sallama, sai da safe." Koda gama wannan furuci sai Lushaira ta mike tsayc ta fice daga cikin tantin gaba daya, ita kuwa Suzaila sai ta bita da kallo cikin tsananin mamaki tana juya al'amarin a cikin zuciyarta kawai. Kashe gari da sassafe kowa ya tashi daga barci aka kintsa sannan aka ci abinci. Bayan kowa ya koshi ne aka cire tantuna aka dora kaya akan Rakuma da Dawakai sannan aka ci gaba da tafiya. Sai da aka shafe kwanaki bakwai ana ratsa dazuzzuka iri-iri. Ba a riski wani gari ba kuma duk inda aka hadu da mugayen dabbobi ko 'yan fashi nan take ake yi musu rubdugu a kashe na kashewa, masu gudu su gudu saboda kasancewar jaruma Suzaila ce a kan gaba ko yaushe. Kwanci tashi, wannan runduna ta sami kwana arba'in da daya tana tafiya sannan suka hangi wani dan karamin kauye a gabansu da yammaci Sakaliya. Har sun yi nufin su shiga cikin kauyen a sannan sai kowa ya nuna cewar gwara dai a kafa sansani anan daji a huta izuwa wayewar gari in ya so a shiga kauyen da safe ido na ganin ido. ls Suzaila ce kadai ba ta yi amanna da wannan shawara ba ta ce, "Ya ya mu da mnuka shafe kwana arba'in da daya muna tafiya a cikin dazuzzuka yanzu kuma mun riski gari zaku ce mu yada zango a jeji? Ai gwara mu shiga cikin wannan kauye yanzu a wayi gari damu' Koda jin haka sai kowa ya yi caa! A kanta ana nuna rashin goyon baya, Yarima Hasnalu ne kadai ya goyi da bayanta, al'amarin da ya fusata ta ke nan ta hakura bisa dole tunda na rinjayesu su biyu. Nan take aka kafa tantuna aka yada za go aka fara shirye-shiryen abincin da za a ci. Ana cikin wannan hali ne aka hango wani mutum daga can nesa ya taho yana dogara sanda yana tafiya da kyar. Mutumin na rataye da kwari da baka, sannan fuskarsa gaba daya a cike take da gemu, kasumba da saje tamkar tsohon da ya Lanyanta a duniya amma da ya matso kusa da'su sai suka ga tabbas saurayi ne ga dukkan alamu dai wahalar duniya ce ta sa ya zama karnar tsoho. Rigar jikinsa ta tsufa 'ainun, har ta fara yayyagewa da kanta, sannan yana rike da wat tsohon Akushi a hannuisa kai ka ce shi ya yankewa Talauci cibiya. Gaba dayan a jikinsa babu wani abu wanda darajarsa za ta kai dinare daya face wani buzu na fatar rago da ke rataye a bayansa a daure. Wata kila dai buzun ne abin kwanciyarsa ko kuma abinda yake shimfidawa ya zauna. Ko takalmi babu a kafarsa, kuma da ganin kafar tasa ta sha wahalar duniya saboda yawan tafiya har dunduniyar ta tsattsage ta fara alamun faso. Kallo daya mutum zai yiwa wannan Almajiri ya san cewa duniya ba ta gabansa kuma idan mutum mai kyankyami ne ma ba ria iya 'zama a kusa da shi ba saboda tunanin zai iya vin warin gawasa. A galabaice mutumin ya durfafo ina su Suzaila yake yana tafe yana herfe kafafu kamayr zai fadi yana sassarfa sabada tsaaanin gajiya gami da yunwa da kishirwa. Tur daga nesa kowa ya kura masa idanunu, wasu na sai suka faie dora hannaye nasu akan kufen takobinsu saboda basu yarda da shi ba, jira suje kawai su ga ya yi wani motsi wanda basu yarda da shi ba su fsr masa. Idan ka dubi fuskar mutuninn baka iya shaida irin kamanninsa saboda yawan gashin da ya lullube fuska gaba deya idanunsa kaiai ake iya kalla a gano cewa bai kasance tsoho ba amma ba Za a iva banbancewa ba ya kasance muimuna ba ko kyakkyawa, kavwai dai ya kasan ce talaka kuma makiskanci wanda bashi a wani gata. Da shigowar wannan Almajiri cikin sansarin su gimbiya Suzailə sai ya fara bara yana mai cewa, "Wa zai taimakeni da ruwa koda mukurwa daya ce, waye zai taimakeni da abinci koda loma daya ne Ubangiji ya biyashi. Ya ku wadannan matafiya ku yi sani cewa yau kwana na bakwai kenan rabona da na ci ko na sha. Sai bilin-bituwa nake yi a cikin daji ni mafarauci ne Kumma ko Kwaro ban sanu ba," Koda jin wannan batu daga bakin Almajirin sai kowa ya bushe da dariya aka fara tunanin cewa lallai Waninan Almajiri mahaukaci ne ko kuna dai kwakwalwarsa ta tabu domin in ba wanda ya sami tabin kwakwalwa ba ya za ai ya ce Kwanansa bakwai bai ci ba kuma bai sha ba amma yana raye? Duk wanda Almajirin ýa dosa yana wannan bara sai ya kyareshi ko ya koreshi. Wasu ma suka rinka daga sanduna kamar za su koreshi. Gimbiya Lushaira ce kadai ba ta kyari Almajirin ba, kumna bata taimakeshi ba kawai dai ta kura masa idanu tana mai jin tausayinsa. Koda Almajirin yazo zai gifa ta gabanta yaga tana yi masa kallon tausayi kuma ta kura masa idanu cikin alamun tana yin wani nazari a kansa, sai ya yi sauri ya sunkui da kansa kas ya wuce ta gabanta ba tare da ya yi ma ta barar ba. Kawai sai ya koma can gefe daya nesa da su kadan ya zauna yana kallonsu kuma ya zuba ido ya ga ko idan sun gama dafa abincin da suke shiryawa Za su ji tausayinsa su san masa? Haka dai Almajirin ya ci gaba da sauraron tsammani yana ta faman zabga hamnaa gami da hadiyar miyau a duk sa'adda ya dubi abinci ya ga AA Misau ke magana yana za6al6ala a cikin katuwar tukunyar da kuyangi ke dafawa. Bai gushe ba a cikin wannan hali har tsawon rabin sa'a, sannan ne aka gama dafa abincin kuyangi suka shiga raba abincin ana baiwa kowa. Gimbiya Suzaila, Lushaira da yarima Hasnalu cikin tantinsu aka kai musu na su abincin, sauran dakaru, bayi da kuyangi kuwa kowa a bakin tantinsa ya zauna ya kama cin abincinsa yana zabga loma Suna kallon wannan Almajiri suna yi masa murmushi da dariyar mugunta. Wasu ma har daga battar ruwansu suke sama suna shan ruwa, ruwan na zubewa kasa a banza. Al'amarin da ya jefa wannan Almajiri cikin tsananin takaici da bakin ciki ke nan, amma sai ya ki tashi ya bar wajen ya shiga cikin wannan karamin kauye da ke gabansu domin ya yii bara. Haka dai Almajirin nan ya ci gaba da jiran tsammani ko wani daga cikin tawagar zai tausaya masa ya taimaka masa amma shiru ya zamana cewa kowa ya sude kwanonsa ko loma daya bai rage ba. Kai da dai Almajirin nan ya tabbatar da cewa wadannan matafiya basu da niyyar taimakonsa gashi kuma yunwa ta isheshi ainun sai ya mike tsaye da kyar ya zagaya bayan wani katon dutse. Sai da ya shafe lokaci mai dan tsawo sannan ya fito daga bayan dutsen ya dawo inda yake zaune ada. A sannan ne ya ga gaba dayan matafiyan sun shiga cikin tantinsu sun kwakkwanta domin su huta gajıyar tafiya, wasu daga cikin dakaru ne kadai a tsaitsaye suna gadi don tabbatar da tsaron sansanin. Koda ganin haka sai Almajirin ya kishingida a kasa kan kasa yana mai yin matashin kai da buzun da ke rataye a bayansa. Faruwar hakan ke da wuya kuwa sai barci ya saceshi mai nauyi. Kamar a mafarki sai wannan Almajiri ya ji ana tashinsa daga barci. A firgice ya farka ya mike zaune yana mai ambaton wata kalma. Kawai sai ya yi arba da gimbiya Lushaira tsugunnc a gabansa rike da akushin abincinta da kuma ruwa a cikin tulu. Kawai sai ta dubeshi cikin murmushi ta ce, "Ya kai wannan mafarauci tashi ka kar6i abinci da ruwa ka ci ka sha." Koda jin wannan batu sai Almajirin ya cika da tsananin mamaki ya dubeta ya ce, "Haba ya ke wannan 'yar Sarki sboda me za ki hana kanki ci da sha ki kawo mini alhalin ni ban kasance kowa ba lace Almajiri mai neman abinci?" Topah nima ganin wannan tausayi na GimbiyA lushaira yasa zan dakata anan saikuma wani lokaci idan Allah ya kaimu zamu ci gaba AA Misau ke magana Masu son shiga grp dinmu a whtsap ku danna wannan rubutun kasa 👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QBUSA A MUTU Littafi Na Biyar (5) Part E Na Abdulaziz Sani M Gini AA Misau ke Magana Jama A Barkanmu Da Wannan lokaci Yaudai Insha Allah Zamu Kammala littafi na 5 Sannan Mu shiga Na 6 A Gaba Koda jin 'wannan tambaya sai Lushaira ta cika da mamaki ta ce, "Kai kuwa ya ya aka yi Kasan ceWa ni 'yar sarkice?" Almajiin ya yi dan guntun murmushi a garela ya ce, "Haba, ai ido ba mudu bane armma ya san kima. Bisa ganin irin yanayin sutura dake jikinki kuma Yadda na ga kuyangi .na shiga cikin tantinki, haka kuma Dakaru suna tsaronki yasa na gane haka. Wai shin ma ke menene dalilinki na taimakona har kika ki cin abincin kika kawo mini?" Koda jin wannan tambaya sai lushaira tayi murniushi ta ce, "Ni ba zan baka amsAr tambayarka ba sai bavan ka gama cinye yannan abinci da na kawu maka ka sani nutsuwa". Koda jin haka sai almajri ya yi murmushi. Ba Tare da wata gardama va ya tsoma yan yatsunsa guda uku rak a cikin abincin ya yi loma uku rak sannan sai ya dauki ruwan tulun ya sha mukurwa uku Nan take ya yi gyatsa yana mai fadin wata kalımar dai wadda Lushaira ba ta taba ji ba. Kawai sai ya wanke hannunsa ya dubi Lushaira ya ce, "Ubangiji ya yi miki sakayya da alharinSa Ni kam na koshi kuma na gode bisa wannan taimako da kika yi mini," Cikin tsananin mamaki Lushaira ta dubi Almajirin ta ce, "Ya ya kai da ka kwana bakwai baka ci ba, baka sha ba, yanzu za ka ci loma uku kacal ka sha ruwa mukurwa uku kawai sannan ka ce ka koshi? Anya kuwa kai mutum ne? Ka gaya mini gaskiya ko kai aljani ne. Almajirin ya yi murmushi ya ce, "Tabbas ni mutum ne kamarki, kuma haka yanayin cin abincina yake. Idan zan ci sama da loma uku amai zan yi, domin zan yi cin haramun ne. Kuma inda zan sha ruwa mukurwa uku to da cikina zai kulle saboda bai saba da daukar ruwa sama da haka ba. Ya ke wannan 'yar Sarki ma'abociyar kyau da taimako, tunda har kin taimakeni nima kuwa zan taimakeki. Idan kuka shiga cikin wannan kauye da ke gabanku gobe da safe kada ki ci ko shan komai. Kada ki yarda ki zauna a ko ina face a cikin kasuwar kauyen. Kuma duk inda kike ki tabbatar da cewa kina tare da dukkan 'yan uwanki. Kuma suma. ki hanesu da duk abinda na haneki. Da wannan furuci nake miki sallama Ni zan Tashi na sake nauswa cikin dajin sai watarana idan muna da rabon sake haduwa Koda gama fadin haka sai almajirin mike tsaye yana mai dogara sandarsa Har ya juya yai gaba sai lushaira tace dakata Almajirin ya tsaya cak a jnda yake, Lushaira ta Shawo har gabansa Suka fuskançi juną sannan tace Dazu kayi mini tambaya ban,baka amsa ba saboda na ce sai ka gama cin abinci ka nutsu tukunna. Shis kana da, bukatar jin amsar tambayar taka? Almajrin ya girgiza kansa cikin murmushi: yan ce, "Ai yanzu kuma ubangijina, ya,nųna mini amsar wannan tambaya da Nayi miki Amsar kuwa itace kina da Tausayi da jin kai sabanin sauran abokan tafiyarki. ina mai yi miki albishir da cewa keçe kadai za ki samu abinda kika fito nema Koda gama fadin haka sai almajirin ya wuce abinsa izuwa cikin daji ba tare da ya sake waigowa ba ko sau daya Ita kuwa Lusihaira sai ta bishi da Kallo har ya bace mata ya zamana cewa almajirin ya 6ace 6at ta daina ganinsa. AA Misau ke Magana A sannan ne Lushaira ta mike tsaye ta shige cikin tantinta ta kwanta. Kashe gari da sassafe Lushaira ta shiga tantin d'an uwanta yarima Hasnalu ta shaida masa cewa kada ya kuskura ya ci ko ya sha wani abu a cikin wannan kauye da za su shiga. Kuma kada ya zauna a ko ina sai a kasuwa. Bayan haka, duk inda yake ya tabbatar da cewa yana tare da 'yan uwansa. Koda jin wannan batu sai Hasnalu ya cika da tsananin mamaki, ya ce, '"Ya ke 'yar uwata ke kuwa mene ne dalilnki an fada min wannan batu?" Nan take Lushaira ta zaiyane masa duk abinda ya faru tsakaninta da wannan Almajiri a jiya da daddare. Koda jin haka sai yarima Hasnalu yai shiru yana tunani da nazari a cikin zuciyarsa har izuwa lokaci mai dan tsawo. Daga can sai ya mike tsaye zumbur! Ya dubi Lushaira ya ce, "Yanzu ina shi Almajirin yake?" Lushaira ta ce, "Ai tun a jiya da daddaren da ya gama cin abincin ya yi mini sallama ya tafi". Cikin tsananin damuwa Hasnalu ya ce, "Shin kin tambayeshi sunansa, kuma ya gaya miki inda ya dosa daga nan?" Lushaira ta gyada kai ta ce, "Ban tambayeshi komai ba, amma ni kaina na yi matukar mamaki bisa al'amarinsa da kuma wadannan kalmomi da naji suna fita daga bakinsa masu yanayi da na irin ma'abota adinin Musslunci". Koda jiin hake sai hankalin Hasnalu ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe ya ce"Ya yar Uwata ki yi sani cewa kin yi babban kuskure da baki tambayi .wannan Almajiri sunansa ba da inda yake nifa Ina tabbatar miki da cewa wannan AImjiri shi ne jarumi Imran wanda muka fito nema, jarumin da si kadai ne zai íya zuwa dajin Kirzufa ya yaki mai kahon BUSA À MUTU yayii Galaba a kansa ya yı rnana magann wannan masifa da ta addabenu" Koda jin wannan batu sai itama Lushaira hankalinta ya dugunzuma ainun itama ta mike zumbur! Ta fice da gudu daga cikin tantin, shima Hasnalu sai ya bita da sauri, duk su biyun suka ruga izuwa cikin daji suna nemnan Almajirin. Sai da suka yi gabas da yamına, kudu da arewa suna dube-dube anma ko duriyar Almajirin basu gani ba. Bisa dole suka hakura suka koma can sansaninsu inda suka iske tuni kowa ya gama kimitsawa za a shiga wannan karamin kauye su kawai ake jira. AA Misau ke Magana Tun daga nesa suka hango jaruma Suzaila bisa dokinta ta kura musu idanu tana sauraren isowarsu. Suna isowa daf da ita sai tå dubesu cikin alamun danuwa ta ce, "Ina ku ka tafi muna ta nemankü oamu ganku ba?" A wannan lokaci gaba dayan abokan tafiyar na tsaitsaye suna kallon Hasnalu da Lushaira suna saurarOn amsar da za su bayar. Cikin nutsuwa Hasnalu ya kwashe labarin duk abinda ya faru tsakanin Almajirin nan da Lushaira har izuwa lokacin da ya yi tafiyarsa. Koda jin wannan batu sai ran jaruma Suzala ya 6aci, itama hankalinta ya dugunzuma ainun ta dubi Lushaira da Hasnalu cikin fishi ta ce, "Tabbas kun yi mana sakaki, na ji a jikina cewar wannan Almajiri shi ne jarumi IMRAN wanda muka

Chapter 3 of 4