Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
cewar har ma ya fi mai kahon BUSA A MUTU jarumtaka sai naji babu abinda nakeso sama da na yi arba da shi kuma na gwada jarumtata akan tasa, maimakon na fara jarrabawa akan nai kahon Busa a mutu." Koda Sarki Huraisu da Sabirat suka ji wannan batu daga bakin Suzailat sai idanunsu suka zazzaro suka kamu da tsananin tsoro. Huraisu ya dakawa Suzaila tsawa ya ce, "Shin baki da hankali ne za ki ce za ki tari sadaukin da babu kamarsa a fadin duniya?" Suzaila ta ce, "Ai tunda ya kasance mai hakuri da gaskiya ko na tareshi da yaki ba zai cutar da ni ba. Ya kai Abbana ka yi sani cewa idan har baka sa da ni a cikin cikin wadannan mutane hudu ba da za su yi wannan tafiya to fa sai jama'ar garin nan sun zageka sun ce ka nuna son kai da rashin gaskiya saboda kowa ya san cewa ni ce jaruma ta farko wacce ya kamata a fara za6a tunda nafi kowa cancanta. Ka tsaya ka yi nazari da tunani bisa wannan gaskiya da na fada maka yanzu don kada ka aikata abinda za ka zo ka yi nadama a kansa. Na barku lafiya". Koda gama fadin hakan sai gimbiya Suzaila ta mike tsaye ta sumbaci goshin Sabirat sannan ta Fice daga cikin dakin gaba daya. Tana fita sai Sabirat ta dubi Sarki Huraisu cikin tsananin damuwa kamar za ta fashe da kuka ta ce, "Ya kai mijina ka yi sani cewa ina jiye maka tsoron ranar da Suzaila za ta gano sirin da muke boye ma ta dangane da yadda aka yi ka zamo Sarki. Ina tabbatar maka da cewa idan ka hanata yin wannan tafiya za ta gan0 wannan sirri da wurwuri, haka kuma idan ka barta ma ta yi tafiyar in dai ta rayu har izuwa karshen tafiyar to babu shakka za ta gano wannan sirri don haka kana cikin tsaka mai wuya don haka sai ka yi tunanin abinda zai fissheka. Ni kam babu wata babbar rana ta bakin ciki a wajena wacce tafi ranar da Suzailat za ta gano wannan Siirri." Koda gama fadin hakan sai Sabirat ta fashe da matsanaicin kuka, al'amarin da ya dugunzuma hankalin Sarki Huraisu ke nan fiye da ko yaushe ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. Nan dai ya shiga rarrashinta ya rinka gaya ma ta maganganu masu tausasa zuciya har dai ya shawo kanta ta daina kuka. AA Misau ke magana A CAN bangaren ragowar Sarakai kuwa, bayan an watse đaga taron da aka yi a fada sai suka shiga sabon taron sirri a cikin tsakiyar dare inda suka taltauna akan batun bakon boka Kirishna wanda ya zo daga kasar Hindu. Kaso takwas daga cikin kaso goma na Sarakunan sai suka nuna Cewa su sam basu gamsu ba da wannan shawara da boka Kirishna ya kawo saboda sun gaji da karyace-karyacen bokaye akan wannan al'amari. Sai da aka shfe sa'a uku da rabi ana ta kacé-nace sannan ka yanke shawarar cewa kowanne Sarki Zai bayar da dakaru dubu arba'in a sirance bisa jagorancin babban bokan kasarsu su tafi izuwa dajin Kirzufa domin yiwa dajin taron dangi a rana guda a shafe duk wani abu mai rai da yake cikinsa. Nan take aka tsaida ranar da za a tara wadannan dakaru kuma aka tabbatar da cewa dakarun za su hadu ne a birnin Ihisar za su hadu. A takaice dai Sarki Jamal ne jagoran wannan taro. Wannan shi ne abinda ya faru a bimin Lairuf bayan Sarakunan nahiyar gaba daya sun zaUna sun tattauna bisa yadda za su sami mafita akan masifar annoba ta jarumi mai kahon BUSA A MUTU. A CAN dajin Kirzufa kuwa Muraisù da mahaifiyarsa Husnaila sun ci gaba da rayuwarsu cikin koshin, lafiya da kwanciyar hankali, amma tun daga ranar da suka yi yaki da su Sarki Zaidur sai suka daura darmarar baiwa juna horon yaki kuma suka rinka baiwa jikinsu horo mai tsanani na yin gudu mai yawan gaske babu hutawa har na tsawon kamar sa'a goma sha biyu sannan idan suka fara yakar juna'suna kai sara da suka nan mà sai su shafe sa'a bakwai suna yi. A haka ne kullun jikinsu ya rinka'sabawa- da jurewa wahalá da gajiya ya zamana cewa kullum jarumtakarsu karuwa take. Su kansu sai suka rińka mamakin al'amarin. Abinda basu sani ba shỉ ne, simin yana daga cikin dajin da suke zaune. Sai da Muraisu da Husnaila suka kwana goma sha bakwai a cikin wannan hali na baiwa kansu, wannan horo su kansu sai da suka ji sauyi matuka a jikinsu bisa wani irin gagarutnin karfi da suka ji ya shiga cikin jikinsu tamkar za su iya yakar duniya gaba dayanta su biyu. A ranar kwana na góma sha bakwan ne da hantsi bayan sun gama baiwa kanşu horon yakin kuma sun záuna suna hutawa sai suka ji sukuwar dawakai ba adadi sun durfafo cikin dajin. Duk da cewa su Muraisu suna jin gagarumin karfi a jikinsu sai da karar sawayen dawakan ta firgitasu saboda ganin yadda kasar dajin gaba daya ta kama girgiza. Ba komai ne ya haddasa hakan ba face tsananin yawan dakarun da suke bisa dawakai. Küma tun daga nesa ana jiyo irin karlin gudun da suke yi da karar kofaton dawakan. Muraisu da Husnaila suka mike tsaye zumbur suka ruga da gudu izuwa cikin kogon da suke rayuwa suka debo makamansu na yaki. IHuraisu ya daga kansa sama ya kurma wani uban ihu. Faruwar hakan ke da wuya sai gaba dayan dabbobin dajin suka rinka firfitowa daga cikin ramukansu wadanda ke kan bishiyoyi suka sauko. Wadanda ke cikin gabar kogi ma suka fito gaba dayansu suka rugo da gudu suka iso inda Muraisu da Husnaila ke tsaye a tsakiyar dajin rike da makamansu na yaki sun yi wata irin tsayuwa ta manyan jarumai wacce ke nuna tsantsar rashin tsoro da yarda da kai. A dai-dai wannan lokacin su Muraisu suka hango DANDAZON MAYAKAN da suka durfafosu masu tsananin yawan gaske tamkar yakin duniya za a yi. Amma wani abin mamaki da ya faru shi ne, ko gezau Muraisu da Husnaila da dabbobin dajin ba su yi ba, kawai sai suka tsaya cak a inda suke aka fara kallon-kallo tun daga can nesa. Lokacin da ya rage saura baifi taku hamsin ba tsakanin rundunar mayakan da kuma ayarin Muraisu, sai Muraisu da Husnaila suka daga makamansu sama a lokaci guda kuma suka falfala da azababben gudu suka durfafi abokan gaba. AA Misau ke magana Nan kuwa surna sauran dabbobi dajin sai suka rufawa su Muraisu baya. Koda rundunar mayakan suka hango su Muraisu sun taso da gudu suma sai suka sakarwa dawakansu Kaimi suka rinka kwalla ihu suna zumudin a hadu domin su yi ta-more saboda ganin cewa yawansu da karfin shirinsu na muggan makaman yakin da suke rike da su gami da yarda da bokayensu bisa sa'ar da suka basu suna ganin cewa lallai babu abinda zai hanasu samun nasara a yau. Ai kuwa ana haduwa a tsakiya sai aka kacame da azabbaben yaki wanda baki bai isa ya iya fasaltashi ba. Ihu, kururuwa da gurnanin mutane da dabbobi ya cika dodon kunne. Kura ta tashi ta turnuke sama da kasa. Nan fa kasuwar cinikin rai ta fara kankama sai gashi jini ya fara tsartuwa, feshi da malala a sama da kasa tamkar ruwan samansa ake yi, wani kuma tamkar daga cikin kasar yake tsattsafowa kai kace idaniyar ruwa ce ta balle. Sassan jikin bil'adama kuwa ya rinka shawagi a sararin samaniya tamkar iska ce ke yawo da takardu. Wani lokacin idan dabba ta wangame bakinta ta daka tsalle sai dai ka ga ta hadiye kan mutum ta gutsure kan tamkar an sa takobo an sareshi. Wani babban abin mamaki shi ne, su kansu dabbobin na dajin Kirzufa wannan karon sun koyi dabarun yaki matuka sun san yadda suke kaucewa sara de suka. Kai hatta harbin kibiyoyi ma kaủce musu suke tamkar an basu horo na musamman kan hakan Wohoho! Wuya ba a sama ta ranaa, ita masita idan ta taho babu abinda yake iya dakatar da ita face Allah. Tun da aka fara warnan azababben yaki kó alamar nasara babu a 6arigaren wannan runduna ta dakerun teron dangi, domin ko dabba daya jal basu sami damar kashewa ba, amma sun yiwa wadansu dabbobin raunika da yawa. Sai ka ga gashi an sari dabba ko an soketa jini na zuba amma naci tana mai ci gaba da yaki babu alamar Jigata a tare da ita. Jarumi Muraisu da Husnaila kuwa duk inda suka sa gabansu sai dai ka ga maza na zubeva kasa ratata tamkar ana sassabe a gona, kuma ko yaushe dada kara samun kuzari suke da karfi maimakon su gaji. Nan dai su Muraisu suka zamewa dakaron alakakai kuma annoba. Koda aka shafe sa'a biyar ana wannan gumurzu sai dakarun TARON DANGI suka ja da baya gaba dayansu sakamakon ganin irin mummunar 6arnar da aka yi musu saboda du sa'adda suka dubi kas gawarwakin 'yan uwan da na dawakansu suke gani. Ai kuwa suna ja da baya sai Muraisu da Husnaila ma suka ja da bayan, dabbobin din ma sai suka yi koyi da su. A sannan ne aka tsaya ana kallon-kallo. A wannan lokaci ne dakarun taron dangin suka firgita ainun domin sun fahimci cewa an kashe kaso daya cikin kaso ukunsu. Nan take fiye da rabinsu suka yunkura za su kada dawakansu su juya da baya don su gudu sai. wani barde mai kirar sadaukai wanda ya kasance shi ne mataimakin Sarkin Yakin Sarki Jamal wanda ake kira da suna BULMAZU ya daka musu tsawa ya ce, "Duk wanda ya yi kokarin gudu ni da kaina zan kure masa gudu na kashe shi. Shin kun manta ne cewa duk wanda ya shigo dajin nan ba isa ya fita a raye ba face ya kashe duk wata halitta mai rai da ke cikinsa? To ku sani cewa bamu da wani zabi wanda ya fi mu yaki wadannan takadiran mutane biyu kuma mu kashe wadannan dabbobi nasu gaba daya". Koda gama fadin hakan sai Bulmazu ya daga takobinsa sama yana mai kwarara uban ihu wanda ke firgita maza a filin daga sannan ya sake sakarwa dokinsa kaimi ya yi kan su Muraisu. A lokacin ne sauran dakarun taron dangi suka taso aka sake kaurewa da sabon gumurzu. Har ya zamana cewa tsakanin Muraisu da Bulmazu bai wuce taku biyar ba Muraisu ko motsawa bai yi ba daga inda yake isaye kuma ko kadan babu alamar tsoro a fuskarsa, kawai jira yake Bulmazu ya karaso. Nima anan zan dakata sai wani lokaci kuma AA Misau ke magana WhatsApp group Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QBUSA A MUTU Littafi Na Biyar (5) Part C Na Abdulaziz Sani M Gini AA Misau ke Magana Barkanmu da wannan lokaci dafatan kuna lafiya ya ku jama ar wannan gida Mai AlbarkA Ba zato ba tsanmani sai kawai aka ga Muraisu ya daka tsalle sama. Kafin Bulrmazu ya sake kawowa Muraisu wani harin tuni gadon bayan dokin Bulmazu. A saman Bulmazu ya kawowa mummunan saraa wuya da nufin ya fille masa kai. Cikin bakin zaffn narna Muraisu ya sunkuyar da kansa kas amma duk da hakan sai da kaifin balkin takobin ya zabtare wani bangare daga cikin gashin kan Muraisu. Nan take muraisu ya gigarawa Bulmazu takobi a makogwaronsa. Gudan jini ne ya bullutso daga cikin wuyan, jijiyoyi kuma suka kama feshin wani jinin. Da karfin tsiya Muraisu ya karasa yanke kan Bulmazu ya daga kan sama yana mai ihu da kururuwa. Al'amarin da ya karya lagon dakarun taron dangin ke nan suka karaya ainun. Duk da sun san cewa ba a fita daga dajin Kirzufa sai suka kara juyawa da baya a guje don su tsira da rayuwarsu amma sai Muraisu da Husnaila da kuma sauran dabbobin dajin suka rinka kure musu gudu suna rafkesu. Saí da aka shafe sa'a biyar ana rafke wadannan dakaru sannan suka kare saboda yawansu. A wannan lokaci ne Mủraisu, lusnaila da Dabbobin suka gaiji likis suka kwanta a kas suna huci Kamar ransu zai fita". Koda Muraisu ya dagokansa ya dubi gawarwakin dakarun taron dangi ya ga dukkaninsu fa mutane ne irinsa sai nan take nadama ta zo masa kuma Ya kamu da tsananin tausayinsu. Kawai sai idanunsa suka ciko da kwallah. hawaye ya fara sartu bisa kumatunsa. Yana juyawa bayan sa ne ya yi arba da mahaifiyar sa . Koda ta ga hawaye na zuba a idanunsa sai ta cika da tsananin mamaki. Cikin sanyin jiki ta taso daga inda take kwance ta iso daf da shi suka fuskanci juna sannan ta ce, Ya kai dana namijin duniya, kuma Sarkin gobe a birnin Lairuf, mene ne ya saka kake zubar da hawaye haka alhalin gashi mun sami gagarumar nasara akan makiyanmu?" Sa'adda Muraisu yaji wannan tambaya sai yasa hannu ya share hawayensa sannan ya dubeta ya ce, "Ya ke Ummina ki yi sani cewa ba komai ne ya sani zubar da wannan hawaye ba face tsananin tausayin wacannan mutane da muka kashe. Ki tuna fa cewa suma suna da iyali. Wani yana da iyaye, wani yana da mata da 'ya'ya wani kuma 'yan uwa kadai gareshi. Ya ya iyalinsu za su kasance? Wane irin bakin ciki za su shiga idan suka san sun mutu?" Sa'adda Husnaila taji wannarn batu na Muraisu sai ta murtuke fuska ta dubeshi a fusace ta ce, "Akan wanne. dalili za ka ji tausayin wadanda basa jin tausayinka kuma basa kaunarka? Shin ka manta ne cewa wadannan mutane sune suka kashe mahaifinka suka sa muka baro cikin garri muka dawo rayuwar daji muka rasa daular da muke ciki. " Gama fadin hakan ke da wuya sai suka hango wata damisa da ke tsaye tana numfarfashi, ta sulale kasa ta baje tana kakarin mutuwa. A dimauce Muraisu da Husnaila suka mike tsaye zumbur suka ruga izuwa kan Damisar suka hau. duddubata. Nan take suka ga ashe gefen cikin damisar a bule yake har hanjin cikinta ya fito. Koda ganin haka sai Husnaila ta fashe da kuka kuma ta sake dimaucewa ta mike zumbur za ta je ta dauko maganin da za ta sawa damisar sai Muraisu yai caraf ya ruko hannunta ya dubeta cikin alamun karayar zuciya ya ce, "Ki yi hakuri ya ke Ummina ki yi sani cewa lokaci ya kure wannan damisa mutuwa za ta yi." Ai kuwa kafin Muraisu ya gama rufe bakinsa sai Damisar tayi ajiyar numfashi na karshe ta sandare ya zamana cewa komai na jikinta ya daina motsi. AA Misau ke magana Koda ganin haka sai Husnaila ta fada kan gawar Damisar ta fashe da matsanaicin kuka tamkar wadda ta rasa dan cikinta ko wani shakikinta. Da kyar Muraisu ya ya bambarcta daga kan gawar Damisar. Nan take sauran Damisoshi suka taru a gaban 'yar uwar tasu, wasu daga cikin suka kama tonon kasa har sai da suka yi rami mai dan zurfi da fadi sannan suka Janyo gawar yar uwar tasu izuwa cikin ramin suka binneta. Sai da aka shafe sa'a daya ana jimamin mutuwar damisar sannan Husnaila da Muraisu suka mike tsaye suka tafi izuwa cikin kogonsu suka zauna. A sannan ne Husnaila ta lura da cewa akwai kananan raunika a jikin Muraisu. Cikin hanzari taje ta d'auko wani garin magani wanda aka yi shi da busasshiyar saiwar wata bishiya ta fara lika masa maganin a jikin raunikan. Koda tazo kan wani rauni da ke gadon bayansa sai tayi arba da wani zanen wuka mai nuna tambarin gidan sarautar binin Lairuf. Al'amarin da ya jefata cikin tsananin mamaki ke nan domin tunda ta haifi Muraisu ba ta taba ganin wani hatimi a jikinsa ba sai yau, don haka sai ta daina shafa masa maganin ta kurawa tambarin idanu kawai. A sannan ne Muraisu ya yi gyaran murya ya ce, "Ya ke Ummina me ya faru kika tsaya ga barin sa mini maganin ?" Koda jin wannan tambaya sai Husnaila ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ya kai dana ka yi sani cewa wani hatimi na gani a gadon bayanka wanda ban taba ganinsa ba sai yau kuma shaidace mái nuna cewar kai jinin sarautar birnin Lairuf ne". Koda jin wannan batu sai nan take Muraisu ya tuno da mafarkin da ya yi a daren jiya. A zabure Muraisu ya juyo ya fuskanci Husnaila ya ce, "Ya ke Ummina ki yi sani cewa jiya na yı mafarki na yi gamo da wani gawrtaccen sadaukin saurayi wanda ya fini karfi da jarumtaka ainun domin duka daya ya yi min na yi sama kamar an cillani daga cikin baka, tun a saman jini yai feshi daga cikin bakina kuma na fado kasa a matukar galabaice. Kafin na tsaye sai na ga wani Sarki mai kwarjini da cikar haiba tsaye a gabana ya caba ado yana ta faman kyalkyala mini dariya. A hannun Sarkin akwai wata sandar mulki mai siffar doki." Koda jin wannan batu sai hankalin Husnaila ya dugunzuma ainun domin itama irin wannan mafarki tayi sak a jiya da daddare babu bambanci. Koda Muraisu ya ga alamun damuwa karara alkan fuskar Husnaila sai shima hankalinsa ya dugunzuma ya dubeta ya ce, "Ya ke Ummina wai shin Mene ne yake faruwa ne haka? Na ga kema kin shiga cikin halin damuwa bisa wuanan mafarki da na baki labari?" Husnaila tayi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Ya kai dana ka yi san cewa nima a jiya cikin barcina na yi mafarki iri daya sak da naka mafarkin. Ko shakka bana yi akwai wani mügun tanadi da Sarki Huraisu an uwan mahaifinka ya yi mana. Hakika hankalina ya tashi ina tsoron kada wani mugun abu ya samcka ko ya samneni a nan gaba" Koda jin wannan batu sai Muraisu ya cika da mamaki ya ce, "Ya ke Ummina ya za a yi wani mugun abu ya samemu alhalin muna zaune a cikin dajin KIRZUFA inda babu wani mahaluki da ya isa ya shigo ya fita a aye?" Husnaila ta ce, "Shin ka manta nc cewa ba anan tamu dauwama ba? da zarar fa ka gama busa kahon Nan zamu yi shiri mu tafi izuwa birnin Lairuf domin ka carbi karagar mulki a hannun azzalurnai Huraisu. Abinda na ke so ka sani shi ne, a wannan lokaci ne Barki Huraisu zai yi amfani da damarsa wajcn cutar da Koda jin haka sai hraisu yayi ajiyar numfashi ra ce, "Amma ai jarumin da aka nuna mini a cikin Barcina ina yaki da shi anan cikin dajin Kirzufa ne ba wai a can birnin Lairuf ba Husnaila ta ce, "Ai shi mafarki wani abu wanda ba lallai bane ya zama gaskiya. To amma dai tunda ni da kai duk mun yi mafarki iri daya a lokaci guda to lallai koda abin da muka gani bại faru ba to tabbas sai makamancinsa ya faru. Tabbas yanzu bamu da wani abin yi face mu ci gaba da jjircewa wajen kefe baiwe kanmu homn yaki kullum babu sassautawa domin mu yi shirin tunkarar duk abinda zai zo mana. Muraisu ya gyada kai sannan ya ce, "Hakika kinzo da bayani mafi cancanta agaremu." Wannar shi ne abinda ya faru a dajin Kirzufa bayan an fafata kazamin yaki tsakanin su jarumi Muraisu da dakarun taron dangi AA Misau ke magana A CAN birnin Lairuf kuwa, sai da aka kwana goma sha hudu ana ta shirye-shiryen gagarumar tafiyar da za a yi ta, bazama a cikin duniya domin neman jaruni IMRAN. A ranar kwana na goma sha uku ne Sarki Huraisu ya yiwa gimbiya Suzaila albishir cewa ya amince ta zama daya daga cikin mutane hudu da zai bayar domin yin wannan tafiya ta neman jarumi Imran sadaukin da zai shiga cikin dajin Kirzufa ya kamo mai kahon busa a mutu Koda jin wannan albishir sai gimbiya Suzaila ta kamu da tsananin farin ciki. Nan take ta fara shirye- shiryen tafiya saboda doki da murna har dare ya yi ba ta rintsa ba. Makamanta na yaki kuwa sai da ta tanaji kala goma sha daya. Bayan Suzaila ta gama shiri tsaf ta shirya dukkan kayanta a gefe daya cikin turakarta sai taje kan gadonta ta kwanta ta rintse idanunta domin tayi barci, dama ta kashe fitilar dakin. Koda ta rufe idanun na ta sai ta rinka ganin hoton jarumin Imran wanda ya kasance kakkyawan saurayi na gaban kwatance mai cikar kyawun sura, kwarjini da haiba. Nan take sai taji ta kamu da tsanánin kaunarsa don haka sai tayi sauri ta bdue idanunta lokacin da zuciyarta ta fara bugawa da karfi. Al'amarin da ya matukar ba ta mamaki ke nan domin a iya rayuwarta ba ta taba ganin saurayin da taji ta kamu da sonsa ba sai Imran. To wai shin ma akan wane dalili za ta kamu da son mutumin da ba ta taba yin arba da shi ba a fili? Ai kuwa dole ne na yi yaki da zuciyata na tursasata ta cire so .0wanne da namiji a cikinta." Haka dai Suzaila ta ci gaba da sakar zuci ta kulla wannan ta kwance wancan har barci ya saceta ba ta sani ba. Kashe gari kuwa da safe bayan Suzaila tayi kalaci sai tayi wanka ta kimtsa tayi gagarumar shigar kayan yaki sannan ta nufi fada inda za ta iske ragowar abokan ta fiya. Tun daga nesa Suzaila ta hango fadar a cike makil da dakarun tafiya. A can sama bisa kan gini mai matattakala inda karagar mulki take, gaba dayan se rakunan nahiyar ne a zazzaune har da mahaifinta Sarki Huraisu. Sarki Imras ne kadai babu shi a wajen. Suzaila ta ci gaba da tafiya har ta ratso ta cikin mutancn da aka zaba don yin wannan tafiya tana wucewa ta tsakiyarsu tana kallonsu da nazarinsu daya Koda ta riski layin karshe ta iso kan gaba tayi arba da wadensu mutane guda biyu tsaye cikin sahu sai ta cika da tsananin mamaki. Ba wadansu bane wad'annan mutane face yarima Hasnalu da 'yar uwarsa gimbiya Lushaira dukkaninsu sun yi shigar yaki. Al'amarin da ya yi matukar baiwa gimbiya Suzaila mamaki ke nan domin ba ta ga amfanin yin wannan tafiyar ba tare da su tun da basu kasance jarumai ba. Kawai sai Suzaila taje ta tsaya kusa da Lushaira ta dubeta suka yiwa juna dan guntun murmushi. Koda yarima Hasnalu ma ya dubi Suzaila ya yi ma ta murmushi sai ta maurtuke fuska ta daka masa harara. Ba shiri ya kau da kansa ga barin kallata. Faruwar hakan ke da wuya sai ga Sarki imras ya shigc cikin fadar shima fuskarsa a murtuke ko kadan babu annuri a cikínta. Koda Sarki Huraisu ya hango Sarki Imras a cikin wannan hali sai bankalinsa ya dugunzuma ya mike tsaye daga kan karagarsa ya sauko kasan natattakalar ya tareshi yana mai rike kafadunsa kuma ya tambayeshi ya ce, "Ya kai abokina waye ya Gata maka rai kå shigo cikin fadar nan tawa haka babu annuri akan fuskarka?" Koda jin wannan tambaya sai Sarki Imras ya yiwa Sarki Huraisu rada a kun. Nan take Sarki iuraisu ya kamu da tsananin fishi ya juya a fusace ya yiwa gaba dayan Sarakunan da ke fadar wani irin kallo wanda ya sa duk suka sha jinin jikinsu kuma suka sunkui da kawuaansu kas cikin alamun kunya da rashin gaskiya. Nan dai Sarki Huraisu ya kama hannuh Sarki Imras ya jashi izuwa can sama Suka Zauna tare akan karagarsa tare sannan sai fuskar Sarki Huraisu ta juye izuwa annuri ya mike tsaye ya dubi kowa da kowa ya ce, "Ya ku 'yan uwa da abokan arziki, ku yi sani cewa yau ne ranar da wakilanmu za su tafi neman jarumin iya sadauki Imran wanda shi ne zai iya yi mana AA Misau ke magana maganin wannan. annoba ta mutuwar ya'yayen Sarakunanmu Duk wadannan mutane da kuke gani a tsaye a tsakiyar fadar nan su ne wadnda aka zabo don yin wannan iafiya. Ni a 6angarena akwai 'yata gimbiya Suzaila wacce kuka fi sani da Sarkin yakin birnin Lairuf sai kuma Sarkin yakina na da, sại kuma tagwayen sadaukai jarumi Shalaru da jarumi Halaru. A 6angaren Sarki Imras kuwa akwai 'ya'yansa guda biyu yarima Hasnalu da gimbiya Lushaira sai kuma Sarkin yakinsa da mataimakinsa. Kowanne Sarki anan shirna ya bayar da mnutane hudu kamar yadda muma muka bayar. Baya ga wadannan dalkaru mun sake ware. wadansu dakaru guda dubu sittin kacal wadanda za su yi musu rakiya. Tunda akwai 'ya'yanmu a cikin wannan tatiya dole nea ware kuyangi wadanda za su rinka yi musu hi dima a cikin wannan tafiya, saboda haka kowanne yarima ko gimbiya an ware masa kuyanga goma. Muna sa ran cewa wadannan matafiya za su dawo garemu cikin nasara a iokacın da ba zai wuce tsawon shekara daya ba. Da wannan furuci nake yiwa matafiyan bankwana da fatan za su yi tafiyar lafiya su dawo lafiya. Idan akwai wani mai koráfi akan abinda na fadi yanzu sai ya yi tun gabannin wadannan matafiya su tafi." Koda gama fadin hakan sai fadar gaba daya tayi tsit! Aka rasa wanda zai ce kala. Har Sarki Huraisu ya yunkura zai daga hannu domin ya baiwa matafiyan umarni su tafi sai Sarki Jamal yai gyaran murya kuma ya mike tsaye ya ce, "Yana da magana". Sarki Huraisu ya dubi Sarki Jamàl ya ce, "An yi maka izini ka fadi korafinka". Sarki Jamal ya sake yin gyaran murya a karo na biyu sannan ya ce, "Ya kai wannan Sarki mai daraja ni ina ganin cewa bai kamata mu dauki har tsawon shekara guda ba muna jiran dawowar wadannan dakaru saboda kafin cikar shekara gudan ba a san iya adadin 'ya'yan Sarakan da za a rasa ba. Kamata ya yi a baiwa matafiyan tsawon wata uku kacal, idan har basu hadu da jarumi Imran ba kawai su dawo gida." Kafin Sarki Jamal ya gama rufe bakinsa tuni Sarki Huraisu ya daka masa tsawa yana mai cewa, "Wannan wacce irin maganar banza kake yi ne haka? To idan suka dawo bayan wata ukun basu sádu da sadauki. Imran ba mene ne amfanin fitar tasu kuma waye zai yi mana maganin wannan masifa? Su. Shi ke nan sai dai mu zuba ido muna gani a ya'yayen namu su ci gaba da mutuwa har a karar da Ka tsaya ka yi tunani ka gani yanzu fa ni da Sarki Imras 'ya'yan namu muka bayar ayi wannan tafiya mai hadari tare da su don kawai a kawo karshen wannan masifa. Shin ka san irin hadarin da ke cikin wannan tafiya kuwa?" Sarki Jamal ya kada kai cikin alamun sanyin jiki da borin kunya. Sarki Huraisu ya matso har izuwa gaban Sarki Jamal ya tsaya daf da shi yadda suna iya jin numfashin juna ya ce, "Kada ka yi zaton cewa duk abinda kuke kullawa a sirrance bamu sani ba kai da sauran sarakuna kun tashi dakaru masu yawan gaske bisa jagorancin bokayenku kun turasu izuwa dajin Kirzufa domin su kashe yaro mai Rahon BUSA A MUTU. To ka sani cewa gaba dayan dakarun naku da bokayensu duk sun hallaka dayansu bai tsira da rayuwarsa ba." Koda jin wannan batu sai idanun Sarki Janal suka zazzaro, hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe ya rasa abin da ke masa dadi. Saukinta ma kamnar a cikin rada Sarki Huraisu ya yi masa wannan jawabi babu wanda ya ji. Nan take Sarki Jamal ya koma ya zauna, sannan Sarki Huraisu ya yiwa matafiyan bankwana. Bayan ya gama yi

Chapter 2 of 4