Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
an biririka su kuma suna kai masa mangari, yakushi, calksa da cizo yana gocewa. Duk sa'adda suka kai masa yakushi da faratan hannayensu ya, goce ko dutse suka, karta sai ka ga ya dare gida biyu saboda tsananin kailin faratan nasu. Shi kuwa Muraisu duk sa'adda ya sari jikin Birirrikan ko ya sokesu sai ya ji kamar karle yake sara. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa ke nan, domin ya san cewa idan áka dade a cikin wannan hali zai iya gajiya. Da zarar kuwa ya gaji birirrikan za su sami lagonsa su hallakashi. Nan fa ya fara tunanin dabarar da ya kamala ya yi ya ccci rayuwarsa da ta Husnaila wacce ke daure a jikin bishiya. Haka dai aka ci gaba da wannan gumurzu har tsawon rabin sa'a ba tare da wata dabara ta fadowa Muraisu ba. A sannan ne kuma ya fara gajiya. Ai kuwa sai shugaban biririkan ya shammaci Muraisu ya gabza ma sa naushi a fuska. Saboda karfin naushin sai da Muraisu ya yi katantan wa sau uku a tsaye sannan ya baje kasa jini na yoyo ta hancinsa da bakinsa a cikin matsanaicin hali mai kama da suma da gushewar hankali. Koda Husnaila ta ga halin da Muraisu ya shiga sai ta saduda ta tabbatar da cewa itama ta ta ta kare don haka saí ta sake kwalla ihu ta fashe da matsanaicin kuka. Shí kuwa wannan shugaban birrrikan sai ya zo : kan Muraisu ya tsaya ya raba kafafu akansa ya. surnkuyo kasa da nufin ya cire kansa ya cinye. Ba zato ba tsammaní aka ga Muraisu ya dunkule hannunsa ya gabzawa shugaban biririkan naushi a ido. Take ruwan idon ya fashe jini ya rinka kwararowa daga ciki tamkar an bude IDANIYAR RUWA. Kawai sai birin ya sulale kasa ya fadi rikica ya zama gawa. AI kuwa sai sauran birirrikan suka yi caa! akansa za su yagalgalashi. yaki. Nan fa aka ruguntsume da sabon azababben Cikin zafin nama Muraisu ya ci gaba da naushin birimikan a idanu suka rinka ihu suna zubewa kasa matattu, amma saboda na ci basu fasa kai masa muggan hare-hare ba. A haka ne suma birimikan suka rinka yi masa raunika a sassan jikinsa. Kafin Muraisu ya sami nasarar kashe gaba dayan birirrikan sai da ya sami raunika a jikinsa sama da guda ashirin, ya zamana cewa gaba dayan jikinsa yai fata-fata da jini. Ai kuwa yana gama kashe birirrikan sai shima ya kife kasa a sumamme. Muraisu bai farfado ba sai bayan rabin sa'a, sannan ya mıke zaune da kyar yana numfashi sama-sama, kamar ransa zai fta. Koda ya dago kai Ya hada ido da llusnaila sai ya ga tayi masa guntun murmushi. Kawai sai ya kau da kai ga barin kallonta ya shiga yiwa kansa magani. Bayan ya gana gyara raunikan jikinsa gaba daya sai ya mike tsaye da kyar ya je yasa bakinsa a ciin wannan koram a ya sha ruwa ya koshi. Kawai sai yaj. Husnaila ta ce, "Ya kai wannan jarumi ka taimakeni ka kwanceni nima na zo na sha ruwan nan, domin ishirwa ta addabeni". Koda jin haka sai Muraisu ya dago kai ya dubeta ya Ce, "Ta ya ya kike tsammanin cewa zan sake aminta da ke? Shin kin manta ne cewa sau biyu kika yi yunkurin hallakani, kuma yanzu sau biyu ke nan ina ceton rayuwarki. Na sani cewa kin tsaneni fiye da komai a duniya, don haka babu yadda za a yi na yarda da ke. Ba zan kwancc ki ba daga jikin wannan bishiya har izuwa kwana biyu, amma duk abinda kike bukata zan yi miki". Koda jin war nan batu sai hankalin Husnaila ya dugunzuma ain un, ta ce. "To yanzu kuma idan bukatar bawali ko bayan gida ta kanani fa?" Murajşu yai numushi ya ce, "Ai sai dai kiyi komai anan inda kike'. Kamar yadda Muraisu ya fada haka al'amarin ya kasance, sai da suka kwana biyu a cikin wannan kogon dutse suna rayuwa. Tsawon wadannan kwanaki Husnaila na daure, a jikin bishiyar take kwana, a jikinta take bawali, Muraisu bai yarda ya kwanceta ba. A ranar kwana na biyu ne da yammaci daf da magariba Muraisu ya kwance Husnaila daga cikin wannan itaciya. Saboda tsananin gajiyar da tayi na tsayuwa a tsaye, sai ta fadi kasa ta kasa mikewa zaune. A wannan lokaci ne tausayin Husnaila ya kama Muraisu ya dubeta ya ce, "Ki gafarceni ya ke wannan ma'abociyar kyawu, ki yi sani cewa na ki kwanceki ne daga jikin wannan bishiya saboda tsoron kada ki sake yi mini abinda kika yì mini a baya", Bisa mamaki sai Muraisu ya ga Husnaila ta juyo ta dubeshi tayi murmushi sannan ta ce, "Hakika abinda ka yi min shi ne dai-dai, domin na tabbatar a wancan lokacin ina jin kiyayyarka a cikin zuciyata fiye da komai a duniya, amma a yanzu ka kwantar da hankalinka ka saki jikinka domin na fahimci, cewa bani da wani masoyi a duniya sama da kai. Hatta dan uwana da ya kasance jinina bana jin zai nuna mini irin kaunar da ka nuna mini a cikin wannan daji". Koda jin haką sai Muraisu ya yi murmushi ya ce. "Na san da haka, kuma lallai ni yanzu na tabbatar da cewa ba za ki cutar da ni ba", Koda jin haka sai mamaki ya kama Husnaila ta ce, "Mene ne tabbacinka cewar ba zan ta6a cutar da kai ba?" Muraisu ya ce, "Saboda tun kafin na fito nemanki na san cewar idan har muka kwana uku a cikin wannan daji na Kirzufa sai kin daina tsanata. Haka bokan mahai fina ya tabbatar mini". Da jin haka sai Husnaila ta gyada kai tayi dan tunani sannan ta ce,"Tabbas biri ya yì kama da mutum. Hakika yanzu na gane cewa dan uwana Sarki Ishmar ya tsafanceni ne da irin tsafin da zai sa na tsaneka. Ina fatan yanzu za ka yi mini gafara bisa abubuwan da nayi maka a baya". Koda jn haka sai Muraisu ya yì murmushì ya ce,"Ai duk abinda kika yi mini a baya na manta da su, domin inda abin na raina ba zan biyoki nan cikin kogon birimika ba na ceci rayuwarki." Haka dai Muraisu da Husnaila suka yi ta hira har dareya fara babu alamar jin barci a cikinsu. Da lokacin cin abincinsu ya yi sai Husnaila ta ki cin abincin da hannunta ta ce sai dai Muraisu ya ciyar da ita da hannunsa. Al'amarin da ya matukır baiwa Muraisu mamakí ke nan. Ba tare da gardamar komai ba kuwa Muraisu ya fara ba ta abíncin da hannunsa. Koda fara ba ta abincin sai ya ga ta kura masa idanu tana murmushí tana yi m asa wani irin kallo fnai nuna tsantsar kauna a zuci.. Haka daí Muraisu ya ci gaba da ciyar da Husnaila har saí da ta koshi sarnnan shima yasa hannu don ya ciyar da kansa. Sai tayi caraf! ta rike hannunsa ta fara cíyar da shí da hannunta. Saí da ta tabbatar ya koshí sannan ta bashi ruwa ya sha, ítama ta sha. Maimakon ta tashi daga kusa da shi ta koma can gefe daya ta kwanta, saí ta kwanta daf da shi ta dora kanta a cínyarsa tana kallon fuskarsa tana murmushi irin wanda ke kuantar da hankalin masoyi. Shima sai ya kura ma ta idanu, tsawon 'yan dakiku dayansu bai ce uffan ba. Daga can sai Husnaila ta dubi Muraisu ta ce, "Yanzu me ka tsara mana a rayuwa?" Koda jin wannan' tambaya sai Muraisu ya yi ajíyar zuciya sarnnan ya ce, 'So nake gobe da sassafe mu bar wannan daji mu lafi izuwa birninmu Domin a daura nana aure mu fara sabuwar rayuwa la jin dadi da kwanciyar hankali", Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa llusnaila, al'amarin da ya matukar baiwa Muraisu mamaki ke nan, ya dubeta cikin tsananin damuwa ya ce, "Ina dalilin zubar da wannan hawayc naki?" Husnaila tayi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Ina JI a jikina Cewa abu nc mawuyaci mu yi rayuwa mai tsawo ni da kai. Ka tsaya ka yì tunani, a halin yanzu mutanen birninku suna cikin tashin hankali na shirye-shiryen yaki da za a yi. Shin za su tsaida hankalinsu ne akan shagalin bikinmu ko kuwa akan shirin yaki? Shawarar da zan bamu ita ce, kawai mu daurawa kanmu aure anan cikin dajin Kirzufa tun kalin mu koma can birninku a fara yaki. Ka ga ke nan da mun je sai mu fuskanci yakin a ci gaba da tanadin yadda zaa fuskanci abokan gaba". Lokacin da Muraisu yaji wannan shawara sai ya yi shiru yana tunanı har izuwa tsawon yan dakiku, daga can sai ya yi ajiyar zuciya ya dubi Husnaila ya ce, "Na yarda da shawararki, lallai idan -gari ya waye za mu daurawa kanmu aure". Koda jin wannan batu sai IHusnaila ta kamu da tsananin farin ciki ta mike Zaune ta rungume Muraisu ta kwanta akan kirjinsa, suka ci gaba da hira a haka cikin murna da tsintar kansu a Cikin sabuwar rayuwa wacce basu taba jin ba duk su biyu.A haka barci ya sacesu basu sani ba. Kashe garí kuwa da sassafe Muraisu da lusnaila suka tashí daga barci, Da yake IHusnaila ta fara tashi sai ta kwabe kayanta ta shíga cikin wannan korama tayí wanka. Bayan la fito ne daga wankan Muraisu ya farka. Ba tare da įin kunyar komai ba kuwa IIusnaila ta zauna ta goge danshin jikinta da kyallen mayafi. Koda ganin haka sai shíma Muraisu ya kwabe kayan jikinsa ya fada cikin koramar ya yi wankansa sannan ya fito ya goge danshin ruwan, amma bisa mamaki sai Husnaila ta ga Muraisu yana sunkuyar da kansa kasa cikin alamun kunya, ya kasa dago kaí ya kalleta, Al'amarin da ya malukar bata manaki kc nan, ta dubeshi ta ce, "Ya kai masoyin raina, ina dalilin da ya sa ka ke dukar da kanka kasa baka son ka kalli kyakkyawar surar jikina?", Muraisu yai shíru kamar ba zai ce komai ba, daga can sai ya ce, "Ya ke abar kaunata kiyi sani cewa kunya na dagą cikin alamun karamci da sanin yakamata. Ilusnaila za ta fadi abu ne mai saukin gaske wanda ba zal yi wuyar nemowa ba. Koda llusnaila ta ga alamun camuwa a tare da Muraisu sai ta sake bushewa da dariya sannan la ce, "Kada ka damu ya kai masoyina, ka sani cewa abin kunya ne a ce sadakin aurena abu ne mai sauki a matsayina na kyakkyawar macen da babu kamarta a wannan nahiya lamu, kuma wacce a ta auri sadaukin da babu kamarsa yana da kyau mu barwa dan da zamu haifa abin alfahari, abin tarıhi". Koda IIusnaila tazo nan bayaninta, sai Muraisu yaji dukkan tsoro ya kau daga zuCiyarsa, wani irin gagarumin karfi ya shigeshi, kawai sai ya mike tsaye ya dubi Husnaila ya ce, "Tabbas yanzu zan je na kawo miki wannan sadaki". Husnaila tayi murmushi ta ce, "Ina yi maka fatan nasara da dawowa lafiya". Gama fadin hakan ke da wuy a sai Muraisu ya juya da baya ya fice daga cikin kogon dutsen ya nausa cikin dajin Kirzufa yana farautar tsohon Zaki. Sai da Muraisu ya shafe sa'a biyar yana farautar neman tsohon Zaki amma bai ga koda macen Zaki ba. Al'amarin da ya girgiza hankalinsa ke nan. Abinda ya matukar bashi mamaki shi ne, duk dabbar da ta hangoshi komai girmanta sai ya Ga ta ratse ta bashi hanya, ko kuma ta koma da baya. Wata ma ta tsre da gudu kamar dodo ta gani. Abinda bai sani ba shí ne, duk mutumin da ya kwana uku a cikin dajin Kirzufa, duk halittar da ke cikin dajin tsoronsa take ji. Haka dai Muraisu ya cí gaba da yawo a cikin dajin Kirzufa har ya gaji sosai ainun guiwarsa tayi sanyi kuma hankalinsa ya kara dugaunzuma domin Idan ya koma wajen Husnaila bai san abinda zai ga ya ma ta ba. Cikin sanyin jiki ya juyo da baya domin ya koma can cikín kogo inda ya baro Husnaila. Ba zato ba tsammani sai kawai Muraisu ya ga wanı Jibgegen Zaki a gabansa bisa wani katon dutse. Koda Zakin yai arba da Muraisu sai ya tsaya cak! Suka kurawa juna idanu suna nazari. Shi dai Muraisu murna ce ta kamashi saboda ganin cewar Zakin tsoho ne tukuf, irin wanda yake ncma. Shi kuwa Zakin ya tsoro ne ya kamashi domin yana kallon Muraisu ya ga shima Zakin ne irinsa kuma ya ninkashi biyu a girma. Ashe sirrin dajin shi ne, idan har bil'adama ya kwana uku -a cikinsa to duk dabbar da ke cikin dajin da ta ganshi sai ta ga ya zama irinta kuma ya fita girma da kwarjini. Ya yin da tsohon Zakin ya ga Maraisu ya durfafoshi ya hawo kan wannan dutse da yake bisa sai Zakin ya juya da baya ya soma tafiya da sauri- sauri. Koda ganin haka sai shima Muraisu ya kara sauri. Koda Zakin ya waigo ya ga Muraisu na sauri sai shi kuma ya fita da gudu. Wohoho! Nan fa aka kasa tsere tsakanin Zakin da Muraisu. Duk sa'adda Zakin ya waigo sai ya ga saura kiris Muraisu ya cinimasa. Koda suka iso karshen dutsen sai Zakin ya yi turjiya ya tsaya cak! Saboda gabansa wani rami ne mai tsananin zurlin tsiya. Duk abinda ya fado izuwa kasa sai dai ya zama gawa. Masu iya magana sun ce, "Abinda ya koro Bere daga Rami ya fada wuta, to labbas abin yafi wutar Zafi! Lokacin da Zakin ya leka ksan wannan rami ya ga zurfinsa sai ya juyo da baya ya fuskanci Muraisu ayi duk abinda za a yì. Bayan sun yiwa juna kallo na isawon 'yan dakiku sai kowannensu ya daka tsalle suka rungumi juna a sama suka rikito kasa saka kaima kokawa da birgimą. Muraisu ya shiga kokarin zaro wata wuka a kugunsa domin ya lumawa Zakin, shi kuma Zakin sai ya dinga turmusheshi yana kai masa yakushi da cizo. Nan fa kowanncnsu ya kasa samun nasarar komai. Sai da suka shafe lokaci mnai tsawo suna tumurmusa juna akan dutsen, duk sa'adda Zakin ya karci jikin Muraisu ko ya cijeshi sai yaji kamar dutse ya gatsa, ko kwarzancwa baya yi. Abinda ya dugunzuma hankalin Muraisu shi ne, ya fara jin alamun gajiya amma shi Zakin ko kadan bashi da alamun gajiya. Suna cikin wannan gumurzu ne Zakin ya danne Muraisu kuma ya cafi wuyan Muraisu đa hakoransa yana kokarin gatsawa. Kaifin hakoran Zakin ya kasa huda wuyan Muraisun, amma kuma sai Muraisu yaji ya shaku ainun. Nan da nan idanunsa suka kada suka yi jawur, kuma suka yi luhu-luhu kamar za su fado kasa. Nan fa ya fara kakarin mutuwa, kafin ya ankara ya suma. Koda Zakin yaji gaba daya jikin Muraisu ya sandare baya motsi sai ya yi wurgi da shi domin a zatonsa ya mutu, don haka sai Zakin ya juya da baya domin ya sauka daga kan dutsen. A dai-dai wannan lokaci ne Muraisu ya farfado daga dogon suman da ya yi. Koda ya bude idanunsa ya hango wannan Zaki...... Topah Wannan Zaki Ya Firgitani ta yadda bazan iya cigabaa da typing yanzu ba Sbd haka sai Kuma wani lokaci...BUSA A MUTU Littafi Na Biyu (2) Part E. Takun Karshe Na Abdulaziz Sani M Gini AA Misau ke magana Marubucin yaci gaba da cewa... A DAI-DAI WANNAN LOKACI NE MURAISU YA FARFADO DAGA DOGON SUMAN DA YA YI. KODA YA BUDE IDANUNSA YA HANGO WANNAN ZAKI SAUKA DAGA KAN DUTSEN, SAI YA MIKE ZUMBUR YA RUGA DA GUDUN TSIYA IZUWA KAN ZAKIN. Kafin Zakin ya waigo tuni ya daka tsalle ya dira a gadon bayansa, kawai sai ya shake wuyan Zakin da hannayensa biyu, suka kama mirgin- mirgin akan dutsen. Zakin ya yi iya kokarinsa akan ya kufce daga hannun Muraisu amma ya kasa. Suna cikin mirgi-mirgin akan dutsen nan suka rikito kasa izuwa cikin wannan rami mai tsananin zurfin tslya, Da Zakin da shi Muraisun sai suka hau ihu da kururuwa bisa ganin hallaka muraran. Tun a saman duk su biyun suka sume saboda karfin iskar da ke kadawa wacce ta hanasu yin numfashi. Ba su iso kasan ramin ba sai bayan cikar rabin sa'a. In da Muraisu ya yi sa'a shi ne akan Zakin ya fado. Ta ke gangar jikin zakin ta dagwar gwaje, shi kuwa Muraisu sai ka farsa ta hagu ta karye. Kansa ya bugu da jikin kan Zakin ya tsage jini yai tsartuwa ya baje a kasa sumamme Al'amarin Husnaila kuwa ya yin da taga Muraisu ya shafe sa'oi shida bai dawoba cikin kogon da ya barta sai hankalinta ya dugun zuma ainun ta kasa zaune ko tsaye don haka sai ta fita da gudu daga cikin kogon dutsen ta bazama a cikin dajin na Kirzufa tana gudu da waige-waige tana kwalawa Muraisu kira. Sai da ta shafe sa'a biyu cur! tana yawo a dajin ba ta ga Muraisu ba ba ta ji duriyarsa ba ya z:amana cewa ta gaji ainun da kyar take iya tafiya tana hada kafafu tana tangadi tamkar wadda ta sha giya ta bugu. A haka ta hau kan wannan dutsen wanda Muraisu da Zakin suka yi gumurzu akai. Tana isa kan dutsen ta tsugunna kasa tana haki. Kwatsam! Sai ta yi arba da guntun igar Muraisu. Cikin rarrafe taje ta dauki guntun rigar ta fashe da kuka ta aiyana a ranta cewa lallai Muraisu ya fado kasan wa inan ami ya hallaka. A haka dai ta mike tsaye ta karasa karshen dutsen ta leka kasa sai ta ga ba ta iya gano abinda ke can kasan saboda nisa. A guje ta juyo da baya ta sauko kasan dutsen ta ruga inda wannan rami yake. Husnaila tayi ta gangarawa kasa da gudu har ta iso cikin wannan rami inda tayi arba da gawar Zaki ta ga Muraisu kwance akan Zakin jini na zuba daga kansa ko motsi baya yi. Husnaila ta cuma uban ihu ta ruga izuwa kan Muraisu ta ru:igumeshi ta fashe da sabon matsanaicin kuki domnin à zatonta Muraisu ya mutu. Tana cikin wannan hali ne taji Muraisu ya yi dogon ajiyar num fashi. Cikin tsanar in farin ciki ta ciro salkar ruwa ta sa masa a baki yi kama kwankwada. Husnaila dai ba ta san sa'adda ta bushe da dariyar farin ciki ba. Ai kuwa Muraisu na gama shan ruwan suka sake rungume juna. Husnaila tayi sauri ta janye jikinta daga cikin na Muraisu ta kama gefen rigarta ta yagi kyalle ta daure kansa don tsaida jini. Kawai sai ta dubi Muraisu ta "Idan za ka iya ka cire kan wannan Zaki ka bani yanzu domin an karba ka zamo cikakken mijina". Ba lare da gardamar komai ba Muraisu na daga zaune ya ciro wukar da ke daure a kugunsa ya yanke kan Zakin ya mikawa Husnaila. Tana karba sai ta soke kan Zakin a jikin mashinta sannan ta dubi Muraisu ta ce, "Tashi mu tafi can kogonmu". Maimakon Muraisu ya mike tsaye ko ya ce wani abu sai ya nunawa Husnaila kafarsa. Take ta ga cewar kafar tasa ta hagu ta fara kumbura. don haka sai ta gane cewa ya samu karaya. Husnaila ta mike tsaye ta samo itatuwa sannan ta zo ta gyarawa Muraisu karayarsa ta daure Rafar da itatuwa da tsummokara. Wannan gawar Zaki kuwa sai tà zamo abincinsu, domin wuta ta hada ta gasa naman Zakin wanda tuni ma ya dagargaje. A cikin wannan ramí suka kwana har suka more anarcinsu duk da cewa Muraisu na đauke da karaya a kafarsa. Sai da suka shafe kwana ashírin da daya a cikin wannan rami Husnaila na jinyar Muraisu kuma kullum ita ce take zuwa ta nemo musu abinci da ruwan sha sannan Muraisu ya warke sumul suka yi shiri suka fita daga cikin dajin Kirzufa. Bayan sun yí nisa da baro cikin dajin Kirzufa da kamar tazarar tafiyar zango biyu sai kawaí suka yi kicibus da mutane uku a gabansu. Ba wasu bane wadannan mutane face Barde Kurzal, kuyanga Sabirat da boka Rufyan. Koda suka yi arba da juna sai dukkanínsu suka cika da tsananin mamaki, Sabirat ta ruga da gudu za ta rungume Muraisu sai Husnaila tayi sauri ta sha gabanta ta tsaí da ita ta ce, "Babu wata mace da za ta sake ta6a jikin mijina". Koda jin haka sai Sabirat ta zube kasa ta ce, "Tuba nake ya gimbiya, ki gafarceni". Nan take Muraisu ya baiwa su boka Rufyan labarin duk abinda ya faru tsakanińisa da gimbiya Husnaila a cikin dajin Kirzufa a tsawon kwarakin da suka shude da rabuwarsu da su, sannan ya tambayi boka Rufyan dalilin da ya sa suka ci gaba da zaman jiransu har izuwa wannan lokaci alhalin ka'idar lokacin da aka diba ta wuce? Koda jin haka sai boka Rulyan yai murmushi ya ce, "Ai na yi bincike ne na sm ai nasarar ganowa kuna raye baku mutu ba," Koda jin haka sai boka Ruíyan yaí murmushi ya ce, Yanzu bani labarin gida. A wanne hali mahai fina da jama'arsa ke ciki?" Koda jin wannan tambaya sąi boka Rufyan ya hade fuska ya ce, "Bani da amsar wannan tambaya a yanzu domin ban san komai ba sai dai ka yi hakuri har mu isa can birnin Liruf inda za a yi gagarumin bikin aurenka da gimt iya Husnaila". Muraisu ya ce. "Bani da bukatar wani bikin aure, ni dai kawai burina shi ne na isa gida lafiya na iske mahaifina a raye kuma Ina sami damar yin wannan gagarumin yaki da za ay da abokan gaba". Ba tare da 6ata lokaci ba su Muraisu suka kama hanya suka durfafi birnin Lairus. Bayan sun shafe tafiyar kwana da kwanaki ba tare da fuskantar wata matsala ba gami da taimakon gajarce nisan tafiyar da karfin s hiri sai su yarima Muraisu suka iso birnin Lairus da farkon dare. Tụn daga nesa suka jiyo sautin busa kaho da tambura. AA Misau ke magana Kawai sai yarima Muraisu ya fashe da matsanaicin kuka domin ba a busa Raho da daddare a cikin birninsu face an yi babbar mutuwa. Tabbas yaji ajikinsa cewa Sarki Samral ne ya mutu. Koda ganin Muraisu yana kuka sai su ma su boka Rufyan suka kama kukan. Itama gimbıya Husnaila sai ta rungume Muraisu a lokacin da ta kamu da tausayin sa ta fashe da kuka. Lokacin da su yarima Muraisu suką iso kofar birnin Lairus sai suka iske kofar garin a kulle ruf sai da suka kwan kwasa aka leko kuma aka haska fuskokinsu aka shaida su sannan aka bude musu kofa suka shiga. Suna shiga cikin garin suka iske garin wayam domin gaba dayan jama'ar sun tafi fada. Babu kowa ma a kofar garin daga cikin face Dakarun yaki nasu yawa don tabbatar da tsaro. Su yarima Muraisu suka iso fada inda suka iske ana bikin binne gawar Sarki. Koda jana'a suka hango yarima Muraisu tare da amaryarsa sai aka rugo gareshi gaba daya cikin tsananin farin ciki bisa murnar ganin dawowarsa. A wannan lokaci Muraisu ya daina kuka amma hawaye na sartu akan kumatunsa. Nan dai aka ci gaba da bikin binne Sarki. Bayan an gama binne gawar Sarki Samral ne kowa ya watse sai yarima Muraisu da gimbiya Husnaila suka rungume kabarin Sarki Samral suka ci gaba da zubar da hawaye, basu bar wajen ba saí da dare ya raba sosai sannan suka mike suka tafi izuwa cikin gidan sarautar. Kashe gari da sassafe fada ta sake cika ta batse aka dora Muraisu akan karagar mulki. Nan lake Muraisu ya mike tsaye ya yi dogon jawabi ga jama'ar birnin Lairuf kuma ya tabbatar musu da cewa zai tafiyar da harkokin mulki kamar yadda mahaifinsa ya yi kuma zai ci gaba da shirye-shirye don tunkarar gagarumin yakin da ke gabansu. Haka kuwa al'amarin ya kasance Sarki Muraisu ya sa aka ci gaba da tanadin makaman yaki kuma kullurn ana baiwa Dakaru sabbin dabaru da horo na yakí har tsawon wata bakwai. A wannan lokaci ne gimbiya Husnaila ta sami juna biyu ta shiga laulayi. A ranar da juna biyun ya cika wata takwas ne babban bala'i ya zo birnin Lairuf domin kawai wayar gari aka yi aka ji duwatsun wuta da kibiyoyin wuta na fadowa cikin garin. Nan da nan garin ya hautsine mutane suka firgice aka kama iface-iface da guje-guje. Nan da nan labari ya riski Sarki Muráisu cewar abokan gaba ne suka iso AA Misau ke magana Nan da nan Sarki Muraisu ya yi damara ya kwashi dukkan kayan yakinsa. A dai-dai wannan lokaci ne ciwon nakuda ya kama gimbiya Husnaila al'amarin da ya matukar dugunzuma hankalin Sarki Muraisu ke nan ya rasa abinda zai yi. Kawai sai Sarki Muraisu ya tura aka kirawo wadansu zaratan samari sadaukan gaske su dar bakwai ya hadasu da malarsa gimbiya Husnaila tare da wadansu mata tsofaffi da yara wadanda gaba dayansu adadinsu ya kai dubu uku. Sarki ya dubi wadannan zaratan samari ya ce, "Ga matata da wadannan mata da yara na baku amanarsu. Duk yadda za ayi komai RINTSI DA TSANANI ku fitar da su daga cikin garin nan ta bayan gari. Kada ku ajiye matata a ko ina sai a bakin dajin Kirzufa, na yi imanin cewa matata za ta iya shiga cikin dajin Kirzufa tayi rayuwa a cikinsa koda ita kadai ce. Sauran wadannan mata da yara kuwa ku yi gudun hijira da su izuwa wata kasar dabam. Mu kam zamu je mu fuskanci abokan gaba yanzu. Ko za a karar damu gaba dayanmu ba zamu ja da baya ba, dole ne mu tsaya mu kare mutuncin kasarmu da jama'armu". Koda gama wannan jawabi sai Sarki Muraisu ya sallami wadannan zakwakuran zaratan samari da tawagarsu suka tafi da su gimbiya Husnaila ba tare da Husnaila ta sami damar yin bankwana ba da mijinta Muraisu domin a wannan lokaci ba ta cikin haiyaçinta sakamakon ciwon nakudar da take ciki. Sarki Muraisu da sauran dakarunsa suka yi hawa suka nufi kofar gari har a sannan ba a daina harbo kibiyoyin wuta ba izuwa cikin birnin ba. Koda Sarki Muraisu ya ga yadda gidajen jama'a suka kama da wuta suka AA misau ke magana babbake kuma ya ga gawarwakin jama'ar birjik a ko ina a kasa sai takaici ya kamashi hawaye ya zubo masa. A sannan ne ya tabbatar da cewa maganar boka Rufyan ta tabbata gaskiya. Nan take Muraisu da dakarunsa suka daga garkuwoyin su sama suka rinka kare kibiyoyin da ake harbo musu. A haka aka bude kofar birnin suka zaburi dawakansu suka tasamma abokan gaba. Kaico! Idan mutum ya ga yawan abokan gaba akan yawan su sarki Muraisu dole ne ya tausaya musu domin sun ninkasu sau uku. Koda su Sarki Muraisu suka badu da su Sarki Ishmar sai akakacame da azababben yaki. Ana cikin gumnurzun ne Sarki Muraisu ya ga dan uwansa Huraisu da sarkí Ishmar sun taso masa su biyu a lokaci guda. Ai kuwa sai ya tare su da dakakkíyar zuciyarsa suka ruguntsume da azababben yaki ya wanzu yana mai kai musu SARA DA SUKA cikin tsananin zafin nama suma haka. Shí kansa Sarki Muraisu ya san cewa sarkin yawa ya fi sarkin karfi, amma sai ya jajirce iya karfinsa ya ci gaba da wannan yakin ba tare da tsoron komai ba. Duk da cewa Ishmar da Huraisu sun hada karfi don su hallaka Muraisu sai ya zame musu alakakai har ya sari kowannensu sau biyu. Koda suka ga ya yi musu wannan rauni sai suka kara zage dantse suka afko masa da dukkan karfinsu. Da yake karfin sihirinsu da na sa ya zo đaya sai

Chapter 3 of 4