Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ßµŠÅ Ä MµTµ Littafi Na Biyu (2) Part A Na Abdulaziz Sani M /Gini Marubucin Yaci Gaba Da Cewa SA'ADDA boka Rufyan ya zo jawabinsa sai hankalin yarima Muraisu ya dugunzuma har kwalla ta zo masa, ya dubi boka Rufyan cikin tsananin takaici ya ce, "Yanzu ke nan kana nufin cewa nima mutuwa zan yi nan ba da dadewa ba kuma idan ban auri gimbiya Husnaila ba shi ke nan babu mai kawar da su azzalumaí Huraisu?". Koda jin wannan tambaya sai boka Rufyan yai shiu ya kasa cewa komai, kawai sai ya mike tsaye ya koma can gefe daya ya zauna yana mai sunkui da kansa kas. Cikin fushi yarima Muraisu ya mike zumbur yaje gabansa ya tsaya ya dubeshi a fusace ya ce, "Saboda me ka ki baní amsar tambayata?" Boka Rufyan ya dago kai ya dubi yarima ba tare da shakka ko tsoro ba ya ce, "Ai ba kowacce tambaya ce ke da amsa ba. Ina so ka sani cewa zamanmnu anan bashi da wani amfani, domin zaman Jaki da kaya ne. Idan kana ganin za ka bi wadannan matakai na samun matar da za ka aura ka tashú mu. bi sawunsu gimbiya Husnaila. Dik da cewą tsakaninmu da su akwai tazarata a kalla tafiyar kwana arba'in, zan iya đaurc mana kasa mu riskesu a cikin kwana shida da yini daya, domin ka yakesu ka rabasu da Husnaila idan ka yi nasara sai mu rakaka izuwa bakin dajin Kirzufa mu -tsaya daga wajensa kai da Husnaila ku shiga cikinsa, ba za ku fito ba sai bayan kwana ukun. Sannan mu rankaya mu tafi izuwa can birnin Lairuf domin a yi shagalin bikinku", Lokacin da boka Rufyan ya zo nán jawabinsa sai jikin yarima Muraisu ya yi sanyi, ya koma can gefe ya zauna kuma ya yi tagumi inda ya fada cikin kogin tunani. Ba wani abu yake tunawa ba face gagarumin aikin da ke gabansa wanda ya i karfin tunaninsa. Abinda ya fara fado masa a rai shi ne, ta ya ya zai iya tarwatsa wadannan dakaru guda dubu dari uku shi kadai alhalin KAIFI DA TSINI baya tasiri a jikinsu? Kuma idan za a kwana uku ana yaki da su ba z4 su gaji ba? Abu na biyu, ta ya ya zai iya shiga dajin Kirzufa ya har ya yi kwana uku a cikinsa alhalin mahaifinsa ma da kyar ya iya yin sa'o'i a cikinsa?" Koda Muraisu ya zo nan a tunaninsa sai ransa . ya baci ya ga cewa boka Rufyan ya raina masa hankali, domin bai ga dalilin da zai sa ya umarceshi yin abinda shi kansa ya san cěwa ba zai yiwu ba. A fusace ya sake mikewa tsaye ya nufi kan boka Rufyan gadan-gadan, kawai sai boka Rufyan ya mike ya tareshi ya ce, "Idan ka so ka zare takobinka ka kasheni yanzu take, amma ka sani cewa zabi daya ne garcka cikin biyu. Walau ka koma gida ka zuana ka įira ranar da makiya za su Z0 Su cimu da yaki, kana ji kana gani, ko kuma ka nemi matar aurenka wacce za ta haifa maka dan da Zai kwatar mana 'yanci anan gaba. Ko ka ki ko ka so baka isa ka sauya kaddara ba. Babu makawa sai an ci mu da yaki kuma ba lallai bane ni ko wadannan abokan tafiya namu dayanmu ya yi nisan kwanan da zai ga ranar da za a karbar mana 'yancin mu ba." Koda jin wannan furuci sai jikin yarima Muraisu ya yi sanyi a karo na biyu, ya koma inda yake ya zauna yai shiru bai ce komai ba, ya shuga sabon tunani. Nan take yaji duniyar gaba đaya tayi masa zali, musamman da ya tuna cewa shi fa yanzu bashi da uwa kuma a ko yaushe ma zai iya rasa mahaifinsa. "To wai shin na akan Wane dalili zai damu da duniya tunda bashi da saran masoyi?" Wata zuciyar kuma ta ce da shı, "To mene ne am fanin kaina ka gushe kamar yadda iyayenka za Su gushe ba. tare ta ka bar. zun ar da za a gania Tinka tunawa da kai ba?" Koda ya zo nan a tunaninsa sai hawaye ya zubo masa. Yana dago kai ya ga kuyanga Sabirat tsaye a gabansa. Sabirat ta zauna kusa da yarima Muraisu ta dubeshi a nutse, sannan ta ce, ""Ya kai jarumin kwarai, ka yi sani cewa namijin baya kuka, kuma bai san tsoro ba. Shi ne wanda baya shakkar shiga ckin kowanne irin bala'i kuma shi nc wanda bai dauki RAI a bakin komai ba, muddin bukata za ta biya." Koda yarima Muraisu yaji wannan batu sai dukkanin tsoro ya kau daga cikin zuciyarsa kawai sai ya dubi Sabirat ya yi murmushi ya ce, "Madallah da kuyanga ta gari wacce ke yiwa ubangidanta tuni bisa abinda ya kamaceshi." Gama fadin hakan ke da wuya sai Muraisu ya mike tsaye ya dubi Boka Rufyan da Badakare Kirzal ya ce, "Ma za ku samu akan hanya wacce za ta kaini inda zan riski gimbiya Husnaila da jama'arta a cikin kankanin lokaci" Kafin Muraisu ya gana rufe bakinsa tuni Kurzan da Rufyan sun mike zumbur sun kama dawakansu sun haye. Saoirat da Muraisu ma suka yi sauri suka hau nasa dawakan. Kurzal ne ya wuce . kan gaba, Boka Kufyan na-biye da shi sannan su yarima. Dukkaninsu suka sukwani dawakansu da gudun tsiya suka nausa cikin daji. Nan fa Yarima, Kurzal da Sabirat suka rinka ganin abin al'ajabi, domin cikin dakiku kadan suka rinka shafe tafiyar sa'o'i. Nan da nan suka ga sun zO wani wuri maj irin yanayi dabam da sauran dazuzzukan da suka wuce. Shi dai wannan wuri da suka zo ya kasance daji ne mai yawan lumshi tamkar rana ba ta taba baiyana ba a cikinsa. Bishiyoyin da ke cikinsa kuwa duk dogaye ne masu fala-falan ganyaye, haka kuma akwai duwatsu manya-manya in-in masu tsawo da fadi. Koda 1SOwar Su yarıma wannan wuri sai Kurzal yai sauri ya sauko daga kan dokinsa ya kifa kunnensa akan kasa yai nazari, sannan ya mike tsayc, ya dubi yarima ya ce, 'Ya shugabana nan gaba kadan tafiyar 'yan dakiku akwai mutanc sama da guda dari biyu a labe cikin duhuwar bishiyoyi". Koda jin haka sai Boka Rulyan ya yi murmushi, sannan shuma ya dubi yarima ya ce, "Sai ka shige ciki ka riskesu ka karbo gimbiya Husnaila ta kowanne hali. Mu kam amu Jiraka ne nan har iZUwa tsawon sa'a bakwaj. Jdan ka fito da nasara sai mu rakaka izuwa bakin dajin KirZula, acan mas mu jira izuwa sa'adda za ku kwana uku a cikinsa ku fito, sannan mu rankaya gaba daya izuwa gida. Idan kuma mu ka ji shiru ba ka fito ba, mun san ccwa ka hallaka sai mu juya mu koma gda". Yarima Muraisu ya gyada kai ya ce, "Haka za a yi". Kawai sai ya juya zai shiga cikin wannan daji mai kwarjini, ai kuwa sai ya hada ido da kuyanga Sabirat. Bisa mamaki sai ya ga hawaye ya zub0 a idanunta. Boka Rufyan da Barde Kurzal kuwa, ko kwalla babu a cikin nasu idanun. Nan take Muraisu yajı zuciyarsa ta sosu kuma ya cika da mamakin dalilin da ya sa Sabirat ta zubar masa da hawayc, alhalin bai kasance komai face ubangidanta. gareta ba Shin tsananin sabon da tayi da shi ne ya sa ta Zubar da wannan hawaye ko kuwa so nc irin wanda ke tsakanin mace da namiji? Nan fa Muraisu ya kasa baiwa kansa amsa, kawai sai ya kau da kai ga barin kallonta, ya kunna kai cikin wannan daji yana mai zare takobinsa. Karar zare takobin tasa ce ta fargar da wadannan dakaru guda dari uku masu gadin gimbiya Husnaila, su ma sai lkowanncnsu ya zare tasa takobin. A wannan lokaci gimbiya Husnaiíla tayi tumbur a cikin wata korama tana wanka, Wasu kuyanginta guda hudu suń rike manyan mayafai sun kare inda take don kada wadannan Dakaru su ga tsiraicinta. Kwatsam! Ba za to ba tsammani sai gimbiya Husnaila da kuyanginta suka ji an barke da azababben yaki banda karar karafa babu sautin da ke cika dodon kunne, har amsa kuwwa yakea cikin dajin. Ko kadan gimbiya Husnaila ba ta tsorata ba, domin ba ta ma san mene ne tsoro ba a rayuwarta, amma su kuyanginta sai suka firgice, jikinsu gaba đaya ya kama kyarma. Nan da nan suka hada gumi sharkaf. Koda gimbiya Husnaila ta ga halin da kuyanginta suka shiga sai ta daka musu tsawa ta ce, "Idan ba za ku iya ci gaba da aikinku ba zan sa takobi duk na sareku". Koda jin haka sai dukkanínsu suka nutsu akan aikinsu. Ita kuwa Husnaila sai ta ci gaba da wankanta tamkar a cikin gidanta take. Cikin tsananin gudu yarima Muraisu ya.ratsa cikin wadannan Samudawan dakau da nufin ya wuce ta tsakiyarsu ya isa inda gimbiya Husnala. take wahka, ámmna sai wadannan Dakaru suka ce wane shi, nan take suka yanyameshi suka haushi da sara da suka. Shi kuwa ya wanzu yana mai karcwa da mai da martani. Shi kansa sai da ya yi matukar mamaki bisa ganin inin tsananih zafin naman da ya samu a yanzu wanda a da can ya tabbatar da cewa bashi da irinsa, in da ya sami matsala shi ne, tunda Dakarun suka kewayeshi a waje daya aka ci gaba da gumurzu sai ya kasa karawa gaba. Domin sun babbake hanya babu ta inda zai iya wucewa. Abinda ya fi daga masa hankali shi ne, duk sa'adda ya sari dakarun ko, kuma ya sokesu da takobinsa sai ya ji kamar karfe ya kaiwa hari, domin tartsatsin wuta ne ke tashi gami da hayaki. Su kuwa duk sa'adda suka sari jikinsa makamin baya tasiri, amna sai jikinsa ya gaya masa, domin ji yake kamar an sa shi a cikin turmi ana yi masa lugude da tabarya. Hakika Muraisu ya yi mamakid a ya ga karfe bai ci jikinsa ba, domin shi dai ya san bashi da wannan sihiri, amma da ya tuna cewa ai ya sami zafin nama irin wanda bashi da shi a da sai ya gane cewa lallai akwai sabon al'amari wanda ya zo masa bako tuntuni. "Mene ne sabon wannan al'amarin ?" Muraisu ya tambayi kansa a cikin zuciya, amma sai ya kasa ftar da amsa. Lokacin da dakarun suka ci gaba da laflawa Muraisu makanansu a dukkan jikinsa, sal ya Zamana cewa ya kasa ci gaba da yaki, har ma ya yarda takobinsa kuma ya fadi kasa. Koda ganin haka, sai suka ci gaba da tattakashi, nan da nan suka yi laga-laga da shi, jini ya rinka tsartuwa daga cikin bakinsa da hancinsa. Kafin cikar 'yan dakiku ya baje wanwar a kasa yana num fashi da kyar ko yatsansa guda ya kasa mnotsawa. A wannan lokaci ne. shugaban dakarun ya yi mnusu inkiya suka ja da baya sannan ya dubesu gaba daya ya ce, "Duk yadda aka yi wannan jarumin ya fito ne daga kasar Lairus, kuma ya zo ne domin ya sace gimbiya Husnaila ya tafi da ita. Tunda dai makami ya ki ya yi tasiri a jikinsa, ma za ku kamashi da karfin tsiya ku murde masa Wuya ku jefa gawarsa cikin wancan ramin". Shugaban dakarun ya yi nuni da hannunsa izuwa ga wani rami mai zurfin gaske wanda ya kai kamu dari da tamanin. Kamar a cikin kunnen yarima Muraisu shugaban dakarun' ya yi wannan bayani, domin ba za to ba tsammani, sai suka ga Muraisu ya mike Zumbur! ya daka tsalle sama ya dira a kan kafadar daya daga cikinsu, Cikin bakin zafin nama Muraisu ya kama kan Badakkaren da ya dira a kafadarsa ya mrde masa wuya. Take Badakaren ya sulale kasa matacce, ji ka ke dam! kamar giwa ta fadi. Zan dakata anan saikuma wani lokacißµŠÅ Ä MµTµ Littafi Na Biyu (2) Part B Na Abdulaziz Sani M /Gini KAICO! Ashe tsuliyar dodo Muraisu ya tabo, domin suna ganin ya kashe daya daga cikinsu sai suka yì kukan kura suka afka masa gaba dayansu aka sake kacamewa da azababben yaki. Wannan karon dayansu bai samį damar koda taba jikinsa ba, domin wata iriyar zulliya ya rinka yi a tsakankaninsu ya inka kama hannaycnsu da kafafunsu yana kakkaryawa tamkar yana karya sillen kara. Gumbiya Husnaila da ke can cikin korama tana ta wanka, sai ta fara jiyo ihun Dakarun tsaronta. Al'amarin da ya matukar ba ta mamaki ke Cikin hanzari ta karbi mayafi daga hannun kuyanginta ta daura iya kirjinta, sannan ta fito daga cikin koramar. Ko tufafinta ba ta tsaya sawa ba ta durfai inda ake wannan gumurzu. Su kuwa wadannan kuyangi na ta sai suka ruga izuwa cikin daji a dimauce ba tare da sanin inda suka dosa ba, saboda tsananin razanar da suka yì domin sun san cewar bala'in da ya sa wadannan samudawan dakarun ihu ba Karami bane. Tun daga nesa gaimbiya Husnaila ta hango dakarunta suna zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona. Koda ta kara matsawa kusa sai ta ga ashe wanda yake ragargazar su ma dan mitsitsı ne akansu, bai fi ta kwatantashi da dan tsako ba a cikin tsakiyar dubunnan Muzurai. A iya rayuwar gimbiya Husnaila yau ne ranar farko da ta ga abinda yai matukar ba ta mamaki, amma ba wai burgcta ya yi ba. Koda ta ga yadda Muraisu ke ta kakkarya dakarunta suna zubewa kasa sai ta sunkuya ta dauki mashin daya daga cikinsu ta ike ta tsaya cak! Tana jiran ta ga abinda zai faru. Kafin cikar rabin sa'a Muraisu ya zubar da dukkan dakarun a kas suna ta koke-koke da iface- iface, babu đayansu da ya iya mikewa tsaye. Koda Muraisu ya ga ya gama da dakarun sai ya yi arba da kyakkyawa Husnaila a tsaye a gabansa ike da mashi, fuskarta a murtuke babu annuri, kuma ga ta a tsayc kyam babu wata alamar tsoro a tare da ita, Koda ya ga kyakkyawar surar jikinta da kuma wani kyakkyaw an gashin kanta sar ya rude ya dimauce, bai san sa'adda ya nufeta ba gadan-gadan da nufin ya rungumeta. Koda ya ragc bai fi saura taku daya su hadu ba sai ya kai ma ta raruma, ita kuwa ta goce ta soka masa mashi a gefen kirjinsa. Bisa mamaki sai ya ji mashin ya nutse a cikin kirjin nasa, bai san sa'adda ya kwalla ihu ba. Husnaila ta zare mashi jini yai feshi daga cikin kirjin Muraisu, ya sake rusa ihu a karo na biyu. Jiri ya debeshi ya yi luu!! kamar zai fadi kasa, amma sai yaı ta maza ya tsaya bisa kafafunsa. Husnaila ta sake saitashi da mashin ta tsaya cak! A waje daya suka fara kallon-kallo. Daga can sai ta dubeshi ta kyalkyale da dariya a cikin sautin murya mai zakin gaske, sannan ta hade rai ta ce, "Kai wayc, kuma me ka ke nufi da ni? Saboda mne ka zo ka ragargaza mini dakaruna? Ka san kO ni wace ce kuwa? Ka amsa mini tambayoyina da gaskiya ko kuma na hallaka ka yanzzun nan!" Koda jin wannan batu sai Muraisu ya bushe da dariya sannan ya ce, "Ni ne yarima Muraisu dan Sarki Salmar mai binin Laius, wato babban makiyi ga dan uwanki Sarki Ishmar. Ina mai sanar da ke cewa na baro gida ne domin neman matar da zan'aura, kuna ba wata ba ce wadda zan aura face ke din nan". Koda jin haka sai Husnaila ta tuntsure da dariya, 1lokaci guda kuma ta hade rai ta sunkui da kanta kas tana tunani. Muraisu ya katse ma ta hanzari ya ce, "Ya ke Husnaila Sarauniyar mata, me kike tunani ne?" Husnaila ta dubeshi ta ce, "Mamaki nake bisa daıyar da na yi yanzu, domin kaine mutum na farko da ya ta6a ganin dariyata.. Hatta dan uwana kuwa Sarki Ishmar sai dai ya Ce ya ga murmushina ko hawaye na, amma bai taba ganin dariyatą ba ko kukana'". Da jin haka sai Muraisu ya yi mumushi ya ce, "Al ni mutum ne na musamman a cikin mutane, da sannu za ki gasgata haka". Husnaila ta ce, "Ai kuwa na ga alama tunda ban taba sukar wani abu da makami ba ya rayu sai kai. Shin za ka iya gaya mini sirrin da ke tattare da kai?" Muraisu ya cire wani rawani da ke ikin damararsa ya daure kirjinsa lamau don tsaida jini, sannan ya dubi Husnaila a nutse ya ce, '"Ina zaton dai irin sihirin da ke tare da ke shi ne a tare dani, domin gashi dakarunki sun kasa cutar da ni da makamansu, amma ke gashi kin cutar da ni". Husnaila tayi murmushin mugunta, sannan ta ce, "Ka yi babban kuskure da kake tunanin za ka aureňi, domin abu ne wanda ba zai taba yiwuwa ba Babu wani da namiji da ya isa ya mallakeni, idan kuma kana ganin za ka iya ka jarraba!" Muraisu ya gyara tsayuwarsa sannan ya ce, "Ai babu wani abu wanda ba zai yiyu ba a wannan duniya, sai dai ba a jarraba b. Ina da labari cewa dan uwanki ya tsarcki da dukkan sihirin tsafinsa, amma ni nayi imanı cewa sirin da nake da shi a yanzu ke baki da shi tunda shi kansa dan uwanki har yanzu bai samu ikon shiga dajin Kirzufa ba. Ba shi da wani buri wanda ya fi haka. Ina tabbatar miki da cewa har ya mutu ba zai cika wannan buri na sa ba, ni kuwa mahaifina ya shiga dajin Kirzufa, Đima kuma zan shigeshi yanzu, kuma tarc da ke, kuma dana ma sai ya shigeshi. Ina mai shawartarki da ki bani hadn kai mu tafi cikin salin-alin, idan kuwa kika ki, to fa ko ta tsiya-tsiya sai mun je". Sa'adda Husnaila taji wannan batu sai ta sake bushewa da dariya a karO na biyu, sannan ta hade fuska ta ce, "Ai sai na ga yadda za a raba hanta da jini!" Kafin Muraisu ya budi baki ya ce wani abu luni Husnaila ta dako tsalle a sama daga inda.take kamar an cillota daga cikin baka ta sake kawo masa mummnunan hari da wannan mashi a ciki. Gimbiya Ilusnaila ta ce, "Ta ya ya aka yi ka san cewa ni ce Sarauniyar kyawawa ta duniya?" Muraisu ya ce, "'Saboda mu a wannan nahiya lamu gaba daya babu kamarki". Gimbiya Ilusnaila ta cC, "Ba zan iya gaya maka ba, saboda ba kowacce tambaya ce ke da amsa ba" Muraisu ya ce, "Maganarki dutse ce, amma akwai gyara". Gimbiya Husnaila ta cc, "To mene gyaran?" "Bari na matso kusa na yi miki bayani, domin wani babban siri ne wanda ba kowa ake fadawa ba'". Kai tsaye Muraisu ya tali inda Gimbiya Ilusnaila take tsaye kamar wani abu zai rada ma ta a kunnc. Koda ya iso daf da ita sai ya shammaceta cikin bakin zafin nama ya debo hodar banju daga aljihunsa ya watsa ma ta a fuska. Nan take Gimbiya Husnaila taji jiri ya kwasheta, la tafi luu! za ta fadi kasa, sai ya sunkuya uya sabata a kaladarsa ya juya da baya ya nufi inda ya baro su boka Rufyan suka tsaya suna Jiransa. Barde Kurzal, kuyan ga Sabirat, boka Rufyan na tsayc suna hangen hanyar da Muraisu ya bi cikin zullumi da fargaba. sai kawai suka hangoshi ya nufosu sabe da Gimbiva Jusnaila a kafadarsa, ga raunı a kirjinsa daure cikin shátar jini, yana tafe yana raba kafa kamar wanda ya sha giya ya bugu. Koda ganin haka sai Barde Kurzal da boka Kutyan suka ruga gareshi cikin matu kar farin ciki suka taroshi. AA Misau Barde Kurzal ya karbi Gimbiya Husnaila ya taho da ita inda Sabirat ke tsaye, shi kuma boka Rufyan ya dauko Muraisu suka kawosu bakin wata bishiya suka shimfidesu. Cikin hanzari boka Rufyan ya kwance raunin Muraisu yana matukar mamakin yadda aka yi ya sami raunin alhalin ya san cewa Sarki Salmar ya bashi gashin sihirinsa. Nan da nan yai sauri ya sa ma sa gan magani akan ciwon nasa, sannan suka bashi ruwa ya sha. Ita kuwa Gimbiya Ilusnaila, tunda aka shim fideta ta ci gaba da barcinta ko motsawa ba ta Bayan Muraisu ya dawo cikin haiyacinsa sai boka Rufyan ya dubeshi cikin jınjinawa ya ce, "Ya kai namijin duniya, dodon maza, ya ya aka yi ka Saml Wannan gagarumar nasara har ka daukO gimbiya Husnaila daga cikin tsaron da aka ba ta?". Koda jin wannan tambayar sai yarima Muraisu ya kwashc labarin duk abinda ya faru ya Zalyane musu. Koda jin al'amarin sai duk su ukun suka sake cika da mamaki, musanman boka Rufyan wanda ytai shiru ya shiga tunani mai zurli. Daga can sai ya dago kai ya dubi yarima Muraisu yą ce, "Ya shugabana hakika shirin sarki Ishmar ba na wasa bane, ban taba tsammanin yana da karfin sihiri kamar haka ba. Ina tabbatar maka da cewa duk wannan jarumtaka da Husnaila ta yi ba gaskiya ba ce, tsabar karfin sihirin tsafi ne kawai. Tabbas itama tana da gashin sihiri a jikinta, amma abinda na ke zargi shi ne, ba irin naka bane a Jikinta, shi ya sa mahaifinta ya kasa shiga cikin da in Kirzufa. Hakika ba don kayi wannan hikima ba ta watsa ma ta banju a fuskarta da babu yadda za a yi ka iya kamota har ka zo da ita nan wajenmu. Ina son ka sani cewar dole ne yanzu ka hanzarta zuwa dajin Kirzufa da Husnaila kafin hodar banjun ta saketa nan da tsawon sa'a daya jal. Idan har ta farfado ko duniyar nan za ta taru a kanta ba za a iya taiya da ita ba, kuma idan ma ka shiga da ita cikin dajin Kirzufa sai ka sa ido sosai a kanta don za ta yi iya shammatarka tayi maka irin abinda ka yi ma ta". Koda jin wannan batu sai Muraisu ya mike zumbur! ya dauki gimbiya Husnaila ya đorata akan doknsa, sannan shima ya hau nasa dokin, suma Su Rufyan sai suka yi sauri suka hau nasu. Barde Kurzal ne ya wuce kan gaba suka zaburi dawakansu da gudu suka bishi a baya. Basu tsaya a ko ina ba sai sai a bakin dajin Kirzufa. Lokaci guda su duka suka yi tirjiya, sannan suka sauko daga kan dawakansu. Yarima Muraisu ya sake đaukar gimbiya Husnaila a kafadarsa. Har ya juya zai shigc cikin dajin na Kirzufa, sai ya Waiga ya dubesu su ukun cikin wani iin kallo mai nuna alamun bankwana, wanda ya sa duk su ukun suka ji tsigar jikinsu ta tashi, kuma dukkaninsu sai zuciyoyinsu suka karaya, nan take tausayin yarima ya tumukesu, saboda sanin cewa masifar da zai shiga yanzu ta ninka wacce ya shiga a baya sau dubu. Muraisu ya tsaida hankalinsa a kan boka Rufyan ya ce, "Bani labarin mahaifina, shin hạr yanzu yana raye ko kuwa ya mutu?" Koda jin wannan tambaya sai boka Rufyan- yai shiru ýa kasa cewa komai, kawai ya kurawa Muraisu idanu. Barde Kurzal da kuyanga Sabirat kuwa, sai hankalinsu ya dugunzumna, suka kama raba idanu a tsakanin Muraisu da Rufyan, jira suke kawai su ji amsar da Rufyan zai bayar. Tsawon 'yan dakiku Rufyan bai ce komai ba, kuma bai fasa kurawa Muraisu idanu ba. Koda ganin haka sai idanun Muraisu suka domin ciko da kwalla har hawaye ya subuto masa, ya ji a jikinsa cewa MAZA SUN FADI! Kawai sai ya juya ya durfafi cikin dajin Kirzufa kai tsaye, a lokacin da ya ji dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyarsa, ji yake ina ma mutuwar za ta zo ta daukeshi da ya fis amun nutsuwa. Da shigar su Muraisu dajin Kirzufa sai ya fara arba da dabbobin daji ii-ii, kuma manya-manyan ababan tsoro, domin sun kasance na usamman ba irin wanda ido ya saba gani ba. Tsananin kwarjinin dabbobin ya wuce misali, ko kwatance. Tsakanin Muraisu da dabbobin sai kallon- kallo kawai, dayansu bai yi yunkurin koda zuwa kusa da shi ba, shima Muraisu ko kallonsu bai yi ba, kawai sau ya je karkashin wata bishiya ya shimfide Husnaila, sannan ya koma gefe daya ya tsugunna ya kura ma ta idanu, kuma ya fada kogin tunani. Abinda ya fara fado masa a rai shi ne, yanzu ya zai yi da Husnaila idan ta farka ta tsinci kanta a cikin dajin Kirzufa? "Lallai akwai kazamar rigima a (sakaninmu" Muraisu ya baiwa kansa amsa. "Kuma saí tayi yunkurin guduwa...Amma kuma ai boka Rufyan ya gaya mini cewar ba tưisa ta fice daga cikin dajin ba har sai mun yi kWana uku a cikinsa, saboda haka zan zuba

Chapter 1 of 4