Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
ma ta idanu ne kawai na ga iyakar gudun ruwanta. " Haka dai Muraisu ya yi ta sake-sake a cikin zuciyarsa har ya gaji, shima saí ya kishingida a jikin wata bishiya. Abinka da gajiyayye, bai dađe da kishingida ba sai barci ya kwashe shi. Bayan 'yan dakiku kadan kuma sai Husnaila ta farka. Koda la bude idanu ta tsinci kanta a cikin wani iin daji na musamman sai ta takarkare ta tsandara uban ihu. Muraisu ya farka firgigit! a razane, dabbobin cikin dajin kuwa, hatta sauran Rananan kwari da tsintsaye sai da suka razana, suka kama guje-guje. Duk dabbar da tayi arba da su Muraisu sai ta yıyo kansu: Nan fa aka kasa uban tserc tsakanin su Husnaila da dabbobin dajin gaba daya. Babu abinda zai baiwa mutumn mamaki face Lsananin gudun da Muraisu da Husnaila ke yi tamkar akan iska suke yinsa ba a kan kasa ba. Duk su biyun sun yi matukar mamakin irin gudun nasu, domin tamkar walkiya suke gifta komai, sai dai karfin gudun nasu duk ya zama na banza, domin duk sa'adda suka waiga bayansu sai su ga dabbobi kusan guda dubu daf da su. Duk inda suka dauke dabbobin suke sa nasu. sawayensu anan da Babu abinda ya fi firgita su Muraisu face cafka kawo musu yadda dabbobin ke bakunansu, don su cinyesu, musamman wani katon Zaki wanda idan ya wangame bakinsa sai ka ga kamar ijiya mai zurfi da fadi aka bude. Sai da su Muraisu suka shafe sa'a guda cif! Suna falfala natsanaicin azababben gudu, sannan suka hango wani katon tsauni a gabansu. Basu tsaya jiran komai ba suka hau kan tsaunin a guje, har sai da suka je can. samansa sanann suka waigo baya. Bisa mamaki, sai suka ga gaba dayan dabbobin sun tsaya a kasan tsaunin đayansu bai yì yunkurin hawowa ba. Al'amarin da ya matukar basu mamakia ke nan, Kawai sai suka zube kasa a saman tsaunin suka kama haki, da fitar da numfashi da saurí da sauri. A sannan nc fa kishirwa ta ischsu, kuma gashi babu damar shawagi a kasan tsaunin tamkar an basu gadin abinda ke kan tsaunin. A dai-dai wannan lokaci ne Husnaila ta dubi Muraisu cikin harara da fushi ta ce, "Ya ya aka yi ka kawoni cikin wannan daji?" Koda jin wnanan tambaya sai Muraisu ya yi murmushi ya ce, "Ba wannan tambayar ya kamata ki yí mini ba a yanzu, kamata ya yí ki tambayeni a ina zamu samu ruwan sha?" Husnaila ta sake murtuke fuska ta ce, "Ba ruwa ne a gabana ba. Ka mayar da ni inda ka daukoni, domin ina da bukatar na koma gida kafin magariba tayi". Koda jin wannan batu sai Muraişu ya bushe da dariya har da bingirewa Kasa, sannan ya nutsu ya ce, "Ai idan har kin ga kin fita daga cikin dajin nan sai kin yi kwanaki uku cikakku a cikinsa!" Cikin fushi da mamaki Husnaila ta mike tsaye ta ce, "Ai kuwa idan ka ga na kara koda dakika đari ne a cikin wannan daji sai idan bana numfashi. " Koda gama fadin hakan sai ta mike tsaye ta fara saukowa kasan tsaunin. Muraisu ya bita da kallo kawai ko motsi baiyi ba daga inda yake zaunc. Lokacin da ya rage saura bai fi taku biyar ba ta iso kasan tsaunin, sai kawia ta ga wannan ma ta haikan Zaki ya taso turmusheta. Ba shiri ta juya da baya da gudu ta koma kan tsaunin inda Muraisu yake. Koda ganin abinda ya faru sai Muraisu ya kama yi ma ta dariya. Al'amarin da ya kara tunzurata ke nan, ta kamu da tsananin fushi. Bisa dole taje gefe daya, nesa kadan da inda Muraisu yake zaune itama ta zauna. Babban abinda ya i daurewa Husnaila kai shi ne, ya ya ita da bata da tsoro ko kadan amma taji tana tsoron dabbobin wannan dajı? Kawai sai ta dubi Muraisu ta ce, "Wai shin wannan wane daji ne muka shigo?" Muraisu ya yi ajiyar zuciya sannan ta ya ce, "VWannan shi ne dajin KIRZUFA! Kanar yadda na gaya miki da farko sai mun yi kwana uku a cikinsa ni da ke, a sannan ne na sami Zan sauya miki rayuwarki, kuma soyayyarki, mu tafi izuwa birninmu na Lairuf mu yi aure". Kafin Muraisu ya gama rule bakinsa tuni Musnaila ta tofa masa yawu a fuska, Cikin tsananin fishí ya mike tsaye zumbur! ya zare takobinsa, itama saí ta mikc Zumbur! ta rike mashinta suka fara kallon-kallo, har gaba dayan jikin Muraisu na tsuma saboda fushi, domnin a íva rayuwarsa ba a taba yi masa iin wannan wulakancin ba a matsayinsa na dan Sarki, kuma gawurtaccen jarumi. Husnaila ta dubcshi a wulakance ta ce, "Na tsancka! Kuma na tsani dukkan zuril'arka, Har abada ba zan ta6a sonka ba, kuma ní da dan uwana Sarki Ishmar sai mun baje birninku, mun konc dukiyoyinku, mun kame matanku da 'ya'yanku sun zama bayinmu. Mazajenku kaf sai mun kashesu", Koda jin wannan batu saí Muraisu yaji ya tsani lusnaila kamar yadda yaji ya tsani mutuwarsa. Duk wannan tsananin kyawu nata sai ta rama kamar dodanníya a idanunsa. IHar ya yunkura zai afka ma ta su yi yaki, sai ya tuna cewa ai sihiri ne a jikinta wanda ya sa ba za ta laba son wani da namiji ba face ta ci ta sha daga abubuwan da ke cikin wannan daji na Kirzufa na tsawon kwana uku. Koda tuna wannan al'amari sai jikin Muraisu ya yi sanyí, ya fasa afkawa Husnaila ya koma ya zauna. Koda ganin haka, sai itama ta koma inda take ta zauna. A sannan ne fa kishirwa ta ci gaba da addabarsu. Babu shiri suka mike tsaye suka kama yawo akan tsaunin kowannensu na neman ruwa, amma babu ko alamarsa. Duk sa'adda suka leko kasan tsaunin kuma sai suka ga wadanann dabbobi suna nan suna kewaya tsaunin, jira kawia suke su sauko su afka musu, Bisa dole suka hakura. Lokacin da 'yan sa'oi suka kara shudewaa sai magariba ta doso kai, gari ya fara duhu, a sannan ne tsananin kishirwa tasa suka baje a kasa suka kama num fashi sama-sama kamar za su muti. Sai da kowannensu ya fara suma, kwatsam! ba zato ba tsammani sai hadari ya gangamo aka fara tsawa da walkiya gami da wata irin gagarumar iska mai karfin gaske. Kafin a jima ruwan sama ya tsuge karmar da bakin kwarya. A sannan ne Muraisu da Husnaila suka farfado, sai kowannensu ya wangame bakinsa suka kama shan ruwan, har sai da suka koshi, sannan suka dawo cikin haiyacinsu, sai dai babu inda zå su fakewa wannan ruwan saman, dole suka hakura ruwa yai ta dukansu har izuwa tsawon sa'a guda, sannan ruwan saman ya dauke dif. Nima Kuma Wanga Ruwa Yana Daukewa Nima Na Dauke Daga Typing hhhhh Zan dakata anan sai kuma wani lokaci Zamu cigaba Insha Allah Likes and comments Domin hakan na sa mu cigaba Ga masu shA award whtsp grp https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QBUSA A MUTU Littafi Na Biyu (2) Part C Na Abdulaziz Sani M /Gini AA Misau Ke Magana MURAISU DA LUSNAILA SUKA MIKE TSAYE SUKA kallo juna kowa ya kau da kai. A wannan lokaci ngar jikin Husnaila ta dame sakamakon wan saman da aka laftla, hakan ne yasa surar jikinta ta baiyana karara a ili tamkar tsirara take, Roda Muraisu ya ganta a cikin wannan hali sai ya ude ya dimauce vaji ya kamu da tsananùn sha'awa, amma sai ya danne zuciyarsa ya juya ma ta baya. Lokacin da suka leko Rasan tsaunin sai suka cika da mamaki, domin babu dabbobin dajin a wajen ko guda daya. Da yake suna jin yunwa matuka, sai suka sauko daga kan tsainin. Suna saukowa sai suka tsaya cak! Muraisu ya juya ma ta baya don baya son ya ci gaba da ganin tsiraicinta. Cikin fushì Husnaila ta bude baki ta ce, "Saboda me za ka rinka juya mini baya alhalin kaine ka kawoni cikin wannan masi faffen daji? To ka sani cewa ni yanzu yunwa nake ji, saboda haka sai ka je ka nemo mìni abìnda zan įi"'. Tana gama fadin hakan taje ta zauna akan wani dutse. Cikin matukar harzuka Muraisu ya juya a fusace ya ce, Yadda kike takama ke yar Sarauta ce nima haka nake. Ni da ke kowa ta sa ta fissheshi a cikin wannan dajı. Idan ma za ki iya sai ki yi kokarin fita daga dajin". Koda gama fadin hakan sai Muraisu ya juya ya tafi ya bar Husnaila a zaune tana binsa da kallo gami da harara da tsananin kiyayya, taji kamar ta ruga kansa ta tsircshi da mashin da ke hannunta. Muraisu ya ralsa izuwa cikin dajin Kirzufa, domin neman abinda zai ci, wata irin iska mai karfin gaske ta fara bugawa, bishiyoyi suka kama rangaji kamar za su kakkarye su fadi kasa. Da yake dama an tafka ruwan sama sai dajin gaba daya ya dume da sanyi, gashi kuma magariba ta yi, duhu ya fara. Nan take Husnaila taji ta kamu da tsananin tsoro, kuma gashi saura kiris Muraisu ya bace ma ta da gani, domin ya yi nisa sosai daga inda take hangoshi. Kawai sai ta mike zumbur! ta ruga da gudu izuwa inda yake tana rike da mashinta, ta riskeshi suka jera suna tafiya, amma ko kallon juna ba su yi - ba, kuma kowannensu fuskarsa a murtuke take. Haka dai suka wanzu suna ta ta fiya a cikin dajin suna hange-hange da waige-waige ko za su ga abinda za su iyaci ya magance musu yunwar da ke addabarsu, amma babu. Hatta bishiyoyin dajin babu mai fure a jikinta bare a samnu dan itaciyar da za a iya ci. Sai da Muraisu da Husnaila suka shafe kusan rabin sa'a suna tafiya a dajin basu ga koda tsuntsu ba ko wata karamar dabba wacce za su lya rafkewa su yanka su ci. A dai-dai wannan lokacin ne suka jı sun gaji likis, saboda haka sai suka tsaya suka zauna a kasa dirshan suna haki. Duk sa'adda suka kalli juna sai kowa ya harari dan uWansa su kau da kai. Kwatsam! ba zato ba tsammani sai suka ga wata katuwar jimina mai giman ban mamaki ta sauko daga sama ta dira a cikin wadansu ciyayi ta kama kiwo abinta. Nan fa Husnaila da Muraisu suka dubi juna suka yiwa kansu inkiyar su tashi su afkawa jminar domin su sami abinda za su ci. Lokaci guda suka mike tsaye a tare. Muraisu ya zare takobinsa, ita kuma Husnaila ta mikar da mashinta suka durfafi inda Jiminar takc. A wannan lokaci Jiminar ta juya musu baya tana ta tonon kasa da bakinta. Koda Jiminar taji motsin taiya a bayanta sai ta dago da kanta tå tsaya cak! kamar gunki suma sai suka tsaya cak amma da Jiminar ta ci gaba da tonon kasa sai su ma suka ci gaba da durfafarta. Da suka ga ba ta sake tsayawa ba sai suka ruga da gudu izuwa kanta. Manufarsu ita ce, su- soketa da makaman hannunsu. Koda ya rage bai fi saura taku daya jal a tsakaninsu da Jiminar ba, sai ta waigo cikin bakin zafin nama ta makesu da dogon wuyanta. Saboda karfin makuwar sai da suka yi sama da baya suka fađo kasa a tare a matukar galabaice. Duk su biyun sai suka raina dukkanin jarumtakarsu suka san cewa tabbas sun shiga dajin Kirzufa. Kafin su yunkura su mnikc tsayc sai jiminar la taso musu haikan, nan da nan ta iso garesu ta karwa Husnaila wawar caka da tsinin bakinta. Cikin zalin nama Muraisu ya fisgo Iusnaila daga inda take kwance. Bakin Jiminar ya caki kasa, ya nutsc gaba daya a cikinta. Koda Jiminar ta zarc bakinta sai ga rarmi zururu mai tsawo da fadi wanda za a iya binne jarini a cikin. Nan fa aka fara masifa ffen artabu tsakanin Jinina da su Muraisu, la wanzu tana mai kai musu suka da tsirin bakinta, su kuma suna buge bakin na, lá da makaman hannunsu. Duk sa'adda makaman nasu suka hadu da bakin na la sai ka ji Rara Ral! kamar karfe da karfe ne suka hadu. Sai da suka shafe lokaci mai dan tsawo suna Wannan gumurzu, ya zamana cewa sun kasa taba jikin Jininar domin ta fisu nama, kuma gashi ko kadan ba la gajiya, su kuwa sai suka fara sarewa. Ana cikin haka ne Jiminar ta shammaci Ilusnaila ta kai ma ta wawar suka a cinyarta, duk da cewar IHusnaila ta gocewa harin da dukkan zafin namanta amma sia da kaifin bakin jiminar ya yanketa. Wani inn dogon yanka tamkar da takobi aka yanketa. Take waycn ya dare, jini yai feshi. Ilusnaila ta kurma uban ihu ta sulale kasa sumammiya. Koda ganin abinda ya faru ga IHusnaila sai Muraisu ya fusata ya yi zumbur! ya daukì mashin IIusnaila ya hada da takobinsa ya ci gaba da yakar jiminar. Ya rinka kai ma ta muggan hare-hare da takobi da mashi cikin matukar fushi da zafin nama. Bisa dole jiminar ta rinka ja da baya, amma kuma wani lokacin saì ka ga la taso masa da dukkanta itama ta kuntalashì tana korashi baya. A haka ta sảmu shima ta yankesbi da kaifin bakin na ta, har sau uku. Yankan farko a hannunsa na dama nc, na biyu a kaladarsa ta hagu, na uku kuma a gadon bayansa, sai gashi jinio na zuba a jikinsa har jiri na đibarsa, amma saboda yana da dakakkiyar zuciya irin ta maza bai fadi kasa ba, kuma bai fasa kaiwa jiminar hari ba. Ana cikin haka sai Jiminar ta sami nasarar buge takobi da mashin da ke hannaycnsa suka fadi kasa, kuma ta matseshi ta hanashi daukar makaman. Bisa dolc Muraisu ya fara ja da baya, gashi bayansa wani katon dutse ne, idan har ta kuresgu a jikin dutsen ba makawa sai ta hallakashi tunda ta cika hanya babu ta inda zai iya tserewa. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa ke nan, zuciyarsa ta karaya domin bashi da sauran wata dabara a zuciyarsa da zai iya kubular da kansa. A dai-dai wannan lokaci ne Husnaila ta farlado daga dogon suman da tayi, ta ga abinda ke shirin faruwa. Koda ta tunkura da nufin la mike tsayc sai taji ta kasa đomin kafarta tayi nauyi tamkar an aza ma ta katon dutsc akai. Kawai sai ta zuba ido tana jiran ta ga iin kisan gillar da jiminar za ta yiwa Muraisu sanann ta Juyo kanta. Ya yin da ya rage bai fí saura taku biyar ba kacal tsakanin jiminar da Muraisu ta kaishi jikin dutsen da ke bayansa, sai kawai ya fusata ainun ya daka wawan tsalle sama izuwa kan jiminar tamkar an harboshi daga cikin baka. A Saman ya kama wuyan jiminar da hannaycnsa biyu ya murdeshi da dukkan karlinsa. Ta ke wuyan jiminar ya karye ya bayar da sauti kararas! Ta ke Jiminar ta yanke jiki ta ladi kasa tim! Tamkar giwa ce ta fadi har sai da kasa tayi girgiza, wala gagarumar kura ta tashi. A sanann ne Muraisu ya yanke jiki ya fadi kasa. Maimakon ya yi kokarin yiwa kansa magani a jikin raunikansa sai ya nufi inda Ilusnaila ke kwancc da jan jiki domin ya kasa mikewa tsayc. Yana isa garcta ya fiddo garin magani a jikinsa ya shafe raunin cinyar Ilusnaila.. Ta ke ta kurma uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogịn da taji ta sake bajewa a kasa sumammiya. Nan take hankalin Muraisu ya dugunzuma ainun,-yaji ya kamu da lsanänin tsoro, domin a zatonsa Ilusnaila ta mutu. Cikin ruđewa ya daure ya míke tsaye da kyar yana tangadi, yaje ya dauko babbar ruwan shansa ya budeta ya zazrAge ruwan akan Husnaíla. Dama sa'adda aka yí ruwan sarma ne ya sarnu ya cika battar ruwan. Ai kuwa yana zuba ma ta ruwan saí ta farfado tana mai dogon ajíyar num fashí. Koda ta bude idanu ta fa Muraisu tsaye a kanta sai ta daka masa tsawa ta ce, "Me yasa ka cecí rayuwata? Ka san cewa na tsaneka fiye da yadda na tsani mutuwata? Da dai a co kaine ka kubular da rayuwata gwara dabbobin dajin nan su yí kaca-kaca da sassan jikina su cnyc". Koda jin wannan batu sai zuciyar Muraisu ta kama tafar fasa, yiji kamar ya sa takobi ya sare kan IHusnaila saboda lakaici. Amma da a tuno da birnin Lairus sai ya danne zuciyarsa, ya mıke tsaye yaje ya koma can gefe daya ya ratIna ya shiga yíwa kansa magani, har sai da ya tsaida dukkan jinin da ke zuba a jikinsa. Bayan ya dz wo cikin haiyacinsa sOsai sai yaje ya samo kirarcn wula ya ncmno kyastu ya kunna wuta sannan ya 1arc wata wuka mai kaifi a ikinsa ya rauna ya fcd: wannan jimina tsaf ya daddatsa naman jikinta. Da kyar ya dauki cinyar jiminar guda ya soketa a jikin ítac mai gwafa ya shiga gasawa. Da naman ya gasu sosaí, sai kawaí ya fara cin abinsa ko kallon Husnaila bai ba. Da yake itama a cikin bakar yunwar take saí ta taho da jan kafa a zaunc don la kasa mikewa tsaye, ta iso har gaban naman ta dinga yanka tana Har duk su biyųn suka ci suka koshi basu kalli juna ba, kuma dayansu bai ce uffan ba. Duk wanda ka dubí fuskarsa sai ka ganta a nurtuke tamkar an aiko masa da sakon mutuwa. Ai kuWa suna gama. cin wannan naman ne hadari ya sake gangamowa, aka fara wata iin bakar guguwa wacce ta firgitasu la firgita dajin gaba daya, domin nan take bishiyoyí suka kama kakkarycwa suna zubewa kasa. Kai duwatsu ma wadanda ba su cika girma ba sai suka kama mirginowa akan kasa da kansu. Ba shiri Muraisu ya mike tsaye ya ciccibi Husnaila tamkar ya dauki dan karamin yaro ya ruga da gudu izuwa cikin dajin yana neman malafa. "Su kansu sauran dabbobin da ke dajin sun firgice suna la gujc-guje suna shigewa cikin ramuka da manyan koguna don su tsira da rayuwarsu. Muraisu dai ba a son ransa ya dauki Husnaila da hannunsa ba, sai don kishin kasarsa, sbaoda lallai nan gaba yana son dansa ya ceto ratyuwar jama'arsa daga sharrin abokan gaba. Ita kuwa Husnaila, koda ta ga Muraisu ya dauketa da hannayensa biyu tana rungume a kirjinsa sai zuciyarta tayi bakikkirin ta kama zancen zuci tana mai cewa, "Saboda me babban makiyina zai taba jikina? Ai kuwa sai na yanke wadannan hannaye nasa duka biyun wadanda suka taba jikina!" Muraisu na cikin wannan gudu ne ya hango wani kogon dutse, kawai sai ya durfafi kogon kai tsaye. lar ya kunna kai zai shiga ciki sai ya dawo da baya ya tsaya cak! ba wani abu banc yasa ya dawo da bayan ba face ganin tsananin duhu a cikin kogon, kuma babu mamaki akwai wata muguwar dabbar a cikin kogon a la6e. Kawai sai Muraisu ya ajiyc Husnaila a kas sannan ya karyO wani icen bishiya kuna ya zura hannu a cikin aljihunsa ya dauko duwasun da ya yi kyastu da su a baya ya shiga kokarin kunna wuta a |ikin wannan ice da ya karyo. Da yake an yi ruwan sama a baya bada dadewa ba da kyar da sidin goshi wular ta kama, sannan Muraisu ya zare takobir sa ya shiga cikin kogon, hannunsa guda na rike da icen mai wuta yana haskawa. Kogon bashi da zuri sosi, haka ma fadi, kuma ko Rwaro daya bai gani ba a ciki. Bayan ya tabbatar da lafiyar kogon sai ya ita ya dauko Husnaila ya shigo da ita ciki, sannan ya ajiycta ya sake lita ya nemo wadansu itatuwan ya kunna wuta mai kari domin su ji dumi. Faruwar hakan ke da wuya sai ruwa ya sake kecewa kamar da bakin kwarya. A dai-dai wannan lokaci nc tsananin gajiya tasa Muraisu ya fara 8yan-gyadi. Yana cikin wannan hali ne lHusnaila ta faki num fashinsa ta suri daya daga cikin itatuwan da ya kunna wular da su ta maka nasa shi a nuka- mukinsa. Ta ke Muraisu ya baje a kasa sumamme har jini ya bul6ulo ta cikin kunnensa ya zamana cewa ko num fashi baya yi tamkar ya zama gawa. Koda IIusnaila la ga la sami wannan nasara sai ta cika da farin ciki, kawai sai ta mike tsaye da kyar tana dingishi ta leka wajcn kogon lana kallon yadda ruwan sama ke kwarara. Ai kuwa bala jima ba a tsaycn sai ruwan saman ya dauke dif! Nan take ta fita itama tajc ta dcbo wadansu itatuwan ta zubasu akan Muraisu. Sai da ta tabbatar da cewa ta lullu6cshi da itatuwan san ann ta debo itatuwa masu cin wuta ta zuba a kansu. Nan da nan kuwa wuta ta sake kama itatuwan da ke kansa. Kawai sai Husnaila ta juya ta fice daga cikin kogon tana mai kyakyata dariy ar mugunta cikin tsananin farin ciki domin ta san cewa ta gama hallaka Muraisu dole ne wuta ta babbakeshi ya konc kurmus! Dama Husnaila ta fita ne ikec da ice mai cin wuta don haska hanya saboda duhun dare. Kawai sai ta ci gaba da tafiya ba tare da sanin inda ta dosa ba a cikin dajin Kirzufa. Koda ta fara nísa a cikin dajin tana Jiyo gurnani da koke- koken dabbobi, kawai sai ta j tsoro ya kamata. Al'amarin da ya matukar ba ta mamaki ke nan, domin ita a saninta bata san wani abu wai shi tsoro ba a rayuwarta, amma tunda ta shigo dajin Kirzufa taji ta zama matsoraciya. Kwatsam! Sai ta hangi wari kogon dutse a gabanta, don hak a sai ta yanke hukuncin ta shiga cikin kogon ta kırasa kwana a ciki, tunda ba zai yiyu ta ci gaba da tafiya a cikin daren ba. Burinta shi ie ta fita daga cikin dajin Kirzufa ta koma can birnin Hutaira. Lokacin da Husnaila la iso bakin kofar wannan kogo sai ta tsaya ta leka cikin kogon tana mai haska cikinsa da wutar icen da ke hannunta, amma sai ta ga babu komai a ciki, duk da haka sai ta kasa shiga ciki, dalili kuwa shi ne, ba ta iya gano karshen kogon. Kogo ne mai zurfin gaske, kuma mai lunguna da sako-sako. Nan take Husnaila taji tsoro ya dada baibayeta har zuciyarta ta kama bugawa da karfi amma da ta tuna cewa babu in da za ta iya kwanciya face a cikin wannan kogo sai kawai ta kunna kai ciki. Maimakon ta shiga can cikin kogon sai ta zauna daga baki-baki. Bisa sa'a sai ta ga tarin wadansu kiraran itatuwa a gefe daya. Al'amarin da ya sa tayi zargi cewa lallai akwai wasu halittu a cikin kogon, ko kuma dai sun shigo sun fita Nan da nan Husnaila ta tara kiraren a gabanta ta hada wuta sannan la kishingida a gaban wutar tana jin dumi. Tsawon kusan rabin sa'a ba ta |l motsin komai ba a cikin kogon, don haka sai ta saki jikinta ta daina jin tsoro. Abinka da gajiyayya, nan da nan sai Huśnaila ta kama gyan-gyadi. Ai kuwa sai bárCi ya saccta bata sani ba. Faruwar hakan ke da wuya sai ga wadansu irin jibga-jibgan Birirrika suna fitowa daga cikin kogon dutsen, Hakika girman wadannan Birirrika ya wuce misali, domin komai jarumtakar mutum idan ya yi arba da su dole ne ya razana saboda kwarjininsu da muninsu. Adadin Birimikan ya kai dari. Takun sawunsu ma kadai ya isa abin tsoro domin yana haddasa karamar girgizar kasa. Amma hakan duk bai sa Husnaila ta farka daga barcin da take yi ba mai nauyin gaske. Lokaci guda Birirrikan suka kewaye Husnaila su duka, suka zuba ma ta idanu kawai. Har sun yunkura za su dasa wawa akanta sai suka jiyo gurnanin Shugabansu. Gaba dayansu sai suka ja da baya suka dare hanya ta samu a tsakiyarsu. Gurnanin da Shugaban asu ya yi ne ya sa Husnaila ta farka daga barcinta a firgice! Koda ta bude idanunta tayi arba da wadannan Biririka zagaye da ita sai ta kwalla uban ihu cikin tsananin razana. A dai-dai wannan lokaci ne Shugaban Birirrikan ya karaso gaban Husnaila. Shugaban Birirrikan ya karewa Husnaila kallo sama da kasa, kawai sai ya sa hannu ya dauko Husnaila da yatsunsa biyu kacal tana ihu da kururuwa ya juya da baya ya nausa cikin kogon, sauran Birimikan suka take masa baya suna ruri da gurnani wanda ya cika dajin gaba daya. Husnaila tayi iya kokarinta akan ta zille daga Cikin yan yatsun Birin nan amrna ta kasa duk da cewa tana ta caka masa mashin da ke hannunta, amma tamkar dutse ta kę cakawa, domin ko kwarzanewa jikin nasa bai yi ba. A wannan lokaci ne hankalin Husnaila ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe, domin ta san cewa rayuwarta ta zo karshe donin babu ta yadda za ta iya kubuta. Bisa mamaki sai taji nadam a ta zo ma ta bisa abinda ta yiwa Muraisu ta hallakashi. Tabbas ta san Inda yana raye, kuma suna tare zai iya tabuka wani abu a yanzu. Duk da cewa Husnaila ta tsani Muraisu kamar yadda ta tsani mutuwarta, amma a wannan karon sai taji tana kaunar ganınsa. A karon farko a rayuwarta sai taji hawaye ya zubo ma ta, kuma tunanin dan uwanta Sarki Ishmar ya fado ma ta a rai. Nan take ta cika da mam akin yadda Sarki Ishmar ya kasa sanin halin da tak e ciki, har ya kasa aiko ma ta da agajin gaggawa a matsayinsa na gagarumin matsafi.... Nima Kuma na cika da mamakin Ganin Masoyiyata yau ta manta dani bata nemeni ba Kuma ta kasa aiko mun da sako hhh Anan zamu dakata sai wani lokaciBUSA A MUTU Littafi Na Biyu (2) Part D. Na Abdulaziz Sani M/Gini AA Misau ke Magana Marubucin yaci gaba da cewa.. AIKO MA TA DA AGAJIN GAGGAWA A MATSAYINSA NA GAGARUMIN MATSAFI. Birimkan suka cì gaba da kutsawa cikin kogon dutsen suna ta tafiya. Sai da suka yì yar doguwar taiya mai tsawo sannan suka iso wanı babban wuri mai cìke da bìshiyoyì da wata korama a tsakiya wacce ruwanta ke gudana ta cikin dutse yana kwarara izuwa cikin wanı kwararo. Bishiyoyin da ke wajen duka sun yì 'ya'yaye nunannu da danyu, kai da gani ka san cewa wadannan Biimka suna jin dadin rayuwarsu a Wannan wu. Da isowar biimkan wannan wun sai aka daure Husnaila a jikin wata bishiya da ke tsakiya da wala inyar danyar jijiyar bishiya aka daureta tamau, tayi ta wutsil-wutsil domin ta kwance kanta ta kasa. Nan fa tayi amfani da dukkan karfin sihirinta domin ta kwance kanta amma sai ta kasa. A sannan ne ta gane cewar babu wanì sihinin tsafi da yake tasiri akan dabbobin da ke cikin wannan dajì na Kirzula, dajin Bala'i da masifa! Nan fa birirrik an suka kama dukan kirjinsu da hannayensu tamkar ganguna- suke dogawa. Karar bugun kirjin nasu ya cika dajin gaba daya A wannan lokacı ne HuSnaila ta gane cewa biririkan kirari suke yiwa shugaban nasu suna zugashi akan ya alka ma ta. Koda fahimtar hakan sai Husnaila ta ci gaba da kwarara uban ihu. Shi kuwa birnin sai ya durfafo kanta Ya yin da ya rage bai fi saura taku uku ba kacal a tsakaninsu sai kawai aka jiyo wani abu ya taho da gudu ta baya. Lokaci guda gaba dayan birirrikan suka juyo har shi kansa shugabansu. Kafin daya daga cikinsu ya yi wani yun kuri sai kawai suka ga mutum ya dako tsalle ya dira a tsakiyarsu ya hausu da SARA DA SUKA. Ba wani bane wannan mutum face yarima Muraisu. Al'amarin da ya matukar daurewa Husnaila kai ke nan, domin a tunaninta tuni Muraisu ya dade da konewa ya zama toka. Abinda ya kara đaure ma ta kai shi ne, ko alamar kuna babu ajikinsa. Muraisu ya Wanzu yana mai sara da sukan wadann

Chapter 2 of 4