Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 4
sai ta wucc kai tsayc izuwa turakar Sarki Salmar. Da shigarta sai ta iske an gyarawa Sarki kwanciya, wannan karon an sanya bayansa bisa matashin kai an jinginashi da jikin gadon shi ba a kwance ba kuma shi ba a zaunc ba. A wannan lokaci akwai hadimai hudu a cikin turakar, biyu maza, biyu ma ta. Koda Sarki ya ga shigowar Kuyanga Sabirat sai ya ce da wadannan hadimai su fita su basu wuri. Nan take kuwa Hadiman suka fice suka turo kofar dakin ya zamana cewa saura su biyu kacala cikin fakin. Sarki Salmar ya daga hannunsa da kyar ya yafito Sabirat yana mai yi ma ta nuni da ta zo ta zauna daf da shi. Cikin hanzari taje ta zauna a gefen gadon da yake kwance suka kuawa juna ido, sannan ya ce, "Ya ke Sabirat bani labarin abinda ya faru tsakaninki da dana iyakar gaskiya". Ba tare da ta boye komai ba Sabirat ta zaiyane masa komai. K.oda gama jin hakan sai Sarki ajiyar zZuciya sannan ya dubi Sabirat cikin alamun tausayawa ya ce, "Yarinya buki da rabo, inda ace baki zuba masa banjua cikin vannan abincin ba, sai a cikin ruwan inibi da sa'adda kica rungumeshi din nan ku ka fadi kasa kika rinka shafar gashin kansa da tabbas sai ya tara da ke, duk macen da dana ya fara tarawa da ita sai ta sami juna biyu da shi. ldan kuwa haka ta faru sai na 'yantaki kin aureshi, kn ga ke nan da tafiyar da zai yi gobe an fasa yin ta, kin ga ke nan abin da za ki haifa shi ne anan gaba zai gaji sarautar garin na. Tashi ki tafi, amma ki sani cewa gobe kina daga cikin mutum uku wadande za su yiwa Yarima rakiya izuwa taftya Deman matar da zai aure. Maganata ta karshe a gareki ita ce, idan kin rayu nan gaba, ki zamo bai kula da ikana da za a haifa, ni kuma ladan da zan biyaki da shi mai tsoka ne, amma ba zai zo hannunki ba sai bayan jikana ya dawo nan birnin ya karbi kujerarsa ta mulki". Sa'adda Sarki Sainar ya zo nan a zancensa sai Kuyanga Sabirat ta cika. da mamaki kuma ta kasa fahimtar abinda ya ke nuii, ta ce a ranta, "To mene ne zai sa jikan naka ya tafi wani wuri sannan kumna ya sake dawowa ya karbi karagar tasa?" Nan dai Sabirat ta mike tsam! Ta fice daga cikin turakar Sarki zuciyarta cike da tsananin bakin ciki bisa damar da ta subuce ma ta ta zama matar Yarirna Muraisu. Kashe gari da sassafe Yarima Muraisu ya yi wanka ya kintsa. Yanafitowa daga wanka ya iske abincin kalacinsa a aiive inda aka saba ajiye masa, amma bai ga mai kawo abincin ba, wato Kuyanga Sabirat. Har ya yi nufin ya kwala ma ta kira ta zo domin ya tambayeta yadda aka yi ya yi barci a jiya da daddare nan da nan cikin dakiku kadan, sai kuma ya fasa. Nan dai ya zauna ya ci abincinsa, da ya kammala sai ya dauko damararsa ta yaki ya daura, ya kwashi dukkan kayan farautarsa sannan ya fita domin yaje turakar Sarki su yi sallama. Lokacin da Yarima Muraisu ya shiga cikin turakar Sarki sai ya iske boka Rufyan, Kuyanga Sabirat da wani barde wai shi Kurzal zaune a gefe daya. Al'amarin da ya matukar ba shi mamaki ke nan, domin bai ga abinda suke yi ba a turakar Sarki a wannan lokaci. Shi dai Kurzal, wani kwararren masanin hanya ne da daji, ko kunnensa ya kara bisa kasa yana iya gane abinda ya wuce a kanta sama da tsawon sa'a guda. Duk irin sawun da ya gani a kan kas, walau na mutum, aljan ko dabba yana iya shaidashi ya yi bayani a kansa. Idan ya kallo hanya yana iya fadin inda za ta kai mutum, walau wajen da za a riski ruwa, tsauni ko bishiyoyi ko duhuwa. A zamanin da Sarki Salmar ke fita farauta daji duk sa'adda zai fita tare da Kurzal yake fita. Idan kuwa Kurzal bashi da lafiya sai dai shima ya fasa fita farautar. Kai tsaye Yarima Muraisu ya nufi gadon da Sarki ke kwance. Da zuwa sai ya sumbaci goshin Sarki, a lokacin ne yaji jikin Sarki ya dume da zafin zazza6i gaba daya. Al'amarin da ya matukar daga hankalinsa ke nan, ya zauna daf da shi ya rike hannunsa a lokacin da suka kurawa juna ido, kowannensu sai kwalla ta cika masa idanu. Sarki Salmar ya budi baki ya ce, "Ya kai dana kayi sani cewa yau ne babbar rana ta bakin ciki a gareni, saboda abu ne mawuyaci mu sake jin muryar Juna daga yau. Haka kuma, yau ne babbar rana ta farin ciki a gareni, domin kana daf da taka babban matsayi irin wanda na taka a rayuwata. Wadannan mutane uku da ka gani yanzu tare da mu su ne za su yi maka rakiya a cikin wannan tafiya da za ka yi, wacce nake son ka je ka dawo a cikin kwanaki arba'in cif-cif. Hakika duk Su ukun Suna da matukar muhimmanci da amfani, amma ba za ka san hakan ba sai kun yi tafiyar." Sarki ya juyo da fuskarsa ya dubi Boka Rufyan, zal ya ce, "Ku yi mini a dana bisa amana". Je, "Mun yi alkawari za Kuyanga Sabirat da Barde alkawari cewa za ku Cikin hadin baki su ukun. mu yi iya kokarinmu wajen kare rayuwar Yarima daga dukkan abin ki". Koda jin haka sai Sarki ya yi guntun murmushi sannan ya ce, "Shi ke nan, ku fita ku bani wuri zan gana da dana, kuma ina son ku rufe marna kofa da dukkan tagogin turakar ran". Ba tare da gardamar komai be su Boka Ruf'an suka cika wannan umarni. A sannan ne Sarki ya dubi Muraisu ya ce, "Bude bakinka ya kai dana". Ta ke Muraisu ya bi umami ya bude bakinsa, shima Sarki Salmar sai ye bude nasa bakin, kawai sai wani silin gashi guda daya tamkar na wuyan doki ya fito daga cikin bakin Sarki ya shiga cikin bakin Muraisu. Faruwar hakan ke da wuya sai Muraisu vaji wanı Iin gagarumin karfi ya shigeshi irin wanda bai taba jin kamar sa ba a rayuwarsa. A sannan ne Sarki Salmar ya turnuke da matsanaicin tari A dimauce Yarima Muraisu ya yi saurin zuba ruwa a kofin zinarc ya baiwa Sarki ya sha, sannan farin da yakc yi ya lafa. Tsawon 'yan dakiku suka ci gaba da kallon juna sannan Sarki Salmar ya yi ajiyar nunfa shi kamar wanda ya farfado daga dogon suma, ya ce, "Ya kai dana kayi sani cewa daga yanzu habu wani sihirin tsafi da zai yi tasiri a jikinka, kuma babu wani daji wanda ba za ka iya shigarsa ba. Babu wala jarumt:aka da ba za ka iya yinta ba. Amma idan makiyanka guda biyu suka hada karfi za su iya kaika kas su rabaka da wannan sihiri da na baka a yanzu. A sannan ne za a ci birninmu da yaki ayi masa ado da jini da gawarwaki. Abinda za ka yi kawai kafin makiya su kai ka kas shi ne, ka tabibalar da cewa ka tscrara da rayuwar matarka da wadansu daga cikin jama armu domin kada a shafemu a doron kasa mu zama Tarihii... Nima Zan dakata anan Sai kuma wani lokaci insha Allah ßµŠÅ Ä MµTµ Littafi Na Daya (1) Part F. Karshen Littafi Na (1) Marubucin Littafin Abdulaziz Sani M/Gini matarka da wadansu daga cikin jama'armu domin kada a shafemu a doron kasa inu zama tarihi. Wannan shi ne kalamina na karshe a garcka. Sauran bayani za ka įi a ɔakin Boka Rufyan. Ina mai yi maka fatan sa'a da nasata bisa abinda za ka fita nema. ldan ka dawo gida ka islc na mutu ka ziyarci kabarina tare da matarka, itama ta sumbaci kabarin nawa ta shatashi da hannunta, wannan shi ne kadai bukatata a garcka" Koda Sarki Salmar ya zo nan a jawabinsa sai hawaye ya zub0 masa.. Nan take zuciyar Yarima Muraisu ta karaya ya dora kansa akan kirjin Sarki ya fashe da matsanaicin kuka. Sai da suka jima kankamc da juna duk suna kuka sannan Sarki ya janye jikinsa daga cikin na Muraisu, ya ce, "Tafi abinka ya kai dana, daga yau kada ka sake yin kuka komai bakin ciki ko wuya, sai dai zubar da hawaye. Idan za ka fita yanzu daga cikin turakar nan kada ka waigo mu sake ganin fuskar juna". Koda gama fadin haka sai Sarki ya lumshe idanunsa a lokacin da hawaye ke shatata bisa kurmatunsa. Cikin matukar sanyin jiki Yarima Muraisu ya mike tsaye ya taka sawayen sa ya nufi kofar fita daga turakar. Kafin ya isa bakin kofar sai ya tsaya sau uku ya yi kamar ya juyo ya yiwa Sarki kallon karshe, amma sai ya kasa saboda biyayya ga furucin Sarki. Tun Yarima Muraisu na yaro karami bai taba ketare maganar Sarki ba, kuma ko a cikin wuta ya ce ya shiga sai ya shiga. A wannan lokaci ne Yarima Muraisu ya rinka tunowa da duk abubuwan da suka faru tsakanin sa da Sarki a baya tun sa'adda ya fara wayo kawo izuwa girmansa. Kawai sai yaji ya kasa daurewa, bai san sa'adda ya fashe da matsanaicin kuka ba ya yi sauri ya fice daga cikin turakar. Yana fita sai shima Sarki ya fashe da matsanaicin kuka, domin ya san cewa shi ke nan har abada ba za su sake ganin juna ba, domin Boka Rufyan ya gaya masa cewa duk ranar da ya rabu da wannan gashin sihirin da ke jikinsa ba zai Rara kwana arba'in ba a duniya, kuma gashi wannan tafiya da Yarima Muraisu zai yi ba zai dawo ba sai bayan kwana arba'in din. Da fitowar Yarima Muraisu kofar turakar Sarki, sai ya iske Boka Rufyan, Kuyanga Sabirat da Barde Kurzal tsaye a jere suna jiransa. Ko kallonsu bai yi ba sai ya wuce gaba ya mufi can bakin kofar fada. Cikin sauri suka bishi a baya. Da zuwansu kofar fadar sai suka iske an tanadar musu dawakai guda uku, gami da guzuri. Nan take suka kama dawakan suka hau, Muraisu ne a kan gaba, sannan Kuyanga Sabirat a tsakiya, sai Boka Rufyan da Barde Kurzal a baya. Haka dai suka ci gaba da tafiya har suka fice daga cikin birnin Lairus suka nausa cikin daji. Ba su gushe ba suna wannan tafiyar har sai da rana ta take, a sannan ne dawakansu suka fara sassarfa, kai da gani ka san cewa suna bukatar su sha ruwa, kuma su huta. Koda ganin haka sai Boka Rufyan ya dubi barde Kurzal ya ce, "Wane irin nisa ne a gabanmu kafin mu riski Rorama ko kogi?" Koda jin wannan tambaya sai Kurzal ya yi murmushi ya ce, "Ya kai abin dogaronmu ai bamu yi nisa ba da barin gida ba fa, ca nake kowa a cikinmu nan ya san a inda muke. Nan da tafiyar zango daya tal zamu riski koramar Salzas". Koda jin wannan batu sai kowa ya cika da murna, saboda sanin cewa koramar Salzas wani wuri ne mai ni'ima inda ruwa ke zubowa kasa daga saman wani dogon dutsc, kuma akwai tarin 'ya'yan itatuwa wadanda suka yi tsuro a wajen. Shi dai wannan wuri ya yi kaurin suna domin ya zama tamkar sansanin Fatake, inda sukan yada zango su huta kafin su shiga birnin Lairus. Wani lokacin ma sai Fatake sun kwana sun yini a wajen suna gyara kayan kolinsu sanann su Rarasá cikin birnin Lairus. Kamar yadda masanin ya Kurzal ya yi bayani, haka al'armari ya kasance, walo sai da suka kara tafiyar Zango guda sannan suka iso daf da koramar Salzas. Tun daga nesa kadan Kurzal ya daga hannu sama yana mai yi musu nuni da su tsaya. Nan take duk su ukun suka yi turjiya da dawakansu suka tsaya cak. Kurzal ya sauko daga kan dokinsa da sauri ya dubi hanyar, sai ya ga sawaycn dawakai, kawai sai a tsugunna ya dora kunnensa akan kasa, har iZuwa tsawon dakiku goma sannan ya mike tsaye ya rike kugu yai ajiyar zuciva ya dubi Yarima Muraisu ya ce, "Ya shugabana wadansu mutane masu yawa sun zo bakin koramar nan sun yada zango, kuma eun huta har tsawon kamar sa'a guda, sannan suka tashi Suka ci gaba da tafiya, kuma maimakon su bi hanyar da za ta kaisu birninmu sai suka bi wata hanyar dabam wacce babu inda za ta kaisu face cižkin muggan dazuzzuka masu matukar hadari". Koda jin wannan batu sai Yarima Muraisu ya dubi Boka Rufyan ya ce, "Duba mana mu ga ko su waye, kuma mu san daga ina suke da inda suka dosa" Boka Rufyan ya ce, "An gama ya shugabana. Amma zai fi kyau mu karasa bakin koramar tukunna mu sauka mu sami nutsuwa". Ba tare da gardamar kormai ba kuwa Yarima Muraisu ya amince da wannan shawara suka karasa bakin koramar suka yada zango. Sai bayan dawakansu sun sha ruwa, suma sun sha, kuma aka ci abinci sannan Boka Rufyan ya share kasa ya rintsa idanunsa ya karanta wadansu dalasimai na tsafi sannan ya tofa akan kasar, sai ga hoton cikin birnin Hutaira ya baiyana akai, aka nuno cikin gidan sarautar Sarki Ishmar. Sarkin yana tsaye tare da 'yar uwarsa Gimbiya Husneila suna sallama zai yi tafiya, duk su biyun suna kwalla. Husnaila ta dubi Sarki Ishmar cikin matukar damuwa ta ce, "Ya kai dan uwana kayi sani ccwa bamu taba rabuwa ba facc idan za ka tafi yaki, kuma ko yaki ka tafi baka wce sati biyu zuwa uku baka dawo ba, amma yau gasni ka ce dani zamu rabu har tsawon wata bakwai, ta ya va kake tsammanin cewa zan iya jure kewar rashinlka a tare dani?" Sarki lshmar yaji wannan tambaya sai hawayc ya Zubo masa ya ce, "Ya ke 'yar uwata ki sani cewa bisa dolc zan tafi na barki ba don ina so ba, kuma wannan tafiya zan yi ta ne don cika babban burin rayuwata wanda idan ya tabbata sai mun sami daula, đaukaka da arziki irin wanda bamu taba samu ba. Na sani cewa za ki cikin kewata matuka, amma akwai abinda zai kawar miki da wannan damuwa. Na sani cewa rayuwarki babu abinda kike so sama da yin rangadi a cikin daji kina kallon kyawawan tsuatsaye da kyawawan namun daji, saboda haka na shirya miki wannan rangadi. A duk bayan wata guda za ki fita tare da Dakaru dubu dari uku wadanda za su baki tsaro, amma duk sa'adda kuka fita kada ku sake ku haura kwana goma baku dawo gida ba. Abu na biyu, akwai dajin Kirzufa wanda ba a shigarsa, lallai ku nisanceshi. Abu na uku wanda shi ne na karshc, kada ku kuskura ku bi hanyar da za ta kaiku birnin Lairuf. Koda kun bi hanvar kuwa ya kasance iyakarku ita ce koramar Salzas, daga nan sai ku juyo ku bi wata hanyar dabam". Sa'adda Sarki Ishmar ya zo nan a zancensa sau Gimbiya Husnaila tayi ajiyar zuciya ta ce, "Ya kai dan uwana shin yanzu kana ganin ccwa wadannan Dakaru da za su yi mini rakiya ya yin da zan fita rangadi za su iya karcni daga dukkan mugun al'amari?" Sarki Ishmar ya yi murmushi sannan ya ce, "A1 koda ba za su iya kareki ba babu wani tsautsayi da zai iya hawa kanki saboda na karc lafiyarki da dukkan karfin sihirina" Da jin haka sai murna ta kama Gimbiya Husnaila ta rungume Sarki Ishmar ta sumbaci goshinsa, sannan ta ce, "Ya kai dan uwana hakika yanzu hankalina ya kwanta kuma na san cewa har watanni bakwai su cika ba zan shiga tsananin damuwa ba tunda zan dinga fita wannan rangadi. Amma abinda nake so da kai shi ne, da zarar watanni bakwan sun cika ka gama shirinka to kafin ka tafi yakin ka dawo gida ka daukeni mu tafi tare". Sarki Ishmar ya ce, "Ai wannan mai sauki ne, na yi miki alkawari cewar lallai haka za a yi". Nan takc Sarki Ishmar ya rungume Husnaila suka yi bankwana sannan ya juya ya tafi. A dai-dai nan ne Boka Rufyan ya goge kasar da ke gabansa, hoton komai ya bace. Yana dago kai sai ya ga ashe Yarima Muraisu, Barde Kurzal da Kuyanga Sabirat sun kame kamar gumaka. Ba komai ne ya haddasa musu hakan ba face tsananin rudewa da dimaucewa da suka yi sakamakon ganin kyawun Gimbiya Husnaila. Ita kanta Kuyanga Sabirat da take mace sai da ta rude matuka, domin tun da tazo duniya ba ta taba ganin mace mai kyanta ba. Ya yin da Boka Rufyan ya ga su Yarima sun dimauce sai ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya. Al'amarin da ya janyo suka dawo cikin haiyacinsu ke nan. Yarima Muraisu ya dubi boka Boka Rufyan ya ce, "Yanzu dama akwai mace mai irin wannan kyau a duniya? Ni kam yanzu na ga matar aure". Koda jin haka sai Boka Rufyan ya sake bushewa da dariya a karo na biyu, sannan ya murtuke fuska kamar an aiko masa da sakon mutuwa. Ita kuwa Kuyanga Sabirat sai taji kishi ya turnuketa kamar ta fashe da kuka. Boka Rufyan ya duk arima Muraisu cikin matukar damuwa ya ce," gabana kayi sani cewa mallakar Gimbiya Husnailaercka ba karamin aiki ba ne. Zan iya cewa dai-dai yake da tafiya neman Jaki mai kaho, ko kuma ace SIYAN AJALI, tun gabannin ajali ya zo. Za ka iya mallakarta, amira za ka iya rasa rayuwarka a ko karin maliakarta, sabod tsananin Rarfin sihirin da ke iikinta wanda xi kaina ban san makarinsa ba. Da farko dai ina so ka sani ccwa Gimbiya Husnaila bata ta6a vin sovavya ba, domin babu ni da namiji da zai burgeta kornai kyansa ko jarumtakarsa. Abu na biyu, an circ mata sha'awa irin wacce ke tsakanin mace da namiii barc tayi sha'awar yin aurc. Duk wadannan abubuwa Sun faru sakamakon sihirin da dan uwanta ya sanya ma ta a Jikinta. In har kana son ka karya wannan sihiri da ke jikinta dole nc sai ka je ka vaki Dakarun da ke tsaron lafiyarta a yanzu su dubu dari uku. Ko ka tarwatsasu ko kuma ka kashesu gaba dayansu sannan ka daukcta ka shigar da ita cikin dajin Kirzufa ku yi rayuwa ta tsawon kwana uku a cikin dajin, kuna ci kuna sha daga dabbobin dajin da 'ya'yan itatuwansa. To fa a sannan ne sihirin tsafin da ke jikinta zai karyc, sai kuma ka san hanyar da za ka bi ka sami soyayyarta har ta amince ta biyoka izuwa birnin Lairus domin ayi bikin aurcnku. Babban abu mai hadari a cikin wannan al'amari guda biyu ne Abu na farko shi nc, yaki da wadannan Dakarn guda dubu dari uku masu tsaron lafiyar Gimbiya Husnaira ba karamin bala'i bane, domin Dakaru ne na musamman wadanda aka siyesu daga can birnin Romaniya. A duniya kaf, babu wadansu mutane masu girma da karfi kamarsu, sannan an tsumasu a cikin tsafin da' babu wani kaifi ko tsini da zai yi tasiri a jikinsu, kuma basa gajiya da yaki koda za a kwana uku ana yakin da su. Duk wuya, duk gumu basa gudu a filin daga. Abu na biyu shi ne, tunda dajin Kirzufa ya wanzu ba a taba samun tnahalukin da ya taba kwana a cikinsa ba. Shi kansa mahaifinka da ya shiga dajin sa'a uku kawai ya yi a cikinsa ya fito saboda bala'i da masifar dabbobin da Ke cikin dajin. Shi kansa ya lura cewa idan ya ce zai kwana a cikin dajin yana farauta to zai iya shiga mugun hali ko kuma gaba daya ma ya rasa rayuwarsa, shi yasa ya hakura ya yi sa'o'i kadan a ciki ya fito. Idan har ka iya yin wannan kwana uku a cikin dajin Kirzufa tarc da Girabiya Husnaila kuma har ka sami soyayyarta ku ka yi aure, tabbas sai kun haifi da wanda ba a taba yin jarumi kamarsa ba a duniya wajen tsananin Karfi da jarumtaka. Amma kuma rayuwarsa a doron kasa za ta zama annoba ga dukkan manyan Sarakunan duniya, matsafa da manyan attajirai, domin za su rinka rasa 'ya'yayensu akan kari, saboda haka za su bazama wajen farautar rayuwarsa. Dalilin da zai sa su rinka farautar rayuwarsa shi nc, akwai wani narkekcn kahon tsafi a cikin dajin Kirzufa wanda ake viwa lakabi da suna BUSA A MUTU. Kullum sai wannan da da ku ka haifa ya daga kahon ya dubi kudu ya busa shi sau uku. Da zarar ya busashi kuwa 'ya'yan manyan mutanc uku za su mutu a kasashc uku. Shi dai wannan kaho idan ya busashi sai an ji sautinsa a ko ina a cikin duniya. Ba wani abu bane zai sa ya inka busa wannan kaho ba sai domin yana son ya ta fita daga cikin dajin Kirzùra ya koma can birnin Lairus domin ya dauki fansar kisan gillar da aka yiwa jama'armu, kuma ya karbi karagar mulki daga hannun dan uwanka azzalumi Yarima Huraisu. Ba zai sami damar fita daga dajin ba, inda anan nc ya girma har sai ya busa kahon sau adadin yawan dabbobin da ke cikin dajin Kirzufa. Har yau, har gobe babu wani matsafi da ya iya gano yawan dabbobin. Amma dai bincike ya nuna cewa yawansu kaf bai kai dubu daya ba.!" Topah Aikin Aikineh *SHIN YARIMA MURAISU ZAI IYA TARWA TSA DAKARUN DA KE TSARON GIMBIYA HUSNAIRA DOMIN YA DAUKETA YA SHIGA DAJIN KIRZUFA DA TTA DOMINv SIHIRIN TSAFIN DA KE JIKINTA YA KARYE HAR TA AMINCE DA SOYAYYARSA? WANNE HALI SARKI SHMAR DA YARIMA HURASU SUKE CIKI? YAUSHE NE ZA SU GAMA DUKKAN SHIRYE-SHIRYENSU DON SU IE BIRNIN LAIRUS SU YẤKESHI HAR SU SAMI NASARAR MALLAKAR GASHIN SIHIRINV DA KE JIKIN YARIMA MURAISU? *WADANNE IRIN HADARURRUKA SU YARIMA MURAISU ZA SU RISKA A YA YIN WANNAN TAFIYA TASU? YAUSHE NE ZA SU HADU DA SU GIMBIYA HUSNAILA DA DARUN U HAR A FAFATA AZABABBEN GUMURZU? YAUSHE ZAA HAIFI JARIRIN DA ZAI ZAMO GUGUWAR ANNOBA GA AL'UMMAR DUNIYA, WANDA ZAI RINKA BUSA KAHON BUSA A MUTU? Mu hadu a kashi na biyu, don jin ci gaban wannan kayataccen, kasaitaccen labari. Daga mai debe muku kewa a kullum da ko yaushe. ABDUL'AZIZ SANI M/GINI. (King of Adventures Story) . Dafatan labari ya kayatar Kowa ya ajiye mana hasashenshi... This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4