Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
musu jagora izuwa can filin motsa jiki. Wani katon fili ne mai tsawo da fadin gaske wanda aka kewayeshi da shingen karfe gaba dayansa, kasan filin an zuba ya shi mai taushi. Da isowar su Yarima Huraisu wannan fili sai suka iske Sarki Ishmar shi kadai a tsakiyar filin a tsaye ya yi gagarumar shigar yaki ta bakin sulke kuma ya rataya zabgegiyar takobi a bayansa. Sarki Ishmar ya dubi Yarima Huraisu ya ce, "Yau ne ranar da zamu fara bin matakin farko don samun nasara bisa bukatar da ke gabanmu. Ya kai Huraisu yanzu sai ka shigo Cikin wannan fli domin mu jarraba jarumtakar junanmu". Koda jin haka sai Huraisu ya yi murmushi ba tare da ya ce komai ba. Nan take ya cire alkyabbar da ke ikinsa ya zama daga shi sai doguwar riga da wando, sai kuma danarar da ya yi a kugun sa. Maimakon ya hude kofar shiga cikin filin ya shiga sai kawai ya daka wawan tsalle sama tamkar an cillashi, daga cikin baka ya dira a cikin filin nesa kadan da inda Sarki Ishmar ke tsaye. Nan fa suka fara kewaye juna suna kallon-kallo. Busara da sadauki Rauhaz suka gyara tsayuwarsu daga bayan filin domin su baiwa idanunsu abinci. Bayan Huraisu da Ishmar sun zagaya jauna kamar sau uku sai suka rugo da gudu izuwa kan juna. Sai da ya rage bai fi taku uku ba su hadu, sai kowannensu ya zare takobi, ai kuwa suna haduwa suka kacame da azababben yaki. Sai da suka shafe sa'a guda cur suna kaiwa junansu sara da suka amma dayansu bai sami nasarar koda yakusar jikin daya ba, kuma cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta suke yakin. Hakika sadaukantaka ta hadu da sadaukantaka, haka ma naci ya hau da naci. Da kansu suka rabu suka ja da baya, kowannesu ya kama haki kamar zakaru. Busara da sadauki Rauhaz kuwa basu san sa'adda suka kama yi mnusu tafi ba, domin su kansu sun san an yi jarumtakar da ta wuce saninsu. Bayan yan dakiku kadan sai Sarki Ishmar va dubi Yarima Huraisu ya yi murmushi ya ce, "Tabbas ka cika jarumi juriya. Yanzu kuma zan sauya salon fada domin na nuna maka cewa ni tsohon hannu ne kuma na fi ka kwarewa da Sanin makamna tunda na kara da mabaifinka ma bai sami nasara akaina ba. Duk sa'adda muka hadu sai dai mu yi jarumi ma'abocin jarumtaka da KARE JINI, BIRI JINI." Koda jin haka sai shima Huraisu ya yi murmushi sannan ya ce, "Tabbas na yarda ka fimi kwarevwa kuma na yarda cewa jarumtakarka tafi tawa tunda har kwanan gobe ni ban isa na kara da mahaifina ba, duk da cewa tsufa ya kamashi, amma zan nuna mmaka ccwa dole ne mahaifina ya fika iarumtaka da juriya, lallai sa'adda kuke haduwa in dai za ku yi gaba da gaba har tsawon sa'a guda Sa'adda Sarki Ishmar yaji wannan batu sai ransa ya sai ya hallakaka. " baci zuciyarsa ta kufulo, ya kasa cewa komai domin ya san cewa abinda Huraisu ya fadi gaskiya ne. Kawai sai ya sake rugawa izuwa kan Huraisu ya rufeshi da SARA DA SUKA cikin sabon salon yaki. Wannan karon dai tsalie-tsalle Ishmar ya kama yi yana shawagi a saman Huraisu tamkar tsuntsu mai fuka-fuki. Nan da nan kuwa Ishmar ya rikita Huraisu ya zamana cewa baya iya inai da martani sai dai kare hari. Koda Ishmar ya ga ya sami wannan nasara sai ya kara ZAGE DANTSE ya dada kuntatashi har ma ya sami nasarar yankarsa akan kirji. Duk da cewa yankan bai yi zurfi ba, amma sai da jini yai feshi. Koda Huraisu ya shafa kirjinsa ya ga jini kuma cewa rigarsa ta yage sai ransa ya baci, zuciyarsa kufulo, kawai sai ya ja d baya ya kama rigar tasa ya ketata gida biyu ya yi wurgi da ita. Kawai sai ya ruke takobinsa da hannu biyu sannan ya fuskanci Sarki Ishmar ya yi masa inkiya da ya sake kawo masa hari. Ai kuwa sai Ishmar ya ka bi tayin nasa ya rugo gareshi da gudu. Maimakon ya tsaya jiransa sai shima ya ruga kansa da gudu. Koda ya rage bai fi taku uku ba su hadu sai kowannensu ya daka tsallc suka hadu a sarma. Ishmar ya kaiwa Huraisu wawan sara a kafada ya goce cikin zafin nana amma duk da haka sai da takobin ta shafi jikinsa aka yi sa'a bata yankeshi ba, amma ta sarce gasin kirjinsa tamkar zabira aka sa aka askeshi. Shi kuwa Huraisu a cinya ya kaiwa Ishmar sara, maimakon takobin ta nutse a cikin cinyar sai ta shafci kadan daga cikin tsokar naman, jini yai tsartuwa. Tun a sarnan Sarki Ishmar ya kwalla ihu sakanakon tsananin zafi da zogin da yaji, amma yana durowa kasa sai yai sauri ya cire rawaninsa ya dauure raunin don tsaida jinin sannan ya sake afkawa Huraisu da dukkan karfinsa da zafin namansa kai ka ce da mutum dubu yake fada shi kadai. Sai da suka shafe sa'a daya da rabi suna gumurzu a wannan karon, gumurzu na tashin hankali wanda ya firgita 'yan kallon nasu domin gani suke yi cewa lallai a ko yaushe dayansu zai iya rasa rayuwarsa donin dukkaninsu neman hallaka juna suke Kamar hadin baki sai duk su biyun suka ja da baya suka tsaya cak! ga barin yakar juna sannan kuma sai suka bushe da dariya a lokaci guda, suka rungume juna. Sarki Ishmar ne ya fara janye jikinsa daga cikin na Huraisu ya dubeshi ya ce, "Hakika yanzu na gamsu cewa kai abokin tafiya nc, kuma albasa tayi halin uwa, domin ka gado wani abu daga cikin jarumtakar mahaifinka. Yanzu bani da wata fargaba akan matakinmu na farko domin nà san cewa idan muka hada KARFI DA KARFE ni da kai zamu iya kai Yarima Muraisu kas. Abu na biyu da zamu yi yanzu shi ne, mu tafi izuwa can gidanka domin mnu fara hada rundunar mayakan da zamu tafi da su yaki can kasarku. A kalla wannan aiki zai daukemu tsawon wata shida kafin mu kammalashi, domin ba zamu tafi wannan yaki ba da Dakaru kasa da miliyan biyu, kuma dole ne mu basu horon yaki na musamman irin wanda zai sa zuciyarsu ta kekashe ga barin tsoron komai. Tuni na aika da wasikar gayyata izuwa ga wadansu manyan sarakuna a wannan nahiya tamu wadanda suka kasance abokaina kuma aminaina na neman gudunmawar Dakarun yaki a wajensu kuma sun tabbatar min da cewa za su bani hadin kai dari bisa dari. Yanzu gobe da sassafe zan sake aikawa da wasiku ga wadannan Sarakuna na sanar da su cewa su turo mini Dakarun izuwa can gidanka mu samesu a can ko kuma su su samemu a can " Sa'adda Sarki shmar ya zo nan a zancensa sai Yarima Huraisu ya yi ajiyar zuciya ya ce, "To yanzu vaushe ne kuma za mu je mu dauko wukar Hirzul Subura." Koda jin wannan tambaya sai Sarki Ishmnar ya bushe da dariya sannan ya ce, "Ni kuwa dadina da kai ke nan ka cika hanzari a cikin al'amuranka. Kada ka damu kafin mu gama baiwa Dakarunmu horon yaki za mu je mu dauko wukar Hirzul Subura". Koda gama fadin haka sai Sarki Ishmar ya yi nuni da hannunsa na hagu izuwa ga raunin da ke cinyarsa wanda bai taba wanzuwa ba. Al'amarin da ya matukar baiwa Huraisu mamaki ke nan domin ya san cewa aikin tsafi ne kawai wannan". Koda Sarki Ishmar ya fahimci cewa Huraisu ya yi mamakin abinda ya faru sai ya bushe da dariya sannan ya sake nuna raunin da ke jikin Huraisu. Take shima na sa raunin ya warke sumul. Kawai sai ya kama hannunsa ya jashi suka fice daga cikin fillin motsa jinin suka nufi cikin gidan sarautar. Busara da sadauki Rauhaz suka take musu baya. Wannan shi ne abinda va faru a birnin Hutaira bayan Yarima Huraisu yaje ncmi hadin kan Sarki Ishnar domin ya biya bukatarsa ta ganin ya mallaki birnin Lairus. A CAN birnin Lain:s kuwa, lokacin da Sarki Salmar ya kamu da cutar ajali va kwanta ciwo sai hankalin Yarima IHuraisu ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi a duniya har ta kai cewa bashi da sukuni dare da rana, kuma baya iya cin abinci sosai baya saraun isasshen barci, al'amarin da ya janyo ya dinga ramewa ke nan tankar shima bashi da lafiya. Ba komai ne ya jefashi a cikin wannan mugun hali ba face ganin yadda ciwo nai zai ya kama mahaifin nasa a kankanin lokaci har ta kai cewa bakinsa ya kulle baya iya yin magana. Idanunsa sun rufe baya ganin komai ku.ma baya iya yin komai da kansa sai dai ayi masa. Bara Yarima Muraisu ba, gaba dayan jama'ar kasar Iarus birni da kauye sai da hankalinsu ya dugunzumna ainun bisa jin halin da Sarkinsu ya shiga saboda sun san cewa shi nc babban katangarsu wacce ta hana makiya yi musu dirar mikiya. Tabbas duk. ranar da aka ce babu Sarki Salmar to fa babu cikakkn tsaro a birnin duk da cewa an san akwai halifansa, wato Yarima Muraisu saboda kowa ya yarda da jarumtakar Sarki Saimar wacce tafi gaban tunani kuma kowa ya san kwarewarsa a yaki da kuma tsabar sa'arsa ta tsawon shckara da shekaru. Kullum Yarima Muraisu na zaune a gaban gadon Sarki Salmar yana kallonsa yana zub da hawaye domin a duniya babu mnutumin da ake shakka sama da Sarki Salmar tunda kusan shire ya renesu tun suna yara shi da Huaisu kamar yadda uwa ke rainon danta. Sabo da tsananin Raunar da Sark Salmar ke yiwa Muraisu da Huraisu hatta wanka da tsarkin kashi shi yake yi musu da kansa tun suna jarirai har suka rirma suka iya yin komai da kansu bai taba bari kuyangi da barori sun yi musu ba. Sai da Sarki Salmar ya kwana talatin da tara a kan gado yana jinya ba. A daren kwana na talatin da taran ne, Huraisu na zaune akan kujera dab da gadon Sarki ya fara gyan-gyadin dole bai sani ba sakamakon bashin barci da ya dauka na tsawon kwana biyu, kawai sai yaji an dafa cinyarsa. A firgice Muraisu ya farka daga barcin, sai ya ga ashe Sarki ne ya dafashi har ma ya kura masa ido hawaye na shatata bisa kumatunsa. Saboda tsananin murna da mamaki sai Muraisu ya yunkura da nufin ya rungume Sarki, armma sai Sarki Salmar yz daga masa hannu yana mai yi masa nuni da ya dakata. Muraisu ya koma kan kujerarsa ya zauna ya ci gaba da kallon Sarki a cikin nutsuwa domin ya ji abinda zai fito daga bakinsa. Sarki Salmar ya budi baki da kyr ya ce, "Ya kai dana, kayi sani cewa wannan sauki da na samu ba sauki bane na samun lafiya, tabbas sauki ne yazo mini dormin mu yi bankwanan karshe. Tabbas tawa ta kare domin zan iya mutuwa a cikin kowacce sa'a ko dakika mai zuwa nan gaba ko kuma a cikin yini ko kwana ko wata. Wata kila ma shekara, bani da tabbaci dai. Kafin na ce da kai komai yanzu ina son ka tashi ka garzaya gidan boka Rafyan yanzu-yanzu ka ce da shi ya zo ina son ganinsa." Cikin tsananin damuwa Yarima Muraisu ya mike tsaye jikinsa a sanyaye kamar zai fashe da kuka domin gani yake kamar idan ya tafi gidan bo ka Rafyan kafin ya dawo Sarki ya mutu. Haka dai ya daure ya tafi. Cikin gudu Muraisu ya isa gidan Boka Rufyan ya isar da sako. Nan da nan kuwa suka juyo suka dawo gidan sarauta suka shiga cikin turakar Sarki. Koda Sarki Salmar ya yi arba da boka Rufyan sai ya yunkura da kyar ya juyo da fuskarsa sosai ya fuskancesu, su kuma sai suka yi sauri suka zauna a gabansa suka fuskanceshi. Sarki Salmar ya kama hannun boka Rufyan ya rikeshi gam a cikin nasa sannan ya ce, "Ya kai amintaccen bokana gaya mini iyakar gaskiya kamnar yadda ka shaida mini a baya kimanin shekaru ashirin da biyar da suka gabata. Mene ne zai faru bayan mutuwata anan birnin Lairus?" Koda jin wannan umarni sai boka Rafyan yai tsuru-tsuru yai shiru bai ce komai ba, ya dinga raba idanu tsakanin Sarki da Yarima. Koda ganin haka sai Yarima Muraisu ya dakawa boka Rufyan tsawa ya ce"Saboda me za ka tsaya kana Jinkiri bisa bin umarnin mahaifina, ko kuwa don ka ga vana kwance nea cikin wannan hali?" Sa'adda boka Rufyan yaji wannan tambaya sai hawaye ya zubo masa sannan ya dubi Sarki cikin matukar damuwa ya risina ya ce, "Ya shugabana shin ka mantane cewa mun yi alkawarin cewa ko ni ko kai dayanmu ba zai tona wannan sirri ba, saboda mc yanzu ka sauya shawara?". Koda jin wannar tambaya sai hawaye ya sake zubowa Sarki Salmar ya cc, "Ai dole ne na sauya shawara tunda bakin al kalami ya bushe ko mun baiyana ko bamu baiyana ba sai wannan al'amari ya faru, kuma ka sani cewa idan ba mu yiwa Y arima bayani ba tun yanzu to fa asarar da za ayi ta rayuka da dukiya sai ta wuce yadda duk ake zato. Na umarceka da ka hanzarta yi masa bayanin komai tun kafin an koma cikin mugun halin da na kasance n rashin' gani da kasa yin magana". Koda jin wannan batu sai boka Rufyan yai shiru isawon 'yan dakiku bai ce komai ba. Dega can kuma sai ya dubi Yarima Muraisu cikin nutsuwa ya ce, "Ya kai gwarzon jarumi magajin ubansa, ka yi sani cewa bayan rasuwar mahaifinka mummunan yaki zai 6arke anan kasar wanda babu mai iya kare rayukan jama'a da dukiyarmu. Tabbas sai an cimu da yaki, kuma ba wani bane zai kawo wannan yakin ba face dan uwanka Yarima Huraisu. A yanzu iaka Yarima Huraisu ya bar nan kasar gaba daya, ya jevcan ya hada kai da makiyanmu suna hada rundunar mayakaa ta mutane masu yawan gaske wadanda Za su yakemu. Tabbas nan da wani lokaci burinsu zai cíka burinmu". Koda boka Rufyan ya zo nan a zancensa sai Yarima Muraisu Ya tari nun:fashinsa ya cc,Tunda dai Yanzu an san da haka me zai hana sarki yayi mini izini na debi dakaru masu yawa mu tafi har can sansanin su huraisu mu yakesu shida wadanda suka hada kai mu kawar da su?", Caraf! sai Sarki Salmar ya ce, "Shin ka manta ne cewa wannan abu da zai samcmu kaddara ce kuma bamu isa mu kaucewa kadiara ba? Babu makawa sai an cimu da yaki, lallai babu abin da za mu iya yi face kawai mu yi kokari mu rage asarar da za ta samemu. Ya kai Rufyan yanzu mcne re abin yi?" Boka Rufyan yai shiru yana mai sunkui da kansa kas tamkar mai daukar karatu ashe tunani da bincike yake yi a cikin hallarar tsafir.sa. Tsawon lokaci bai ce komai ba, can kuma sai ya dago kai ya dubi Sarki Salmar ya ce, "a shugabana idan har muna son mu rage asarar rayuka da ta dukiya da za ta biyo baya dole ne Yarima Muraisu ya gaggauta yin aure a cikin watannin da basu wuce biyu zuwa uku ba, kuma dole ne matar da zai aura ta zamo daga cikin zuri'ar abokan gabarmu. Lallai idan ya yi wannan aure zai sami haihuwa da ita kafin zuwan ranar da warnan yaki zai Zo kuma Allbarkacin dan da za su haifa ne ita da dubunnan daruruwan mutane za su iya yin ayari guda su yi gudun hijira su bar winnan kasa tamu. Suma ba Zai yiyu ba dukkaninsu su tsira da rayuwarsu da dukiyoyinsu ba face sun isa dajin Kirzufa." Sa'adda Boka Rafyan yazo nan a zancensa Sal Yarima Muraisu ya cika da tsananin mamaki ya dubeshi cikin tsananin damuwa ya ce, "Yanzu ta yaya zan auri 'yar abokan gabar mu a cikin wannan yanayi da mahaifina ke ciki? A ina ma zan ga 'yar abokan Gabar tamu har na aureta alhalin bani da lokacin da zan tafi ko ina?" Boka Rufyan ya tari numfashin Muraisu ya ce, "Ai kuwa zema bai samcka ba dole ne ka mike ka yi shiri ka bazama neman matar da za ka aura. Kuma bincike ya nuna cewa ta hanyar farauta za ka hadu da sirikarmu wacce za ta zamo uwar dan da zai gaji sarautar kasar nan a nan gaba, wanda shi kadai ne zai iya karbar mulkin da za a kwace daga hannunmu da karfin tsiya. Bincike ya dada tabbatar da cewa baka da sasshen lokaci na zama a gida, ya zama wajibi ka gaggauta shirin fita farauta a daji idan har muna son wannan bukata tamu ta biya Sa'adda Boka Rufyan yazo nan a jawabinsa sai hankalin Yarima Muraisu ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe, saboda jin cewa dole ne ya yi shiru ya fita farauta a wannan wannan lokaci da Sarki ke tsakanin MUTUWA DA RAYUWA. Nan take hawaye ya subutowa Muraisu ya durkusa a gaban Sarki ya đora kansa akan cinyarsa. Sarki Salmar ya đaga hannunsa na dama da kyar ya dora akan Muraisu yana wasa da gashin kansa a lokacin ne shima hawaye ya kubuce masa domin yana Ji yana gani zai rabu da babban masoyinsa a duniya. Hakika ko a mafarki Sarki Salmar bai taba Tunanian cewa wannan rana za ta zo masa ba a rayuwa. Shi kansa boka Rufyan saadda ya ga Sarki da dansa suna zubar da hawaye sakamakon wannan rabuwa ta dole da za su yi sai da ya kamu da tsananin tausayinsu, domin ya san irin shakuwar da ke tsakaninsu ta fi gaban kwatance. Boka Rufyan ya mike tsaye sannan ya ce, "Ya kai Yarima Muraisu, ka tashi ka je ka fara shirye shiryen wannan tafiya da za ka yi gobe, kuma ka tabbatar da cewa ka dawo gida a cikin kwanakin da basu haura arba'in ba tare da matar da za ka aura." Da jin haka sai Muraisu ya mike zumbur! ya dubi boka Rufyan cikin rashin fahimta da damuwa ya ce, "To wai shin yanzu wane daji zan je na yi farautar har na hadu da wannan mace wadda zan aura, kuma ya za a yi na san ita ce wadda zan aura din? Wai shin ma ta ya ya za ta amince da ni har ta biyoni nan birnin mu zo a daura mana aure?" Koda jin wadannan tambayoyi sai boka Rufyan ya ce, "Amsar wadannan wannan tafiya da za ka yi. Amma a yanzu duk duniya babu wani boka da ya isa ya baka amsar komai bincikensa da matsayin a hallarar tsafi........ To NimA dai Bari Naje FarautAr Yarinyar da Zan aura Daga India Ko zata Amince Ta Biyoni Gida Nigeria hhhhhhh Anan Zan Dakata Saikuma Wani lokaci Insha AllahßµŠÅ Ä MµTµ Littafi Na Daya (1) Part E. Marubucin Littafin Abdulaziz Sani M/Gini babu wani boka da ya isa ya baka amsar komai binciken sa da matsayin sa a hallarar tsafi". Koda gama fadin haka sai boka Rufyan ya juyo sosai ya risina ga Sarki ya cc, "Na barka lafiya ya shugabana. " Nan take ya juya ya fice. Har Muraisu ya yi yunkurin ya sake zama a gaban Sarki sai ya yi masa nuni da cewar ya tashí yajc ya fara shiryc-shiryen tafīya. Cikin sanyin jiki Yarima Muraisu ya juya ya nufi kofar fita. Har ya sa kafarsa guda wajen kofar sai ya kira sunansa ya waigo suka dubi juna. Sarki ya yi masa wani dan guntun murmushi, ya ce, "Kafin ka tafi a goben ka zo mu yi sallama domin na baka gudunmawata ta kariya, domin ba lallai bane ka dawo ba ka riskeni a rayc". Koda jin wannan batu sai zuciyar Muraisu ta karaya, nan da nan idanunsa suka ciko da kwalla amma sai ya daure ya juya ya fice daga cikin urakar zuciyarsa cike da sake-sake yana mai cewa a ransa, "To wai shin wacce irin kariya Sarki zai bashi alhalin ya yarda da kansa kuma ya san zai iya kare kansa daga kowacce irin masifa?". Tun da Yarima Muraisu ya bar turakar Sarki ya koma tasa sai ya kasa zaune ko tsaye, tunani da fargaba suka cika masa zuciya. A haka dai ya samu ya Byara kayau yakinsa kuma ya kimtsa kayayyakinsa Wadanda zai yi wannan afiya da su. A sannan ne ya zauna ya yi tagumi ya shiga sabon tunani. Abinda y fara fada masaa rai shi nc wai shin waccc irin sabuwar rayuwa ce ne ta zo masa haka? Ya ya shu da bai taba yin soyayya ba, bai ta6a magana da budurwa ba ta tsawon dakiku za a cc da shi ya tafi neman wadda zai aura a lokaci guda haka?" Muraisu ya sake zurfafawa a tunaninsa sai ya fahimci cewa akwai alamun cewa wannan sabon yanayin rayuwa da ya tsinci kansa a ciki yana da matukar rikitarwa da tashin hankali domin ya fahimci cewaa lokacin da zai rasa komai da kowa nasa ne ya zo tunda an cc lallai za a ci su da yaki. To abin tambaya anan shi ne shi yana ina har za a zo a cisu da yaki? Abinda ya yi imani da shi shi ne, idan har za cisu da yaki, tabbas baya nunfashia doron kasa. Muraisu na cikin wannan hali hali ne wata Kuyangarsa mai kula da abincinsa ta shigo cikin turakar ta ajiye masa abinci da ruwan inibi a cikin tambulan da kofi a gabansa. Maimakon ta juya ta fita sai ta zauna a gefe daya ta zuba masa ido kawai. Al'amarin da ya matukar bashi mamaki ke nan domin sama da shekara bakwai kenan wannan Kuyanga tana yi masa wannan bauta amma duk sa'adda ta kawo masa abinci ajiyewa take ta fita. Hasali ma basu ta6a yin magana ba da juna a tsawon shckarun zamansa da ita. Ita dai wannan Kuyanga kyakkyawa ce sosai kuma launin fatar jikinta ruwan kasa ne mai ban sha'awa, sannan akwai kuruciya a tare da ita, domin sa'adda ma ta fara yiwa Muraisu bauta ba ta fi shekara goma ba a duniya, don haka yanzu tana da shckara goma sha bakwai ne kacal, kuma ana kiranta da suna Sabirat. Lokacin da Yarima Muraisu ya ga Sabirat ta zauna kuma ta Kura jnasa idanu sai ya daka ma ta tsawa ya ce, "Ke kuma fa, lafiya, akan wane dalili za ki zauna mini a cikin turakata?". "Ka Cikin firgici Sabirat ta mike tsaye zumbur! sannan ta durkusa bisa gwiwoyinta ta ce, gafarceni ya shugaban a, Sarki ne ya ce lallai yau idan na kawo maka abinci kada na fita sai na tabbatar ka ci ka sha tukunna sannan na korna na bashi labari". Koda jin wannarı batu sai Yarima Muraisu yaji wari irin dadi ya shigeshi, bai san sa'adda ya sakia murmushi ba ga Sabirat. Wannan shi ne karo na farko da ta taba ganin ya yi ma ta murmushi a iya tsawon rayuwarta da shi. Shi dai Yarima Muraisu ko kadan mace bata dameshi ba, domin ba a taba ganian ranar da ya bukaci wata baiwa ba ko Kuyanga, kai har ma wasu suna zargin ko bashi da cikakkiyar lafiya. Babu abinda ya sa a gabansa kullum dare da rana face horar da kansa yaki da kuma yin ladabi da biyayya ga Sarki yana gudanar da duk aikin da aka umarceshi da yi. Lokacin da Kuyanga Sabirat ta ga Yarima Muraisu ya dubeta har ya yi ma ta murmushi sai hankalinta ya kwanta ta mikc tsam daf da shi ta zauna yadda har suna iya jin num fashin juna ta ce, "Shin ka yi mani izini na civar da kai da hannuna? Maimakon ya ba ta amsa sai ya dubcta kawai ya sake yin murmushi. Nan take Sabirat ta dinga đebo abincin tana bashi a baki. Fara hakan ke da wuya sai ta ga hawaye ya zubo masa, al'amarin da ya matukar girgiza ma ta hankali ke nan ta firgita ainun ta ce, "Ya shugabana ka yafeni, idan wannan abu da na yi maka ya bata ma ka rai?" Da jin haka sai Muraisu ya yi mnurmushi sannan ya dubeta ya ce, "Mene ne sunanki?" Cikin matukar mamaki ta ce, "Sunana Sabirat." Ba komai ne ya sa Sabirat tayi mamakin jin wannan tambaya ba face sanin cewa bata da matsayin da zai tambayi sunan na ta kuma ta san lallai bai sani ba, tunda a shi da wani amfani a wajensa. Muraisu ya sake yin murmushi a karo na biyu a gareta, sannan ya sa hannu ya share hawayen da ke zuba a idonsa ya ce, Ya ke Sabirat kiyi sani cewa a iya sanina ke ce mutumn na biyu a duniya wanda ya taba ciyar da ni a hannunsa. Mahaifina shi ne mutum na farko. ba wani abu bane ya sa ni kika ga ina zubar da wannan hawaye ba face na tuna cewa a rayuwata ban san dadin uwa ba, tun ina jariri ta mutu ta barni. Mahaifina ne ya ci gaba da renona har na girma, yau gashi shima mutuwa za ta rabamu a ko yaushe daga yanzu. Yanzu an umarceni da na fita neman matar da zan aura gobe, kuma zan tafi na bar mahaifina a cikin wannan hali na matsanaiciyar rashin lafiya. Bani da tabbacin zan dawo na sameshi a rave. bani da tabbacin zan zamo abinda zan tafi nema, Shin mene ne karshen rayuwata? Ga dukkan alamu zan rasa komai da kowa ke nan tunda dan uwana ma guda daya da ya rage mini ya zama abokin gabata, kuma ya gujeni. Ashe haka rayuwa take da rashin dadi idan mutum ya rasa masoyi?" Sa'adad Yarima Muraisu yazo nan a zancensa, Sal Kuyanga Sabirat taji ta kamu da tsananin tausayinsa, bata san sa'adda ta rungumeshi ba, suka fadi kasa, kawai sai ta shiga shafar gashin kansa. Ashe abinda ta bashi ya ci akwai banju a ciki. Nan take kuwa barci ya kusanceshi, cikin tsananin farin ciki ta mike tsaye ta kura masa idanu. Nan take taji ta kamu da tsananin kaunarsa, domin shi ne da namiji da ta taba runguma a rayuwarta a lokacin da balaga ta zo ma ta. Kasancewar babu inda tayi bauta face a wajensa, kuma musaranan Sarki Salmar yasa aka siya ma sa ita domin ta rinka debe masa kewa, kuma ya yi saboda ita tunda tun tana karama aka siyota, shima a lokacin bai fi shekara ashirin ba a duniya, amma sai gashi bai yi sabon da ita ba, kai ko sunanta ma bai taba sani ba sai a yau din nan. Lokacin da Kuyanga Sabirat ta kurawa Yarima Muraisu idanu sai ta ce a cikin ranta, "Hakika duk macen da ta auri Yarima ta garma morewa, dormin duK abinda mace take so akwai a tarcd a shi. Ga kywawan halaye, kuma gashi dan Sarki. Ina ma dai a ce ni ce matar aurcn da zai tafi ncma a gobc. hakika da na Zama tauraruwa a cikin matan wannan zamani. Koda gama fadin haka sai Sabirat ta tafi da baya da baya ta fice daga cikin turakar tana kallon Yarima kamar za ta fasa fitar ta koma ta zauna a gabansa. Fitarta ke da wuya

Chapter 3 of 4