Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
rawa sai ya ji zuciyarsa ta yi fari, wani lokacin ma har yi musu tafi yake. Da zarar ya yi tafin sau daya sai ka ji gaba dayan jama'ar da ke fadar ma sun yi koyi da shi. Ana cikin wannan nishadinc aka ga wani. Bardc daga cikin Dakarun da ke gadin gidan sarauta ya ratso ta tsakiyar 'yan matan da ke rawa da sauri ya iso gaban Sarki Ishmar. Da zuwansa sai ya zubc a kasa ya kwashi gaisuwa sannan ya budi bakı da nufin ya yi bayani, sai Sarki Ishmar ya yi masa nuni da cewa ya yi shiru. Cikin farin ciki ya mike tsaye sannan ya dubi wannan Barde da ke tsugune a gabansa, ya ce masa, "Ma za ka kona can bakin kofar gidan nan ka shaidawa masu gadi cewa su budewa bakona Yarima Huraisu kofa ya shigo da sauri. Kuma ka yi musu albishir da cewa ina sane da zuwansa, ina yi masa barka da zuwa." Koda jin wannan umarni sai Barden ya mike zumbur! Ya juya ya fice daga fadar. A sannán ne 'yar matan da ke rawa suka cigaba da rawarsu, sauran fadawa da jana'ar gari kuwa sai suka cika da tsananin mamaki bisa jin cewar Sarki yana marhabin da dan Sarki Salmar babban makiyinsa a rayuwa. Maimakon Sarki Ishmar ya koma kan karagar mulkinsa ya zauna, sai ya daga hannunsa na đama sama, ta ke masu kida suka daina, masu rawa suka kame, fadar tayi tsit! Tamkar babu nmai rai a cikinta Sarki Ishmar ya kada tafin hannunsa, kawai sai Makadan nan da 'yan rawar nan suka juya suka fice daga cikin fadar. Sarki Ishmar ya sake tafa hannunsa, sai ga wadansu kuyangi su tamanin sun fito daga can cikin gidan sarautar sun caba ado na gani na fada. Kuma kowacce daga cikinsu tana dauke da karamin Kwando wanda aka cika da fure mai ruwan dorawaa. Arba'in daga cikin kuyangun sun jeru a layi tun daga bakin kofar shigowa fadar har izuwa daf da karagar Sarkin hannun dama. ragowar arba'in din su ma suka jeru 6angaren hannun hagu. Tsakiyar fadar ta zama wajen babu kowa kuma ba a hango kowa face Sarki shi kadai tak! da karagar ta mulki ya tsaya cak! Yana kallon kofar shigowa, yana ta murmushi. A dai dai wannan lokacin ne aka ga Yarima Huraisu tarc da yaransa bivu Busara da Sadauki Rauhaz sun shigo cikin fadar. Huraisu ne akan gaba. Busara da Rauhaz na take masa baya, dukkanninsu a cikin gagarumar shigar yaki suke. Koda suka sawo kafafunsu cikin fadar, suka fara tafiya, sai wadannan kuyangi suka rinka debo wannan fure suna watsa musu a jikinsu yana ta zubewa kasa. Ya yin da kamshin furen ya doki hancin su Huraisu sai suka cika da farin ciki, domin alamace ta cewar ana nurna da zuwansu. Koda Sarki Ishmar ya hango tahowar Yarima Huraisu sai ya kasa jiran karasowarsa inda yake ya taho gareshi da sauri fuskarsa cike da annuri kamar wanda ya ga dan uwansa na jini wanda suka dade ba su hadu ba. Sarki Ishmar ya bude hannayensa biyu ya tari Huraisu shima sai ya bude nasa hannayen, ai kuwa suna haduwa suka rungume juna. Saboda murna har sai da Sarki Ishmar ya sumbaci gosbhin Huraisu ya ce, "Lale marhaban da haske mai yaye duhun bakin cikin Zuciya," Huraisu ya janye jikinsa daga cikin na Sarki Ishmar suka fuskanci juna ya ce,"Ya ya aka yi na zamo haske mai yaye duhun bakin cikin zuciya? Sarki Ishmar ya ce, "Ba komai bane ya sa na yi maka kirari da wannan suna ba face kaine mutumin da zai cika mini burin zuciyata burin da ya addabi iyaycna da kakannina." Koda gama fadin haka sai Sarki Ishmar ya kama hannun Huraisu ya ja shi suka nausa cikin gidansa sarautar. Har Busaru da sadauki Rauhaz sun yunkura za su bisu a baya, sai Dakarun Sarki Ishmar suka sha gabansu wani daga cikinsu ya ce, "Ai ku iyakarku ke nan." Kamar Sarki Ishmar ya bayansa sai ya waigo ya dubi Busaru ya ce da shi, "Akai su san abinda ke faruwa a Badakaren da ya tare su Busaru na su masaukin". Nan take Badakaren ya yiwa su Busaru jagora suka shige cikin wata kofa mai zurfi. Sarki Ishmar da Huraisu ma suka shiga cikin wata kofar dabam suka kulle. Faruwar hakan ke da wuya sai fadar ta fara watsewa, kafin a jima ta zama wayam kowa ya kama gabansa. Lokacin da Sarki Ishmar ya kama hannun Yarima Huraisu ya ja shi izuwa cikin gidan sarautar sai suka yi ta tafiya tamkar gidan bashi da karshe, duk inda suka wuce sai dai ka ga Dakarun tsaro suna rabc musu suna basu hanya. Abinda ya daurcwa Huraisu kai shi. ne yadda Sarki Ishmar ya saki jiki da shi kuma suke ta hira a ya yin da suke tafiyar tamkar dama can,sun saba da juna. Cikin wani katon falo suka tsaya. Da shigarg Huraisu ya ga babu komai a ciki facc wani katon zagayayyen tebur wanda a kansa an jcra farantan abinci iri-iri sama da kala dubu kuma a gaban kowannc faranti akwai Kuyanga guda daya wacce ita ce za ta zubawa mutum kalar wannan abinci idan yana da bukata. Madakin Gini Duk da cewa Huraisu dan Sarki ne sai da ya rinka hadiyar miyau domin kamshin abincin ma kawai ya addabi hancinsa, so yake kawai su zauna su fara cin abincin in ban da ma yana jin kansa da tun kafin ayi masa tayi zai fara gusar da yunwarsa. Kamar Sarki Ishmar ya san abinda ke ran Huraisu, suna zama ya dubi kuyangin gaba daya su dubu ya ce, "Kowacce ta zubo kalar a cikin falle biyu ta kawo. Aka tara kalolin abinci a gaban su. Sarki Lshmar ya dubi Yarima Huraisu ya ce, "Ya kai babban bakona ai sai kayi sauri ka ci abincin nan domin mua da aiyuka da yawa a gabanmu." "Ko da jin wannan batu sai mamaki ya kama Huraisu. domin shi a ganinsa bai ga wasu aiyuka da za su yi ba facc tattauna maganganu. Nan dai suka dukufa wajen cin abincin. Da farko sai Huraisu ya tsaya yana ruwan ido, domin va rasa kalar abincin da ya kamata ya ci. Duk wanda va kalla sai ya ga cewa dole ne ya yi dadi. Kawai sai ya rinka yin loma daya a cikin kowanne tamka yana dandanawa ne. Kafin ya ankara tuni ya koshi, kuma bai đancfana koda kala arba'in ba. Bisa dole ya hakura ya sha nuwan inibi sannan ya dauki tulun giya ya fara sha. Koda Sarki Ishmar ya ga Huraisu na neman shan giyar da yawa, sai yai sauri ya fisge kofin giyar da ke hannunsa ya ajiye a gefe daya ya dubeshi ya kyal kyale da dariya, ya ce, "Ya kai wannan dar Sarki, ina mai shawartarka da ka rage shan giya, in ba haka ba kuwa, wata rana za ta sa ka aikata abin da za ka yi ta nadamarsa har izuwa karshen rayuwarka. Yanzu haka fa kafin ku iso nan Kasata ka shanye ganga biya: ta giya a cikin kwana ashirin da daya. Kuma a can gidanka na dajin Hirzul, a kullum sai ka sanye tulu uku na giya." Sa'adda Sarki Ishmar yazo nan a zancensa, sai Yarima Hraisu ya yi gyatsa, sarnan ya ce, "Ya kai wannan Sarki mai daraja, ka y1 sani cewa giya tana kankare damuwa da bakin cikin zuciya, shi ya sa ba zan iya rage shanta ba a lokaci guda, sai dai a sannu. Bakin cikin da ya addabi zuciyata kuwa. komai ba ne face tsananin kiyayyar da ke tsak tia da mahaifina da kama đan uwana, na rasa hvar da zan bi na kar6o mulkin birnin Lairis daga hannunsu ya Zamana cewa na shafe Su a doron kasa." Lokacin da Yarima Haraisu yazo nan a Zncensa, sai Sarki Ishmar ya bushe da mahaukaciyar dariya har ia fadowa Rasa daga kan kujerar da ya ke zaune. Nima saboda jin wannan dariya haka yasa zan dakata anan saikuma lokaci na gaba Insha Allah Fatan AlkhairiMungyarA Matsalar ßµŠÅ Ä MµTµ Littafi Na Daya (1) Part C Marubucin Littafin Abdulaziz Sani M/Gini Likes and comments Domin Mu cigaba Al amarin da va matukar baiwa Huraisu mamaki ke nan. Ya mike da sauri ya taho gareshi da nufin ya tashe shi tsaye, kawai sai ya ganshi tsulum! A kan kujerarsa tamkar iska ce ta daukoshi ta mai da shi kan kujerar. Shi kansa Haraisu ya san cewa wannan abu aikin tsafi ne. Nan take Sarki Ishmar ya murtuke fuskarsa ya daina dariyar, sannan ya dubi Huraisu cikin tsananin damuwa tamkar zai fashe da kuka, ya ce, "Ya kai Huraisu, ka yi sani cewa lokaci ya yi da burinka zai cika, amma anan gaba bayan wadansu shekaru da za su z0, ni da kai zamu shiga cikin tsananin tashin hankali wanda idan tun yanzu ba mu yi wa tufkar hanci ba sai mun tozarta. Ina son ka saurarcni da kyau da kunnen fahimta, kuma ka kiyaye dukkan abubuwan da zan zaiyana maka domin idan ka yi kuskure daya sai nun shiga cikin fargabar da bana son mu shiga. Da farko dai, na san ka sani cewa a halin yanzu mahaifinka ya kwanta ciwo, kullum sai dai a kwantar a tayar, baya iya yiwa kansa komai. Bisa bincike da na yi na gano cewa abu nc mawuyaci nan gaba ya yi shekara guda a duniya ba tare da ya mutu ba. Tabbas wannan wata dama ce muka samu da zamu iya tara mayaka masu tsananin yawan da zamu iya cin birnin Lairis da yaki a cikin watannin kađan. Ka sani cewa, a halin yanzu ma yawan mayakana ne yasa Sarki Salmar da jama'arsa suka kasa samun nasarar yaRi a kaina. Koda yake, yakin da makayi a shekarun baya ne sa'adda kai da yayanka Muraisu kuna yara kanana bare kuma ayi yakin da ku, amma nayi imani cewa ko a yanzu ne za ayi yakin da ku ba za ku sami nasara ba akan jama'ata ba, musamman saboda na san cewa kai ba za ka yake ni ba. To yanzu fa Sarki Salmar ba zai iya yin yaki ba sai dai Yarima Muraisu ya wakilceshi. Na sani cewa, Sarki Salmar yafi Muraisu juriya, na ci, kwarewa da sanin tuggun yaki kuma koda ya koyar da Muraisu duk wadannan abubuwan Muraisu ba zai iya yin abin da ya yi ba, domin kama da wane bata wane. Shima Salmar ba zai yi irin jamurtakar da Kakanka ya yi ba. Bisa wannan dalili ne na ke son daga yau ka fara tanadin mayaka a can gidanka da ke daji, ya zamana cewa kullum muna basu horon yaki har tsawon kamar wata biyar, sannan sai mu yi gagarumin shirin yaki mu tasamma bimin Lairis. Tabbas idan har mu ka yi haka sai mun sami nasarar kama birnin. Matakin farko da zamu lura da shi, shi ne, dole ne mu hada karfi ni da kai mu yaki đan uwanka Maraisu a lokaci guda. Wannan ita ce, kadai hanyar da za abi a kai shi kas. Idan muka kuskura dayan mu ya tareshi har aka fafata sama da tsawon rabin sa'a sai ya sami nasara a kansa, Ina tabbatar maka da cewa, ni da kai zamu iya kai Muraisu kas idan har mun hada karfi. Da zarar mun kaishi kas kuwa, ni da kaina zan tsaga kirjinsa na dauko sirrin da za'a iya shiga dajin Kirzufa da shi. Ina so ka sani cewa duk fadin duniyar nan babu wata wuka da za ta iya bude kirjin Huraisu face wacce ake kira "Hirzul Subura". Ita dai wannan wuka ta Hirzul Subura, a yanzu haka tana nan acan birnin Darul Wasus, birnin da duk duniya babu kamarsa a fagen sarrafa karafa iri-iri, kuma 'anan ne makera na duniya kaf suka gama kure basirarsu ta kera makaman yaki da sauran kayan alatu na rayuwar yau da kullum. Fiye da shekaru dubu kawo i yanzu ba a taba kera Wuka mai kaifi ba tamkar Wukar Hirzul Subura, babu abin da bata yankawa, walau karfe ko dutse, kuma komai taurin abu ko kwarinsa, bayan ta yanka shi ba za aga ta dakushe ba, kuma kaifinta ba zai ragu ba. Idan akai yanka da ita sannan ne ma kaifinta ya ke karuwa. Wukar Hirzul Subura an bata mugun tsoro na gaban kwatance domin an ajiye ta ne a tsakiyar fadar birnin Darul Wasus, kuma an sakaleta a sama jikin rufin gini. Ba mna mutum ba, komai hatsabibancin aljani bai isa ya rabi inda takobin take ba, saboda karfin sibirin tsafin a ke jikinta duk abinda ya yi yunkurin taba wannan wuka take yake zama gawa. Bays ga haka, a kullum Dakaru dubu dari tara ne suke gadin wannan wuka dare da rana, kuma an kasa Dakarun gida biyu masu aikin rana dabam, haka ma masu aikin dare. Bisa binciken da na yi, mutum uku ne kacal a cikin fadin duniyar nan za su iya zuwa birnin Darul Wasus su iya dauko wannan wuka. Daga mabaifinka sai fan uwanka Muraisu sai kusna kai kanka." Koda jin wannan batu sai Huraisu ya dubi Sarki İshmar, cikin tsananin mamaki to mene ne dalilin da yasa Sai mu uku kacal za mu 1ya dauko wannan wuka?" Sarki Ishmar yai ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ainihin wukar Hirzul Sabura wani mashahurin mayakine ya kerata wanda ya kasance Rasurgumin matsafi kuma shi ne, tushen zuri'ar dangin mahaifinku. A yadda ya kera muku wukar babu wanda ya isa ya yi amfani da ita face ya kasance jinin zuri'arku. Wani abin mamaki shi ne, gaba dayan zuriar tasa ta kare babu irinta a doron kasa face ku ukun nan kacal." Yarima Huraisu ya yi shiru yana nazarin al'amarina cikin zuciyarsa har izuwa wani dan lokaci sannan ya dago kai ya dubı Sarki Ishmar ya ce, "Na ji ka ce an baiwa wukar Hirzul Subura mugun tsarc ta ya ya zan iya kavar da tsaron har na daukate?"h, Ishinar ya yi munushi ya ce, "Ta hanyar hada karfi da ni gami da kiyaye dokokin da zan shimfida mana. Duk za ka san wadannan al'amura anan gaba kəfin ranar zuwanmu birninku ta zo. Mataki Da farko da za mu oi don cimma nasara b:sa wannan gagarimin aiki da ke gabanmu shi ne, doic mu baiwa juna horon yaki [ni da kai domin kowanncnmu ya kowa domin na koyar da kai abinda baka sani ba, kaima ka koyar da ni abinda ban sani ba. Ta haka ne san iyakar jarumtakar kadai zamu larwatsa Dakarun da ke tsaron wu kar Hirzul Subura Kuma mu sami nasarar a yakin da zamu je mu yi a Rasarku. iya hada karfi biyu wanda Mataki na biyu shi ne, dole ne mu ci gaba da tara nayaka wadanda ba za su gaza miliyan daya da rabi ba, kuma mu basu horon yaki irin wanda A kalla sai wadannan mayaka sun shafe Suna karbar wannan horo sannan za su kware ainun su Zama GUGUWAR ANNOBA mai shafe birni komai girmansa da karfin tsaronsa. Mataki na uku wanda shi ne na karshe kuma shi ne mafi hadari, dole ne mu kama Yarima Muraisu da hannunmu ya yin da muke yaki da su sannan mu kaishi kas mu tsaga kirjinsa mu ciro wannan gashin sihiri da ke jikinsa sannan ne burinka zai gama cika idan na sanya wannan gashin sihirin a cikin kirjinka yadda za ka iya zuwa dajin Kirzufa ka yi farauta a cikinsa kamar yadda mahaifinka ya yi har ya sami daukaka a duniya fiye da kowannc Sarki." nuke da shi. wata bakwai Sa'adda Sarki Ishmar yazo nan a zancensa sai hankalin Yarima Muraisu ya dugun Muraisu ya. dugunzuma saboda tunanin wasu al'amura guda biyar da suka fado masa a rai. Abu na farko shi ne, yanzu mece ce ribar Sarki Ishmar idan har ya taimaka mani na ci kasarmu da yaki, kuma na sarni damat shiga dajin Kirzuts? A bayaninsa bashi da wani buri wanda ya fi ya mallaki dajin Kirzufa, Babu yadda za ayi ya iya nallakat đajin Kirzufa face ya mallakí yashin sihirin mahaifina. Waninan yana nufin ke nan ba lallai bane idan ya ciro gashin sihirin a kirjin dan uwana ya mallaka mini ba. Ashe kuwa akwai alamun cewa Sarkí ya yaudarata, wato ya yí amfaní da ní don kawai ya biya bukatarsa, idan kuwa haka ne dole ne ya dauki tsattsauran matakí akan hakan," Huraisu na cikin wannan tunanin zuci ne shmar ya dafa kafadarsa ya ce, "Wai shin tunanin ne kakec yi ne haka ina ta nagana armma hankalínka ya tafi wani wurí? Huraisu ya yí firgigit kamar wanda ya farka daga barci sannan ya dubi Ishmar ya ce, "Ka yafarceni ya kai wannan Sarki, ka yi sani cewa hankalina ne ya dugunzuma bisa jin wadannan tsauraran matakai uku da zamu bi don ganin mun címma burinmu, ni kam guiwata ta fara yin sanyí, dornin ganí nake karmar ba zai yiwu ba," Koda jin wannan batu saí Sarkí Ishmar ya bushe da dariya sannan ya ce, "Ai idan har mun bi wadannan matakai daí-daí tabbas bukata za ta biya. Yanzu sai ka tashi mu tafi na kaika izuwa masaukinka domin ka samí barci da isasshen hutu saboda gobe da sassafe zan turo a tashcka domín mu je filin motsa jini mu jarraba jarumtakar juna ni da kai". Koda jin wannan batu sai Yarima Huraisu dubi Sarki Ishmar ya yi masa murmushin mugunta sannan ya ce a ransa, "Ya zai hada jarumtakata da tasa kasance sa'an mahaifina. Lallai kuwa Zan nuna masa cewa sabon kashi da sabon jini ba dai-dai take da tsohon kashi ba ma za ayi wannan dattijon Ganin murmushin da Huraisu ya yi ne ya sa Sarki Ishmar ya yi zargin irin abinda Huraisu ya aiyana a ransa don haka sai shima va maida masa da mnartanin murmushin kuma ya ce a ransà, "Lallai yaro, yaro ne, domin bai san wuta ba sai va tabata da hannunsa. Tabbas sai na nunawa Huraisu cewar ko Zaki ya mutu gawarsa ta fi gaban wargi." Gama aiyana hakan ke da wuya sai Sarki Ishmar ya mike tsaye shima Huraisu sai ya mike tsayc suka kama harnun juna suka ice dana cikin dakin cin abincin, a sannan ne wadannan kuyangi guda dubu suka kwashe farantan abincin da ke kan tebur din suka fice a su zuciyoyinsu cike da takaicin an sa su sun dafa abincin da mutum dubu za su iya ci su koshi, amma gashi mutum biyu ne kacal suka taba dan kadan sai dai su je su ci iya Cinsu ragowar kuwa su zuba a shara. Kullum haka suke faman wannan aiki darc da rana, sbaoda wadatar da tayi musu yawa a gidan Sarautar. Lokacin da Sarki Ishmar da Yarima Huraisu suka baro cikin dakin cin abincin suka ci gaba da tafiya a cikin harabar gidan sai kwatsam! Suka hango wata: santaleliyar halitta abar kwatance daga necsa adan da ta nufo yaresu, fuskarta cike da annuri tana murmushi, wanda yasa tsigar jikin Yarima Huraisu ta tashi gaba daya ya tsaya cak a waje daya kuma ya Rame kamar gunki. Tunda Yarima Huraisu yazo duniya bai taba ganin tsaleliyar byaklyvwar budurwa ha ha kamar wannan. Kai ko a tarihi ko labaran duniya bai taba jin labarin mace mai kyau kamar na ta ba. Mace ce doguwa mai matsakaicin kaurin jiki, Kirjinta a cike yake, cikinta a shafe, kuma kugu mai fadi da matukar tudu daga Laya, grshin kanta baki ne sidik yana ta kyalkyali da shcki kuma ya zuba har kasan kwankwasonta. Idan tana tafiya sai ka ga kanuar dukkan gabban jikiría karyewa za su yi, domin ko ina motsawa yake. Fatar ¡ikinta fara ce sol irin farin nan mai kyau wanda babu ratsin komai, kuma tana sheki da taushi tamkar idan aka latse jini zai fito. Tun daga nesa kyakkyawar budurwa bude hannayenta biyu ta rugo izuwa ga rkr ishmar ta rungumeshi cikin farin ciki. Sarki Ishtaar ya janye jikinsa daga cikin na ta ya dubcta cikin damuwa ya ce, "Mene ne ya hanaki zuwA dakin cin abinci yau? Tun dazu ina tare da bakona a can har mun kammala cin abincin mun fito". Budurwar tayi murmushi ha kyawawan fararen hakorarta suka baiyana a fili ta ce, "Ka gafarceni ya: kai dana uwana, ka yi sani cewa jiya da daddarc na muka yi da kai wacce ta sa idanuna suka bushe, shi ya sa na yi ta barci har na makara ban fito da wuri ba". Sarki Ishmar "Ya ke ya yi murmushi ya ce, Husnaila rabin jikina, kin san cewa ba kya laifi a wajena koda kuwa kin karva dukkan dokokin da na kafe a garin nan, saboda haka ban ga dalilin da zai sa ki nemi gafarata ba. Yanzu zan raka bakona izuwa masaukinsa don haka ki je turakata ki zauna ki jirani Zan dawo mu tattauna muhimmanci." wani al'amari mai Cikin murna Husnaila ta juya ta nufi inda bangarcn turakar Sarki Ishmar take, ko kallon Yarima Huraisu ba ta yi ba, bare ma ta yi masa magana, tamkar ma ba ta san da shi ba a tsaye a wajen. Shi kuwa Huraisu tun sa'adda idanunsa suka yı arba da ita ya rude, ya kidime kuma ya dimauce ainun domin ji ya yi kamar an zare masa ransa gaba daya don haka sai ya kame kamar gunki kuma ya kura ma ta idanu ko kiftawa ba ya yi, har moa ya tafi duniyar tunani inda ya tsinci kansa a cikin wani kcrarren gida kuma akan wani luntsumemen gado shi da Gimbiya Husnaila suna morewa Soyayya. Yana cikin wannan tunani ne Sarki Ishmar ya girgiza kafadunsa ya dawo cikin haiyacin sa, sannan ya daka masa tsawa ya ce, "Koda wasa kada ka taba tunanin za ka kusanci wannan yar uwa tawa, domin ba: irin sauran 'yan matan da kake yiwa fyade bane a can Kasarku. Wannan kanwata ce uwa daya uba daya, kuma ita ce kadai ta rage mini a duniya. Ina sonta fiye da yadda nake son kaina, kuma na rantse da darajar iyaycnmu zan iya karar da dukkan mutanen wannan nahiyar tamu idan har aka taba lafiyarta ko mutuncinta. Duk wata alaka da ke tsakanina da kai za ta iya rushewa idan ka kuskura ka kusanceta. Abinda nake so da kai shi nc, ka dauka cewa a mafarki kuka hadu, mafarkin da har abada ba zai taba zama gaskiya ba. A karshe ina mai sanar da kai cewa kariwata Gimbiya Husnaila ba za ta yi aure ba kuma har ta bar duniya babu wani da namiji da ya isa ya santa 'ya mace koda kuwa bana numfashi a doron kasa, domin na cire ma ta sha'awar da namiji, kuma na tsareta da dukkan karfin sihirina na tsafi. Kai in takaice maka zan ce ko mutuwa tayi namijin kuda ma bai isa ya taba jikinta ba bare bil'adama ko aljan". Koda gama fadin haka sai Sarki Ishmar ya wuc gaba ya ci gaba da tafiya abinsa ya bar Yarima Huraisu a tsaye cikin tsananin mamakin wannan jawabi da ya yi masa. A sannan ne ya gano dalilin da ya sa Gimbiya Husnaila ta shareshi ya zamana cewa ko kallonsa bata yi ba a sa'adda suka hadu. Nan dai Sarki Ishmar ya kai Yarima Huraisu har masaukinsa inda suka yi sallama ya juya ya tafi ya barshi. Huraisu ya kunna kai izuwa cikin tafkeken: falon wanda Sarki Ishmar ya yi masa nuni a matsayin masaukinsa. Falo ne babba mai fadi da tsawo wanda ke shimfide da koren kilishi mai taushi, ga kujeru manya da kanana suma duka koraye. Kai hatta labulayen da aka sa a jikin tagogi da kokofi duk koraye ne, abin dai gwanin ban sha'awa. Da shigar Yarima Huraisu cikin wannan falo sai ya tsaya ya yi turus! Ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin abokan, wato manyan yaransa guda biyu Busaru da sadauki Rauhaz a kwance bisa wannan kilishi ga abinci nan a gabansu iri-iri birjik da 'ya'yan itatuwa sun ci sun bari. Sannan sai ya ga wadansu kuyangi guda shida a tare da su suna yi masu tausa. A can gcfe daya kuma wadansu kyawawan kuyangi ne guda goma a zaune waje daya suna jiransa domin su tayashi kwana. Kallo daya Yarima Huraisu ya yiwa kuyangin ya ji ko kadan baya bukatar su kusanceshi. Cikin hanzari Busaru da Rauhaz suka mike tsaye zumbur! Suka risina suka yi gaisuwa ga Yarima Rubaisu suna wadannan kuyangi gaba dayansu sai suka zube suka gaisheshi. Busaru ya yi gyaran murya ya cc, "Ya shugabana ga kuyangi nan masn tayaka barci suna jira, kuna akwai giya ganga-ganga guda a cikin dakinka an tanada Kafin Busaru ya gama rufe bakinsa sai Yarima Huraisu ya tari numfashinsa ya ce, Bana bukatar komai yanzu, zan shiga dakina na kwanta, kada kowa ya dameni Koda gama fadin haka sai Huraisu ya bude daki ya shiga ya kwanta akan wrani kasaitaccen gado wanda ke dauke da shimfida mai tudu da taushin gaske ya kwanta. Kwanciyarsa ke da wuya sai ya daga kansa sama ya kurawa rufin cakin ido. Nan take fuskar Gimbiya Husnaila ta baiyana akan rufin dakin, yaji wani farin ciki ya lullubeshi. Kawai kuma sai ya ga hoton fuskar ta ta ya Bace. A dimauce ya mike zaune daga kan gadon ya kama kalle-kalle a cikin dakin ko zai sakc ganin fuskar Husnaila a jikin bango ko a kasa, Nima kuma a dimauce Na tashi Na tuna cewa zanfita kasuwa sbd haka sai Anjima Likes and comments Zai bamu zummar cigabaaßµŠÅ Ä MµTµ Littafi Na Daya (1) Part D Marubucin Littafin Abdulaziz Sani M/Gini Likes and comments Domin Mu cigaba Amma bai gani ba. Nan take ya gano cewa tsananin begenta nc ya sa ya ga kamar tana yi masa gizo. Al'amarin da ya matukar girgiza hankalinsa ke nan domin shi a rayuwarsa bai taba yin soyayya ba kumna bai laba jin yana son wata 'ya mace ba face da lalata, amma sai gashi wannan karon yaji yana son ya mallaki Gimbiya Husnailaa matsayin matar da zai aura". Koda Huraisu ya luno da kashedin da Sarki Ishmar ya yi masa akan Husnaila da irin maganganun da ya shai ia masa sai hankalinsa ya dugunzuma ya rasa abinda ke masa dadi. Shi kam yanzu ya san cewa ba zai iya cire son Husnaila a zuciyarsa ba, kuma ba karamin tashin yankali ne ya ce zai nemi soyayyarta tunda ita ba ta ma san meye so ba, kuma ba ta taba yin soyayya ba. Huraisu ya ci pgaba da tunani cikin matukar damuwa har izuwa lokaci mai tsawo, daga bisani sai ya yanke hukuncin cewa ya yi hakuri har izuwa lokacin da zai zama Sarkin birnin Lairus, tabbas a sannan ne zai iya mallakar Gimbiya Husnaila ko da tsiya-tsiya tunda a sannan ma ya mallaki gashin sihirin da ke kirjin mahaifinsu, in kuwa ya mallaki wannan gashin sihirin ya san cewa babubwani tsafi da zai yi tasiri a kansa. Idan kuwa tsafi ba zai yi tasiri ba a jikinsa lallai ya fi karfin Sarki Ishmar. Koda Huraisu ya zo nan a tunaninsa sai ya cika da farin ciki ya ji kamar ma ya mallaki Gimbiya Husnaila ne. Kashe gari da sassafe bayan su Yarima Huraisu sun yi buda baki sai aka turo wani hadini ya yi

Chapter 2 of 4