Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng BUSA A MUTU!!! Littafi Na Daya (1) Part A Marubucin Littafin Abdulaziz Sani M/Gini Marubucin ya fara da cewa... A YARIN Fatake ne da 'yan gudun hijira daga wata babbar kasa da ake kira Lairus. Yawansu ya kai dubu uku, wasu akan dawakai suke tafiya, wasu a rakuma da alfadarai. A kalla wadannan mutane sun shafe kwana tara suna tafiya a cikin daji suna keta kwazazza bai, koramai da duhuwoyi. A cikinsu akwai zaratan samari majiya Rarfi, sannan akwai mata, yara da tso fafffi kuma yawancinsu iyalai ne, wato wani zaka ga tarc yakc da matarsa da kuma dansa ko 'yarsa ko kuma 'ya'yansa guda biyu ko uku. Wani kuwa tarc yake da mahaifinsa ko mahaifiyarsa. Wani yana tare da dan uwa ko 'yar uwa. Kuma gashi suna daukc da dukiyoyinsu wasu ma har da dabbobinsu. Abin tambaya anan shi nc, ina wannan ayari suka nuta, kuma daga ina suka fito, sannan ina suka dosa? Ba wani abu banc ya sa wannan ayari suka yi gudun hijira ba face masifar yaki da ta 6arkc a kasar tasu ta Lairus wadda ta haddasa asarar miliyoyin rayuka da dukiya. Shi dai wannan yaki ya faru nc sakamakon wadansu 'yan tawaye wadanda suka yiwa Sarki Muraisu borc domin tabbatar da cewa sun tunkude mulkinsa da karfin tsiya saboda kawai ganin cewa shi. mutum ne adali wanda baya zalunckuma bai yarda da zalunci ba Su dai wadannan 'yan tawaye sai da suka shekara bakwai suna tanadi na wannan yaki suna tara dakaru a baye a can wata kasar daban gami da kayan yaki. Sai da suka tara mayaka miliyan biyu da rabi kuma ya zamana cewa kullum a cikin basu sabbabbin horon yaki ake. Babban abin takaici shi ne ba wani bane ya dauki nauyin wadanma Dakarun iawayc ba face Yarima Huraisu kanin Sarki Muraisu wanda suka kasance uwa daya uba daya. Tun Muraisu da Huraisu suna yara kanane suka taso basa jituwa saboda bambancin halaye sa ra'ayi suka zama tankar abokan gaba, ya zamar.a ccwa basa yiwa juna ga maciji. Babu abinda ya tsananta gaba a tsakaninsu face Huraisu ya san ceva idan mahaifinsu Sarki Salmar ya mutu, Muraisu ne zai hau kan karaga saboda tuni Sarki Salma ya yi nuni da hakan har ma ya bar wasiyar hakan. Halayen Sarki Saimar iri dayane dana Muraisu wato suna da son taiakawa,tausayi da taimako. Kwata- kwata abin duniya bai danesu ba. Begu da kari Muraisu ya kasance saurayin mai farin jini matuka a wajcn jama ar gari saboda ganin cewa ya taso da halaye na mahaifinsa. Duk inda ya wuce ma sai dai ka J1 ana yi masa kirari da Magajin Sarki. Shi kuwa Huraisu jama'a sun tsaneshi kamar yadda suka tsani Mutuwarsu saboda bakar zuciyarsa ta zalunci. Ko kallonsa mutum ya yi ya tsargu Sai ya zare makami nan take ya sareshi. Idan ya ga budurwa mai kyau ko 'yar gidan uban waye sai ya yi ma ta fyade haka kurma duk dukiyar da ya gani in dai ya ji yana bukatarta to fa sai ya kwaccta. A duk sa'adda Huraisu ya yi irin wannan mugun aiki baya yarda ya dawo gida sai dai ya shiga daji ya buya saboda sanin cewa saii Sarki ya sa an yi masa hukunci mai tsauri dai-dai da laifin da ya aikata. Sarki ya sha sawa a yiwa Yarima Huraisu bulala arba'in ko hamsin a farfasa masa jiki har sai ya yi jinya. Kuma duk sa'adda ya aikata laifin ya gudu daj babu mai iya zuwa ya kamoshi da karfin tsiya sai dan uwansa Muraisu. Muraisu da Huraisu sun kasance gawurattun Sadaukai na gaban kwatance kuma kwararrun mayaka wadanda suka yi shuhura a cikin nahiyarsu sai dai Muraisu ya fi Huraisu karfi, jarumtaka da iya yaki nesa ba kusa ba. Wani lokaci idan Muraisu ya tafka laifi sai Sarki ya sa a daureshi tamau a sama a jikin dirka a gasashi a cikin rana, ba ci ba sha har tsawon sa'a ashirin da hudu amma saboda naci da bakin hali idan aka sakeshi gobe ma sai ya kara aikata wani laifin da ya fi na baya. Azaba ko bazarana ba ta firgita Huraisu koda kuwa ya san cewa zai iya rasa rayuwarsa sakamakon azabar da za a yi masa. Sarki Samral yana matukar kaunar Yarima Muraisu saboda ladabinsa da biyayyarsa da kuma halayensa da ya gado gami da yadda ya ga jama'ar birnin Lairus ke tsananin kaunarsa suke girmamashi. Ko kara Sarki Salmar ya ajiye Muraisu ba zai ketarce ba. Mahaifiyar Muraisu ta rasu ne a ranar da ta haifesu suka zo duniya lokaci guda tagwaye. Muraisu da Huraisu suna matukar kama da junansu tamkar an tsaga kara. A wannan rana an cc Sarki Samral ya yi matsanaicin kuka da bakin ciki. Al'amarin da ya matukar baiwa mutanen kasar gaba dayansu mamaki ke nan, domin a tarihin rayuwar Sarki Samral tun daga kuruciyarsa kawo izuwa girmansa ba a taba ganin kwalla ba a idanunsa, amma sai gashi an ga ranar da yake ta kuka kishin6ar! da hawaye daki-daki, wani na bin wani. Sarki Samral kasaitaccen sadauki ne kuma gabjcjen mutum mai kirar mutanen farko, domin duk sa'adda yaje nahiyar da ba a sanshi ba da zarar mutane sun ganshi sai su firgice su kama guje-gujc, wasu su ce sun yi gamo da aljani, wasu kuma su ce ai fatalwa ce. Komai girman bishiya da hannu daya Sarki Samral ke hankadeta ta fadi kasa. Komai girman dutse da nauyinsa idan har ya ritsashi da hannayensa biyu to fa zai iya rabashi da kasa ya dagashi sama ya yi doguwar tafiya da shi ba tare da ya gaji ba.. Idan kuwa zai fita yaki saj dai a tanaji giwaye kamar guda arba in a matsayin ababcn hawansa, kumna babu wacce za ta , AA Misau Nake, iya daukarsa sama da tsawon rabin sa'a ba tare da ta gaji ba ta durkushe kasa saboda tsananin nauyinsa. Kai idan Sarki Samral ya fusata yana iya daukar ita kanta giwar ya yi wurgi da ita tamkar ya yi wurgi da hoge. Labarin Jarumtakar Sarki Samral ya bazu ko ina a nahiyarsu har ma da sauran nahiyoyin da ba nasu ba. Kuma ba a ta6a samun GWARZON MAYAKI ba kamarsa. A tarihin yake-yaken da ya yi a rayuwarsa tun kafin ya hau karagar mulki har izuwa sa'adda ya bar duniya ba a taba cinsa da yaki ba, kuma ba a taba ji masa ciwo ba. Idan yana tsakiyar abokan gaba yana saransu da sukarsu da takobinsa sai ya shafe sa'a goma sha biyu bai gaji ba, kuma tsananin zafin namansa da Rarfin gudunsa ya wuce misali kamar iska ce ke sarrafa gababen jikinsa. Da yake mutum ya kan haifi kansa sai gashi Sarki Samral ya haifo zakwakuran sedaukai da suka gado wannan girman jiki irin nasa da kuma jarurntaka tasa sai dai inda aka sami akasi Muraisu ya fi Huraisu komai ya ma ninkashi. Lokacin da fitinar Huraisu ta yi yawa kuma ta damu Sarki Samral ya zamana cewa duk irin azabar da aka vi masa da irin hukuncin da ake yi masa mai tsauri a duk sa'adda ya aikata laifi sun zama a banza sai Sarki ya kafa masa doka ta karshe ya sanar da shi cewa dukLa ranar da aka sake kamashi da laifin yin fyade ko sata ko kuma cin zali sai an yanke masa hannayensa biyu Domin kowa ya huta da fargabarsa saboda ya addabi Gaba dayan jama'ar birnin da Rauyuka. Sa'adda mutane suka ji wannan gagarumin bukunci da aka dauka akan azzalumi Huraisu sai suka cika da tsananin farin ciki. Tun daga wannan rana kyawawan 'yan mata suka sami 'yancin yawo a ko ina, attajirai suka rinka fatauci a ko ina a kasar cikin kwanciyar hankali, sabanin da can da 'yan fashi suka yawaita a ko ina a cikin kasar, kuma gaba dayan 'yan fashin yaran Yarima Huraisu ne. Lokacin da Yarima Huraisu ya ke kan sharafinsa na aikata duk irin laifin da ya ga dama ne ya tara yara a karkashinsa sama da dubu dari, kuma a kowanne birni da ke cikin kasar yana da wakilai. Duk sa'adda Fatake za su ratsa wata hanya ko kuma a duk inda za a yi wani gagarumin kasuwanci da dukiya mai yawa sai labari ya riskeshi sai dai kawai aga shi da yaransa sun baiyana a wajen sun tafka gagarumar 6arna. Ran biladama kuwa sun mai da shi tamkar na kiyashi. A wannan lokaci ne Huraisu ya tara dukiya mai tsananin yawan gaske saboda haka sai ya så aka gina masa wani tafkcken gida a tsakiyar waii daji da akc Kira Kirzufa, wanda ke tsakanin iyakar birnin Lairus da wani birni mai suna Hutaira. Shi dai wannan daji na Kirzufa dade ana rigima a Kansa a tsakanin kasashen biyu domin kowacce kasa kuma sau ashirin da daya ana yaki a zamanin Sarki Samral akan dajin, amma duk sa'adda aka yi yakin sai dai ayi ragas, duk da cewa Sarki Samral ya zama dodon maza kuma gagaraba dau. ba komai ne ya janyo Madakin Gini hakan ba face tsananin yawan mnayakan birnin Hutaira ya wuce misali. Akwai lokacin da Sarki Samral ya kwana arba'in Cif yana yaki da su shi kadai amma sai ya kasa karar da koda rabinsu, suma suka kasa hallakashi ko kaishi Ras. Duk sa'adda ya ga ya gaji ainun sai ya falfala da matsanaicin gudu su kasa cimmasa har yaje wani wurin ya buya sai ya huta sannan ya dawo a ci gaba da gumurzu. Gashi dai yana kashesu tamkar ana kakkabe ganyaycn bishiyoyi a daji, amma sai ka ga kamar matattu ne suke tashi saboda azabar yawansu. Kai a wannan zamani sai da masu bincike suka gano cewa ko mutan cn birnin Sin ba su kai rabin yawan mutancn birmin Hutaira ba. A karshe bisa dole Sarki Samral ya janye yakin da kansa ya koma birninsa ya hakura da mallakar dajin Kirzufa. Har Sarki Samral ya bar duniya da takaicin rashin mallakar dajin Kirzufa ya tafi, kuma kafin ya mutu sai da ya barwa Muraisu wasiyyar cewa duk yadda zai yi ya tabbatar da cewa ya mallaki dajin Kirzufa kafin shima ya bar duniya. Muraisu ya dauki alkawarin cewar koda kuwa zai rasa rayuwarsa a kokarin mallakar dajin Kirzufa ba zai Gaza ba Sarkin da ke mulkin birnin Hutaira, wani gawurtaccen boka ne mai suna Ishmar ibiní Suraifa. Shima Sarki Ishmar babu abinda bai yi ba akan ya ga bayan Sarki Salmar domin ya mallaki dajin Kirzufa amma abu ya gagara. Abinda yake daurc masa kai shi ne, "Me ya sa tsafī baya tasiri akan Sarki Samral? Babu irin binciken da bai yi ba a hallarar tsafi domin ya gano wannan matsala amma abu ya gagara. Kawai abin da ya iya ganowa shi ne akwai wani babban sirri a tarc da Sarki Salmar wanda yasa tsafi baya tasiri a jikinsa kuma ya ziyarci bokaye da yawa a duniya wadanda ma suka fi shi karfin sihiri amma dukkaninsu sun kasa gano wannan sirri. Abinda bokaye suka gaya masa shi ne duk duniya babu wanda ya san wannan sirri face shi kansa Sarki Samral kuimna kafin ya bar duniya sirrin zai koma kan dansa Muraisu, shima kafin ya mutu dansa zai gaji wannan sirri. Haka al'arnarin zai ta bibiyar zuri'arsu shckara da shekaru, zamani bayan zamani. Ba za a taba rabasu da wannan sirri ba face a ranar da aka kai mai sirrín kas a filin yaki aka sami nasarar hallakashi. A sannan nc za a tsaga kirjinsa a ciwo wannan sirri wanda ya kasance dan siriri tamkar silin gashin da ke wuyan doki guda daya. Sa'adda Sarki Ishmar ya ji wannan jawabi sai hankalinsu ya dugunzuma ainun, domin ya san cewa , AA misau nake, : shi dai abu ne mawuyaci a zamaninsa ya ga wannan rana sai dai nan gaba a zamanin 'ya'yansa ko jikokinsa. Akan haka ne ya rungumi kaddara bisa tunanin mallakar dajin Kirzufa a wannan lokaci amma sai ya ayyana a ransa cewa komai darcn dadewa sai an sami wani daga cikin zuri'arsa ya mallaki wannan sirri. Shi dai Sarki Ishmar Allah Ya albarkaceshi da yayye har guda talatin da tara, amma gaba dayansu mazane babu mace ko guda daya, kuma a binciken da ya yi zuri'arsa ba za ta taba samun damar mallakar wannan sirri ba na Sarki Samral face an haifi gagarumar BASADAUKIYA jininsa wacce za ta shahara a ko ina cikin duniya. Wani babban abin takaici shi ne gaba daya 'ya'yan Sarki Ishmar manya wadanda suka yi aure duk wanda matarsa za ta haihu sai aga namiji ta haifa ba a taba samun wacce ta haifi 'ya mace ba bare Sarkı İshmar ya sa ran cewa ita ce za ta kar6i wannan sirri ga zuri'ar Sarki Samral. Saboda wannan dalili. ne duk sa'adda aka yi haihuwa Sarki Ishmar ya ga namiji aka samu sai ya kamu da tsananin bakin ciki ya rufe kansa a cikin daki ya yi ta kuka domin ya san cewa har abada ba zai ga ranar da zai raba Sarki Samral da wannan suri na sa ba Wanda zai sami damar cuiar da shi da zuri'arsa da Carfin sihirin tsafi. Babban abin takaici a gareshi shi ne lsufa ya riskeshi ya shekara tamanin da hudua dunivai ya san cewa ajali ko yaushe ajali zai iya riskarsa : De jin Kirzufa wani irin sihirtaccen daji ne wanda sama da shekaru dari baya ba a aba samun mahaluin da ya shiga cikinsa ya iya dauko wani abu ba face mutum aya rak, wato Sarki Samral. a wannan ikokinsa. Shi dai wannan daji na Kirzufa Allah Ya albarkaceshi da tsuntsaye iri-iri gami da dabbobin daji kala-kala masu yawan tsiya. Wata dabbar ma ko a labari mutum bai taba jin labarinta ba. Babban sirrin dajin Kirzufa shi ne, idan mutum ya shigeshi in dai bai yi ko Rarin đaukar wani abu ba ko cutar da wata dabba ba to fa zai shiga lafiya kuma ya fito lafiya, amma da zarar ya yi yunkurin daukar wani abu ko cutar da wata halitta, to fa sunansa gawa! Mafarauta da mayaka sun sha hada runduna su shiga dajin don đebo albarkatun cikinsa, amma dayansu baya dawowa a raye. Shi kansa Sarki Samral sau daya ya taba shiga dajin ya yi farauta inda ya kamo wadansu giwaye guda shida. Nan take ya kashe guda hudu ya ciro haure guda biyu kuwa ya sabosu a kafadunsa ya fito da su daga cikin dajin. Koda va iso inda ya bar Dakaru hamsin wadanda suka yi masa rakiya izuwa farautar suka ganshi da wadenan giwaye da kuma haure sai suka cika da tsananin mamaki suka rinka shewa suna yi masa iinjina domin shi ne mutum na farko da ya karya alkadarin dajin Kirzufa..... Sbd haka Nima Ku Tafamin😂 Dafatan Kowa yana lafiya SaikumA Mun sake haduwa a part BBUSA A MUTU!!! Littafi Na Daya (1) Part B Marubucin Littafin Abdulaziz Sani M/Gino Marubucin yaci gaba da cewa.... Nan da nan labarin wannan jarumtaka da ya yı ya bazu a ko ina a nahivar. Wani abin mamaki shi nc, hauren giwayen da ya farauto a cikin dajin sai da suka zamo sanadiyar samun dukiyarsa mai tsananin yawa irin wacce bai taba samu ba a rayuwarsa domin manya-manyan Sarakunan duniya ne suka rinka yin tattaki suna zuwa har birnin Lairus suna siyan hauren giwa daya jal akan miliyoyin dirhami. Duk wanda ya sayi hauren giwar sai ya kaishi masarautarsa ya adanashi a gidan tarihi mutane suna Zuwa suna gani suna biyan kudi. Shima ya sami abin samun kudi. Shima Sarki Samral sai da ya ajiye hauren giwar guda daya jal a tsakiyar fadarsa saboda barin tarihi, kuma yasa aka sassa ka gunki mai kamanninsa da girmansa sak! Yana gumurzu da giwaye shida na gumaka. Duk mutumin da ya shigo fadar Sarki Samral ya ga wadannan gumaka na giwaye shi da Sarki Samral dole ne ya yi sha'awarsu domin sun yi matukar kyau, kasancewar an yi su ne da zallan zinare, kuma masassakin ya kwarance ainun, da ka kallesu sai ka ga kamar za su yi motsi tamkar na gaske ne ba gumaka ba, Daga wannan rana da Sarki Samral ya shiga dajin Kirzufa ya yi wannan farauta ya dawo gida bai sake sha'awar sake zuwa daji ba Shekara na zagayowa ne ya kamu da cutar ajali. ya kwanta ciwo. Kuma a wannan lokaci ne Yarima Huraisu ya yi fishi ya bar birnin Lairus ya koma can daji inda aka gina masa wannan tafkcken gida ya zauna tare da yaransa manya-manyan 'yan fashi suka ci gaba da sharholiyarsu. A sannan ne labari ya riski Yarima Huraisu cewar mahaifinsa Sarki Samral ya kwanta cutar ajali. Koda samun wannan labari sai Huraisu ya cika da matukar farin ciki ya fara tunanin hanyar da zai tara mayaka masu yawan gaske wadanda za su zama 'yan tawaye su je su yaki birnin Lairus su karbi mulki da Rarfin tsiya tunda Sarki na kwance ba lafiya amma sai abu daya ya fađo masa a rai wanda ya firgitashi. Ba komai bane wannan abu ba face dan uwansa Yarima Muraisu wanda ya tabbatar da cewa ya fishi jarumtaka nesa ba kusa ba, kuma duk abinda Sarki Samral ya yi shima zai iya yinsa, don haka Muraisu shi kadai zai iya tarwatsa mayakan da zai tanada ya hanashi cika burinsa. Abu na biyu da ya kara dugaunzuma hankalinsa ya jefa masa tsananin bakin ciki shi ne, ya san cewa duk sa'adda Sarki va mutu lallai Muraisu ne zai gajeshi, kuma hatta wannan sirrin sihiri na shiga dajin Kirzufa sai ya mallaka masa shi. Babban burin Yarima Huraisu shi ne bayan ya Zama Sarkin Lairuf ya shiga dajin Kirzufa ya yi farauta a cikinsa kamar yadda mabaifinsa ya yi ya shahara A ko ina a duniya. A takaice dai yanzu burin Yarima huraisu guda biyu ne. Yana son ya zama Sarkin Lairuf kuma yana son ya sami daukaka irin wacce mahaifinsa ya samu a sanadiyar shiga dajin Kirzufa. Lokacin da tunanin wadannan abubuwa biyu suka yi tsanani a cikin zuciyar Yarima Huraisu sai hankalinsa ya dugunzuma ya rasa abinda ke masa dadi a duniya, ya kasa zaune ko tsaye, ya yi ta zarya a cikin wannan gida nasa na daji. A wannan lokaci manyan yaransa na zazAune sun zuba masa ido kawai an rasa wanda zai tambayeshi abinda ke damunsa. Daga cikin yaran nasa akwai wani jajurtacce, mara tsoro, wanda shi ne shugabansu, kuma ya kasance gawurtaccen mayaki wanda shi kansa Huraisu yana ji da shi, yana alfahari da shi, ana kiransa da suna Busara ibini Kalhur. Ba tare da fargabar komai ba Busara ya nikc tsaye ya tari gaban Huraisu ya ce, "Ya shugabana wai shin mene ne yake damunka ne a yau alhalin a jiya da daddare mun fita sana'a mun dace tunda mun. samo dukiya mai yawan gaske...Sannan ga giya ganga-ganga a gidan nan babu adadi, ga mata nan ba na banza sai Wacce kake sha'awa, komai na jin dadin duniya akwaishi a cikin gidan nan". Sa'adda Yarima Huraisu yajı1 wannan tambaya sai ya kyalkyale da dariya lookaci guda kuma ya murtuke fuska ya ce, "ya kai Busara, kayi sani cewa buri baya yankewa a zuciyar dan'Adam. Na sani cewa a halin yanzu na mallaki komai na jin dadin duniya. Duiciyar da na tara a yanzu har na bar duniya ban isa na karar da ita ba! Amma ai har yanzu ban sami mulkin birnin Lairus ba..AA Misau Nake, Har yanzu ban mallaki sirrin shiga dajin Kirzufa ba. Ta ya ya zan samu daukaka irin wacce mahaifina ya samu a duniya?" Sa'adda Yarima Huraisu ya ZO nan a zanccnsa sai Busara ya yi murmushi ya ce, "Ya shugabana ai babu wata cuta a duniya wadda bata da magani. Ina ganin cewa idan ka jc wajen Sarki Ishmar ibini Suraifa zai iya sanar da kai hanyar da za ka bi ka sami bivan bukatunka." Cikin matukar mamaki Huraisu ya dubi Busara ya ce, "Ta ya ya kake tsammanin ccwa Sarki Ishmar zai bani hadin kai alhalin ya kasance babban makiyin mahaifina. ?" Busara ya sake yin murmushi a karo na biyu ya ce, "Ai Sarki Ishrnar ya san duk abinda ke tsakaninka da mahaifinka, kuma ya san baka da wai buri wanda ya fi ka ga bayan mahaifin naka, don haka tabbas zai ba ka hadin kai tun da fadnwa ta zo dai-dai da zamna," Ya yiin da Huraisu yaji wannan shawara, sai nan Take ya cika da farin ciki, ya dubi Busara ya ce, A shirya mini tafiya izuwa bimin Hutaira gobe da safe Kuma mu uku ne kacal zanu tafi ni da kai da sadaulki Rauhaz". Sadauki Rauhaz shi ne na biyu a cikin manyan yaran Yarima Huraisu wadanda yake takama da su, kuma baya shakkar turasu aiki ko ina. Sadauki Rauhaz jarumi nc na gaske, kuma Allah Ya horc masa basira da kaifin tunani da hangen ncsa, don haka in dai ya shirya yadda za a yi sata sai an sami nasara. Ba a taba samun akasin hakan ba. Haka kuma idan aka shiga RINTSI ko wani bala'i da zarar ya bada shawarar abinda za a yi a kubuta, ana yin amfani da shawarar tasa take ake samun mafita. Bisa wannan dalili ne Yarima Huraisu in dai zai yi tafiya sai tare da sadauki Rauhaz, domin ya ri ga ya camfa cewa in dai suna tare duk abinda zai yi sai ya sami nasara akansa. Har ma kirari yake masa yana cewa da shi, "Kai ne mabudin hanya! Kai ne tutar Nasara Rauhaz!!m Kashe gari kuwa da sassafe Yarima Huraisu, Busara da sadauki Rauhaz suka yi shiri suka hau dawakansu suká durfafi birain Hutaira. Daga wannan daji wanda Huraisu da yaransa ke zaune zuwa birnin Hutaira, tafiya ce ta kwanaki ashirin da biyu. Haka kuwa su Huraisu suka shafe wadannan kwanaki suna tafiya. Kai tsaye suka rinka ratsa dazuzzuka ba tarc da fargabar komai ba tamkar a cikin gari suke tafiya, kuma komai dare ko rana basa jin tafiyar. Babu abinda yake tsaida su face gajiyar dawakansu da yankewar ruwan sha. Duk inda suka riski korama ko kogi sai su yada Zzango a wajen su huta, idan kuwa dare ya yi sosai sai su kwana a wajen. Duk lokacin da suka yi gamo da muggan 'yan fashi ko aljanu da sauran dabbobin daji ababan tsoro, cikin kankanin lokaci suke ragargajesu, su kashe na kashewa, na gudu su gudu. A haka suka isa birnin Hutaira lafiya sumul. Fadace Rasaitacciya wadda ta kawatu ainun fiye da tunanin mutum, kai a tsaya yin bayanin abinda ke cikinta ma kauyanci ne sai abinda mutum ya gani da idanunsa. Sarki Ishmar na zaune a bisa karagar mulki, fadawa sun kewaye shi, ga mutanen gari sun taru da yawansu, AA Misau Nake, wato dai fadar ta cika ta batse sai tafiyar da harkokin mulki ake. Sarki Ishmar ya kasance gajeran mutum mai katon ciki kuma kakkaura amma kuma kyakkyawane shi a fuska kuma yana da matukar kwarjini, domin mutum bai isa ya kura nasa idanu ba. Wata irin kyakkyawar shiga ya yi ta fararen kaya da doguwar riga da wando da farin alharini wanda akayi musu dajiyar baki da zaren lu'u-lu'u, sannan ya đora bakar alkyabba mai tsananin sheki da walwali. A kansa ya dora wani dan karamin rawani mai kyau gwanin ban sha'awa, takalmin kafarsa fari ne sol. Hakika shigar tayi masa matukar kyau kamar da kavan aka halecceshi a jikinsa. A hannun sa na hagu kuwa yana rike da farin kwagiri wanda saman sa sifface ta Zaki. Kallo daya mutum zai yiwa Sarki Ishmar a Wannan lokacin ya fahinmci cewa yana cikin farin ciki domin fuskarsaa cike take da annuri sai murmushi ya ke yi kamar wanda aka yiwa busharar samun Sarautar duniya. A wannan lokaci wasu Makada ne suka baje kolinsu a fadar, wadansu kyawawan 'yan mata na ta faman tika rawa. Babu abin da zai baiwa mutum mamaki face ganin yadda wadannan 'yan mata su ashirin da hudu kamanninsu ya zo duk iri daya tamkar tagwaye. Wani karin abin sha'awa a tare da su shi ne, dukkaninsu sun yi wata iri shiga co ta Zakara, wato da siffar Zakara aka dinka tufafin jikinsu. Duk sa'adda Sarki ishmar ya dubi wadannan kyawawan 'yan mata suna ta cashe

Chapter 1 of 4