Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 6
mamakin yadda talatu take dago masa hannu tare da kara masa kwarin gwiwa duk da yake kuwa ita ya biyo don ya kamata ya mayar da ita gida . Ita kanta tasan ita yazo nema amma ganin ana dambe dashi kuma shine dan uwanta wada tafi sani a garin yasa take goyon bayanshi tare da sabbin kawayenta wadanda suke zaune tare a benci daya Amadu yaji tsigar jikinshi ta tashi yaji sabon karfi ya shigo masa Idan har ya yarda shagon sadi ya kashe shi to ya bayar da talatu don kuwa tuni yasa ta bayar da labarinshi a wajen kawayenta cewar dan garinsu ne kuma ita yazo nema juyawar da Amadu yayi ne yaba shago damar kawo masa wani dukan ya sameshi a hanci Amadu ya girgije bai yarda ya fadi ba yaja baya ya kalli shago wanda yake huci yana gyara hannu hancin Amadu ya fara zubar da jini yana tsaye Garban kauye ya garzayo yasa riga ya gogewa Amadu jinin aka raba damben kafin a sake juyowa turmi na biyu Ganin nasarar da ya samu ne akan Madu baligi sai shagon sadi ya koma gefe yana kirari makadan suka sa kidansa ya fara rawa yana wasa da hannunsa 'yan tsirarun mutane da suke sonshi suka fara ihu suna yi masa tafi amma da yake mafi yawan sunfi son Amadu baligi gidan yayi sanyi babu hayaniya sosai . Amadu ya juya ya sake kallon talatu wacce ranta ya baci ganin shago ya bata masa hanci Amadu yayi mata murmushi talatu ta sake dago masa hannu Idan har yabar shago ya kasheshi ya kunyata dimbin masoyansa da suka cika gidan musamman talatu wacce kadan ya rage ta fashe da kuka amadu baligi yaji ya canza ra'ayinsa a dan lokaci kankani dole ne ya kashe shagon sadi kome zai faru ya faru" bazai taba kunyata dumbin masoyansa ba dake a wannan gida Bayan sun huta sai aka basu fage don su dawo su sake raba raini da shago yaga shi yake samun nasara sai ya sake tasowa Amadu ya kawo masa duka a kwibin wuyansa Amadu ya tokareshi ya hanashi karasowa da hannun kafin shago ya sarrafa jikinsa ne yayi wata hikimar Amadu yadan zunguri hancinsa" wanda hakan yasa shago yayi baya kamar zai fadi har mutane sun fara ihu da murna" sai shago ya dake a jajirce" to amma kowa yasan yaji dukan" mutane suka dawo hargowa suna kiran sunan Amadu baligi muryar talatu ta kere muryar mutanen dake a kusa da Amadu baligi" yaji tana cewa Yayana Amadu ka dage..... Yaya Amadu ka kashe shi . Wannan muryar ce ta sake zaburar da Amadu baligi yayiwa shago bakandamiyarsa lokacin da shago ya wartsake ne sai Amadu yayi fitar sauri ya takewa shago kafa ya hanashi ja da baya akan lokaci a lokaci guda yasa bakandamiyarsa ya daki muka-mukin shagon sadi baya bukatar ya tsaya kallon irin faduwar da yaron zaiyi yasan a duniya babu mutumin da zai iya shanye wannan dukan" Amadu ya juya ya fara dagawa masoyansa hannu wadanda suke hargowa kamar zasu fasa gidan Shagon sadi ya dade a sume kafin ya fadi kasa a sandare kamar kifin miya" sadi ya bude baki a rikice yana kallon cin amanar da amadu yayi masa Garban kauye ya rugo a guje ya dauki amadu duk da nauyinsa ya dagashi sama mutane suka fara zubo da ruwan kudi 'yan kore suna kwasa suna tarawa Amadu Garba ya fara zagayawa dashi mutane suna dafa kanshi a haka har saida suka zagaye filin talatu tare da kawayenta sai tsalle sukayi suna tafi cikin murna tana basu labarin Amadu yayanta ne . An kai minti ashirin ana murna a gidan kafin a gyara filin" Garba ya tattaro KAZAR KARFIN da kuma kyautar da Amadu ya samu ya damka mashi yana dariyar farin ciki sannan ya dauki makirfon yayiwa mutane godiya sannan ya tabbatar masu kudu ce tayi kisa a wannan ranar ba arewa ba"" Harare da Iro bahago suka shigo cikin fage suka dauki shagon sadi wanda bai farfado ba sukayi waje dashi mutane suka basu hanya ana tayi musu ihu da gwalo sadi ya tashi daga kan bencin ya shigo cikin fagen yana murmushi yaje har gaban Amadu baligi ya dafashi yace dashi "Na tayaka murnar nasarar da ka samu ya kalleshi har cikin idanunsa sannan ya kara da cewa "kada ka mance da alkawarin da na dauka akan idan kaci amanata....... Muna nan muna jiranka zakazo hannunmu bayan ka gama murnar . Ya juya a fusace ya tafi yabar Amadu tare da masoyansa da masu son su gaisa dashi... . INTERVAL.... . TAKUN FARKO KENAN....KAZAR KARFI--> 19 . . Wadansu kuma suna so su dauki hoto tare dashi duk abinda akeyi hankalin Amadu yana kan talatu ya nunawa Garban kauye ita yace kada ya bari ta bace masa ita yazo nema suna cikin haka ne saiga Balan dubarudu ya keto mutane ya shigo ya kama Amadu yana murna Amadu ya nuna masa talatu wacce take a cikin karuwan da suke akan benci yace da Bala Gata can bala mutane bazasu barni in tasa ta ba ka tafi da ita gidanku zanzo in dauketa idan na gama sallamar mutane Bala yaje ya sami talatu ya fara yi mata magana Garban kauye ya dawo wajen Amadu baligi suka samu da kyar suka fita daga fagen sun kai awa daya suna fama da hayaniya da mutane kafin su sallami makada da sauran 'yan koren da suke aiki a gidan damben Amadu ya kullo kudinsa a buhu suka dawo gida tare da garban kauye Har zuwa lokacin bai mance da gargadin sadi ba inda yake cewa ....IN HAR BAKA CIKA MANA ALKAWARINMU BA SAINA KASHE TALATU KISAN WULAKANCI.. . BAßI NA BAKWAI . Bayan Amadu baligi ya huta a gidan Garban kauye sai hankalinsa ya koma kan talatu yanemi jaka ya zuba kudinsa a ciki ya kirga dubu hamsin ya ba garban kauye ya mayar masa da kazar karfinsa daya sa masa ya kuma bashi dubu goma kyauta Garba yayi masa godiya ba kudin da ya bashi sukafi damunsa ba ya riga ya share masa hawayensu a garin ya fitar dasu kunya tunda dai ya kashe musu wannan yaron wanda ya gallabesu kwana da kwanaki Amadu yayi bankwana da Garban kauye wanda ya dage kan sai sun nemo mai mota wacce zata mayar dashi gida Amadu ya nuna rashin amincewarsa yace ya gode yasan ya tono rigima a tsakaninsa da sadi baya son ganin ya shafi kowa a cikin mutanen garin ba wanda yasan abinda sukayi shi da sadi bai fadawa kowa ba Amadu ya garxaya gidansu bala don ya dauki talatu su koma gida da zuwanshi ya sami Bala a kofar gidansu a kishingide cikin jini makwabtansu wadanda suka damu dashi sun cire masa riga anje nemo mai babur a kaishi asibiti jikinsa duk raunin sara jini sai zuba yakeyi . Amadu ya durkusa ya dafashi a kidime Bala ya akayi..... Me ya faru..... Wa yayi maka haka? Bala ya dago kai da kyar ya dubi Amadu yace dashi "Su sadi ne suka tareni suka kwace talatu daga wajena a lokacin da na taho da ita daga gidan wasa zanzo da ita nan gidanmu" yace in fada maka idan kana sonta kaje ka samesu acan bayan gari a wani daji da muke cewa MAI KWATAMI... Bala ya cije baki saboda azabar dake damunshi wani mutum dake a wajen a tsaye yace da Amadu baligi kaje ka fadawa 'yan sanda halin da ake ciki wadannan 'yan damben ba mutunci ne da su ba Kai Amadu kada kaje ka fada musu su kassara ka a banza kaga dai abinda suka yiwa Bala Amadu yace da mutumin Wannan rigimace tsakanina da su abin bai shafi 'yan sanda ba nina san dalilin da yasa suka yi min haka ni suke so su gani don haka zanje in samesu a bayan garin ina ne MAI KWATAMI ? Mutumin yasa Amadu baligi a hanyar mai kwatami yace ya mike hanya zaije har inda suke Amadu yasa kai ya tafi ba wani fargaba a lokacin gari ya fara duhu an kusa kiran sallar isha'i ba kanshi yake ji ba talatu yafi ji saboda a dominta yazo wannan gari" gashi abokan adawa sun kamata sunyi garkuwa da ita . MAI KWATAMI. . MAI KWATAMI wani karamin daji ne dake bayan garin dubarudu tafiyar kilomita daya daga wajen ana iya hango kyallin rufin gidajen garin a nesa kuma ana iya jiwo sautin dake da kuma kukan jakuna ko haushin karnuka lokaci-lokaci Babu gonaki a dajin mai kwatami kananan itatuwa ne irinsu kayar dundu da kuma tsamiya da faru kasancewar wajen baya rabuwa da tsuntsaye da rana dajin yakan cika da yaran garin dubarudu wadanda suke zuwa harbi da gwafa ko kuma su ajiye keji don tsuntsaye su fada ciki ya rufe dasu Da zuwan Amadu baligi wajen tun kafin ya karasa ya hango dandazonsu sadi kare garke yana zaune a tsakiyarsu su kuma suna a tsaye Amadu ya gane hakan ta hanyar dosashin jan tabar da sadi yake sha wacce ke kara yin haske duk lokacin da ya zuketa a cikin daren saida Amadu yazo dab da inda suke sannan yaga talatu a daure tamau a jikin wata kututturen icce a kusa dasu ga alama tayi kukanta tuntuni harta gama kafin Amadu yazo . Sadi kare garke da yaransa sun hangi Amadu tun daga nesa kafin ya matso kusa dasu da zuwanshi wajen sadi ya mike ya tarbeshi da cewa Barka da zuwa jarumi dama kai nake nema yau kazo inda bazaka taba komawa gida da rai ba Amadu wanda yake rike da jakar kudinsa a hannu yace kun bani kunya bansan ku matsorata bane kuma kananan yara saida na samu labarin kun kama mini kanwata ni zaku kama idan kun isa ba karamar yarinya zaku tsare ba a daji wacce batayi muku laifin komai ba . Tun kafin sadi ya mayar masa da martani Iro bahago ya taso a fusace zai fadawa Amadu sadi ya dakatar dashi da hannu Saurara Bahago Zan Baka Damar . BARKAN KU DA JIMIRIN SAURARON WANNAN QAYATACCEN LABARIN MAI CIKE DA NISHADANTARWA FADAKARWA WA'AZANTARWA DAKUMA BOYAYYIYAR SOYAYYA...KAZAR KARFI--> 20 . . SADI ya juya ya sake fuskantar Amadu babu wadataccen haske a wajen don haka ba wanda yake iya ganin munin dake tattare da fuskar kowa Sadi yace da Amadu Kaci amanata Amadu ka karya mani alkawari ka bata mani yarana biyu dukansu suna asibiti yanzu zamu dauki fansa wannan dalilin yasa muka kama talatu saboda mun san ta haka ne kawai zamu kama ka kazo inda muke ka samemu Amadu yace da sadi kare garke Gani nazo na sameku din amma ina tabbatar muku yadda nazo da kafafuna a kansu zan koma tare da kanwata bazaku iya cin nasara akaina ba Sadi yayi dariya kayi kuskure Amadu saboda dambe kawai ka iya anan ne kake da ido fiye damu mu kuwa bayan dambe akwai abubuwa da yawa da muke iyawa wadanda zamu iya kare kanmu dasu a ko ina Sadi ya hade rai yace da iro bahago a fadace shiga ka nuna masa abinda bai iya ba Bahago kamar dama jira yake yi a taboshi iro bahago yayi kukan kura ya fadowa baligi ya rumbabeshi suka fadi kasa tare Amadu ya saki jakar kudin gefe guda ya mayar da hankali akan fadan dake gabanshi . Iro Bahago yana da karfi don haka sun dauki lokaci suna turmushe juna a kasa ya kasa tureshi Amadu ya tokari iro bahago da gwiwar kafarshi ya sameshi a ciki wanda hakan yasa dole ya dafe cikin nasa ya saki Amadu sadi da ragowar yaransa suna tsaye suna kallon Amadu ya mike ya haye kan iro bahago ya naushi wuyansa Iro yayi makararriyar tsuwa ya koma lagwaf ya saje da kasa Amadu ya tashi daga kanshi don ya sumar dashi kuma bazai fardado da wuri ba tun kafin Amadu ya huta sadi ya fizgo yaransa biyu MIKO da RAGIJE ya turawa Amadu su da fadawarsu suka kamashi da kokuwa basu yarda ya sarrafa hannuwansa ba suka murdeshi da karfi suka tausheshi suka kaishi kasa miko ya murde hannuwansa ta baya Ragije kuma ya shake wuyansa suka tankwarsa shi Ganin irin rikon da kartin biyu suka yi masa yasa talatu ta fara kuka tana a daure a inda take sadi ya fara dariyar mugunta ya kalleta yace tukunna ma yarinya zamu zo kanki ki jiramu . Kafin sadi ya gama tsorata talatu ne Amadu yayi kururuwa ta tashida kartin biyu ya watsar dasu suka fadi yayi saurin cire hannuwansa ya daki miko a fuska wanda saida yayi kuli-kulin kubura a sama sau biyu sannan ya fadi kasa baya numfashi Ragije ya cire hannu shima ya daki Amadu a fuska wanda dole tasa ya fadi kasa wanwar to amma a saboda zapin nama a lokacin da Ragije yayi sufa zai tausheshi sai Amadu ya mirgina ya goce ya bashi wuri Ragije yayi karo da dutse ya fasa hanci Amadu yasan hakan bai ishe shi ba yasa kafa yana a kwancen ya tokareshi a habarshi ya cilla dashi can gefe guda ya hadu da iro bahago suka ci gaba da sumarsu tare Sadi ya rude da yaga Amadu ya sumar da yaransa uku saura hudu suka rage wadanda ya taho dasu ya dubesu su dukansu yace dasu a fusace Me kuke jira dashi kuna kallonshi yanayi mana illa ? ku tarar masa mana ku cinyeshi danye. . Sauran kartin hutu Wurure da Gwanyo da martai ajali sai kuma shagon ajagu suka fadawa Amadu baligi kamar kuraye sun sami akuya a daji Amadu yasan bazai iya karawa dasu su duka ba a lokaci daya zai iya amsar mutum biyu yayi fada dasu amma bazai iya ja da mutum hudu ba a lokaci guda Don haka sai yaja baya bai yarda sun cakumeshi su duka ba ya rika kai musu duka dai-dai da dai-dai idan ya sami sa'ar wannan ya mangara sai ya komawa waccan ya buga sai yaja baya ya ruga idan wani ya taso mashi sai ya nausheshi Sun dade a haka suna bugi in buga basu sami nasarar yiwa Amadu tarko ya fado tsakiyarsu ba a haka sai da ya galabaitar dasu suka gaji da ya tabbatar karfinsu ya ragu sosai sai ya fada tsakiyarsu yanzu kam zai iya amsarsu su duka hudun tunda dai sun dawo kamar karfin mutum biyu Shagon Ajagu ya fara bazarwa a kasa ta hanyar tokareshi da kafa a kirji sannan ya duka a lokacin da warure ya aiko masa da tasa kafar kafin kafar warure ta gama yawo a saman ne ta dawo kasa Amadu ya kama daya kafar ya goceta warure yayi sama kamar toton masara duk da girmansa koda ya fado kasa baiyi yunkurin sake tashi ba don kuwa akwai yiwuwar kashin bayansa ya motsa sosae . Martai ajali ya fadowa Amadu suka nufi wata kayar dundu suka afka ciki Amadu yaci maganin tsini don haka kayar bata raunatashi ba martai ya makale a cikin kayayoyi yana kokarin banbare kanshi da kyar ganin haka sai Amadu ya sake danneshi ciki sosai ya barshi a haka ba tare da ya jigatashi ba koba komai martai zaisha wuya kafin ya iya ciro kanshi a cikin kayoyin da suka sossokeshi Saura Gwanyo wanda tuni ya gama razana amma saboda karfin hali bai fasa garzayowa ya cakumi Amadu ba sai da suka hadu Amadu yaji zafi a gefen cikinsa ya ture gwanyo gefe guda yaja baya ya taba inda yaji zafin da hannu ya shafo jini sai a lokacin ya fahimci aikin wukane . Amadu yasan wuka bata kamashi to amma.. . AMMA ME KUMA ? HABA UBAN BALIGA ME YAKE SHIRIN FARUWA NE HAKA ? 21 Loading . (c) SHAFIU DAUDA GIWA KAZAR KARFI--> 21 . . SAI da suka hadu Amadu yaji zafi a gefen cikinsa ya ture gwanyo gefe guda yaja baya ya taba inda yaji zafin da hannu ya shafo jini sai a lokacin ya fahimci aikin wuka ne Amadu yasan wuka bata kamashi to amma dai yaga kwallin balati a hannun gwanyo yaja daga saiya daina mamaki don kuwa wani mafarauci daya bashi lakanin wuka ya taba fada masa wani sirri dake tattare da balati yawanci da ita mata suke yanka kayan miya a gida A cewar mafaraucin duk taurin mutum ko maganin me yaci da ka dauko wukar da mata ke yanka albasa ka danna mashi zata wuce kamar ka sami kubewa ko kankana! Gwanyo ya sake garzayowa rike da balati Amadu ya goce ya kauce gefe daya ya hambari gwanyo a baya ya kara masa gudu gwanyo yaje ya hadu da itacen tsamiya ya watse kasa goshi yana zubar da jini kamar an bude famfo tuni ya saki wukar tasan inda dare yayi mata . Tun kafin Amadu ya juya bangaren da SADI yake yaji ihun talatu a lokacin ne yaga tuni har sadi ya kwanceta ya shake wuyanta da hannunsa daya ya hadata da jikinsa yana rike da guntuwar bindigarsa a daya hannun wacce ya tsorata Amadu baligi da ita a daren da ya gabata ka tsaya a inda kake idan ka motsa daga nan zan harbeta kaima kuma zan harbeka yanzun nan Sadi ya gargadi Amadu da kakkausar murya Amadu ya tsaya a waje daya yana kallonsa Sadi ya daka matsa tsawa "Ina KAZAR KARFIN da kaci a wajen wasa dazu ? naga ka taho da ita yi sauri ka dauko min ka jeho min ya sake dannan kan bindigar a goshin talatu tayi kara mai razanarwa Amadu ya daga hannayensa sama ya juya inda ya ajiye kudin da yaci a wurin damben ya duka ya dauko su da hannu daya a cikin jakar ya juyo inda sadi yake tsaye rike da talatu "jefo min jakar ka koma baya... Kada ka sake matsowa inda nake zan harbeka kai da ita Amadu ya tattara karfinsa waje guda yayi saitin fuskar sadi ya cilla masa jakar kamar kibiya jakar ta sameshi fas ta bugi idanunsa yayi baya kamar zai fadi bai san lokacin da ya saki talatu ba Amadu ya tashi cikin sauri ya fitar da kafa daya ya doki sadi a daidadi tafin hannunsa dake rike da bindigar sadi ya jefar da ita saboda karairayewa da yatsunsa sukayi sakamakon dukan da Amadu yayi masa . Talatu ta kauce gefe daya a tsorace ta tsaya baya tana kallon fadan Amadu da sadi kare garke kamar yadda taga sauran fadace- fadacen da suka wakana a gabanta sadi yana kwance a kasa kafin Amadu ya dira kanshi tuni har ya jawo kaho ya kaiwa Amadu suka ta gefen hannun Kahon yayi saitin idonsa daya Amadu yaji zuke" to amma duk da tsinin kahon bai sami idonsa ba ya sami gefen fuskarsa kahon bai hudashi ba saboda wannan alkawari ne a tsakaninsa da tsini sai dai yaji zafi sosai saboda dafin dake tattare da zafin dukan Amadu ya fadi baya sadi ya tashi a fusace kamar bai nakasa ako ina ba" yayi tsalle ya dira akan Amadu baligi ya shake wuyansa da karan hannuwansa ya danneshi Amadu yayi kokarin mikewa ya kasa ya fara tirje-tirje a kasa talatu ta fara kuka don kuwa yanzu ne Amadu yake shan wahala . Amadu ya tattara karfinsa waje guda ya fara bude rikon sadi ya naushi kirjinsa sadi ya kife baya kamar an jefar da diron mai Amadu ya tashi da kyar saboda ya galabaita" da kyar yake iya numfashi Sadi ya mirgina cikin sauri ya jawo bindigarsa Amadu ya kabeta a hannunsa ya nuna Amadu da ita yaja baya don ya sami damar da zai harbeshi sosai Amadu bai nuna alamar ya tsorata ba a wannan karon sadi ya dora hannunsa akan kunamar bindigar ya harba bindigar amma bata tashi ba sadi ya sake danna kunamar bindigar taki tashi Amadu yayi masa murmushi yace dashi Ka daina wahalar da kanka sadi bazata tashi ba tun farko dama ina sone mu gwada karfi ni da kai shiyasa na nuna maka na tsorata da bindigarka Sadi ya saki baki a tsorace ya tashi ya sake komawa baya ya nisanta kanshi da Amadu wanda ya taso ya biyoshi Sadi yace dashi a fusace Na yarda kafi karfina yanzu..... Amma zan sake yin shiri na musamman a kanka saina ga bayanka Amadu ka guji haduwata da kai a lokaci na gaba . Yana gaba fadar haka ya ciro wata laya yasa a bakinsa ya cizata ya bace bat!! kamar walkiya ko sama ko kasa Amadu yayi ajiyar zuciya ya juya inda talatu take tsaye ta tambayeshi a tsorace Ina yake Amadu ina yaje ? kada ya fito ya kashemu bamu sani ba Amadu baligi yayi mata murmushi Bazai sake fitowa ba talatu yaji tsoro ya gudu amma zamu sake haduwa watarana Idan kere yana yawo zabo yana yawo ai za'a hadu yace da ita cikin sauri zomu tafi gida duk ke kika jawo min wannan wahalar dama na fada miki ko ina kika shiga a duniyar nan saina biki na mayar dake gida kin sha wasa nake yi maki ko talatu . Yarinyar ta fara neman afuwar Amadu tana kuka Don Allah kayi hakuri yaya Amadu wallahi bazan sake guduwa ba daga yau ka yafe min Amadu yace da ita.... . ME KUMA YAKE SON FADA MATA ? . KU BIYO NI DAN JIN YA ZAKA ƘAYA . . . .KAZAR KARFI--> 22 . LAST PAGE--> THE END . @ YARIMA A. GANGARIYA . Amadu yace da ita shinkenan! Mu tafi gida ko ba komai a dalilinki ai gashi na wasa jinina na rabu da samun wannan damar kada kiso kiji farin cikin da nayi don in ba ana haka ba sai jinin mutum ya kwanta ya mutu Amadu ya dauki jakar kudinsa ya tasa talatu suka tafi suka bar dajin tare da karti bakwai din da ya bazar dasu fululu a wajen wata kila su farfado su dawo haiyacinsu a kwanaki biyu masu zuwa sunci sa'a don kuwa hannun Amadu baligi gudumace lafiyayya a boye ba tare da kowa ya sani ba Tun sanda ya fara dambe ya nemi lakanin gudumar makera dake dukan mutane aka kamar da hannunsa yake aiki shi kadai kawai yake iya ganin gudumarsa amma ba hannunsa ne yake irin wannan ta'asar ba . KAMMALAWA Ina yiwa daukacin jama'ar da suka bibiyeni a wanga dan guntun labari kuma suka bani karfin gwiwa ta hanyar comment ALLAH yayi muku albarka ya kuma albarkaci rayuwarku . Wadanda kuma burinsu kawai su karanta labari ba tare da sun mika comment nasu ba suma ina godiya gare su matuka wayanda kuma basa son ganin rubuce-rubucena sai dai suyi hakuri ba tare da goyon bayansu ba Allah ya sanya mun karasa wannan labari lafiya . BaZan cikaku da surutu ba bara in karkata birona In koma bakin Zaren labarin" saboda nasan kun kagu kuji karshen labarin Amadu baligi da kuma talatu . Da komawarsa gida lokacin da Alhaji Danjuma yaga 'yarsa talatu ta dawo gida Amadu baligi kuma yana shirin tafiya saiya rikeshi ya kara yi masa godiya sannan ya rokeshi ya taimaka masa ya auri talatu tunda dai su tafi karfinsu amma shi zai iya riketa "Idan baka aureta ba bamu san yadda zamuyi da ita ba ka taimaka ka aureta Amadu da zaran ka tafi zata sake guduwa . Amadu yace dashi "to Alhaji kaga bani da daki ban shirya yin......" tun kafin ya karashe korafin Alhaji Danjuma yace zanje insa a gina maka dakin da zaku zauna" kai in kana da fili na amince zan gina maka gidan da zaku zauna" ka taimakeni" . Amadu ya sake cewa "matsalar bani da kudi a hannuna ne yanzu Alhaji Alhaji Danjuma yace "Banason ka kawo komai ko kayan lefe bance kayi ba ka kawo sadaki duk abinda Allah ya hore maka ka kawo zan amsa . Amadu ya sake cewa Bayan anyi auren ne Alhaji bani da sana'ar da zan rike mata yanxu saboda..... Alhaji Danjuma yace zan rika aiko maka da abinci da kudin da zaku rika kashewa iya bukatunku kai da ita idan ba kai din ka aureta ba hankalinmu bazai kwanta ba bazata zauna ba . GODIYA Ina kuma gaishe da daukacin jama'ar dake biye dani awannan labari musamman ma members dakuma jajirtattun Admins dake group dinmu mai albarka na "TASKAR GIDAN LITTAFI" Ƙarkashin Jagorancin Jajirtattun Shuwagabannin mu dakuma ilahirin members Wanda bisa tallafinsu wannan labari yazo karshe . Kada ku gajiya ku biyoni har yanzu birona aiki Yake bazan dage ta ba daga bakin aiki ba har sai nazo karshen wannan labarin na KAZAR KARFI . Amadu baligi ya amince da yaji saukin yakai sauki da ya koma gida ne ya sanarwa iyayensa ya sami mata zai aura su kansu sunji dadi don kuwa a yadda Amadu baligi ya baci da neman mata ba wanda ya zaci zai taba yin aure a duniya don haka tanan ana iya cewa SAM bARKA! . Anyi haka da wata biyu aka daura auren Amadu da talatu Idan ya ajiye kara bata isa ta tsallaka ba saboda tsabar biyayya" Idan kuma yace ta zauna a guri to ko kwana zatayi bazata motsa ba a wajen sai yace ta tashi Aikin gida kuwa ba kama hannun yaro sai ya bari manyan wandunansa sunyi datti sannan ya tattarosu ya watso mata su ba kudin sabulu da ruwa zata wankesu fes! surfe da hannunta take yi kuma a dutsen nike take yin markade baya bayar da kudin nika to dama dai ance maganin shege dan banza dole Amadu baligi zai iya riketa" da wani mutumin arziki ta aura da yanzu tana can tana gasa masa gyada a tsakiyar kai . Bana gajiyawa da nuna farin cikin akan zuwa karshe wannan labari" tabbas akwai manazarta da suke bibbiye dani a wannan labari na kuma yaba da kokarinsu Godiya nake musu mai tarin yawa sai kuma Allah ya sake sadamu a wani sabon labarin mai SUNA........ . Bari in sake karkata birona saboda babu dalilin da zai sanya in bata muku lokaci saboda akwai sauran labarin . Alhaji danjuma yayi zaton idan ya rabu da talatu shikenan masifu sun daina fado masa to amma tunda talatu tayi aure sai kuma matansa suka dawo suka fara bugi in BuGA kwari ta dauki tabarya ta rotsawa amarya kai aka je kotu akayi shari'a ya kashe kudi . Anyi haka bada dadewa ba annobar faduwar motoci ta sameshi" ba ayin wata sai motarsa tayi hadari ba'a jima ba duk motocin suka balbalce suka kare da aka gama aikin gona an tara buhuhhunan a sito sai gobara ta tashi a ciki ba'asan ko menene musabbabinta ba . Bala'i dai yayi ta rafkowa dukiyar Alhaji Danjuma tako ina daga wannan sai wannan aka rasa mafita : ABINDA BAI SANI BA SHINE ZAKKAR DA BAYA SON FITARWA NE TAKE FITAR DA KANTA BA TARE DA YA SANI BA" . KARSHE.... . DAGA FASIHIN MARUBUCIN NAN SHAFI'U DAUDA GIWA An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend

Chapter 5 of 6