Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
a karshe to za'a kai lemu ne babu biskit dayyabu! ka dauko kwali daya a bude shi a gabanta shima duk karin gada guri ne Dayyabu yace ba matsala bari in dauko Ya sake shiga cikin shagon ya dauko kwalin biskit mai 'ya'ya wanda ba'a budeshi ba daya fito ne yace Bari in kulle shago na muje kada mu barta ita kadai . Ya dauki kwalin biskit din kamar wanda zaije wajen baikon aure" baban yara ya dauki samirar dake cike da indomi da kwai an shimfida a sama" yana ta kwarara kamshi" shi kuma Auwalu ya dauki biredi da shayin suka dugunzuma su ukun suka tafi dakin" Baban yara suka sa gaba tunda shi yasan yarinyar" shi ya jagorancesu suka shiga" talatu tana a zaune kamar wacce aka dasa Baban yara yace yana fara'a to gamu mun shigo Ya ajiye kwanon samirar a kusa da kires din lemun Auwalu ya ajiye mata nasa kofin shayin da biredin" Dayyabu ya ajiye mata kwalin biskit" talatu ta kalli lodin kayan sun cika tsakar dakin kamar wadanda suka fito da kayan lefe a gani" "ta tambaye su" "duk wadannan kuma na menene? Baban yara yace da ita Duk abinci ne" kin san ance yana da kyau ka karrama bakon ka" Ya juya kan abokansa biyu da suka rakoshi" suna zare idanu suna kallon talatu yace da ita wadannan abokai nane sunzo ne su gaisheki suma" talatu tayi murmsuhi" "sannunku malamai" ina wuni?" Dayyabu da Auwalu suka kware baki suka amsa a lokaci guda "lafiya lau" . Suka ci gaba da murmushi ba tare da sun san abinda zasu ce da ita ba" baban yara ya dubi lemun yaga bata dauki ko daya ba" ya tuna baizo da abin bude kwalba ba" yayi saurin daukar kwalba daya yace "Bari a bude maki lemun ki fara dashi" yara sun dauke mani ofiner" bana rabuwa da ofina a dakin nan Yasa hakori ya fara kici-kicin bude lemun da karfi har yana rintse idanu" Dayyabu yace "mancewa nayi" ni kuma dana taho da tawa ofina ta shago" Da kyar baban yara ya bude kyalbar lemun ya taso da karfi ya fito ya jika mashi fuska" yayi saurin ajiye kwalbar yana borin kunya" "Gas yayi yawa a wannan kwalbar shi yasa take da wahalar budewa" ya turawa talatu kwalbar a lokacin ne tace dasu" "to ku dan bani wuri mana inci abincin naku..." tayaya zan iya cin wani abu ku uku kun tsareni da kallo ? . Kamar wadanda suke jiran umarninta tana fadar haka su duka ukun sukayi waje" suka fito suka tsugunna a bakin kofar suka fara yin kus-kus cikin rada suna magana Dayyabu ya fara yiwa baban yara korafi "kana ganin zata bada hadin kai kuwa baban yara ? "Ba matsala dayyabu" Baban yara ya karfafa masa gwiwa Kasan yanzu tana jin yunwa ne" bata ci abinci ba" mu jira taci ta koshi sannan sai mu shiga mu fada mata abinda muke so zata amince" Auwalu mai shayi wanda ya kasa kunne yana sauraron radar da suke yi yace a karshe Nima ina ganin kamar haka- haka take" kada fa kaja muyi wahalar banza baban yara! ya juyo bangaren Auwalu dake a gefensa daga hagu yayi kasa- kasa da muryarsa yace dashi "kada muzo da kosawarmu a fili Auwalu" kasan irin wadannan wayayyun yaran na gari sai anbisu a hankali" ba gaggawa ake musu ba" Suka yi shiru suna jiran talatu ta gama cin abincin" Baban yara ya leka dakin ta hanyar wasu huje-huje dake a jikin tsohuwar kofar tasa" ya sameta a kishingide akan gadon har taci abinda taci ta fara shirin yin barci" yayi saurin juyawa inda sauran abokan nasa suke a zaune sunyi jigum suna jiran tsammani" yace dasu ta hanyar sirri . "ta gama cin abincin" ya za'ayi kenan?" Dayyabu ya mike yace "to kunga dai na fiku bayar da kayayyaki a harkar nan" gaskiya nizan fara shiga" Auwalu ya kwabeshi da sauri kaji kauyancin banza haka kawai zaka shiga sangwam-gwam ba ayi mata bayani ba fa ai sai an dan yi hira tukunna an nuna mata inda aka fuskanta sannan zata yarda" ku kuna abune da jahilci har yanxu Baban yara yace Gaskiya ne Auwalu to kuzo mu shiga muyi mata bayani kada tayi barci naga ta fara gyan-gyadi . Bayan samarin uku sun gama gudanar da shawarwarin su a waje sai suka sake shiga cikin dakin su duka suka sami bakuwar a kishingide a kan gadon tadan tsakuri abincin kadan... . INA UBAN BALIGAI YAKE NE GA GILLI NAN BATA TAFI BA FA . (c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 08 . . Bayan samarinn uku sun gama gudanar da shawarwarinsu a waje sai suka sake shiga cikin dakin su duka suka sami bakuwar a kishingide akan gadon ta dan tsakuri abincin kadan ta kurbi lemun baifi sau biyu ba bata taba shayin da suka ajiye mata ba ballantana kuma dirkeken kwalin biskit din dake jiranta Da taji motsin shigowarsy saita bude idanu ta tashi zaune tayi hamma sannan ta dan bata ranta Barci take ji fa gaskiya Baban yara wanda yake son ya kwantarwa da abokansa biyu hankali don kada su damu yace da bakuwar Haba tun yanxu zakiyi barci ko hira bamu yi ba? Sai a lokacin Auwalu yayi kokarin yin magana Ai bata ci abincin ba ma naga koma yana nan bata taba ba Da yake baya iya yi mata magana baban yara yake yiwa korafin to amma duk da haka sai ta bashi amsa tace dashi kai tsaye . Don kada ma kuce nayi muku wulakanci ne banci ba shiyasa na dan tsakura nagode samarin uku zazzaune a kasa babu ko tabarma suka tasa bakuwar tasu suna kallonta wacce take a hakimce akan gado ita ta fara yi masu magana akwai alamar sun fara isarta tace dasu to naji kunce zakuyi hira wacce iriyar hira kuke so ayi na fada maku barci nake ji A lokacin dayyabu ya dunguri baban yara da kafa yana nuna masa ya fito fili yaya magana ba boye-boye Baban yara ya fara inda-inda yace Eh to kinsan ai idan aka ce miki ga samari da 'yan mata dole ayi hira ayi soyayya koba haka bane? talatu tace Gaskiya kuwa haka ne baban yara yaci gaba da cewa yauwa, to dama haka nake nufi" amma dai ina jin ga Auwalu yana da magana" bari kiji komai a bakinsa" Auwalu yi mata bayani" Auwalu mai shayi ya gyara zama yadan sosa kai yace "Eh..ai duk abinda ka fada baban yara ba kuskure daman dai shi komai na rayuwa ance taimakeni in taimakeka.. Ko ba gaskiya ba?" to amma ga dayyabu bari yayi maki bayanin abinda ya kamata Dayyabu kayi magana . Auwalu da baban yara suka dubi dayyabu wanda baiyi tsammanin shi zasu dorawa wannan nauyin ba" ya fara dabircewa ya ce "to...ai kun gama magana" mudai soyayya ce ta hadamu dake" kuma yadda muka fara da mutunci" to bazamu kare da rashin mutunci ba" Rayuwa juyi- juyi ce... Duk wannan abu da kikaji muna fadi maki to soyayya ce" mun san ke wayayyiya ce" kin gane abinda muke nufi" talatu ta yatsine fuskarta kamar zata yi kuka "Nifa malamai gaskiya ban fahimci abinda kuke nufi ba" kunki fitowa ku fada min magana sai kewaye-kewaye kuke tayi mani" ina ga da zaku fito ku fada mani abinda kuke nufi gaskiya zaifi" samarin kauyen uku suka kalli juna Auwalu tace Baban yara kayi magana mana" ya zatayi mana haka? Baban yara ya juya ya kalli dayyabu yace" Dayyabu ka sake yi mata bayani yadda zata gane Dayyabu ya kalli talatu ya tambayeta yanzu ke malama duk wannan maganar da muke yi baki gane inda muka dosa ba" baki fahimcemu ba" talatu ta girgixa kai tace Gaskiya ni ban gane ba . Auwalu yayi karfin hali yace da ita" Amma dai ai kin san Hausawa sunce ita rayuwa ka taimakeni ne in taimake ka! talatu tace cikin fushi-fushi "Eh, tun dazu ai kuke ta fadar haka" to me kuke nufi da taimakeni in taimakeka? gani nayi baku sanni ba" nima ban sanku ba" sai yau muka hadu" to kun bani wajen kwana" gashi har na kwanta" kun kawo mani abinci naci" to me kuke so kuma inyi maku" sai ku fito ku fadi gaskiya" na gaji da wannan dogon turancin" barci nakeji" in zakuyi magana kuyi magana" in bazaku yi magana ba" don Allah ku tashi ku fita barci zanyi" zan kulle kofa Samarin uku suka sake kallon juna kowa yana tsammanin dan uwansa zaiyi magana da bakuwar tasa suna ta bata mata lokaci sai zare idanu suke yi saita tashi daga kan gadon ta tsaya kansu tace ku dan fita in rufe kofar.... Sai da safenku" su duka ukun suka tashi jiki babu kwari suka fice daga dakin" suna fita ta turo kofar ta kulle tasa sakata" suna ji suna gani . Rufe kofar keda wuya suka fara yiwa juna banbami kamar zasu bugi in buga" Dayyabu wanda a fusace yace "Duk abinda ya faru laifinku ne" ku fito kuyi mata bayani kuce ga abinda muke so" amma kowa yayi shiru" kun barni sai ni kadai nake ta magana Kuma sai wani abu ya taso kuce ku wayayyu ne" haka ake wayewar? ance kuyi mata bayani yadda zata gane kunki Auwalu ya karba da cewa duk wa yayi mata maganar bani bane? Nine fa nace mata mun taimaketa ya kamata muma ta taimakemu kuna ji kukayi shiru baku yi karin bayani ba Gaskiya kun cucemu kawai asan abinda za'ayi ni bazan yarda ba . Baban yara yace Ni ai na gama nawa tunda nina ganta na daukota nazo da ita kuya kamata kuyi mata magana dalla-dalla harta fahimci ga halin da ake ciki amma kuna abu kamar kuna jin tsoro Har yanxu wallahi baku waye ba Dayyabu ya sake duban sauran abokanansa Wai kuna jin da gaske bata gane abinda muke nufi ba Ni ina ganin fa kamar so takeyi ta raina mana hankali . GASKIYA TA RAINA KU KARKU YARDA HAHAHAHAHA MAGANIN SHEGE AI SAI SHEGE DAN UWAN SA . (c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 09 . . Auwalu ya katseshi da cewa bata gane komae ba Ya za'ayi ta gane bayan kowa ya kasa cewa da ita komai Ni banga laifinta ba..Ko menene mu kuka jawo . Samarin kauyen uku sun dade suna ja'-inja a tsakaninsu kafin Amadu baligi da yaransa uku su zo wajen a fusace Da zuwansu ko sallama basu yi ba Amadu baligi yaci kwalar rigar baban yara ya fara yi masa kwaratsi Ina wannan bakuwar yarinyar da aka ce ka dauko tana ina? Baban yara da sauran abokanansa biyu sun san matsayin Amadu baligi a kauyensu don haka ba wanda yake son rigima ya hadashi da uban baligai indai mutum bazai yi kokari yayi abota dashi ba ko ya zama yaronsa to babu wani mutun da zai zama makiyin Amadu baligi Baban yara ya nunawa Amadu baligi dakinsa yace tana ciki tana barci kafin Amadu baligi yace wani abu yaransa uku DAMINA DA GARUJE DA KWATSAMI suka hada karfinsu suka bangaje kofar dakin baban yara wacce tayi tsawa ta fada cikin dakin hade da wani tsohon bulo da yake rike da ita shekara da shekaru da kuma baragunsan kasa wannan ya faru a lokaci guda da farkawar talatu daga barcin da ta fara" Dayyabu da Auwalu suka koma gefe a tsorace suka zama 'yan kallo" Amadu baligi ya saki kwalar rigar baban yara ya nufi dakin da yake fayau babu kowa" da shigarsa ya sami talatu a tsorace tana kokarin fitowa" Ganin yadda fuskar Amadu baligi take cike da fushi da kuma rashin tausayi sai talatu ta hutar da kanta wajen tsayawa bashi hankuri don kuwa ba yau maza suka fara dukanta ba a wajen yawace-yawacenta na dandi ba" akwai yanayin da ake samu idan namiji yayi fushi baya jin magiya da kuma neman afuwa dole sai ya buga sannan zuciyarsa zata lafa ya hakura daga baya Don haka sai talatu bakuwa ta dora hannuwanta biyu akai koda Amadu baligi ya shara mata mari bai sami fuskarta ba sai dai ya bugi hannunta talatu ta fara kuka acikin dakin ragowar samarin dake a waje suna saurare basu yi yunkurin shiga su ceceta ba . "Ba kece nace kibar garin nan ba ki koma gida ba? kin dauka ina wasa dake ne? Amadu baligi ya ware karfi ya rika gabza mata hannu kamar ya samu kato dan uwansa hakan yasa dole talatu ta bada kai" don kuwa bazata iya jure kare kanta ba ta fadi war-was tana ihu hancinta yana zubar da jini a tsakar dakin faduwar da tayi ne tana haure-haure yasa tayi baza- baza da tarkacen abincin da su baban yara suka kawo mata Amadu baligi ya jawo kwalbar lemu daya a cikin kires zai rusawa talatu a goshi kenan sai yaji an rike hannunsa ta baya ya juya a fusace a lokacin ne yaga ADO GARUJE" yana yi masa murmushi "Afuwa uban baligai" ya amshi kwalbar daga hannun Amadu baligi" sannan ya shiga tsakaninsa da yarinyar wacce ganin mai cetonta ya shigo sai tayi saurin ja baya tana kokarin gyara zaninta da ya kwance bata daina kuka ba "me yasa ka shigo garuje baka barni na karyata ba don ubanta? har kudin mota fa na kawo na bata nace ta koma gida bana son ganinta a wannan kasar tawa amma da yake 'yar iska ce ta zauna bata tafi ba . Garuje wanda ya tabbatar ba dole bane Amadu baligi ya hakura indai yana ganin talatu a dakin don haka sai yayi kokarin fitar da yarinyar zuwa waje idan aka rabashi da ita na wani dan lokaci ya daina ganinta bayan komai huce sai a barta ta fito kafin aji umarnin da zai bayar a lokaci na gaba Ado garuje ya janyeta suka fita waje inda su DAMMA suke tsaye suna dariya wasu daga cikin mutanen dake a layin 'yan ba ruwanmu suka tsattsaya a waje suna kallon abinda ke faruwa don kuwa indai za'a ga wata mace a tare dasu Amadu baligi to an san ba 'yar mutunci ba ce komai akaga suna yi mata ba wanda zaice musu uffan Da Amadu baligi ya fito daga cikin dakin ne ya kalli baban yara dake a gefe guda tare da dayyabu ya nuna musu yatsa yace dasu cikin kakkausar murya ku kuma daga yau idan gilli ta sake zuwa garin nan kuka dauketa saina aikata ku zan nuna muku ku kananan marasa kunya ne anan gida kuke iskancinku ana kyaleku baku je ko ina ba . Ba wanda ya mayarwa Amadu baligi martanin maganarsa saboda sun san ba tsaransu bane ko ba komai maganarsa da ya fada sun san gaskiya ne su ukun marasa kunya ne a kauyensu kawai shi kuma ya zauna a layin jan bulo yayi karen babbar motar kaya na wata takwas daga arewa zuwa fatakwal" yaje abuja yayi wata tara yana amsar hannun kwaryar babur yana acaba a kowanne dare idan masu babur sun gama aikinsu na rana" Wadannan kadan ne daga cikin shaidar karatun yawon duniyar da Amadu baligi ya mallaka kuma akan biyun da za'ayi masa jarrabawa a cikinsu zai fito da sakamako mai gamsarwa" shiyasa idan ya dubi mutum yace dashi karamin mara kunya baza'ayi wani musu ko jayayya ba . Su damma suka daukowa talatu kayanta suka tasata a gaba suka tafi da ita suka bar su baban yara da abokansa suna tunanin gyaran barna da asarar da ta dado musu a cikin wannan dare . AI KADAN MA KENAN KUKA GANI . (c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 10 . . Anyi haka da minti talatin Amadu baligi ya huce kamar yadda ya saba ya dauko babur dinsa a gida yazo gidan karuwai inda su Damma suke tare da talatu a waje suna yi mata nasiha ko don gaba kada ta rika yin taurin kai duk garin da ta sauka ta rinka ladabi idan baligi ya kafa doka a kasarsa kada tace zata karya Amadu baligi wanda ya sake ranshi yace da ita zoki hau muje in mayar dake gida talatu ta taso daga cikin karatan uku dake tsare da ita ta hau babur din Amadu baligi tana rike da ledar kunshin kayanta kamar yadda tazo da su kafin Amadu baligi yaja babur din ne su tafi ya dubi yaran nasa yace dasu Zan kaita tsaunin yalwa sai can cikin dare zan dawo kada kubar wadannan makadan borin su kafa wasa saboda naga abin nasu akwai rainin wayau kwanaki sunyi wasa dan alherin da zasu yiwa mutane ma suna ganin asara haka suka tafi dama nace zasu dawo garin su same ni kada kubar kowa yahau bori yau . Amadu baligi yaja babur din suka sheka a guje shida talatu a zaune ta danne masa baya baiji lokacin da kwatsami yace Duk shegen da yace zai hau bori yau kafin ya kira aljanun suzo kanshi mu zamu fara mu hau kan nasa mu turmumusa mutum yaji irin tamu dafin Ragowar karatan biyu suka fashe da dariyar shekiyanci a lokaci guda . BABI NA HUDU GARIN DUBARUDU Ban gunduma ce dake da hakimai da kuma kansila idan aka koma sashin mulki" akwai karamin ofishin 'yan sanda wadanda suke sasanta kananan rigingimu" idan kuma abin yayi karfi sai su dauka sukai babban ofishin karamar hukuma" Garin dubarudu" yayi suna wajen gidajen mata masu zaman banza kamar yadda ake sakaya masu muguwar sana'ar tasu yadda za'aji dadin fada wasan dambe a garin dubarudu wani muhimmin abu ne mai zaman kansa idan lokacin wasa yazo baki sukan zo daga kowanne lungu na cikin kasa da kuma wadanda baza'a rasa ba daga jamhuriyar niger . Babban gidan dambe yana daukar mutane fiye da dubu shida" idan aka hada da 'yan kallo da suke mikewa a saman katangar da ta zagaye gidan" Da yamma tayi za'a fara rugunguntar zuwa a sami wuri a lokacin ne makadan dambe suke fara kida suna kirawo mutane don kowa yazo bakin aiki" Raba garin dubarudu da karuwai abune da zaiyi wahala badon komai ba sai don nan ne matattarar tsayawar motocin safara idan mutum yazo wucewa ta garin motocin da suka yada zango a bakin titi zai fara gani wanda irin wadannan direbobin ne suka ajiye karuwan" saboda su rika tsayawa wajensu duk sanda suka kai kaya kudu suka dawo Idan dare yayi ba abinda mutum zaiji sai tashin kade-kaden mawaka da 'yan amshi a gidaje daban-daban bayan karuwai akwai 'yan daudu dake sana'ar abinci sannan kuma jefi-jefi masu wasa da maciji sukan kawo ziyara don garin dubarudu ya tattara duk wani nau'in holewa da sharholiya irin na mutanen karkara Wani direban tangul ya taba dawowa daga aiki tare da yaronsa suka sauka a garin direban ya tambayi yaron motar ko nawa suke dashi a hannu yanzu yaron motar ya kirga kudin yaga suna da tsabar kudi dubu dari da arba'in direban ya amshi dubu arba'in din ya bawa yaron motar izin daukar dubu ashirin yace yace ya zabi yarinyar da zasu kashe kudin tare shi dama yana da tasa da ya ajiye a garin . Direban ya tafi dakin karuwarsa sai yaron yayi kwanciyarsa a cikin mota ya adana kudinsa Bayan kwana biyu direban ya sake dawowa wajen yaron motar ya kara amsar dubu talatin yace da yaron ya sake dauka dubu ashirin shima yaje ya huta Da yaron motar yaga ya sami tsabar kudi a hannu dubu arba'in kuma da yaga kudin zasu kare a banza a wajen karuwai sai ya hau mota yaje gida yakai nasa kudin aka sai masa maraki na dubu talatin da biyar aka daure masa Yaje gidan ubangidan nasa ya sami matansa biyu ya tambayesu menene matsalarsu ? matan wadanda suke zaune cikin yunwa kwana da kwanaki ba abinci suka lissafawa yaron motar maigidansu abubuwan da suke bukata tun daga kan abinci da sutura duk takalmansu sun tsinke ko silifa basu dashi ga katangarsu ta rushe mutane suna ganinsu idan sunzo wucewa yaron motar ya kashe masu ragowar kudin duka yasa aka gyara musu gidan yayi musu komai da zai barsu ya koma wajen aiki har kuka suka rinka yi suna cewa ya gaida musu mijinsu Sun Gode ! Sun Gode! . Dole ne matan suyi godiya dan kuwa a shekaru goma sha uku da mijin nasu yayi yana jan tangul bai taba tsinana musu komai ba sai yanzu da yaron motar nasa yazo musu da wannan abin arzikin . Da yaron motar ya koma direban ya tambayeshi ragowar kudi yace sun kare duka bai damu ba saboda yayi zaton karuwarsa ya kashema wa sai da suka koma gidane yaga abinda yaron motar yazo yayiwa iyalansa sannan yaji labarin har yaron ya sayi maraki da fara zuwa dashi aiki zai zama mai arziki gashi shiko kaza bai mallaka ba a duniya daga shi sai rigarshi . Aranar ya kira yaron ya zazzageshi fata-fata.. . . Loading page 11 KAZAR KARFI--> 11 . . A ranar ya kira yaron ya zazzageshi fata-fata yace ya koreshi ya nemi wani dan shaye- shaye don kuwa a cewarsa yaron sakarai ne bai san aiki ba. . Irin wadannan garuruwa wadanda suka tara karuwai suna jawowa mutane da dama rashin tattali da kuma fadawa tashin hankali da fatara Dubarudu gari ne wanda matan aure suke fushi dashi don kuwa akwai mazajen da suke wata da watanni a dakin karuwansu ba tare da sun tuna gida ba Wadansu matan kuma dake a kusa sukan hada kansu su zo har gidajen karuwan su nemi karuwar da ta rabasu da mijinsu su casata su kwashe kayan dakinta duka su ba 'yan dako su kai musu gida Shiyasa don kaje garin kaga mutane suna sana'a da kuma harkokin arziki amma kullum suna a tsiyace to bata lokaci ne mutum ya tsaya tambayar yadda akayi kada mutum yaje garin yaga matasa suna noma buhu dari a shekara amma riga tana neman kauce musu har ma a tsaya mamakin ko meyasa? . Dirka-dirkan karuwai ne da suka cika garin dubarudu dama sauran garuruwan dake a jahohin kasar nigeriya suna taimakawa wajen koma bayan tattalin arziki kuma suna habbaka talauci da rashin aikin yi . Da karfe daya na rana Amadu baligi yazo garin dubarudu ya sami abokinsa Bala yana jiransa a bakin titi da fitowarsa daga mota suka tafa suna dariya kura gareku masu awaki bala yace da Amadu wanda ya bashi amsa da kurari sa'a dai ko dare ko rana wuya koda magani ba dadi yaro. Suka sake jinjinawa sannan suka kama hanya zuwa inda gidajen holewar suke acan yamma da garin suna cikin tafiya ne bala ya fara yiwa Amadu tambaya akan talatu ban hada komai da ita ba bala kawai na mayar da ita gida wajen babanta shine jiya yake fada mani ta sake guduwa Bala yace Na ganta da idona tana wajen wani dan dambe cikin bakin 'yan wasan da suka xo sunansa TAMARKE ko dazu na gansu tare sun fito sun sayi nama sun koma ina jin daki ya kama mata . Amadu ba tare da wani zullumi ba yace muje in sameshi in fada masa kanwata ce Balan dubarudu bai kai Amadu baligi wauta da jarumta ba kuma bashi da wani tarihi mai kayatarwa a yawon duniya dan tarihin laifinsa bai taka kara ya karya ba kawai dai an taba kasashi a wajen neman wata yarinyar da yake so a ranar da aka daura auren yaje da yaransa suka sami angon suka kamashi da tsiya suka samu filayar kwance noti suka cire masa faratan kafafuwa dana yatsun hannu saida yayi wata biyu yana jinya kafin wasu faratan suka sake fitowa sannan kuma ya taba ajiye wani mugun kare wanda ya addabi mutane ba damar a wuce ta kofar gidansu karen bai tasowa mutum da cizo ba idan kuma mutane suka bugi karen da adda Bala yake fitowa ya bisu a guje dole sai ya ramawa karen sannan zai hakura" sai da 'yan sandan tuhumar manyan laifuka na jiha suka kamashi yayi wata daya a hannunsu sannan suka cusa masa ladabi na wucin gadi aka sami saukinsa yadan saurara Idan aka dauke wadannan abubuwan bashi da wani tarihi da 'yan sanda suka adana a fayil dinsa . Amadu baligi da balan dubarudu suka isa inda sansanin 'yan damben suke suna a zazzaune a gindin wata katuwar bishiya inda wani mai balangu yayi sabon gashi wani mai gurmi yana zaune a benci a gefe guda yana kada gurminsa yana waka da katuwar muryarsa dake kama da banbaro ba tare da kowa ya mayar da hankali ya saurari abinda yake cewa a wakar tasa ba batare da shi kuma hakan yasa ya gaji yayi shiru ba Karuwai shida ke tare da 'yan damben tara wanda hakan ya nuna uku daga cikinsu ne kawai basu tare da nasu karuwan yawancin 'yan damben suna sanyene da matsattsun singileti wadanda suka fito da kwanjinansu da kuma jijiyoyin hannun kamar igiyar daure dami Ba wanda zaiso ya kalli fuskokinsu don kuwa dukan yau da kullum ya canjawa kowa halitta a cikinsu wani hancinsa ya murgude wani kuma habarsa ta karkace wani kuma bashi da hakoran gaba wani idonsa daya ya mutu da wahala a sami wani dan dambe daya a cikinsu wanda komai nasa yake lafiya garau kamar yadda babarsa ta haifeshi . Amma matan da suke tare dasu basu damu da muninsu ba saboda kowacce tana sane da dubban kudin da ake ajiyewa a matsayin ( KAZAR KARFI ) A Filin wasa kuma duk wanda yayi nasarar yin kisa kacokan ake daukarsa a bude huluna ana zagayawa dashi cikin fili 'yan kallo suna zuba masa kudi suna yi masa jinjina saboda in dai kato zaiyi kisa ya sami kudi mezai hana su zauna dashi suyi nema? . Kafin Amadu baligi yayiwa kowa magana a cikinsu ne Bala ya kira daya daga cikinsu wanda yafi sabawa dashi Akwai tamarke a wajen yana zaune yana gyara wata katuwar layarsa wacce ta fara barewa a hanci babu talatu a wajen me yiwuwa tana dakin da tamarke ya kama mata Amadu da bala da daya daga cikin 'yan damben suka kebe gefe guda mai kada gurmin wanda ya karkace hularsa kwaurin ladi ya fara yiwa bala waka saurayin ya juya ya harareshi sannan da ya dawo da hankalinshi kan dan damben yace dashi.... . ANA WATA GA WATA KENAN TALATU TA ZAMARWA UBAN BALIGAI CIWON KAI 12 LOADING.. . (c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 12 . . Ka gane ko WARURE wannan aminina ne ba anan garin yake ba to wata kanwarsa ce ta gudu daga gida tazo nan garin jiya ita ce yarinyar nan da tamarke yayi kwanan gida da ita jiya dazu ma na gansu tare to shine muke so a taimaka mana ka fadawa tamarken ya sallami yarinyar ta fito mu tafi da ita Warure ya girgiza kai yace dasu kun san halin wancan dan iskan ba mutunci ne dashi ba ba lallai bane ya bada hadin kai ya fito da ita ba ina jin yarinyar ma bata nan yanzu tabi wasu yara sun tafi wajen wani ajo da akeyi sai a lokacin Amadu yasa baki yace kayi masa magana mana kanwata ce ya fada mana inda akeyin ajon sai muje mu sameta acan warure ya juya ya dubi inda abokan sana'ar tasa suke zaune suna hayaniya da zage-zagen wasa a gindin bishiyar ya daga murya yace tamarke ji mana . Katon wanda Zai iya kayar da bajimin sa idan suka hadu ya dago kai a fusace me ye fa? ya bukata da kakkausar muryasa yana zaro idanu da warure ya tabbatar tamarke bazai zo ya samesu ba saiya tambayeshi ka gane wai gillin nan daka tsinta jiya suke nema ina take ne? tamarke ya hada rai ya mayar masa da martani su waye suke nemanta? me zasu bata? Da Amadu baligi yaga kamar kan yaron ya cika da zapi sai yace dashi a fusace shima aki kada ka daukemu kananan yara mana! Muna tambayarka inda talatu take ne Ina ruwanka da abinda zamu bata kasan yadda muke da ita ne? tamarke ya tashi tsaye kamar wanda aka watsawa wuta yace da Amadu kai dan Iyayenka kasan ni ko wanene kake fada mani haka? to na boyeta bazan fito da ita ba Ka ware in daina ganinka anan in ba haka ba zan aikata ka billahillazi Bala ya dafa Amadu baligi don kada fada ta shiga tsakaninsa da yaron sauran 'yan damben suka fara ba yaron baki yawane tamarke wannan ba tsaranka bane kawai ka barsu su ware wata karuwa tace dashi tana dariya kisan kai kake so kayi tamarke! saboda waccan abin kake mikewa? to kace kayi fada dawa idan ka bugeshi ya fadi? idan karfi kakeji ka bari anjima zan sa maka KAZAR KARFIN Sarkata in hada ka da mai gidana . Ta bugi kirjin wani faskeken kato wanda yayi dariya ya tona asirin wawulonshi babu hakuran gaba Haba barshi dai yayi da tsararrakinsa kada ki zuga yaro ki jawo a binneshi anjima da daddare Amadu baligi yayi murmushi ya tambayi tamarke kai ni kake zagarwa iyaye? tamarke ya sake tasowa ya matso gaba "Dan uwarka an zageka! Me zaka yi? Kafin bala ya rike Amadu tuni har ya nufi inda tamarke yake a guje warure ya bishi don ya shiga tsakaninsu da tamarke sauran 'yan damben suka yi zaune suna kallon yadda fadan zai kasance suna dariyar mugunta don kuwa a yadda suka san zafin hannun tamarke ba karamin wauta wannan bako yayi ba da zai fada masa" TO AMMA ZAFIN HANNUN TAMARKE SUKA SANI BASU SAN ZAFIN HANNUN AMADU BALGI BA . Kartin biyu suka hadu da juna tamarke ya fara kawowa Amadu duka wanda ya rika bahaguwarsa ya dakatar dashi ta hanyar tokareshi baya" kafin tamarke ya samfa daya hannun nasa tuni har Amadu baligi ya aika badamiyarsa wacce tafi illa a fuskar mai tsautsayi . Da fadawar hannun Amadu akan fuskar tamarke ya fada ihu ya fadi a rikice saurin dukan da Amadu yayi masa kamar yanayin da zai faru da mutum ne idan hannun fanka ya mareshi idan ya mike akan kujera bai sani ba fuskar tamarke tayi dameji kamar fuskar gilashi a duka daya tayi ratsi-ratsi kamar tamarke yayi hadarin mota 'yan damben suka tashi a fusace tare da karuwansu suka ja baya suna kallon Amadu baligi saboda basu

Chapter 3 of 6