Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 6
taba ganin wani hannu yayi irin wannan barnar ba koda kuwa a wajen dambe ne! Idan an fito fage shi kansa balan dubarudu abin ya kidimashi yaja baya yana kallon Amadu baligi wanda ya yiwa shahararren dan dambe duka daya ya watse Shiru kowa ya kasa magana kamar ruwa ya cisu Amadu baligi bai sake waiwayar tamarke ba wanda ya baje kasa yasan ai irin dukan da yayi masa zai dauki kwana masu yawa yana jinya kafin ya warke ya sake yiwa wani rashin kunyar . Ya fuskanci sauran 'yan damben yace dasu "Bana son rashin mutunci ya shiga tsakanina daku saboda nasan mutuncin sana'arku kuje duk inda kanwata take ku fito min da ita na baku nan da awa daya idan ba haka ba komai ya faru tsakanina daku ku kuka jawo! Amadu baligi ya juya ya tafi a fusace" bala ya biyohi a baya suka koma 'yan damben sun dade a tsaye babu wanda ya motsa a cikinsu saboda sun tabbata ko daga ina wannan jarumi ya fito hannunsa a cike yake da zarce! Bazai taba yiwuwa ace hannu yayi irin wannan ta'asar a bugu daya ba batare da an dade ana girka hannun ya nuna da dafi ba . BA'A JIMA BA labari ya wasu ako ina a cikin garin dubarudu mutane suka fara yayata dukan da Amadu baligi yayiwa tamarke . Abinda tafi daurewa mutane kai shine babu wanda yasan ko Amadu baligi wanene shi kuma ba'a san ko daga ina ya fito Ba . UBA MA ASHE DA UBANSA KENAN Ku Biyoni Domin Jin Cigaban Labarin KAZAR KARFI . (c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 13 . . Mutane suka fara hasashen idan har a wajen dambe Amadu baligi yayi irin wannan dukan zaifi birge 'yan kallo ya sami alheri bai kamata ace a wajen fada yayi irin wannan dukan ba ya barar da dafi a banza Amadu baligi yaje gidan bala suka zauna a waje suna zantawa kan fadan da ya shiga tsakaninsa da dan damben mutane suka fara tururwar zuwa ganinsa don kuwa a yadda aka dauko tamarke a babur fuskarsa tayi dameji tana zubar da jini aka wuce dashi asibiti kowa ya kadu da akace duka daya kawai wani bako yayi masa kuma bai nade hannu ba ba wani shiri yayi dukan tsabar dafi ne kawai da sinadarai Akwai dalili kwakkwara da yasa mutanen garin suka rika zuwa suna jinjinawa Amadu baligi tun zuwan wadannan bakin 'yan damben suka disashe tauraruwar duk wani dan dambe na cikin gida duk wasan da za'ayi sune suke yin kisa har yanzun ba'a kashe kowa nasu ba . Mutanen garin suna son wani bako yazo ya daukar musu fansa ya kashe koda mutum daya ne a wajen wasa don su rage yiwa mutane kuri suna cika baki Akidar mutanen garin su suna goyon bayan 'yan damben kudu ne ba'a goyon bayan arewa amma tun zuwan wadannan baki kudu batayi kisa ba duk kisan da akayi daga bangaren arewa ne dole ne hankalin 'yan kallo ya tashi Garban kauye shine fitaccen jagoran shirya wasan dambe a garin dubarudu yana da yaransa wadanda suke wasa a gida wadanda tun zuwansu tamarke ba'a jin motsin yaran Garban Kauye ya damu matuka yana son ya sami wani sabon dan wasa daga kudu wanda zai kashe masa koda mutum daya ne a cikin 'yan arewan nan Yana a gida labari ya sameshi cewar wani bako abokin bala yazo sunyi fada shi da tamarke yayi masa wani duka wanda ba'a taba ganin irinsa ba a tarihin dambe Garban kauye ko gida bai shiga ba ya garzaya a babur dinsa yaje gidansu bala don yaga bakon da yayi wannan abin alheri . Da zuwanshi ya samesu su biyu a zaune suna shan fura Garban kauye ya kashe babur dinsa ya sauko yana dariya tun kafin bala yayi masa sannu da zuwa yace "ina bakonka shi nazo nema Bala ya nuna Amadu baligi Garban kauye ya kama hannun Amadu baligi ya jijjiga yayi masa jinjina Amadu baligi yayi murmushi kadan Mun gode! Mun gode. Don Allah ya sunanka ya fada masa sunana Amadu Garban kauye ya tambayeshi Amadu kai mutumin ina ne? Ina acan tashar Dan amarya ne gundumar muje- dawa Garban kauye yace da Amadu ina gida yanzun nan na sami labarin abinda ya faru tsakaninka da tamarke wadannan yara sun gallabemu tun zuwansu garin nan suke yi mana garari kullum su kadai suke yin kisa mun rasa yadda zamuyi dasu Amadu baligi yayi dariya Shi dama wasa haka ya gada bashi da gwani sai mai sa'a Sun sami sa'ar shigowa garin ne amma da sa'arsu ta fadi zakaga Hannunsu ya kwanta Garban kauye ya bata rashi da daya tuno illar da wadannan 'yan dambe suka yi masa a sati uku da zuwansu Duk KAZAR KARFIN Da ake kasawa yaransa basa ci saboda su ake kashe wa . Bayan ya gama sauraren bayanin Amadu baligi sai yace dashi "Ina so ka taimaka mana Amadu ka daure kayi mana wasa ko sau daya ne kafin ka tafi na tabbatar kai kadai kawai zaka yi mana kisa muma mu sani nasara Amadu baligi ya girgiza kai yace Gaskiya ba wasa nazo yi ba malam.... Dan gajeren mutumin mai kamar a kifashi da kwarya ya fada masa sunansa daya fahimci bai san abinda zai kirashi ba "Garban kauye nake Amadu yauwa.... To sai dai kayi hakuri malam Garban kauye ni zumunci ya kawoni garin nan nazo neman wata kanwata ce wacce ta gudu ta baro gida jiya ba dambe nazo yi ba kuyi min afuwa Garban kauye ya nuna damuwarsa a fili "ka taimaka mana Amadu" ko sau daya ka tsaya kayi mana wasa na tabbata kai kanka zaka sami alheri mai yawa a wajen mutanen mu dake garin nan saboda kowa ya gaji da wadannan yara kayi hakuri kayi mana wasa Amadu" Sai a lokacin balan dubarudu yasa baki Amadu ka taimaka in kaga da sarari" tunda kwana daya kawai zakayi" dama gobe ne ranar babban wasa ka tsaya zuwa goben idan kayi wasa saika koma da yamma . Garban kauye ya kara da cewa "mu da kanmu zamu daukeka mu mayar da kai har gida kada kaji komai Amadu akwai yaron da muke so kayi wasa dashi a cikinsu" shi kadai ya gallabi yaranmu da kisa sunansa SHAGON SADI idan har ka kashe mana yaron nan" to mu ka gama mana komai Amadu baligi ya sake yin dariya To idan kuma yaron ya kashe ni fa? bani da tabbacin zan iya kashe muku shi saboda kaga ban ga wasanshi ba kuma banzo da wani shiri ba" ba wasa nazo nayi ba" bana fadawa dambe irin haka ba shiri ko a zamanin da ina wasa bana daukar KAZAR KARFI sai na san ko dawa zanyi wasa na dade banyi dambe ba yanzu ko karamin yaro zai iya bugeni . Yaci gaba da dariya Garban kauye yace dashi Kada ka karaya Amadu zaka iya buge kowa a cikin 'yan arewan nan..... In dai irin wannan dukan da kayiwa tamarke.... . ASHE DAI UBAN BALIGAI SHIMA GWARZO NE FANNIN DAMBE. . KU BIYONI A WHATSAPP 08082035050 . (c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 14 . . To duk fadin kasar nan ba wanda bazaka iya bugewa ba ka daure kayi mana dambe kazo muje in kaika gidana ka sauka acan ni zan dauki komai naka yanzu kai bakona ne ba bakon balan dubarudu ba ne Kafin Amadu baligi ya sake yin jayayya ne Balan yace dashi kada ka damu Amadu na amince Garban kauye namu ne wannan abu idan kayi mana gida kayiwa ni dasu duk daya ne Amadu yace to yaya maganar talatu kuma? banason hankalina ya rabu biyu nafi so in fara ganinta in tsareta kada ta sake guduwa wani garin ta bamu wahala Balan ya karfafa masa gwiwa wannan ka barmu da ita zamu tare maka nan bangaren dama don tana wajen tamarke shiyasa bamuyi wani yunkuri akan dawo da ita wajenmu ba zamu lura da ita idan ta dawo ba zamu barta ta matsa ko ina ba idan kayi wasa gobe sai mu fito maka da ita ku tafi gida . Amadu yadan rage fara'a kafin yace zamu gwada mu gani Allah ya bamu sa'a Garban kauye ya sake kama hannunsa suka sake gaisawa Mun gode Amadu. Bari inje in fadawa mutanenmu aje ayi shela cewar gobe muna da bako wanda zai yiwa kudu wasa Garban kauye ya hau babur ya koma cikin zumudi ya fara sanarwa mutane cewar sunyi bakon dan wasa kuma gobe zai fito yayi dambe da arewa . Kafin dare yayi labari ya watsu ako ina a kauyukan mutane suka fara fatan ganin goben don suzo suga wasan AMADU BALIGI . BABI NA BIYAR . SADI KARE GARKE Ba boyayye bane a wajen wadanda suka shiga duniyar takadarai kuma sukayi rayuwa tare da manyan masu laifi Yafi shahara a wajen sata don kuwa anan ne ma har ya samo sunan KARE GARKE Bayan sata sadi ya iya sana'o'i da yawa maganin fashewar taya Idan satar ta kulle sai ya juya wani bangaren yaci gaba da rayuwarsa sadi ba irin kananan barayin da aka saba gani bane wadanda suke tsallaka katanga a biyosu da gudu su sha da kyar kuma ba irin barayin da suke farke aljihu bane a kasuwa al'amarin sadi duk ya dame nan ya shanye . Inda nasa sharrin yake shine idan zaiyi sata da yaje riga inda garken shanu suke" zasu biyoshi a cikin dare ba tare da wata tirjiya ba kuma idan ya balle garke guda ya shigo gaba shanu suka bishi a baya kada mutum yayi zaton zaibi sahun sadi da shannun ya cimmasu don sadi yayi lalatarsa ya kore garken a cikin dare! Da ya nufi yamma sai sawunsa dana shanun ya rika yin gabas Idan kuma kudu ya nufa to a arewa za'a ga sawunsa Don ba karamin jarumi ne zai kama kare garke ba idan yayi masa sata Sadi yana sha'awar wasan dambe duk da yake dai ba kasafai yake yarda ya dauki KAZAR KARFI Ba shi kansa yasan bashi da isasshen dafi a wajen dambe da dai a wajen sata ne anan ba wanda yake jin tsoro shiyasa yaja baya ya kama girmansa yabar yaransa suna fitowa wasa shi kuma yana kulawa da nasarorinsu yana basu shawarwari idan kuma rikici ya balle a wajen wasa har jami'an tsaro suka shigo sukayi kamu anan sadi yake yin ranarsa wajen amso yaran da ake je dasu aka kulle . A duk cikin tawagar da sadi yazo da ita na 'yan dambe goma sha daya zuwa kauyen dubarudu yafi ji da yaransa biyu wato SHAGON SADI da kuma TAMARKE yana son yaran ne saboda suna da lokaci da wahala su fita wasa wani ya kashe su indai basuyi kisa ba to sai dai a raba wasa a tashi babu kisa Akwai labarin SADI KARE GARKE Acikin Littattafai kamar su *JAMILA *GANI KASHE NI *BOYAYYEN MAKIRCI *GOßE JAR KASA . Tun zuwansu garin dubarudu dambe suna samun alheri idan sunzo gidan wasan sadi yake basu umarni duk wanda zai dauki KAZAR KARFI shi yake turashi kamar yadda duk kudaden da aka samu shi yake amsa yaba wanda yayi kisa abinda ya kamata ya dauki nasa ya kuma yagawa abokan tafiyarsu wani abu Sadi yana kwance a dakin karuwarsa da yayi a garin dubarudu daya daga cikin yaransa yaje ya sameshi cikin damuwa ya fada masa wani ya bugi tamarke an kaishi asibiti sadi ya tambaye yaron tare da tashi ya zauna Da wannen makami ya bugeshi har yaji masa ciwo? . Da hannu ya bigeshi oga.... Wani bako ne da yazo neman wata yarinya kanwarsa akwai dafi mai karfi a hannunsa fiye da namu duka daya yayiwa tamarke ya karya masa haba Sadi ya tashi zaune akan katuwar katifar karuwar wacce take wanke kwanukan cin abinci a waje DUKA DAYA DA HANNU YAKAI TAMARKE KASA ? KUMA HAR AN KAISHI ASIBITI ? Sadi ya rika nanata maganar cikin zullumi don kuwa in har wani zai iya zubar da tamarke a duka daya to zai iya bige shagon sadi kuma zai iya buge kowa a cikin yaran da yazo dasu garin yaron sadi da yazo masa da bakon labarin ya kara da cewa Yanxu maganar da ake tayi a gari shine wai mutane sun roki gayen ya tsaye yayi dambe gobe kuma ya amince xai tsaya Sadi kare garke yayi shiru yana tunani zuwa can yace da yaron nasa Ina shagon sadi yake a halin yanzu ? Yaron yace dashi Ban san inda ya shiga ba. Baya wajen abin ya Faru Amma nasan yanzu.. . WASH NA GAJI DA RUBUTU WA ZAI TAYANI ?KAZAR KARFI--> 15 . . Sadi yace ba komai zan kirashi a waya kaje zanxo in sameku mu hadu musan yadda zamuyi a goben yaron ya juya ya fice daga dakin karuwar A lokacin ne ita kuma ta shigo taga ran abokin neman nata a bace da yake ba matar aure ba bace maimakon ta tambayeshi ko me yake damunsa ta tayashi jimami sai ta tsaya a kansa kerere tace dashi tun dazu nake tambayarka kudin nan.. Ina sone zan cika ayimin sayayya ka bani kada kokaci ya kure Sadi kare garke dake zaune ya daga kai ya kalleta suka hada ido ba wani alamar tausayi a fuskarta a karo na farko a rayuwarsa ya tsinewa bariki a zuciyarsa da kuma karuwai baki dayansu karuwa.? ya sake tabbatarwa da kansa bata yi ba . DAKIN DA AKA sauki Amadu baligi a gidan garban kauye jere yake da kofar shiga gidan wanda yake fuskantar yamma tun sanda aka yayata labarin zuwan Amadu baligi da kuma wasan da zaiyi washe gari wuni mutane sukayi suna zuwa gidan garban kauye suna gaisawa dashi wadansu suna sayo masa nama suna kawo masa wadansu kuma lemu mutane sai karramashi suke yi don kuwa suna saran washe gari zaiyi wasa zai kashe masu daya daga cikin bakin damben da suka sauka a dubarudu Da dare yayi ne GARBAN KAUYE ya bashi dakin saukar baki dake a kofar gidansa suka yi bankwana dashi sai da safe ya shiga cikin gida shi kuma Amadu baligi ya rufe kofa Sai da karfe biyu na dare yayi kokacin da kafa ta dauke sai Amadu baligi yaji ana kwankwasa kofar dakin daga waje da ya tabbatar ba garban kauye bane sai ya tashi daga tsohuwar katifar da yake kwance a kanta wacce ke kasa da harshe aka sake kwankwasa kofar Amadu baligi ya lalubo wukarsa a kwankwaso wacce ko bacci zaiyi baya rabuwa da ita da ya ciro wukar ne sai ya fara kokarin kai hannu zai bude kofar dakin bai damu da ko wanene yake bubbuga kofar ba ko mugu ne ya kawo masa ziyarar dare yasan indai yana tare da wukarsa zai iya tunkararsa koda wanne nufi yazo . Saida Amadu baligi ya bude kofar ne sannan ya gane kuskuren da yayi da yayi zaton karamin mugu ne mutane ukun da sukayi masa lale marhabun sun banbanta da irin miyagun da ya saba gani sadi kare garke ne a tsakiya rika da karamar bindiga a hannunsa tana kallon fuskar Amadu" a kowanne gefensa yaransa ne" daga habu wurure ne" a dama kuma Iro bahago Sadi kare garke yayi murmushi da yaga Amadu baligi yayi saranda don kuwa wuka komai kaifinta bata kai bindiga hadari ba mayar da wukarka Amadu" nima zan mayar da bindigata Munzo ne sada zumunci ne ba fada muka zo muyi dakai ba" Sadi yace dashi a sanyaye don kada wani yaji muryarsa a kusa Amadu baligi ya saki wukar ta fadi kasa don ya nuna musu ya basu hadin kai sadi ya sauke bindigar ya sakata a cikin aljihun wandonsa" A lokacin ne ya sako kai ya shigo cikin dakin bayan Amadu ya wuce ya basu hanya . Karamar fitilar zamani mai batir uku wacce kusa take sakale da ita a jikin bangon dakin bata haske sosai amma hakan bai hana ya baiyana mutanen uku a fili ba da kuma kayan da suke sanye da su Dukansu bakaken kaya suka sanya kanana wadanda zasu taimakesu wajen sajewa da duhu sadi ne kawai yasa hula kaboyi ya bambanta da yaransa biyu Babu wurin zama a dakin in aka dauke samfotin katifar ba sauran wani abin arziki a cikin dakin sai wani karamin buhun dawa na ajiya dake a jikin bango a kwance Sadi ya zauna akan buhun a yayin da Amadu baligi ya koma kan katifar ya xauna warure da Bahago suna a bakin kofar sun toshe iskar da ke shigowa su basu fita ba su kuma basu shigo ba me yake tafe daku ? Amadu baligi ya tambayesu cike da masaniyar sune bakin 'yan damben da garban kauye yake bashi labari Da ganin kafadunsu da kunnuwansu ya fahimci hakan saboda aikinsa ne Sadi yace dashi Nasan bazaka rasa jin labarina ba ni da yarana? Nine sadi kuma nina zo da wadannan yara nan garin muna wasa sati uku kenan muna samun alheri. Dazu da rana kayi rigima da daya daga cikin yarana wato tamarke kuma harka batashi a fuska..... Yanxu haka yana asibiti an kwantar dashi . Amadu baligi yace "Ban so hakan ya faru ba ni kaina.... To amma yaron tsagera ne Nazo neman kanwata ne talatu aka ce dani shiya ajiyeta na tambayeshi yarinyar shine ya zagi iyayena kaji dalilin dukanshi da nayi sadi yayi murmushi kamar abin bai dameshi ba wannan namijin dukan da kayiwa tamarke shiya jawo maka farin jini a garin nan har garban kauye ya rokeka daka kwana kayi wasa gobe suna so ka karya mana lago ka farke mana laya ne saboda tun zuwanmu babu wanda yayi nasara akan daya daga cikin yarana "Nasan haka.... Amma ni ba ruwana da gabar dake tsakaninka da garban kauye ni zanyi wasane kawai don nishadi da kuma soyayyar da mutanen garin nan suka nuna min . Bana dambe da gaba kuma sanda nayi tashena bana yarda inyi fada a wajen wasa... . WAI JAMA'A WA KUKE GOYON BAYA ? AMADU BALIGI KOKUMA SU YARAN SADI KARE GARKE ??? KAZAR KARFI--> 16 . . Bana Fada da gaba agurin wasa Idan mutum ya kasheni nasan Allah ne ya bashi sa'a a kaina ba wani gaba idan kuma nina kashe mutum nasan ba karfina bane ko iyawata wasa haka yake ni ba fada nazo yi ba Sadi ya girgiza kai cikin gamsuwa da bayanin Amadu baligi Naji dadin wannan kalamai naka kuma na fahimceka Amadu muma ba fada muke so ba mun zone mu rokeka wata alfarma kuma muyi yarjejeniya dakai akan wannan wasa da za'ayi gobe ina so kayi mana alkawari kuma ka fada mani gaskiya inka amince in ma kuma baka amince ba to ka fada min gaskiya don in sani Amadu baligi yace da sadi Ina jinka ci gaba da magana Sadi ya gyara zama akan buhun dawar yace mun san cewar idan dambe za'ayi kafi karfinmu ba wanda zai iya kasheka a cikinmu Amadu Wannan wata magana ce a tsakaninmu da kai ka sani muma kuma mun sani idan kayi wasa gobe koda wa muka hadaka zaka iya bigeshi kuma idan kayi mana haka ka karya mana kwari a garin nan . Wanda hakan zaisa kwarjininmu ya fadi muna samun abinci dai-dai gwargwado a garin nan don haka nake so ka taimakemu idan kayi wasa damu gobe ka bari yarona ya bigeka yayi nasara akanka ni kuma nayi maka alkawari zamu bar maka duk KAZAR KARFIN da aka sa ko nawa ne bamu so mun bar maka Ni dai ina so ne kawai ka kare mani mutuncina a garin nan tunda kaga zuwa kayi kuma gobe zaka koma mu kuma anan muke zaune nan ne wajen cin abincinmu. Kayi mana wannan halaccin kaji Amadu ko nawa aka sa KAZAR KARFI zamu bar maka A karo na farko tun zuwansu dakin Amadu baligi yayi murmushi sau daya yayi tunani a gajarce sannan yace to wannan ba wani damuwa bane a gareni indai kana ga yin hakan shizai baku damar ci gaba da yin sana'arku. Ba wata matsala dawa anyi wasa goben a cikin yaranka ? Sadi kare garke wanda shima yayi murmushin jin dadi yace Da shagona zakayi dambe karamin yaro ne ka bishi a hankali Amadu bazai iya daukar dafin ka ba . Amadu yace dashi "In dai don wannan ne ka kwantar da hankalinka na daukar maka Alkawarin zan barshi ya bugeni ni dama ba wasa nazo yi ba nazo neman kanwata talatu ne wacce yaronka ya boyeta sadi yace cikin sauri Ba boyeta yayi ba na bincika naji" wata karuwa ce ta jata suka tafi ajo wani gari sai gobe zasu dawo da zarar ta dawo saika tasata ku koma gida Amadu yace shikenan ba damuwa sai goben Sadi ya mike tsaye yasa hannayensa biyu cikin aljihun wandonsa (jeans) "Na gode Amadu ina fatan zaka cika min alkawarin da ka daukar min nima zan cika maka alkawarina bazamu taba ko kwabo a KAZAR KARFIN da za'a sa ba kai zamu baiwa duka Amadu ya tashi don ya rufe kofar dakin idan sun fita sun fara isarsa haka nan Shikenan sai goben Sadi ya kama hanyar ficewa daga dakin yaransa biyu suka fita suka bashi hanya tun zuwansu basuyi ko tanba sun hade fuskokinsu kamar dodanni" Lokacin da sadi ya fita ne kafin Amadu ya turo kofar ya rufe dakin sai sadi yace dashi daga can waje . Wata kila ka canza ra'ayinka kafin goben" ko kuma in lokacin yayi ka karya mana alkawari idan kayi mana haka muna da hanyar da muma zamu dauki fansa na tabbatar bazaka so ka koma gida da gawar talatu gida ba" in har baka cika mana alkawarin mu ba saina kashe talatu kisan wulakanci Sadi ya tafi cikin sauri tare da yaransa biye dake take masa baya a cikin duhun daren" Har sukayi nisa Amadu bai daina jiyo sautin tafiyarsu ba kamar wadanda suke kwaba kasa . LOKACIN WASA YAYI . AN DADE BA'A TARA jama'a a gidan damben dubarudu ba irin wannan rana da yake dama anyi yekuwa an sanarwa mutane bakon wasa tunda wuri 'yan kallo suka rinka tudadowa daga kowanne lungu kafin karfe biyar tayi gidan ya cika ba masaka tsinke" An kafa itatuwan zama a gidan damben" daga gaba kuma bencine aka ajiyewa inda yawancin 'yan wasan suke zama da kuma wadanda suke da ruwa da tsaki a wajen shiya wannan wasannin dambe a gidan" filin da 'yan wasan suke tsayawa a zagaye yake da turakun itace da igiya" ta yadda koda filin ya rikice dai babu dan kallon da zai tsinka ko ya shigo cikin da'irar . Ba'a bata lokaci ba kowa ya hallara a gidan wasan" makadane suketa aikin buga kalanguna suna yiwa 'yan wasa kirari" da yake kowannen dan wasa akwai wakarsa wadda akeyi masa kirari da ita" lokaci- lokaci 'yan damben sukan je inda masu kidan suke suyi musu ruwan kudi su dawo baya suna rawa da kirari mutane suna tafi da ihu Garban kauye yafi kowa kazar-kazar a wannan ranar" ya kasa zaune ya kasa tsaye yana ta kaiwa da komowa fuskarsa cike da farin ciki A bangare guda Amadu baligi ne zaune ana daura masa zare a hannu A daya bangaren kuma sadi kare garke ne tare da yaransa goma sun taru a gungu daya kowa ya daura zare sunyi shirin wasa . Shagon sadi wani garjeje ne tattirna wanda ga alama idan har zai kwatanta yin fara'a sai yafi yadda yake muni . KAI YAU ZA'A SHA KALLON TUMURMUSA MAZAJE . KU BIYONI DON JIN YANDA WANNAN DANKEN ZAI QARE . (c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 17 . . To amma baya yin fara'ar ballantana har a gane hakan yana kusa da sadi kare garke yana wasa jini yana kaiwa iska duka da hannunsa dake a nade wani lokacin kuma yakan yi kirari ba tare da kowa yaji abinda yake cewa ba saboda hayaniyar dubban mutanen dake cike da gidan 'yan kallon da suke zaune a saman katanga suna ta miko gaisuwa suna gaishe da jaruman wadanda sukazo gidan Bayan kowa ya gama shiryawa sai Garban kauye ya dauki makirfon din magana ya fito fage ya fara da cewa Jama'a 'yan kallo yau fa babban bako wanda yazo mu gabatar dashi a wannan fage yanzu wanda kuma ni Garban kauye a ckin aljihuna nasa masa KAZAR KARFIN Naira dubu hamsin wannan jarumi ba wani bane face Amadu daga tashan dan Amarya Gidan ya kaure da ihu da tafi a lokacin da Amadu baligi ya mike tsaye ya fito a sanyaye ba wani barazana ko kirari ya shiga da'irar wasa inda kowa zai ganshi yana sanye da wando iya kwauri wanda ya tona asirin wata bakar laya dake kaure a kafarshi ba riga a jikinshi ya fito da bakar tsoka waje wacce ko ita mutum ya gani ya isa ya karaya don kuwa Amadu yaci sunansa Baligi tsattsagagge wanda ya kama kasa akwai kambu a kowanne hannunsa sannan kuma akwai guru wanda shacinsa ya fito ta cikin matsattsun wandonsa . Garban kauye ya dauko fatar buhu ya shimfidata a kasa a gaban Amadu ya ciro kudi daga aljihunsa dubu arba'in ya zuba su akan buhun mutane suka ci gaba da ihu da tafi a lokacin ne mutane suka fara ciro kudi daga aljihunsa suna mikowa wasu 'yan kore suka cire hulunansu suka fara mikawa mutane suna zuba kudi a ciki Idan hulunan suka cika sai su shiga cikin fagge su juye akan buhun su sake komawa Haka 'yan kallo suka rika miko tasu gudunmawar KAZAR KARFIN ana zubawa a gaban Amadu baligi kafin wani lokaci an tara makudan kudi timm! Akan buhun wanda in za'a kirgasu zasu kai dubu dari hudu Da gayyar mutane suka bayar da KAZAR KARFI mai yawa sun san daben da za'ayi damben gaba ne kuma kowa yana saran Amadu ne zaiyi nasara . Sadi dake a zaune akan benci daya da karuwarsa ba abinda yake yi sai dariya" yasan cewar Amadu yaji gargadin da yaje yayi masa a daren da ya gabata" ba kudin bane suka dameshi" indai shagon yayi nasarar ya bugeshi Amadu bukatarsa ta biya kada dai mutuncinsu ya fadi a garin...... A bangare guda gaba daya wasu bencina hudu duk karuwai ne sunci kwalliya wadanda sukazo da mutanensu suna zaune tare suna hira da dararraku wasu kuma suna jayayyar wanda zaiyi nasara a tsakaninsu Bayan an gama tara KAZAR KARFI sai garban kauye ya sake tsayawa yace da 'yan damben Ga KAZAR KARFI an tare" muna jiran wanda zaixo ya dauka..... Ina 'yan damben suke ? Makadan damben suka fara kida suna kirari a lokacin ne sadi kare garke yace da shago yace ya dauka suyi wasa shagon sadi ya shigo yana rawa mutane suna ihu da tafi Da zuwansa gaban Amadu baligi ya duka ya dafa kudin don haka damben ta hadu Garban kauye ya tattara kudin ya kunshesu a cikin buhun ya ajiyesu gefe guda a kusurwar da'irar wasan kusa da tirken da aka daura igiyar a jikinsa . Shagon sadi da Amadu baligi suka ja daga kowanne yana caja hannunsa suna zagaya filin zuwa can suka hadu suka gaisa mawakan suka sassauta kida ya koma kasa 'yan damben suka sake gaisawa sannan kowa ya shirya ya gyara damtse Shagon sadi ya fara kawowa Amadu duka a fuska wanda yayi saurin dukawa hannun ya wuce a tsuyace kamar farfelar jirgin sama Amadu yaja baya yayi murmushi tunda yake bai taba yin damben karya ba sai a wannan karon sun riga sunyi yarjejeniya shida sadi bazai kashe masa yaro ba baya son yin rigima da wadannan 'yan damben yafi son yayi wasansa ya gama lafiya ya koma gida dama ba dambe ya kawoshi ba talatu yazo nema har ya kwana ya wuni bata dawo ba amma ance ya kwantar da hankalinsa yau zata dawo kuma idan ta dawo da wuri ma zata zo gidan damben kallon wasa tunda duk karuwan garin suna zuwa su halarci gidan kamar yadda sukayi sansani a gaba a halin yanzu ana ihu da tafi tare da su . Shago ya sake kaiwa Amadu wawan duka a fuska Amadu ya zuge ba tare da yakai masa duka ba suka canja waje suka sake raba rana Amadu yasan da ace damben zaiyi da tuni ya gama da shagon sadi yana dai jan wasa ne yadda zaiyi tsawo kafin yaba yaron damar da zaiyi masa duka daya ba inda zaiyi masa illa ba sai ya fadi "yan kallo suna ta kiran sunan Amadu don ya jajirce kada yayi wa yaron lagwa-lagwa har yayi nasara akanshi sun bayar da KAZAR KARFI ne don suji dadin ganin an kashe shagon sadi wanda tun zuwansu garin ba'a sami wanda ya kashe daya daga cikinsu ba "Amadu! Amadu!! Amadu!!! Masoya suka rika kiran sunansa saboda kowa shiyazo gani a gidan Wasanshi ne ba'a taba gani ba. . TATABURZA KENAN IRIN WANNAN LAMARIN AKWAI TAYAR DA HANKALI . NIDAI INA BAYAN UBAN BALIGAI . KAI FA ? KE FA ??KAZAR KARFI--> 18 . . Amma idan akayi la'akari da mahaukacin dukan da ya yiwa tamarke jiya dole ne kowa yazo ya biya kudi ya ganshi Sadi kare garke yana zaune yana kallon yadda damben ke gudana yana murmushin mugunta yasan duk ihun banza mutane suke yi su zasuci wannan damben kamar yadda ya shirya shida Amadu baligi a daren jiya A cikin dubban mutanen da suke kiran Amadu baligi ne yaji muryarta daga baya Amadu zai iya gane muryar talatu bai dade da saninta ba amma ko ina yaji maganarta ko dariyarta dole ne ya ganeta Amadu ya waiga baya cikin sauri a lokacin ne yaga talatu a kusa dashi a bencin gaba tare da wasu karuwai uku yara da suka shigo gidan tare ga alama yanzu daga wajen ajon ta shigo gidan Amadu yayi

Chapter 4 of 6