Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
yara ya nufi shagon wani abokinsa mai katon kai kamar dan ruwa" wanda baya son fitar kudi a hannunsa" kuma ba karamin kunyar mutum zaiji ya bashi bashin kaya ba" Amma da yake shima ba mutumin arziki bane" Idan aka zo masa da zancen bakuwa bata da gurin kwana yakan yi rawar jikin zuba nasa hannun jarin akai mata Baban yara ya sanarwa dayyabu yana son lemo kwalba biyar manya" amma fa zai lamunce shi cikon kudin sai gobe" Dayyabu dake cikin shagon yana sauraron baban yara" ya mirgina katon kansa cikin rashin amincewa" "Gaskiya kayi hakuri baban yara" saboda ina son zanje sayayya ne gobe" kudin nake ta faman hadawa basu gama haduwa ba ma" lemun nan bazai samu ba gaskiya" Baban yara ya rokeshi a karo na biyu" "duka nawa zaka biyoni ? ina da dari biyu a hannuna gata" baifi ka bini dari da hamsin ba dayyabu" saurayin ya sake mirgina katon kansa" Tab! Dari da hamsin?" ya fada cikin jimamin yawan kudin" . "Gaskiya baxan iya ba baban yara" duka nawa muke cin riba a sana'ar ? kasan tireda fa ba wani riba gareta ba" yanzu kaga biskit sai ka sayar da kwali daya baifi ka sami naira ashirin ba sai in wuni anan banci dari da hamsin din ba" sai ai ta ganin mutum wasu kudi yake samu kuma duk abin hakuri ake yi Dayyabu yayi tsaki don kuwa har ya tuno da lissafin da yayi dazu da safe na wasu kudi yana zaton zaiga dubu uku yaga dubu biyu da dari shida baisan abinda yaci dari hudun ba yau wuni yayi yana fada da kwastomominsa akan fushin wadannan kudi da ya rasa inda suka makale Ga kuma wannan baban yara ya wani zo wai a bashi bashin lemu bazai yiwu ba gaskiya! Da baban yara ya tabbatar bazai samu bashin lemu a wajen dayyabu mai shago ba sai ya koma gefe yayi kamar zai tafi ya fara sake-sake a xuciyarsa yana magana yana cewa a baiyane kamata yayi kawai in sayi kwalba uku in hankura ai sun isheta dama dai zai danfi dacewa ne taga anzo da kwalaben lemun da yawa babu harkar karanta . Da Dayyabu mai shago yaji baban yara yana maganar ashe wata bakuwa zai kaiwa lemun sai ya daga murya daga cikin shagon ya tambayeshi kunyi bakuwa ne baban yara? ya bashi amsa sau daya a takaice Eh sanna ya koma kan lissafin da yake yi da hannu Dayyabu ya sake tambayarsa cikin kosawa yar uwarku ce tazo ko kuwa dai tsintuwa ce Baban yara? wata tsintuwa ce nayi dayyabu yace da mai shagon Dayyabu yayi saurin fitowa daga dan tsukin shagon nasa da yafi kama da dakin tantabaru ya saki ranshi ya fara fara'a har zuwa lokacin da yazo ya tsaya a inda baban yara yake yace dashi to ai kai baban yara ai gayamun abinda ake ciki zakayi tunda wuri ban san bakuwa kayi ba ai da babu abinda zai gagara bari in debo lemun kwalba nawa kake ganin ya kamata akai mata a wadace? . Baban yara wanda yayi mamakin yadda dayyabu mayen kudi ya canza ra'ayi lokaci kankani yace dashi Dama kwalba biyar nake so a kai mata" ko dai bazata shanye su duka ba ai kaga anyi mata burga Dayyabu yayi farat yace dashi" "kwalba biyar din me kuma?" ai irin wannan kiras daya ake kaiwa a ajiye baban yara" tasha-tasha har ta gaji" idan ta tafi sai a dawo da ragowar ko nawa ta rage" bari in shiga in hado kiras daya akai mata" kaga sai muje tare koya ka gani?" shakiyan samarin kauyen biyu suka tafa hannuwansu suna dariya" Baban yara yace "Ba komai dayyabu ai duk daya ne nima idan kayi tsintuwa ai kana tunawa dani Dayyabu ya koma cikin shagon da sauri" ya bude katuwar randar da yake zuba lemuna a ciki" ya jawo kiras din da babu komai a ciki ya fara tsamo kwalaben lemun daga cikin sabuwar randar dake cike makil da ruwa har wuya" ya rinka shirya kwalaben a cikin kiras din kala-kala bakake da jajeye da shudaye" saida ya cika kowanne gurbi sannan ya kinkimi kires din yayi waje dashi" inda baban yara yake a tsaye yana jiranshi" . "Ai kaga haka yafi baban yara" ince dai kwana zatayi ko bada sauri zata tafi ba? Baban yara ya tarbeshi ya amshi kires din lemun cikin farin ciki" sannan yace dashi "kwana zatayi mana" ta isa tace zata tafi ne" a ina zata kwanta"" na fada maka tsintuwa ce ta fado hannuna a banza" sai yadda nayi da ita" Dayyabu ya fashe da dariyar jin dadi" baban yara yace bari in kai mata lemun sai in dawo akwai Auwalu shima yana can zaizo" shi kuma a bangarensa indomi za'a samu da kwai da shayi Dayyabu yace "yauwa, to ai kaga haka yafi baban yara" shi dama harka irin wannan idan zamuyi ita" to mu rika nuna muma fa mun waye" ai abin duk barazana ce! Ko acan gari suma ba wata tsiya suke kashewa matan ba" duk karya ce" gara mu nuna mata muma wayayyau ne" don kada ta rainamu" . Baban yara yayi dariya" ya juya zai nufi dakinsa ya kaiwa talatu bakuwa kires din lemun wanda ya rikeshi hannu bibbiyu" kafin ya tafi ne dayyabu ya kalli kwalaben dake cike da kires din da kuma makudan kudin da suka lashe" sai ya matsa yace da baban yara cikin sanyin jiki" "to baban yara" dan Allah ka rike amana" ita kadai zata sha" mu hakura zamuyi" idan muka samu tasha ko kwalabe biyu ne" sai mu dawo da sauran idan ta tafi" ba tararwa lemun zamuyi muyi ta sha ba kaga bashi nake amsoshi a gari kuma gobe zanje inyi musu balas in amso wani Baban yara yace dashi "Ai na sani dayyabu" kada ka damu bazan sha maka lemu ba" ita kadai za'a ajiyewa" Dayyabu mai shago ya saki ranshi yauwa to yi sauri ka dawo mu shirya yadda za'ayi Baban yara ya kinkimi kires din lemun ya kai dakinsa ya samu bakuwar a zaune a bakin gado kamar yadda ya barta dazun" da shigarsa yayi murmushi kiyi hakuri" na barki a zaune ke kadai tun daxu ko? tace dashi a sanyaye kamar wacce take mura! ba komai . Baban yara ya ajiye mata kires din a gabanta cikin barazana yace da ita To ga abin sanyaya makoshi fa na kawo maki bana so ki rage mani koda kwalba daya bari in dawo kada dai ki kosa talatu tayi murmushi bata ce dashi komai ba har baban yara ya sake bazama ya fita jikinshi na rawa yazo daidai shagon dayyabu kenan yaci karo da Auwalu mai shayi ya gama hado tasa gudumawar yana dauke da katuwar samira a hannu daya a daya hannun kuma kofin shayi ne da katon biredi guda daya akaiKAZAR KARFI--> 04 . Baban yara da dayyabu suka tarbeshi kowanne ya amshi hannu daya Auwalu yace cikin damuwa ya ake ciki ne tun dazun inata jiranka ka dawo ka dauki indomin mu tafi najika shiru Baban yara yace dashi Na tsaya nan wajen dayyabu ne na amshi lemun nakai mata Auwalu ya kalli dayyabu cikin rashin amincewa da ganinshi tare da baban yara suna maganar bakuwa tare bai so dayyabu ya shigo cikin al'amarin ba Da dayyabu ya fahimci haka a fuskar Auwalu sai yayi saurin cewa Na bada kires din lemu akai mata saboda kada mu nuna mata karanta ta daukemu kauyawa . Jin hakan yasa Auwalu ya saki ranshi don kuwa dama baya so ace shi kadai zaiyi asara su kuma su kwashi gara basu bayar da komai ba duk da haka don dai ya kara ba dayyabu wani aikin sai yace a karshe to za'a kai lemu ne babu biskit dayyabu! ka dauko kwali daya a bude shi a gabanta shima duk karin gada guri ne Dayyabu yace ba matsala bari in dauko Ya sake shiga cikin shagon ya dauko kwalin biskit mai 'ya'ya wanda ba'a budeshi ba daya fito ne yace Bari in kulle shago na muje kada mu barta ita kadai . Ya dauki kwalin biskit din kamar wanda zaije wajen baikon aure" baban yara ya dauki samirar dake cike da indomi da kwai an shimfida a sama" yana ta kwarara kamshi" shi kuma Auwalu ya dauki biredi da shayin suka dugunzuma su ukun suka tafi dakin" Baban yara suka sa gaba tunda shi yasan yarinyar" shi ya jagorancesu suka shiga" talatu tana a zaune kamar wacce aka dasa Baban yara yace yana fara'a to gamu mun shigo Ya ajiye kwanon samirar a kusa da kires din lemun Auwalu ya ajiye mata nasa kofin shayin da biredin" Dayyabu ya ajiye mata kwalin biskit" talatu ta kalli lodin kayan sun cika tsakar dakin kamar wadanda suka fito da kayan lefe a gani" "ta tambaye su" "duk wadannan kuma na menene? Baban yara yace da ita Duk abinci ne" kin san ance yana da kyau ka karrama bakon ka" Ya juya kan abokansa biyu da suka rakoshi" suna zare idanu suna kallon talatu yace da ita wadannan abokai nane sunzo ne su gaisheki suma" talatu tayi murmsuhi" "sannunku malamai" ina wuni?" Dayyabu da Auwalu suka kware baki suka amsa a lokaci guda "lafiya lau" . Suka ci gaba da murmushi ba tare da sun san abinda zasu ce da ita ba" baban yara ya dubi lemun yaga bata dauki ko daya ba" ya tuna baizo da abin bude kwalba ba" yayi saurin daukar kwalba daya yace "Bari a bude maki lemun ki fara dashi" yara sun dauke mani ofiner" bana rabuwa da ofina a dakin nan Yasa hakori ya fara kici-kicin bude lemun da karfi har yana rintse idanu" Dayyabu yace "mancewa nayi" ni kuma dana taho da tawa ofina ta shago" Da kyar baban yara ya bude kyalbar lemun ya taso da karfi ya fito ya jika mashi fuska" yayi saurin ajiye kwalbar yana borin kunya" "Gas yayi yawa a wannan kwalbar shi yasa take da wahalar budewa" ya turawa talatu kwalbar a lokacin ne tace dasu" "to ku dan bani wuri mana inci abincin naku..." tayaya zan iya cin wani abu ku uku kun tsareni da kallo ? . Kamar wadanda suke jiran umarninta tana fadar haka su duka ukun sukayi waje" suka fito suka tsugunna a bakin kofar suka fara yin kus-kus cikin rada suna magana Dayyabu ya fara yiwa baban yara korafi "kana ganin zata bada hadin kai kuwa baban yara ? "Ba matsala dayyabu" Baban yara ya karfafa masa gwiwa Kasan yanzu tana jin yunwa ne" bata ci abinci ba" mu jira taci ta koshi sannan sai mu shiga mu fada mata abinda muke so zata amince" Auwalu mai shayi wanda ya kasa kunne yana sauraron radar da suke yi yace a karshe Nima ina ganin kamar haka- haka take" kada fa kaja muyi wahalar banza baban yara! ya juyo bangaren Auwalu dake a gefensa daga hagu yayi kasa- kasa da muryarsa yace dashi "kada muzo da kosawarmu a fili Auwalu" kasan irin wadannan wayayyun yaran na gari sai anbisu a hankali" ba gaggawa ake musu ba" Suka yi shiru suna jiran talatu ta gama cin abincin" Baban yara ya leka dakin ta hanyar wasu huje-huje dake a jikin tsohuwar kofar tasa" ya sameta a kishingide akan gadon har taci abinda taci ta fara shirin yin barci" yayi saurin juyawa inda sauran abokan nasa suke a zaune sunyi jigum suna jiran tsammani" yace dasu ta hanyar sirri . "ta gama cin abincin" ya za'ayi kenan?" Dayyabu ya mike yace "to kunga dai na fiku bayar da kayayyaki a harkar nan" gaskiya nizan fara shiga" Auwalu ya kwabeshi da sauri kaji kauyancin banza haka kawai zaka shiga sangwam-gwam ba ayi mata bayani ba fa ai sai an dan yi hira tukunna an nuna mata inda aka fuskanta sannan zata yarda" ku kuna abune da jahilci har yanxu Baban yara yace Gaskiya ne Auwalu to kuzo mu shiga muyi mata bayani kada tayi barci naga ta fara gyan-gyadi . Bayan samarinn uku sun gama gudanar da shawarwarinsu a waje sai suka sake shiga cikin dakin su duka suka sami bakuwar a kishingide akan gadon ta dan tsakuri abincin kadan ta kurbi lemun baifi sau biyu ba bata taba shayin da suka ajiye mata ba ballantana kuma dirkeken kwalin biskit din dake jiranta Da taji motsin shigowarsy saita bude idanu ta tashi zaune tayi hamma sannan ta dan bata ranta Barci take ji fa gaskiya Baban yara wanda yake son ya kwantarwa da abokansa biyu hankali don kada su damu yace da bakuwar Haba tun yanxu zakiyi barci ko hira bamu yi ba? Sai a lokacin Auwalu yayi kokarin yin magana Ai bata ci abincin ba ma naga koma yana nan bata taba ba Da yake baya iya yi mata magana baban yara yake yiwa korafin to amma duk da haka sai ta bashi amsa tace dashi kai tsaye . Don kada ma kuce nayi muku wulakanci ne banci ba shiyasa na dan tsakura nagode samarin uku zazzaune a kasa babu ko tabarma suka tasa bakuwar tasu suna kallonta wacce take a hakimce akan gado ita ta fara yi masu magana akwai alamar sun fara isarta tace dasu to naji kunce zakuyi hira wacce iriyar hira kuke so ayi na fada maku barci nake ji A lokacin dayyabu ya dunguri baban yara da kafa yana nuna masa ya fito fili yaya magana ba boye-boye Baban yara ya fara inda-inda yace Eh to kinsan ai idan aka ce miki ga samari da 'yan mata dole ayi hira ayi soyayya koba haka bane? talatu tace Gaskiya kuwa haka ne baban yara yaci gaba da cewa yauwa, to dama haka nake nufi" amma dai ina jin ga Auwalu yana da magana" bari kiji komai a bakinsa" Auwalu yi mata bayani" Auwalu mai shayi ya gyara zama yadan sosa kai yace "Eh..ai duk abinda ka fada baban yara ba kuskure daman dai shi komai na rayuwa ance taimakeni in taimakeka.. Ko ba gaskiya ba?" to amma ga dayyabu bari yayi maki bayanin abinda ya kamata Dayyabu kayi magana . Auwalu da baban yara suka dubi dayyabu wanda baiyi tsammanin shi zasu dorawa wannan nauyin ba" ya fara dabircewa ya ce "to...ai kun gama magana" mudai soyayya ce ta hadamu dake" kuma yadda muka fara da mutunci" to bazamu kare da rashin mutunci ba" Rayuwa juyi- juyi ce... Duk wannan abu da kikaji muna fadi maki to soyayya ce" mun san ke wayayyiya ce" kin gane abinda muke nufi" talatu ta yatsine fuskarta kamar zata yi kuka "Nifa malamai gaskiya ban fahimci abinda kuke nufi ba" kunki fitowa ku fada min magana sai kewaye-kewaye kuke tayi mani" ina ga da zaku fito ku fada mani abinda kuke nufi gaskiya zaifi" samarin kauyen uku suka kalli juna Auwalu tace Baban yara kayi magana mana" ya zatayi mana haka? Baban yara ya juya ya kalli dayyabu yace" Dayyabu ka sake yi mata bayani yadda zata gane Dayyabu ya kalli talatu ya tambayeta yanzu ke malama duk wannan maganar da muke yi baki gane inda muka dosa ba" baki fahimcemu ba" talatu ta girgixa kai tace Gaskiya ni ban gane ba . Auwalu yayi karfin hali yace da ita" Amma dai ai kin san Hausawa sunce ita rayuwa ka taimakeni ne in taimake ka! talatu tace cikin fushi-fushi "Eh, tun dazu ai kuke ta fadar haka" to me kuke nufi da taimakeni in taimakeka? gani nayi baku sanni ba" nima ban sanku ba" sai yau muka hadu" to kun bani wajen kwana" gashi har na kwanta" kun kawo mani abinci naci" to me kuke so kuma inyi maku" sai ku fito ku fadi gaskiya" na gaji da wannan dogon turancin" barci nakeji" in zakuyi magana kuyi magana" in bazaku yi magana ba" don Allah ku tashi ku fita barci zanyi" zan kulle kofa Samarin uku suka sake kallon juna kowa yana tsammanin dan uwansa zaiyi magana da bakuwar tasa suna ta bata mata lokaci sai zare idanu suke yi saita tashi daga kan gadon ta tsaya kansu tace ku dan fita in rufe kofar.... Sai da safenku" su duka ukun suka tashi jiki babu kwari suka fice daga dakin" suna fita ta turo kofar ta kulle tasa sakata" suna ji suna gani . Rufe kofar keda wuya suka fara yiwa juna banbami kamar zasu bugi in buga" Dayyabu wanda a fusace yace "Duk abinda ya faru laifinku ne" ku fito kuyi mata bayani kuce ga abinda muke so" amma kowa yayi shiru" kun barni sai ni kadai nake ta magana Kuma sai wani abu ya taso kuce ku wayayyu ne" haka ake wayewar? ance kuyi mata bayani yadda zata gane kunki Auwalu ya karba da cewa duk wa yayi mata maganar bani bane? Nine fa nace mata mun taimaketa ya kamata muma ta taimakemu kuna ji kukayi shiru baku yi karin bayani ba Gaskiya kun cucemu kawai asan abinda za'ayi ni bazan yarda ba . Baban yara yace Ni ai na gama nawa tunda nina ganta na daukota nazo da ita kuya kamata kuyi mata magana dalla-dalla harta fahimci ga halin da ake ciki amma kuna abu kamar kuna jin tsoro Har yanxu wallahi baku waye ba Dayyabu ya sake duban sauran abokanansa Wai kuna jin da gaske bata gane abinda muke nufi ba Ni ina ganin fa kamar so takeyi ta raina mana hankali . . .KAZAR KARFI--> 05 . Matar tace dashi "ka ga dari biyu nan akan kabet" to wallahi ita kenan dani" ita din ma kudin adashi ne ban riga na aika ba Baban yara sai dai kayi hankuri da ita" ta miko masa" ya amsa cikin sanyin jiki" saurayin dan kimanin shekaru ashirin da uku" gwani ne wajen kure kai indai akan mace ne Yace da ita Bani samira inje in hado masa abinci Hada min kofikan zuba lemo ta dauko masa samira a cikin dakinta a sama ta hado da cokali da kofikan zuba lemo biyu" har zai fita sai ya sake tuno wani abin "Dan taimaka mini da mafici da rikoda Da yake ta saba da irin wannan are-aren kayan sai ta dauko masa rikoda da maficin" Ban daiyi zubi ba batiran sunyi sanyi sai ka sayi sababbi Baban yara ya fice ba tare da ya tsaya sauraron shawararta ba ya koma dakinsa dake kofar gida ya kaiwa talatu maficin ya ajiye rikodar a kusa da ita ya ce "wani shashashan kani gareni zuwa yake yi yana daukar mini kaya yana shiga dasu cikin gida" baya dawo min dasu sai naje na dauko da kaina na rasa inda ya kai mani bidiyona da janareton da nake tayarwa yana ba dakina wuta har fankata ma ban san inda ya kaita ba . Baban yara yayi tsaki" talatu tayi murmushi a karo na farko tace "Ai ba komae ko haka ma ya isa ta daga kanta ta duba ko ina a cikin dakin bata ga inda turken kwan lantarki yake ba babu kuma wani soket a jikin bango" babu wuta a garin" bata san yadda wannan saurayi yake ba dakin nasa wuta da janareta ba tare da waya ba Bata yi masa bayani ba ko tambaya a game da haka ta barshi ya tafi dauke da katon kwanon da zaije sayo mata abinci" Ya isa dandalin garin inda masu abinci da masu sayar da shayi da kwai suke da rumfuna" ga jama'a nan a zazzaune a ko ina akan benci" samari da kuma matasan dattawa" Baban yara ya sami daya daga cikin masu sayar da shayin da kuma indomi" ya kebeshi don kada mutane suji bayanin da yazo yayi kafin ya sayi abinda yake so" su koma bayan rumfar" Da zuwansu baban yara ya mika masa dari biyun yace dashi "ka gane Auwalu wata bakuwa nayi yanzu-yanzun nan to ina son ka hadani sosai dari biyun nan kawai gareni" ka hada mani indomi guda biyu ka soya kwai biyar ka hada mani shayi dabam a kofi ka zuba madara gwangwani daya muji nawa ka biyoni gobe zan baka kudinka... Ba wasa Auwalu" . "Dan siririn mai shayin mai kama da karas" ya washe baki da zumudi yace da baban yara "to kai irin wannan idan ta samu ai muma ya kamata ku rika tunawa damu baban yara a ina ka samota ? Baban yara yace a banza na ganta dazu a bakin gari ina jin bakuwar gilli ce tazo bata sami daki ba" Auwalu mai shayi yace "A to gaskiya nima ina ciki baban yara" bari in hada mata komai da komai muje sai in bar yaro ya tsare min shagon kafin mu dawo Baban yara yaba Auwalu mai shayi hannu suka tafa faa!!" sukayi dariya" "kai mutumin nan" ashe kaima baka barin banza ta wuce ka? "Ina fa zan bari baban yara ? Auwalu mai shayi ya koma cikin rumfar ya fasa kwayaye yana kadawa" yasa yaronshi ya dora taliya a wuta baban yara ya zauna a benci yana jiranshi ya gama su tafi" Akwai alamar yaji dadin wannan hadin gwiwa da Auwalu mai shayi ya nemi su yi Dama bashi da kudi dari biyu ne da yazo da ita ta huta itama to amma akwai bukatar ace sun sayi lemun kwalba ya mance ashe da sauran cefane gashi kuma Auwalu baya sayar da lemo" to amma tunda dayyabu mai shago yana dashi" bari yaje su shawota Yace da Auwalu" "kafin ka gama hada indomin da kwan" bari inje wajen dayyabu in sayo lemu in dawo" Auwalu yace dashi "to, kayi sauri fa" ba dadewa zan gama" . Baban yara ya nufi shagon wani abokinsa mai katon kai kamar dan ruwa" wanda baya son fitar kudi a hannunsa" kuma ba karamin kunyar mutum zaiji ya bashi bashin kaya ba" Amma da yake shima ba mutumin arziki bane" Idan aka zo masa da zancen bakuwa bata da gurin kwana yakan yi rawar jikin zuba nasa hannun jarin akai mata Baban yara ya sanarwa dayyabu yana son lemo kwalba biyar manya" amma fa zai lamunce shi cikon kudin sai gobe" Dayyabu dake cikin shagon yana sauraron baban yara" ya mirgina katon kansa cikin rashin amincewa" "Gaskiya kayi hakuri baban yara" saboda ina son zanje sayayya ne gobe" kudin nake ta faman hadawa basu gama haduwa ba ma" lemun nan bazai samu ba gaskiya" Baban yara ya rokeshi a karo na biyu" "duka nawa zaka biyoni ? ina da dari biyu a hannuna gata" baifi ka bini dari da hamsin ba dayyabu" saurayin ya sake mirgina katon kansa" Tab! Dari da hamsin?" ya fada cikin jimamin yawan kudin" . "Gaskiya baxan iya ba baban yara" duka nawa muke cin riba a sana'ar ? kasan tireda fa ba wani riba gareta ba" yanzu kaga biskit sai ka sayar da kwali daya baifi ka sami naira ashirin ba sai in wuni anan banci dari da hamsin din ba" sai ai ta ganin mutum wasu kudi yake samu kuma duk abin hakuri ake yi Dayyabu yayi tsaki . 06 LOADING....... KAZAR KARFI--> 06 . . Dayyabu yayi tsaki don kuwa har ya tuno da lissafin da yayi dazu da safe na wasu kudi yana zaton zaiga dubu uku yaga dubu biyu da dari shida baisan abinda yaci dari hudun ba yau wuni yayi yana fada da kwastomominsa akan fushin wadannan kudi da ya rasa inda suka makale Ga kuma wannan baban yara ya wani zo wai a bashi bashin lemu bazai yiwu ba gaskiya! Da baban yara ya tabbatar bazai samu bashin lemu a wajen dayyabu mai shago ba sai ya koma gefe yayi kamar zai tafi ya fara sake-sake a xuciyarsa yana magana yana cewa a baiyane kamata yayi kawai in sayi kwalba uku in hankura ai sun isheta dama dai zai danfi dacewa ne taga anzo da kwalaben lemun da yawa babu harkar karanta . Da Dayyabu mai shago yaji baban yara yana maganar ashe wata bakuwa zai kaiwa lemun sai ya daga murya daga cikin shagon ya tambayeshi kunyi bakuwa ne baban yara? ya bashi amsa sau daya a takaice Eh sanna ya koma kan lissafin da yake yi da hannu Dayyabu ya sake tambayarsa cikin kosawa yar uwarku ce tazo ko kuwa dai tsintuwa ce Baban yara? wata tsintuwa ce nayi dayyabu yace da mai shagon Dayyabu yayi saurin fitowa daga dan tsukin shagon nasa da yafi kama da dakin tantabaru ya saki ranshi ya fara fara'a har zuwa lokacin da yazo ya tsaya a inda baban yara yake yace dashi to ai kai baban yara ai gayamun abinda ake ciki zakayi tunda wuri ban san bakuwa kayi ba ai da babu abinda zai gagara bari in debo lemun kwalba nawa kake ganin ya kamata akai mata a wadace? . Baban yara wanda yayi mamakin yadda dayyabu mayen kudi ya canza ra'ayi lokaci kankani yace dashi Dama kwalba biyar nake so a kai mata" ko dai bazata shanye su duka ba ai kaga anyi mata burga Dayyabu yayi farat yace dashi" "kwalba biyar din me kuma?" ai irin wannan kiras daya ake kaiwa a ajiye baban yara" tasha-tasha har ta gaji" idan ta tafi sai a dawo da ragowar ko nawa ta rage" bari in shiga in hado kiras daya akai mata" kaga sai muje tare koya ka gani?" shakiyan samarin kauyen biyu suka tafa hannuwansu suna dariya" Baban yara yace "Ba komai dayyabu ai duk daya ne nima idan kayi tsintuwa ai kana tunawa dani Dayyabu ya koma cikin shagon da sauri" ya bude katuwar randar da yake zuba lemuna a ciki" ya jawo kiras din da babu komai a ciki ya fara tsamo kwalaben lemun daga cikin sabuwar randar dake cike makil da ruwa har wuya" ya rinka shirya kwalaben a cikin kiras din kala-kala bakake da jajeye da shudaye" saida ya cika kowanne gurbi sannan ya kinkimi kires din yayi waje dashi" inda baban yara yake a tsaye yana jiranshi" . "Ai kaga haka yafi baban yara" ince dai kwana zatayi ko bada sauri zata tafi ba? Baban yara ya tarbeshi ya amshi kires din lemun cikin farin ciki" sannan yace dashi "kwana zatayi mana" ta isa tace zata tafi ne" a ina zata kwanta"" na fada maka tsintuwa ce ta fado hannuna a banza" sai yadda nayi da ita" Dayyabu ya fashe da dariyar jin dadi" baban yara yace bari in kai mata lemun sai in dawo akwai Auwalu shima yana can zaizo" shi kuma a bangarensa indomi za'a samu da kwai da shayi Dayyabu yace "yauwa, to ai kaga haka yafi baban yara" shi dama harka irin wannan idan zamuyi ita" to mu rika nuna muma fa mun waye" ai abin duk barazana ce! Ko acan gari suma ba wata tsiya suke kashewa matan ba" duk karya ce" gara mu nuna mata muma wayayyau ne" don kada ta rainamu" . Baban yara yayi dariya" ya juya zai nufi dakinsa ya kaiwa talatu bakuwa kires din lemun wanda ya rikeshi hannu bibbiyu" kafin ya tafi ne dayyabu ya kalli kwalaben dake cike da kires din da kuma makudan kudin da suka lashe" sai ya matsa yace da baban yara cikin sanyin jiki" "to baban yara" dan Allah ka rike amana" ita kadai zata sha" mu hakura zamuyi" idan muka samu tasha ko kwalabe biyu ne" sai mu dawo da sauran idan ta tafi" ba tararwa lemun zamuyi muyi ta sha ba kaga bashi nake amsoshi a gari kuma gobe zanje inyi musu balas in amso wani Baban yara yace dashi "Ai na sani dayyabu" kada ka damu bazan sha maka lemu ba" ita kadai za'a ajiyewa" Dayyabu mai shago ya saki ranshi yauwa to yi sauri ka dawo mu shirya yadda za'ayi Baban yara ya kinkimi kires din lemun ya kai dakinsa ya samu bakuwar a zaune a bakin gado kamar yadda ya barta dazun" da shigarsa yayi murmushi kiyi hakuri" na barki a zaune ke kadai tun daxu ko? tace dashi a sanyaye kamar wacce take mura! ba komai . Baban yara ya ajiye mata kires din a gabanta cikin barazana yace da ita To ga abin sanyaya makoshi fa na kawo maki bana so ki rage mani koda kwalba daya bari in dawo kada dai ki kosa talatu tayi murmushi bata ce dashi komai ba har baban yara ya sake bazama ya fita jikinshi na rawa yazo daidai shagon dayyabu kenan yaci karo da Auwalu mai shayi ya gama hado tasa gudumawar yana dauke da katuwar samira a hannu daya a daya hannun kuma kofin shayi ne da katon biredi guda daya akai . KOWA DA IRIN GUDUNMWARSA KENAN A HARKAR BARIKI ? . (c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 07 . . Baban yara da dayyabu suka tarbeshi kowanne ya amshi hannu daya Auwalu yace cikin damuwa ya ake ciki ne tun dazun inata jiranka ka dawo ka dauki indomin mu tafi najika shiru Baban yara yace dashi Na tsaya nan wajen dayyabu ne na amshi lemun nakai mata Auwalu ya kalli dayyabu cikin rashin amincewa da ganinshi tare da baban yara suna maganar bakuwa tare bai so dayyabu ya shigo cikin al'amarin ba Da dayyabu ya fahimci haka a fuskar Auwalu sai yayi saurin cewa Na bada kires din lemu akai mata saboda kada mu nuna mata karanta ta daukemu kauyawa . Jin hakan yasa Auwalu ya saki ranshi don kuwa dama baya so ace shi kadai zaiyi asara su kuma su kwashi gara basu bayar da komai ba duk da haka don dai ya kara ba dayyabu wani aikin sai yace

Chapter 2 of 6