Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels KAZAR KARFI--> 01 . SHAFI'U DAUDA GIWA . AMADU BALIGI" shine shugaban matasan dake tashar dan amarya" tun a shekarun baya kafin siyasa ta kankama shine saurayin dake fada aji a hanyoyi da dama Alal misali Idan aikin gayya ta taso za'a gyara hanyoyin kauyensu a fitar da magudanan ruwa Amadu baligi shine akan gaba wajen gayyato matasa da karuwai ako ina da kuma nemo makada wadanda zasu dinga gabzar ganguna suna karawa ma'aikatan kwarin gwiwar kartar kasa suna ihu da kirari . Idan kaka tayi aka kawar da amfanin gona aka kawo gida Amadu baligi shine yake fita ya nemo mawaka da 'yan rawa suzo kauyensu su kafa dandali a wani gidan danni wanda idan dare yayi aka tayar da karamin jannareto aka fara waka da cashewa samarin dake lardina na nesa dana kusa sukan zo su biya kudi su shiga suyi kallo da lika kudi kuma idan aka gama waka da safe komai aka samu Amadu baligi yake tarawa ya sallami mawakin da yaransa" sannan sauran abinda ya ragu kuma nasa ne Idan mutane suka fara gajiya da wake-wake sai Amadu baligi ya kafa gidan dambe ko kokawa wanda anfi samun alkairi don kuwa masu kudin kauyen sukan sa gasar babura da shanu gaduk jarumin da yayi kisa mai kyau" kuma kome aka samu ta hannun Amadu baligi yake biyowa" . Sanin kowa ne cewar duk wata sabuwar karuwar da tazo tashar dan amarya" dole ne Amadu baligi yasan da zuwanta" a matsayinsa na shugaban matasa" ko kuma shugaban 'yan iska" kamar yadda dattawan dake da mutunci a kauyen suke kiransa" . Amadu baligi gwani ne shi kanshi wajen dambe da kokawa" yasha fita wasa har xuwa jamhuriyar nijar kuma yayi kaye da kisa ba sau daya ko sau biyu ba" Ganin yafi samun alheri a gida wajen jagorancin duk wani aikin tabara ya sashi ya kwance wa hannu sa damara ya dawo yana shugabantar matasa duk abinda yace shi akeyi a kauyen" . "To amma tun sanda siyasa ta kankama sai Amadu baligi ya fara samun fada a wajen shugabannin kauyukka musamman ciyamomi da kansiloli Idan shugaba yazo kamfen dole ya fara neman Amadu baligi don kuwa shine muryar matasa Idan akayi nasara aka kafa gwamnati" Amadu baligi yana samun alheri" don kuwa yana samun kyautar kudi da sabbin babura akai-akai wasu suna cewa duk wata yana samun kudi a wajen 'yan siyasa fiye da naira dubu dari da hamsin mutane idan sukaji haka zasuyi zaton duk a fadin lardin tashar dan amarya babu wani matashi mai kudin Amadu baligi to amma a zahiri abin ba haka yake ba don kuwa sau da yawa sutura takan yankewa saurayin kuma yasha kwana bashi da ko anini saiya roki na karin kumallo a wajen mutane . Tayaya kuwa kudi zasu zaunawa Amadu baligi bayan kullum idan ya zauna a tamfal din caca tun safe baya tashi sai dare yayi" su kunna fitila karuwansa shida a garin" kuma kowacce saiya bata kudin cefane kullum tunda dai ya hanasu mu'amala da kowanni namiji shiyasa kudi basa rayuwa a hannunsa kamar yadda wuta bata rayuwa cikin ruwa . Amadu ya samo sunansa na BALIGI ne tun yana yaro dan shekara sha biyu" wannan ya samo asali ne a zamanin da yke shiga cikin manyan kartin dake zuwa kamun gafiya a kauyen wadanda basa yadda yara suna binsu sai Baligai tsararrakinsu" . Babu irin dukan da Amadu baisha ba a wajen azzaluman kartin kauyen wadanda suke korarshi ya koma gida idan ya biyo su shi kuma yana sake binsu A ranar da wani a cikinsu yace dashi basa zuwa kamun gafiya tare da yara sai "BALIGAI" sai Amadu yace dashi- "Nima ai "BALIGI" Ne! Fadar hakan ya bawa kowa dariya a cikin kartin kuma tun daga lokacin suka 'yantashi ya rika binsu din kamun gafiya yana yi msu kananan aikace-aikace" dangin debo ruwa a rafi da kuma iza wutar gasa nama idan sunyi sa'ar kama abubuwan da suka fita nema a ramukan da ke a bayan garin Kamar yadda kowanne mutum a duniya yake da ka'idojin aikinsa ko sana'arsa haka shima Amadu baligi yana da tasa dokar wacce ta dade takai shekara da shekaru a kauyensu babu wanda ya isa ya karyata ko kuma ba'a riga an samu wanda zai karyata ba har yanxu" . Dokar ita ce yana maraba da duk wata karuwa wacce ta sauka a garin komai tsufanta da muninta" kamar yadda yasha fada" Amma bai yarda wata "GILLI" tazo ta zauna ba kuma bai yarda wani yazo da ita garin ya ajiyeta ba" . Sau da yawa wadanda basa cikin harkar bariki dole ne sai nayi musu dogon bayani kafin su iya bambance tsakanin "KARUWA" da "GILLI" . KARUWAI-: Sune wadanda suke fitowa yawon dandi bayan sun taba yin aure sun fito" . GILLI-: Bata taba yin aure ba" yawancinsu yara ne kanana wadanda shekarunsu ya kama daga goma sha hudu zuwa sha biyar" wadanda suke kangarewa su fito shalli da sharholiya" sune yawanci akan samu a rabe tare da iyayen dakin su mata agidan karuwai saboda idonsu bai riga ya bude sun san yadda rayuwar bariki take ba da yadda ake samun kudi a wajen maza ba . Sune yawanci suke bin mawaka sunayi musu rawa" 'yan kallo suna manna musu kudi a goshi Idan an tashi wasa a kawo kudin abinci a basu su kama gabansu ba tare da sun tsaya tunanin ko nawa mawakin ya samu a dalilinsu ba su dai ko ina dare yayi musu nan ne gidan su kuma anan zasu kwana kamar kajin turawa ne Idan mai kula dasu ya mutu kowa nasu ne indai zai basu abinci ya faranta musu rai . Sune wadanda yarintar soyayyar gida bata gama sakinsu ba ko mutum bashi da kudi sai su like mishi wani kuma yazo da kudi su zageshi ta uwa da uba irin wannan rashin hankali da rashin sanin mutuncin sana'a yake yawan hadasu fada da manyan karuwan dake rike dasu wadanda suke basu wurin zama idan kaje gidan mata kaga karuwa ta kama gilli tana lakada mata duka kamar zata kasheta" Ko kuma kaga ta debo kayanta ta watso mata su waje tana zaginta to karka tsaya wahalar tambayar kowa yadda akayi don kuwa dalilin bai wuce kuruciyar da gillolin suke yi ba wajen rashin ba masu kudi hadin kai suna bin yara kanana wadanda basu da komai sai kodadden wando da fasashen takalmi" . "To amma shi a bangaren Amadu baligi ba rashin hankali ko yarintar gilla yasa baya son su zo kasarsa ba" haka kawai yaji baya so yaga karamar yarinya ta fito dandi duk da lalacewarsa baya so yaga yara sun lalace" su dai manya tunda sun riga sun gama lalacewa to gwara abin ya tsaya a kansu amma banda yara" Amadu baligi kakkarfa ne baki kuma mummuna wanda ko a jajayen idanunsa kawai aka tsaya ya isa ya tsorata duk wata mace tabi umarninsa indai tana so ta zauna lafiya a kasarsa bai taba rabuwa da singileti ba da ita yake kwana da ita yake tashi kuma komai sanyi komai zafi "To ko a lokacin da akayi bikinsa a watannin baya tun ranar daurin auren har zuwa tashin bikin da singileti ya gama angwancinsa ya shiga dakin amaryarsa ba abinda ya dameshi" . Ana kan haka ne a yammacin wata ranar lahadi yaje 'yar bajau suna caca shi da mutanensa" wani yaronsa mai suna "DAMMA" yazo ya sameshi yace dashi "Sarki kayi bakuwa fa a kasarka" Amadu baligi ya tambayeshi yana kallon kartar dake a hannunsa ba tare da ya dago kanshi ba" "wacece?" Damma yayi murmushin takadarancin abinda zai fa" wata GILLI ce" ina jin ba'a dade da yayeta a nono ba" Amadi baligi ya dago kanshi ya kalli Damma yace dashi" "kaje kace da ita ni sarki nace ta gaggauta barin kasata tun kafin inzo in sameta" kace da ita ta koma gida tun kafin muyi ido biyu" "Damma ya koma ba'a jima ba ya dawo wajen cacar yace da Amadu baligi sarki tace wai ba inda zataje ko kasheta za'ayi tun kafin Damma yakai karshe Amadu baligi ya watsar da kartar dake a hannunsa ya tashi cikin sauri" "muje inga kowacce 'yar iskar yarinya ce wannan" Damma ya takewa sarki baligi baya suka nufi gidan karuwan dake gefen garin nesa kadan da gidajen matan aure" . *SUNANTA TALATU* Sekarunta zasu iya zama kodai tsakanin goma sha hudu zuwa goma sha shida" tana sanye da kodaddiyar atamfa mai ruwan toka" wacce zaninta yasha yagewa anayi masa faci daga kasa" Gajeriya ce" dirarra mai nagari wacce kai tsaye bazai yiwu mutum ya yanke hukuncin fara ya cancanta a kirata ko kuma baka ba A yanayin fatarta fara ce" to amma wani abu da ya lullube fatarta dake kama da rashin kwanciyar hankali da yunwa shiya dabirta sakamakon da mutum zai iya bata a kamaninta to koma dai me yake damunta bazai yiwu ace da ita mummuna ce ba ko ba komai tana da faffadar fuska wacce ke dauke da manyan idanu da kuma dan madaidaicin bakinta" tana da saurin fara'a da murmushi bazata iya jure hada ido da mutum tsawon dakika uku ba ba tare data fara yi masa murmushi ba koda kuwa bata taba ganin mutum ba tana dauke da leda gari yayi zapi" kuma ganin yadda ledar ta koshi fal kamar xata yage xa'a fahimci kayanta ta zubo a ciki" suturu da kuma 'yan abubuwan da baza'a rasa ba" koda kuwa mudubi ne da hoda" . "Tun shigowarta garin da dan acaba ya kawota gidan matan" saita sami gefe guda tayi tsaye bata yiwa kowa magana ba" tana kallon duk abubuwan dake kaiwa da komowa babu wacce ta kalleta sau biyu a cikin tsofaffin karuwan dake a gidan" don kuwa sun san kowacece da ganinta GILLI ce kuma ba zama zatayi ba" sunsan da SARKI BALIGI yayi ido biyu da ita zai koreta tabar garin kota shirya kobata shirya ba" Jefi-jefi mazan da basu nema da mace a gidan sukanje inda take suyi mata magana" amma bata saki jiki da kowa ba" to dama dai a haka suke zuwa da dan kullin kayansu suyi shiru ayita magana suna ji su wuni a zaune a waje daya suna jin kunyar magana da kowa" da an basu kwana uku zasu goge su zama 'yan gari" wanda ya tafi ya barsu a haka da sati ya zagayo inyazo zai samesu suna shan taba suna rawa" don kuwa suna tare da manyan shaidanu wadanda zasu bude musu idanu su nuna musu bambancin rayuwar gida da kuma RAYUWAR BARIKI . TALATU...KAZAR KARFI--> 02 . TALATU tayi shiru taki magana wannan bashi ne zaisa ace bazata shiga layi ba Da haka suke farawa su dukkansu sai sun gama ganin tafiyar ruwan kowa daya bayan daya sannan zasu fara yin tasu carar suma talatu tana nan tsaye a jikin katangar gidan karuwan inda bai gama rushewa ba ta sauyawa ledar hannun kenan daga dama zuwa hagu saiga Amadu baligi ya shigo gidan a fusace tare da Damma . Da shigowarsa gidan ya dubi talatu tana tsaye dauke da ledarta suka hada ido da ita dashi tayi masa murmushi don kuwa halinta ne dazun nan da Damma yazo yace ta gudu kafin sarki ya ganta tace bazata tafi ba don haka yanzu ga sarkin yazo ya sameta Bayan sun gama kallon juna ita da Baligi ba tare da jin tsoron jajayen idanunsa ba da kuma bakar fuskarsa wacce ke cike da gargada da kwazazzaban duka a wajen dambe sai yace da ita. "ke bakiji sakona bane?" talatu tace dashi cikin ladabi" "wannan ya fada mini" talatu tace dashi" "Indai bazaku barni in zauna anan garin ba gwara ku kasheni in huta da bakin cikin da ya sameni" . Maimakon baligi yaji tausayinta sai yayi dariya kadan ya girgiza kai" irin wannan tatsuniyar daba bakin sabbin shigowa ya dade yana jin irinsu" to amma karya suke yi" su dukansu babu wacce zata so a tambayeta ta fadi gaskiyar abinda ya fito da ita ta baro gida" komai zasu fada idan aka bincika za'a samu ba gaskiya bane" wata zatazo tace iyayenta ne suka mutu" marainiya ce babu wanda yake kulawa da ita don dai aji tausayinta a amsheta a bata wajen zama" Wata zatace mijinta ne ya saketa" kuma yake nemanta zai kasheta" don haka tazo don buyar masa" wata zatace auren dole za'ayi mata kuma bata son wanda za'a bata shiyasa ta gudu to amma fa zaiyi wahala idan aka bincika labarin ya zama gaskiya shiyasa ga wanda ya saba da ganinsu indai bakuwar karuwa ce ko "GILLI" komai zasu fada ba abin yadda bane kuma wanda ya tsaya bata lokacinsa akansu ya tausaya musu shine babban shashasha a wajensu . Baligi ya kebe yarinyar a gepe guda ya bar Damma a baya suka koma kusa da wani sabon daki da ake ginawa a gidan wanda ya ruguje a kwanakin baya" Daga inda suke tsaye a faffadan gidan suna iya jin komai na surutan da wasu karuwai hudu suke yi tare da wani mai tsire a tire wanda ya saba zuwa gidan talla kullum" . "Talatu ta mayar da hankalinta akan hayaniyar da matan sukeyi da mai tsiren" tana so tayi murmushi ga alama rayuwar matan yana birgeta" ganin yadda suke da 'yancin yin komai babu mai hanasu" A lokacin da take kallon nasu ne Amadu baligi ya fara yi mata magana" "Ina so ki bude kunnenki da kyau" kiji abinda zan fada maki" Ya kara kausasa muryarsa da yaga kamar bashi take saurare ba" "Sunana Amadu Baligi" Yace da ita "Nasan wata kila kin taba jin labarina a garinku To idan ma baki taba ji ba yanzun nan zan fada maki don kisan koni wanene!" Nine shugaban duk wani takadari dake a wannan gari namu" An bani wannan sarautar kuma na Amsheta da hannu bibbiyu" Baligi ya saurara" sannan yace da yarinyar "Nasan abinda ya kawoki wannan garin" bana bukatar saikin fada min komai" to amma abinda nakeso dake shine" ki koma gida wajen iyayenki ki rokesu gafara su yafe miki... Zaman bariki ba zaman arxiki bane" muma da kika ganmu nan a ciki don kawai abin ya zame mana bala'i ne" amma ba dadi muke ji ba don haka kiyi sauri ki koma yanzu-yanzun nan tun kafin dare yayi miki" banason ganinki anan! "Talatu ta juya tana sauraron kalaman wannan kato wanda batasan koshi wanene ba a gidan" Amma dai da ganin yadda kowa yake tsoronsa ga alama shine sarki kamar yadda ya fada" batayi masa magana ba tadai girgiza kanta sau daya alamar ta gamsu da bayaninshi . "Duk wadannan matan da kike gani anan indai zaki tambayesu su fada maki gaskiya" na tabbata wannan magana dana fada maki irinta suma zamu fada miki duk lokacin da mace ta gudu tabar iyayenta cikin fushi da takaici" to duk inda zata shiga a duniya" kuma kome zata zama bazata taba gamawa da duniya lafiya ba idan kuma kina jin karya nake yi kiyi tunani a zuciyarki ki gani" wacce mace ce ta taba yin yawon dandi da sharholiya tayi karshe mai kyau ? Indai ba dainawa tayi ta zama mutuniyar kirki ba tayi aure toki zura mara ido kina nan zaki ga yadda karshenta zaizo a wulakance kada kiyi la'akari da yadda manyan karuwai suke gina gidaje suke shiga manyan motoci suke dinka suturun kece raini suna kashe kudi kiyi zaton zasu dauwama a haka bazasu taba dauwama ba wahalar da suke gudu har suka zabi yin karuwanci tana nan biye da su kuma komai dadewa indai suna a cikin harkar sai sun wulakanta wannan dole ne muda muke cikin wannan harka mun san illolinta ciki da waje shiyasa nake fada miki don ke ma ki sani ki koma garinku tun kafin ma ki fara har wani ya bata ki a banza TO" akwai alamar taurin kai a muryarta a karshe Amadu baligi yace da ita "kada kiyi tunanin idan kinki komawa gida kin canza gari bazan sani ba duk inda kika shiga a fadin kasar nan indai yawon dandi zakiyi dole ne in sami labarinki kuma ko ina kika shiga saina biki na kamaki saboda haka ki koma gida ni SARKI BALIGI na haramta miki dandi a duniya kuma dole ne kibi Umarnina ko kina so ko bakya so . Bayan Amadu baligi ya gama jan kunnen talatu sai ya tambayeta "Kina da kudin motar komawa garinku ? ta girgiza kai ba tare da tayi magana ba alamar bata da kudin mota A wanne gari kike ? talatu tace a sanyaye A Tsaunin Yalwa . Shugaban matasa uban baligai ya ciro kudi a aljihunsa ya bata naira dari biyar takarda daya ki hau babur da mota ki koma gida kada ki sake fitowa kome iyayenki zasu miki kiyi hakuri kada ki sake guduwa zamanki a gida komai wuya yafi fitowa dandi Amadu baligi ya tafi ya barta tana tsaye tana wasi-wasi dauke da ledarta gari yayi zafi ya samu Damma yana jiranshi a kusa da kofar gidan wacce ta fadi tuntuni" komai dare idan mutum yazo gidan zai iya shigowa ba doka" babu birki" "Nayi mata fada" zata koma garinsu yanzun nan Damma" na bata kudin mota . Damma yace- "Allah ya taimaki Uban Baligai" karatan biyu suka fice daga gidan karuwan" suka kama hanyar komawa dandalin cacar" suna tafiya suna hira" talatu tana nan a tsaye tana kallon karuwan" har zuwa lokacin da wata takadara ta daukarwa mai tsiren dogon tsinke biyu" ta ruga aguje ya bita yana kiranta ta dawo masa da tsirensa bazai bata shi ba" Karuwar ta shige dakinta ta turo kofa ta kulle mai tsiren ya danna kofar da karfinsa da yaga taki budewa sai ya dawo yana korafi kamar zai fashe da kuka A karo na farko talatu bakuwa tayi dariya tun zuwanta garin . Duk wannan abu da yake faruwa Amadu baligi da yaransa basu sake waiwayar bakuwar yarinyar ba har dare yayi" zuwa karfe goma Amadu baligi yana tsugunne a wajen cacar da suke wuni suna yi" yayi zufa sharkaf" yana jiran kartagi yasa mashi fare ko zuwa daya ne" tunda dai an cinye dubu ashirin din da ya tashi dasu a wannan rana" kuma kuma ko a gida bai ajiye komai ba Yana cikin wannan fushin ne" Damma yazo ya tsuguna kusa da shugaban baligai yace dashi cikin damuwa!" "Sarki yarinyar nan fa tana nan a garin bata tafi ba" Ance an ganta da Baban yara ya dauketa ya kaita dakinsa zata kwana a can Amadu uban Balaigai yayi shiru kamar abin bai dameshi ba" to amma a xuciyarsa tuni har ya fara tunanin irin dukan kawo wukar da zaiyi mata . BABI NA BIYU "DA karfe takwas Baban yara ya hadu da talatu dauke da kayanta a bakin garin da ganinta yafahimci 'yar hannu ce" Baiwar Allah ya akayi ne..... Ina zuwa ne ? talatu tace dashi "Ni bakuwa ce" ina neman wajen kwana ne Bban yara yace Kin samu zo muje ya tayar da babur dinsa yace "Hau mu tafi talatu ta haye babur din" wani tsohon (jingchen) ne" wanda in ba saurarawa mutum yayi da kyau ba" sai yayi zaton injin nika aka tayar a kusa da wajen Baban yara ya murza ya tafi da talatu zuwa dakinsa" Da zuwansu ya bude dakin yayi sauri ya shiga ya kunna fitilar kwai kafin talatu ta shigo ne yayi saurin gyara shimfidar dake akan gadonsa na karfe wanda ke dakon wata mukekiyar katifar ciyawa yar sale . Shigo mana ya kika tsaya a waje ? ya bata umarni yana dariya" akwai alamar yayi farin cikin wannan tsuntuwa da yayi don kuwa indai bakuwa tazo a irin wannan lokaci bata san inda zata nufa ba ko ina aka kadata zatabi talatu ta shigo dakin ta zauna akan gadon daga gefe Ki saki jikinki fa nan gida ne yace da ita yana fara'a "kinci abinci kuwa ? talatu ta girgiza kai tace A,a banci komai ba Baban yara yace To jirani Ina Zuwa Ya bazama ya fice daga dakin cikin gudu-gudu jikinsa yana rawa" A zahiri bashi da ko kwabo daga wajen gyaran babur dinsa yake" yau baiyi aikin komai ba" can ya wuni a gareji akayi masa garambawul a injin babur din har kudi aka biyoshi" "to Amma tunda yanzu sha'ani na bakuwa dole ne ya shiga cikin gida wajen matar yayansa ya samo rancen kyudi don ya fita kunyar wannan bakuwa tunda dai hadin kai yake nema . Baban taya ya shiga cikin gidansu da sauri bai zame ko ina ba sai dakin matar yayansa wacce indai ta ganshi tasan kome ya shigo dashi kodai yazo neman rancen kudi ko kuma yazo a bashi aron rikoda da kofikan shan lemu Idan yayi baki zaiyi karya yau duka yake so ta taimakeshi ta bashi da rancen kudin da kuma samira da kofikan tangaran Baban yara ya marairaice yace da matar yayansa Dawowa na kenan daga gari na sami wani abokina yazo daga Abuja a wajen acaba muka hadu dashi acan sanda naje barato nadawo bani da ko kwabo ki taimakeni salamatu dubu daya kawai nake so ki bani" Matar tace dashi "kaga dari biyu nan akan kabet.....KAZAR KARFI--> 03 . Matar tace dashi "ka ga dari biyu nan akan kabet" to wallahi ita kenan dani" ita din ma kudin adashi ne ban riga na aika ba Baban yara sai dai kayi hankuri da ita" ta miko masa" ya amsa cikin sanyin jiki" saurayin dan kimanin shekaru ashirin da uku" gwani ne wajen kure kai indai akan mace ne Yace da ita Bani samira inje in hado masa abinci Hada min kofikan zuba lemo ta dauko masa samira a cikin dakinta a sama ta hado da cokali da kofikan zuba lemo biyu" har zai fita sai ya sake tuno wani abin "Dan taimaka mini da mafici da rikoda Da yake ta saba da irin wannan are-aren kayan sai ta dauko masa rikoda da maficin" Ban daiyi zubi ba batiran sunyi sanyi sai ka sayi sababbi Baban yara ya fice ba tare da ya tsaya sauraron shawararta ba ya koma dakinsa dake kofar gida ya kaiwa talatu maficin ya ajiye rikodar a kusa da ita ya ce "wani shashashan kani gareni zuwa yake yi yana daukar mini kaya yana shiga dasu cikin gida" baya dawo min dasu sai naje na dauko da kaina na rasa inda ya kai mani bidiyona da janareton da nake tayarwa yana ba dakina wuta har fankata ma ban san inda ya kaita ba . Baban yara yayi tsaki" talatu tayi murmushi a karo na farko tace "Ai ba komae ko haka ma ya isa ta daga kanta ta duba ko ina a cikin dakin bata ga inda turken kwan lantarki yake ba babu kuma wani soket a jikin bango" babu wuta a garin" bata san yadda wannan saurayi yake ba dakin nasa wuta da janareta ba tare da waya ba Bata yi masa bayani ba ko tambaya a game da haka ta barshi ya tafi dauke da katon kwanon da zaije sayo mata abinci" Ya isa dandalin garin inda masu abinci da masu sayar da shayi da kwai suke da rumfuna" ga jama'a nan a zazzaune a ko ina akan benci" samari da kuma matasan dattawa" Baban yara ya sami daya daga cikin masu sayar da shayin da kuma indomi" ya kebeshi don kada mutane suji bayanin da yazo yayi kafin ya sayi abinda yake so" su koma bayan rumfar" Da zuwansu baban yara ya mika masa dari biyun yace dashi "ka gane Auwalu wata bakuwa nayi yanzu-yanzun nan to ina son ka hadani sosai dari biyun nan kawai gareni" ka hada mani indomi guda biyu ka soya kwai biyar ka hada mani shayi dabam a kofi ka zuba madara gwangwani daya muji nawa ka biyoni gobe zan baka kudinka... Ba wasa Auwalu" . "Dan siririn mai shayin mai kama da karas" ya washe baki da zumudi yace da baban yara "to kai irin wannan idan ta samu ai muma ya kamata ku rika tunawa damu baban yara a ina ka samota ? Baban yara yace a banza na ganta dazu a bakin gari ina jin bakuwar gilli ce tazo bata sami daki ba" Auwalu mai shayi yace "A to gaskiya nima ina ciki baban yara" bari in hada mata komai da komai muje sai in bar yaro ya tsare min shagon kafin mu dawo Baban yara yaba Auwalu mai shayi hannu suka tafa faa!!" sukayi dariya" "kai mutumin nan" ashe kaima baka barin banza ta wuce ka? "Ina fa zan bari baban yara ? Auwalu mai shayi ya koma cikin rumfar ya fasa kwayaye yana kadawa" yasa yaronshi ya dora taliya a wuta baban yara ya zauna a benci yana jiranshi ya gama su tafi" Akwai alamar yaji dadin wannan hadin gwiwa da Auwalu mai shayi ya nemi su yi Dama bashi da kudi dari biyu ne da yazo da ita ta huta itama to amma akwai bukatar ace sun sayi lemun kwalba ya mance ashe da sauran cefane gashi kuma Auwalu baya sayar da lemo" to amma tunda dayyabu mai shago yana dashi" bari yaje su shawota Yace da Auwalu" "kafin ka gama hada indomin da kwan" bari inje wajen dayyabu in sayo lemu in dawo" Auwalu yace dashi "to, kayi sauri fa" ba dadewa zan gama" . Baban

Chapter 1 of 6