Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
Tuni yasa gatari alokaciguda yafaskara kan aljannu uku yafasa kijin biyu yamurde wuyan daya kawai sai ragowan aljaninnan yabace ajikin Kifi Kurdum sannan kifin yatashi Sama daniyyar guduwa Sarki Kaushatu yahade guri daya yai girgixa yatashi saman yariski katon kifinnan sukacame da yaki asama shida kifinnan kayya lallai wata tsiyasai dangado koda masifatai masifa sai sukarika sakema juna bala,i,daga kofofin tsafi tuni suka haifar dawani hayaki gamida rugugi maitada hankali kifi Kurdum yabusama Sarki Kaushatu wata Shu,uman wuta takama ilahirin jikinsa bakidaya hankalin jama,arsa yatashi shikuma kifinnan sai yatsaya asararin samaniya yana wani juyi kamar yana wasan Farinciki kayya da kifinnan yasan masifar da xata sameshi da yakara gaba aguje domin lokaci daya wutar tamutu sai SarkiKaushatu yabayyana yaya wani baki sannan yakunbura yakara girmatsanani girama yaninka kifinnan biyu yakwarara ihu yamika hannunsa tadanki Kifinnan yakafa hanna yensa abakin Kifin kamar Gora haka Sarki Kaushatu yabara kifinnan gida biyu yai jifada sassan jikin kifinSai Sarkan ajalii tabayyana asama Sarki Kaushatu yakaimata kamu amma shu,umar Sarkan saita xille tayo kasa xata fada cikin ruwan tekum Xurum Sarki Kaushatu yabiyota da tsananin gudu yana kwarma ihu yanacema dakarunsa kucafeta kada kubarri ta afka ruwannan aisai aljannu da mutane sukai cincirundo suka daga hannayensu domincafe sarkannan shikuma Sarki Kaushatu sai yarika saukowa ahankali domin yasadakar cewa Bamakawa Dole Sarka ajali tasauka ahannun daya daga cikin Dakarunsa kawai sai yarika kyakyata dariya abinsa Kayya da Sarki Kaushatu da jama,arsa sunsan masifarda xata afkamusu toda kowa yai takansa domin lokacinda Sarkar tayo kasa taxo dabda Dakarun Sarki Kaushatu Sai tafudda wani masifaffen haske haske yaketa tacikin dakarun Sarki Kaushatu abin bakyan gani domin haka hasken yarika shiga jikin aljannuda mutane yanafasasu kama tangaran haka suke tarwatsewa wohohonanfa tekun yarikede yaxama tekun jine yacika da gawawwakin aljannu da mutane, Sarkan tatsundumacikin ruwa Sarki Kaushatu yakwarara ihu shima yatsunduma cikin ruwan yakunna nutsu inda yabar dakarunsa suna cigaba da fashewa can yafuto yatsaya asaman ruwa yakama karanto kalaman tsafi gamidasuburbudo warkoki daga Warkokintsafi saiwani janhaske yashigi jama,arsa take sudaina fashewa alokaci guda kuma ruwa tekun yakafe halittun ruwan suka bayya afili tsananin Fushi sai Sarki Kaushatu yabusa musu wutar tsafi yakonesu bakidaya shida Jama,arsa suka koma kan tudu yakalle dakarunsa wanda adasunkai miliyan bakwai amma yanxu basuwuce miliya ukuba yakwarma ihu yace ahalin yanxu Sarka ajali tabar cikinruwa kuma wata Matsafiyar aljana maisuna Jajira itace tawufce sarkan Yadagamurya yacekuma tadauki ajalinta kawaisai yaigudu maxaje rufamar baya INASUNUFANE SHAYI YA ISO #BANGON DUNIYA PART 1 G Lokacin da Sarki Kaushatu yakumbura kuma ya harxuka yakwarara ihu sai ya afkama Macijiya Dallura da wani irin yaki maitada hankaili itama ta ruftamar sushiga farautan ran juna amma awannan karan labari yasha banban domin tuni Sarki Kaushatu yama Dallura raunika fiyeda Sittin yasare mata kawuna biyar inda yatasata agaba yana sauke mata axabar yaki dakanta taja baya sannan ta xubbda makamanta tai sujjada ga Sarki Kaushatu tace daga yau nibaiwarkace domin kai shaidanine uban Shaidanu Sarki Kaushatu yakeceda dariya akarke yakwarara ihu yace wane yaro kuma wane uban yaro ni Sarki Kaushatu dan kan,ana jikan Sarki Kurungu tsinanne uban mutsiyata Yadubi jama,arsa yace kowa yashirya xamu tunkari Dutsan wuta domin acanne Aljana Jajira take Rayuwa ahalin yanxu ta ajiye Sarkan ajali atsakiyar Fadanta sannan takewaye ilahirin dajin da shaidanun aljannu masu mutukar hadari lallai su iblisaine wadanda atarihinsu basusan faduwaba balle tsoro sukashe mutum kuma sunacin naman mutu haka kuma suna kashe aljani kuma sunacin naman aljani tabbas mudasu xamu gwabxa yaki mai take sai mai tsawon kwana kawai sai yadaka tsalle yahaye dokinsa yasaki Linxamin doki yanna cikin Dokar daji bakida dakarunsa suka rufamar baya hada maciya Dallura saida sukai tafiyar wata guda cur bisa alkaluman tsafi Sannan Suka isa Dutsan wuta wani kasur gumin Dutsene da yaxagaye dajin kaf babu wata hanyar wucewa sannan da xaran katunkareshi to xaima feshin wuta kakone kurmus dankari koda suka iso wannan waje sai suka tsaya inda Jama,ar aljannu da mutane gamida Dodanni suka tsorata daganin wannan Shu,umin Dutse domin aman wuta yakeyi bakakkautawa babu wata hanyar wucewa Sarki Kaushatu dankan ana yakarema Dutsannan kallo tsaf sannan yadubi jama,arsa yace yaku jama,ata lallai kusani bamuda wata hanya face muketa tacikin wannan gagarumar wuta mu haura dutsannan muriski aljana Jajira domin fadarta nabayan wannan tsinannen Dutse ai sai Hankalin jama,a yatashi domin kowa yasan shiga wannan wuta tamkar sallamama Mutuwace Koda sarki Kausahatu yafahimci Jama,arsa suntsorata ainun sai yabushe dadariya inda akarke yakwarara ihu sannan yaxarce takaranto wasu kaman tsafi yanuna wutarnan dankari ai amaimakon wutar ta mutu sai akwarara ihu wutar takara toroko tai Sama tashiga feshi tanayin harshe tana laso jama,ar aljannu da mutane daga rundunan Sarki Kaushatu tana kone su tuni jama,a Sukaja baya ran Sarki Kaushatu Yabaci yatunkari Wutar yanarike da wani bakin mashi da bakin Garkuwa tabbas iblishi iblishine domin tilas Wuta tadaina feshi takoma gudaya tairmi tanaci balbal Sarki Kausatu yaci gabada kusantar Wuta sai akara kwatsatsa ihu anacewa kai tsinanne lallai yauce ranan mutuwarka kawai Sai wasu jajayan Gwaggo birai girmansu yakai girman katuwar bishiyan kuka jajur suke kamar Garwashin wuta jikinsu harcida wuta yakeyi suka rika futowadaga cikin wutannan suna rikeda takubba yawansu yaxarce misali muninsu baxai fasaltuba suka afkama Sarki Kaushatu dayaki irinna amatu ko airai nanshima yafada musu sushiga gogawa dankari yaki yakaure inda sukarikaimai sara da suka yanakarewa gamida gocewa yana maida musu da martani wani abin takaici shine kwata kwata makami baya tasiri ajikinsu hankalin Sarki Kaushatu yatashi yafusata yarafka ihu yadaga hannayansa sama yarintse idanunsa yana karanto karatun Sur kulle inda biroyinnan suka rika tafkamar Sara dasuka amma kamar suna saran Dutse sambaidamu da suba takubbasu suka rika kararayewa can amaka wata tsawa da walkiya mai tsoratarwa dankari jama,asuka furgita anemi Sarki Kaushatu arasa yabace bat nanfa Dadakarusa da abokan artabusa sushiga xare,idanu amma bashi ba alamansa can akwarara tsawa gamida walkiya jama, sukadaga kai sama,atsorace kayya tsinanne tsinanne ai saiga Sarki Kaushatu na saukowa daga sararin Samaniya yana cikin wata damaran yaki jakur yanarike dasu jajayan gatura wata naci ajikinsa balbal kai inka ganshi saikadauka Iblishin Tabdijama ai Saikallo yakoma Sama domin al,amari yaxama masifa dabala i sannu ahankali yadira akasa kasa tai girgixa duwatsu suka ammsa koramu sukama ammbaliya dawakai suka xarya suna neman shiga dajiiiAmma gwaggwannin biriroyinnan sai suka jadaga dashiri Gumu KAI WANNAN SHAIDANINE NANUFI RUMFARDHAYI ABOKAI {#BANGON DUNIYA PART 1 {-I~}Lokacinda Sarki Kaushatu dan,Kan,ana Tunku maikai yaro makasa yadira akasa saida hankalin kowa yatashi domin tunikasa takama girgixa koramu sukama ambaliya hankalin Halittun daji manya dakanana yatashi sukama xarya acikin daji sarki Kaushatu yakwarara ihu yajijjiga gaturan hannayansa yadubi Makamakan gwaggon birannan yace kai tsinannu ganinan gareku yafalfala aguje yatunkaresu suma sukwarma ihu sutunkaroshi ahassale suka hadu atsakiya akai kwaram kwatsam dankari ainan halittunnan suga balbalin bala,i da masifa domin wani,irin kisan gilla yakemusu tamkarbarnan iska haka yake fatalidasu tamkar guguwar annoba haka yake turasu kiyama duk inda yakutsa sai kaga gawawwaki naxuba kawuna natashi sama yasare yabanke gamida Farkewa dankari koda masifataimasifa halittunnan suji masifa aisai suka tarwatse amma saboda bala,i irinna Sarki Kaushatu sai yakwarara ihu tuni watamasifaffiyar wuta tabisu daya bayan daya takonesu kaf Sai yajuya yaceda jama,arsa kubiyoni mutnkari tsinanniya Jajira take yanufi Wutan yana wanidam dam yanaham aisai wutan tarabu biyu hanya tasamu kai tsaye sarki Kaushatu yafada hanyar shida Jamarsa sukawuce lami lafiya sannan suka riski katom dutsennan mai aman wuta dankari babu wata hanyada xasu wuce face wutarnan tababbakesu nanfa akai cirko cirko Sarki Kaushatu yaceda,dakarunsa lallai babu watahanya sai mungifta tagaban dutsennan mai aman wuta sai yadaga murya yace lallai kowa yashirya domin xan aikata wani tsafi lallai xandakatarda wutar na tsawon dakika Sittin lallai duk wanda baiyi kokari yawuce adan wannan lokacinba to yahallaka nantake yafara karanto wasu sarkakkun kalmomi daga kalmomin tsafi damatsanancin Sauri yake Karantowa yarintse idanunsa yaigumi Sharkaf tundaga sama harkasa can akwarara tsawa mairudarwa saiSarki Kaushatu yabude idanunsa take wutantadauke aibaicema kowakomaiba sai yasaki linxamin dokinsa kamar walkiya yagilma hakasuma tawagarsa suka rika gilmawa suna wucewa amma tsananin yawansu saida lokacinnan yacika basugama wucewaba take dutsen yacigaba da aman wutansa yababbake wadanda suka rage Kowaige Sarki Kaushatu da dakarunsa basuyiba sukabi wata siririyar hanya maitsayi take wasu Aljannu masu sufar batoyi sukarika shawagi asamansu suna yunkurin daukansu sarki kaushatu yadagamurya yace yaku jama,ata lallai kadawanda yadaga kai yakalli aljannunnan koyai kokarin yakarsu xai mutuhaka sukaci gabada tsula gudu a yar karamar hanyarnan batoyinnan suna musu baraxana, Amma,al,amarin Boka Barnuhu da tawagarsa masu kokarin samama duniya,sauki sunutsa acikin tafiya domin su isaWadil Maut domin sumallaki Miyagun takubba tafiya suke babuSassauci kamar xasu tashi Sama suna keta kwaxaxxabo gamida haure duwatsu suna tsallake koramau da tsaunuka harsu isawata doguwar sahara mai tsananin xafida kuna saidasukai tafiya tatsawon sa,auku cur sannan sukawuce Saharan sai su hangi wani bahagondaji maitarin duhuwa dadogayen itatuwa gamida manyamanyan Duwatsu sunadab dashiga daji Sai Boka Barnuhu yakwarara ihu gamida tsawa yace yaku taron maxaje lallai kada wanda yakuskura yashiga wannan dajin cik dakaru sukaja linxamin dawakansu dawakai sukai turjiya gamida Haninya bayan ansami Natsuwa sai Boka Barnuhu yace yaku maxajen fama lallai kowa yashirya yagyara damaransa domin tunkaran mutuwa gamida shirya shirin Gumu Gimbiya Eela tace yakai babban boka shin wace masiface acikin wannan daji Boka Barnuhu yace akwai wasu arnan daji masu tsananin karfigamida taurinkai da jaraban tsafi sam basabarin wata bakuwar halitta tawuce tawannan daji lallai tarihi yanuna samada shekaru dari biyubaya babu wata Halitta mutum ko,aljan ko gungun dabbobi dasuka keta wannan daji batareda arnan dajinnan sun hallakasuba kod boka Barnuhu yagama wannan bayaniSai Sadauki Amirul Jaishi yakwarara ihu yace lallai yau tarihi xaikaryerayuka xasu salwanta kuma saimunma kasa ado dajini yadaga murya yace tabbas ko,amutu ko,airai saimunketa dajinnan mun wuce ai yanarufe bakinsa Sai aka kwarma wani ihu mai furgitarwa gamida raxanarwa kwatsam sai cincirundon arnan dajinnan surika futowa daga cikin dajinnan yawansu yawuce misali,girmansu yakaigirman katuwar Bishiya sunarike dawasu miyagun makamai marasa kangado bakakenekirin munana masu kamada aladu sukai sahusahu saimuxurai sukeyi gamida lashe bakunansu tabbas insun sami naman mutum bashakkaci xasuyi Sarkinsu Maisuna Karkuxu yadakama Su Boka Barnuhu tsawa yanamaicewa ku mazzaje lallaikusani bama yaki Saida dalili dan haka inamai baku Shawara daku juya kukoma baya kunemi wata hanyar mutukar kunason kucigaba darayuwa aduniya turkashi lallai maza basa daukan Raini aituni Yarima Fawan yadakamai tsawa yace kaimutumin daji karyanka tasha karya lallai babu abinda xaisa mukomadabaya saidai mugo gamida Gwabxawa karfida karfi dantse da dantse wanda xai mutu ya mutu wandaxairayu yarayu wohoho ai sai Sarkin,arnan dajinnan yahassala yakwarara ihu yaima Jama,arsa tsawa gamida ambato wasu kalamai marasa Fassara aisai Jama,arsa sukai Ihu sukaikan Su Boka Barnuhu Suma sukai kainsu ahassale kowani bangare na Ihu gamida kururuwa sukai taho mugama akai karambatan karfe jini yakwaranyeda tsoka afara neman ranjuna ashiga Kairuwa ranadankari nanfa ihun maxaje yawaita arnan dajinnan sukarikama maxaje kisangilla wani abintashin hankali sukuma kaifida tsini baya tasiri ajikinsu kaiya aikoda adaulokaci anawannan bakin gumurxu Sai arnan dajinnan suka furgita Dakarun Boka Barnuhu ran maxaje yabaci Sadauk Amirul Jaishi yakwarara ihu maraxanarwa wanda saida tai sanadiyar yaki yatsaya cik NIMA NAYI RUFARSHAYI BANGON DUNIYA Littafi na biyu 2 Na Ibn Abdullahi Complet Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com #BANGON;;;;DUNIYA;;;;#PART 2A Lokacinda aljannu masu suffan batoyi sukai dandaxo agaban dakarun Sarki Kaushatu dan,kan,ana sai sukama babbaka dariya kamar mahaukata akarke suka tsuke fuskokinsu kamar an aiko Musu da sakon,Mutuwar ahlinsu shugabansu yadakama Rundunan Sarki Kaushatu tsawa yace kai tsinannu lallai kusaniMe Girma Jajira tasha gabanku kuma taxarce tunanin ku domin ahalin yanxu Sarkan ajali na hannuntatsawon kwanaki goma kuma tairantsuwa da iyayanta babu wani mahaluki daxai rabatada wannan Sarka harsai taxama nata yaxare takobi yanuna tawagar Sarki Kaushatu yace kai tsinannu shin xaku juyanekukoma kuna bukatar mutuwa awannan dajin tabdijam kalaman shugaban aljannunnan yafusata Jama,ar sarki Kaushatu sukwarara ihu gamida xare takubba xasu afkama aljannunnan suma aljannun suka yunkuro Kaiii wani ihu maikarfigamida tsoratarwa yaratsa kunnuwan maxaje tilas kowani bangare yatsaya acigabada hararan juna cikin tsananin tsana da kiyayya Sarki Kaushatu yace aa Maxaje lallai kusani yaki ba,ama faraba domin mallakan sarkan ajali abune da saitaci rayukan mutum da aljan mara adadadi yacigaba dacewa domin yanxu ana kashe rayukane daruruwa da dubabe tabbas nangaba Garuruwa xa,arika shafewa kamar ba,ayisuba yakine da xa,ayishi harxuwa bangon Duniya Sai yabusheda dariya yakalli tarin cincurundan aljannunnan yace kai iblisai lallai kusani domin mallakan Sarka ajali ina bukatan karin maxajen fama daga aljannu da mutane dakuma dodanni damiyagun dabbobi shin xakui mubaya,ane gareni koko sai mungoga kunjini na jiku Aljannu sukara gyara tsayuwansu gamida rikon makami sarki Kaushatu yakallesu yace baxaku sallamaba kenan to kutaho inbaku jikinku aljannu sukwarma ihu gamida kururuwa sutunkaro Sarki Kaushatu Tunku maikai yaro makasa yanatsaye ko motsawa baiyiba saiwani simi simi yakeda baki yana karanto kalaman surkulle da tsatsuba suci gabada tunkaroshi suna ihu gamida kugi saura kiris su af kamasa Sai yadaki kasa dakafarsa dakarfi ya,ambaci wasu klaman tsafi take kasa takama girgixa tana rawa gamida ruftawa bakidaya Kasan tahadiye aljannunnan iya kunguru sukai sukai sufuta sukasa gashi kasa nadada matsesu sai kwarma,ihu aljannu sukeyi Sarki Kaushatu yadubesu yakeceda dariya yace kaikananan hatsabibai shin xaku Sallamane kokun xabi kumutu kasatahadiyeku shugaban dakarun aljannunnan yace ina aihar,abada baxamuma wani halitta biyayyaba kawai mumun kasance bayine na Matsafiya Jajera Fasa taro koda Sarki Kaushatu yaji kalaman aljannu sai yakara bushewada dariya yace karya kukeyi lallai bakutaba toxali damutuwabane amma yanxu xaku ganta yadaga murya ya,ambaci wasu kalmomi take wata gagarumar wuta tawanxu mai tsananin xafi tanufi aljannunnan gadan gadan sai wani turoko wutar take tana wani mele mele ai sai aljannunnan sukatsorata wasusuka fasa ihu gamida rushewa dakuka aikoda shugabansu yagacewa shida jama,arsa xasu mutu,sai yadaga murya yanacewa yakai Sarki Kaushatu dan kan,ana lallai muntuba kuma kaine jagorammu take wutar tamutu tabace bat kasa tasakesu sUka nufi Sarki Kaushatu sukayi sujjada agareshi sarki Kaushatu yafashedadariya yace dole kamwar naki wane mutum kuma wane aljan take aljannu suka shigatawagar Sarki Kaushatu suka tunkari bakin Dutse tafiya kadan sukayi sai sukai kicibis da bakar Runduna tawagar Matsafiya Jajira dankari yawan dakarunta yaninka na SarkiKaushatu sannan akwai aljanu da mutane da miyagun halittu masu cin naman mutane Matsafiya jajira tafuskanci Sarki Kaushatu tace lale Sarki Kaushatu dan kan,ana Hatsabibi dan hatsabibi inamakabarkadaxuwa yankina Sarki Kaushatu yadaka mata tsawa yace ke kamar Iblishiya lallai kisani Nibana wasa kuma ba,amin wasa shin xakibani Sarkan ajaline kirayu koko saikinga taurarin mutuwa Jajira tabushedadariya tace kai bakin hatsabibi abin dasaukine haka lallai kasani komutuwa baxata iya rabani da Sarkan ajaliba saida tadaukemu tare tace kadubi tarin mayakana sunninka taka karfida yawan makamai gamida hatsabibanci kawai saitanufi jama,arta surika budamata tana tafiya tanacewa yakai sarki Kaushatu xanje tsakiyar dakaruna inxauna abisa karagata yayinda shikuma Sarkan ajali yana rataye a sandar mulkina sandar kuma nakafe akasa abayan karagata tana shigewa cikin dakarunta suna kulle kowace kafa hartabace amma anajin muryanta tana cewa indaikacika hatsabibi toka fasa rundunata katarwtsa Dakaruna kaxo muikwaram dakai inkakasheni saika mallaki Sarkan ajali Sarki Kaushatu yafusata yaima dakarunsa tsawa yace kai maxaje Ku,afkama tsinannunan domin sugane banbancin yawan da jarumta Dakaru sukai ihu gamida kuwwa suka afkama dakarun Matsafiya Jajira dabalbalin bala,i nanfa yaki yakaure masifa tawanxu ashiga asaranrayuka kura tahadu tai sama ShikoSarki Kaushatu saida yakwarara ihu sannan yai kundunbala ya,afka filin yaki kayya wuyar aiki ba,afaraba domin wani irinkisan kiyashi yakema dakarun Jajira babu mutum ba,aljan duk inda yatunkara saidaka fifi gawawwaki kwance yaxamo kamar wani aljani yarika feshin wuta yana kone makiya wani xubin sayai aman wata hatsabibiyar iska taita watsida maxaje damasifa ya,isagaban matsafiya Jajira kafin tai waniyunkuri yaxabga mata sara tamkar yasari dutse haka takobin tai tsalle akarke takobin tanannade shi kansa Sarki Kaushatu yasha mamaki domin samada shekaru arba,in baitaba Sarin mutum ko,aljan yarayuba amma sai Jajira ta girgije tabusheda dariya takalle Sarki Kaushatutace kadauka kaikadaine hatsabibi,Lallai kasani Iya sammakoka towani ahanya yakwana taxare takobi Shima yaxare takobi sukaja baya taku bakwai sannan sukwarara ihu suyanko aguje SHAYIIII#BANGON DONIYA PART 2;;B;;IIBLocinda Sarki Kaushatu da Matsafiya Jajira suka jada vaya taku bakwai sukwarma ihu sannan suka sheko aguje suka tunkari juna afusace suka hadu sukai Kwaram kwatsam hankalin yammaxa yatashi domin haduwace ta hatsabibai namfa masifa takullu inda Sarki Kaushatu daJajira sukarika kaima juna sara da suka cikin matsanancin sauri kamar walkiya karan haduwan takubba sucika ko ina tsananin karfin kai sara insukaima juna sara takubba suka hadu to sai tartsatsi wuta yatashi tsananim masifa kura tarufesu har va,aganinsu idanuwan masu kallo sudaina ganin komai sai vakar kura sai kunnuwa kawai ke,iyajin karan haduwan takubba maitada tsigar jiki nanfa hankalin kowani bangare yatashi domin yakine aduhu basusan meke aukuwa shin Sarki Kaushatune xaiyi nasara ko Matsafiya Jajira can akadaina jin karan takubba sannu ahankali Kura tayayaye ai sai ga Sarki Kaushatu yashaki wuyan Jajira yacirata Sama yamakata dakasa takwalla ihu yasa kafa yai kwallo da ita tai gare akasa tayunkura tamike gamida kwarara ihu tanunu sarki Kaushatu da yatsa,take wasu kananan macixai da kunamu masu fiffike suka tunkari Sarki Kaushatu Yakece dadariya ya,ambaci wasu kalmomi na tsafi yanunasu da Sandar tsafinsa take wata bakar wuta tafuta takonesu kurmusMatsafiya jajira takama jujjujayaHannayenta take tasarrafa wata dunkulallaliyar Wuta metafe da wata mahaukaciyar guguwa tawatsama Sarki Kaushatu Shu,umin sai yabude bakinsa take wani ruwa yafoto daga bakinsa aguje tamkar datsi yabarke yaje yakashe wutannan Jajira takwarma ihu tace karya kake tsinanne indai tsafi gadonane to saika mutu Sarki Kaushatu dan Kan,ana Tunku mai kai yaro makisa sai yakece dadariya akarke yadaure fuska yace ke mahaukaciya badan ina sankiba datuni kimmutu amma jarumtarki da hatsabibancinki tabirgeni lallai inaso kixamo daya dagacikin makusantana domin Mumallaki Sarkan ajali tare musarfa duniya atare Jajira tace ina niJajira nafikarfin inxauna akan wani domin niruwane indauki wasu kuma in boye wasu Ran Sarki Kaushatu yabaci yarafka ihu yace tokuwa lallai xakimutuwar kannuka asaura take yanunata gamida simisimi dabaki tareda motsa yan yatsunsa kaiyya tsafigaskiyan meshi tabbas komai sammakonka akwai wani agabanka kuma tsafi kogini saidai kai iyanutsonka kafito domin lokacinda Sarki Kaushatu yanuna Jajira dahannunsa sai wasu igiyoyi suka fota a yan yatsunsa guda biyar damasifan gudu sukaje suka shaki wuyan Jajira,taji masifa kamar ana kafamata kibiyoyin dasuka kwana ana hura musu wuta takwarara ihu tsananin masifa saida tasaki Futsari abujenta,tuntana ihu atsaye harta durkushe visa Guiwowinta tsananin masifa takama aman jini kunnuwanta na xubda jini hancintama naxuvar kiniaikoda Jajira taji xata mutu sai tadaga hannayanta Sama alamar ta Sallama kuma tamika wuya ga Sarki Kaushatu aiganin haka Saidakarunta suma sukaxubarda makamai gamida Durkushewa akasa SarkiKaushatu yakwarara ihu yace wane mutum wane aljan Ni Kaushatu dan Kan,ana tunku maikai yaro makisajikan Sarki Kurungu mugun kifi Kaitsaye yanufi Sandar tsafin matsafiya Jajira wanda ke kafe akasa abayan karagarta Sarkan ajali na rataye asandar cikin takama Sarki Kaushatu yatunkari sandar yana murmushi kayya wani avuda Baisanibashine tun lokacinda Matsafiya Jajira takafe wannan sanda wasu jama,a daga jama,ar aljannu ruwa karkashin Jagorancin Sarki Sayyanu vn Siyam sunbiyo takarkashin kasa sunyi haki subiyo ta kogin kasa sunraruke kasar Sanndan sunaso sujanyeta ailokacin da Sarki Kaushatu yakai hannu daxumman yadauki Sarkannan kwatsam saikasa taburmewani wawukeken teku yabayyana ruwa yakai yakawo sandar tatafi akan ruwa Wasudaga cikin alajannun ruwa sukaima Sandar wawa domin sucire Sarkar Ajali dankari Sarki Kaushatu yakwarara ihu yanuna aljannunan take wata koriyar wuta takonesu tabdiijam aljannun ruwa suka bayyana asaman ruwannan suna kokarin riskan Sarkarajali Sarki Kaushatu yakwarma Ihuyai umurnida da Jama,arsa cewa kai maxaje ku afka cikin ruwannan domin gwabxawa da makiyammu lallai kadamubari dayansu yarayu tuni dakarunsa dana Matsafiya Jajira suka kwarma ihu gamida kundumbala suafka ruwannan nanfa afara cinikinmaxa Ma,ana yaki atsakiyar teku ,Acankuwa Dakarun xumunci masukokarin mallakan Miyagun takubba domin Raka sarkar ajali xuwa Bangon dununiya sunnutsa acikin daji gudu sukeyi tamkar xasu tashi sama saida sukai kwanaki casa,in suna keta daxuxxuka da kwaxaxxabai gamida tsallake duwatsu da tsaunuka sai suka isa Bakin Dutse wanda awannan dutsene xa,sami miyagun takuvba koda suka iso Sai BokaBarnuhu yaitsawa runduna tatsayakura taigaba Boka Barnuhu yace yaku dakarun Xumunci kusani munxo Dutsennan maitsanani hadari yanxu xanyi kokari ingano mana kofar daxamushiga cikingogon dutsennan munemi Miyagun takubba nanfa yakama tsumburikaida tsatsube tsatsube yana wani damdam yana hamham idanunsa sukada sukaijajur gumi yarufeshi yarika nuna yanki yanki na Katon dutsen dominneman kofa duk inda yanuna saikaji wani tsawa gamida tashin wutamai karfi yacigaba danunawa har yanuna wanguri take gurin yaburme wani wawukeken kogo yabayyana zududu yaicikin Dtsennan Aihakan na faruwa sai wasu miyagun halittu sukarika futuwa acikin kogonnan suka taru sukai dandaxo yawansu yafi karfin irga hallitun sunada suffar mutane amma sunada bindi kamar birai sannan sunarikeda miyagun makamai bakinsu na fudda wuta Boka Barnuhu yace yaku maxaje lallai kusani miyagun takubba nacikin kogonnan sukuma wadannan halittu baxasu bari wani yashigaba saidai basa nunfashi sannan,kusani kashe wadannan Halittu daida yake da YAKIN DUNIYA tofa ankawo SHAYI #BANGON DUNIYA PART 2C Lokacinda Boka Barnuhu yagama jawabinsa Sai Gimbiya Eela takwarara ihu taxare takobi takalli maxaje tace lalla kusani domin samama duniya sauki sai mun gwabza yaki da koma waye tasaki linxamin dokinta tanufi halittunnan tana Ihu Sai Sauran dakaru surufa mata baya suma suna rafka ihu dankari suma halittunnan saisuka kwarara ihu suka nufu dakarun Xumunci ahassale kayya masifa bakyau kuma maitasota tsinannene domin wani irinhaduwa akayi irinna mayakar asalinanfa akai kwaram kwatsam masifa takullu afara asaran rayuka iface iface yayawaita jini yarika watsi ako ina mutane nakashe dodanninnan kisan kiyashi sukuma sunama mutane kisan gilla Boka Barnuhu yakwarara ihu yarika babbake halittunnan da wutar tsafi yanacewa yakudakarun Zumunci lallai kui yakiiya karfinku kukashe hallittunnan kisan kiyasghi domin kushiga kogonnan kusani duk wanda yainasaranshiga wannan kogo har yaikokari yamallaki daya daga cikin miyagun takubba tozaizamo daya daga cikin Dakarun Xumunci goma Shabiyu wanda kuma sune xasuima,Yaro Kairuf Rakiya xuwa BANGONDUNIYA domin yaron yakai Sarkar ajali muhallinta Karr uba akoda maxajesuji cewa duk yawansu Sai, mutun goma shabiyune xasuzama cikakkun Dakarun Xumunci sai yaki yakara tsamari wutar yaki taruru tai sama kowa so yake yasami kofa yashige kogon Zurum domin yamallaki dayadaga cikin miyagun takubba suma halittunnan sukara xage dantse ganin basubar wani mahaluki yashiga kogonnanba dankari Sarauniya Atine yarmama kura ajalin garke takwarara ihu ta fudda wasukananan gatura gudabiyu masu tsananin kaifi tarika Faskara kawunan halittunnan tana sassabe kafadunsu damasifa tabude hanya tanufi bakin kogon gadangadan saura kiris tafada ciki sai Halittunnan suka taru su yanyame kofar kogon Atine yarmama takwarara ihu tasaki gaturannan turkashi tsafi gaskiyar maishi domin gaturannan kaitsaye suka afkama halitunnan dasara hanya tasamu damasifan gudu tafada kogon Inda Yarima Marwan yabiyo bayanta dabalbalin bala,i shimayashige kogo dankari Sarki Marhux yatunkari Kogonnan halittun sukaimar dafifi yakwarma ihu yafadasu dasara dasuka yatarwatsasu sukadare yafada kogon shima, Kaiyya al,aamrin yaikamari hallitunnan hankalinsu yatashi xuciyarsu takufulasukarika kashe mutane bashara,a inda suma gayyar mutane sukai kaimi daomin fadawa kogonnan Gimbiya Ela sadauki Imfal yarima Imkal Jaruma Mira sarki Yaki Suduf sukai kumaji gamida kundumbafa sutunkari kogon da masifada bala,i domin duk halittan data kusancesu to tamutu suka gallabi halittunnansubudemusu kofofin mutuwa tilas dole kanwan naki Halittun suka tarwatse gamida darewa sukuma suka afka cikin gogon Xurum yaki yacigaba Inda boka Barnuhu da Sadauki Amirul Jaishi da sarauni Mehalsuma suka hadu sucure sukarika ma halittunnan yayyafin kibau gamida feshin wuta daga Sirin tsafi damasifa suma suka shige cikin gogon nanfa dakaru dadama suka shigecikin kogon anyi ittifaka kimanin dakaru miliyan dayane suka samidamar shigewa cikin Kogon Xurim sannan Bakin kogon yashafe halittun da,ake dauki badadi dasu suka bace wohoho lokacin da maxaje suka tsinci kansu acikin kogon Zurimsai hankalinsu yai mutukar tashi domin wani makadedan kogone maitsananin duhu wanda wani baya iya ganin wani sannan sai wani ihu gamida kuwwa dadararraku ketashi acikin ramin hankalin kowa yatashi domin duhundare abin tsorone can sai boka Barnuhu yakama Magana cikin madaukakiyar murya yanacewa yaku tarom maxaje lallai kusa awannan kogo babatun dan,uwa ko,aboki komasoyi kokuma masoyiya domin mutuwace kekewayedamu tabbas mu miliyan gudane acikin wannan kogo ammafa kusaniMutum goma shabiyune kawai xasu futa araye kuma sune mamallaka miyagun takubba wanda akemusu lakabida Dakarun Xumunci dankari nanfa kowa yashiga taitayinsa gamida gyara rikon takobinsa, Acankuwa tsakiyar ruwa yakine mai tsanani yacigaba da wanxuwa tsakanin Dakarun sarki Kaushatu dakuma aljannun ruwa yaki yakaure arika asaran rayuka takowani bangare jini yacika kogin mutuwa tarika xirga xirga aruwan tana daukan masu karan kwana tana turasu kiyama dankari miyagum mutune da shaidanun aljannu surika tuttudowa tako ina burinsu kawai sudauki sandar tsafin Matsafiya Jajira sucireSarka Ajali amma kafin sukarisa gunta sun hallaka daga harin magabtansu Sandar tarika gudu asamanruwa inda Sarki Kaushatu dankan,ana yarika bin sandar aguje dominyakamata kwatsam sai wata shirgegiyar tsuntsuwa tabayyana asararin samaniya girmanta yaninka girman giwa sau bakwai taima jama,a,runfa tarika yimusu yayyafin wuta hartakai ga Sandar Jajira taikasa kasa xatadauka aisai Sarki Kaushatuyakwarara ihu yasabi karanto wasudalamusants afi yanuna katon tsuntsunnan dasandar tsafinsa tuni wani janhaske yaratsa sassan jikin tsuntsunnan take tai bindiga tatarwatse namantayai daidai asama Wasu bakaken,aljannu suka ketokasan ruwa sukafoto sukaima Sandar tsafinJajira kuri sunakokarin dauka SarkiKaushatu yakwarma ihu yaiwani yunkuri tuni,yatashi sama yadira atsakiyar bakaken aljannunan Take sukaure da yaki inda yarika ketasu gida biyu yana wattsarwa kamar annoba tankar barnan isaka hakaSarki Kaushatu ke saukema aljannun bala,i da xaxxabin mutuwa dukda irinkisan gillada Sarki Kaushatu kema aljannunan amma saikara tuttuduwa sukeyi suka yamyameshi sukaimai kuri sukahadu xasumai rufdugu ammada Sarki Kaushatu yakwarma ihu yaikururuwa ya,ambaci wasukalamai dagakalmomim surkulle saiwata mahaukaciyar iska tawanxu tarika sunkutan aljannun tana watsidasu cikin kankanin lokaci,iskar taima bakaken aljannunan kacakaca Sarki Kaushatu yakwarmaIhu Mairaxanarwa KAINATSORATAWLH SAINASHAYI ;;;;#BANGON DUNIYA PART 2D;;;; Lokacinda Dakarun xumunci sutsinci kansu acikin Kogon Xurim sai hankalinsu yatashi domin munin kogon ya isa gaduhu gawasu gurnanaimarasa kangado can akasaki wani kara gamida tsawa anacewa yauceRananr mutuwarku kawai sai wasumanya manya gauraki sukabayyana ackin kogonnan surika shawagi suna feshin wuta gamida sunkutar mutane suna jefasu acikin wani mahaukacin rami kayya ainan masifa tabude ashiga dauki badadi,tsakanin mutane da tsuntsaye anacikin,wannan bala ine sai akara Kwalla ihu saikuma wasu kananan aljannumasu kama da tsulan biri suka bayyana acikin kogonnan suhau maxajeda cixo duk wanda suka cixa to take xakaga jikinsa yakama rubewasuna xubewa matattu masifa ta gauraye kogo jini yarika kwarara gawawwaki su yawaita wuta takama acikin kogo inda bakidaya Kogon yadauki rawa kamar xai Kife,Dankari can sai,aji Murya Boka Barnuhuyanacewa yaku Dakarun Xumunci nidai na mallaki daya daga cikin miyagun takubba lallai kugaggauta mallakan

Chapter 2 of 6