Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 8
din,i can't jst hurt you! Hajjo ta ce gwara kin yi hurtn kan ki Ayush? For you information,wallahi ban taba jin soyayyar Suraj cikin rai na ba,I was doing it for u mumu! It was all for ur sake!Duka su ka sa dariya,budurwar ce ta kara dawowa,kafin ta yi magana Hajjo ta ce gata nan,pls a yi hakuri. Ta ce da Ayush ina ne wajan bikin? Ayush ya ce ta yafe ma ta wlh ga hadari ga tsohon ciki! Hajjo ta ce wlh babu abunda ya isa ya hana ta zuwa auren Ayush da crush,so kawai ta fada ma ta,ta na fada ma ta,Hajjo ta taya ta share hawayen fuskarta,su ka fito. DIYA MACE Tin shigar ta mota Aysuh ke kokarin gayawa angon na ta suna da babbar bakuwa,amma ina mitar ta ki fitowa da wuri ga hadari da ya ke ta ma ta ya ki bari ma ya ji,dan haka sai ta yi fushi ta ma sa banza. Sai da su ka shiga su ka zauna a dakin taron sannan Hajjo ta sami damar karasawa a na ta motar. Har ta fito sai ta tuno alkawarin da ta tabawa yiwa Suraj,ta ga lalle tin da Allah ya nuna ma ta ranar,dole ta cika,dan haka sai ta dauko ajiyayyar lapcoat din ta da ke cikin mota,ta sanya. Tin da ta shigo ya ke kallanta,ba komai ne ya ja hankalin sa ba sai lapcoat din da ya gani sanye jikin ta,haka ma dayawa daga cikin jama'ar wajan kallan ta su ke,mace mai tsohon cikin da ke rinjayar ta dan girma,ta na taku da kyar ga lapcoat ta daura,likitocin da su ka gane ta kuwa dariya kawai su ke,dax Doc Hajara for them,komai na ta da gaske ta ke yi. Suraj was lyk wacece wannan? Maganar sa da Hajjo ce ta fado ran sa,lapcoat? Sanya lapcoat ranar bikin sa? Mutum daya ce da wannan aiki! Ya juya ya kalli amaryar sa da alamar tambaya,murmushin da ke fuskar ta ya gasgata ma sa Hajjon ce ba kowa. Kai tsaye wajan ango da amarya ta nufa,ta isa gaban su Suraj ya dara tare da Fadin dax Hajjo for us! kin dai sa hankalin ki ya kwanta! Duka dariya su ka sa,da ke ya taba bawa Ayush lbryn sanda suna shawarar irin shigar da za su yi. Hajjo ta ce ana bikin Doctors ai ban yi adalci ba idan na kasa cika alkawari. Suraj ya gyada kai,ya ce yes,thank you for dat,amma you tooo heavy,ya kamata ki koma gida kar ki haihu wajan bikin doctors! Ayush ta ce menene ciki? Gwaggaro za mu aje mu karbi dam bebyn mu. Duka dariya suke,Hajjo ta tsaya tsakiyar su da tambatsatsen cikin ta aka mu su hoto,sannan ta mu su sallama da fatan alkhairi,zuciyar ta fari fat da annuri ta baro wajan. Tana shiga gida gaban ta ya fara faduwa,Khalid jingine jikin motar Hauwa,kallo daya za ka ma sa ka tabbatar da bacin ran da ke tattatare da shi,ya cika yayi fam dawowar Hajjo ya ke jira,tin dawowar sa da ya ga ba ta nan gaba daya hankalin sa ya gama tashi,gashi ba ta daga waya. Gefe ta faka,ta fito da fa'ar ta ta ce sannu da zuwa...bin ta yayi da kallo ya tabbatar da lfyn ta lau,fuska tsuke ya ce ke ce da sannu ke da ki ka fita bayan kin san na hana tsabar ba ki san ciwan kan ki ba! Nxt tym idan za ki fita ki aje min ciki na a gida sai ki je duk inda za ki! Ban mukullin motar! Rai ba dadi ta mi ka ma sa,tare da fadin ka yi hakuri! Banza ya ma ta,ya shige ciki ta na biye da shi,sai shunan sa ta ke da baki,ta na fadin masifaffe kawai! Da su ka shiga ciki ya juyo ya ce mekika ce? Ta ce ah ah ba magana na ke ba! Cikin takaici ya ce ina ma ki je? Ta ce wlh bikin Ayush ake,yace wacece Ayush? Ta ce kai Khalid kawar tawa ka man ta? Aysha? Ya ce cousn din tsohon saurayin ki? Ta ce yauwa Suraj din ma ta aura...WHAT bikin tsohon saurayin ki ka je! Hajjo ta ce Khalid! Ina ya hau ta inda ya ke shiga ba tanan ya ke fita ba,gaba daya ya masife ta tsaf! Kafin ya haye bangaran sa,sai ga Hauwa ta fito ganin Hajjo tsaye ta kuma jiyo masifar Khalid din ta ce lfy kuwa Hajjo? Hajjo ta ce wannan masifaffan mijin na ki ne ke masifar rashin gaskiya. Hauwa ta ce ahh ran maza ya baci,aje a lallabo shi. Hajjo ta tabe baki ta ce caf bar ni na ji da kai na kin ji,can ma sa,sai dai ke ki lallabo shi din ba dai ni ba. Hauwa ta ce ah ah wane ni,ban shiga wannan fadan Hajjo. Hajjo ta ce toh ya je can ya karata,ina jin dan ciwo kadan,bari na je na kwanta ko zai lafa. DEDICATED to The Women Of Virtue (group) [6:42PM, 6/14/2015] +234 816 848 0287: [2:35pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE Hauwa ta ce ko dai abun ne? Tana tafiya Hajjo ta ce ah ah,da saura dai,kawai ban jin dadi ne. Ta shige ciki Hauwa na ma ta sannu. Da aka zo cin dinner Hajjo ba ta fito ba,haka ma Khalid da ke fushi. Da ke Hauwa ta san haka sai su ka ci abuncin su ita da Neena. Sai da ta gama ta leka Hajjo,sai ta ga ta na bacci,ta kyale ta ba tare da ta tashe ta ba. Garin yayi baki matuka,hadari ya hadu sai walkiya,dan haka Hauwa da Neena ma da wuri su ka yi kwanciyar su. Cikin bacci ta ke jin ciwan na tsikarar ta sama sama,tin tana iya jurewa kamar a mafarki,abu ya zama unbearable har sai da ta farka,ta tashi zaune cikin zufa,sai da ciwan ya lafa sannan ,ta duba agogo ta ga karfe tara na dare. Tashi ta yi ta watsa ruwa,ta sanya wata rigar ta iyaka gwiwa,ta koma ta kwanta. Ciwan be kara motsa ma ta ba sai kusan wajan goma,one hour interval kenan,da ta ga haka ta tabbatar naguda ta ke,amma ta san da saura,za ta iya kaiwa ma zuwa asuba. Sai ta saki jikin ta ba ta kira Khalid ba,shi da ma ya ke fushi da ita ta ma kashe wutar dakin dan ta san ba shigowa zai yi ba. Haka ta yi zaman ta,tin tana kan gado sai ga ta ta sauko kasa,wato ya kara motsa ma ta kenan. Khalid kwance bisa gadan sa,ya na so ya kaurace Hajjo yau dai daya,amma abu na so ya gagare shi. Kamar wanda aka kira ya tashi da sauri,ya sauko sai gashi bakin kofar dakin Hajjo. Ya bude kofar a hankali,ganin wutar dakin a kashe ya san ta yi bacci,amma idanun sa na matukar san ganin ta duk da ita mai laifi ce. Dan haka sai ya shiga dakin,makunnin wuta ya danna,haske ya gauraya a dakin,ga mamakin sa gadan na ta ba kowa,ya na tunanin ko ta shiga bandaki,ya nufi bandaki da niyar kwankwasawa,sai ya hange ta can gefe,zaune dai dai bisa carpet,da sauri ya karasa wajan ta yana Suger ya dai? Ta na murmushi ta ce labour na fara. Ya ce ya salam! Ya ba ki kira ni ba! Bari na kira Hauwa mu tafi hsptal! Ta yi saurin ruko hannun shi ta ce da saura,pls ka dan barta tukunna,ina ga sai ma zuwa asuba zan haihu. Kallan ta yake kamar ma neman gaskiya daga fuskar ta,daga bisani ya ce tun yaushe ki ka fara jin ciwan? Ta ce tin dawowa ta gida. Ya ce da hadari Hajara,tin kafin ruwa ya sauka mu je asibiti. Ta ce blv me da saura Khalid. Sai da ya dan yi tunani,sannan shi ma ya zauna kusa da ita,ya janyo ta jikin sa. Bini bini sai yayi kissing kumatun ta,ko hannu ko wuyan ta. Can ya ce Hajara? Ta ce ummm ta yaya za mu gane kin kusa ne mu tafi? Ba ana gwadawa ba?ya ake yi?da me ake yi? Da ke ciwan ya lafa sosai,kamar ba ita ke yi ba,sai ta murmusa ce ita diya mace in tana labour abin da ake fara dubawa shine wannan hanyar da dan yake futowa aga yana budewa to in ya na budewa,budewar shine Cervical dilation ko Dilatation of cervix,sai a gwada hw many Cm ta ke,yatsa daya shine 2cm,biyu 4cm,uku 6cm,hudu 8cm, biyar kuma 10cm. Idan diya mace tana 2cm xata iya kaiwa 6hrs bata haihu ba, Idan taje 5 still she is on the way xata Iya taking 3hrs kafin ta haihu, It depends on multip ce ko primid, In primid ce xata dade saboda itace haihuwarta ta farko, In multipce baxa takai hrs din primid ba saboda tataba haihuwa,kamar ni kenan, Buh duk inda akaje 8 haihuwa taxo kusa xata iya haihuwa within 30mint, In kuma akace fully dilated dax 10cm tofa yanxu xa aga kan da. Khalid ya ce yaya kenan ke da ba wanda zai iya dubawa? Ta ce kar ka damu,na riga na kintati lokaci base on yanda ciwan ya ke tashi. Shiru su ka yi,daga bisani ya ce yaushe raban ki da abunci? Ta ce kafin na fita na ci. Ya ce kin dade,bari na samo mi ki,ta ce noo i can't eat,bazan iya ba,ka dai bani black tea,shi zai iya keeping dina strong,ya ce owk ina zuwa ya fita jiki na rawa,sai gashi ya dawo dauke da flask din ruwan zafi,ya hada ma ta tea din,ya dawo ya dada jawo ta jikin sa,ta na sha suna dan hira. Tin suna jin saukar yayyafi sama sama,tuni ruwa ya tsuge kamar daga bakin kwarya,Khalid ya ce Allah ya taimake mu ruwan nan ya tsagaita san da za mu fita. Ta ce amen amen. Sai da ma ta manta shaf sannan ciwo ya dawo,mara ta fara juyawa,ta damki hannu Khalid, gaba daya ya kideme sai sannu Hajara,sannu sannu Hajara,me zan yi? Me zan mi ki na rage mi ki ciwo? Baki cize ta dafa bayan ta,ganin haka sai ya fara shafa ma ta bayan,sai sannu da surutai ya ke kamar shi ke jin ciwan ma. Can kuma kamar abun iska sai ciwo ya lafa,yayi hugn din ta gam daga zaune,ya na da ana daukewa da na dauke mi ki suger,I love you soo much! Ita dai uhum kawai ta ke cewa,ita ta san abunda ta ke ji. Haka su ka kusan raba dare,ciwo ya tashi ya lafa,tin yana after one hour,ya dawo 40mnts,30,25,20.....wajan uku da rabi sai fa abu yazo gangaganga,gashi ruwa ake sosai,ba karamin tashin hankali Khalid ya shiga ba. Da gudu ya taso Hauwa,tare su ka dawo kan Hajjo,gwara Hauwa atlest yayar ta Zeena ta taba haihuwa a gida dan haka ta na dan san kadan daga yanda za ta yi. Khalid ya kira wayar Jabir ba adadi amma saboda ruwa wayan be shiga,haka na matar sa. Gani ya ke laifin sa ne da yarda da maganar Hajjo,da sun tafi asibiti tuntuni da tuni hankalin su kwance. Carpet mai kamar leda Hauwa ta shimida gaban Hajjo,Khilid ya ce me ki ke yi haka? Asibiti fa za mu kai ta! Hauwa ta ce cikin ruwan nan? Kan mu karasa ta haihu,dubi kafar ta ka ga! Wani farin ruwa ne mai jini jini ya ga na bin kafar Hajjo,ta ce wannan zaki ne ke fita,daga shi sai faya,sai kuma kan da fa! Khalid ya ruko hannun Hajjo da ta ke ta nishi,ta na wayyo,wayyo,Hauwa ta ce addua Hajjo,summas sabila yassara! Summas sabila yassara! Caraf kuwa sai ta kama,tin tana fada a hankali,har ta fara fada da karfi. Idanun Khalid cike da kwalla,ya ce Hauwa ki taimaka min! I can't bear this! Hauwa ta ce ka fita kawai Khalid,ya tashi zai fita,wani ihun da Hajjo ta yi sai gashi ya dawo da sauri ya na sannu! Sannu Hajara! Haka mata ke yi! Haka Hajiya ta ta yi? Hauwa Hajara ta jigata! Wanda be daraja uwar sa ba yayi asara! DEDICATED to The Women Of Virtue (group) [2:55pm, 6/14/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE Hauwa ta ce taimaka mu sa ta on her kneels,ga faya ta fashe,na kuma ji kan da, Ko da ya ga yanda Hajjo ke zufa,tana cize lebe kamar za ta gatsa,sai ya tashi a gigice ya na fadan i can't take it,I can't take dis! A guje ya fice ko takalmi be sanya ba,haka ya fita cikin ruwa ya tada mai gadi ya bude ma sa gate,sai gidan Jabir. Da fitar shi,Hauwa ta ce da Hajjo yi nishi,yi nishi Hajjo da yardar ubangiji! Hajjo ta ce dallah kyaleni! Ba zan yi ba! Ba zan iya ba! Wayyo Inna! Allah ka ji kan Inna ta! Wayyo Inna! Allah ka gafartawa Inna...wayyo summassabilayassara! Innalillahi! Wayyo Allah! Hauwa ta ce ga kan dan ki,yi nishi! Ai kuwa da yardar ubangiji wani karfi ya zowa Hajjo,ta nisa da karfi sai ga katan dan ta ya sullubo mai kama da Khalid sak,har tsayin! Tuni ya fara callara ihu Hauwa ta yi saurin riko shi,Allahu akbar Khalid ya yi da. dan murna hawaye wiwi ke zuba daga idanun Hauwa,ji take kamar ita ta haihu,ta aje yaro a gefe ta ce saura mabiyiya,sa hannu mai za ta ji? Cike da mamaki ta ce Hajjo..Hajara...wani kan ne! Ai kuwa sai Hajjo ta fashe da kuka,ta ce kumamawa?na baki wlh,dan Allah na baki,wlh bazan iya ba,bazan iya haifo shi ba! wayyo Inna ta!. Hauwa ta ce na gode,amma sai dai kimin addua ni ma na haihu dan bazan iya haifo na cikin ki ba,ke kadai za ki iya,yi nishi ya fito. Hajjo ta ce na mi ki,Allah ka sa Hauwa ta haihu,Allah ka sa ta haihu,Allah ka sa ta haifo har na ciki na! Hauwa ta murmusa,cikin lallabi ta ce Allah ya amsa,amma sai kinyi nishi,Hajjo ban yi nishin ba! Ke ki yi nishin mana! Dallah ki barni na ji da abunda ke damu n! Wayyo Inna,karfi na ya kare,Hauwa ta ce daure....da karfi duk da dai be kai wanda ta yi na fari ba,ta nisa,sai kuwa subul na biyun ya fito wanda be da bambamci da na farko! Ya na fitowa shi ma ya callara na shi kukan,tuni mabiyiyi ta biyo sa,ba kari sam ba ta karu ba,nan ta kwanta ta na mayar da numfashi,Hajjo mai kuka sai gashi ta na murmushi. Hauwa ta ce Khalid sak mu ka samu har su biyu,ya zan yi na yanke cibiyar? Daga kwance murya shake tana mayar da mumfashi Hajjo ta ce duba cikin waccan drawer akwai saban reza da zare,ki dauko. Jarirai na kuka Hauwa ta dauko,Hajjo ta ce awna da danyatsan ki na tsakiya,daidai tsayin za ki yanke,sai ki daure karshen da kyau,in be dauruba jini zai zo yana zuba tawajan. Yanda ta gwada ma ta,hakan ko Hauwa ta yi,ta nade su cikin shalw,ta ba ta daya ta bashi nono,sannan ta fara gyaran wajan. Kafin Hajjo ta shiga wanka sai da ta ba su nono dukkan su,sai dai wannan karan ma tana wannan ciwan cikin kamar na haihuwar Neena. Ruwa ya tsagaita sai yayyafi,da ke asuba ta yi ,an fara kiraye kirayen sallah,tana wanka Hauwa zaune da babies sai ga Khalid jike jagab,Jabir biye da shi,shi ma din ya jige amma ba sosai ba. Ganin jarire har biyu Khalid ya rikice,gashi jike ya ke ba damar dauka,hugn din Hauwa yayi, fadi ya ke dukwannan nawa ne? Alhamdulillah ka ga kyautar Allah,da ya tashi bani sai ya bani biyu!!! Jabir ya ce dama yanda cikin nan kamar tulu ya kumbura sis dina ai sai dai biyun!Ya Hajaran ta ke? Hauwa ta ce lfy lau,sai dai ciwan ciki,Jabir ya ce yea dama wasu na yi,PCM ya kamata a mata,da an yi mata allurar za ta sami sauki inshaAllahu,idan gari yayi haske sai kawai ku kai ta hosptal dan duba su da kyau,haihuwan gidan nan ban fiya san shi ba,gaskiya ka yi sakaci,Allah kuma ya kawo da sauki. Toh toh toh Doctor!ahhh ai bazan sake ba! Khalid ya fada cikin murna. Hauwa da Jabir dai uziri kawai su ka ma sa,Gaba daya a rude ya ke,ya kalli wannan sai ya dawo ya kalli wannan,ya daga waya ya kira Hajiya,ita ma Hajiya murnar gun ta kamar ta fito ta wayar,cewa ta yi gari na haske za su ganta. Masallaci su ka tafi,kafin su dawo Hajjo ta fito ta shirya tsaf. Hauwa ke ba ta lbryn kyautar da ta ma ta tin kan ya fito duniya,har da gwada maganar ta Hajjo. Dariya su ke sosai,har Khalid ya shigo,ya na mata murmushi cike da kauna,ya ma manta Hauwa na wajan ya jawo ta jikin sa,Hauwar ta shige bandaki ta wayance da wanke hannu,shikuwa Khalid hugn matar sa yayi gam,sannan ya bi fuskarta da kiss ta koina,ya na na gode maman yan biyu,na gode na gode. Jabir zai iya shigowa ya gan ki? Ta ce eh bissimillah. Sai da ya shigo da Jabir Hauwa ta fito. Cikin nuna kulawa su ka gaisa. Khalid ya dau babban dan sa,ya zauna kusa da Hajjo ya ce Suger da wani suna zan ma sa huduba? Ta kalli Jabir sannan ta ce sunan yaya na,ka ma sa da suna JABIR! Farin ciki da alfahari su ka bayyana fuskar Jabir,sai gyada kai ya ke. Khalid ya ce toh Khalid ya haifi Jabir kenan! Sai a yi din. Duka su ka sa dariya,yayiwa yaran huduba da Jabir,Jabir ya karbi takwarar sa,Khalid ya karbi na biyun,ya ce wannan fa? Sabir ne? Hajjo na dariya ta ce wannan kuma sai dai ka tambayi maman sa,baki bude Khalid ya ce wata maman ta sa kuma? Hajjo ta ce ga ta kusa da kai. Ya juya ya kalli Hauwa,sai murmushi ta ke,ya ce ta yaya ki ka zama maman shi? Hauwa ta ce tin kafin ya fito aka min kyautar sa ai,kai amma Hajjo daban ki ke,da gaske ni zan zaba ma sa suna? Hajjo ta gyada kai,Hauwa ta ce toh a sa sunan Baba na,Abbakar. Khalid ya gyada kai,ya ce madallah da Baba,ya ma sa huduba da sunan Baban Hauwa,shi ma ya ce da ya sani ya tsaya da kila ta haifi uku,shi ma ya sami na shi. Da wasa da dariya ya raka Jabir. Ya dawo ya tadda Hauwa da Neena wajan Hajjo,murna ya cika Neena,atlast! Ita ma ta na da kanne. Hauwa ce ta janye ta,su ka fita suna jin ta ta kira baban ta tana Baba an sami karuwa fa,na haifo takwarar ka! Sai murna ta ke! Khalid ya janyo Hajjo jikan sa,ya ce ba fa ko dayaushe za ki na ba su nono su ta tsotsa ba,daga ganin yaran nan tsotso za su yi! Hajjo ta ce toh idan ban ba su ba me zan yi da shi? Kayya! Me za ki yi da su? Ai nawa ne! Bazan barai su lalata min mata ba! Hajjo ta ce Ah wannan ai child abuse ne!! Ya ce eh na yarda,in kin ga dama ma kira ni Child abuse in dai kan wannan ne zan amsa! Duka dariya su ke,ya ce kara kara dai in dai kara ce sai DIYA MACE! Ya bazan so ki ba? I love you big. Ta ce hw big? Ya ce bigger nd larger than lyf. Ya fara kissing din ta,babies su ka callar kuka a tare,ya dago da sauri ya na nifa ba za a matsa min ba!kar fa a bata min rai na!! Hajjo na dariya ta ce me aka ce da maza?? Takura indai irin wannan yanzu ka fara gani! Ba dai ka zama Baba ba? Wlcm to d system..........!!!! "Every female is an angel Don't west tym in selecting Unique,instead spend tym in Undstanding them........" ALHAMDULILLAH TAKU KHADIJÀ SIDI Dan Aunty An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 8 of 8