Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 8
amen. Allah ya bada zaman lfy. Hajiya ke neman ta ido rufe,da ta tashi daga aiki sai ta biya gidan ta. Hajiya ta na ta tsokanar ta wai Hajjo ta zama sirika. Wani nauyi da kunyar Hajiya ta ke ji sosai,ta ka sa sakin jiki su yi maganar auren da kuma sauran abunda Hajjo za ta bukata saboda kusan rabi tare su ka siya da Hajiya kafin ma Khalid ya dawo a fara maganar auren su. Da Hajiya ta ga dai Hajjo ta ka sa sakewa sai ta hada ta da kanwar ta,tare su ka cigaba da shirye shiryen biki,ba Jabir ba,har Hajiya sai da ta dunkula dukiya mai tsoka ta damkawa Hajjo dan shirye shiyen biki,ba shakka sun ma ta karamci kwarai. Gyara kam Hajjo na sha kwarai daga wajan Doc Hussaina,dake Doc Hussaina duniya ce. Hauwa kuwa sai da Khalid ya hada ta da Hajiya tai ma ta nasiha sosai sannan ta sauko. Ana sauran sati guda daurin aure ta tare saban gidan Khalid. Gidan ya hadu ya tsaru kamar gidan turawa,da ke ma su abu da abun su,abu na so Khalid bluiders of d world. Bangare uku ne,bangaren Khalid a sama,sai kuma katan falo a kasa wanda ya sada ban garan Hauwa da Hajjo matan na Khalid,sai kuma katan kitchen ma dauke da dining area,dakin Neena ma bangaran Hauwa ya ke,Gidan cike ya ke fal da kayan more rayuwa,gashi very spacious. Hatta bangaran Hajjo Shi ya zuba kaya,ya dai aika Sani ya tambaya ma ta colour din da ta ke so. Ranar juma'a aka daura auren Khalid da Hajara,Khalid ya biya sadakin sa dubu hamsin. Su Ayush ne amara,duk da ba wani bidi'a aka yi ba,daga wuni da aka yi a kumurya,sai walimar da aka yi gidan Hajiya sannan aka wuce da amarya akai Hajjo dakin ta. Kuka wajan Hajjo abun ba magana,rayuwa ta sake canzawa,ta shiga saban babi... DIYA MACE Hannu Hauwa aka damka amanar Hajjo,sai cika ta ke ta na batsewa ita da yan uwanta,habaici da guda kuwa yan uwan Hajjo sun sha. Ga wani ado da kyau da Hauwa ta yi kamar ita ta yi kanta dan kyau,sai a sannan Indo ta gane matsalar da Hajjo ke gujewa kan ta dan gaskiya Hauwa ta cika mace,su Doc Hussaina kuwa ba dan sun san wacece Hajjo ba sun kuma yarda da shirin da su ka ma ta da sai sun daura hannu a ka sun ce sun shiga uku. Bayan su Indo sun kara ma ta fada sai su ka watse,su ka bar Hajjo tsakiyar gadan ta ta na sharbar kuka. Ango Khalid ya shigo cikin shigar angwaye na alfarma,sai ma ya dada zama yaro kamar wanda ya yi auren fari.Hauwa zaune bangaran ta,ita ma yan uwanta sun watse,Neena na dakin ta ta yi bacci,Hauwa ta sake ado ta yi kyau kamar ita tai kanta ango Khalid ya shiga ya same ta. Shi kan shi kyan na ta ya ruda shi,ya janyo ta jikin sa ta zille ta na malam yaya ne,ba fa ni ba ce da kwanan ba yau! Ya dara tare da fadin an ma fara min gori kenan. Ta ce ya bazan ma ka ba gori ba tunda irin rayuwar da ka tsarawa kan ka kenan. Ya murmusa gami da sake janyo ta jikin,ya na hussssh,say no more. Ina Neena? Ta ce ta dade da kwanciya ita dai kam. Ya ce toh ki fito falo ki same mu,bari na kira kanwar ta ki. Da kamar za ta ce ba za ta zo ba,sai kuma ta ga kamar hakan zai sa Hajjon ta raina ta,ta ce toh ta na fitowa. Bangaran Hajjo ya shiga,ya tura komar a hankali,wani kamshi mai dadi ya daki hancin sa. Yayi sallama tare da shiga daki. Idanu ta daga ta kalle shi,wannan karan Khalid Khalid ne ke neman numfashi ba Hajjo ba,tsabar kyau da kwarjini irin na amare gaba daya ta sauya yanayin sa. An ma ta ado cikin farin leshi,ga farar lufaya an nada mata,ga gyaran jiki da ta sha wajan su Doc Hussaina fatar nan na ta wankan tarwada har wani sheki yake. Da kyar ya daure,ya na wani basarwa dan kar ta gane tarkon ta ta kama kurciya ya ce muna jiran ki falo amarya. Juyawa yayi ya fita ba tare da ya ji amsar ta ba. Falon kasa da yayi dan zaman iyalan na sa duka ya zauna. Hauwa ce ta riga fitowa,ta zauna kusa da shi suna dan hirarrakin su,sai ga Hajjo ta fito,idanun ta a kasa,fuskar ta rufe da mayafi ta zauna a na ta kujerar da ga gefe,Khalid ya ce ta so ta zauna kusa da shi kamar yanda Hauwa ta zauna,ma'ana su sa shi tsakiya. Ran Hauwa ya sosa da kishi,wato dai sai ya jera su,ya nuna ma ta matsayin su daya,bare ma fitowar Hajjo yanda ta ji tana kamshi kamar diyar shuwa ya sa zuciyar ta tsinkewa. Ba musu da ke gaban uwar gidan sa su ke sai ta tashi ta koma kusa da shi din. Ya mu su nasiha sosai da fatan za su hade kan su,ya kuma roki Hajjo da ta kara yiwa Hauwa kara akan Neena,tin da duk an zama daya,dan Allah ta karanta. Cikin ranta kuwa cewa ta ke indai kara ne kunzo wajan ta,ita ba matsala gare ta ba. Ya kare nasihar shi da addu'a. Hauwa ce ta fara tashi ta tafi,Khalid ya bi bayan ta. Ita ko Hajjo tashi ta yi ta koma na ta bangaran. Ta yi wanka fito daure da shawl dan yanda Khalid ya dade be fito ba sai ta dauka can zai kwana ta saki jikinta,ta zauna ta na shafa mai. Kamar da ga sama sallamar shi da shigowar sa lokacin guda ne... DEDICATED to The Women Of Virtue (group) [1:14am, 6/11/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE Da sauri Hajjo ta tashi,ta kuma koma ta zauna ta na jan shawl din kan gwiwar ta. Da ganin na ta da kuma yanda ya ga ta rude sai ya bashi dariya,dariyar ta sa ya bawa Hajjo haushi,dama kuma kule ta ke da shi. Ta yi saurin jan lufayan ta ta rufe jikin ta tana mallam menene za ka shigo min daki ba sallama! Ya na murmushi ya ce na yi sallama Suger,ta ce me ya sa ba ka tsaya na ba ka izinin shigowa ba kawai za ka shigo min?ya ce gida na ne,auren ki na ke. Ta cije leba gami da ka fita ka bar min daki,pls ka fita! Ya ce ni ki ke kora Hajara? A daren auren na mu na fari ki kore ni? Idanun ta kwalakwala,sai a sannan ta tuna fa ashe wai daren auren ta ne,ta tuno yanda na ta ta kasance da Garbati,tuni idanun ta ya rufe,ta ce eh kai na ke kora,pls ka fita. Duk da hakan be ma sa dadi ba,amma jin kai ya sa ya ki nunawa,sai ma murmushi da ya sakar ma ta,ya karasa cikin daki,gaban ta ya kara faduwa. Ya lura da hakan,sai da ya kai dab da ita,ta dada dunkulewa cikin mayafi,ya na murmushi ya aje ledar gaban ta yana fadin ga abunci,na san yunwa ki ke ji. Ya sunkuyo fuskar ta,Hajjo ta runtse ido,kumatun ta yayi kissin ya dago ya na dariyar yanda ta sankare,kana ya ce suger,Khalid is a gentle man,so ki sa a ranki ba zan taba kwana cikin dakin ki ba sai dai idan ke ki ka gayyace ni da kan ki. Ya juya ya fice. Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta saki jikin ta. Cikin azama gudun kar ya dawo ta sanya rigar baccin ta iya gwiwa. Sai da ta nutsu sannan ta bude ledar da Khalid ya aje,kaza ce gashasshiya da fresh milk,ta ci ta koshi,sannan ta dan taka a tsakar dakin gudun bacin ciki,ta kwanta ta sha baccin ta dake dama ta tara gajiya. Sai da ta yi sati daya a gida ta koma kan aikin ta. Sam Khalid ba ya gaban ta bare kuma matar sa,kwana uku uku su ka raba kwanan duk da kuwa duk ranar kwanan Hajjo dakin sa ya ke kwana bisa ga alkawarin da yayiwa Hajjon,ita kuwa Hauwa da ta lura da haka,sai ta kara jin kan ta,wato da gaske dai ba san Hajjon ya ke ba tinda ya aje ta tamkar fanko ne kawai. idan ranar girkin Hajjo ne kafin ta fita ta ke musu brkfast da abuncin rana,da ke 7:30 ta ke fita,8 ta ke fara aiki. Da ta dawo 4 sai ta daura na dare. Kuma bisa al'adar su,tare a ke zama a ci abuncin kan dinig table da ke cikin kitchen din na su,nan Hajjo ta ke ganin kissa da kisisi na wajan Hauwa,ita abun har mamaki ya ke ba ga Neena na wajan ita ko kunya ba ta ji? Tai ta jan shi da hirar da be ma shafi Hajjo ba yanda za su ware,ita kuwa Hajjo ko a tafin kafarta,ita dai ta cika cikin ta tashi idan ma hadiye shi za ta yi tayi can ma ta.Khalid ya dame ta da korafin shi ba zai juri hawan adaidaitan ta ba,kullum wani gardi ya ke jin kamshin ta,dan haka lalle ta yi shirin koyar driving dan ba zai juri yay kai ta ya na dauko ta ba,haka kuma ba zai dau driver ba. Tsakanin ta da diyar ta nesa nesa,dan ita ganin ta take kishiyar uwa ba ma uwa ba,ita kuma Hajjon sai ta ke wa Hauwan kara,ta ke dauke kan ta daga kan Neenan. Randa ta cika sati biyu a gidan ta,bayan ta gama girki an zauna anci,sai ta tashi ta shige bangaran ta ta bawa Hauwa waje ta yi abunda ta ke so. Ta na shiga ciki Khalid shi ma ya tashi,ya sake kaya cikin sport wears din sa ya fita jogging. Wanka Hajjo ta yi,ta sanya rigar baccin ta pink mara hannu da nauyi,ga laushi iya gwiwa ta tsaya ma ta,ta kama kan ta da ya ke a tsefe ta rasa mai kitso,ta yi kalaba guda biyu,abun ku da kan ba gashi sai kuwa su ka tsaya gudil gudil da su kamar kaho. Ita kanta da ta kalli kanta a madubi sai da ta yi dariya,ta yi kama da yar yarinya sak. Ta ja kujerar karatun ta gaban table,ta kunna system ta fara sana'ar na ta,wato research. Bayan Khalid ya dawo,a tsakar dakin sa daga shi sai gajeran wando da shawl a rataye wuyar sa ya na shirin shiga yayi wanka,sai ya ji duk duniya idan be tsokano Hajjo ba ba zai ji dadi ba,dan yanzu ba wacce ya ke son zolaya kamar ita. Kawai sai ya fasa shiga na shi toilet din ya nufi bangaran na ta. Ta yi nisa cikin research,ba ta ankara ba ta ji an bude kofa,da sallamar sa da shigowar sa lokaci daya ne. Ta daga ido ta kalle shi,ganin yanayin shigar ta sa ta yi saurin yin kasa da ido. Murmushin nan na sa na tsokana ya sakar ma ta,tare da fadin nawa toilet din is faulty,i wil use urs in ba damuwa....ya na magana ya na nufar kofar bandakin,jin ta yi shiru ya juyo ya kalle ta,ya ga sam hankalin ta ma ba ya wajan sa,sai a sannan ya lura da kahon gashin ta biyu,ya ce like seriously Suger iyakan gashin ki kenan ko kuwa kin boye wani karkashin filon ki? Dagowa ta yi ta kalle shi,sai kuma ta tuna yanayin da ya ke ta kara saurin kau da kai,gaba daya magana ma ta kasa dan takaici da kuma takurar da shigowar sa ya sa ta. Ganin ta ma sa shiru ya shige ban daki ya rufo. Sai a sannan ta saki ajiyar zuciya. Kamar za ta koma falon ta,sai kuma ta fasa gudun kar yayi tunanin tsabar tsoran sa ya sa ta gudun. Amma gaba daya ta ma kasa gane komai,burin ta ya zo ya fita ko ta sami nutsuwa. Ile ko sai gashi ya fito daure da shawl,kirjin sa duk a waje ga ruwa na diga daga cikin sa,hannun shi ruke da dan karamin shawl din ta ya na goge kan sa. Da wayo ta saci kallan sa,su ka kusa hada ido ta yi sauri janye na ta ido. Ya na murmushi ya ce ba sai kin saci kallo na ba Suger,am ol urs,saki jikin ki u can stare as long as u want. Maganar ta sa sai ta bawa Hajjo haushi,ta yi karfin hali ta kalle shi ido cikin ido sannan ta ce ni Hajjo na saci kallan ka? Me zan kalla Khalid? U ar nt man enough for me.....sai da ta fada sannan ta yi dana sanin dan subul da baka da ta yi,da za ta iya shanye kalmomin ta na karshe da ta shanye ganin yanda idanun sa ke shining,fuskar sa dauke da mischievous smile ya nufo in da ta ke,dan tsoro kasa motsawa ta yi,kamar wacce aka sa igiya aka daure,har ya karasa kujerar da ta ke,ya sunkuyo da fuskar sa dabda na ta,Hajjo ta yi kasa da na ta idon gaban ta na dukan uku uku,ya sa hannu ya dago da haban ta ya na kokarin sanya kwayar idanun sa cikin ta,amma ta ki dagawa ta kalle,ta na jin saukar numfashin sa kan fuskar ta,ya ce maimaita abunda ki ka ce Hajara. Tsit ka ke jin Hajjo kamar wacce ruwa ya shanye,ya ce fadi na ji,who is nt man enough for u? Ta yi shiru,hannun sa bisa fuskar ta,ya fara wasa da yatsan sa kan lips din ta da yake kallo kamar mai nazari,kan ta ankara tuni ya mikar da ita ya hada da jikin sa ya fara kissing din ta. Da ke Hajjo ta ji saban abu,abun da sai dai ta gani ana yi a tv ta dauke kai ko kuma ta karanta a littafafai wai shi Khalid ke ma ta, ta fara kokarin zullewa har ta hakura ta dai na... DEDICATED to The Women Of Virtue (group) [11:30am, 6/14/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE Ya kusa shagala ya manta da inda ya ke haka ita ma Hajjo da ta shiga wani duniyar,da kyar ya iya yaki da zuciyar sa,ya dago ya na kallanta,idanun ta runtse tana numfashi a hankali,ya maida ta jikin sa,yayi hugn din ta sosai kamar za ta shige cikin sa,sai da ya sami nutsuwa,cikin rada ya ce mata dis is jst a kiss Suger,ba dan Khalid is a gentleman ba da na gwada mi ki ya Man ya ke,amma a sannu Suger,cikin kunnan ta ya rada ma ta am much more dan Man enough for all the women in d world Suger......ya janye jikin sa a hankali,sai da Hajjo ta yi saurin dafa table dan gani take ba za ta iya tsayuwa ba, shi kuwa ficewa yayi da sauri kafadar nan a tsaye dan jin kai. Da fitar shi ta yi saurin hayewa gado,ita dai kam ta shiga nau'i,bargo ta ja ta dukunkuna,abunda ya faru tsakanin ta da Khalid ya sa ta dai na gane komai,ya tsayar ma ta da duniyar cak. Shima wajan gugan na ta hakan ta ke,tin komawar sa daki ya kasa sukuni,he jst can't blv Hajjo can b dis innocent yea Innocent nd sweet at thesame tym,sam da dukkan alamu yanda ta yi reactn ya san saban abu ne a wajan ta,hakan ya kara sa shi san more,he love every bit of it,He want her dan da kyar ya iya jurewa be koma ba,amma daran ranar sam bacci ya nema ya rasa,tunin Hajjo ne ya raya ma sa daren. Washagari ko karyawa ba ta yi ba ta gudu wajan aiki gudun haduwa da Khalid,dake ta yi sa'a ba girkin ta bane. Dab da la'asar bayan ta dawo daga aiki,ta yi wanka,sai ta fito babban falon su,nan ta tadda Neena a na game,ta ce Neena ba gaisuwa? Hankalin ta kan game tace ai ban gan ki ba Aunty,sannu da zuwa. Hajjo ta ce sannun ki,ta sami waje ta zauna,sai ga Hauwa ta fito daga kitchen ta ce Neena a tashi a yi shirin islamiya. Neena ta make kafada,ni wlh na gaji. Ga mamakin Hajjo sai ji ta yi Hauwa ta ce toh ai shikenan,ta cigaba da aikin ta. Har Hajjo za ta sa baki,sai kuma ta yi shiru,amma har ranta ba ta ji dadin abun ba. Ana kiran sallar la'asar,Hajjo ta tashi ta yi na ta,ta na zaune kan dadduma Hauwa ta sake shigowa ta ce da Neena a tashi a yi Sallah ma na. Idanun ta kan game ta ce sai an min game over Momma,Hauwa ta ce toh ai sai ki ta yi,ta shige kitchen. Ran Hajjo ya baci,ta ce ke aje game din nan ki je ki yi sallah. Ko kallan Hajjo ba ta yi ba bare ta aje game din,ta ce ai na ce sai an ce game over.....a fusace Hajjo ta tashi ta fizge handle din,tashi maza ki je ki yi sallah ko na sabar mi ki! Ta daka ma ta tsawa,a kideme Neena ta tashi,ta fashe da kuka da ke ba a saba ma ta tsawa ba,ko a jikin Hajjo dan ji take kamar ta make ka ta huta,ta ce dan iskanci ana mi ki magana ki na jin mutane sai kin gama game za ki yi sallah! Ki je islamiya kin ce kin gaji! Wlh ba zan juri wannan saken ba! Sai ga Hauwa ta shigo da sauri,ganin ta Neena ta karasa wajan ta da gudu ta na kuka,sai tambayar ta take lfy? Dukan ki ta yi? Kuka ya ci karfin Neena ta ka sa magana,sai Hauwa ta ce je ki dakin ki ina zuwa,sai kuwa ta shige bangaran Hauwa da gudu,ta na jiyo Hajjo na fadin ki tabbata kin yi sallah! Hauwa ta kalli Hajjo ta ce me ki ka ma ta? Kar dai dukan ta ki ka yi. Hajjo ta ce ban dake ta ba,amma kiris ya rage na dake ta,yarinyar is too spoiled,ya kamata a fara handling din ta wit iron hands. Hauwa ta ce ke kar ki nemi ki fada min magana! Me ki ke nufi? Ki na nufin ban iya tarbiya ba? Hajjo ta girgiza kai,ta ce ba haka na ke nufi ba,Hauwa ta ce haka ne mana,wato iko za ki nuna min,ban iya tarbiya ba muna sangantar mi ki da diya. Hajjo ta ce ba ki fahimce ni ba,gyara kayan ka ai ba zai zama sauke mu raba ba...ke tsaya matsayin ki! Hauwa ta daka ma ta tsawa,ta ce har ke kin isa ki fada min magana dan mijina ya auro ki,ki na ganin ba na haihuwa shi ki ke tunanin za ki iya min gori kan diyar ki......Hajjo dai tura ta kai bango,ita ma ta fusata ta ce eh an mi ki gorin,karya ne? Ba diyar tawa ba ce? Ko ke ki ka haifa min......karaf sai a kunnan Khalid da shigowar sa kenan ya tsinci maganar Hajjo,ran sa ya baci matuka. Ganin sa tsaye Hauwa ta juya ta shige bangaranta da gudu. Hajjo ta yi kasa da idanun ta,yanda ta ga idanun Khalid sun kada sun yi ja ya sa ta kokarin ma sa bayani....ya dakatar da ita ta hanyar fadin dama haka ki ke? Na zaci ke me rufa min asiri ce,amma ji yanda ki ke gorantawa mata ta? Ki da ki ke haihuwar ba Allah ne ya baki ba? Ko dabarar ki ce aka ce mi ki? Idanun Hajjo cike da kwalla ta ce ba haka ba ne,she pushed me to d extrem wall ne,dole na yi magana,ba zan iya jure ganin yanda Ameena ke tashi ba kwaba ba! Ba zan iya jure ganin ta na tashi kamar Baban ta ba,God shez becoming d personication of her biological father! Khalid ya cize lebe,ni ma gorin za a min? Na ji ba ni ne baban ta ba am so what? Hajjo ta ce me zan yi ku gane? Menene laifi dan na gyarwa diya ta tarbiya? Karya ne ba diyar tawa ba ce?yanda na san ciwan ta wlh ba zan sa ido ta tashi yanda ta ke yanzu ba,ba gata ba ne wannan,diya mace ce,uwa kuma za ta zama nan gaba...Hajara! Ya daka ma ta tsawa,enough of ur insult! Ita din da ki kewa gori ba taimaka mi ki ta ke ba?ki na da lokacin diyar ta ki ne?idan ki ka sa kafa ki ka bar gidan nan tin 8 ba ki dawowa sai 4,ina ki ke da lokacin kan ki bare na tarbiyar yara? Murya kasa kasa Hajjo ta ce no you ar mistaking,ku bani diya ta mana kuga ko zan gaza tarbiyartar da ita,ko bani ita ku ka ko za ta gaza samin lokaci na! Never underestimate d power of mother! Zan iya zama both! A responsible mother as well as a dedicating Doctor!Khalid ya daga kafada,Wuce ki bawa mata ta hakuri! Hajjo ta ce Khalid dan me ya sa? Dan me ya sa zan ba ta hakuri? Dan ni ba mutum ba ce ko dan ni ba a sona? Dan me ya sa? Me na mata da zan ba ta hakuri? Fuska murtuke ya ce a matsayi na na mijin ki na ce ki ba ta hakuri,it is an order! Rai bace,kwalla na shirin sauka ta makale,da sauri ta nufi bangaran Hauwa,ko da ta shiga dakin ta,ta ganta kwance,sai ta sake shawara,ta juyo za ta fita ashe Khalid na biye da ita,ya ce juya ki ba ta hakuri! Hajjo ta juya ta ce Hauwa Allah ya baki hakuri. Ta juyo tana kallan Khalid ido na spark din kwalla da bacin rai ta ce na bawa matar ta ka hakuri,ta fice da sauri. Shigewa dakin yayi,ya jawo Hauwan jikin shi ya na kara ba ta hakuri. Hajjo na shiga dakin ta sai ta fashe da kuka,sam ba za ta iya zaman gidan ba,dama ta san wulakanta ta Khalid ke da niyar yi shi ya sa ya auro ta. Tuni ta hada yan kayanta cikin karamar jaka,ta dau kudin mota,ta fito ba tare da kowa ya sani ba sai hanyar Kumurya. Sai da ya tabbatar Hauwa ta saki ranta,sai kuma hankalin sa ya koma ga Hajjo,ya fara ji kamar be kyauta ma ta ba tunda be ma ta uziri ba ya ji kanun zance,kawai tsintar ta yayi ta na gorantawa uwar gidan sa rashin haihuwa. Dakin Neena ya je,ya tambaye ta me ya faru ta yi kuka? Da ke yaro be fiya karya ba sai ta bashi lbrn yanda aka yi har kin zuwan ta islamiya da ma kin yin sallah. Jikin shi ya yi sanyi,ya tashi da sauri ya nufo bangaran Hajjo,amma me zai gani? Wayam babu Hajjo babu alamar ta,ya bi daki daki na bangaranta,har bandaki ya duba amma shiru,tuni ya rude,hankalin sa ya tashi. Da sauri ko takalmi be iya sawa ba ya fito wajan maigadi ya na tambayar ko ya ga fitowar amaryar sa? Maigadi ya ce kai be gani ba,in ma ta fita watakila sanda ya zaga bawali ta fita din..... DEDICATED to The Women Of Virtue (group) [11:55am, 6/14/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE A kidime ya koma ciki,takalmin da ya sako ma hadin bauta ne be sani ba,tashin hankalin sa ina Hajjo za ta da yamma likis haka? Ko sallama be yiwa Hauwa ba ya figi motar sa dan bin sawun Hajjo. Ko da ta isa kumurya,idanun ta sun kumbura da kuka,sai tadda Indo ba ta nan sai yara,su ke fada ma ta wai Indo ta na gida dazu aka zo aka ce Baba ya kone. Nan tsakar gida ta saki jakar ta,bayan shekaru da dama sai ga ta ta dau hanyar gidan su,dan idan ba ta ga halin da Baba ya ke ciki ba hankalinta ba zai kwanta ba. Ganin yanda kofar gidan ya kwarabe sai da gaban ta ya fadi,bare da ta shiga gidan,kamar ba nan ne Innar ta ke rayuwa ciki ba da,gidan ya lalace,ya kazance. Muryar Indo ta ji ta na musayan magana da matan su Mudi,Indo na fadin wlh sam ba ku kyau ta ma na ba,amma ba laifin ku ba ne,laifin mazajen ku ne,idan ku be haife ku ba ai su ya haife su. Tare su ka ce eh mun ji din,yo ba shi ya ce a bashi garwashin ba,sai mu hana shi?ace mun yiwa siriki rowa? Muna fama da yara muna fama da tsoho,ai idan ba a gode mana ba ba a zage mu ba. Baba kwance gaba daya hannun sa na dama ya kone,yatsun duk sun durkushe,sai nishi ya ke dan azaba,bakin sa karkace daga alama barin jikin sa ya shanye. Hajjo ta yi sallama jiki sanyaye. Indo ta amsa ta na yauwa Hajjo gwara da Allah ya kawo ki,ji yanda Baba ya sanya hannun shi cikin garwashi ya kone dan Allah! Sai ta sa kuka...Matan Su Mudi su ka rude ganin Hajjo,dake sun santa tin kafin ta auri Garbati,tare su ka yi wasa,amma zaman kauye sun tsufe sun tsomare kamar ba sa'annin Hajjo ba. Su ka fara laha'ila Hajjo,Hajjon ce kuwa! Ko ta kan su ba ta yi ba,ta karasa wajan Baba da tin randa ya ce ta zauna wajan Indo ba ta kara sa shi a ido ba,gaba daya ya tsufe ya tsomare saboda cuta da rashin gata. Gaban shi ta zauna ta na hawaye. Jin ana Hajjo Hajjo! Idanun sa runtse sai yayi sauri ya bude ya na ina Hajjo? Ina diya ta Hajjo,ku hada ni da Hajjo na nemi gafarar ta! Indo ta ce yi magana Hajjo,taba shi ya jiyo ki! Hajjo ta sanya hannun ta cikin na Baba,ta kasa magana sai kuku. Tana kuka Indo na kuka. Su kuwa matan su Ayuba sai abun ya zama mu su na kallo. Sani Hajjo ta nema,su ka yi sa'a shigowar sa kumurya kenan,ya ce gashi nan tafe. kafin su iso Indo ke ba ta lbryn yanda aka yi Baba ya kone,wai cewa yayi a bashi garwashi zai yi turare,da ke Baban ba lfy gare shi ba,ya na cikin turaren ya yanki jiki ya fadi,sai hannu ya fada garwashi,gashi bangaran jikin sa ya shanye,ba daman ihu,baki ya karkace ko ya yi ihu ba mai ji bare a ka masa dauki,matan 'ya'yan sa ba sa iya kula da shi,sai da babban dan Mudi ya gifta ta dakin ya ga Baban ya fasa ihu,shi ne fa aka zo aka cire hannun. Mudi da Ayuba sun dawo,sai mita su ke wai laifin Baba ne,shegen rigima na tsoho,ina shi ina turare! Abun mamaki da kudirar ubangiji a nan shine diyoyin matan na sa da ya guja ya ke kyama,ya ke kira da jidali su ke jin kan shi su ke tausayin shi,su kuma 'ya'yan na sa maza da ya nunawa gata sam ba su damu da shi ba,shi ne ma ya zame mu su jidali su

Chapter 6 of 8