Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 8
ki ka fita zaki sa na yi abunda daga ni har ke za mu yi danasani,i tell you! Rai bace ta ce zan fita,ka yi duk abunda ka ga dama,idan har abunda ka yi jiya be hana Suraj kara zuwa waje na ba,to babu abunda za ka yi ya hana shi,no way! Ya saki murmushi tare da fadin way! Yayinda ya bude motar,ya ce as u wish. Ai kuwa sai ta fita. Khalid ya girgiza kai tare da fadin dax it! Da ba ki fita ba Hajjo,wit d feelings am having ryt now,I don't knw wat am capable of. Fitar ta ta karasa wajan Suraj ta na dan Allah ka yi hakuri,ban san za ka zo ba. Rai bace ya ce wayar ki fa? Me ya sa ba ki dagawa? Ta ce wlh ya na jaka ban san....ganin Khalid gefen ta,ya sanya hannun shi cikin na ta ya sa ta daskarewa,za ta fincike da karfi sai ta yi tuntube,da sauri ya dago ta ba tare da bari Suraj ya gane tuntuben ta yi ba,ya hada ta da jikin sa,ya yi hugn din ta kam a jikin shi. Daga ita Har Suraj ba wanda be yi mutuwar tsaye ba! Kwakwalwar ta daskare,ji ta yi kamar zuciyar ta ta daina bugawa...ta yunkura da niyar kwacewa,Khalid ya ruke ta kam,ya kalli Suraj ya ce she mine,stay away! Suraj ya gyada kai tare da fadin na gane,kar ka damu,ya juya zai shige motar shi,Khalid ya saki Hajjo ta daga hannu ta sauke kan kuncin shi,ji ka ke tas ko motsawa be yi ba. idanun ta na spark sanna ta bi bayan Suraj da tuni ya shige motar sa,ta ce Suraj dan Allah,dan Allah fito ka saurare ni! Duk da idanun sa sun yi jajur,sam ba ya gane komai sai ya murmusa,ya ce bazan iya ba Hajjo,idan har zai iya mi ki haka a gaba na,Allah ya kadai ya san me zai yi a bayan ido na,ni namiji ne mai kishin kan sa da abunda ya ke so,na barki lfy,wish you d best in lyf! Ya tada motar sa,ta na Suraj! Suraj! Suraj!! Ina hankalin ya yi gaba,ba ko waiwaye ta na ji na gani ya fita daga rayuwar ta. Ta juyo ga Khalid da ke jingine jikin ta sa motar,ta ce Khalid na tsane ka fiye da tunanin ka,na gode da gudunmawar da ka bani a matsayi na na diya mace! Ta juya za ta shige cike,ya biyo bayan ya da niyar dakatar da ita,amma ina ta shige da sauri. Ya yi aiken yara har ya gaji,gashi wayar Sani na wajan sa bare ya kira shi,dan ya san tabbas Sanin ba ya nan ne,da ya na nan aiken da ya ke ta mu su da tuni ya fito. Da wannan ya juya ya koma kano,ran sa shi ma ba dadi ganin halin da Hajjo ta shiga. Wata daya ba Suraj,duk yanda za ta yi ta ji daga gare shi ya yanke. Ta yi kokan har ta gaji,ita bakin cikin ta zubar ma ta da mutunci da Khalid ya yi a gaban Suraj,ya ma zai yi ya ma ta haka,Khalid da ko hannun ta be taba kokarin rukewa ba yayi hugn din ta gaban wanda ya ke san ta,ya ke so ya aure ta tsabar shi bai da adalci! Kamar Suraj din shi ma Khalid raban ta da shi wata daya kenan,ya raba ta da me san ta ba dole ya dauke wuta ba! Abunda Hajjo ke fadi kenan duk sanda ya zo ranta,gashi kuma ya na yawan zuwa din. Ta yanke shawarar yin aure da gaggawa ta karbe diyar ta ko Allah ya raba ta da Khalid ta huta. Bangaran Khalid kuwa karfin hali kawai ya ke,so dayawa ya kan dauki mota yayo hanyar kumurya sai ya kai rabi sai kuma ya sake shawara ya dawo. Ko hanya ba ta hada sa da asibiti ba sai ya san yanda yayi ya yi zagaye ya biyo ko Allah zai sa ya sa ya hadu da Hajjo. Har cikin ransa missing din ta ya ke,missing din kallan ta,kamshin ta da uwa uba fadan su. Wani sa'in shi kadai sai a ganshi ya ma murmushi har dariya ma,toh ya tuno wata rigimar ta sa da Hajjo,hatta randa ya fara ganin ta tana fada da dan adaidaita akan naira hamsin ya tuna dariya ya ke sosai,it appears dat Hajjo ta shiga rayuwar sa. Ba kuma mai yawan tado ma sa da Hajjo kamar Neena,da ta yi wani abu ko be yi niyar tuno Hajjo ba sai ya tuno ta,kan ka ce mai sai ga Khalid ya fara fita hayyacin sa,hankalin Hauwa ya fara tashi dan ta kasa gane me ke damun mijin na ta,har ta fara zargin ko rashin haihuwan ta ne,ita ma ta fara daga hankalin ta,ta zaunar da shi tai ta ma sa kuka,ya ce kar ta damu,ba komai amma ta ki ji,sai kawai ma ta kai korafi wajan Hajiya. Hajiya ta yi kiran sa,su ka sa shi a gaba ita da Jabir a lalle sai ya fada mu su damuwan shi,Hajiya ta ce ji fa har ya fada,ko wani abu Hauwan ta yi ma ne? Khalid ya girgiza kai ya ce lfy lau fa,ita dai ta damu kan ta,na fada ma ta ba damuwan ta ba ne! Jabir ya ce ya za ka ce damuwan ka ba zai zama na ta ba? Shez ur wife bro. Hajiya ta ce Khalid,na san da akwai da abun da ke da mun ka,hakan nan ba za ka fada ka ramr haka ba,let d cat out of d bag!ya kalli Jabir,ya ce Hajiya ya dan ba mu wuri...Jabir ya ce ku ji mara kunya,ba in da zani,Hajiya ta ce ka dan ba mu wurin ma na Jabir,Jabir ya ki motsawa,ya ce ai damuwar Khalid shi ma damuwar sa ce. Da dai su ka ga da gaske be motsawan,Hajiya ta ce Khalid ya yi hakuri ya kyale sa,ya fadi damuwar sa. Khalid ya dan sunkuyar da kai saboda nauyin abunda zai fita da ga bakin sa,ya ce Hajiya wlh kan maganar Hajara ne......wato wani irin dariya Jabir ya sheke da,har da mingirowa daga kan kujera!,ita kan ta Hajiyar daurewa ta yi ba ta yi na ta dariyar ba,ta fara yiwa Jabir fada ka ga yayan banza,menene abun dariya?.dole ya ce ka bashi wuri. Khalid ya murtuke fuska,dan ya san za a yi haka. Jabir na kwalla tsabar dariya ya ce Khalid yau kuma ina tunkaho da ji da kan na ka? Ina kuma takamar? Nan fa ce min kayi da ka fada ma ta murna za ta hau,ai ni da na ji shiru na zaci an gama magana,ashe kanina na nan ya na garuwa! Khalid ya ta shi a fusace zai fita,Hajiya ta dakatar da shi,ta ce dawo ka zauna,shi ya kamata ya fita,idan ba za ka bashi shawara ba ka tashi a sauka lfy. Da kyar ya iya daina dariyar. Hajiya ta ce ba na so na sa baki zancen nan na ku da Hajjo,shi ya sa ka ji na mu ku shiru,amma yanda za a yi yau ka sake komawa,ka gwada shawo kan ta,idan ba ta yarda ba,sai mu sa baki,ko Jabir? Ya na murmushin mugunta ya ce haka Hajiya,ka je ka lallabo child abuse din ka,ka kwantar da kai,ba wai ka je da gadara da jiji da kai yanda ka saba ba,kila ka shawo kan ta. Duk da dai ta shakiyanci ya ke maganar,shawarar ta yiwa Khalid,ya tashi da sauri ya na fadin yanzu hudu na san ta na kan hanyar komawa,bara na yi sauri na shirya na tafi,ya fita da sauri,ya na jiyo dariyar Jabir,shi abun ya ma sa dadi. DEDICATED to The Women Of Virtue (group) DIYA MACE Har in da za ta sami mota Ayush ta sauke ta,ta na dada ba ta baki akan halin da ta ke ciki. Hajjo ta ce ba komai,ta so dai in ma rabuwa za ta yi da Suraj suyi na girma da arziki,ba irin wanda su ka yi yanzu ba. Ayush ta ce kar ta damu,a hankali zai gane. Su ka yi sallama,ta hau motar da zai kai ta kumurya. Da ke a tasha ta sauka sai da ta kara hawa wata motar,ta sauke ta a titi,ta tako dumin karasawa gidan Indo. Ta wuto ta wata majilasar yan zaman banza,suna ganin ta su ka fara maganar ta kamar yanda su ka saba duk sanda ta gifta ta wajan,wani ya ce ummmm ga fa iyayen boko,wa zai ce wannan diyar garin nan ce! Gaba daya sai saura su ka sa baki a ka sa Hajjo a faifai,cikin su har da Nuhu abokin Garbati,sam ba ta lura da shi ba. Takalmi ya sa bi bayan ta,ya ga gidan da ta shiga ya tabbatar Hajjon ce da gaske sannan ya juya da sauri sai gidan su Garbati. A kofar gida ya tadda shi,ya yi dakal dakal da shi,ga kazanta ga talauci,ga rashin haihuwa,ya yi aure auren har ya gaji amma shiru be sake samun haihuwa ba,sai ma mata da ya ke aure mai nakada ma sa na jaki duk sanda be kawo na cefane ba,Iyalle da Baba kadai ke iya cetan sa. Yanzun ma tunanin inda zai samu na dare ya ke Nuhu ya zo ya tadda shi. Bayan Hajjo ta yi wanka ta na cin abunci sai ga yaro ya zo ya ce wai ana sallama da Hajjo,ni kuma? Kai ka ce ba ta nan. Indo ta ce ba a haka Hajjo,ko lekawa ne ki yi mana ki ga wake sallamar,je ka ce ta na zuwa. Rai bace ta cire hannu daga abunci,tuwo ne miyar yauki,ta wanke hannu,ta yafa mayafi ta fito. Lekowar ta ta yi arba da Garbati da Nuhu. Cikin mamaki dan ta gane su sarai ta ke kallan su,shi kuwa Garbati sam be gane ta ba,zubewa kasa yayi ya na Hajiya ina wuni? Nuhu ya dan bige shi tare da fadin kai dallah tashi Hajjon ce fa,dallah Hajjo ce,gane ta ne ba ka yi ba! Garbati ya tashi da sauri ya na aw aw ashe! ya kalli Hajjo da kyau ya ce yasin ita ce,Hajjo ai kin zama kamar diyar yan birni shiya sa ban gane ki ba! Murmushin ta kaici ta saki,ta ce lfy? Garbati me ya kawo ka guna? Garbati ya ce eh na'am? Nuhu ya zingure shi. Sannan ya ce dama dai kin san saki daya na mi ki,na zo ne mu sasanta mu gyara auren mu ko kuwa ki bani diya ta......dariya Hajjo ta sa,har ta kusa kwarewa,Garbati ya ce yo menene abun dariyar? Kar fa ki bata min rai na! Ta na dariya ta ce ko ba ran ka ba? In yayi dubu toh zai dauwama a bace Garbati! Tin dosowar Khalid layin ya hangi Hajjo tsaye tare da wasu,har zai fara kunar rai sai ya ga wasu almajirai ne ma,ba shakka sadaka su ka zo nema,sai ya saki ran sa ya faka motar ya fito. Tin da Hajjo ta ke ba ta taba farin ciki da ganin Khalid ba sai yau,ya fito tas da shi cikin farar shadda ta sha bugu da guga,dinki boda an masa aikin sama da shudin zare,ga wani shudin hula da ta sha kari ya sanya ta a karkace,ga takalmin sa shudi,hunnun ruke da mukullin mota ya karaso wajan su Hajjo,tuni kamshin sa ya maye su,su kan su su Garbati sun kiyaya. Ta kasa dauke ido da ga kallan shi,ya ce Suger yanda ki ke kallo na.... kar ki damu i miss you more!ya kashe ma ta ido. Ta dauke kai ta na fadin in ba ka yi fariya ba ba sunan ka Khalid ba. Murmushi yayi tare da fadin na zo mi ki da magana mai muhimmanci yi sauri ki sallame su,taimako su ka zo nema gurin ki ko? Ya sa hannu a aljihu ya fito da dubunne farare kal ya ce nawa ku ke bukata bayin Allah? Ganin kudi makudai hannun Khalid tuni hankalin su ya tashi,Garbati ya ce eh na'am diya ta na zo karba,diyar ka? Khalid ya maimaita,ya kalli Hajjo ya ce Suger kin kuma fara ruke diyar mutane? Turo ma sa diyar ta sa ma na ya kama gaban sa,if u realy need a daughter dat much da kin fada min na kawo mi ki Neena. Hajjo ta murmusa tare da fadin ai Neena ya ke nufi! Khalid ya kalli Garbati ya ce kina nufin wannan local champion din is ur.....ex- husband ta karasa ma sa. Sai da yayi dariya mai isar sa,sannan ya ce amma Allah ya isan ki Suger. Ya mayarda kudin sa cikin aljihu,Nuhu ya hadiyi yawan bakin ciki ganin komwar kudin,Khalid ya ce kun ga wannan? Mata ta ce! Karo na farko da ya kira ta mata ta ba tare da ta musa ba. Ya kuma ce diyar da ka ke magana akai,tin shekara gomashabiyu da su ka shude ta zama diya ta. Ran da na sake ganin ku anan sai na sa an kama mun ku,an kulle am batar mun da ku! Abun ku da yan kauye tuni su ka tsorata,dama ga damin kudi sun gama gani hannun Khalid ba mamaki ma su ne masu kasar. Garbati ya ce ba ma sai an kai ga haka ba,bara mu tafi,ya ja Nuhu,su na dan yin gaba Nuhu ya fara sirfa ma sa masifa,wai ai gashi ya mu su asara,mai makon ya hakura su zauna a almajiran da Khalid ya yi zato,ko ya ce a ba shi wani abu ko a bashi diyar sa,yanda su ka yi za su fada. Shi ko Garbati ganin yanda Hajjo ta koma,ga kuma wanda ke kiran kansa mijin ta ne ya kashe ma sa jiki,wai yar Hajjon sa da ya sani a matsayin matar sa,Allah kenan! Allah kenan! Allah kenan! Abunda ya ke ta maimaitawa kenan. Bayan tafiyar su Hajjo ta ce me ya kawo ka mallam? Khalid ya murmusa ya ce is dat a way of sayin thank you? Ta ce thank you for wat? For saving u from dat local champoin u ar callin an ex-husby!Hajjo ta ce ko ba ka zo ba dama zai tafi,ya ce u ar glad am came Suger,admit it. Ta yi shiru. Da ya ga ba ta niyar magana ya ce magana za mu yi,za mu iya zama a soro? Kafin ta ba shi amsa ma har ya shiga,ta ce dan ma su gida! Ya ce na'am biyo shi ta yi ta ce no ba magana na yi ba. Murmushi kawai ya ma ta dan ya ji abunda ta ce saraj. Ta shige ciki dauko abun zama,ta ke fada ma Indo Khalid ne fa ya zo. Indo ta ce shi ne za ki zaunar da shi a soro? Cikin awaki,ki shigo da shi tsakar gida mana. Ta ce toh,ko dan darajar korar ma ta da Garbati da ya yi. Sai ta dauko tabarma duk da ta san ba ya zama kan tabar ma ta shimfila,sannan ta ce ya shigo ciki. Ya shigo sai ya ga tabarma,ta na jira ya ce ba zai zauna ba sai kuma ya ba ta mamaki ya zauna. Indo ta fito suna gaisawa sai ga Hajjo nan ta kawo ma sa ruwa a kofin roba,bayan ta san baya sha ko cin abunci a roba. Indo ta ce ya za ki kawo ma sa kofin roba ga na karfe Hajjo,ta na murmushin mugunta ta ke kallan sa,ta ce ya fi san na roba,ko Khalid? Shi ma murmushin yayi,ya san abunda ta ke yi,dan haka sai ma ya daga sha ya koshi ya aje sannan ya ce kwarai kuwa. Cike da mamaki Hajjon ta ke kallan sa. Sai ta kara da bara na kamasa abunci,na san shi da san miyar yauki. Ihu ne kawai Khalid be kurma ba,ba shakka Hajjo niyar ta ta kashe shi,duk abun da ta san ba yayi shi ta ke ma sa,wa ya sani ma ko guba za ta sa ma sa a abacin ya mutu ta huta,duk duniya idan akwai abuncin da ya tsana ya bi bayan miyar yauki. Ciki Indo ta koma ta na fadin saka ma sa mana,ki hado da yajin daddawa ma. Toh ta amsa cike da farin ciki. Ta kawo ma sa tuwon. Ga mamakin ta sai ya wanke hannu,ya dan ci kadan,dandai ya kunya ta ta,amma da kyar ya ke hadiya,har ya dan bata ma sa gaban riga. Bayan ya wanke hannu ya zauna ya ji zuciyar sa na tashi,ya ce dan Allah suger taimaka min da leman tsami,da har za ta hana shi,sai ta tausaya ma sa,ta dauko ta yanka ma sa,sai da ya dan sha kadan sannan ya samu nutsuwa,ya dago ya kalle ta,ya ce come here Suger,ya nuna kusa da shi. Ta harare shi ta ce Hajara ce ba diyar ka ba da za ka min irin kiran yara. Tashi yayi ya na murmushi,ya zo gaban ta,ya durkusa gwiwowi biyu a kasa,ya ce Hajara yau ga Maighty Khalid gaban ki,ya zo da kokan baran sa......baki bude ta tsaya ta na kallan sa. DEDICATED to The Women Of Virtue (group) [11:38pm, 6/10/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE Hajara ki yi duba da soyayyar da mu kewa diya daya,diyar ki,kuma diya ta,ki amince na zama miji a gare ki dan cigaba da gina zuri'ar da za su kasance tsatso daya,idan ki ka ki aure na,za ki raba ni da diyar ki,ta riga ta shiga rayuwa ta,haihuwan ta ne kawai ban yi ba. Kuma za ki iya auren wanda kuma zai hana ki rukon ta,tin da uba aka sani da alhakin riko 'yaya ba uwa ba,kin ga kenan mun yi biyu babu. Hajjo ta ce dan Allah ka tashi,kar wani ya gan ka haka na banu. Ya ce answer me first sai na tashi. Ta ce ba zan iya auren ka ba Khalid...saboda me ya sa? Saboda am nt ur type? I wil try to adjust to ur type,kawai ki fada min ya type din na ki ya ke. I promise to b good,zan yi respectn din ki untill my last breath,zan kuma so 'ya'yan mu na ba su kulawa kamar uba na kwarai. Hajjo ta ce ba soyayya,ka san ba na san ka,ta ya za mu zauna? Khalid ya murmusa,ba soyayya,amma akwai respect,ba kya so na,i can do wit dat,ni ma wai san na ki na ke ba,amma ina san diyar ki Ameena zan kuma so yaran da za mu samu a gaba inshaAllah..duk da dai ita ta fara furta zancen rashin soyayyar sai da amsar ta shi ta ma ta daci,ita ta fada ne dan ta na san ji ya yake ji game da ita,ashe it is ol abt haihuwa da kuma diyar ta da ya ke so. Gashi ita har ran ta ta na jin sa,wanda kuma ke san na ta ya raba ta da shi. Yawun takaici ta hadiya dan jika makogaranta da ya bushe,ta ce ba ni kadai ba ce mace mai haihuwa a duniya,ka ne mi wata mana! Ya murmusa,ai nan gizon ke saka,ke zuciya ta ta zaba,ke ce zabin rai na,ba dan haka ba da ina tuni ma na yi watsi da zancen,i don't go after gurls,gurls come after me,nd olryt u ar an exceptional. Babu yanda zan yi. Hajjo ta ce ka raba ni da mai sona,Khalid ya amsa da ba zai so diyar ki ba Hajara,dan haka be dace da ke ba! Ajiyar zuciya ta yi,sannan ta ce zan yi tunani a kai. Tunani akai? Kamar ni Khalid na zube gwiwowi na kasa na rokeki amma ki ce sai kin yi tunani?gaba daya kin taba tsarin rayuwa ta,har kin min gibi. Hajjo ta daga kafada ta sauke tare da fadin dax in za ka iya jira,idan kuma sauri ka ke sai ka sake saban lale. Tashi yayi ya na murmushi,ya ce ba sauri,amma ki sani da ga yau bazan sake bibiyan ki ba,da fatan za ki yi tunani da kyau,dan Allah ki yiwa sirika ta sallama,sai na zo maganar auren mu,ya zira takalmi,ya na murmushi ya fice,Hajjo ta bi bayan shi da kallo,kamar ta ce ya dawo ta yarda,dan ba wai yardan ne ba ta yi ba,ta na jin tsananin tsoran kishi da Hauwa,dan ta fita komai,bare uwa uba mai san auren na ta ba ma san ta ya ke ba.nan ta yi zaman ta sai da Indo ta fito ta same ta,ta yi nisa cikin tunani. Da ta matsa sai Hajjo ta fada ma ta damuwar ta ne sai ta fada ma ta yanda su ka yi da Khalid. Indo ta ce to menene na ki na kin yarda? Menene laifin Khalid,Hajjo kar fa ki yiwa kan ki asara! Mutum mai asali ga ilimi da komai na rayuwu? Ya na san ya aure ki,ya na kuma san diyar ki,ba kowani namiji za ki aura ba ya yarda ki zauna ma sa da agola ba,shi gashi saboda ita din ma ya dage ki aure shi,wani zancen ba ya san ki ki aje,ki ka iya zama da Garbati ma bare mutum kamar Khalid? Hajjo ta nisa tare da fadin ni fa kishi da matar shi ne bazan iya ba,ta fini komai,ni da ita ba gami. Indo ta ce Hajjo,ya fa san da matar ta shi ya dage sai ya aure ki,saboda kina da abunda ya ke bukata matar shi ba ta da shi,yar ki da kuma 'ya'ya tsatson ki ya so,kin ga kuwa ba ta fi ki komai ba din kenan. Hajjo ta ce wulakanci ne ban so Indo. Indo ta ce ai kin fi karfin wulakanci Hajjo,bare ma Khalid ba zai wulakanta ki ba,a de bar shi da jin kai,amma ba wulakanci....Hajjo ta dara,ta ce aw ashe ke ma kin san halin nan na shi. Indon ma dariyar ta yi,ta ce waye be sani ba. Allah dai ya tabbatar da alkhairi,ki dai kara nazari Hajjo,ki kuma cire san zuciya ki zabi hanyar da zai fisshe ki. Hajjo ta ce amen amen,inshaAllahu,Allah ya sa mu dace. Ta amsa da amen. Da tunanin Hajjo khalid ya isa kano,shi kan shi ya kasa gane dalilin da ya sa ta mamaye zuciyar sa,gaba daya ta mamaye zuciyar sa,ji ya ke kamar ya kusa fara numfasa sunan ta tsabar yawan yanda ya ke tunanin ta a rana. Duk da haka ya ki yarda wai san Hajjon ya ke,shi a na shi daga Hauwa ba zai iya kara san kowace diya mace ba. Shigar shi gida be ga Hauwa da Neena a falo ba,kai tsaye bankaran Hauwa ya nufa,ya jiyo su a daki. Da shigar sa dakin kamshi da ya sani,ya ke balain so ya shaka,ya bi ta hanci ya shige har cikin zuciyar sa,be san sanda ya yi subul da baka ba ya ce ya na ke jin kamshi Suger? Hauwa da ke zaune kan gado ta na yiwa Neena kalaba,da tuni ta ankare da shigowar sa,ta amsa ma sa zuciya daya ta ce ba Suger ba ne,Humrah ne fa ya dade ajiye a kan dressing mirrow na Neena ta zubar garin tabe taben ta. A sannan ya gane kwaban da ya kusa tafkawa,yayi saurin bin ta ta hanyar yin kwana shi ma ya ce aw Humrah sunan turare? Kai amma yayi dadi,ki na da shi amma ba ki amfani da shi? Hauwa ta ce wlh be dame ni ba ne. Khalid ya karaso kusa da su,ya zauna tare da fadin ni ya dame ni,ki na amfani da shi daga yau. Hauwa ta dara,toh zan sa a kawo min wani,ina kasan kamshin humrah? Tambayar ta sa gaban sa ya fadi,ya na tuninin amsar da zai ba ta da gaggawa Neena ta ceto shi, Daga yanda ta ke a durkushe,ta ce sannu da zuwa Dady. Da sauri tare da maraba da gaisuwar ta ta ya amsa da yauwa sannu my beloved one. Ya kiriniya? Hauwa ta ce kasan ba kiriniya sai shagwaba. Ya na murmushi ya tashi gudun kar a koma maganar humrah,ya ce ki yi san ranki indai shagwaba ba ce,diyar Khalid ki ke. Neena ta ce yauwa Dady. Hauwa na dariya ta ce dama kai ka ke kara shagwaba ta. Ya ce ita diya tilo ya bazan shagwaba ta ba? Hauwa ta ce gaskiya fa. Ya ce in kun gama kwasame ni a bangare na. Hauwa ta amsa da toh. Ya fice ya na dirga sa'ar shi na yau,amma lokaci yayi da zai sanar da Hauwa kudirin sa akan Hajjo. DEDICATED to The Women Of Virtue (group) [11:50pm, 6/10/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE Kusan sati daya kenan raban Hajjo da Khalid,kamar yanda ya ce ma ta din ya daina bibiyan ta,amsar ta ya ke jira. Da ya sanar da Hajiya da Jabir yanda ya yi da Hajjon amma be fada mu su har tsugunna ma ta ya yi ba gudun sharrin Jabir. Jabir ya ce ahaf,dama na fada mi ki Hajiya,jin kai irin na Khalid ba zai bari ya iya shawo kan ta ba,gashi kullum rama ya ke kamar kudin guzuri. Hajiya ta ce Jabir ai sai ka sa baki. Jabir ya ce toh Hajiya,gobe zan je na same ta inshaAllahu. Hajiya ta ce toh Allah ya kai mu. Ba karamin dadi ya ji ba jin Jabir zai sa baki,ya san Hajjo ta kusa shiga hannu kenan. Tattaunawar Hajjo da Jabir a asibiti Hajjo ta nuna amincewar ta kan auren Khalid. Jabir ya ji dadi matuka da yanda Hajjo ta ke ma sa,komai ya ke so ta yi,wuyan ta ya yi magana kamar yanka wuka haka ta ke aiwatar da shi. Ya ma ta alqawarin tsaya ma ta a komai kan auren,sannan kuma ta ba su sati biyu za su zo su nemi iyayen ta dan yanke maganar auren. Da kamar za ta fada ma sa tsakanin ta da Baba,sai ta ga ai kamar tonawa kan ta asiri ta ke,gwara su je da kan su,su ganewa idan su. Da wannan maganar su ka yi sallama. Cikin dalleliyar motar shi da ya sake ya nufi gidan Khalid. Bayan ya gama ma sa tsiya da Allah ya san ya alkhairi,Jabir ya ce albishirin ka? Khalid ya ce goro,bayan motar ka siyi private jet ko? Jabir ya make shi tare da fadin shegen maza,sai na siya ai,ka san da kudin. Khalid ya ce ni ko na san da su,ci ne dai kawai ba a yi. Jabir ya murmusa tare da fadin da kasan albishirin da zan ma ka da ba ka tsaya jan wannan shirmen da ka ke fada min ba...Khalid ya gyara tsayuwa,ya ce toh fadi na ji. Jabir ya ce na ga Hajjo yau. Cikin kaguwa ya ce dan Allah,ya ku ka yi? Jabir ya ce sai ka biya. Khalid ya ce kaiya! Dan

Chapter 4 of 8