Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
Allah ka fada min mana,ban san wasa da irin wannan maganar,haba yaya na na kai na! Jabir na dariya ya ce na ji wannan social bribe din,toh ka shirya nan da sati biyu za mu kai gaisuwa da kuma sa ranar auren ka da Hajjo....baki Khalid ya bude kamar zai yi magana,sai kuma ya rufe,ya kara budewa ya na rufewa kusan sau uku,Jabir ya ce fadi ma na,Khalid ya ce Alhamdulillahi rabbi alamin!Jabir ya ce ko kai fa! Murna ce ta lullube Khalid,fiye da tunanin kuwa,gani ya ke ya haihu ma ya gama dan daga ganin Hajjo za ta yi kwayaye,baze bari ta yi fmly planing ba,yara za ta jero ma sa kamar bene. Ya ce Jabir wlh da na isa na ma ka kyauta da na ma ka,maganar da ka fada min ta yaye min rabin matsala ta. Jabir ya ce ka min mana,girman ka ne. Khalid ya ce ni din banza,me na isa na baka. Jabir na murmushi ya shige motar shi ya na fadin sauran mtsalar ta ka,ka yi saurin kau da shi,ka kuma tuna ma ta Allah ne ya bamu damar mu yi,kar ta yi jayayya da fadar Allah. Darawa Khalid ya yi,ba shakka Jabir ya san sa kwarai ya na iya karantar sa,ya ce madallah da wannan yaya nawa,na gode,Allah ya bar zumunci. Ya tada motar shi ya ce ameen dan rasulillahi,kar fa ka fara ma ta jiji da kan sosai,ka bari a daura kar ta ce ta fasa! Ya na dariya ya figi motar sa,Khalid na daga ma sa hannu,sannan ya juyu gida,ya fara tsara wasikar da zai karantowa uwar gida Hauwa. Kwance jikin shi,bayan ya gama nuna ma ta duk duniya ba diya mace kamar ita. Ya kira sunan ta,Hauwa?Jin ya kira ta ba tare da ya ce baby-luv din da ya saba fada ba musammam lokaci irin yanzu ta san da wani abu. Ta amsa da na'am. Ya ce kin san shekaran mu nawa da aure? Ta ce sha daya. Ya murmusa tare da fadin,ol those years da san ki ke kadai na ke kwana na ke tashi,haka ma har tsawan shekarun da Allah ya kindaya ma na,you ar d love of my lyf. Maganar ta sa tai ma ta dadi,ta dada kwanciya jikin sa,tare da fadin tell me more,ba ta san more din ba mai dadi ba ne. Sai da yayi shiru,sannan ya ce kin san dai Allah ba ya cutar da bayin sa,sai dai bawa ya cutar da kan sa,Hauwa ta ce haka ne. Ya ce kin san kuma kowa akwai kaddarar rayuwar sa..gaban ta ya fara faduwa,ta ce haka. Ya kara da kin san Allah na jin kunyar macen da be bawa haihuwa ba? Hauwa ta gyada kai,ta ce eh,ki tabbatar Allah na tare da ku,ya kuma san da ku,ku din ma mata masu daraja ne. Ya sake yin shiru,Hauwa ta ce ina jin ka. Ya ce Hauwa ki saurare ni da kyau dan Allah,wlh ban taba san kowace diya mace ba sai ke...zuciyar Hauwa ya fara kaduwa,ta ce dan Allah fada min,menene wai. Khalid ya nisa,ya ce aure n ke son na kara.......a razane ta dago daga jikin sa ta na kallan sa kamar wanda ya yi sabo,ta ce aure? Wasa ka ke ki Khalid! Aure fa? Kai ba da gaske ba ne! Yi shiru kawai mu kwanta mu yi bacci. Shi ma tashi yayi zaune gami da ruko hannun ta,ya ce ba wasa na ke ba,ba kuma ba dan ba na san ki ba ne....idanu cike da kwalla ta ce Khalid,me ka ke fada haka,ba ka san abunda ka ke fada ba! Ta ficge hannun ta,ya ce Hauwa ki saurare ni! Ta ce me za ka ce min? Ina jin ka! Ya ce Hauwa ki tausaya min,tsufa na ke,wlh duk yanda na so na hakura na kasa,ina san yara......sai ta fashe da kuka,ta na fadin dama na sani,dama na sani. Ka kasa hakuri? Dole ka kasa mana tunda ba kai ba ne da ralural ba! Bambamcin diya mace da namiji kenan,da kai ne da matsalar ka san haka zan hakura na zauna da kai ba ma me ji,amma yau dan ni ce gashi za ka tuzar ta ni....ya yi saurin rufe ma ta baki,ya ce haba Hauwa,kar ki manta bambamcin diya mace da namijin har da umarnin ubangiji da ya ce mu auri hudu,ko uku ko biyu har zuwa daya,manzo sallallahu alaihiwasallam be zauna da daya ba Hauwa,ya ce mu auri fiye da daya har zuwa hudu in har za mu iya adalci. Hauwa manzo sallallahu'alaihiwasallam ya ce mu hayayyafa dan mu zamo abun alfahari a gare shi ranar gobe kiyama,shin da wannan damar Hauwa na cigaba da ruyuwa yanda mu ke ki na gani na yiwa kai na adalci kenan? 'Ya 'ya na ai na ki ne Hauwa...ta na hawaye ta ce ni da ban haifa ba,ta yaya za su zamo nawa? Sanin kan ka ne Neenan da na ke gani kamar tawa ma an kusa raba ni da ita. Ya ruko hannun ta tare da fadin babu mai raba ki da ita,saboda na tabbatar da hakan ya sa na zabi na auri mahaifiyar ta.....dif Hauwa ta ji ta dai na ji,ta daga ido ta kalli fuskar Khalid da ke ma ta haske duk sanda ta daura idanun ta akai,yau sai gashi ya ma ta duhu dulum. Hauwa ba ta ji ba ta gani ta cire hannun ta daga na Khalid. Ta tashi za ta fita,shi ma din tashi yayi da sauri ya na Hauwa,Hauwa! Ina ba ta tsaya ba,ya bi bayan ta da sauri,ganin haka sai ma ta sa gudu,ya na biye da ita,ta yi saurin shiga bankaranta ta kulle. Sai ta zube kasa ta na kuka mai ban tausayi. Khalid yayi yayi ta bude ta ki,dan haka shi ma sai ya sami waje ya zauna daga jikin kofar,ya na jiyo kukan ta,ya rasa me ke ma sa dadi nan duniya. DEDICATED to The Women Of Virtue (group) [12:02am, 6/11/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE Hajjo ma a na ta bangaran bacci nan ba ta yi ba. Tin da ta amince da auran Khalid ta kasa nutsuwa. Sai da ta dage da karatun alqur'ani,da kuma nafilfilu Allah ya sa hakan alkhairi ne. sannan ta samu idanun ta su ka rufe. Washagari da sassafe Hauwa ta tafi gidan su. Da ke iyayen ta na arziki ne sai su ka ma ta tatas,su ka zarge ta da san kanta,mutum ya iya zama da ita tsahon shekarunnan ba haihuwa,dan ya ce zai kara sai ta tada hankalin ta,ita ba mai ba shi shawarar ya kara ba ne! Yayyar Hauwa mai suna Zeena wacce bayan iyayen Hauwa sun gama ma ta fada ta zo,tare da kanan ta ne su ka ta zuga Hauwa,wai wlh ta bari ya auri yar aikin gidan su ta fado,duk matan da ke garin nan in ma kishi za su yi auro ma ta class din ta mana! Hauwa ta ce da ta ke mai aiki,yanzu fa doctor ce. Zeena ta ce sai me? Kowa dai ya san asalin ta,turan gini ran zane! Ke ce ma kin dau diya kin manne kamar ta ki! Yanzu kya gane kuran ki! Daya daga cikin kannan ta su ka ta ce Hajjon mummana ma da ita! Dayar ta ce ai kamar ta daya da Neena! Wlh kar ki kara kawo ma na yarinyar gidan nan. Ita kuwa Hauwa har lokacin jin Neena ta ke har ranta,dan haka ta ce ah ah fa,ba ruwan yarinya,ku dai taya ni bakin ciki amma kar ku kyarar min Neena! Hada baki su ka yi su ka ja tsaki. Mahaifiyar Hauwa ta shigo,da ke ta dan cinci maganar,ta ce maza ki biye mu su ki yi biyu babu,su zuga ki Neenan ma ki rasa,kin dai ji shawarar da mu ka baki! Hauwa ta ce uhum. Khalid da ya tashi ya ga Hauwa ba ta nan ya san za a yi haka. Sai cewa yayi da Neena maman na ta ta je gida ta yiwa dady sallama dan ba ya so ta gane ta yi abunda ba ta taba yi ba,wato yaji,shi zai kai ta makaranta,da ke Hauwa ke kai ta kulli yaumin,ko ya ce zai kai ta hanawa ta ke. Duk da hakan ya yiwa Neena wani iri,sai ta amsa da toh. Da ya sauke ta makarantar ya biya ta gidan su Hauwa. Iyayen ta su ka ce ta fito ta bi mijin ta,har da bashi hakuri,tare da mu su dan nasiha. A hanyar komawan su gida ba wanda ya ce da dan uwan sa kala. Sai da su ka shiga gida,Hauwa ta ce da Khalid me ya sa Hajjo? Me ya sa za ka zabi Hajjo maimakon wacce ta isa,na san yes isasshiya ce zan iya kira da sunan kishiya?yayi mamakin maganar na ta,dan shi zaman sa da Hauwa ya san mace ce wacce ba ruwanta da arziki ko rashin arzikin mutum,mace ce mai saukin kai,amma kishi na neman sauya ma ta hanya. Murmushi kawai yayi ya ce ki yi hakuri Hauwa. Zai wuce ta shagaban sa,ta ce me ya sa ita? San ta ka ke? Ya girgiza kai,alamar ah ah,ya ce ke kadai na ke so. Ta ce toh ka sake wata! Ya ce ba zan iya ba! Ta ce y her? Ya ce ita zuciya ta ta zaba,ki yi hakuri Hauwa. Yayi saurin shige ta ya shiga bangaran sa gudun ganin saukar hawayen ta. Nan ta zube ta na kuka,ta na fadin wlh san ta ya ke! Mayaudari! Makaryaci! Santa ya ke wlh!!!nan ta karaci kukan ta ta koshi. Jin Khalid shiru ta san ya bi ta kofar baya ya fice,ita ma ta lallaba ta shige dakin ta ta kwanta,tuni ta fita da ga hayyacin ta. Da azahar ta na tunanin Neena a makaranta dan ba ta ji za ta iya fita,sai ga ta ta shigo dakin sanye da kayan makarantar ta,da alama dawowar ta kenan. Ta ce Momma sannu da gida,ya ba ki zo dauka na ba sai dady? Ba ki da lfy? Ta zauna gaban ta kamar za ta shige cikin ta. Hauwa ta kau da kai ta na ban da lfy,Neena ta yi saurin ruko hannun ta,Dady ya kai ki asibiti? Cikin ranta cewa ta yi ai shi ne asibitin tinda shi ya daura min,azahiri kuma hawaye ne su ka fara zuba daga idanun ta,ganin haka Neena ta rude,tuni ta fara kuka ita ma,ta na pls Momma ki yi shiru na kira Dady mu je hosptal,bara na kira Uncle Jabir. Hauwa na hawaye ta ce rashin lfy na ba na hosptal ba ne Neena,ki min addua kawai dan na kusa zaucewa,aure Dadyn ki zai kara... a razane ta ce aure? Me ya sa? Ya dai na san mu? Hauwa ta ce ki tambaye shi da kan ki. Ai kuwa sai ta tashi fuuuuu ta fice,a falon sa ta tadda shi,ganin yanda ta shigo ga fuska shabe shabe da hawaye sai ya tsuke fuska,ya ce ya dai? Ta dan yi kasa da murya ta ce Dady wai za ka kara aure? Ya ce haka ne. Ta ce Dady saboda me ya sa? Ya ce kin yi kankanta,ba za ki fahimce ni ba yanzu. Ta ce ka dai na san mu ne? Ya ce na fi san ku akan kowa...ta ce plss Dady idan ka na san mu kar ka yi. Ba ta taba rokansa abu ya ki ba,amma wannan karan ta zo da maganar da ba wacce ta isa fadan ta ya amince idan ba Hajiyar sa ba. Ya ce ki yi hakuri Neena,it is for your own gud,dukkan ku,ina san ku,amma dole sai na yi. Idanun ta cike da kwalla,yayi mamakin yanda yar yarinya wai itama ta san ta ya wacce ta dauka mahaifiyar ta kishi,kai kishin mata daban ya ke. Juyawa ta yi za ta koma,sai kuma ta dawo ta ce wa za ka aura Dady? Ba tare da ya ji komai cikin ran sa ya ce Hajara ce wacce ake kira Hajjo,ta ce Anty Hajjo ta gidan Hajiya? Ya ce eh. Ta ce Momma ba ta so,Allah ya sa ka fasa Dady. Kallan ta ya ke kawai,Hajjo kawai a tsaye,da ta san matsayin Hajjo a rayuwar ta,da ta fi kowa farin ciki,amma a sannu za ta fahimta,har yanzu yarinya ce. Sai da ta fice,sannan ya koma ya kishingida. Ya shedawa Hajiya,har ta fadawa yayye da kannen Baban maza,su za su yi komai har sa rana da kai lefe,lokaci ya canja,ya fi san mazan su kai dan a rage bidi'a. Sati biyu su ka dauka kafin Sani ya mu su jagora zuwa wajan Baba,da ke dama Baban ya san Khalid sosai,sai gashi har da gayyato yayan sa da kuma Alhaji Baso baban Garbati,duk da kuwa ba wai warkewa yayi garau ba,jikin na sa na tashi lokaci lokaci,karfin hali ya ke kawai. Lokaci guda su ka bada kudin na gani ina so,ga kuma kayan sa rana da lefe,su ka ce wata uku su ke so a sa,ba mu su su Baba su ka amince,musamman yayan Baba da ya gaji da surutan jama'a wai kanin sa ya bar yarinya ta lalace ta zama yar boko ta ki aure. Lefe ma na gani na fada da Khalid ya hada cikin gaggawa su ka sauke su gaban su Baba. Su Baba sun yi mamakin yawan akwaitinan,ko da bakin su ka tafi bayan an basu tukwicin su daga kudin da su ka kawo bisa al'ada tuni magana ya fara zagaye gari,an kawo laifen birni gidan Alhaji Mamman,an sauke arziki gidan Alhaji Mamaman. Shiko Baba da ya san wacece Hajjo da irin rayuwar da ta yi a baya ya san kadan ma ya gani daga sakayyar alkhairi da Allah ke yiwa Hajjo. DEDICATED to The Women Of Virtue (group) [12:17am, 6/11/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE Hajjo ta na zaune tsakar gida,ta cika ta yi fam,fashewa ne kawai ba ta yi ba. Sai ga Indo ta shigo ta na guda,wato ta gano kayan Hajjo kenan,har da takawa,ta na rai dai,rai dai,rai dai! Ina ma Inna ta na raye ta ga arzikin autar ta,Hajjo? Tin da na ke ban taba ganin kaya,kaya dai irin na akwatin lefan ki ba!anjiman nan ma Baba ya ce a zo a kwasa a kawo mi ki idan Sani ya sami lokaci. Ko a jikin ta,Hajjo ta ce hmmm. Indo ta kara da wata uku aka sanya ranar ma.....nan Hajjo ta fusata,ta ce na fasa auren na shi! Indo ta ce iyye? Hajjo ta ce eh na fasa! Indo ta na tafa hannu ta ce ku ga wacce ba a yiwa abun arziki dangin gidan maza! Akan wani dalili? Dan an sa rana wata uku? Hajjo ta ce haba Indo,ki na fa gani tun da na amince da auren mutumin nan be sa kafa ya tako ya zo gidan nan ba,ko waya ma be min ba,ba shawara ta ba komai an tashi an samin aure wata uku,na san Baba zai iya sa awa uku ma ba wata uku ba tinda dama ba kauna ta ya ke ba,amma shi ba sai ya tambayi shawara ta ba!! Indo ta ce gaskiya be kyauta ba,ai na zaci kun yi shawara ne,amma ki ma sa uziri be kai ga a fasa aure ba,ki yi kiran sa mana....Allah ya sauwake! Hajjo ta katse ta,wlh ba zan kira shi ba Indo! Indo ta ce toh sai ki yi hakuri tin da ke ma na ki jin kan ya hana ki neme shi,maganar fasa aure babu...ta na magana ta shige ciki ta bar Hajjo na ta faman kwafa. Khalid kuwa Hauwa ce ta ke gasa ma sa gurasa danya a hannu,gaba daya ta birkita shi,ta hana shi kwanciyar hankali,tashin hankalin yau da ban na gobe da ban. Har ya gwammaci zaman Abuja akan kano,ba dan ya na so ba sai dan ya ba ta lokaci ya yi nesa da ita ko ta huce. Idan ya zo kano shirye shiryen auren sa ya kai shi ko kuma ya leka site din sa ne,inda ake dankara ma sa hadadden gidan sa da ya yi designing da kwakwalwar sa dan zaman mata biyu. Hajjo na ransa kwarai,ya na son zuwa ya ganta,amma ba dama saboda abubuwa sun cude ma sa,gashi ya daga waya yay ta kiran ta,amma ba a dagawa,ashe wayar ta ta faduwa ta yi. Har ya yi fushi ya ce shi ma ya dai na kiran na ta,ta zo gidan sa sa na gaisawa gaba daya. In dan zai aika ma ta da sako Sani kawai ya ke bawa,idan aka kai ma ta ta ki karba,sai Sani da Indo sun ma ta ca ta ke hakura. Ana saura wata guda biki,su Doc Hussaina da yan uwanta likitoci aka kawowa Hajjo kayan gyara,su cikwaidi,zuman mata,tsumi har da turarukan tsugunno. Doc Hussaina ta ce matso nan ki ji diya ta,dan ni fa Hajara diya na ke da ke ba abokiyar aiki ba. Cikin jin kunya ta matsa kusa da ita,sauran matan ma matsowa su ka yi dan sun san Doc Hussaina ba da ga nan ba. Ta gyara murya ta ce Hajara kin shirya yin aure kin shirya zaman aure? Hajjo ta yi shiru,Doc Hussaina ta ce amsa min mana. Hajjo ta gyada kai alamar eh. Ta ce toh saurare ni da kyau,auren dai kin taba yi,amma ki sani wanda ki ka yi da da na yanzu ba daya ba ne,da bambamci,da ba ki san ciwan kan ki ba,yanzu kuwa kin san wacece ke,kuma kin san wa za ki aura,toh fa Hajara sai kin yi hakuri,dan hakuri shi ke zaunar da ko wace diya mace gidan mijin ta,Hajara da ba hakuri da aure dayawa tuni ya mutu,ki yi hakuri,ki toshe kunnuwan ki,ki kuma runtse idanun ki,ki sai ta harshen ki,ki ji ki ji,Hajara ki gani ki ki gani,kar ya hau ki hau,idan ya hau,shafawa zuciyar ki salama ta hanyar ambaton ubangiji,ki tuna Allah ki ke bautawa,ba wai dan shi wanda ya aje ki gidan na sa za ki yi ba,sai ki ga ke kin sauko,da iyaye ma sai an yi hakurin zama bare wani can da ya ganki da hakoran ki ras da wayan ki. Sauran su ka ce ba shakka. Doc Hussaina ta ce kin ga watannin farko na aure,nan su ke fara nuna isa,su a lalle sai sun gwada wannan ikon da Allah ya ba su kan mace tin da ta zama mallakin su,ke kuma daure ki gwada wannan sallamawar da Allah ya yassare mi ki,kwantar da kai,ba komai ba shi girman sa,girmama shi,yi ma sa ladabi da biyayya muddin be wuce gona da iri ba,kar ki yarda ki yi abunda zai rai na ki,duk da ba ke bace matar sa ta farko,dole da tambiyar uwar gida zai tafiyar da ke,da kin ga abunda be dace ba a musulunce da dabi'ance gyara ma sa a dabarance. Kar ki taba yarda wai kin zama daya da miji ki saki jiki,ki na zama anyhw,idan an yi abun dariya ki saki baki ki ta dariya kamar shashasha! Ah ah Hajara raini ya ke kawowa,wlh ba ko wani irin sakin jiki za ki yi da shi ba,kar ki yarda idea din an zama daya ta shiga ran ki,idan ki ka bari ya rai na ki kin shiga uku,ki yi yanda zai yi respectn din ki,ja girman ki ki ja ajin ki,yan da za ki yi reapectn din sa yayi respectn din ki,reapect beget respect. Uwar gidan sa gaba ta ke da ke,ko da kuwa kin girme ta,ita ma ba ta girmanta, tare ki ganta da mijin ta,kar ki yarda daidai da rana daya tunanin ki fitar da ita ya tsurga cikin zuciyar ki,ke ma diya mace,kuma ki na da diya diya mace,ki na da yan uwa,ba za ki so a yi mi ki ko na ki haka ba,ke ma ki yi adalci kar ki yiwa wata,amma fa kar ki yarda ta raina ki. Haka dangin miji,zama da su sai da dabara,zama da su iyawa ne,ki saki jiki a raina ki,ki ja jiki a ce kin ki su,toh sai dai ki ti kaffa kaffa da su,ko uwa tushe daya ku ke sai kin iya takun ki,bare ke zama ki ka taba yi sa su,da kin auri na su toh sun zama dangin miji,tsakanin ki da su kyautatawa,ki bude hannu,ba su,ke dai ba su,kyauta ta na raba ki da su,kar ki zura jiki,kar kuma ki janye jikin ki gaba daya,sama sama,sai wa kanki mutunci kar ki yarda a rai na ki. Tsakanin ki da facalolin ki mutunci,wacce ta ku ta zo daya sai ku yi,wacce ta ku ba ta zo daya ba ruwan ki da ita,kowa ya tsaya matsayin sa,I keep repeatn dis,kar ki yarda a raina ki,kar ki raina kowa. Ki zama mai tsafta,mai kula,mai tattali,mai boye sirri,Hajjo ki rufa sirrin mijin ki,ban da tona sirri,kin san duk abunda ya fita daga bakin ki zuwa kunnan wata ya tashi daga sirri,sirrin ma iri iri ne,akwai na dakin mijin ki,akwai na aljuhun shi,akwai kuma na tsakanin ku,akwai kuma na zamantakewa. Na zamantakewa ne mai wuyan boyewa,yau da gobe dole akwai randa za ki bukaci ki yi sharing abunda ke damun ki akan yanayin zaman auren na ku,ko da kuwa ba solution za a baki ba,ke dai ki fada ki sami sauki,wannan ba laifi idan kin sami wacce za ki yi sharing da ita,toh amma me? Ba kowa za ki fadawa ba,ban da ma iyaye,ke za ki manta,su ba sa mantawa,rukewa su ke a ransu,kawaye ba ko wacce kawa ba ce mai ruke sirri,wasu rashin ruke sirri ma a hilittar su ya ke musammam wacce ta fiya surutu,dan ko gawa za a wanka ba a yi a gaban mai surutu ko wanda ba na ka ba saboda kar ta ga wani abu suruta ya sa ta furta,dan uwa sai kin sami wacce ta ke very close da ke kuma kun saba sharing problems dinki,san samu ki sami mace wacce ta ke ta manyanta,cikin yan uwa ne kawayen mamanki ne,aunties ko ma maman kawar ki,idan kuma kawayen na ki ma akwai ta sirri wacce ki ka aminta da ita shi ma din ba laifi,dan ba a rasa na kwarai,kafin a same su ne aikin,inshaAllahu sai ki ga kin sami mafita asirin ki a rufe... DEDICATED to The Women Of Virtue (group) [12:36am, 6/11/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE Waje yayi shiru,Doc Hussaina ta kara da batun gyara,kin san dai ganyen magarya ko? Hajjo ta gyada kai. Doc Hussaina ta ce toh ki ruke shi,ya na da amfani matuka,musammam da aka hana amfani da soaps da kuma antibacteria,saboda any thing antibacteria is powerful,kuma ur private part is the most delicate part of ur body a matsayin ki na diya mace,wajan akwai flora wanda su ke da amfani,shi kuma antibacteria idan ki ka yi using ba ya iya bambamce tsakanin flora da bacteria,duka ya ke hadawa ya kashe,kin ga anyi ba a yi ba,haka kuma ya na sane mace yawan amfani da su,plus soap wari ma ya ke sawa. Shi ko ganyen magarya na tsaftace jiki kwarai,ya na hana warin gaba,ya na matsi,ya na maganin toilet infections, ya na kuma kara ni'ima,tin daga yanzu ki same she danye ko busasshe, ki fara daurayewa,sannan ki tafasa ki ta ce ki na tsarki da shi da dumin sa ba da sanyi ba. Haka farin almiski,dan kin ga shi ana ma kiransa miski Aisha,wanda ya samo asali daga wajan Nana Aysha Allah ya kara yarda da ita,duk san da ta gama period ta ke amfani da shi,ya na matsi kuma ya dauke wannan karni da gaifi na period. Kin ga ni duk juma'ar duniya na kan yi amfani da shi. Ni yara na da sun fara period na ke koya mu su amfani da ganyen magarya da miski badan komai ba sai dan period kadai kara budurwa ya ke,musamma idan ya na fita da yawan nan,tashi guda ka ji bulum ya sauka,gasu yawancin su suna shiga toilet na makaranta,akwai every possibility na kwasar toilet infection,so da sun gama sai na ba su ganyan magarya su kama ruwa sannan na ba su miski su shafa,ba wai sai sun zo aure ko sun yi ba. Daya daga cikin Docs din ta ce Anty Hussaina tin da kin ce period kadai ya na bude budurwa,ba laifi kenan budurwa ta yi amfani da abun matsai idan ta tashi aure? Doc Hussaina ta ce eh ba wai ba laifi ba ne,kamata ya yi ayi daidai ruwa daidai tsaki,kin ga lokacin mu dake at our tender age ake ma na aure,da yawa dakin mijin mu mu ke fara period,so idan aka tashi mana aure ba wani maganin matsi da mu ke bukata,amma yan matan mu na yanzu an yi period na kusan shekara da shekaru,ga daukan abu mai nauyi,ga tsallake tsallaken kwata mai girma dadai sauran su ya sa mu ke dan bawa yaran mu kayan matsi,shi ma din ba wai na matsi sosai ba,irin su ganyan magarya,ake tsarki da shi,da miski,dama kuma idan za ta yi gyaran jiki za ai mata dukkan da dirot ko farar kaya,wannan ma ya wadatar,ba a dinga tsugonno a wannan,a waccan, a shafa waccan,tusa waccan,garin neman gira a rasa ido,ku ga yarin ta matse gam kamar bango,wata dama a matsen ta ke sosai ba ta san kanta ta kara,sai daga baya a zo ana jinya,wasu har dinki ma,toh ina amfanin haka? In ma matsin sosai za ki yi gwara ki jira a kai ki ki san kan ki,ki gane irin ki sai ki yi matsin da hujja. Toh ga gudun mawata gare ki Hajara amarya. Doctors su ka ce ita kadai ko har mu? Doc Hussaina ta ce har ku da ma da ku ke gidajan ku za ku iya yi,amma yanzu da ita na ke magana ta,duk su ka sa dariya. Doc Hussaina ta ce ki na ji na Hajara? Hajara ta ce eh. Ta ce idan biki ya matso kusa sosai,kafin a fara sai ki sami kankanar ki wanda ki ka san za ki iya shayewa kwallo guda,sai ki yi sallah raka'a biyu nafila,ki fafaye saman kankanan,ki dan caccaki cikin yanda ruwan zai tsatso,sai ki karanta suratul Khafi,Maryam da Rahman ki tofa ciki,ruwan da ya tsotso na kankanan sai ki disa cikin turaren ki da ki ka ware dan amfanin ki ke kadai,kamar humrah,bayan ki tabbata ruwan kankanan ya zuba ciki sai ki aje kayan ki. Ki shanye kankanar ki tsaf ki koshi,turaren ki kuma ki na amfani da shi,inshaAllahu mijin ki zai girmama ki,ya martaba ki,yayi respect din ki,za kuma ki sami daukaka wajan sa wanda shi ake fata. Gaba daya kowa ya fara kai gaskiya ni ma zan yi,ni ma zan yi. Hajara ta ce na gode Anty Hussaina,Allah ya kara girma. Doc Hussaina ta ce

Chapter 5 of 8