Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 8
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels DIYA MACE Khadija sidi Creat by Shuraih Usman Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521 Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya Hakkin mallaka (m) khadija SIDi Khadija Sidi: DIYA MACE Jabir na dariya ya ce da Hajjo kamar fa kin ruda kanin nawa,cikin girmamawa da kuma jin nauyin maganar Jabir ta gaida Khalid,ya amsa idanun sa kanta. Jabir ne ya janye shi ya na fadin wallahi child abuse din nan ta ka ce ka ma bar kokanto yaro! Ta na jin shi ya na wlh Jabir kada fa ka matsa min! Sai na fadawa Nabeela abunda ka fada min rannan! Shegen maza! Ta ciyo Jabir na zagen Khalid,ga dariyar su na tashi kamar su kadai ne a gidan. Hajjo ta saki ajiyar zuciya,damuwar da ke kwance cikin ranta ce ta taso,gaba daya ji ta ke ranta a dagule,ya za ta haifi diya ta na gudun ta? Su ma su rikon ta ba su sheda ma ta wacce mahaifiyar ta ba? Me ma su ke nufi ne? Kai lokaci ya yi da za a dawo ma ta da diyar ta gaskiya! Da wannan tunanin ta cigaba da wanke wanken ta,tsabar bacin rai ma ta kasa katsewa ta je su gaisa da Hauwa. Sai da ta gama tsaf. Can falo kuwa Hajiya zaune tare da su Khalid ana hirar ya bayan rabuwa,Jabir ya tafi gidan sa. Tin fitowar su hankalin sa ke kan hanyar fitowa daga kitchen,Allah Allah ya ke ya kara sa Hajjo a idon sa,ya ga baiwar Allah,kamar da diyar ta kamar an tsaga kara,kawai dai dan ita yar fara ce,ita kuma uwar wankan tarwada,da kuma ita Innar yarinya ce da sai ma ace yan biyu ne.bini bini Hajiya sai ta kalli Inna ta ce yarinya fa ta zama budurwa,yanzu wa zai kalle ta ya ce mahaifiyar ta ce ta haife ta,ai sai dai ayi zatan yaya da kanwa ne. Khalid ya ce wlh kuwa,ni kai na na yi mamaki kwarai da na ga uwar! Ita dai Hauwa da anyi maganar Hajjo gaban ta faduwa ya ke,duk da dai ta san Neenan ta ta ba diyar ta ba ce,amma ba ta ji za ta iya rabuwa da ita,shi ya sa ma ko zancen Hajjon ba ta ma ta,kunga karfin hali barawo da sallama. Hajjo ta fito fuskar ta dauke da murmushi,da Khalid ta fara hada ido saboda dama dai shi ne ya kasa ya tsare ya ke jiran tsammanin sake ganin ta. Ta yi saurin janye idanun ta da ga na shi gaban ta na faduwa,wajan Hauwa ta karasa ta na maraba sannun ku da zuwa,ita ko Inna da ta ga haka sai ta koma gefan Khalid. Hajiya ta ce aw ku ga yar butan uwa! Uwar ta ki ki ke gudu? Hauwa ta ce ina ruwan Neenan Mama,kin san ba ta san ta ba. Maganar ta yiwa Hajjo daci,amma sai kawai ta boye,ta ma dauke kai daga kan Innar. Bayan sun gaisa ta tashi ta ba su wuri,wanda hakan be yiwa Khalid dadi ba,ita kuwa Hauwa hakan daidai ya ma ta. Bayan tashin Hajjo, Hajiya ta bijiro mu su da maganar Inna,hankalin Hauwa ya tashi gudun kar Inna ta gane zancen da ake ta ce da ita ta Neena tashi ki je daki ki kwanta abun ki. Tana tafiya Hajiya ta ce kun dai san ya kamata ba sai an fada mu ku ba,amma na ga alamar ba ku ma shirin yin abunda ya kamata,kamata yayi ayau dinnan ku taho da komai na yarinyar nan ku damkata hannun mahaifiyar ta,ta mu ku kara ai. Idanun Hauwa yayi rau rau zai kawo ruwa,Khalid ya gyara zama,ya ce dama Hajiya za a yi hakan,dama so mu ke mu gama settle....ah ah! Hajiya ta katse shi,yarinyar nan fa alkunya ta ke mu ku,it is high time auta,ku dawo ma ta da diyar ta. Khalid ya sosa kyeya,idanun sa kan Hauwar shi,ganin yanda gaba daya ta sauya yanzu yanzu sai ta ba shi tausayi,dole ya nemo mu su mafita. Ya ce toh Hajiya ta,yanda ki ka ce haka za a yi,ta ma yi kokari ai,amma dan Allah ki ba mu zuwa sati na gaba sai mu dawo da ita din. Hajiya ta ce ko ku fa,Allah ya nuna mana,ya ce amen. Farin cikin Hauwa ya gushe,daurewa ta yi kawai har su ka gama wuni a gidan,amma kowa ya san ta na cikin damuwa. Suna komawa gidan su kuwa,ta samu ta kebe da Khalid sai kuka. Kuka sosai ya ma kasa rarrashin ta dan tuni ta riki ta shi,sai da kukan na ta ya tsagaita,kwance cikin sa ya ke ba ta baki,haba baby-luv,toh menene na kukan? Ta na ajiyar zuciya ta ce ya bazan yi kuka ba? Kasan matsala ta Khalid,kasan ba na haihuwa ba zan taba haihuwa ba ma wasu likotocin da ba su iya magana ba su ka ce....shhhhh ya toshe ma ta baki da dan yatsa,ya ce kema kin ce wanda ba su iya magana ba,ki sa Allah a ranki baby-luv,shi kadai ne mai iya bawa bawan sa kyauta sanda be yi zato ba,shi zai ba mu haihuwa...Hauwa ta ce haka ne,ban fidda tsammani ba duk da kowani indication ya nuna kishiyan haka,amma Beb idan aka dauke min Neena ban san inda zan sa rai na ba,ya zan yi da rayuwa ta,na riga na saba yarinyar ta shige jiki na.. shiru ya yi daga bisani ya ce ba yanda za mu yi,dole mu mayar ma ta da diyar ta,kar ki damu,Allah na sane da mu. Nan fa sai Hauwa ta kara fashewa da kuka,tin ya na rarrashi,har ya kyale ta,kusan kwana ta yi ta na kuka,wai za a raba ta da diyar da ke kiranta Momma. Washagari abun duniya ya ishi Khalid,shi ma din tafiyar Neena na damun shi,babu yanda zai yi ne kawai,da ga shi har matar ta shi babu mai walwala,zuciyar sa na sake sake kala kala,hez 37 yanzu,Hauwa 31,amma ko kwai be taba ajewa ba,shekaru na ja,tsufa da mutuwa na gabatowa,shin rayuwa za ta yiyu a haka kuwa? Da sam haihuwar ba ya gaban shi,sai yanzu da ya manyanta ya fara damun shi,duk da kuwa be taba nunawa baby-luv din ta shi ba. Da yamma ta yi sai ya wuce gidan Hajiya,ganin ta tare da Hajjo zaune cikin dakin Hajiyar sai abun ya bashi sha'awa,ita Hajiyar ma kenan da Allah ya ba ta haihuwa,dan dai kawai ba ta da diya mace ji soyayyar da ta kewa Hajjo da ta yi kusan rabin rayuwar ta a hannun ta,bare shi da be san dadin haihuwa ba,sai akan Neena,wacce tin ta na shekara biyu ta ke tare da shi. Hajjo sanye da doguwar riga baka,ta rufe kanta da mayafin rigar,daga gani fita za ta yi ko kuma daga fitar ta dawo,ganin sa ta yi saurin tashi za ta fita,Hajiya ta ce ina dawo ki zauna,kin ga shigowar Khalid za ki sami damar fita,zauna shima ya taya ni ai,Hajjo ta koma ta zauna a takure. Idanun Khalid kan ta,shi dai mamakin girma,kyau da wayewar ta ya ke,gaba daya ta canza kamar wacce makirin mata ya kyera. Ya dan kalli Hajiya ya gaishe ta,sannan Hajjon ma ta gaisheshi,yanda ta saba cikin girmamawa. Khalid ya ce Hajiya kamar ki na zan taya ki,me zan ta ya ki? Hajiya ta ce jin ta baki Hajjo,sam na ga alama ba zancen aure a gaban ta,ya kamata ta yarda tsayayye ya fito. Dim! Ya ji wani irin mummunar faduwar gaba,sai da ya koma ya dan jingina da bango.... DEDICATED to The Women Of Virtue (group) [7:06pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: DIYAMACE Ya gyara murya ya ce Hajiya ai gwara dai kar a ma ta shisshigi,tin da ba yarinya ba ce,auren nan ta yi na fari dama,kar a azalzale ta a jira na gari ya zo sai ta tsayar din. Hajiya ta ce ahaf,kar ka mai da mu baya kai kuma,wani na gari ya zo? Ai tuni Hajjo na da nagarin ta a hannu...da sauri ya daga ido ya kalli Hajjo,wani abu ne ya tsaya kamar kashi cikin ransa,well obviously mace kamar Hajjo ya kamata ace ta na da manema,plus shi ina ma ruwan sa ne? Tambayar da yayiwa zuciyar shi kenan! Ina ruwan ta da kaduwa akan maganar child abuse? A zahiri tambayar Hajiya ya yi waye shi na garin? Hajjo ta saci kallan sa ta wutsiyar ido,see dis man! Ina ruwan shi da ni da har zai na tambaya kan rayuwa ta! Ni fa shisshigi ne ban so,dan ya na ruke da Inna ta be zama uba na ba! Tafasar da zuciyar Hajjo ke yi kenan. Hajiya ba tare da ta kawo komai ba cikin ran ta,ta ce wani likita ne,Surajo,Jabir ma ya san shi,yaran arziki wlh. Ran sa idan yayi dubu ya baci,ya kasa gane mai ke ma sa dadi,wai ma ina ruwan sa ne! Toh Allah ya sa a yi da mu. Hajiya ta ce amen amen. Hajiya bari na tafi,dama gaishe ki na zo yi na yi da Jabir zan dauko sa daga asibiti,akwalar motar ta sa da ya kasa rage ciki ya sake ta kara samin matsala. Hajiya ta dara ta ce kamar a kunnan sa. Shi ma darawan yayi duk da de ba dadi ya ke ji ba,ya ce kin san dai gaskiya na fada. Zuciyar Hajiya daya ta ce in dai haka ne ka ragewa Hajjo hanya.....Hajjo kamar ta kurma ihu,sam ba ta san abunda zai hada ta da Khalid,da sauri ta ce ah ah Hajiya ba ma sai ya rage min ba sai na hau a daidaita sahu. Hajiya ta ce AKTH zai je,kin ga ina kundila ina AKTH,ai ya fi sauki ya sauke ki..dan kar na bata ma sa lokaci Jabir na jira Hajiya,Hajjo ta kara kan bayanin ta. Da ya fuskanci bin shi ne ba ta so,sai ya ce no ba bata lokaci,mu je na sauke ki kidin. Kamar ta yi kuka ta yiwa Hajiya sai ta dawo,Khalid ya ma ta sallama,su ka fito ya na gaba ta na biye da shi,sai watsawa bayan sa harara ta ke. Ko da su ka kai mota,ya bude ya shiga sai ta bude baya ta shiga ta rufe. Sai a sannan kamshin ta ya mamaye hancin sa,ya bi numfashin sa,kamshi ne mai dadin gaske ga sanyi,da ke ta na amfani da turaren the body shop(indian nyt jesmine) wanda Suraj ke yawan aiko ma ta da su,sai kuma wani hadadde kuma dadadden Humrah da Aunty Hussaina ta ba ta,so wani kamshi ta ke mai rikitarwa,kaji kamar ka janyo ta jikin ka ko ka samu kai ma ka shafa. Ya lumshe ido ya bude,gaskiya babu abunda ya kai kamshi dadi a duniya dadi,zaman Hajjon a baya ya sa ya ki tada motar,sun kai kusan minti goma a haka,shi dai be damu ba,as long as ya na jin kamshin nan,zaman is worth. Hajjon ce ta gaji,ta ce ko motar na da matsala ne?ya ce me ki gani? Ta ce na ga ba mu motsa ba. Ya gyada kai, Yes ta na da matsala,as long as u sitting der,ba za ta tashi ba. Cikin mamaki ta ce ikon Allah,me ya hada zama na a nan da kuma tashin mota? A hankali ya juyo suna fuskar tan juna,tini Hajjo ta daina numfashi na dan sakanni,ganin yanda mischievous idanun shi ke kallan ta,ta yi saurin nisar da na ta idon. Ya lura da yanayin da ta ke shiga duk sanda ya kalle ta,she catches her breath duk sanda ya kalle ta su ka hada ido,kamar yanda shi ma his hrt beat faster dan normal duk san da ya sa ta a ido. Ya na murmushi ya ce am nt a driver Hajiya.....ido a kasa ta ce nan ne wajan zama na a motar ka 11 years ago,u knw dat as well Alhaji... darawa yayi,indeed ba wai kamannin Hajjo ne kadai ya canza ba,hatta maganar ta ta sake,ta za ma brazen! Juyawa yayi ya na murmushi mischievously,ya ce yes u made ur point,noted,so dawo gaba in ki na so mu tafi,idan kuma kina san ki ta zama ne,i wil nt mind,cos i love ur scent,ya sunan turaren ne? Ta ma sa banza,ya dara tare da fadin shi ya kamata a kira a ba rai dadi,i soo much luv it. Ji ta yi kamar ta fasa fitar,sai dai sakon na Hajiya ne,kuma ba ta so Hijiyar ta ga ta ki bin maganar ta da ta fita ta hau dan sahu. Da wannan tunanin ta fito ta shiga gaban,kamshin na ta ya kara shigar Khalid har cikin ran sa,cikin zuciyar sa ya ce Astagafirullah! Allah ka yafe mana ni da wannan baiwa ta ka,dan gaskiya kamshin na ta ya ma sa,kamar ba shi ne mai sauke glass ko dauke numfashi da ta gifta shi. Hmmm duniya juyi juyi kwado ya fada ruwan zafi. Ganin ta dawo din,kuma be motsa ba,ta ce na dawo. Murmushi ya sakar ma ta,wacce ita kanta ba ta san na menene ba,yayinda ya kunna mota su ka fito su ka dauki hanya. Babu wanda ya sake magana har ya sauke ta,ta bishi da Allah ya tsare. Ya amsa amen. Sai da ta shiga gidan da ya kai ta sannan ya kunna mota ya tafi,ran sa cike da sake sake iri-iri ya karasa AKTH. Maimakon Jabir ya taho shi kadai sai ya taho da abokin aikin sa,Doc Ahmad,wai za su aje shi na'ibawa. Khalid na driving amma gaba daya hankalin sa ba ya wajen,kamar daga sama yaji Jabir ya ce wata kanwar ta wa ka ke so? Hajara?....kiiiiiiiiiiiii Khalid ya yi saurin ta ka birki,dan ya kusa bugawa wani jin inda maganar ta su ta dosa. Jabir dake zaune tare da shi a gaba ya daki kafadar sa ya na dan uban ka ka goga yar motar ta ka da ka ke ji da shi kamar kwai! Khalid yayi karfin hali ya murmusa gami da dagawa wanda ya kusa bugawa hannu,cikin ba da hakuri,ya ce ahaf tawa za ta siyi akwalar motar ka goma,ka ga ko dole na ji da ita! Jabir ya ce karya ne wlh,yaro karya ka ke! Gaba daya dariya su ke,Jabir na shirin cigabawa da maganar Doc Ahmad ya ce pls mu yi maganar Hajara,na kusa sauka,ya za a yi ne? Wlh shez exactly the womon of my dream,ga kyau,ga kwalliya irin na matan da su ka san ciwan kan su,ga sanin darajar mutane,ga tsafta.... o yes! Jabir ya katse shi,she is neat,exceptionally neat wlh,ga ga ga ga din Hajjo da yawa su ke Alhaji. Khalid dai ya baza kunne,ya na jira ya ga iya gudun ruwan su. Jin Doc Ahmad ya ce ka tabbata ba maganar kowa as in ba ta sasansan ta da kowa ba? Jabir ya ce etoh gaskiya.. kafin ya karasa Khalid ya saurin dakatar da shi ta hanyar tare maganar...gaskiya nauyin bayani ya ke ma,wato kai ma Jabir ka iya bugan cikin mutum,ka ma sa shiru ya na ta sakin layi,baki bude Jabir ya ke kallan Khalid,Khalid ba kunya bare shakka ya ce Doc Ahmad,na gode kwarai da yabon my wife to be da ka yi,amma an ba da ita. Jikin Doc Ahmad yayi sanyi,Jabir ya ce kut! A gidan ubanwa...... Jabir ka yi shiru kawai,ya dan kifta ma sa ido,ai Ahmad wil undstnd,kawai so ka ke na ji ana yaban Hajarar a gabana dax y,ryt? Jabir ya ma sa banza. Cikin jin kunya ya ce amma gaskiya Jabir ba ka kyauta ba,kullum na ta ma ka maganar yarinyar nan,ashe kanin ka ne zai aure ta ba ka fada min ba? Jabir ya ce kasan Allah Ahmadu....be yi da niya ba! Khalid ne ya kara katse shi,duk bakin Jabir sai gashi be da ta cewa. Doc Ahmad ya ce na gode Khalid,tsaya na sauka a nan. Khalid ya ce haba ai ba mu kai ga layin dan Hassan din ba,bari na karasa da kai ma na. Doc Ahmad ya ce kar ka damu,nan ya isa. Innocently Khalid ya faka,cike da burin kunya Doc Ahmad ya sauka,ko sallama be yiwa Jabir ba. Ya na fita Jabir ya fara sirfowa Khalid zagi,har da kun ga shegen maza! Gidan ubanwa ta zama ur wife to b? Kai wai haka ka dada lalacewa? Karya kuma Khalid? Ko a jikin sa ya ce karya kuma sai ka ce yaro Jabir? Jabir ya ce in ba karya ba har yau she ka dawo da za ka ce kun sasanta da yarinyar nan? Hankali kwance ya ce ni na ce ma da ita na sasanta? Toh da uban wa ka sasanta? Idanun sa kan hanya ya amsa da zuciya ta,yanzun nan na yanke shawara da zuciya ta dat i hav no choice buh making her my wife......ko da kuwa za a maimaita yakin badar! Dariya mai karfi Jabir ya saki,ya ce ko ba da zuciyar ka ba? Ga fili ga doki,ba ma yakin badar kadai ba,a ma yi na uhud!caf kai rigimar ma ka ma ba ta sallah wlh. Na ga dai ba wanda ya kai ka kyarar Hajjo,child abuse ma ka ke kiran ta,amma daga dowar ka ka ga ta zama very beautiful nd sophisticated woman har ka fara san ta? Cikin takama da dagawa ya ce har akwai wani beauty da sophistication da ya dara na ma tar sa na ke aure? Ta hada komai na diya ma ce,she got everyting na diya mace,Kasan ba maganar so,Hajara is nt even my type,kawai larula ce ta sa na ke considering auren na ta,Hajiya ta ce na mayar da Neena,hankalin wife dina ya tashi,plus am getting older kullum,at 37 ban da kids,so zan aure ta ne saboda abu biyu,na fari ka ga Neena za ta zauna guna,logically i wil remian her dad,na biyu kuma d woman wil bear my kids as many as i want.... hmmmm Jabir ya gyada kai,very selfish nd arrogant brother i have,ka san Allah? Kar ka sake ka matsawa yarinyar mutane saboda selfish interest din ka,ta na da wanda ta ke so,u better stay away from her. Khalid ya daga kafada,wannan na ka ra'ayin kenan,wat if shez interested? Bare na san she is,dole shi is cos ko wata mace burin ta ta sami miji kamar ni,ol women wants an outstanding man as a husby,kasan ma ta nawa ke sona ina mu su yabs bare kuma ni da baki na ce zan aure ta,God she should even b grtful,ai ina fada ma ta za ta hau murna,I tell u bro! Jabir ya murmusa,ya ce ba ko ba Hajjo ba? Ayi mu gani,.. Da haka su ka isa gidan Jabir,zai fita Khalid ya ce ya za a yi a min hanyar Hajara ne? Na ga da kai ake kama kafa....Jabir ya ce for ur imformation,yarinya na da correct man,a Doctor so kar ka bata lokacin ka!Khalid ya ya yi mika ya na mischievous murmurshi ya ce ko kai ne correct man din,d so called doctor sai ka saurara ka bar wajan bare kuma wani bare,Khalid ne fa kanin ka,taba neman mace na rasa ba! Sai dai ban nema ba! Jabir ya murmusa ya ce wannan karan ka ma rasa! Khalid ya ce no ka bani five month za ka ga Hajara a gida! Jabir ya na dariyar yanda Khalid ke da gadara,ya ce get lost! Ya na dariya Khalid ya tada motar shi,ya na a gaida uwar yan mata,Jabir ya daga ma sa hannu ya shige gidan sa. Khalid ya kama hanya da tunanin kudirin da zuciyar sa ta yanke,if realy goin to hav a second wife,den she should b Hajara. DEDICATED to The Women Of virtue (group) [4:22PM, 6/6/2015] AAG: [7:32pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE Da zancen Hajjo cikin ran sa ya kwana,washagari Allah Allah ya ke yamma ta yi ya samu ya je gidan Hajiya ya ma ta zancen Hajjo ya ji ta bakin ta kafin ya yiwa Hajjon magana,dan ya san sai da yamman ake samun Hajjo a gida in dai ba weekend ba. La'asar sakaliya a gidan Hajiya ta ma sa,ya ko ci sa'a Hajjo ta dawo. Maganar ta sa ta yiwa Hajiya dadi,toh amma sai ba ta nuna ma sa sosai ba kar yayi taking advantage of it ya yi tunanin Hajiya za ta sa baki. Ta ce auta ba laifi idan za ka kara aure dan matar ka ba ta haihuwa,hakan ma dole ya faru tinda kowa ya na so ya ga zuri'ar sa ta cigaba from generation to generation,zabin ka na Hajjo shi ma ba laifi,amma ka same ta da kanka ku sasanta,dan ni na san Hajjo na da manemi,idan ta ga za ta aminta da kai,tin da waccan iyaye ba su shiga ba,fyn tsakanin ku,idan kuma ta ce ah ah,ban da takura,ka nemi wata. Ni dai fatan alkhairi mu ke,bazan sa baki ba sai Hajjo ta amince dan kanta dan sa baki na zai iya sawa ta yarda ko da kuwa ba ta so. Khalid ya ce Hajiya ta za ma ta so ai,am very sure of dat. Hajiya ta dara ai dama kai dai kam u ar olways full of urslf,toh Allah dai ya sa. Khalid ya ce amen. Hajiya ko za ki yi kiran Hajjon sai na sheda ma ta ko? Bara na jira ta a karamin falo,Hajiya ta ce toh bari na kira ta din. Hajjo kwance bisa gadan ta,ta gama waya da Suraj kenan ya fada ma ta wata daya ya rage ya dawo,sai sakar yanda za ta tarbe shi ta ke cikin ran ta,dan a zahiri ta fara sabawa da Suraj sosai ta damu da shi ba kamar da ba. Wayan da ke kan bedsyd din ta ne ya fara ringn,da ga kwance ta sa hannu ta dauka gami da karawa a kunnen ta,ta ce Hajiya na zo ne? Daga dayan bangaran Hajiya ta ce Khalid ne ke san magana da ke,ya na jiran ki karamin falo. Hajjo ta dan yi jim..Khalid? Ni kuma? Ta ce tam Hajiya,zan same shi yanzu. Ta aje wayar ta na tunanin me kuma ya faru? Ko ya dawo ma ta da Innar ta ta ne? Bari dai ta fita ta ji. Da ke ba kayan arziki ne a jikin ta ba,sai ta ja hijabin ta har kasa ta sanya,kai tsaye ta fito ba tare da ta damu da ta duba kamannin ta a madubi ba. Ta na shiga falon kamshin turaren shi ya daki hancin ta,ya harde kafa daya kan daya kan kujera,sanye da kanana kaya da ke matukar ma sa kyau. Ido su ka hada,ya sakar ma ta murmushi,ta ki maida ma sa da murmushin,sai ma sallama da ta ma sa,ta sami waje a kasa ta zauna gefe guda.

Chapter 1 of 8