Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 5
tabbatar d alkairi in rabontane,saidai tayi alkawarin bazata tari abba d maganarba har sai sun daidaita kansu . Karfe 3:30am yaya kamal ya iso cikin gidansu, bayan sun gaisa d mama taimasa barka d gama karatu lafiya yanufi dakinsa toilet y fada yai wanka zaifito Kenn, yaji kiran sallahr laasar saida yai alwala sannan y fito, yagabatar d sallahr dan acewarsa baxai iya zuwa masallaciba ya gaji sosae,byn y idarne ya haye gado d niyyar baccin, jin shuru yayi yawa b alamun yaya kamal Zai fito yasa sumy tashi ta nufi dakinsa,knocking tayi lokacin ya fara bacci taji shuru saida tai knocking sau uku sannan yai magana d cewa yes, shiga tai taganshi kwance baida alamar fitowa, ta karyar d murya tace haba yaya kasan cewa nashiryama dishes fa inacan inata jiranka a dining amma saika kwanta, dan tabe baki yayi azuciyarsa yace wai yarinyar nan metake nufi dani tafa dameni idanma,take takenta sona takeyi nikuma banida raayin aurenta,jin yayi shuru baice komaiba ne yasa takara magana sannan yace Ok yanxu dai zan hutu ki kawomin abincin nan idan n tashi saina ci ko? Aa kayi baccin anjima inka tashi na kawoma saboda akwai wata magana d zamuyi yace no probs ya juya yaci gaba d baccinsa, ganin da sumy tayi baida lokacinta ne yasa tajuyo cikin fishi ta nufi dakinsu. Bayan y tashi dg baccin sumy ta kawo masa abincin dakinsa,byn tayi servin dinsa ne ta janyo stool din dake gaban dressing mirror ta zauna tana kallonsa yanaci, saida y gama tace yaya kamal yace na'am sai kuma tayi shiru bata kara maganaba, ganin tayi shuru ne yace ehim yanaji kinyi shuru kuma,cikin siririyar murya tace gaskiya yaya kamal kana birgeni zuciyata tana cike d tunaninka kullin dashi take kwana t tashi tana muradin kasancewa a cikin taka ina roka mata alfarma ko zata samu bigire? (Nikam yau naga tsantsar rashin t ido agun sumy)shiru yaya kamal yayi ganin baida niyyar bata amsa yasa tace yaya kayi shuru,dago kansa yayi y kalleta yace kije zanyi tunani,marairaicewa tayi tace tinani kuma yaya yace eh karki damu,jin yace karta damune yasa taji kwarin jikinta,mikewa tayi cike d hope taimasa sallama ta fito. Kwana biyu a tsakani sumy taji shuru yaya kaml baice mata komaiba, shiko tin randa taimasa maganr ya manta dan a gurin d taimasa nan ya barta,sake sumunsa tayi ta tareshi d mgnr ya bata amsa da cewa yana d wadda yakeso,tinda y fada mata haka farinciki ya kaurace a fuskarta b abinda zuciyarta take sai kuna da danasanin karya billenta d tayi dan vata taba tinanin zai watsa mata kasa a idoba. Iya kokarin yaya kamal yayi wajen ganin y bayyanawa sarah son d yake mata amma y kasa sabida kunyar d yakeji dan duk randa yai yunkurin fada mata sai ya kasa haka y hakura yaci gaba d addua Allah y kawo masa mafita d saukin lamarin. *BA DAI KAFI SON TA BA daga www.hausaebooks.com.ng* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 176 to 180 *Bayan wata daya* Abbane zaune a palo bayan sallah magriba y tara iyalinsa mama na daga gefensa axaune,gyaran murya yayi yace abinda yasa na taraku wata muhimmiyar maganace zanyi dan haka kowa yabani hankalinsa nan ya saurareni,kallon kamal yayi yace kai kamal tinda Allah yasa kagama karatunka service ne ya ragemaka to zaka fara zuwa kasuwa dan akwai wani shago sabo d na bude yanxu haka anzuba komai zaka ringa zama acikinsa dan bazakaita zama a gida kamarka ba,wani dadi kamal yaji yaimasa godiya sosae mama itama tayi godiya. Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 15 Abbane y cigaba d magana yace, sannan kuma yadace ace kana d iyali dan haka idan kana d wacce kakeso ka fadamin? zarrr kamal yaji ajikinsa wata zuciya tana cewa kawai kace sarah kakeso ,candai y dake ya kalli sumy y kauda kai yace aa abba babu,wani mugun kallo sumy ta watsa masa lokacin d suka had'a ido aranta tace lallai ma yaya kamal ni zai dizga tai k'wafa,batare d abba y sake yiwa kamal magana b ya kai duban sa ga sarah yace, sarah kema tinda kingama makaranta kuma ka'idar gidana dg secondry baa cigaba d karatu dan haka kema idan kina d wanda kikeso ki fadamin,tsuru tsuru sarah tayi tana raba ido azuciyarta tace inason mahmoud amma nasan yaya kamal yana sona kin fade yayi dan haka nima cewa zanyi banida kowa Allah yasa abba y hadamu aure saida t kai karshen tunaninta kanta n sunkuye tace babu abba,hamdala g Allah abba yai ganin burin d yadade yana son ya cika zai cika, dan da ace kamal ko sarah suna da wanda suke so da baxai musu doleba dan son ya cika burin zuciyarsa,cigaba d magana abba yayi yace tinda dik cikinku babu wanda yake d masoyi kamal ga sarah nan tinda itama tagama secondary ku daidaita kanku y kare maganar yana nunashi d hannu, duk cikinsu b wanda yai magana saidai zuciyoyinsu cike suke d farinciki, mamace t nisa tace Allah y daidaita su, abba yace amin kuma sati n baku,idan daya yaga d matsala bayaso y sanar dani dan banason abinda za ayi ya janyo matsala dg baya,yana kaiwa nan yace kutashi kuje Allah yai muku albarka, kansu a kasa sum sum suka tashi kowa y nufi dakinsu,wai wazai gane min sumy d tacika kmr t fashe. Gyara zama mama tayi ta kalli abba tace alhaji gaskiya kayi dogon tinani da kai tunanin hada auren nan, dariya abba yayi sannan yace wllh hajiya a iya tunanina banga wanda zan aurawa sarah hankalina y kwanta ba sai kamal da ace abdullh shine gaba d kamal dashi zan aurawa sarah,mama tace ai da kamal d abdallh duk dayane alhji yace hakne dan nafison wanda zai kula d ita y nuna mata gata bazai wulakanta taba,yar dariya mama ta saki tace ai insha Allah kamal yaron kirkine zai riketa d amana abba yace amin Allah ya daidaita tsakaninsu karsu bamu kunya,amin mama tace saidai mu yita addua Allah y tabbatar mana d wannan abu d alkairi yace amin. Wannan rana kwanan farinciki masoya biyun sukayi, amma bangaren sumayya abin baxai faduba dan ni kaina banga fuskar rabar ta bama balle n nado rahoto sai hakura nayi. A wanna daren sarah ta yanke shawarar datse alaka d mahmoud, zata fadamasa abbanta yai mata miji kuma y zamo dole tayi mishi biyayya ,nikam nace dama kinsan kawai kina rage zafin soyayyar yaya kamal ne d shi, lolllll *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 181 to 185 Toh fa akuyoyin d'aure ansamu sake wato sarah d yaya kamal soyayya tsantsa aka finjima nunawa juna cikin kwana biyu rak soyayya tayi nisa inka gansu suna xaune suna hirar love ka rantse shekararrune a harkar. D yamma suna xaune a farfajiyar gidansu suna hira ne sumy t kawo kai zata wuce, wata dariya d taga yaya kamal ya sakarwa sarah wadda tin sanin d sumy tai masa bata taba ganin yayi irin taba sai yau,batasan duk acikin love bane, tsaki tayi, aranta tace *BA DAI KAFI SON TA BA daga www.hausaebooks.com.ng*tare d yin k'wafaa ,ashe abinda ta fada din y futo fili ,A firgice sarah ta juya dan ganin mai fad'ar wannan muguwar kalmar d ko amafarki bata k'aunar tasake jinta,ganin sumy tayi a tsaye fuska a daure d sauri sarah tace A uxubillahi minash shaidanir rajim gami d dafe kirjinta a ranta tace me sumy take nufi? Ganin tsoratar da sarah tayi ne yasa yaya kamal cewa d ita lafiya dear naga kin tsorata ko wani abin tsoron kika gani? Itadai sarah d hankalinta rabi b ajikinta yake b tace masa ba komai gami d murmushin yake sukaci gaba d hira. Mahmoud ne ya aika aimasa sallama d sarah,bayan ta fito sun gaisa ne take sanar dashi abbanta yai mata miji dan haka yayi hakuri ta kara d cewa ina sonka saidai baxan bijirewa zabin iyayena tinda dama mahmoud baisan matsayin sarah a gidanba ya dauka yar gidance, babu irin abinda d mahmoud bai fad'awa sarah b akan son d yake mata amma tace sam bazata bar zabin iyayenta haka sukai sallama ransa a dagule. *Bayan kwana goma* Ganin shak'uwar da sarah da yaya kamal sukayi ne yasa abba bai k'ara tuntubarsu batun son jubansu b kamar ydd yace idan sati yayi zai sake tambayarsu yaji sun daidaita kansu dun, dan mama ta shaida masa suna son junansu,haka yauma y kara tarasu a palo kamar wancan lokacin ya tambayesu sun aminta d juna sudai basu bada amsaba tinda hadisin Annabi SAW yace shurun budurwa shine amincewarta,haka y kara karfafawa abba guiwa take y sanya ranar biki wata biyu. Shirye shiryen biki abba d mama suka shigayi duk abinda y shafi uba abba ya dauke nauyinsa hakama abinda uwa xataiwa yarta mama t dauki nauyinsa wannan shi ake cewa tuwona maina,abba yaje dangin baban kamal ya sanar musu d maganar aure sunyi murna sosae d adduar Allah y sanya alkairi,shawartar mama yai d cewa yadace afadawa baban sarah,tinda abba yasan shi shine dai baisan abbanba dan tinda sarah t nuna musu gidansu abba yakan dan zagaya yana tuntubar mazauna unguwar saida y tabbatar d lallai nanne gidansu kuma shine mahaifinnata, shawara mama ta bashi d karya fadamusu sabida sharrin ammi zai ta bibiyar sarah muddin taji labarin aurenta, tabbas abba y yadda d shawarar mama, bai sanar d dangin sarah b. Takowane bangare shiri yai nisa ana saura sati biyu bikine aka kawo lefen sarah dg dangin mahaifin kamal, abbane y hada lefen amma yakaiwa dangin mahaifinsa sukawo dan basu girma d daraja ,hakika suma sunyi murna d irin karamcin d abba yake musu bai wulakantasuba dan suna matsayin talakawa, lefe nagani n fade aka kawo akwati takwas kwanne cike yake d kayayyaki daban daban. Ango d amarya kowa y gama shiri rana kawai suke jira duk wanda sukasan xasu gayyata sankai masa invitation card, su sury m sun gayyaci wanda zasu gayyata.mama Kuwa tinda aka tsaida ranar bikin t fara gyara amaryarta Ana saura sati daya biki aka fara gyaran amarya, haka sumy d surym baa barsu a bayaba wajen gyara nasu jikin duk d sumy na bakin ciki d auren. Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 16 *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 186 to 190 Kasancewar ranar juma'a ake daurin auren yayan abba bayan sallahr jumaa sannan rabar asabar a kai amarya, haka wannanma aka saka batare d an canja b,tin ranar talata gidan alhji yusuf yadau haramin biki dangin kamal bus guda sukayo maxansu d matansu, dangin hajia rukayya wato mama itama sunxo kwasansu d kwarkwata , ya'ya'n abba da suke gidan miji suma baa barsu a baya b sunxo, damuwa sarah t shiga ganin b kowa nata d yaxo a bangaren amarya, ganinta b walwala yasanya mama janta daki take tambayarta lafia, sanar d ita tayi kawai tina ummanta tayi d tana d rai d da ita xaayi, dakyar mama t lallasheta tadan saki jikinta. Yau takama ranar alhamis inda amarya d k'awayenta sukai walima a farfajiyar gidan kasancewarsa mai yalwa,iya haduwa amarya tayi,tsadadden material tasa golden ammasa ado brown colour,takalmi hill tasa tarike purse duk brown colour, decoration dinma kalar kayan d tasaka akai a gurin d xata zaayi occasion din, iya hadu ta hadu,tsararriyar walima akai inda aka gayyato manyan malamai dg hukumar hisba,sun zarara hadisai d ayoyin akan hakkin miji akan matarsa d hakkin mata agun mijinta dan anan najiyo wasu hadisai dasuka raxanan duk iya biyayyar d mace takewa mijin ta sai manzon Allah SAW yace *"Da ace dg kwakwalwar mijinki zuwa kafarsa akwai wani gyambo da yake xubda ruwa mai wari d doyi d jini, sai matar tasa bakinta ta lasheshi to lallai bata biya hakkin aurba."* yakara fada *" Da mace tasan hakkin mijinta d yake kanta da tasa kuncin fuskarta ta goge kurar da take kafarsa."* y kara d cewa *"Duk matar d ta cutar d mijinta d harshenta Allah baxai karbi aikinta n farilla ko n nafilaba mai kyau harsai y yarda da ita koda ta axumci yininta ta tsayawa darenta ta 'yanta kuyangu ta bayar d zababbun dokuna saboda Allah takasance itace farkon wadda zata fara shiga wuta haka shima mijin idan y kasance azzalumine agareta."* Hakika wad'annan hadisai sun razanani kamar yadda suka razana sarah d zata taka matakin aiki dasu, dan hk mata mudage d aiki ja agabanmu sai munyi takatsantsan, Allah y datar damu amin.Haka akaita lecture mai tsuma jiki d zuciya agurin walimar,bayan angama akaci akasha b karya walimar t hadu dan t burgeni naci burin ranar bikina irinta za'ayi. Washe garin d akayi walima wato jumaa bayan an idar d sallahr jumaa aka daura auren *KAMAL DA SARAH*akan mafi karancin sadaki, inda abba yai waliccin sarah,kawun kamal kuma dg bangaren mahaifinsa yaiwa kamal walicci, an daura auren akan sadaki naira dubu hamsin lakadan b ajalanba,daurin auren y samu halartar manyan yan kasuwa d maaikatan gwamnati haka abokan kamal suma baa barsu a bayaba wjn halartar daurin auren. Bayan angama daurin auren anyi reception an ci an sha anyi hani'an sannan kowa y watse. Ranar asabar hajiya rukayya tasha kan shagalin yinin biki itama inda yan'uwa d abokan arxuki suka samu halartarsa. Misalin karfe 5:00 na yammane aunty maimuna wato babbar ya'r abba ta umarci sarah dataje tai wanka dan karfe 8:00 xaa kai amarya, sarah daketa faman kuka tinda aka daura aure ido yai jawur jiki a sanyaye ta mike t shiga toilet, bayan tafito ta shirya mama tasa aka kirawo mata ita, wani abu a kofi shi b madarab shi b kunuba b kuma nono ba,naga mama t bawa sarah tace ta shanyeshi haka t kafa kai tana sha tana yamutse fuska har tashanye. Bayan anyi sallahr magriba abba yasa aka kira sarah d kamal y tasasu a gaba yayi yana yimusu fada da jan kunnen su akan su zauna lafiya karyaji karya gani sannan suyi hakuri d juna, mama itama ta kara yimusu fada sannan y sallamesu. Karfe 8:02 n dare motocin daukar amarya suka iso, wata hadaddiyar mota naga ansa sarah aciki tanata kuka, niko nace gobe d safe rasss zamuzo musameki b alamar kukahaka akaita shiga sauran motocin sai gidan amarya. Misalin karfe 9:30 n dare ango y shigo d abokansa guda biyu bayan anyi siyan baki kamar yadda alada t tanada , nan sukai adduar zaman la [12/8, 8:51 AM] Ayusha iliasu: *BA DAI KAFI SON TA BA daga www.hausaebooks.com.ng* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 196 to 200 _*LAST PAGE*_ *~AFTER FIVE YEARS~* Sarah ce dauke d wani tumbulelan ciki wanda lokitoci suka tabbatar d cewa 2wins ne acikin sa maza,cikin shiga ta alfarma ta jero 'ya'yanta mata guda uku *Naufaliyya,Nabwiyya d Naubiyya* duk kusan kansu daya gwanin ban sha'awa daga gefenta kuma kamal ne shima yasha hadaddiyar shadda y sabe babbar riga a kafadarsa t hagu,jerowa naga sunyi sun nufi motarsa d kansa naga y budewa sarah front seat tashiga haka yaranma y bude musu gidan baya sannan y xagaya y shiga ya tada motar, atakaice bansan inda suka nufaba dan hk nima n tada tawa akwalar motar nace muje zuwa tinda abin ba notice balle gayyata. Binsu nake tiryantiryan banyi auneba naga kamal y karkata kan motarsa wani layi, tinani nashiga yi anya na taba shiga wannan unguwar amma a iya tinanina n kasa tina gurinwa naje,ina tsaka d tunani ban idashi b kawai naga kamal yai parkin a kofar wani gida tini kwanyata (brain )t tinamin OOOhh!!! gidan su sarah ne ashe,ganin fentin gidan y jeme ba kamar sanda mukazo dasu abba b sharrrr dashi shiyasa ban gaskata b saida n fito nai tozali d malalen sumintin kofar gidan sannan na gaskata,futowarsu kamal d yaransu yai daidai d fitowata nima, hada idon d mukai d kamal y dokon uwar harara dan b shegiyar harara bace d ubanba wnn can n tsinkayi muryarsa yana cewa d sarah maman Naufaliyya kinga waccan Ayushan mai nacin tsiya saida t biyomu y karasa mgnr yana nunani d yatsa cikin mamak sarah tace ikon Allah waya sanar mata zamuzo nan yace ohoo niko nace kwasantata kwasan zanin daura mata dan tabe baki kamal yai yace gayyar sodi saiki taho ai amma a xaure zaki tsaya nace naji dai muje d murnata n bi bayansu muka shige cikin gidan. Rakabewa nayi a saro ina leqensu suka shiga ciki,suna shiga sarah tai toxali d abbanta yashe a wata karaunin tabarma duk t gutsitstsire yai kashangararai yana wani nishi atakaice dai rai yazo gargara ko ince rai kwakwai mutu kwakwai, d hanzari tana tura ciki ta karasa gareshi ta rungumoshi,daga ido yayi yace wace? Cikin kuka tace sarah ce abba, sarah! sarah!! saida y maimaita sau uku sannan y fashe d kuka yace dama kina raye sarah? tace eh abbana ina nan d raina harma nayi aure mamakine y kamashi yace aure? tace eh ko gaisawa basuyiba ta kwashe labarin abinda y faru tindaga fitowarsu dg prison har kawo yanxu sannan tace g mijina d yayana kuma cikin kuka abban nata yaita samata albarka d neman gafararta tace ta yafe masa, tambayrshi ammi d rufaid tayi yace ai bilki taga sakamako tun a duniya dan hauka takeyi tibiran itace kan waccan bola itace cikin waccan kwalbati taxama mahaukaciya ita kuma rufaida tayi aure ashe mijin dan giyane yai mata dukan tsiya ya sakota yanxu haka ta fada yawon karuwanci, innalillahi w inna ilaihir rajiuna abinda sarah d kamal suka furta kenannan hardani d nake rakabe,cigaba Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 17 d magana abbanta yayi gami d kamo hannunta yana shafawa yace sarah ki yafemin abinda y faru a baya ba laifina bane duk sharrin bilki ne yasanya na tozartaku gashi yau kece cikin wannan gatan, Allah abba na yafe maka Allah y yafe mana baki daya,amin yace gami d kalmar shahada yana rufe bakisa y mutu,kasancewar umman sarah a hannunta ta mutu yasa tasan mutuwa kawai ji mukai sarah tace innalillahi w inna ilaihir rajiuna kullu nafsin zai'katul maut. *ALHMDLLH!* *ALHMDLLH!!* *ALHMDLLH!!!* *KULLU BIDAYAH NIHAYA* Yan uwa anan n kawo karshen wnn littafi mai taken *BADAI KAFI SONTA BA* ina fatan zamuyi amfani d darussan d ke cikinsa, dan munji ydd karshen mai bin boka tana asiri karshe kanta y koma, km yar d akebin bokan akanta a cusa sonta a xuciyar uban g halin d tafada,wdd akeyi dan ita km ga ydd allah y daukakata. *GODIYA* _Dukkan yabo d godia sun tabbata g kwal,tal,rak,tilon sarki gwani buwayi gagara misali wanda bai haifaba km ba'a haifeshi ba tsira d aminci su tabbata g fitila mai haske mai haskakawa tsani abin takawa zuwa g mataki mai garma wato Annabi Muhammad SAW .Godiya dolece g babban sarkin da yabani ikon kammala wannan littafi_ *BADAI KAFI SONTA BA* _Ina roka Allah y shafe mana kurakuranmu ya bamu sakamako mafi cancanta g daidaidin d mukayi._ *Bani d tamkar ki Yar uwa, kanwa, qawa, abokiyar shawara, Allah y barmu tare HAWWA SALEH* *jinjina gareku marubuta* Earhart tsafe Humaira B melody Aneesa A. R Huwailart Herwwerh jidda AKA Hapsart rano sadnas fertymerh zzahra umma yahya Mmn mahbu ummi hnbali Manshat faxy Farah muku jinjina, *D sauran d ban anbaci sunayenku b, ina Mai Adduar Allah y karemu daga sharrin mahassada* *Godiya t musamman gareku* Hafsat iliasu Hajara iliasu Musa iliasu Amina iiliasu Asmau lilasu *lna tare d ku har kullum* Hawwa saleh Ummu abdulhi Qawas mmn afeefa Bestyna fatyma Aisha Iliasu bauchi Abeada n basira( kunfi kowa bibiyar littafinnan) Princess xuhra Neenerh Ummylolo Rashida Xynor *Mu hadu a littafina n gaba Mai suna Yar boko*lov u oll TAMMAT BIHAMDULILAH A BA DAI KAFI SONTA BA A story by Hauwa Saleh Written by Ayusha iliasu Complet Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 5 of 5