Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
*Ayushailiasu.blogspot.com* Page 126 to 130 Tinda yaya kamal yai tozali d sarah yakasa gane wane irin abu zuciyarsa ke saka masa gaba daya tinaninsa ya koma kanta gashi baisan ita wace ba amma zuciyarsa ta addabeshi d tinaninta ya kasa tantanceshi kuma,yana zaune a dining amma abincin d yakecima kawai ci yake yana hararo kyakkyawar surar sarar, ajiye spoon din hannunsa yayi akan plate ya dau cup y zuba juice,lokacin d yakai bakinsa y saki wani tattausan smillin shi kadai sannan y kurbi juice din. Bayan y kammala cin abincin y watsa ruwa ne yace d su mujahid su shirya zasu fita su dan zaga gari, murna gurinsu mujahida kamar me ,nan da nan suka shirya sukaiwa mama sallama,sunkai dai dai kofa sumy tace yaya kamal ina zuwa? Yace zamu dan zaga garine, cikin shagwaba tace plxx yaya nima zanje,kallonta yai yana murmishi yace srry sistr we will b back soon insha Allah yaja hannunsu mujahid suka fice suka barta saroro tsaye a gurin. Da yamma sakaliya bayan abbah y dawo dg kasuwa yana zaune a palo suna hira da mama yake cewa kinga yaran nan har yanxu basu dawo ba sun shiga gari,mama tace aikuwa kaga shuru har yanxu, yace Allah y dawo dasu lafiya dai tace amin sukaci gaba d hirarsu. Ana kiran sallahr magriba yaya kamal dasu mujahid suka shigo lokacin abba ya tafi masallaci suma alwala sukai suka nufi masallacin. Suna zaune a palo ne byn anyi sallah isha,abba cikin murna d farin cikin ganin yayan nasa yake musu barka d dawowa d tanbayar ya karatu? cikin farin cikin ganin mahaifin nasu sukace alhmdllh tare d bashi labarin wahalar boarding, kallon tausayi abbah yaimusu yace aidama karatu sai hakuri dan haka ku kara hakuri d dagewa wajen karatu Allah yai muku albarka ya bada ilimi mai amfani gaba daya suka amsa d Amin harda kamal daya budo labule yashigo palon,karasowa yai y zauna kusa d abba y gaidashi,y amsa masa tare d tambayrsa ya karatu yace alhmdllh. Cigaba d hira sukai amma kwatakwata hankalin kamal baya kan hirar, dan gyara zama yayi yace inasu sumy ne bangansu b? Mujahid ne yace wllh yaya kamal suna daki danaje m koro ni aunty surayya tayi, abba ne yace je kiramin su d sauri ya tashi yanufi dakinsu, shiko kamal azuciyarsa murna yake yana cewa dama ina sane n tambayesu dan so nake na kara ganin wannan kyakkyawar halittar d ………… bai karasa zancen zucin d yake b suka shigo palon d sallama,sallamar d sukai ne t katseshi d sauri y dago kansa tare d sauke idonsa akan sarah,bayan sun xauna ne suka gaida abba d yaya kalam,abba yace kamal kaga munyi bakuwa ko? Dasauri ya amsa da eh wllh abba dg ina take? Nan abba ya fayyace masa matsayin sarah a gurinsa take kamal yaji tausayinta y mamaye masa zuciya. *BA DAI KAFI SON TA BA daga www.hausaebooks.com.ng* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 11 Page 136 to 140 Tinda yaya kamal y koma dakinsa b abinda yake hararowa sai kyan surar sarah a yanxu xuciyarsa ta gama tabbatar masa da lallaifa inba kallon tausayi kake mataba to kallon so kake mata, tinani yashiga yi to wane bangare n xuciyarsa xai bi? Furzar d iska yai dg bakinsa ya mike yake ta zagaye tsakar dakin hannunsa n makale a bayansa ya daga kansa sama sai sintiri yake yana kaiwa d kawowa a dakin, haka y kwashe tsawon mintina ashirin yana zazzagayawa bai samo amsar b, fitowa yai dg dakin ya nufi farfajiyar gidan dan hutawa. Sannu d fitowa abbah cewar sury d sarah da suke tsaye a bakin kitchen sun gama wanke wanke,kallonsu abba yai yace sannunku d aiki Allah yai muku albrk suka amsa d amin abba, cigaba d magana yai yace sarah ki shirya d yamma idan nadawo xamuje ki nuna mana gidanku, wani zar taji a cikin jininta saida tai jimmm kafin tayi magana sannan t nisa tace to abbah Allah y dawo dakai lafiya yace amin,cikin marairaicewa sury tace abba damu za'a yace a'a yasa kai yai waje. Tinda sarah taji batun zuwa nuna gidansu gaba daya kuzari yai kaura dg gareta zazzafan zazzabi taji yana neman kawo mata farmaki sbd tsabar tsoron d takeji n matar uba, ta ke taji tunanin kuncin rayuwar da tafada abaya yana dawo mata, gado ta nema t kwanta, tinda t kwanta b abinda take sai kwaranyar d zafaffun hawaye tsoronta Allah tsoronta kar aje acewa ammi anganta taje ta sake bunko mata asirin d zai rabata da wannan gidan,haka tai ta tinane- tinane ba ita t tashiba saida akai kiran sallahr azahar,toilet t shiga t dauro alwala ta gabatar d sallahr axahar sannan t jero nafila raka'a biyu, addua ta shiga jerowa tare d ambaton sunayen Allah tsarkaka d siffofinsa madaukaka akan Allah y tseratar da ita dg sharrin ammi ya makantar d ganinta dg kanta ya toshe kunnunwanta dg jin labarinta y daure kafafunta dg zuwa gurin boka. tadau lokaci tana jero addua gami d kamun kafa d Annani muhammad SAW afadar Allah sannan ta shafa,byn ta idar d sallahr saida t jima sannan t tashi ta fito palo gurinsu sumy. Hirar makarantar islamiyya su sumy suke amma sam sarah hankalinta baya kansu dan tuni jikinta yai la'asar ta gama tsinkewa d wannan tafiyar d abba ya bijiro mata d ita,abincin rana kasa cinsa tai sbd tinani ya cushe mata cikin, haka dai tai yinin wannan ranar b dadi,byn tayi sallahr laasar ne ta sake wanka d shiri karfe 4:30 n yamma daidai abba y dawo, shima shiga yai yasake shiri sannan ya ce tafito, yaya kamal shine yai driving abba yana seat din gaba mama d sarah d kuma auta mujahid suna seat din baya,kafin yaya kamal y tada mota abba yace d sarah tai directin din shi zuwa unguwar,tsaf tai masa saida abba y tabbatar kamal y gane sannan suka dau hanya sai shagari quarters,tinda suka fara tafiya b wanda yai magana shiko yaya kamal sai satar kallon sarah yake ta mirror,sarah kuwa batasan yanayi ba dan hankalinta baya jikinta ta tafi duniyar tinani wanda ni kaina bazance g irin tinanin d takeyiba ganin sun shiga lungunsu ne yasata yin wani gwauron ninfashi d ajiyar juciya k'wallace ta gangaro dg idonta kan kuncinta daidai lokacin sukai ido hudu d umma, kallo daya za kaiwa sarah ta baka tausayi, ninfasawa umma tai tace alhji kaga kuka takeyi d sauri ya juyo yace haba sarah kukan me kikeyi?cikin shasshshekar kuka tace wllh abba idan ammi t ganni saita sake yimin asiri kun koreni, tausayinta ne y mamaye zuciyar abba cikin tattausar murya yace insha Allah baxata ganki ba kuma nace miki ai b gidan zamu shiga ba kawai nuna mana zakiyi mu juyo,handkchf din dake hannun yaya kamal abba ya karba y mika wa sarah yace t share hawayen,kanshin tiraren jikin sane y xiyarci hancinta take taji wani sanyi a ranta, shiko yaya kamal xuciyarsa cike d tausayin sarah. Haka sukaci gaba d tafiya har suka isa kofar gidan,saida suka dan gota gidan kadan sannan sarah tace g gidan can t nuna musu shi d hannunta, gidane matsakaici n bulo yasha filasta d malale a kofar gidan anmasa milk din fenti atakaice gidan masu rufin asirine baxa'a ce gdn talakawa ba,sai da abba y tabbatar d nan ne gidan sannan suka juyo d motarsu suka dau hanyar komawa gida,ganin d sarah tai sun bar lungun ne yasa taji wani nishad'i a zuciyarta rufe fuskarta tayi d handkerchief din hannunta tana murmushi. Niko d nake biye dasu nace ikon Allah ashe akwai masu gudun mahaifarsu. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 141 to 145 Isowarsu gida yaya kamal yai parkin kowa y fito,bayan sun shiga ciki ne,yaya kamal y kwallawa mujahid kira yace yaje gurin sarah y karbo masa handkerchief dinsa yace to, d sauri mujahida y nufi dakin su sarah yace aunty sarah yaya kamal yace kibashi handkerchief dinsa ido suka hada d sumy d mamaki sumy tace meyakawo handkerchief din yaya kamal gunta a zuciyarta take maganar,kauda kai sarah tai dg kallon sumy ta mikwa mujahid badan tasoba dan baxata iyacewa y bar mataba gashi tana son kamshin turaren jikinsa,karba yai d sauri ya juya y kai masa. Tinda yaya kamal y karbi handkerchief din y shige daki b abinda yake illa san sanar sa yana kissin dinsa ynx y tabba xuciyarsa ta kamu d son sarah ji yai baxai iya wanke hawayen b sbd lipstick d tasanya a lebanta ya gogu a jikinsa yai alamun kiss tamkar ita yakewa ,tinani y shigayi ya xaiyi y isarwa zuciya sakonta zuwa wata zuciyar, zancen zuciya y shigayi yana cewa gashi gobe zan koma schl gaskiya baxan iya tafiya b tare d na bayyana wa sarah ina sonta b,wata zuciyar tace haba malam kayi azarbabi kavari ka dawo wani hutun mana lokacin ta kara wayewa d girma,banyi aune ba naga yaya kamal y daki side drower din gadon sa d karfi saida n dan tsorata afili yace what? yama zaai n bari saina dawo kafin lokacin kuma wani ya ganta sun kulla soyayya tinda bata san ina sonta b kuma nasan abba aura mata shi zaiyi indai tace tana son sa, kama habarsa yayi ya karasa maganar d tirkashi wannan babban lamarine, ya zan kamo bakin zarensa gashi gobe xan koma schl?. Ilailika dai,ka nemo kai kadai bada niba dan nayi nan ni. Tinda sarah tai sallahr isha ta haye gado taja blanket t rufa ba abinda takeyi sai tinano kamshin tiraren yaya kamal, tambayar kanta tashigayi dalilin meyasa nake son kamshinsa?xuciyarta tace t bata amsa d cewa sonshi kikeyi shiyasa kike son kamshin sa kuma duk lokacin d kuka hada ido dashi gabanki yake faduwa bakya kara kallonsa,lallausan murmushi tasaki saboda t amince d abinda xuciyarta tafada mata dan ta tabajin friends dinta suna hirar alamomin soyayya a schl kuma dg cikin abinda sike fade harda wadannan d ta tsinci kanta a ciki,gyara kwanciyarta tayi tai rigingine idonta a sama tana kallon fan din dake busa mata ni'imtacciyar iska,limshe idonta tayi game d sakin murmishi taci gaba d tunani karfa na fad'a tarkon son yaya kamal naje nashiga tasku shi baya sona,daga can barin zuciyarta tace mata dalla banza ke baki lura d abinda yake mikiba ne kamar b mace ba musamman idan kuka hada ido bakiga yanayin d yake miki d giraba gami d kashe ido to ai suma alamun nuna soyayya ne,wata muguwar k'ara naji sarah t saki ta juya ta rungume pillown d ta tada kai tace Alhmdllh indai hakane kuwa na dace d masoyi,kara rumgume pillown tayi gami d kissin dinsa tace I love u yaya kamal,rufe bakinta ke dawuya tana murmushi sury t shigo, dan dukan kafarta tayi tace mutuniyar smillin din me kike ne? ko kodai kodai……………? sbd sury ta gama karantar yaya kamal tsaf ya fada tarkon son sarah, harara sarah t watsa mata tace kodai me? Dariya sury tayi tace ba komai munacan muna jiranki a palo kinanan kina smillin ke kadai har yaya kamal yashigo yana tambayarki, dad'i ne y kama sarah d taji ta ambaci sunan abin sonta saidai t basar d zancen t hanyar cewa kyaji dashi dai suka topic n hirar. *BADAI KAFI SONTA BA* Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 12 *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 146 to 150 Yaya kamal ne kwance kan gadonsa yai d'ai-d'ai tinani yake yadda ya zaiyi y tari sarah d wannan maganar? haka yaita t sakawa d kuncewa baisamo mafitaba, gashi bai kara sa sarah a idonsa b balle yai yunkurin bayyana mata manufarsa ga km sammako zaiyi ya tafi,hk dai har bacci ya daukeshi. Bangaren sarah kuwa abin sharrr yake gwanin ban sha'awa dan baccinta tasha bil hakki ba tare d tinane tunane ba dan ta gama ydd da abinda zuciyarta ta shaida mata yaya kamal sonta yake. Yaya kamal ne cikin shirin tafiya makaranta fuskarsa a daure ya karaso cikin palon inda su abba suke xaune, rissinawa yai y gaidas,yanayin d abba yaga dan nasa y shigane yasanyashi tambayarsa meya faru naganka haka? ko bakason komawane kaji dadin gida?sakin fuskarshi yai yace bakomai abba bacci ne kawai a idon nawa shiyasa,d mamaki abba y sake kallonsa gami d dafa kansa yace haba son meya hanaka bacci? Kamal dai y kara bashi amsa d bakomai,fatan alkairi abba d mama sukai masa tare d adduar Allah y kaishi lafiya,amsawa yai d amin y mike jiki sakaka b kwari ya nufi kofa,saida yakai bakin kofar ya juyo yace mama inasu sumayya bamuyi sallama b? Kaji su yaya kamal d wayo dan yaga sarah ne y tambayesu fa mikewa mama tayi tace bari nakirasu to,dad'ine y kamashi zaiga abar begensa d sauri y karasa yin waje yana cewa a ransa sa biyoni yadda zanfi karewa dear ta kallo. Yana tsaye jikin motar abba suka karaso inda yake suka tsaya, face to face sukai d sarah wani dadi ne yaji kamar me ya dinga aika mata sakonni iri-iri, sundau lokaci suna hira idan yai yunkurin kiran sarah gefe ya sanar d ita bukatarsa sai km ya kasa sbd kunyar d yake d ita hakadai y hakura har sukai sallama sukai masa Allah y tsare hanya ya tafi. Abba ne y kalli umma yace hajiya anya yaron nan k'alau yake kuwa kinga yadda y fito fuska a daure? Umma tace nagani ko bayason tafiyar ne ko?oho dai abba yace ya kara da cewa koma dai menene Allah y kyauta y kuma kaishi lafiya umma tace amin (nan kuwa basusan soyayya ce take dawainiya dashi b). Bangaren sarah kuwa bataso tafiyarsa ba dan yanzu batason yai nisa d ita burinta kawai ya bayyana mata soyayyarsa gareta tai alkawarin zata karb'eta hannu bibbiyu dan ta tabbata tayi dacen masoyi dan kamal yarone nitsattse mai hankali g biyayya, uwa uba g ilimi addini d n boko, kyau kuwa kamar shi yayi kansa,gashi dogo b gajere b km yana d dan jikin d baxa'ace masa siririba ga kunya kamar wata mace dan ita kanta sarah tayi mamakin yadda yake kallonta ido cikin ido dan yadda sury t bata labarinsa ba haka bane, niko nace soyayya ce t sanyashi canjawa , d ganinsa zai iya soyayya tinda bai cika surutu any how b,sarah nima n tayaki murna Allah y sa kamal y zamto abokin rayuwarki dan nasan zaki samu kulawa d kwanciyar hanka. Karfe 12:00 daidai mota t saukeshi a bakin gate din schl karasawa cikin hostel yai ya ajiye kayansa sannan ya nufi toilet y watsa ruwa,gado ya hau y kwanta bayan y fito dg wankan ko yayi bacci ya rage gajiya, nan bacci yace ina baiga mahalli a idon sa ba tinda soyayya ta k'ek'asar dashi,wata duniya ya tafi a takaice dai akirata d suna duniyar tunani, iya bakin k'ok'arina nayi na naga n bishi dan jiyo irin tinanin d yake amma inaaaa tuni jirginsa y daga y barni a kasa inata zare ido kamar mazarin tsirehaka dole ina gani n hakura d rahotan gurin amma f nasan b wani abu bane banda sak'onnin son sarah d zasuyi tamai zarya suna miko gaisuwa d jinjina a fadar zuciyarsa suna fadin angaida masoyin sarah………… gaisheka mai kaunar sarah ………… takawarka lafiya masoyin sarah………taka asannu asannu ka isar d sakon zuciyarka a zuciyar sarah………… haka dai zasuyita kawo gaisuwa. *BA DAI KAFI SON TA BA daga www.hausaebooks.com.ng* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 151 to 155 *AFTER 4 WEEKS* Yau juma'a yaya kamal yai niyyar zuwa gida sabida y kasa samun nutsuwa, tinanin sarah ya addabeshi dan haka ya kud'iri aniyar yau zaije y bayyana mata sirrin zuciyarsa, bayan sallahr jumaa ya hau kiciniyar shiri, misalin karfe hudu n yamma ya baro cikin schl zuwa , titi yai saa yana zuwa y samu mota y hau sai birnin dabo,ana kiran sallahr magriba ya sauka gida, lokacin abba yatafi masallaci, mamakine y kama mama sabida zuwan kamal ba zato b tsammani,abinda bata tab'a ganin yai musu irin wannan zuwanba, gaisawa d mama sukayi take tambayarsa lafiya dai kamal kake tafe yanzu yace lafiyalau mama, tambayar abba yayi, tace y tafi masallaci, alwala shima yayi ya nufi masallacin. Dawowar abba dg masallaci ne mama ke sanar dashi zuwan kamal,baki bude yace kamal tace kwarai,yace inceko lafiya yake tafe yanzu? Mama tace na tambayeshi yace lafiyalau, yace to madallah abba yana rufe baki kamal ya shigo y nemi guri dan nesa d abba y zauna sannan ya gaida abban, bayan sun gaisane abba yake cewa kamal lafiya kake tafe yanxu ba notice, dan murmushi ya saki gami d shafo keyarsa yace wllh lafiya lau abba kawai dai naji inason nazo nai weekend a gidane, shima abba mamakin abin yake yace to madallah sannan y tambayeshi y karatu yace alhmdllh,tashi yai yashiga dakinsa ya watsa ruwa sannan y kara fitowa palo lokacin su sarah suma suna zaune suna kallon wani film,dagowar d sumy tai suka hada ido dashi tace laaaaaa yaya kamal yaushe ka dawo, guri y nema y xauna yace dazu nazo wallahi, sannu d xuwa sukai masa harda sarah d bakinta yaki rufuwa dan murna, cikin shagwaba sumy tace amma yaya b notice da banyima delicious ba,dariya tabashi yace ayi hakuri aunty sumayya,gaba dayansu saida sukai dariya hardasu abba dan jin yace aunty,turo baki tayi tace to yaushe zaka tafi sainayi maka snack? yace sunday zan tafi tace yawwa yayan Allah y kaimu sukace amin. Yau asabar antaso dg islamiyya su sumy d kawarsu aisha suna tafiya dan sarah bata jeba kanta na ciwo, sumy ce t kamo hannun aisha suka koma gefe sukabar sury ita kadai,sury tace gulma dai b kyau sukace eh din,sumy tace k'awata wallahi nakamu d son yaya kamal fa ya zanyi ya gane? Dariya aisha tayi tace haba qawas bakisan dabara xakiyi ki janyo hanlalinsa b? Sumy tace kedai fadamin, nan aisha ta zayyana mata yadda zatai sai d tagama sumy tace wllh aisha duk b wanda banyib amma yaki ganewa, (ashe dama duk abinda sumy keyiwa yaya kamal sonsa takeyi)kaka tsara kaka,aisha tace tabb saidai ki fadamasa to, wani mugun kallo sumy t watsawa aisha tace a matsayina n mace zance inasonsa lallai aisha soma kike y rainani, batare d taji me aisha zatace ba t janyo hannunta tace zomu tafi dalla, itakam sury d ke tsaye a gefe tana jiransu tace angama gulmar kenan sukace eh sanna suka rankaya sukaci gaba d tafiya. Weekend haka y kare yaya kamal bai samu y cimma burinsaba sbd matsanancin ciwon kai dayake damun sarah ko palo bata fitowa,haka ya shirya ya koma schl cike d tunanin sarah, d daddare ne abba yaga ciwo na k'ara gaba yace d mama tinda gobe monday d safe sai kuje asibiti tace to Allah y kaimu. Gari n wayewa suka shirya sukaje asibiti,gwaje gwaje akaiwa sarah an rasa abinda ke damunta, haka likita yayi mata yan tambayoyin d yayi mata prescribing magani suka dawo gida, bayan abba y dawo gidane dg kasuwa mama ke shaidawa abba abinda likita y fadamata cewar baiga wani ciwoba iya gwaje gwajen d yai mata,abinne y daurewa abba kai ya shiga tinani wannan to wace irin cuta ce. Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 13 *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 161 to 165 Kwana biyu a tsakanin zuwansu asibiti ciwo y canja salo,duk maganin d aka bata a asibiti kamar k'ara ciwon sukeyi,ashe dai wasa farin girki ciwo y ta'azaxxara har takai sarah tana sumbatu zantuttuka barkatai ba kan gado bare n kujera hankalin abba d mama yai matukar tashi,shawara suka yanke akan sukaita gurin mai maganin hausa,aikuwa basuyi wata wataba suka dauketa saigun mai maganin,yadda mai maganin yaga sarah nayi ne ya sanyashi karanto wasu ayoyi dg cikin alkurani mai girma, take wata murya tafara bayyana kamar muryar yan yara tana cewa aikosu akai su salwanta hankalin sarah, wata zabura d mama tayi d jin mugun nufinsu neman tsari tashigayi d ambaton Allah,mai magamin ne y tambayesu waya aikosu sukace masa bilki ce tasa aka aikomu,take mai maganin yaita karanto musu ayoyin alk'urani saida y tabbatar sunbar jikinta sannan y hado musu magunguna d zata dinga amfani dasu yace kuma azo a ringa karbar mata rubutun tsari duk sati, take abba y biyashi kudin maganin d alkawarin shine zai dainga zuwa yana karbar rubutun. Alhamdullih sati biyu d fara amfani d maganin sarh t warke kamar ba itaba amma duk d haka abba yace baxata daina amfani d maganin ba saboda kariya d neman tsari dan haka duk sati saiyaje ya karbo mata rubutun. Bangaren yaya kamal kuwa yaga b sarki sai Allah y hak'ura d tunane tunanen sarah ya mik'awa Allah yinsa indai rabansa ce Allah ya bashi idan b rabonsa bace Allah yaimasa canji d mafi alkairi dan haka yanzu y hada hankalinsa guri daya kan karatunsa tinda shekarar karshe yake ,so yake ya kawowa abba excellent grade, dan shi kadai zaiyi ya nunawa abba godiya da dawainiyar d yai dashi tin yana tsimman goyo dan hk y maida hankali kan karatunsa. Ita kuwa sumy d son yaya kamal yai mata katutu a xuciya ta rasa yadda zatai dashi kullin adduarta Allah ya karkato d hankalinsa gareta tinda duk wata hanya tabi taga bamai b'illewa bace ko daidai d rana d'aya bataga ya nuna mata wata alamar so ba dan haka t fara bayyanar da son d take matsa a tsakanin sarah da sury duk sanda suke hira zata sako maganarsa tana dan nuna alamun sonsa azatonta acikin sury d sarah wani zai tunkareshi y fadama sa,tinda sarah t fuskanci sumy son yaya kamal take ta sawa zuciyarta ruwan sanyi dan tasan b yadda zaai yar gida tana sonsa abawa yar tsintuwa aurensa dan hk ta cireshi a ranta. Haka rayuwa tacigaba d tafiya kwanci tashi b wuya gurin mai duka yanzu sarah tashiga SS3 daf suke d fara SSCE, sumy d sury kuma suna SS2 suma qualifying exam zasuyi, yaya kamal kuma yafara final paper dinsa, dan hk karatu ka'in d na'in sukasa agaba saboda su samu abinda d ake nema kuma su faranta ran iyayensu dan haka suka dukufa wajen karatu b dare b rana. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 166 to 170 Sury d sarah ne ke tafe sun dawo dg gidan aunty fateema kasancewar gidanta d gidansu b nisa Sosai, yasanya sukai strawling sukaje, sarah ce rik'e d Najma yar aunty fateema da taketa shashsheqar kuka saita biyosu suna tafe suna hira, sun kusa kaiwa gida ne wani matashi ya kunno kai a mota saura kiris y bigesu yai saurin taka birki ya tsaya cak, agigice ya fito y karaso gurinsu hakuri y shiga basu sudai kallonsa kawai sukeyi basuce qalaba saida y gama sarah tace bakomai malam amma dan Allah a ringa kula Allah y kare gaba,tinda sarah t fara magana ya saki baki y layar uban tafiya yana kallonta,ita kuwa sury t tacika tai famm dogon tsaki taja mtswwwwww wanda y dawo masa d hankalisa jikinshi, hannunta Sarah taja fuuuuu afusace tace sarah zomu tafi suka wuce sukabarshi tsaye, tinda suka tafi yake kallonsu batare d ya motsa ba, ganin sun shiga wani gida ya sanyashi juyawa y shiga motarsa ya tafi. Gobe monday su sarah xasu farah SSCE exam tin dare take ta bosho, she s ready for d exams, atakaice zamuce kawai jiran question paper takeyi ta tsarge answer,cikin dare ta tashi ta jero nafilfilu ,addua takeyi Allah yasa abinda t karanta ya fito kuma Allah y basu nasarar jarrabawar. *Bayan sati daya* Mahmoud ne xaune cikin d'akinsa b abinda y keyi sai faman tinanin wannan kyakkyawar surar d yai toxali d ita kuma yaji an kirata d suna sarah, tinda yaji muryarta mai kama d busar sarewa yaji sonta ya mamaye xuciyarsa kullin d ita yake kwana yake tashi hatta cikin baccinsa gizo take masa,yanke shawarar zuwa wannan gidan dayaga sunshiga yayi batare d bata lokaciba dan sonta d yake addabar shi, baxai yi sanya b kar wani ya rigashi,mik'ewa yai yadau key din mota da niyyar tafiya yana adduar Allah yasa nanne gidansu. Karfe 4:00 n yamma ya isa kofar gidan, maigadi ya tambaya dan Allah nanne gidansu sarah yace masa eh,ajiyar zuciya yai yace alhmdllh dan Allah zan samu wanda zaimin sallama d ita? Baba mai gadi yace to dakata dg waje n kirata tukunna yace to nagode,baba megadi d sallamarsa y iske mama a palo y rissina sika gaisa sannan y shaida mata ana sallama d sarah, cikin Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 14 mamaki tace waye yace shidai baisanshi b tace to tana zuwa,sarah kuwa dake kitchen tana girki wiki wiki tai dan taji abinda baba maigadi yace, maman ce t kwallamata kira ta amsa saida t karaso inda take tace maza kije ana sallama dake kiyi saurin ki dawo kuma banda shashanci tace to,komawar baba maigadi y sanar dashi tana zuwa b dadewa sarah tafito,ganin fuskar mahmoud ne yasa t fara tinanin inda t taba ganin fuskar amma har t karasa inda yake tsaye bata tinaba,bayan sun gaisane taimai ixini d yashigo dg farfafajiyar gidan,daya dg cikin kujerun d aka jera dan hutawa tamai umarni y zauna, bayan y zauna suka k'ara gaisawa ne yake cewa dftn kin ganeni,murmushi tayi tace gsky na taba ganin face din amma namanta inda na santa, nan mahmoud ya fada mata inda suka taba ganin juna gami d wayancewa da cewa hak'uri ya kara zuwa y bayar,yar dariya sarah tayi tace kaimadai wllh mun manta abinma,nan suka taba hira kadan sukai sallama batare d mahmoud ya fada mata abinda ke cikin ziciyarsa b. *BA DAI KAFI SON TA BA daga www.hausaebooks.com.ng* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 171 to 175 Wasa-wasa soyayya tafara k'arfi tsakanin sarah d mahmoud saidai duk wainar d suke soyawa su mama basu saniba dan sarah bata nuna alamun tana sonsa a gabansu. Hakika duk abinda akasawa rana zaizo yau ne yaya kamal y zana final paper dinsa zai dawo gida, shirye shiryen taryarsa sumy tafara tin jiya,meatpie,springrolls cake shawarma, bugga, pizza n samosa taimasa sannan tai white cuscus n vegetable soup n liver soup sai pineapple juice,karfe 2:00 n rana tagama komai ta jerasu a dining, wanka taje t sheqa tasha kwalliya tana jiran karasowarsa dan tadauki kudirin yau zata bayyana masa sirrin zuciyarta. Abin sha'awa y baiwa mama yadda taga sumy n rawar jiki akan yaya kamal tasan d walakin goro a miya, dan ruwa baya tsami banxa tini ta rafko diyar tata son kamal takeyi addua tayi Allah y

Chapter 4 of 5