Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
kara maimaita maganar sai a lokacin yusuf ya dago yai murmushi yace ai alhji bansamu wadda nakeso ba, jin yusuf ya fadi hakane yasa alhjin yin hamdala g Allah a zuciyarsa dan dama yanada kudiri azuciyarshi nasan ya hadashi da yarsa saidai yana gudun ya tareshi d maganar ko yana d wadda yakeso amma yanxu komai zaixo d sauki,cikin hikima alhji ya'u yace kamarka yusuf kace bakada wadda kakeso? Yusuf y sosa kai tare d sunkuyar d kai yace babu , jin amsar d yusuf y bada yasa alhjn cewa to indai wannan ne ga yar wajena nan rukayya kaje ka ganta idan kana sonta na baka,amma idan kaji bata kwantama a raiba dan Allah karka boyemin sai ahakura Allah ne baiba tinda shi aure yine na Allah, godiya yusuf yaimasa sukai sallama. A daren wannan ranar yusuf ya je gurin rukayya, alhmdllh sun daidaita kansu ba bata lokaci suka amincewa juna dan rukayya yarinyace mai kamala d nutsuwa g kunya gata da kyau daidai gwargwadon yadda Allah yayita dadin dadawa kuma wankan tarwadace , a lokacin ta gama makarantar sakandire b dadewa. mlm sule yasamu labarin abin arzikin d ubangidan dannasa yayi,yayi farinciki da adduar Allah y tabbatar d alkhairi yasa ayi dasu, haka shima alhji ya'u yai murna da hakan gami da adduar sanya albarka,alhji yau dakansa yasa lokacin biki wata biyu tare da cewa zaiyi komai da yakamata su yusuf suyi hatta gidan da zasu zauna zaibasu dan yadau yusuf tamkar dan da yahaifa tinda y rikemasa amana kuma yazamo sanadin yalwatar dukiyarsa,mlm sule har gida yaje yaimsa godiya,kwanci tashi ba wuya lokacin biki yazo akasha shagalin biki aka kai amarya gidanta,zaman lafiya sosae tsakanin yusuf da rikayya har Allah ya kawo rabo,murna agun yusuf baxata misaltuba, kullin adduar Allah y sauketa lafiya yakeyi, lokacin d cikin rukayya yashiga wata n tara Allah ya karbi ran mahaifiyarsa Halimatu, tsiran sati uku d mutuwar mahaifiyarsa rukayya ta haihu tasamu 'ya mace,da kanta tabawa yusuf shawara asawa yarinyar sunan mahaifiyarsa wato halimatu, hakika yusuf yai farin ciki d hakan, ranar suna yarinya ta amsa sunan halimstus sa'aadiyya ba dangin yusuf b har dangin rukayya sunyi murna da hakan sosae. Haka rayuwa tacigaba tsakanin yusuf d rukayya cikin kulawa da kwanciyar hankali,lokacin da rulayya ta haifi yarta ta biyu ne alhaji ya'u ya mallakawa yusuf shagon daya bude masa inda akai takarda d shaidu da sahannun alhj ya'u Data mai unguwa cewa ya mallakawa sirikinsa yusuf shagonsa kyauta halak malak, ranar yusuf kasa magana yai acewarsa baida bakin godiya,har gida yusuf da iyalinsa sukaje suka sake wa alhjn godiya,haka yanuwan yusuf ma baa barsu abayaba suka dinga zuwa godiya harsaida alhjin yace ya isahaka,ana cikin wannan farin cikin aka sanya lokacin auren kannen yusuf wato maryam d hadixa,mlm sule yaci burin bikin yayan nasa saidai Allah baya barin wani dan wani yaji dadi,ana saura wata biyu bikin mlm sule y amsa kiran ubangijinsa,ba yusuf, maryam d hadixaba hatta alhj ya'u mutuwar nan tadakesu dan har lokacin bikinsu maryam basu daina jimamin mutuwar ba, alhji yau ya taka radar gani a auren su maryam yaxame musu jigo a rayiwarsu wato uba suma sun rikeshi matsayin uuba. Allah y sa albarka akasuwancin yusuf inda ya bunkasa ya zama babban dankasuwa, a shekara daya yabiya wa kanshi da rukayya kudi sukaje suka sauke farali, shekara data zagayo yabiyawa maryam da hadiza suma sukaje, bayan dawowarsu ne hadiza tasamu ciki a wajen haihuwa Allah yaimata rasuwa, haka yusuf ya dakko yaron data haifa ya kawowa rukayya ta raineshi, saboda lokacin ta yaye fatima,haka rukayya ta raineshi tamkar dan d tahaifa cikin kulawa irin ta uwa. A yanzu haka alhji yusuf yana da yaya bakwai,mata biyar maza biyu,halimatu itace babba sannan fatima sannan mariya sai abdullah sai sulaiman sai sumayya da surayya,sai kuma dan yar uwarsa d yake ruko kamal,tsarin alhji yusuf ne daga sakandire yayansa mata basa jami'a dan haka halimatu,fatima d mariya duk ya aurar dasu inada halimatu keda yara uku, fatima d mariya kuma biyu,yanzu haka abdullh yana aji 6 a sakandire sulaiman kuma aji 4, sumayya da surayya kuma aji 2, kancewar alhj yusuf mai kudi baya tsawwalawa kansa da sai yayansa sunyi makarantar kudi,abdullah d sulaiman suna boarding schl wato Govt Boys Secdry Schl Gwarzo, Sumayya kuma suna Day Science kano,shi kuma kamal yana jamiar Ahmadu Bello dake zariya,alhji yusuf ya kasance mutum mai takatsantsan d gudun duniya dan haka a gidansa ko yar aiki babu komai matarsa hajiya rukayya dakanta takeyi tare da taimakon yayanta, driver d maigadi ne kawai a agidansa sai almajirin da suke aike, shima dan drivern aikinsa kawai ya ringa kai su sumayya makaranta da yadawo dasu zai ajiye motar sai wata safiyar,hakika alhji yusuf ya tarbiyyantar d yayansa akan tarbiyyar islama ya nuna musu tausayi, hakuri da kaskantar da kai tare da nuna su ba yayan kowa bane, wani lokacin zasu tambayeshi kudi yace baidashi kuma yana dashi saidai yaki basune dan ya nuna musu in yau akwai gobe fa babu,kuma alhmdullh yaran sun taso akan irin tarbiyyar da yadorasu akai. A halin yanzu alhji yusuf yana da shaguna da dama a kasuwar kwari inda shima yaja yara ajiki ya bude musu kamar yadda mahaifin rukayya wato alhj ya'u yaimasa. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayisha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* Page 41 to 50 *CIGABAN LABARI* Ranar da sarah ta cika kwana goma a gidan alhji yusuf da safe bayan sun gama breakfast suna zaune a palo da iyalinsa alhajin ya gyara zama gami dacewa sarah firgigit t dago kai takalleshi tace naam abba (kmr ydd taji su sumayya nafada masa) cigaba d magana yai yace yanzu kinga yau kwananki goma a gidannan batare da munsan daga ina kike ba dan haka nakeson yau kifadamin meye dalilin dayasa kika baro gidanku da wannan daren? Shiru ne ya ratsa gurin nawani lokaci batare da sarah tace komaiba, su sumy n sury anbaza falafalan kunne anson jin kwaf, shurun d alhj yaji yai yawane yasanyashi dakawa sarah tsawa da kakkausar murya kasancewarsa mutum da bayasan wasa yace badake nake ba, kwallace ta zararo tabiyo kunnucintalokacin da tadago, ganin hawayen yasa alhji yakara cewa duk kukan da zakiyi saikin fadamin ,dan bazai yiyu muyita zama dakeba alhalin bamusan kewaceba, jin alhj yafadi Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 4 hakane yasa sarah ta goge hawayenta gami da cewa abbah labarina mai tsahone zamudau lokaci ban gama sanar dakuba,alhaji yace komai yawansa ina sauraronki dago kanta tasakeyi sannan tafara magana cikin dakushewar murya kamar haka:- Nidai sunana sarah muhamma, mahaifina yakasance yana da matan aure guda biyu,ummana Hajara d kishiyarta bilkisu, ummana tana da yaya biyu ni d kanina khalid, itakuma kishiyarta tana da ya guda daya rufaida, babana mutumne d Allah y doramai son ummana saboda hakurinta da biyayyar da takemasa koda yaushe yana nuna mata soyayya a fili hakan nabatawa kishiyarta rai tin tanai aboye har take nuna kishin haka agabansu ,duk randa abbana yaiwa ummana wani abu najin dadi ko yayabeta agaban idanunta yana juya baya a gaban ummana zata gyada kai tace wayaga buyouts, takara d crew zata gani ne wllh,wannan kalma tanaiwa ummana ciwo amma bata taba fadawa abbana abinda d take cewa saidai tai hakuri taita addua, akwana atashi tin abin nadamun ummana har tasaba da wannan kalmar ta hassada, ganin ummana bata taba tarar abbana dan fadama sa, hakanneyasa yasa kishiyar tata ta bullo da sharri kala kala, idan abbanmu ya tafi aiki yana dawowa zata fadamasa ummana tafita batare da izininsa saba ko tace ta gayyato mutane ta dafa abinci ta juye musu tahansu ita da yarta, ko idan tai baki ummana tai girki bata basu, sharri d tuggu dai kala kala tin abbanmu yana yiwa ummata fada agabanta, har yagane sharri kawai take mata ya daina yimata fada, idan tafada masa saidai yace tayi hakuri zaiwa ummana fada, ganin yadaina yiwa ummana fada ne yasa ta bullo d wani makircin duk ranar girkin ummana saita daidaici tagama miya ko abinci saita faki idobta taje takara gishiri aciki,duk mu kasa cin abincin hakama idan abbanmu yazo zai ci yakasa ci yai taiwa ummana fada, tanaji yana fadan saita sallallabo ta zo ta cewa abbanmu yunwa sukeji sunkasa cin abinci, haka komai dare abbanmu zaicewa ummana ta tashi ta dora wani abincin, batare d musu ba ko kosawa zata sake wani girkin, akwai randa abbanmu yakawo nama a soya kuma ranar ummanace da girki saita soya naman nan takai kitchen, tana ganin ummana tashiga wanka dan lokacin abbanmu yakusa dawowa gida saitai sauri tadau galan din kalanzir ta tsiyaya acikin naman ta jujjuya tamayar tarufe, abbanmu yana dawowa aka xubo masa naman yanacin yanka daya yace da ummana ya akai kalanxir kalanzir y taba naman ,abinne ya daurewa ummana kai tace kalanzir yace eh, tace wllh ita batasan yadda akaiba, nan abbanmu yafara yiwa ummana fada yana zaginta yana cewa wace muguntace wannan tasan d yadda yai yasiyo naman zata zubamasa kalanxir aciki, budar bakin ummana tace yai hakuri kawai ya wanketa da mari, (sarah tanakaiwa nan sai naga sumy d sury harma d hajiy sun zaro ido suka hada baki mari tabdijan, nima kaina ayusha saida tausayinta y shigeni,abinda y baiwa su sury d Sumy mmki shi ne tin tasowarsu basu taba ganin abbansu y mari mamansu b, amma take cewa nata uban y mari mahaifiyarta. Jin karar saukar marin da kukan ummana ne yasa na zabura da gudu nayo waje dg cikn dakinmu dan ganin meke faruwa da ummana take kuka,ina fitowa mukai idohudu d kishiyar ummana ta watsomin hararagami dacewa indai nice zata yabawa aya zakinta tinda,aranta tace *Badai kafi sonta taba* kadanma kenan sai tagwammace kida da karatu, jin abinda da take fadene yasa jikina yai sanyi nakasa karasawa inda ummana take kukan banyi auneba sai jinai nima kukan ya subucemin. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayisha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* Page 51 to 60 Sarah ta share hawayen dake gagarowa a fuskarta taci gaba da cewa ganin da ummana tayi na taho nakasa karasawa na tsaya ina kukane yasa ta karasowa inda nake tsaye ta kama hannuna muka shiga daki, bayan munshiga ne take tambayata meyasa nake kuka nace mata naji kara kamar ta duka ne sannan najiyo muryarki kamar kina kuka shine nai hanzarin fitowa naga meya sameki shine naji ammi (wato kishiyar babata dan haka muke kiranta) tana fadin wasu maganganu da ummana bata bari na fada matasuba, hakuri tashiga bani tana cewa ba abinda yasameta, taki fadamin ne dan kar kima da mutuncin abbanmu ya ragu agurina, amma tabbas ni naji komai yafaru, haka naita bawa ummana hakuri akan duk abinda ake mata a gidan nake cemata malamin islamiyyarmu yana fada mana Allah yace acikin alkurani mai tsarki *( _Hakika masu hakuri su ake cikawa ladansu batare da hisabiba_)* kuma ya kara fada mana annabi SAW acikin hadisinsa ya cewa *(Hakuri haskene)*jin haka ne yasanya ummata tai murmushi tace Allah yai miki albrk ya kara mana hakuri nace amin. Tin daga wannan ranar abbanmu yace duk sanda ya kara kawo wani abu gidansa kar ummana t kara tabawa koda ranar girkinta ne saidai ammi tinda ummana mugunta take masa a kan kayansa,dadi kuwa kamar yakashe ammi dan farin ciki, haka muka hakura intai girki tadan zuba mana baikai ya kawoba haka zamu karba muci da dadi ko badadi mun koshi ko bamu koshi bamu isa mufadawa abbanmu ba saidai muyi hakuri, ganin haka ummana ta hakura tazuba ido ba yadda ta iya saidai kullin tana kaiwa Allah kukanta yai mata magain abun, nima kullin addua nake Allah ya bayyanar d mai gaskiya. Haka rayuwar ummana taci gaba cikin kunci da takaici batada ikon tai kwakkwaran motsi acikin gidan, in kaganta a tsakar gida saidai alwala ko wata bukatar amma koyaushe tana daki tana kaiwa Allah kukanta, ita kuwa ammi gari nata kasuwa tata,gari na wayewa abbanmu y fita aiki zatai ta shewa da habaice habaice taci karenta b babbaka duk dan ummata takulata suyi tashin hankali itakuwa ummata tai banza da ita ta nuna batasan tanaiba. Tsananin adduar d ummana takeyine Allah ya fara karkato da abbanmu kan ummana,godiya ga Allah muka shigayi sanda abbanmu yace da ummana zata cigaba da girkinta tare d yimata gargadi data kula kar irin abinda ya faru a baya ya sake faruwa,wai acewarsa yagaji dacin abincin ammi baya dadi kamar na ummana baisan tsananin adduar da mukeyi bane yasashi fadar hakan,hajiya ce ta katsere sarah ta hanyar cewa ai dama addua bata faduwa kasa banxa,tabbas sarah tace takara d cewa Allah ai yafada a cikin Alkur'ani *"Duk wanda ya dogara dashi (Allah) zai isar masa".* mamakine ya kama alhj jin yarinya karama da hankali ga uwa uba ilimi ta iya zaro ayaoyi da hadisai kamar wadda ake kitsawa, take yaji kaunarta takuma shiga zuciyarsa. Ranar da ummana taci gaba da girki takaici da bakin ciki ba wanda ammi bata nunaba har tana cewa bari munafikin mijin naki y dawo yasameni, ai baifadan zaki cigaba da girkiba shine ya zage kuka kulla muna fircinku a daki wallahi indai nice bilki zamusa kafar wando daya dake tinda *Badai yafi sonki ba*,maganganun ammi sunyiwa ummana zafi saidai tadanne zuciyarta taki kulata saida taji abun ya isheta ta dago tace aimu da Allah muka dogara kuma ba haka kawai yafi sonaba hali nagari shikesa aso mutum, idan mutum yana so asoshi shima saiyai koyi da irin halin ibaiga ansoshi ba, wannan maganar da ummana t fad ita takara ruta wutar kiyayya da gaba tsakaninsu fuuuuu tashige dakinta tana cewa zaki ganine,ummana tace Allah yasa muga alkhairi, tindaga ranar ta dau gaba da ummana harma damu ta daina yimana magana hatta yarta rufaida tasa tadaina kulamu,duk ranar girkin ummana intai abinci bataci bata barin rufaida taci koda yunwa zata kasheta. Idan abbanmu yadawo taita kuka taba fada masa karya d gaskiya shikuwa bayabin takan magamarta tinda y fahimci duk karyane kawai batason zaman lafiya ne saidai yace tayi hakuri, ganin zaman lafiya yadawo kamar ada tsakaminshi da ummana ne yasa ammi kullatar saita raba tsalaninsu kotawani hali nan tafara zuwa gurin yan bori d yan tsibbu d bokaye ahada ummana d aljanun da zasu sa abbanmu ya tsaneta yaji baya son………….sai kuka ya subucewa sarahbata iya karasawa ba. *BA DAI KAFI SON TA BA daga www.hausaebooks.com.ng* *Written by Ayisha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* Page 61 to 70 Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 5 Duk lokacin d ammi zata gurin boka sai tabari abbanmu ya tafi aiki saita fita batare d ta tambayeshi ba,tinda ummana ta fahimci tafara zuwa gurin bokaye tasake dukufa addua da salloli ba dare ba rana tana kaiwa Allah kukanta y kareta dg sharrin da take son kulla mata,akwai ranar da tadawo dg gidan bokan tazo kofar dakin ummana ta barbada wani magani wai indai ummana ta tsallaka shikenan abbanmu xai saketa, ita ummana batasan tazuba ba data tashi zata fito dg dakin tai bismillah tafito,murna ammi tashiga yi ganin ummana tsallaka maganin tana jiran abbanmu y dawo taga yasaki ummana amma daya dawo sai taga baice yasaketa ba saidai ma cewa yai d ummana ta shirya zasuje unguwa, nan takaici y isheta, abbanmu suna fita unguwar tasa kafarta itama tafita, ashe gurin bokan takoma take fadamasa aiki baiyiyuwa, nan boka yace mata ai sharadin maganinsu ba'a ambaton Allah idanko aka sake aka ambaceshi aiki ya lalace,jin boka yafadi haka yasa abin duniya yaiwa ammi yawa ya zatai da ummana tinda bata wasa da addini, sake dabara tai takoma gurin yan tsubbu kullin d kala kalar abubuwan d zata zo dasu taita binnewa a gidanmu muna kallonta tanayi tana maganganu d habaici, ummana bata taba tanka mataba balle tafadawa abbanmu, saidai dagewa da addua da mukeyi. Haka kullin d abbanmu yana fita itama zata fita bazata dawoba sai tadaidaici yakusa dawowa sannan ta dawo dan tasan ummana baxata taba fadamasa b, ganin duk abin d takeyi baya kama ummana saidai zaman lafiya d kwanciyar hankali da yake karuwa tsakanin ta d abbanmu,nanfa ta tashi a tsaye d gagarumin asiri yau da gobe tafi karfin wasa dare daya abbanmu y juyawa ummana baya ko ta gaisheshi baya amasa dg karshe ya daina shiga dakinta ya daina cin abincinta balle yadau butar ta,kukane yaci karfin sarah cikin shashsheqa taci gaba d cewa tindaga wannan lokacin ummana ta fara mugayen mafarki tana bacci saitai ta ihu tana tsorata tana cewa zasu kasheta gasunan sun taho ku tainaka min zasu kasheni haka zatai t ihu tana zabura amma abbanmu baxaizo gurinta ba saidai y daga labule y leko yace taimusu shiru mahaukaciya kawai ta hanasu bacci, haka zan rungumeta ina karanta mata ayatul kursiyyu har tasamu bacci, farin ciki agun ammi bazaya misaltuwa, haka ummana tashafe wata uku a wannan halin kullin cikin dare bama bacci makaranta ma daina zuwa nai saboda indan natafi bansan abin d ammi zataiwa ummanaba,ganin abbanmu yaki nemawa ummana magani ne yasa naje nafadawa kawu sani wato kanin ummanmu halin da muke ciki. Zuwan kawu sani gidanmu yaga irin halin da ummana take ciki duk ta rame ta susuce kamar mahaukaciya tayi baki ba yadda yasanta ba dan duk danginsu ba wanda y kaita kyau da kwarjini gata fara mai manyan idanuwa d dogon hanci idan tai murmushi sai wushiryarta ta bayyana kyanta ya karu,kasa magana yayi kawai kuka yakeyi yana cewa yanxu haka ummana takoma,tambayata yashigayi meya sameta? Meya janyo mata fadawa wannan halin? nan na zayyana masa abinda yake faruwa da yadda ummana take tsorata cikin dare d kalmar d ammi take fadawa umman kullin ta *BA DAI KAFI SON TA BA daga www.hausaebooks.com.ng* wallahi zata gani ne,abinne ya daurewa kawu sani kai shi kanshi kalmar tayimasa zafi a rai dan yadda fuskarsa ta nuna alama, atake ya dauke ni d ummana a motarsa bamu tsaya ko inaba sai gidan mai magani tare d cewa zai dawo y sami abban namu,sautin kukan su sumayya ne yasa sarah yin shuru. Nima danake sauraransu kukan nake shabe shabe d hawaye. ina fadin Allah y rabamu da sharrin kishiya.amin *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayisha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* Page 71 to 80 Sanda kawu sani y dawo y samu abbanmu yake tambayarsa ya akai y bar ummana a wannan halin?abin d yafito dg bakin abbanmu sai yace baisan batada lafiya ba sabida kin Allah, kawu sani ya jinjina maganar d abbanmu ya fadamasa y zaai suna gida daya yace baisan batada lafiyab,kawu sani shiru kaeai yai masa batare d ya tanka masa b a matsayinsa n mijin yayarsa. Haka muka zauna a gidan magani tahom wata daya batare d inaganin sauki a tattare d ummana b saidai kullin abu karuwa yake har takai saidai a kulle ta a daki inba hakaba neman guduwa takeyiashe dg wannan somi somine, wasa farin girki wata rana muka wayi gari ummana t fara hauka tibiran duk wnd yaje kusa d ita sai duka amma abin takaici duk wannan halin d muke ciki abbanmu sau daya yazo ya ganmu sai randa muka cika kwana 35 sannan y dawo, ganin haukan d ummana takeyi ne y sanya jikinsa yai sanyi nan ya ashiga nema mata magani ka'in d na'in sbd tsananin son d yake mata. Alhamdulillah daga sanda abbanmu y fara neman maganin ne tafara samun sauki ganin haka yasa kawu sani y daukemu dg gidan mai maganin y maidamu gidanshi, har gidan abbanmu yake zuwa y kawo mana maganin batare da ammi tasan yana yiba,wasa wasa cikin ikon Allah sauki y dada samuwa satinmu biyu muna amfani d magungunan ummana ta warke, lokacin d abbanmu yazo yaga t warke yace mukoma gidanshi nanfa kawu sani yace ai baiga abinda xaisa ta koma gidan ba, saida abbanmu yaita bashi hakuri kan cewar insh Allah hakan bazata sake faruwa ba nanma dakyar kawu sani y yadda amma yace saitayi wata daya kafin t koma badan abbanmu yasoba ya hakura sai randa ta cika wata gudan sannan ta koma. Ganin ummana t dawo gidan cikin koshin lafiya ya dada tinzira ammi wjn yin asiri,shikuma abbanmu baifasa kawowa ummana maganin neman tsari b,haka kuma muma bamu fasa dagewa d addua ba, haka alamari yaci gaba d tafiya agidan ba dadi saidai zaman hakuri d mukeyi,duk sanda muke hira d ummana tana cewa yanzu sarah haka zamu kasance a gidannan b dadi sai nace tayi hakuri har ranar d Allah zai tona mata asiri,sai tace min wannan wace irin masiface, hakuri nake kara bata tare d kawo mata misali da Allah yana fada cikin littafinsa mai girma cewa *"Dasannu zamu jarrabeku da wani abu na dg tsoro d yunwa d tawaya ta dukiya d rayuka d 'yayan itacuwa, amma kuyi bishara d masu hakuri"* ko kuma *"Zakuce kunyi imani ne sannan kuce baxamu jarrabeku ba"* haka zanta bata hakuri d cewa jarrabawace dg Allah ita wannance jarrabawar d akai mata idan tai hkri zataga sakayya a gaba kamar yadda Allah yace *Yaku wadanda kukai imani kuyi hakuri kuyi juriya kuyi dako (ma'ana ku jira sakanakon d Allah zaiyi)"* dan hk kowane bawa d akwai gwargwadon ydd ake jarabtarsa a duniya, wani iya wahalar da yasha adunia zata zamemasa sauki d rangwame ranar lahira, wani a saka masa tin aduniya wani kuma a barshi sai ranar hisabi, dan annabin rahma yace *"Idan Allah y nufi bawansa d alkairi saiya gaggauta yimasa azaba a duniya idan kuma yaso saiya kyaleshi d zunibinsa har xuwa ranar alkiyana."* hakadai zanta bata hakuri d kalamai mai nutsar d zuciya nace mubarwa Allah zai saka mata,kuma kowane abu yana da iyakarsa kmr yadda annabi yace a hadisi *"……………Hakika kowane abu akwai lokacin da aka iyakance masa dan hk kuyi hakuri ku nemi lada.………"* take zanga fuskarta ta bayyanar d nishadi d annashuwa. Haka zamuci gaba d hira cikin jin dadi d nisha lokacin d nake cewa d ita insha Allah wannan jarrabawar alkairice a gareta tace kamarya wahala zata zama alkairi ga bawa nace saboda annabi saw yace *"Duk wanda Allah yake nufinsa d alkairi saiya dora masa wata larura."* ko kuma ta zama makankarin laifin d yake aikatawa kamar yadda annabi saw yace *" Duk abin d yasamu mumini na wahala kona cuta kona damuwa kona bakin ciki kona cutarwa kona bacin rai harta kayar d ya takata har sai Allah y gafarta masa zunubansa da ita."* sanda n karantaw ummana wannan hadisin sai tacemin amma wata jarrabawar d akewa bawa tana tsanani a gareshi sai nake cewa d ita babu wata jarrabawa d xata zamo mai tsanani g bawa kuma Allah baya jarabtar mutumin d bayaso kinga kuwa b kowa Allah yake gwada imaninsa b sai bawa n kwarai tinda manzon Allah saw yace *"Hakika mafi girman sakamako yana tare d girman bala'i,lallai Allah madaukakin sarki idan yana son mutanensa saiya jarabcesu, duk wnda ya yarda d wnn jarrabawar Allah y yarda dashi hk duk wnda yai fishi akan jarabawar Allah zai fishi dashi."* kawai sai naga ummana tana kuka saboda jin wannan hadisi tan rungumeni tana cewa jarrabawar d Allah yaimin kenan y hadani zama d azzalumar mata, ya Allah ka bamu ikon hakuri akan dukka musibar d zata samemu ka kuma bamu ikon cin jarrabawar d kai mana, gaba dayanmu da muke sauraron sarah muka hada baki mukace amin. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 6 *Ayushailiasu.blogspot.com* Page 81 to 85 Haka muka zauna a kurkuku tsahon wata biyar batare d ko saudaya wani yazo ya ganmu ba kamar yadda ake zuwawa sauran yan kurkukun,ummana saida tai wata cuta kamar baxa tai raiba, shugaban gidan kurkukun yasa aka fadawa abbanmu amma yaki zuwa haka takaraci ciwonta har Allah y bata lafiya. Tsananin adduar da mukeyi ne ya sa wata ranar juma'a d misalin karfe 3:00 na rana abbanmu yazo yai umarni da a sakemu, bayan munfito dg kurkukun azatanmu tare d abbanmu zamu tafi gida sai mukaji yana cewa karmu sake mu dosarmasa gidinshi duk inda zamuje mutafi amma banda gidanshi, ummana kasa magana tai saini nai karfin halin cewa yanzu abba idan ummana tana d inda zataje ta tafi gidansu aini 'yarka ce ina zanje, abinda yafito dg bakinshi sai cewa yai nashiga duniya mana, bansan lokacin dana fadi a gurinba ashe suma nayi, yana gani nasuma ya juya yai tafiyarsa ya barmu a gurin, bayan na farfado ne ummana tace mutafi gidansu,haka muka kama hanya a kafa muna ta tafiya har mukaje. Dakyar dangin ummanna suka yadda muka zauna agidan,sakakon ammi duk tayi asiri ta rabamu dasu, wani daki dake hanyar kofar gida suka bamu ko kofa babu sukace anan zamu zauna bamu d zabi illah zama a cikinsa dan idan ba hakaba bamuda inda zamu,,bayan fitowarmu dg kurkuku da kwana goma ne ummana ta kwanta ciwo ashe ciwon ajaline bazata tashiba, amma duk gidan babu wanda zai leko ya dubata ni kadai naita dawainiya d ita,idan tana ninfashi kirjinta yaita bugawa kamar zuciyarta zata fito,lokacin da sa'i yai take cemin sarah kiyi hakuri da duk halin d xaki tsinci kanki a ciki ki rike gaskiya d amana a duk inda kike karki yadda ki cutar da wani dan ni tawa takare baxan tashiba,dan haka nake miki fatan alkairi Allah yai albarka a rayuwarki, tana kaiwa nan naji tayi salati shikenan ashewai ta mutu, kuka na rusa ina ambaton Allah, jin kukan d nake yine yasanya mutan gidan zuwa inda nake suna tambayata lafiya, gawar ummana n nuna musu suka karasa inda take bayan sun tabbatar tamutune suke cewa ai gara haka sun huta d jaraba dunguremin kai sukeyi suna cewa nima dole nabar gidan dan baxan zauna ba basu barni d radadin mutuwa b suka dinga fadamin maganganun da sukaga dama. Bayan anyi sadakar uku ne yayan ummana yace nabar masa gidansa ba yadda n iya haka fito batare danasan inda zaniba tafiya kawai nake saida naga dare yayi nasamu wani kango nashiga saida nai kwana biyu acikinsa ba ci basha. A bangaren ammi kuwa batasan abbanmu yasa anfito damu dg kurkuku b saida taji labarin mutuwar ummanmu sannan tasan anfiti damu, haka da taji labarin yayan ummana ya koreni farin ciki kamar y kasheta, gida ya dawo dg ita sai yarta koshi abbanmu bashida katabus a cikin gidan sai dai ita. Tsananin yunwar da t dameni ne yasanya nafito dg cikin kangon ko Allah zaisa nasami abinda zansa a bakina,wani gida dake dan nesa d kangon nashiga danyin bara,nayi sa'a mai wanke wanken gidam t hado kayan wnke wnken zatayi rokarta nashigayi ta taimakamin d ragowar abincin d akaci aka rage a wani kwano,da tai kmr bazata baniba saidai t mikomin, sabida da ka ganni kaga siffar mahaukaciya dan nagama fita a hayyacina sbd yunwa d kishir ruwa,d hanzari n karba na koma gefe n rakube nafaraci,daidai lokacin d nakai wata loma bakina ne yai daidai d fitowar mai gidan daga ckn gidan ganin ydd nake cin abincin hannu baka hannu kwarya ne yasashi tsayawa yana kallona,niko kallanshi ban karayiba nacigaba

Chapter 2 of 5