Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
yasa ya hak'uri ya janyo filet d'in, yana Kai lomar farko take ya zabura ya Fara lezaya amai tamkar zai amayar da hanjin shi. Ita ko ta bishi da kallon takaici, to miye illar wannan abincin, gashi nima naci tawa har na k'oshi, don ma in k'ara gyra mashi ita har da k'wai na saka aciki, zancen da take yi azuciyar ta kenan. A fili kuma ta taso tana yi Mai sannu had'e da tambayar miye? Nan yakai duban shi gare ta yace yanzu fisabilillah Lateefa haka ake dafa indomie, kin tashi kin zabgama Abu tarugu haka, ga k'arnin k'wai na tashi, sannan kin cika gishiri. Tace duk Kai ka jiyo wa'annan abubuwan ni dai naci abata lafiya lau. Hakan yaja jiki ya shiga kicin ya had'a tea yasha, sannan yayi wanka yayi kwanciyar shi. Jin shiru yasa Lateefa ta biyo bayan shi koda tazo har ya kwanta. Hakan tazo kusa dashi ta kwanta sai k'amshi take zabgawa, tace Kimba kayi hak'uri kar ka fara kawo muna matsala a rayuwar auren mu. Yace Lateefa matsala ta d'aya dake rashin kulawa ta 6angaren girki, ko so kike yi afara tsegumin cewa mijin ki na yawon restaurant? Tace to kabari muyi ma Mum magana ta samo muna y'ar aiki. Yace au bama ki koyi aikin ba sai dai anemo Mai aiki. Tace gaskiya sai dai kayi hak'uri ni ban iya zaman shiga kicin girki. Hakan suka yi ta rigima tsakanin su saida Shureim yace shikenan za asamo y'ar aiki d'in, nan suka shirya sai gashi anfara shan soyayya, nan na fito na janyo k'ofa har Ina cin Karo da k'ofa ```lolx``` ****************** *WACE* *CE* *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng*? BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng d'iya ce gun malam salisu da Inna uwani. Gwaggo lami itace Mace ta farko a wurin malam salisu, auren zumunci ne akayi dashi da ita. Sun kusa shekara takwas da aure Gwaggo lami ko 6atan wata bata ta6a yi ba. Daga baya ne Allah ya had'a malam da uwani wurin yawon saye da sayarwar shi ya had'u da ita can k'auyen raha. Lokacin da yazo da maganar Gwaggo lami hauka ce kawai bata yi ba, duk iya abinda zata yi tayi amma kash Allah ya k'addari sai uwani ta shigo gidan. Bayan anyi aure ne uwani ta tare, ta Fara cin karo da uk'uba hd'e da masifa gurin Gwaggo lami. Amma fa duk abinda take yi bata yi gaban malam akan tsananin makircin ta. Cikin hakan Allah yaba uwani ciki Wanda Gwaggo na hango hakan ta k'ara tsanan ta k'iyayyar ta had'e da takurawa zuwa ga uwani. Ta yita samo abubuwa masu zubar da ciki tana bata har tayi nasarar zubar da ciki uku. Akan BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ne Allah yayi ikon shi da iyawar shi har aka haife ta. Zun azab tu kuma sunga takura a hannun Gwaggo, har uwani ta had'u da ciwon hawan jini Wanda yayi ajalin ta. Koda ta rasu BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng nada shekara uku da haihuwa, y'an uwan uwani sun so su kar6e ta malam ya basu hak'uri ya rik'e abar shi. Tun tana da shekara biyar ita ke ebo ruwa rafi ta cika duka kayan gidan. Lokacin har islamiya malam ya saka ta cikin makircinta ta janye BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng daga zuwa makarantar saboda yawon talla. Ta boko ma malam yaso ya saka ta Gwaggo tace makarantar y'an iska ce. Hakan ya hak'ura ba don baya so ba sai don baya da yadda zai yi ne. Akwai lokacin da yayan uwani yazo duba BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ya d'an yi Mata siyayya, nan Gwaggo ta kar6e kayan ta k'ona su, kuma ya nemi alfarmar zuwa da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta yi masu kwana biyu Gwaggo ta hana saboda lokacin malam bai gari. Hakan BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng taga renon azaba hannun Gwaggo har zuwa yanzu da aka yi Mata aure tana da shekara goma sha hud'u. © *SDY* *JEGAL* [10/28, 1:33 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng* *80*- *85*🍒 Kwanaki sun shud'e, watanni ma haka har gashi shekaru sun shud'e. A cikin hakanne BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng take batun zana jarabawar junior living. An samu fahimtar juna sosai tsakanin ta da Murtala. Ta waye sosai ta 6angaren girki da kuma kwalliya, hakan ma tana tarairayar mijin ta dai-dai yada ta iya. Cikin hakanne arzik'in Murtala ya bunk'asa kasuwan cin shi sai ci gaba suke yi. **************** Lateefa ta kowane 6angare tana bama Shureim kulawa, sai dai matsala guda har yanzu tak'i mayar da hankali 6angaren girki. Lokacin da abin yayi yawa har Mum yaje ma da maganar, kuma ta yi iya yin ta Abu ya gagara, dole haka ta hak'ura ta basu Bizzy ta rik'a taya su aiki. Sai dai koda tazo itama girkin sai a slow saboda gurin Mum ba girki ta keyi ba goge- goge da shafe-shafe ne aikin ta sai kuma shara. Koda tazo tayi girki ranar farko ta dafa farar shinkafa da miyar tumatur, hakan Shureim ya daure yaci ba wai don abincin ya yima shi ba. Shiyasa Mum ke bashi shawa ko ruwan tea bata bari y'ar aiki ta dafa Mata. Yanzu da ace Ina da mata biyu ko Lateefa bata iya girki ba ai d'ayar ba zata rasa iyawa ba. Tuno da furucin ta akan kishiya yasa gaban shi ya fad'i dammm. Koda ta shigo d'akin yana shiri gaggauce zai je asibiti, hakan ta yi sauri ta kawo Mai ruwan tea ta had'a Mai. Nan dai ya jure yasha ba wai don ya yi mashi dai-dai ba. Tare suka fito ta shiga gidan mak'wab ciyar ta Mmn zahra, saboda Allah ya had'a jinin su. Tana shiga suka gaisa nan suka shiga hirar duniya, har suka fad'o kan wata mak'waf ciyar su da za ayima abokiyar zama cikin satinnan. Mmn Zahra tace kinji ranar assabar za akawo ma Mum Zee abokiyar zama ko? Take ta zabura ta gwalo ido waje tace yaushe Abban Zee ya dai na son ta? Mmn Zahra tayi dariya sosai tace ke ko Lateefa waya ce maki in an daina son Kane ake yima kishiya, ai shi aure nufin Allah ne kuma matar mutum k'abarin sa. Kuma kin ga ita Mum Zee wallahi tamkar bata damu ba, saboda matar akwai ta da tawakkali. Lateefa tace bata dai son mijin ta, in har tana son shi dole zata yi kishin sa. Eh to shi kishi wani Abu ne da Allah ke dasawa k'ark'ashin zuciyar Mace, kuma ko wace Mace Nada kishi duniya amma na wata yafi na wata. Saboda akwai masu kishin hauka, kuma akwai Mai na tsabta. Lateefa tace ke nifa in zaki sauke min littafin kishiya ban ta6a gane wannan bitar, maybe ma koda aka haifeni 6angaren d'aukar wannan bitar ya shafe duka. Mmn Zahra tayi dariya sosai tace to Allah ya kyauta. Ta amsa da Amin tace kin dai ji magana. Tace ya Kama ta ranar auren mu daure mu lek'a Mata. Lateefa tace ke ni fa ko gidan da keda Mata biyu bana shiga. Mmn Zahra tayi murmushi tayi tace ki daure muje kinsan Mum zee akwai k'ok'arin sada zumunci. Tace ya yi Zan duba in har Zan iya zuwa to Zan Kira ki. ********************* Yau ne BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ke ta shirye-shirye zata je suna k'auyen su, sanadiyyar lantana k'awar ta data haihu. Murtala ya yi Mata siyayyar kayan jarirai da sabulai yace takai ma lantana, ya had'a Mata da kayan da zata kaima iyayen ta ciki kuwa har da kayan abinci, hakan ma ya had'a na iyayen shi. Amma dai ba can zaki kwana ba ko? Tace naso kabar ni in kwana d'aya, amma tunda kace ba sokoto zaka kwana ba nima Zan dawo yau. Yace to shikenan in kin shirya direba zai kaiki don munyi magana da Mum tun jiya. Tace nima mun yi magana har ta bada sak'on da za aje dashi. Hakan ya gaggauta shirin shi har ya fita kuma ya dawo ya gaya Mata magana cikin kunne, tayi murmushi ta soke Kai, ya sumbaci goshin ta ya wuce, har ya tada mota tana tsaye tana yi Mai bye- bye. Ta juya ta shiga part d'in Mum bayan ta gaida ta take gaya Mata ta shirya, nan tayi ma direba magana ya fitar da mota yasa kayan ta suka d'auki hanya sai Kimba. Gidan su Murtala ta fara sauka nan aka yita tarairayar ta, k'annen Murtala duk sun cika d'aki ana murnar BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng tazo. Bayan ta sallame su ne tace zata lek'a sunan lantana daga nan ta shiga gidan su, haka yaran gidan suka cika mota sai k'ofar gidan su. Gidan su lantana ta Fara shiga nan suka rungume juna suna murna, ta kar6i jaririya ta ganta. Inna habiba sai murna ake yi BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng tazo, sai ga yara sun cika gida Ana lek'en ta ana cewa eh wallahi y'ar Baba ce. Hakan ta cika su da goma ta arzik'i sannan ta shiga gidan su. Baban ta ta fara cin Karo dashi ta durk'usa ta gaida shi, ya rik'o ta yace mashaAllah y'ar Baba, kina jin dad'in ki. Tayi murmushi, ta juya ta gaida Gwaggo. Ta amsa ba yabo ba fallasa, sai harara take binta da ita, nan dai suka ta6a hira ta fitar musu da nasu kayan. Baba nata godiya yana saka Mata albarka, Gwaggo ko cewa take yi an gode. Hakan tayi sallama da kowa ta Kama hanyar Jega saboda tana so ta yima Murtala abinci kamin ya dawo. Tana shigowa part d'in Mum ta Fara shiga bayan sun gaisa ta tashi tace Mum Zan shiga in dafama Murtala abinci, munyi waya yace ya kusa k'arasowa. Mum tace ai na ajiye maku abinci in kika tashi ki shiga maku dashi, keda kika dawo yanzu ko hutawa baki yi ba. Tace Mum an gode sosai, nan ta zauna suka rik'a hirar k'auyen su BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng. Can taji wayar ta na ruri cikin jaka, koda ta d'auko taga Murtala ne takai duban ta ga Mum tayi murmushi tace inaga ya iso. Tana d'aga wayar take gaban ta ya fad'i jin muryar wani daban. Tace eh nan ne, kawai Mum taji ta furta innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, take ta fad'i k'asa sumammiya. © *SDY* *JEGAL* [10/28, 1:34 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng* *85*- *90*🍒 Mum ta yi saurin tasowa ta gir gizata sai dai bata numfashi, nan Mum ta jawo wayar BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta duba no taga Murtala ne ya Kira, nan ta Kira taji ko lafiya can taji wani ya d'aga nan ya yimata bayanin Allah ya yiwa Mai wayar rasuwa yanzu haka suna asbitin Aleru. Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, hakan Dad yaji Mum na furtawa da k'arfi. Koda ya sauko yaga BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng zube k'asa bata ko numfashi ga Mum tsaye kanta duk ta rud'e. Nan yake tambayar meke faruwa haka? Mum ta gaya Mai saiga Dad zube saman kujera cikin tashin hankali da rud'u. Mum ta yi sauri ta d'auko ruwa fridge ta zuba ma BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng nan take taja wani dogon numfashi, Mum ta rik'a ta ta tashi sai ido take bin ta dashi. Dad ya Kira Shureim ya gaya Mai meke faruwa, yace yaje asibitin Aleru yazo da gawar Murtala. Kamin kace kwabo duk inda y'an Uwa suke labari ya Kai musu. Mutanen Kimba sun zo cikin tashin hankali, in da akazo da gawar shi aka yimai sutura sai gidan shi na gaskiya. Ashe lokacin da zai dawo daga sokoto har ya kawo Aleru sai wani sa ya gitta Mai wurin ya kauce Ashe akwai tilera bayan shi, hakan direban yayi k'ok'arin kauce mar amma abin ya faskara saida yabi ta kan shi shida wasu mutum biyu saman mashin inda su duka uku basuyi rai ba. Bayan an Kai shi gidan shi na gaskiya ne aka zo zaman makoki. Duk Wanda ya kalli BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng sai ta bashi tausayi komi rashin imanin shi, dai-dai da Gwaggo yau an d'an tausaya ma BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng. Saboda da ita da mutum mutumi basu da maraba, bata yiwa kowa magana sai dai tabi mutum da ido. Yau kwanan Murtala biyu da rasuwa BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng duk ta fita hayyacin ta, tun jiya babu mahaluk'in da ta yiwa magana har yau, sai dai ko gaisuwa ake yi Mata ta bi mutum da ido kawai. Abin har ya Fara bawa mutane tsoro, har yau Dad ya shigo da Baban ta har d'akin da take ciki. Baban ta na kallon ta shima ya rik'a Shafar hawaye, yace y'ar Baba haka kika koma, kiyi hakuri ki barwa Allah, Wanda ya bamu Murtala yafi mu son shi ya kar6i abinshi. Kiyi tawakkali kinji BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng, Kai kawai ta d'aga Mai sai hawaye dake zubowa duk sun wanke Mata fuska. Lateefa na gefen ta tana sa tissue tana goge Mata fuska ita ma tana hawaye. Babu abin da ke damun ta sai rashin maganar BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng, abinci ma ta kasa ci sai da k'yar Lateefa ke samu tasha fresh milk. Baban ta yace in akwai zam-zam kusa abashi. Nan Mum ta tashi ta d'auko ta bashi ya yi addu'a yaje da kanshi kusa ga BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ya bata yace tasha, nan ta kauda kanta. Ya k'ara bata, ta kalleshi taga ya had'e ran shi, nan Lateefa ta kar6a ta bata tasha kad'an. Ko ruwa ta sha ji take yi tamkar zuciyar ta zata k'one. Duk Wanda yazo gaisuwa yaga BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng sai ya tausaya Mata yanayin da take ciki. Lokacin sallar la'asar tayi zata tashi tayi sallah kawai akaga ta zube, nan kuka ya koma sabo. Nan Mum ta Kira wayar Shureim daga waje tace tayi sauri ya shigo. Hakan aka Kama BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng aka shiga d'akin Mum da ita. Shureim na shigowa kallo d'aya ya yi Mata ya kauda fuskar shi saboda duk ta zabge tamkar wadda tayi sati kwance. Nan ya fita ya siyo allura da ruwa aka yi Mata k'arin ruwa. Lateefa ta kasa d'agawa daga wurin ta, ko sallah da k'yar aka rarrashe ta sannan ta je tayi. Tana k'are addu'a tazo gurin ta ta zauna, malam ma yana gefen ta yana tofa Mata addu'a. Sai bayan isha'i sannan ta farka, tabi d'akin da kallo, koda ta Kai duban ta gefen ta Lateefa ta gani zaune idon ta sunyi jazir, sai Mum dake saman dadduma tana lazimi, malam ma na gefen ta. Tamkar a T.V komi ya dawo Mata take ta tuna meke faruwa, nan ta fashe da kuka tana cewa Murtala haka zaka yimin, ka tafi baka cika burin ka akaina ba. Nan Mum ta taso tana rarrashin ta, malam yace a k'yale ta tayi kukan shima rahama ne gare ta. Sai da taci kuka ya ishe ta sannan tayi shiru, nan ta tashi tayi sallolin ta ta fara lazimi duk da hakan sai dai tabi mutane da ido. Dangin mahaifiyar ta suma sunzo gaisuwa daga raha Mata uku maza biyu. Dangin malam ma gwaggon shi kawai ta rage Mai da yaran ta biyu suma duk sun zo gaisuwa. Yau ne kwana uku da rasuwar Murtala kuma yau ne za ayi addu'a kowa ya watse. Da k'arfe biyar aka yi addu'a, nan mutuwar ta koma ma dangin shi sabuwa su da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng. Kowa ya Kama gaban shi sai dangi na kusa, irin su Hindatu k'anwar margyayi da Lateefa, sai kuma Gwaggo da tace zata zauna sai an kwana biyu, Gwaggo Allah yasa zaman arzik'i ne zaki yi. ( ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﺤﻴﻨﺎ ﻭﻣﻴﺘﻨﺎ ﻭﻟﺠﻤﻴﻊ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻭﺍﻟﻤﺴﻠﻤﺎﺕ) © *SDY* *JEGAL* [10/28, 1:35 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng* *90*- *95*🍒 Yau ne BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta gama takaba. Duk Mai imani ya gan ta zai San cewa mutuwa ta ta6a ta, duk ta kod'e ta fita hayyacin ta. Bayan sati d'aya da gama takaba d'in ta an raba abinda yake hakk'in ta an bata. Malam yazo saboda zuwa da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng gida, Dad na wurin da Baban margyayi da Mum. Nan Mum tace malam salisu ina neman alfarma da Ku bar min BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng har salisu ina neman alfarma da Ku bar min BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng har zuwa lokacin da Zan cika burina akan ta. Kaga yanzu ta gama makarantar gaba da primary har anfara ciku-cikun shigar ta health sai ga wannan rasuwar Allah ya kawo. Nan malam yayi shiru ya kasa magana. Sai da Mum ta sake magana sannan ya Kai duban shi zuwa gare ta. Yace yanzu abinda nake dubi kinga can k'auye za a yita maida magana cewa mijin ta ya rasu amma nabar ta wurin Ku zaman kwad'ayi. Sai yanzu Baban Murtala yasa baki yace malam salisu yanzu ba abiyar ta mutane, kuma shi d'a na kowa ne, kaga ko bada auren margya yiba in har zaka duba zaman takewa to zaka iya bama Alhj Suleiman BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng. Kuma in har Kai ga taka zuciya zaka iya bashi ita har ta gama karatun ta to kar kabi ta surutun mutane. Malam yace to shikenan, Allah ya saka maku da alkhairi kuma yabar k'auna. Mum ta amsa da ameen, ta d'ora da cewa inshaAllah duk juma'a zata sa direba yakai BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng can gida Kimba ta zaga y'an Uwa in yaso lahadi ya koma ya d'auko ta. Da hakan suka tashi ya samu ke6ancewa da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ya k'ara yi Mata nasiha da kuma hak'uri da k'addarar da ta samu bawa. Tace ba komai Baba, amma ina jin kewar ka har cikin raina. Yace to kiyi hak'uri kinga hajiya Safiya tace duk sati zata sa akai ki kiyi muna kwana biyu, ke dai ki kula da karatun ki kuma ki tsare mutuncin ki. Tace tau Baba Allah ya Kai Ku gida lafiya, ka gaida min su Gwaggo. Bayan angama ciku-cikun shiga makaran tar BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng, ta Fara karatun ta ba laifi tana maida hankali, kuma bata cika shiga sabgar mutane ba dama tun farko bata da tarkacen k'awaye lantana ce kawai k'awar ta. Yanzu ma ta had'u da k'awa guda wadda tasu tazo d'aya wato Aisha Yagani. Babu ruwan su da shiga sabgar mutane karatun su kawai suka sakama gaba. ****** ********* Can kuma 6angaren Shureim yana fama da matsalar Lateefa, tana bashi kulawa ko ina musamman wurin kwanciya, amma fa har yanzu bata shiga kicin da sunan girki. Tun Bizzy na Jagal-gala musu abinci har ta fara iyawa ba laifi, Mum da Mamar Lateefa sun yita fad'a har sun gaji sun saka Mata ido. Wani lokaci haka k'anwar ta Shema'u zata zo gidan ta yi Mata girki Mai rai da lafiya, saboda ba kalar girkin da Shema'u bata iya ba, don ma'abuciyar son girki ce tun tana k'arama. Tana zaune falo tana waya da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng tana complain kan cewa bata son tahowa gidan su. Tace kiyi Anty Lateefa Zan zo satinnan amma fa sai na fasa zuwa Kimba kenan. Lateefa ta ce gaskiya kam abamu wannan satin. Jin sallamar Mmn zahra yasa ta tsinke wayar. Nan ta zauna suka gaisa ta kar6i zahra tana Mata wasa. Maman zahra tace ki tashi mu shiga gidan Mum zee muyi Mata Allah sanya alkhairi tunda bamu samu zuwa auren ba sanadiyyar rasuwar da aka yi maku. Har zata Fara complain kuma tayi shiru ta figi gyalen ta suka wuce. Suna shiga gidan sukayi part d'in Mum zee bayan sun gaisa sun Mata Allah sanya alkhairi, sai suka shiga hirar duniya duk yawancin hirar tasu akan kishiya ne. Sun tashi zasu wuce ta raka su part d'in Amarya, nan ta tarbesu hannu biyu suka gaisa mutunce suka tashi. Lateefa ta kalli Mum zee tace yanzu wannan kishiya ce kenan, kun raba miji kenan. Tayi murmushi tace ba laifi muna zaman fahimta tsakanin mu, don tana bani girma na. Hakan suka fito ta dubi Mmn zahra tace in banda jarabar namiji me wannan amaryar zata nuna ma Mum zee. Nan Mmn zahra tayi murmushi tace baki ganewa ne. Tace banko ta6a gane wa in dai akan kishiya ne. Hakan suka rabu kowa ya shige gidan shi. © *SDY* *JEGAL* [10/28, 1:37 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng* *95*- *100*🍒 Lateefa ta shirya ta dawo falo tana jiran shi, yana fitowa suka wuce, saboda zai sauke ta gidan su Muftah shiko zai wuce wurin d'aurin aure. An d'aura auren *MUFTAH* da matar shi *BILKISU* *BILYAMIN* sai dai fatar zaman lafiya tsakanin su. Sai zuwa dare da aka Kai Amarya Shureim ya rako ango sannan ya wuce da Lateefa. Nan yake yiwa Muftah sharri kan cewa sai sun zo barka nan da wata tara, saboda naga zumud'in naka yayi yawa. ******** ********* Yau tun safe Lateefa ke Kai kawo a gidan, tana ba Bizzy umurnin abinda zata dafa. Can ta shiga d'akin Shureim yace wai yau me ya hana ki zama haka? Tace ka manta na gaya ma Sis zata zo muna yini yau. Yace OK shine kike ta rawar Kai haka, ni na zata daga wata k'asa za kiyi bak'i, saboda naga wataran baki tashi daga bacci sai k'arfe goma, amma yau kece da tashi tun takwas. Tayi murmushi tace Kimba wallahi Ina ji da Sis BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ne tamkar k'anwata Shema'u, naga Kai ko tausaya Mata baka yi. Nan yayi murmushi yace asha aiki lafiya, koda bak'uwar taki ma sai dai taci girkin y'ar aiki ya bita da gwalo. Gane cewa tsokana yake ji yasa ta k'yale shi ta shiga wanka. Koda ta fito ta shirya sai ta dawo falo ta zauna, bata fi minti goma da zama ba sai ga BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta iso ita da k'awar ta Yagani. Hakan ta shek'o ta rungume BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng sai murna take yi, tace ma Yagani bismillah zauna mana. Hakan suka zauna tasa Bizzy ta cika masu wuri da kayan tand'e-tand'e da lashe-lashe. Suna zaune suna hira ne sai ga Shureim ya fito cikin shiga ta alfarma, ya saka k'ananan kaya ga sajen shi ya kwanta luf, ya had'u iya had'uwa ga kwarjini da ya cika fuskar shi. Nan BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta durk'usa har k'asa tace yaya ina wuni. Ya amsa da k'alau ya d'ora da cewa ya karatun, ya kuka baro Mum? Tace k'alau Alhmdulillah. Nan ma Yagani ta gaida shi, ya amsa yace to akula da karatun. Nan yakai duban shi ga Lateefa yace to ni zan fita, nan ta rakashi sai da ya tada mota sannan ta dawo. Bayan su BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng sun ci iya abin da zasu ci, nan ta jasu har bedroom d'in ta suna ta hira, Lateefa tace yaushe zaku gama karatun? Tace nan da shekara guda. Jin kiran azzahar ne yasa suka tashi domin sauke farali. Bayan sun gama sallah ne BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta shiga kicin ita da Yagani ta had'a masu abincin dare, sannan suka kimtsa zuwa tafiya gida. Lateefa tace kiyi hak'uri Kimba ya dawo sai ya sauke Ku nima inaso in bishi in gaida Mum. Da k'yar ta samu suka zauna, sai da Shureim ya dawo yaci abinci yayi wanka ya canza kaya yayi shigar manyan kaya. Nan ya kwashe su suka wuce, Yagani ya fara saukewa Lateefa ta bata ledar kayan Shafa tayi godiya sannan suka wuce gida. Nan suka zauna gurin Mum suna ta hira sai daga baya suka wuce. ********** ********** ```BAYAN``` ```SHEKARA``` ```D'AYA``` Yau ne BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng suka gama exam d'in su ta k'are health, daka dube su zaka San cewa suna cikin farin ciki. Bayan fitowar su da kar6ar address d'in juna kowa ya Kama gaban shi. Hakan kowa yaje gida cikin farin ciki da murna. _BAYAN_ _KWANA_ _UKU_ Kamar yadda suka yi alk'awari da Mum kan cewa in ta gama karatu yazo ya wuce da ita. Hakan yasa yau malam ya zo domin zuwa da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng gida, koda yazo ya taradda Baban margyayi ma yazo hakan suka zauna aka tattauna rayuwar yau da kullum. Cikin hakan ne Dad yace malam salisu Zan k'ara Neman wata alfarma Karo na biyu zuwa gare ka. Malam yace haba Alhj wace irin alfarma ce wannan, na gaya ma babu shamaki tsakanin mu. Ya yi murmushi yace d'an ka Shureim zaka bawa BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng aure. Baban margyayi yace Alhj ya akayi kasan abinda ke cikin zuciya ta, dama wannan maganar ce ta kawo ni. Nan dai suka yi maganar aka aje d'aurin aure sati guda masu zuwa. Malam yace to zai je da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng gida sai ranar alhamis zata dawo. Hakan suka d'ungu ma sai Kimba, saida suka sauka malam yake gayama BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng meke faruwa. Tace Baba don Allah ka taimakeni Ku janye wannan maganar, bazan iya auren Yya Shureim ba, innayi hakan na yaudari Anty Lateefa. Yace kiyi hak'uri y'ar Baba ba yin kaina bane, kuma kinsan mutanen nan sunfi k'arfin komai a wurin mu. Gwaggo tace kiyi hak'uri shi aure nufi ne na ubangiji, nan suka rarrashe ta sannan ta tashi ta koma d'aki. Tana shiga d'aki ta fasa kuka maicin rai, tace mutuwa Mai yankan k'auna, yanzu da wane ido Zan kalli Anty Lateefa naje Mata matsayin kishiya. Tana cikin tunanin ne taji Gwaggo saman kan ta, tace shegiya mayya kin lashe musu yaro ya mutu yanzu kin koma ga d'an cikin su. To wallahi Bari in gaya maki ko Zan tafi tsira ra ba zaki aure shi ba, makwad'aiciya Mai idon cin nera ta Kai Mata rank'washi sannan ta fita. Bayan taje ziyara dangin innar ta, kuma taje gidan su margyari har gidan lantana sai da taje. Yau Mum ta turo direba ya koma da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng, sannan tasa aka d'auko Mata Lateefa. Nan ta had'a su tana yi masu nasiha sannan ta furta ma Lateefa abinda ke faruwa. Dama an gaya ma Shureim ya amsa ba yabo ba fallasa sai dai fargabar had'uwar shi da Lateefa. Lateefa ta bi Mum da ido tace bangane ba. Mum tace saura kwana biyu auren Shureim da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng. Idon sun k'ank'ance ta bud'a baki zata yi magana kome ta tuna, sai ta zabura ta nufi hanya tamkar zararra. Mum na kiran ta ko waiwayo ta bata yiba da saurin ta tafita daga gidan. BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta rik'a kuka maicin rai tace Mum kiyi hak'uri ki janye maganar nan, kin ga Lateefa ba zata ji dad'i ba. Mum tace mu mukasan dalilin wannan had'in, in kema zaki bijiremin ne kamar yada Lateefa ta yimin to bisimillah, ta tashi ta wuce d'akin ta tabar BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng nan. Yau ne mutane suka shaida auren _SHUREIM_ _SULEIMAN_ *DA* _BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng_ _SALISU_ A garin Kimba, Allah ya basu zaman lafiya. (Masoyan BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng Ku fito Ku taya ta zaman kishi da Lateefa, _lolx_) © *SDY* *JEGAL* [10/28, 1:38 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng* *100*-

Chapter 3 of 5