Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
tana cewa ki Bari ayi maki zazzab'in zai sauka. Ganin Gwaggo ta taso tace bara a rik'a ta yasa ta zabura da k'arfi, don tasan muguntar da zata yi Mata sai tafi allurar zafi. In har bata manta ba akwai lokacin da tayi wani zazzab'i akazo za ayima ta allura Gwaggo tazo rik'e ta, amma tana ta mintsi ninta da wani Abu tamkar allura, Wanda ita kanta bata gane miye ba. Ganin ta mik'e ne tace azo amata yasa Gwaggo ta bita da murmushin mugunta. Nan hamisu ya yimata allurar ya bada magani, bayan ya gama ne Malam yace ta ara mashi kud'i zai sallami hamisu in ya fita kasuwa ya dawo zai bata. Ba kudin ne bata son ba dawa ba saidai ganin su sababbi dal take dubin yada zata rabuwa dasu, don a tunanin ta in har zata yi wani waken zata je gidan mero Mai adashe ne tabata rancen kud'i in tayi an saida ta bata kud'in, (_lolx_ Gwaggo anga sababbin kud'i.) Nan dai ta fitar bada son ranta ba taba Malam suka fita. Bayan ya sallami Hamisu ya dawo ya ebi ruwa ya shiga d'akin yace y'ar Baba tashi kisha magani. Nan Gwaggo ta karb'i magani tana b'allawa tana ba Malam shiko yaba BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng, da hakan har Tasha maganin. Malam yace in akwai ragowar waken ki sakama y'ar Baba ko zata ci, kamar zata ce babu bansan me ta tuna dashi ba zumbur ta mik'e ta ebo Mata ta kawo. Nan Malam ya matsa BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng sannan ta ci waken duk da tana jin yunwa sosai, saidai tsoron Gwaggo ya hana taci sosai. Ai wallahi don ina tsoron in hana ta waken nan ne malam ya karb'e ragowar kud'in yace zai je ya siyo Mata abinci, shiyasa na saka Mata waken, zancen da Gwaggo keyi a zuciyar ta kenan. Tace amma ba komai shegiyar zata tashi ne wallahi duk Zan fanshe kayana ajikin ta, zatayi bayani ne. © *SDY* *JEGAL* [10/28, 1:25 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng*40-45🍒 Yau kwana biyu ne kenan Murtala bai sa BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng a idon shi ba, sai mamaki yake yi me ya hana mata fitowa. Yau dai ya yanke shawarar cewa zai je k'ofar gidan su yaduba meke faruwa. Yana isowa k'ofar gidan su lantana zata shiga gidan. Nan ya tsaya suka gaisa, yace Ina mutuniyar kwana biyu ban ganta ba? Nan ta gayamai meke faruwa, ta d'ora da cewa zazzab'i ne ke damun ta shiyasa, amma raunin da sauk'i. Yace in tana iya fitowa kiyi min magana da ita Zan duba ta. Suna maganar ne saiga Malam ya fito daga gidan, nan Murtala ya durk'usa har k'asa ya gaida shi, itama lantana ta gaida shi. Lantana tace Baba yazo duba jikin BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ne. Malam yace to Ku shiga daga ciki mana, Kai da gidan ku Murtala, Ina maigari da jiki? kwana biyu ban samu lek'awa ba sanadiyyar ciwon y'ar Baba. Yace yaji sauk'i sosai har ma yana fitowa yanzu. Malam yace to kushiga daga ciki ni Zan d'an fita ne, in ka koma Ina gaida maigari, inshaAlla Zan lek'o zuwa gobe. Lantana tayi mashi jagora suka shiga gidan, nan Gwaggo ta tsare su da masifar me suka zo yi gidan ta? Inda sabo lantana ta saba da masifar Gwaggo don da wuya ta shigo gidan basu saida hali ba. Lantana tace munzo duba jikin BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ne, tace to taji sauk'i sai asamu damar juyawa gayyar tsiya wai arna a idi. Lantana ta doshi hanyar d'akin BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng, tayi banza da Gwaggo nan ta taradda ita dunk'ule amma jikin da sauk'i tace kid'an taso Murtala ne yazo duba jikin ki. Hakan ta tashi jiki ba k'wari ta fito, nan suka gaisa da Murtala yana tausaya Mata, har cikin ranshi yake jin bak'in cikin halin da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng take ciki. Hakan ya fita ya bar gidan Gwaggo na binshi da muguwar harara, lantana ta zauna suka yi hira da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng Gwaggo na binsu da zagi da muguwar harara. Tana shakkar dukan BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng gaban lantana saboda akwai ranar da ta dake ta lantana tace sai ta gayama Malam, dak'yar BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta shawo kanta ta bar maganar. Saboda tasan cewa in har lantana ta gayama Baba zata sauke haushin saman kanta tunda dama bata dukan ta gaban shi. 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻 Bayan sun je ya yimata sayayya ne suna kan hanyar dawowa tace "tace Kimba yaushe za ayi maganar auren mu? Yace Latee ban manta da maganar muba, amma fa Ina da sharad'i guda in har kin kiyaye to Ina Mai tabbatar miki auren mu ba zai wuce wata d'aya ba. Nan ta bishi da kallon murna had'e da tambayar miye sharad'in? Ya bata amsa da cewa matsala ta d'aya ce dake, saka matsattsin kaya a gaban kowa kuma ki fita dasu ba tare da kin damu ba. Wannan ba tarbiya bace kuma ba wayewa bace, in har kika gyra Ina Mai tabbatar miki auren mu na kusa. Tace in dan wannan ne kar ka damu, kasan cewa Ina yima son da duk abinda kace in daina Zan daina. Amma fa nima inada nawa sharad'in. Nan ya bita da kallo had'e da murmushi a fuskar shi, yace Lateefa rigima, Ina sauraren naki sharad'in. Tace Kimba bani ba kishiya a gidan ka, saboda wallahi nak'i jinin kishiya a rayuwata, bazan iya shearing d'in ka da wata ba, ranar da duk ka yimin kishiya Zan iya kashe Kai na. Nan ya bita da kallon mamaki, "yace nima a matsayi na na doctor bani da tsarin yin Mata sama da d'aya, sai dai wani iko na ubangiji, saidai in kanada niyya ta bashi amsa. Hakan suka doshi hanyar gida kowa da abinda yake tunani a zuciyar shi. Suna shiga Mum ta tari Latee tace kun dawo? Ta bata amsa da eh, Mum tace ta shiga ciki ta gwada kayan. Hakan tayi ta gwada kayan tana fitowa Mum na yaba kayan, tace kinga kayan duka sun maki kyau tamkar don ki akayi su. Shureim ya karb'e da cewa sai ta fitar da wa'ancan ayi sadaka, nan ta bishi da harar wasa ta shige d'akin. Shureim duk jikin sa yayi sanyi da maganganun Lateefa, dama haka kishi yake ga Mata, gaskiya abin yayi yawa. Maganar Mum ta dawo dashi hayyacin shi, tace zaka samu zuwa kaiwa Maigari sak'o ko in aiki direba? Yace Zan duba in inada time, nan shima ya wuce part d'in shi. (Dank'ari mak'ari, Lateefa muje zuwa, _lolx_🙊) © *SDY* *JEGAL* [10/28, 1:25 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng* 45-50🍒 Bayan ya shigo garin ne direct yaje shagon Hamisu suka gaisa, nan yake tambayar shi gidan su yarinyar da ya kad'e da mota. Hamisu yace oh BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng, jiya ma sai da naje aka yi Mata allura. Shureim yace inaso ne ka gayamin gidansu zanje in duba jikin Nata. Nan hamisu ya yimai misali har ya gane, saboda dama garin ba bak'on shi bane. Ya kawo gidan kenan malam zai shiga, nan ya durk'usa har k'asa ya gaida shi, yace dama Baba nazo ganin BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ne saboda ni ne tsautsayi ya fad'a na kad'e ta da mota. Malam yace Allah sarki, sannu yaro zo mu shiga daga ciki. Suna shiga Gwaggo anga bak'o daga birni jiki ya Fara rawa, nan aka d'auko shimfid'a sabuwa aka shimfid'a. Sannu da zuwa malam, ina muka had'u da bak'in birni,? sai washe baki take yi. Yace shine Wanda ya kad'e y'ar Baba yazo duba jikin ta ne, take annurin fuskar ta ya kau. Ko me ta tuna sai kuma ta Saki fara'a tace bara akira ta. Nan ta shiga d'aki ta sassauta murya tace yanzu don kina makirar yarinya saida kika gayama Wanda ya kad'e ki gidan Ku, saboda azo aduba ki abaki sababbin kud'i, shegiya Mai mugun hali. In ma an rasa mashinshi ni ne za a lab'a ga wannan kinsan dai ba abinda d'an birni zaiyi da kucaka irin ki. Jin malam yace ko bacci take yi ne yasa tace tashi muje kin sako min ido haka tamkar shege a rabon gado. Har k'asa ta durk'usa ta gaida d'an birni, ya amsa had'e da tambayar ya jikin nata? Tace taji sauk'i sosai. Ya cewa malam zai k'arasa cikin gari dama yazo gidan maigari ne. Malam yace ko Kaine d'an gidan sulemanu na birni? Yace eh nine Baba, yace Allah sarki ya Baban naka kwana da yawa bamu had'u ba? Ya bashi amsa da yana nan k'alau zai ma shigo gobe inshaAllah. Malam yace to madallah, in ka koma kagaya Mai malam salisu na gaida shi. Yace Zan gayamai, nan ya fitar da kud'i ya aje gaban malam ya tashi. Malam yace Kai ko yaro har da wata wahala, nan ma Gwaggo ta saka baki tana cewa an gode yaro Allah yayi albrka, Allah ya maida ka gida lafiya. Malam ya raka shi har waje yana k'ara godiya. 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻 Sun had'u shi da Murtala sai Sheri suke wa maigari. Murtala yace ka ganshi nan yak'i tafiya yabamu wuri haka nan. Shureim ya karb'e da cewa k'ila ya zata kujerar maigari muke so ya bar muna gado, ni ko ban komai da ita kujera ta ta doctor ta ishe ni, sai in Kai zai bama. Murtala ya karb'e da cewa ni ma ban komi da ita. To ja'irai babu Mai gadon kujerar daga cikin Ku, kun zo kun saka shi gaba da jarabar surutun ku, cewar Baban Murtala. Nan suka gaida Baban suna dariya. Yace yaushe Baban naka zai shigo? Shureim yace gobe zai zo, nima Mum ta matsamin sai nazo na kawo ma maigari dambun nama tare da ferfesu. Baban yace ai gaskiya hajiya safiya akwai k'ok'ari, Allah dai ya saka mata da alkhairi ya nuna Mata naku matan sun yi Mata. Nan suka amsa da Ameen. Shureim yaja Murtala suka fita waje, nan yake bashi labarin yarinyar da ya kad'e. Murtala yace ayyah BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng kenan marainiyar Allah. Yace yanzu haka inaso in kaima Baba maganar ta saboda ita nake so in Aura. Nan take gaban Shureim ya fad'i, sai kuma yace ni da nake da Lateefa Me zanyi da wannan y'ar k'auyen, amma nasan tana bani tausayi sosai. Maganar Murtala ta dawo dashi daga tunanin, yace inaga in baka tashi ba sai na Riga ka aure, da Dad yazo gobe zanyi maganar. Shureim yace in baka rigani ba Zan rigaka, don nima magana ta da Lateefa na nan inshaAllah. Yace to Allah ya taimaka kuma ya nuna muna lokacin. Shureim yace sai yaushe zaka b'ullo? Yace kasan rigimammen tsofon nan ne ya tsaida ni in ya samu sauk'i Zan shigo. Nan suka rabu Shureim ya Kama hanyar garin su. © *SDY* *JEGAL* [10/28, 1:26 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng* 50-55🍒 Baban Shureim yazo duba jikin maigari Wanda ciwon nashi ya had'a da tsufa, nan Murtala ya tunkari Dad da maganar yana so aje nema mashi auren BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng. Hakan suka kwashi jiki sai gidan Malam salisu, nan akayi gaisuwar yaushe rabo kuma suka tattauna kan maganar nema ma Murtala auren BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng. Malam yace ba komai Alhj Kai kanka Mai bada auren BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ne, amma duk da hakan na bawa Murtala ita halak malak. Amma Ina neman alfarmar a d'an d'agamin k'afa in har na shirya maganar auren Zan tunkari Alhj saminu inshaAllah. Alhj yace in har maganar da ka fad'i cewa d'iya tawa ce to Zan so kabar komai a Hannuna, ni Zan d'auki nauyin komai na Amarya da ango. Kuma inaso a d'aura aure yanzu, saboda gobe Zan wuce England wurin wasu harakoki nawa. A hakan aka d'unguma sai babban masalacin garin aka d'aura auren ```Murtala``````Saminu``` Da *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng* *Salisu* A kan sadaki Mai sauk'i. Ansamu halartar mutane da dama saboda lokacin sallar azahar ne, kuma in har Alhj ya shigo garin to mutane zasu k'ara taruwa, saboda shi mutum ne Mai yawan kyauta da taimakon mutane. Hakan suka rabu kowane b'angare suna murnar had'a auren yaran su. Sai dai sun ajiye maganar kan sai wani sati Mai zuwa za ayi sauran al'adun aure sannan Amarya ta tare gidan ta. Hakan Malam ya doshi gida cikin murna da farin ciki, saboda ganin yau Allah ya cika Mai burin shi na ganin ya aurar da y'ar Baba. Yana shigowa Gwaggo ta tarbeshi, tace malam yau na ganka cikin farin ciki meke faruwa? Nan ya kwashe komai ya gaya Mata, Gwaggo tayi wata irin zabura tace ban gane ba malam, wane irin aure d'iya tamkar d'iya roba za ayi neman aure da d'aurin aure lokaci guda. Kawai malam kace ka saida y'ar ka saboda kaga kud'i, aini yau an nunamin iya kata kuma an nunamin ban Haifa ba. Nan taja wani irin kuka had'e da sharce majina tace yau da ace uwar yarinyar nan na raye na tabbata ba za ayi Mata hakan ba. Haka taci kukan ta da gunzar ta tamkar wadda aka yiwa mutuwa. Malam yace kiyi hak'uri lami nima ban san da zuwan maganar ba, kuma kinsan Alhj yafi k'arfin komai a guri na. Mun taso tare tun muna yara, kuma duk sana'ar da nakeyi kinsan da bazar shi nake rawa, kinga ko in har na hana yaron shi y'ata banyi halacci ba. Da k'yar malam ya shawo kan lami ta sassauto, nan tace to yanzu yaushe ne tarewa? Yace sai nan da sati, don ina so gobe inje aljannare in gayama dangin mahaifiyar ta saboda a fita hakk'in su. Lami tace ko baka jeba babu komi, nima na isar musu, malam yace aah kam lami gara agaya masu. Zanso ma inje musu da ita koda wuni ne ta yi masu. Hakan Gwaggo ta tashi tamkar zata had'iyi zuciya ta mutu kan tsabar bak'in ciki da hassada. BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng na d'aki tana sauraren maganar Gwaggo da Baban ta, sai murna take yi cikin ran ta jin cewa an d'aura Mata aure, duk da cewa bata San miye auren ba. Amma tasan ana canja ma mutum gida daga gidan su zuwa wani gidan. Ita kam in hakane zata yi murna da cewa zata bar gaban Gwaggo ta koma gidan su Murtala da zama, amma fa tasan zata yi kewar Baban ta. ************* Koma war Dad gida yake gayama Mum an d'aura auren Murtala yau. Mum tace yaushe Murtala ya nemi Mata har magana tayi tsayi haka? Dad yace zuwa na ne yake gayamin cewa yana tausayin yarinyar kuma tana shan uk'uba ga matar Baban ta. Asali ma yace bai ta6a furtama yarinyar yana son ta ba, suna dai mutunci sosai da ita, kuma yarinyar bata ma isa aure ba nan garemu saidai can d'in, y'ar wajen abokina ce Malam salisu. Mum tace ayyaah, yanzu to ina zasu zauna? Dad yace shine nake tunanin inda za agyra Mai kamin nan da sati d'aya. Mum tace me zai hana cikin gidannan abasu part guda, kaga gidan yana da girma kuma akwai part kusan biyar da ba kowa a ciki. Dad yace kin kawo shawara, nan ya Kira wayar Shureim yace Son kazo falo Ina Neman ka. Yana zuwa Dad ya gaya Mai maganar auren Murtala, ya d'ora da cewa inaso ka duba part d'aya cikin gidannan duk abin da ake buk'ata asaka nan zuwa sati d'aya. Shureim yace lallai Murtala ya yimin wayo, Allah ya sanya alkhairi. Dad ya kar6a da Ameen, yace saura Kai, kuma ka bincika Jega international furnitures show room, ka za6a ma yarinyar kayan d'aki, komai ka tabbatar ansa saboda ni gobe Zan wuce England. © *SDY* *JEGAL* [10/28, 1:26 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng* 60-65🍒 Yau ne BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta cika sati biyu da aure, ta murje tayi jikin ta dai-dai gwargwado. Duk wata iya kwalliya ko dressing tana koyo wurin Lateefa. Lateefa ta Mai data tamkar k'anwar ta, duk in da ka gansu gidan suna tare. Mum tasa an saka BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng makarantar islamiya kuma an samo wani malami dake yi Mata lesson gida, gwargwado tana fahimta ba laifi, saboda akwai ta da saurin d'aukar Abu cikin kanta. Tana zaune part d'in Mum ta fito daga kicin kenan taji sallamar Shureim. Nan ta kar6a ta durk'usa har k'asa tace yaya Shureim sannu da dawowa. Yace yauwa BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng, Ina Mum halan? Tace yanzu ta shiga wanka. Yace latee fa? Ita ma ta kar6a mashi da cewa tana d'aki bacci take yi. Nan ya girgiza kanshi ya wuce d'akin shi, ita ko ta gama jera kaya a dinning ta yi part d'inta domin tayi wanka. Saboda wannan na daga cikin al'adar da Lateefa ta koya Mata cewa duk ta shiga kicin ta k'are girki to tayi wanka. Hakan ta shiga tayi wanka ta fito, ta yi kwalliyar ta dai-dai gwargwado duk da bata iya sosai ba. Shureim na falo zaune yana kallo sai ga Mum ta fito, bayan ya gaida ta yace Mum wai me yasa kullum Zan shigo Zan taradda BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng na taya ki aikin gida, amma Latee na d'aki tana bacci ko charting? Mum tayi murmushi ta bashi amsa da cewa nima matsalata guda da ita bata k'aunar shiga kicin ko kad'an, inaga ko ruwan coffee bata San ya ake dafa suba. Shureim yace Mum ki rik'a saka ta girki mana. Tace son kasan halin Lateefa zata iya aikin komai amma bada girki ba kam, sai dai ayi ta hak'uri zuwa gaba in kun yi aure nasan tunda tana son ka zata yima. Tace kaga yanzu haka BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng in dai tana part d'innan bai ta6a yuyuwa in shiga kicin ba tare da ita ba koda kuwa zance tayi zaman ta, yanzu haka ta fara gano kan wasu girke-girke. Nan ya ta6e baki yace Allah ya kyauta, ya tashi ya yi nashi d'akin. 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻 *WA CECE* *LATEEFA*? Lateefa d'iya ce gun Alhj Isma'il Mai dala da Hjy Saratu. Alhj Isma'il fitaccen Mai kud'i ne kuma sananne a garin Jega, yana da yaran shi Mata guda hud'u, Wanda Allah bai bashi d'a namiji ba. Ta farko itace Nafeesa wadda tana sokoto tana aure da yaran ta uku, sai kuma Bilkisu dake aure a Birnin kebbi da yaron ta guda. Sannan Lateefa, Shema'u itace Autar su, Lateefa ta taso cikin jin dad'i da sangar ta Wanda duk abinda tayi ga mahaifan ta bata laifi, musamman gun Abban ta, don ma Hjy Saratu na k'ok'arin kwa6ar ta in tana wasu abubuwan. Da Hjy Saratu da Hjy Safiya mahaifan su guda su kad'ai iyayen su suka haifa. Tun tasowar Lateefa Allah ya had'a jinin ta da son zama gidan su Shureim, Wanda yanzu hakan ake gab da auren su. ******************* A yau ne iyalan gidan maigari Alhj Abubakar suka tashi da bak'in cikin rasa maigari, Wanda ciwon shi ya tashi jiya akayi dai-dai da ajali. Dama ya d'an jima baida lafiya Wanda an yita yawo dashi asibitoci da dama har Egypt Alhj Suleiman ya fita dashi, sai dai ciwon ya had'e da tsufa. Hakan su Hjy Safiya suka Kama hanyar Kimba domin zuwa zaman makoki, Wanda har da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng aka zo. Gidan su na garin suka sauka, dama suna da gida a garin wanda in Abu ya samu nan suke sauka. Haka su kayi koke-koken su suka hak'ura, saboda sun yi rashin dattijo Mai nagarta da kamala. Nan aka yi mashi sutura sai gidan shi na gaskiya. Bayan sadakar uku ne Mum tace BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ki shirya muje gidan Ku ki gaida mutanen gida. Nan take gaban BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ya rik'a bugawa, saboda har ga Allah tama manta da wata halitta Gwaggo, tun auren ta da sati d'aya da Gwaggo taje ranar ma taci masifa har da rank'washi aka Kai Mata. Hakan dai ta wuni gidan ta hana BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng sakewa, data tashi tafiya Hjy Safiya ta had'a Mata sha tara na arzik'i, amma duk da hakan Saida ta kwashi sabulayyen wanka dana wanki, ta ebi mayukkan Shafa duk da wasu bata Masan ya ake amfani da suba. Maganar Hjy ta dawo da ita daga tunanin da ta Lula, tace ki tashi muje kinsan gobe zamu wuce. Hakan ta tashi jiki babu k'wari suka nufi gidan su BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng d'in. Sun shiga gidan Gwaggo ganin Hjy aka tashi jiki na rawa aka shimfida tabarma hakan suka zauna aka kawo ruwa da fura taji nono, nan suka sha aka gaisa, sai ga malam ya shigo suka gaisa ya yima Mum gaisuwa. Ya Kai duban shi ga y'ar Baba yace haka kika koma, kin k'ara girma kinyi 6ul-6ul. Tayi murmushi ta ce Baba kaga Mum ta sakani islamiya kuma yanzu na iya karatun boko. Nan yayi murmushi ya yima Hjy godiya sosai. Gwaggo sai binta take yi da harara tamkar ta shak'e ta take ji. Hakan Hjy ta basu kud'i suka fito, nan BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng tace Mum Ina so in lek'a lantana ga gidan su nan mak'waf tan mu. Nan suka shiga gidan lantana na ganin ta ta shek'o suka rungume juna, saiga Inna Habiba ta fito nan suka gaisa da Mum. Hakan mak'wab ta ke lek'o wa ana kallon BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng sai mamaki ake yi yadda ta koma. © *SDY* *JEGAL* [10/28, 1:27 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng* 65-70🍒 *BAYAN* *SATI* *UKU* Yau ne dubban mutane suka shaida d'urin auren *SHUREIM* *SULEIMAN* *DA* *LATEEFA* *ISMAIL* Bayan d'aurin aure da shagul gulan biki Amarya ta tare a gidan angon ta. Shureim yaso ya zauna part guda daga cikin gidan su, saidai Lateefa ta nuna cewa gaskiya bata iya zama gida guda da Mum, dole suka tare tasu anguwa daban. Bayan masu kawo Amarya sun watse abokanen ango suka rako shi, bayan y'ar nasiha da tsokanar juna da suka yi nan Muftah ya rufe taro da addu'a. Nan Shureim ya raka su suka wuce ya dawo ya rufe gidan. Ya umurce ta data tashi ta d'auro alwala domin gabatar da nafila, bayan sun idar ya yima ta tambayoyi gwargwado ta kar6a wa'anda ta sani. Nan ya fitar da kazar amarci suka ci saida sukayi k'attt (ina gefe ko taya ni basu yiba sai had'iyar yawu nake yi). Da suka k'are ne suka yi wanka, su Lateefa Amarya sai tashin k'amshi ake yi, hakan suka zo suka kwanta saman gado Mai alfarma Shureim ya ja masu bargo. (Koda na fito daga nawa wankan Shureim ya rufe k'ofa Ina waje, ```lolx```😜) ******************** *WAYE* *SHUREIM*? Shureim d'a ne gun Alhj Suleiman da hajiya Safiya, Wanda shi kad'ai ne Allah ya k'addare su da haihuwa. Ya taso cikin gata b'angaren iyayen shi duka, hakan bai hana mashi samun tarbiyya yadda ya Kama ta ba. Yayi karatun shi na boko da Arabic duk a garin Jega, daga baya ne ya fita India ya had'a masters d'in shi b'angaren likita akan matsalolin Mata. Yawancin abokanen shi sunfi kiran shi da S.S Kimba, wato Shureim Suleiman Kimba. Kimba ta samo asali ne sanadiyyar k'auyen mahaifin shi, saboda Can ne tushen shi. Alhj Suleiman da Alhj saminu sai Gwaggo Fati sune y'ay'an maigari, Wanda tun tashin Alhj Suleiman yake da sha'awar shiga jega ya siyo kaya yazo Kimba ya sayar. Cikin hakanne Allah ya had'ashi da mahaifin Safiya wato Alhj Ilyasu, Wanda rik'on amanar shi yasa ya jashi jikin shi har ya zama tamkar d'an gida. Daga hakan ne Allah ya had'a jinin shi da Safiya, saboda Mace ce Mai hankali da sanin ya Kama ta, kud'in Baban ta basu sa ta wulak'an ta mutum. Hakan akayi auren su har zaman shi ya koma can Jega duka. ***************** ```Murtala``` kuma yaro ne gun Alhj saminu k'anen Alhj Suleiman, tun tashin shi yake d'an zama wurin Alhj Suleiman d'in. Har ya fara Sana'a can sanadiyyar shagon sayar da yadukka daya bud'e Mai, sai dai yaje Kimba yayi kwana uku hud'u ya koma. Baiyi karatun boko Mai zurfi ba, iya kacin shi primary da secondary. *WASHE* *GARI* Bayan tashin su daga bacci, Lateefa an yi wanka an fito tsab sabuwar Amarya. Mum ta aiko direban ta ya kawo musu breakfast. Nan suka karya, sai bak'i ke zuwa masu ciki kuwa har da k'anwar ta Shema'u da kuma k'awar ta Shafa'atu. Nan suka shige d'aki sai shewar su kake jiyowa. *BAYAN* *SATI* *DAYA* Suna zaune suna hira Shureim yace inaga yau ya kamata ki fara girki saboda Mum ta huta da kawo muna abinci hakanan, ko ya kika ce? Tace ai inaga kabar shi kawai Mum ta rik'a aiko muna. Nan ya bita da kallon mamaki yace ban fahimce kiba. Tace ni gaskiya kasan ban iya shiga kicin girki saboda ban saba yi ba. Shureim yace kenan Mum ce zata rik'a ciyar damu mu ko muna zaune gamu masu Uwa. Da taga ya takura ta da magana, tace shikenan zata yi girki da dare d'in. Hakan yasa yaji dad'i ya janyo ta saman jikin shi ya Kai Mata kiss. Yau yana gidan Mum sai da akayi kiran magriba ya tashi yayi salla nan masallacin gidan shida Dad da Murtala, basu shigo gidan ba sai da akayi isha'i. Nan Mum tace ko azuba abinci yaje masu dashi? Yace basshi Mum nasan koda Zan koma Latee ta gama girki yanzu. Nan Murtala ya shiga tsokanar shi kan cewa za aci abincin uwargida babu ko gayyata. Yayi murmushi yace zaku ci saidai ba yau ba kam. Hakan ya fita gidan ya biya ya siya musu kayan buk'ata, yana shiga gidan Lateefa ta tarboshi ta kaimai kiss, tace dear kafa dad'e a waje. Ya bata amsa da cewa wurin Mum yaje shiyasa. Nan suka shiga d'aki ta rage Mai kayan jikin shi ta had'a Mai ruwan wanka, koda ya fito ta fitar Mai da jallabiya Fara k'al ta feshe ta da turare, nan ya shirya suka fito falo sai danning. Suna zama ta bud'e cooler ta zuba abinci ga filet, shiko yana waya da Muftah. Yana k'are waya ta turo Mai filet tana murmushi, yana jawowa zai Fara ci, me zai gani. (Fan's Ku taya ni addu'ar saduwa da rahmar ubangiji zuwa ga margyayi Babba *HASSAN*) © *SDY* *JEGAL* [10/28, 1:30 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng* *75*- *80*🍒 Shureim nakai duban shi zuwa ga abinci yaga indomie, nan ya maida duban shi zuwa ga Lateefa ita ko sai murmushi take yi. Yace yanzu don Allah Lateefa indomie ce abincin dare? Tace haba Kimba ai ko indomie ce abinci saboda ni ita nake ci da daddare in kwanta. Yace amma ni dai kina zama gurin Mum kinsan favorite food d'ina. Tace haba Kai ko Kimba ya Kama ta yada rayuwa ta canja abinci ma ya canja, kuma fa kasan ban girki ko a gida, yanzu ka takurani na yima duk da hakan banyi gwanin taba. Ganin cewa ta 6ata fuskar ta

Chapter 2 of 5