Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 6
shaida masa alhalin na fada masa bana kaunarsa wallahi ina kaunarka ina sonka shahid kaine ruhin rayuwata ka taimaka min ka saki matarka a saura mana aure muyi rayuwa.BANA KAUNAR KA 46 A daren ranar haka na kwana jiki babu qwarie, ko baccin kirki ban samu nayi ba, da zarar bacci ya daukeni sai in tuno da abnda idona ya gane min, dakuma abnda kunne na yajiye min. Tabbas na cuci rayuwata, na yaudari kaina, idan masoya sukaji labarina na tabbatar da zasu shekara dubu suna tsine mun. Washe garie tunda safe na shirya cikin riga da skirt na atamfa mai manyan flowers red, hijab na dauko shima red madaidaici na saka, na jawo flat shoes suma red ina qoqarin sakawa mom ta shigo dakin mu tace "Wahida wai me kike ne da har yanxu baki fito break fast ba?" Nace "mom am ok fa" "Kamarya kin qoshi? Me kika ci tunda safen nan", "Mom banci komai ba, kawai dai bana jin yunwa ne", Karki 6oye mn komai Wahida, nasan dole akwai abnda yasa kika qoshi", Neman wuri tayi ta zauna tukuna tace dani "Wahida! Ya kamata ki fada mn damuwarki, kinga dai ni mamanku ce, baki da wacce tafini idan kuma akwai sai inji", Kai kawai na gyda mata alamar "a'a", Batace komau ba ta fice daga dakin nabita a baya ina fadin "mom na tafi skul", A parlour na samesu da Dad yana braekfast yace "auta har anyi shirin skul din kenan?", "Ehh dad na fito ken...", ban gama maganar ba naji sallamah, na dago kaina ina shirin ansa sallamar, wa zan gani? Bom boy ne tafe bayanshi da wannan mummunar matar rashi mai zubin kilaki, da qyar na iya ansa sallamar, dad fuskarshi da annuri yace "aahhh mutane lagosi sannu sannu, yaushe a garin?", Bom boy yace "wlh dad yau kwanan mu uku kenan", Mom ta 6ata rai tace "au yau har kwananku uku amma sau yau zakazo mana? Munyi fushi a koma", "A'ah mim ayi mana afuwa, wlh mun dawi a gajiye ne, jiya kuma munje gidan Mahida ne daga can muka wuce gidan farouk, daman dan mu kankare laifin mu ne yasa nace mata muyi sammakin zuwa yau, sai dare mu tafi", Dad yace "tou sannunku da hanya, amaryarmu an same mu lafiya?", Cikin kisisina tace "lafiya qalay dad" har qasa ta duwa tace "Gud morning ma'am", "Morning too dear, ya mutanen gida ya baqunta?", "Alhamdulillah mom", Sai a lokacin Bomboy ya kalle ni yace "sister Waheeda ina kwana?" Mom tace "yanzu ke wahida bakiji kunya ba? Ace yayanki shine zai gaishe ki?", Nace "mom banfa ganshi bane", fita nayI ko bankwana ban masu ba, zuciyata cike da qunci da nadama, a raina ina fadin "ashe sama su dad sun san Shahid zayyi aure shine suka qi su fada mun?" Dan guntun tsaki nayi nace "tou kuma ai bai zama dole su fada mn ba, tinda sun san BANA KAUNARSHI, da wanann tunanin naja mota ta na kama hanyar skul.BANA KAUNAR KA!!!! 47 A 'bangaren su Bomboy kuwa da fita na mom tace "Zainab ai sai kuzo ku karya, nasan dai bakuci komai ba", Bomboy yace "wlh mom mun gode Alhamdulillah saida muka karya tukuna muka fito", Mom tace "ai sai kabari "yata ta bani ansa, nasan dai bazata qi cin girkina ba", Murmushi Zee baby tayi tace "mom wlh karki damu a qoshe muke, ai anan zamu yini dole zamuci girkin ki insha Allahu", Mom tace "tou shikenan, kuma gashi Wahida da zata taya ki firar ma ta tafi makaranta ko bankwana babu, amma da yake yau friday lecture daya kawai takeyi (10-12)", Zee baby a ranta tace "aikuwa bazamu shirya da wannan yarinyar ba, dan da alama 'yar rainin hankali ce, jifa yanda take kallo na tun daga sama har qasa, ba wai dan ta fini da komai ba kuma". A zahiri kuma tace "tou mom allah ya dawo da ita lafiya". Haka nayi lecture cikin rashin fahimtar abnda lecturer'n ke fad'I, har ya gama ban san ya gama ba saida Hafiza ta ta'boni tukuna na zabura nace "ya akayi ne?", "Au baki ma san menene ba kenan? Tun dazu fa aka gama lecture har kowa ya watse, na sa miki ido ne inga iyakar ki dama", Jaka ta kawai naja tana tambayata "me yake faruwa dake ne Wahida?" Ban bi ta kanta ba na qara gaba, direct inda aka yanada domin ajiye motoci (parking space) na dosa kamar mahaukaciya nake jan motar da qarfi. A hankali maganar Shahid ke dawo mn, ina tuna furucinda dad yayi, da qarfi na doki sitiyarin motar nace "ohh shetttt! Na cuci kaina ni Wahida, me yasa na za6i kin bin umurnin iyaye na? Me yasana za6o karatun boko akan sunnar manzon Allah (SAW)? Me yasa nayi ZURFIN CIKI? Daga d'ayan 6aren zuciyata kuma tace mn ai Wahida mace dole sai tana da class, mace babu aji ai bata cika mace ba, ni d'in da maza ke bi suna so ina wulaqanta su taya zan iya nunawa wani soyayya ta?. Zafafan hawaye keta ambaliya a fuskata nace "qarya kike, baki isa ki zuga niba domin kuwa girman kai rawanin tsiya ne, "A'UDHUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM, ALLAHUMMA AJIRNI FII MUSIIBATI, WAKHLIFNII KHAIRAN MINHA" Na fada tare da parka motata a bakin titi, saida na samu natsuwa sannan naja mota ta, har na kama hanyar gida kuma na tuna da Bomboy yace sai dare zasu tafi, corner nayi na kama hanyar gidan Mahida. Na sameta kwance bata da lafiya duk tabi ta qare cikun kwana biyu, a hankalu nake taku har na isa inda take, a kidime nace "sister me yake damunki?", Murya qasa qasa tace "wlh ciwo ne jiya jiyan nan na kamu dashi, sai fama da zazza6i nake, ga amai baya ko qaqqautaw.....", bata gama fadi ba saiga wani aman, dafe bakinta tayi tare da saurin zuwa toilet, acan na sameta tana ta nishi bayan aman data gama. Bayan samun natsuwa sosai nace "amma fa sis psychologically kina dauke da juna biyu, duk da ba likita nake karanta ba kawai sai na karanto hakan, but ya kamata ki ziyarci dr. Yayi miki awon jini". Maheeda tace "sis ai ba sai naje asibiti ba, ko kin manta da miji na likita ne?" Ta qasara maganar fuskarta dauke da annuri. "Sis nidai sai inga kamar kina cikun damuwa, ya kamata ki fada mn damuwarki idan ina da mafita wlh zanyi bakin qoqari na dan ganin na fitar dake daga cikinta, d'azu mom ta kirani tace duk yanda zanyi ince kizo gidana in bincike ki saboda bata son ganinki cikin damuwa, cikin ikon Allag kuma sai gaki kinzo", A hankali na fara share hawayen daya fara bin kumatuna, tabbas nasan idan ban fadawa mahida damuwa ta ba tou babu wanda zan iya tunkara da Ita ciki kuwa harda mom.BANA KAUNAR KA 48 Ganin banda niyyar fada mata ne yasa tace "Wahida talk mana", A hankali na share hawaye nace "Mahida tabbas idan nace bana son Bomboy nayi qarya, tun dama can da nake ce maku BANA KAUNARSHI wlh qarya nake, kawai dan ina tsantsar son yin karatu ne, ina ga kamar idan na yarda na auri Bomboy zai hana ni karatu na, sai yanxu nake ta faman da na sani, ina zagin kaina, yanzu da nasan banda mafita, saboda ya riga da yayi aurenshi"... Sosai nake kuka dan ba qaramin tausaya mn Mahida tayi ba, ta rasa abnda zata fadi sai runguma ta da tayi tana share min hawaye. A hankali muke jin qarar taku kamar ana tafiya, ban dai daga kai na kalli masu tafiyan ba, saboda qarar tafiyar tafi karfin ta mutun daya, muryar dad mukaji yace "Assalamu Alaikum", "Wa Alaikumus salam" Mahida ta fada. Tuni na gama kidimewa dan a tunani na dad ya gama jin zancen da mukeyi. Ban gama kidimewa ba sai dana dago kaina naga jerin mutane sun qura mn ido cikin tausayi suna kallo na. Cikin dattako dad ya qaraso ya zauna kusa dani ya rungume ni, tsam nima na rungume shi hawaye na na sauka a jikin shi, yace "Wahida ina so ki sani qaddara ta riga fata, duk abnda kika ga ya faru to daman can Allah ya gama tsara shi. Ni nasan kina son Shahid ko dama, kawai dai rudin zamani ne yake dibarki da kuma son karatu da kikeyi. Zainab da kike gani yarinya ce mai hankali da sanin ya kamata, ina so ki sani zata dauke ki tamkar kanwarki ta jini, bazata taba yin kishi dake ba domin kuwa ni nasan halinta sosai saboda ni na hada aurensu da Shahid". Zumbur na miqe tsaye cikin rashin fahimtar furucin dad, naji yana maganar Zainab bazata iya kishi dani ba, tunda niba matar Bomboy bace ba dama ya za'ayi tayi kishi dani? Ya akayi dad ya aurawa Ya Shahid mata ba tare da na sani ba?", Ban gama tunani ba naji dad yace "zauna duka zan baki ansar tambayoyinki", Ashe maganar zucin da nakeyi ta fito waje, zama nayi cikin son jin labarin na fuskanci Dad. "Labari ne mai tsawo Wahida, tun kafin Shahid ya tafi Lagos ranar da yake shirin tafiyar, Small yake fada mn wai Shahid yana shirin tafiya kuma wai bazai dawo ba sai da mata, nayi baqin ciki sosai a lokacin da naje gidan har ya tafi, numbern wayarshi a kashe, sau uku ina neman wayarshi bai kunna ba, ganin haka yasa na rubuta mashi text kamar haka: Assalamu Alaikum Son, Naji labarin tafiyarka a bakin Small, amma lokacin danazo gida har ka tafi, ina ta kiran numbernka kuma shiru, kuma kace bazaka dawo nan ba sai kayi aure, to ni kuma gaskiya kusan duk ban yarda da matan Lagos ba musamman na bariki, akwai wani abokina dake zaune Lagos da iyalinshi, yana da 'ya'ya duka 'yan mata, zan mashi magana sai ka zabi guda daya a ciki saboda yaranshI suna da tarbiyya, amma bazan mashi magana ba sai ka kirani dan in tabbatar da kaga text dina. BISSALAM. Bayan kamar sati biyu naga kira da wata sabuwar number, na dauka nayi sallamh najI muryar Shahid, munyi magana sosai kuma ya amince da za6i na, yaje gidan amini na wato baban Zainab, ya za6i zainab saboda tafi duk sauran yaran hankali, ba'a dauki lokaci ba aka daura aure".BANA KAUNARKA!!! 49 Cikin damuwa na miqe tsaye saboda wani irin ZAFIN SO (A novel din amrah) da naji na Ya shahid, ya kishin shi da nake ji. Dad yace "koma ki zauna mana, ai ban gama ba". Komawa nayi na zauna jiki babu qwarieh na fuskanci Dad, yaci gaba da "tunda aka daura auren Shahid kullun sai munyi waya dashi, ganin ya kasa daurewa da rashinki yasa na yanke hukuncin a hada aurenku dana mahida, ba tare da kin sani ba, yanxu haka maganar da nake miki ke matar Shahid ce". Ido bud'e nace "what? Dady me kake fada ne? Yaushe na auri Bomboy?", Dad yace "ki kwantae da hankalinki zaki fahimci komai", Kai kawai na daga sannan yace "har mahaifiyar ki ta san da maganar auren, kuma kema inda kin kula a lokacin da ake maganar auren kusan komai sai an ambace ki, duk dangi sun sani ke dai ce baki sani ba, sannan kuma tunda aka daura aurenku na hanaki fita mara muhimmanci, ko a skul na hana ki hulda da maza baki daya sai dai mata, matan ma wanda na yarda dasu kawao". Sai a lokacin na tuna da duk maganganun Dad, na tabbatar da ni matar shahid ce, tou ni yanzu murna zanyi ko baqin ciki? Na ma rasa abnda ya kamata nayi, gashi fai ina son Bomboy amma bazan iya zama da kishiya ba. Note: gareku mata masu qin kishiya. Ehh tabbas kishiya abar qi ce, amma kuma sai musan kalar qiyayyar da zamu nunawa kishiyarmu. Allah da kanshi ya bada ixinin auren mata hudu indai namijin zai iya adalci a tsakaninsu. Tambaya anan itace ; shin zamu haramta abnda Allah ya halalta ne ko kuwa?, yana daya daha cikin abnda ya halakar da mutanen da sukazo kafin mu, haramta abnda Allah ya halalta, da kuma haramta wanda ya halalta. Tabbas Qur'ani shine babban abn koyi, domin kuwa a cikin shi yake dauke da duk wani abu da muka sani da wanda bamu sani ba, haka zalika Qur'ani yana kawar da duk wani baqin ciki ko damuwa, a duk lokacin da mijinki ya fada miki zai qara aure dan Allah 'yar uwa kar kiyi hauka ko nuna rashin class, dauko Qur'an kiyi karatu insha Allahu zakiji komai yazo miki da sauqi, zakiji duk wata damuwarki babu ita, zakiji kishin yayi sauki fiye da kafin kiyi karatun. Ya Allah ka qara tsarkake mana zukatan mu, ka raba mu da jahilin kishi.BANA KAUNAR KA 50 KARSHE A hankali Shahid ke taku har ya iso Inda nake, hanky din hannun shi ya fara goge min hawaye dashi, sosai naji kunya amma sai na samu kaina da kasa hana shi. Sai daya ga babu sauran hawaye tukuna ya daina gogewa, yace "Wahida ina so kiyi haquri ki dauki kaddara, ki cire duk wata damuwa dake ranki, duk abnda kike gani ya faru tou dama can rubutacce ne. Zainab da kike gani wlh bazata taba yin kishi dake ba, ki dauke ta tamkar kanwarki ta jini, Wahida ina sonki, son da bazan taba iya yiwa wata mace ba". Zainab tayi saurin zuwa inda nake tace "qwarai kuwa Wahida, tunda nake a rayuwa ta ban taba ganin soyayyar gaskiya irin wadda shahid yake miki ba, so da yawa yana yi mn maganarki, sai dai naita mashi adduah akan Allah ya karkato da hankalinki ki so shi, sai gashi yau ke da kanki kin furta kina son Shahid, nafi kowa jin dadin hakan. Dan Allah ki riqe ni tamkar yar uwarki ba kishiya ba". Tsam ta rungume ni tana mayar da numfashi, hawaye na na sauka a kafad'arta. Babu wanda baiji dadi ba musamman Mahida da harda sajdatul- shukr tayi, mom ma har da hawayen murna tayi tana shi mana albarka. Bayan shekara hudu. Wasu yara muka hango su uku kusan duk girman su daya, sai dai daya tafi biyun girma. Biyun siffar su daya baka ita banbance su, sanye suke da kaya pink iri daya. Tun daga nesa mukaji suna fadin "Momy! Momy where you dey?", "I dey here my bebes, ba dai kuna nufin har kun dawo ba?", wadda tafi girman ce tace "Momy Afrah ce ta fara kuka wai Ita sai an dawo gida, shine momy Mahida tasa driver ya dawo damu". Wadda aka kira da Afrah tace "Momy fa Farhat ce tace wai tunda gobe Monday muyi saurI mu dawo yunda bamuyi Home work na Friday ba", Farhat tace "Laa Momy fa babu ruwa na, dan Allah Aunty Meenat ba Afrah ce tace mu dawo ba?". Tun daga cikin gida mukaji muryar Zainab tana fad'in "kai yaran nan akwai ku da rigima, ku dai dole sai kowa yasan kun dawo". Da gudu Farhat ta rungume Zainab tace "My dear wlh babu ruwa na Afrah ce", nan suka hau rigima kowa na fadin babu ruwanta. Zainab itace ta fara haihuwa bayan tarewar Wahida, ta haifu kyakkyawar yarinya aka saka mata Aminatu (Meenat). Bayan shekara daya kuma Wahida ta haifi twins duka mata aka saka masu Afrah da Farhat. Yanzu haka Wahida na dauke da juna biyu haihuwa ko yau ko gobe. Zaune suke cikin farin ciki da qaunar juna, idan ba an fadawa mutun ba bazaka taba gane kishiyoyi bane. THEY LIVES HAPPILY. TAMMAT BI HAMDULILLAH. ANAN WANNAN LITTAFIN MAI SUNA "BANA KAUNAR KA" YAZO QARSHE. KURAKUREN DAKE CIKIN SHI MUNA ROQON ALLAH YA GAFARTA MANA. MUNA FATAN AN FADAKARTU KUMA AN NISHADANTU A CIKIN WANNAN LABARIN. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 6 of 6