Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
yai saurin rike ni don ganin lokacin kankani na zafge abba yace wahida dama baki da lafiya natsunguna don kafafuna ba zasu iya dauka taba ya amin neya kama ni taso mu tafi asibiti abin ka da yar gatan al'amin tuni ya kaita babban asibiti inda aka bata gado hankalin al'amin bai kwanta ba sai da yaga ta samu bacci bayan azahar ina kwance dakin ni kadai sai ga ya shahid da haidar da yake a asibiti din ya haidar aiki sukai sallama na amsa da sauri bom boy ya karaso sannu sister yauwa ya shahid ina anti?BANA KAUNAR KA!!! 9 tana miki sannu ina amsawa baku biya ta gidanmu ba? mun biya mom da anty sunan nan zuwa ya haidar don Allah ku bani sallama naji sauki sai gobe na tura baki ni wallahi tafiya ta zanyi ki fita mana mu gani asibiti din da karnuka cinye ki basai in ari bindiga gun ya shahid ba in sn biyo ni in harbe su dariya suka dinga yimin ya shahid ya zauna bakin gadon kusa dani ya janyo ledar da suka shigo da ita ci mata ce tarkacan kayan zaki aikuwa tuni na shiga lashe-lashe haidar yace um su wahida ba dai kwadayi ba bom boy ya kai masa duka tare da fadin akwai wacce takai mahida kwadayi yarinyar da take cin faea naga alamar ka raina wahida,wahida fa antinka ce Allah ko Allah matar yayanka ce tunda ga lokacin ban kara magana ba har suka karaci surutunsu suka fice,koda naji shiru gashi ni kadai tsuru ai sai na zari mayafina na fice nayi sa'a likitocin bbu wanda ya ganni na zagaya ta baya kamar wadda tazo dubiya na fice ina fita na samu me adaidaita sahu na shiga sai gida ko kudin ban bashi ba na fice sai me gadi na ya bashi ina shiga na tadda suna shirin fitowa har anty tazo ina shiga mahida tace mom kinga wahida ta dawo da sauri suka fito wahida wa yace ki taho? to mom sai a barni ni kadai ni kuma naga naji sauki nai tahowata ai shikenan ke da al,amin.bayan kwana biyu abba ya tara mu yana son jin ra'ayin kowa,ya amin yace ni dai abba ba yanzu zanyi aure ba asali ma niko budurwa bani da itw ai min afuwa zuwa nan gaba Abba yace faruq ya faruq yace abba aure zanyi don na samu wadda nake so wacece a ina take? abba mamy ce yar baba rabi,u da kyau inji Abba mahida ina jinki nima abba na samu wanda nake so haidar din anty da kyau wahida ina jinki tuni nai raurau hawaye ya soma shatata,abba yace ban da kuka cikin rawar murya nace Abba ni karatu zanyi ya faruq yai farat yace ba wani karatunda shahid za,a hada ku ai kuwa na saki kuka ni wallahi bana sosa karatuna zanyi abba yace yi shiru bbu me yi miki dole yadda kowa ya ce ga wacce yake so ke ma sai kin furta sannan zan hada ki da wanda kike so abba kana ji ya faruq yace da ya shahid za,a hada mu rabu dashi bbu me yi miki auran dole ni a ra,ayina bani da niyyar tauye muku hakkinku duk da ina da right din da zan zaba muka maxan da suka dace daku amma nafi son ku kawo da kanku tunda kin zabi karatu Allah ya bada sa,a Allah kuma yai muku albarka amin ya faruq bai so haka ba domin so yai ko ina so ko bana so a aura min bom boy,koda abba ya tara yan uwansa ya fada musu ra,ayin ya,yansu sunyi farin ciki ainun sai dak sun so ace wahida ta zabi shahid ko da abba ya fada musu ra,ayin wahida na son karatu sun yi na,amm sannan sunyi mata fatan alkairi shi kanshi yaji dadin yadda yan uwan nasa sukayi na,am da ra ayin wahidar dama su yake ji domin in sun tubure sai wahidar ta amince da shahid din dole na ta amince ko bata so domin yayansa alh.rabi,u zai iya cewa ba a isa ba dole abi son ransa.BANA KAUNAR KA!!! 10 bayan kwana biyu da yin maganar ina zaune dainmu ina karatun wani littafin addu'o'i ya shahid yai sallama na amsa ciki-ciki'domin yanzu haushi yake bani ya zauna kusa dani bai magana ba sai da ya shafe kusan minti goma sannan ya kalle ni 'ba ki iya gaisuwa ba ne ?na dago " sorry na manta ka tafi lafiya? gani nan lafiya ba lafiya ba lafiya nan da sauki wahida ina son muyi wata muhimmiyar magana okey ina jinka wahida kin san ina sonki ko? what nikake so? wahida me yasa kike son wahalar da dan uwanki...? ban gane nufin ka ba kin san mahida ta zabi dan uwana a matsayin abokin rayuwarta ina so kema ki sauke ra,ayin son karatu ki amince min billahillazi nayi alkawarin barin ki ki ci gaba da karatunki nai murmushi shahid kenan na fada maka bani da lokacin soyayya kwata-kwata ba zan iya hada karatu da soyayya ba shikenan zan iya jiranki ko nan da shekara goma ne no ka nemi wata kawai wahida kin san kuwa irin azabar da nake ji? oho kai kaso ka don haka bbu abinda ya demeni domin na fada maka gaskiya wahida nifa dan uwankine wahida me yasa ba kya sona in wani hali nake dashi wanda ba kya so dan girman Allah ki fito ki fada min kaga na farko bbu abin dana tsana irin shan taba kai kuma kana shan taba,maganar gaskiya ina zarginka da abubuwa da dama shahid ko ba haka ba dama ance sojoji suna shaye shaye kuma suna neman mata wa'iyazu billahi yace tare da mikewa ya cillo min kati gashi nan na baki cikakken sati kiyi bincike a kaina bayan taba me take sha tabar ma koki ka sank sha amma insha Allahu daga yau na barta har abada yana gama maganar ya fice jiki babu kwari.tunda wannan lokacin na shiga bincike kan bom boy har har sati biyu amma ban ga wani aibunsa ba in ban da da yake samu gun jama,a da dama sai dai wani abu ko kadan bana jin sonsa sai ma hausinsa da nake kara jiba kamar in na tuna shi soja ne kuma mugu ne na karshe domin bana mantawa ina karama mugun tsoransa nake innai abu aka ce za a fada wa shahid na kanyi kuku domin ban bashi da wasa gashi da girman kai rashin son magana yanzu ne fa da yake sona yake sakar min iska ni na san yana aurata zai daina sakar min fuska koda dama ance matar soja sai hakuri.kamar kullum ina zaune ya shigo da sallama tun kan ya karaso kamshin turaransa ya cika dakin kai gaskiya ina son turaransa haka nan kamshin kan sani farin ciki ko da kuwa ina cikin bacin rai gashin ban san sunan turaran ba bare in siyo gashi ina ganin kamar zubda ajine in tambaye shi sunan turaransa,kamar kar in amsa sallamar sai kuma na tuna girman sallama da darajarta sai na amsa ciki ciki na janyo remote na kunna T.V domin ta taya shi hira na mike domin in bar masa dakin suyi hirar da T.V caraf ya kamo hannuna sai naji hannunsa dumi ga wani irin taushin ji nai kamar in kwace hannun don wani irin sanyi dadi naji yana ratsa zuciyata na daddage na tofa masa yau a hannu ya daga hannun a tunanina mariina zai ko ya goge min yawun a jikina amma sai naga akasin haka domin ganina yasa harshe ya lashe yau din yace baki san yawunki yafi ice cream ba a gurina na yamutsa fuska ashe kai kazami ne??BANA KAUNAR KA!!! 11 ya harare ni ban sani ba ya sassauta murya wahida kome ya fito daga bakinki zan iya cinsa har in nemi kari nai tsaki ni dana ji ance sojoji zuciya gare su ko wannan bashi da zuciyane nai tsaki a fili nace bani da lokacin aure amma ka like kamar tsohon maye ina gama fadar haka na bar masa dakin,yau ma ina zaune ya shigi yana shigowa ya tsugunna yace good morming my sweet heart na mike cikin fushi kai tsaya kaji BANA KAUNARKA dama haka kake son in fada to na fada BANA KAUNAR KA so what? ya rike baki cikin mamaki nai tsaki tare da murguda baki na juya zan fita ya finciko ni na fada kirjinsa a hanzarce na dago cikin zafin nama na fidda hannu na sharara masa mari na ce kar ka kara taba ni ko an fada maka nima irin yan iskan yan matan nan ne niki ka mara wahida? an mare ka who are you? mahida ta shigo a fusace ta finciko ni ta kai min mari tare da hande ni tace shegiya mara mutunci don kinga yana sonki, da gudu na fita ina kuka nai dakin yaya amin,mahida tace don Allah shahid kayi hakuri hannu ya daga mata tare da ficewa ina shiga yace wa kuma ya taba ki? nai shiru mahida ta shigo yace mahida me kikai wa yar uwarki? yaya wallahi wahida bata da mutunci bata da kunya ya shahid fa ta mara mari wahida! shahid din kika mara? to me yasa zai dinga yi min naci nace bana kaunarsa dan me zai takura min ko ana dole a so ni wallahi.......tswa ya daka min cewa nai me yai miki? to meyasa zai dinga yi min naci shi kenan zan masa magana amma ki bar saurin marin babba ko zaki iya marina? na girgiza kai na ce na daina yaya ya mike ya shiga wanka na kalle take kuma munafika meye dalilin na marina na mare ki dan kuma na isa ne karki ga na kyale ki yanxu wallahi kika kara marina sai na ram........kan in karasa ta kuma marina,tuni fada ya kaure muka kama fada ya faruq ya shigo la! fada kuke yi ba za ku bari ba sai na zane ku ko da taga na sata kuka sai ta ruga gun mom tana kuka sosai mom tace zo auta me ya hada ku? nace mum marina tai nima na rama mum ita fa yaya shahid ta mara mari wahida? to me yasa zai takura min nace bana kaunarsa anya wahida baki da kunya to mom,mom ta ture ni ba ruwana dake mara kunya me zagin manya la! mom ba fa zaginsa nai ba tunda kika mare shi wata rana zaginsa zakiyi,Allah mom bazan kara batun daga wannan ran ban kara sa bom boy a idona ba ni kan hakan ya fiye min sauki ina falonmu mom tace wahida zo in aike ki gidan sister khadiya tana nufin gidan anti nace to mom mum ta bani sakon a motar mahida na tafi ina zuwa nai fakin na fito nai sallama falon yana kwance kan 3 sitter nai wuce wata dakin antin ina ji yana ba gaisuwa wahida? nai masa banza nai sallama dakin antin sai gashi ya shigo yana fadin anti bata nan na juyo zan fita sai ya tare kofa bana son wula............BANA KAUNAR KA!!! 12 ya janyo ni ya rungume tsam yana fidda wani irin numfashi nace ka manta na hana ka taba ni? juyo dani yayi ya zubo min mayatattun idanunsa duk na dabarbace da kyar na ture shi nace ashe dama ba sona kake ba sha'awata kake yace what? na hankade shi da gudu yasha gabana wallahi sone ba sha'awa ba ce kauna ce na ce cikin tsawa kai dallacan rufe min baki ya finciko ni tare da doke min baki ya kara yi min wawuyar runguma anyi sha'awar taki ba a kaunarki za'ayi sha'awarki stupid kawai,nace ashe ai ban san kai dan iska bane.....yau ai kin sani nan gaba zaki karasa ni kin gane, yawu na tofa masa nace mara zuciya kawai kamar jira yake ya lashe yawun da sauri na fice.tana fita ya fadi a gurin yana numfashi sama sama me yasa wahida bata sona me nai mata ko dai hakura zan yi da ita kai ba zan iya hakura da ita ba ba zan iya ba ya fada cikin karaji da gudu haidar ya shigo ya rike shi kayi hakuri bom boy ya fincike haidar fada min me nake dashi wanda ban cancanci a soni ba? ka cancanci aso ka bom boy kana da kyau kana da aji kaine yammata ke rubibi a kanka ne zai hana ka hakura da wahidar nan ka nemi wata ba zan iya ba small ina so wahida so bana wasa ba.....tobya zaka yi tunda ita bata sonka kana ganin irin rashin kunyar da take maka kai dana sonka da zuciya kana gani fa har yawu take tofa maka kawai ka share ta no ba zan iya ba small ina sonta zan jure duk wani salon kiyayyar da wahida zata nuna min. wannan shine takaitaccen labarina amma ku biyo ni don jin ci gaban labarin.mamy ce ta dawo dani daga duniyar tunanin da na shiga tace wahida mun shiga uku me kika yiwa bom boy na tashi zaune wani abu yace miki nai masa a,a yanzu naga dan uwansa ya kamo shi ya fita dashi hannunsa kan kirjinsa ko meke damunsa na tabe baki Allah ya kyauta atu tai sallama tace lafiya na ganki cirko cirko umh wai bom boy ne ba lafiya subahanallahi ba muga ta zana ba meke damunsa mamy ta nuna itace wallahi atu wahida yake so ita kuma take gara shi ta kalleni cikin fada tace kin san Allah muddin jikana ya mutu akan sonki wallahi mun kulla kun san duk cikin jikokina nafi son shahid nace ai sai ki aure shi tunda kin fi sonsa ni dai bana sonsa amma fa a zuciyata a fili kuma nace inma ya mutu shi sayo ni kan ko a kaina da gudu ta wawuro tsintsiya ta bini. Ranar litinin al,amin ya dawo bayan ya huta sai kiran mahida yace mahida ina wahida? wallahi ai tun ran daka tafi ta bar gidan....saboda me? dan ya furuq yai mata duka shine ta tafi abba yace inje in taho da ita amma tace in munga ta dawo gidannan to dan uwanta ya dawo al,amin ya mike dakin faruq ya shiga ya finciko shi wai kai wanne irin mugune azzalumi me wahida taimaka faruq yaja shaka yace yi hakuri big brother ba zan kuma ba so nake ka fada min abin da tai maka da har ka raba tada gida faruq ya fada masa duk yadda akayi tsaki yayi ya juya ya fita bai zame ko ina ba sai gidan atu ina sharar tsakar gida yai sallama nai ciki datsin tsiyar na rungume shi ya dago ni ya dunguran goshi me ya rabo ki da gida nai raurau yaya in baka nan ab tsaneni kullum cikin duk ni kuma na baro musu gidan yace min fa rashin kunya kike masa ni ba rashin kunya nai masa ba wai dan nace ba zan cewa mahida anti ba to shikenan ki shirya mu tafi ya wuce dakin atu.BANA KAUNAR KA!!! 13 muna zuwa gida da gudu na fada jikin mom ina murna mom ta ture ni ni daga ni kai mom baki gane ni ba autar ki ce fa wahida me nai miki mom? kin fi kowa sani to yi hakuri mom na daina mahida ta fito tana hararata kai anti mahida me nai miki ta dungure ni ni ce ai zan ce miki anty ta kamo hannuna taso muje dakinmu na bita gaba daya dakin ta zagaye shi da manyan hotunan haidar da bom boy wani muduka sai wanda tasa aka hada mu nida bomboy ina sanye da wani material me tsananin kyau domin hoton ya dauku domin nayi kyau ainun mun dauki hotanne lokacin da mukai partin candy dinmu shima yayi kyau dama tare muka dauka amma lokacin bai nuna manufarsa a kaima ba yadda mu kai hoton in kin gani sai ki rantse muna son juna don gannin yadda na shisshige masa munyi kyau sosai ni kaina ina son hoton na kalle ta sai naga tana faman dariya na karaso yana da manyan idanu masu tsananin kyau da idanunsa ban tsoro domin in ya zare min ido sai nayi fitsari amma a yanxu suna birge ni inason kalar idanunsa masu zubin ruwan gol sam bana iya hada ido dashi domin wani shokin yake sakar min idanunsana hargitsa min lissafi sannan suna tsuma min zuciya toko shine so? kai ni na so ba son sa nake yi ba kauna ce ta yan uwantaka sannan yadda wannan dogon sajan dake kara fito da samartaka dogo ne shi domin bashi da kiba sai dai yana da faffafan kirji sannan yana da kirar karfafa jaruman maza fuskar nan kulum dauke da annuri kamala,kwarjini duk fa yadda naso fasalta muku bom boy ya wuce haka sai dai ince duk inda namiji ya kai da kyau iya diresin bom boy ya kai har ya wuce. mahida kin san abin da yake hada ni dake kuwa? a,a kin gan ki wallahi za,ayi muguwar kazama saboda me kika ce haka? a farko kin ga dakin nan ina tunanin tunda na bar gidannan baki taba daukar tsinstiya da sunan zaki share dakin nan ba ko kin share? to ai bai yi dauda ba da kyau kinga kan kayan kallonnan kalli yadda sukai mugun kura mahida kalli zanin gado kalli tunin kayan dauda ke dai sai dai ki fidda goma ki tsoma biyar Allah kar ki ce na rana ki kece me son auro muddin kika ce kazanta zakiyi wallahi kinyi asara soyayyar kanta bata yiwuwa sai da tsafta ko ba komai da tsafta tafi inganci tsafta cikon addini ke kenan daga kallo sai karatun soyayya Allah ya kyauta nai shigewata (toilet) ina shiga na fito saboda wani zarni (toilet) keyi nace mahida kin banu toilet din ma ba kya wanke wa??BANA KAUNAR KA!!! 14 zagewa nai na wanke toilet din nasa turare sannan na hada kayan wanki na bayar na cire zanin gadon na sa wani na share na goggoge ko ina nasa wa dakin turaran wuta ina sallah haidar yai sallama ita kuma tana kwalliya bayan na idar na gaishe shi na fice a zuciyata nace da haka zai zo ya samu dakin kamar bola? ina kwance a falo bom boy ya fito daga dakin yaya al'amin ya karaso ya tsugunna gabana wani kallo nai masa tare da nace lafiya dai ko? yace lafiyar ce ta kawo haka please ki taimaka min in taimaka maka da me? so? ya furta nace so menene kuma so? kina son sanin menene so? look at me na mike domin na san ba zan iya abin daya sani ba caraf ya kamo hannuna a fusace na juyo tare da tofa masa yau ina daga idona muuka hada ido daya al,amin gabana yai wani mumunan faduwa shi kenan ta faru ta kare an yiwa me zani daya sata wata irin harara ya wullo min ai da gudu nai dakin mom na fada jikinta mom ki yiwa bom boy magana nace bana sonsa bana kaunarsa! meye zai dinga takura min?,yakike so in yi masa wahida? so kike in tare shi ince kar ya kara kula ki? in kin yi tunani koba komai shahid ai dan uwankine da mahaifiyarsa da ubanki cikin su daya haba auta kiyi hakuri ki sassauta wannan bawan Allah ni wallahi nafi miki sha'awar shahid ko kina da wanda ya fishi,gaskiya mom ku hana shi zuwa gidannan in ba haka ba sai in bar masa gidan in koma katsina mom inaji ana cewa soja akwai zuciya shi kuwa wannan ba shi da zuciya mom tace ai so daban zuciya daban kuma wallahi na amince da son da shahid ke miki na mike na fita don bana son zancan daki na koma dakin bbu kowa da alama sun tafi yi musu rakiya na kwanta sai ka na mike na shiga toilet nai wanka gidansu wata yar class dinmu tun muna primary ina kallo yaya alamin ya shigo fuskarsa bbu walwala yace wahida duk irin rashin kunya da cin mutuncin da ake cewa kina wa bom boy ban taba yadda zaki aikata ba sai yau ashe baki da kunya a gabana kika tofa shahid yau na zumburo baki nace to yaya ai shi ne bashi da gaskiya dan me zai dinga rike min hannu ni kuma na dau alwashin muddin zai taba ni sai na tofa masa yau amma komai ya mike kekikaja tunda kin san yana sonki wahida ya kamata ki sassauta wa shahid ki dinga fada masa kalamai masu kwantar da hankali ko ba kya sonsa bai kamata ki dinga yi masa abin da kike masa ba yaunzu ki taso muje ki bashi hakuri tabdijan gaskiya ba san iya ba ni dai na fada miki kai don Allah yaya kana gani na ci kwalliyata gidansu da yar ajinmu zani yai tsaki ni dai nace ki jira ni in shirya ya fice nai zaune ina mamakin yaya al'amin naga alama so yake inji kunya yanzu ba kunya sai inje in bawa ya shahid hakuri hum'um ai ba zata zabu ba ina nan zaune ya shigo yayi kyau sosai ya rankwafo ta mudubi na kalle shi yaya kana kama fa da bomboy ainun wahida bom boy bai fini kyau ba no haske kawai ya fika amma kamarku har ta baci na dauko hijabina muka shiga dakin mom,BANA KAUNAR KA!!! 15 ya amin yace mom zamu gudan anti to amma kar ku dade kun san abbanku ya kusa dawowa nace anty mahida zo muje mana ta kara makalkale mom tace wallahu naji dadin kwanciyar bacci zanyi nace mom ki ture ta kar ta karasa ki min isa gidan bom boy a falo tare da small suna kallon kwallo mu kai sallama suka amsa na zauna kusa da ismail yaya amin yace ina anty? anty ta tafi katsina gaisuwa amma yau zata dawo inji bom boy, ya amin ya kale ni nina so na manufarsa amma sai na share,bom boy ya taso ya dawo kusa dani yace anti wahida ba gaisuwa? na kalle shi ya rame sosai yayi wani irin kyau yace me kike so in kawo miki ne nai masa banza haba my dear daure mana ki min magana caraf ya kamo hannna ya murza Allah ba dan na tuna maganar ya amin ba da tuni na tofa masa yau,cikin kasa da murya kamar yadda yake min magana kasa-kasa nima nace "bana so kana tabani,no ki barni in samu nutsuwa....... Allah sai dai kar ka samu muddin sai ka........shut up kina so tara min tawage ne kike daga murya,ai gani nai irinku sai da daga murya........me kike nufi wallahi wahida ki shiga taitayinki muddin kika shigo hannu sai kin.....Allah abbana ko ince Allah Al'amin kanina ne Allah ya kyauta kaine ka girmi ya Al"amin? to ki tambaye shi mana na mike domin ya ishe ni ni lambun gidan na wuce nai kwanciya iska na kada gashin kaina duk saiya lullub min fuska. jin motsi kusa dani sai na tattare gashin tsugunne yake gabana ya zuba min mayatattun idanunsa na hararw shi yai murmushi yace sahiba tunanin me kike? wace sahibar kaje ka nemi sahibarka ba dai wahida ba wahida me yasa kike garani kike gasa min gyada a hannu? saboda BANA KAUNARKA! inda wanda nake so,ko ka gane? keh! wallahi na fara gajiya da wannan wulakancin na ki ko don kinga ina sonki? to kayi zuciya mana ka sake wata zan baki mamaki ba zan sake wata ba amma zaki gane kuranki,aikin banza ai na dauka zaka yi zuciya ashe ba a da ita,ya finciko ni cikin zafin nama sai gani wanwar a jikinsa sai kawai na saki kuka ya hankade ni ya barni gun a zuciyata na ce Allah ya isa mugu kawai na mike na goge fuskata. kicin na shiga na dan yi wa anti girki kasancewar na san dadin su bomboy yafi son tuwo sai nai tuwan shinkafa nayi sa,a tuwan yayi kin yadda nake so na nannade shi a leda sannan na daura miyar agushi wadda ta amsa sunanta domin taji nama ina gamawa sai na daurawa shahid nasa domin sam baya cin tuwo miya ina soya sannan na dafa shinkafa na yanka salat na ajiye gefe sai dana kammala nasa sannan na hada lemuka kala uku nasa a firij kasancewar na san shahid na son gashasshen nama sai na gasa sannan na yanka kanana-kanana daidai yadda zai iya hada da abincin koma wa nai na gyara falon domin gaba dayansu suna dakin small na kunna turaran wuta.BANA KAUNAR KA 16 ina gyara dakin anti antin tai sallama nace sannu da zuwa anty yauwa wahida sannu da aiki small ya shigo anti tace lafiya na ganka kamar mara lafiya? ya shafa cikinsa yunwa muke ji tun daxun muke jiranki bafa abin da muka ci sai take away ao sorry my son bari inyi sallah in shiga kicin bayan kowa yayi sallah anty na zaune dukkanin su sun hallara a falo sai na shiga jera abinci kowa na kallona sai dana zauna anti na soma zubawa sannan mu kuma na shimfida dadduma domin nafi son cin abinci a kasa gaba dayanmu na hada mana bomboy yai tsuru domin yasan wahida ta san baya son tuwo shine kuma tai tuwo amma kuma zai bata mamaki,Allah sarki bai gama tunani ba yaga ta janyo kula da filet ta soma hada masa nasa na musamman tuni su al'amin suka ce ba,a isa ba sai dai suci tare kasancewar da yawa sai na hada yadda zai isa ai kuwa suna ci suna santi gaba daya sai da suka share abincin nan suka koma kan tuwo nan suka dinga santin tuwan bom boy na gefe small yace Allah bom boy cikaji tuwan yafi dadi loma daya yayi ya kada kunne gaskiya yai dadi amma na koshi sosai,bayan sun gama an sha lemu ba kwashe kayan sannan na gyara gurin,ya amin yace ki zo mu tafi dare nayi anty tace ka barta tai min kwana biyu yace shi kenan,har gun mota na kara shi ya kalle ni yace yanzu sister sai yaushe kenan? sai randa anti tace in dawo zan dawo to duk randa zaki dawo ki yo min waya,Allah wahida nafi sonki kusa dani sam bana son ki min nisa nai murmushi yayana kenan,ni kaina nafi son zama cikin yan uwana to amma yaya zan yi? ya tada motar na daga masa hannu har ya fice ina tsaye tabbas ina bana son rabuwa da yaya dan dai ba yadda zanyi ne. Da safe da wuri na shiga kicin na hada breakfast anty ta shigo oh wahida break fast din ma bazaki kwanta ki huta ba anti ina kwana lafiya lau wahida ya gajiyar jiya ba gajiya , daki na koma nai wanka sannan na fito cikin doguwar riga gaba daya suna falo na tsunguna na gaida dad dinsu ya shafa kaina yace ina mahida nace tana gida dad dinsu bomboy yana da kirji ga wasa da dariya mutum ne mai kirki sam bashi da wulakanci.bom boy ne zaune yasa hoton wahida gaba yana ta faman sambatu yace wahida me nai miki me yasa ba kya sona? me nake dashi wanda ba kya so ko sana'a tace ba kya so? billahillazi in ba kya so na ni kuma zan iya bari,me yasa ba kya sona wahida me nai miki ki tuna fa ni dan uwanki ne ya kamata ki sassauta min ki tausaya min ya daga hoton wahida kin yadda kina sona? za ki kasance me farantamin? zaki zamo uwar yayana daure ki ban amsa haba yar uwata abar alfaharina haidar ganin dan uwansa na shirin zautuwa akan mace yace haba my big brother ne yasa kake wahalar da kanka akan mace? kai rufe min baki ko dan kaga ka samu taka shine kake min bakin ciki akan tawa? haba bom boy in ban da zarewa sai kasa hoto gaba kai ta sambatu ni wallahi dana dauka kai da wahidar ne sai dana shigo naga ashe hoto ne kai small tashi bani guri don na

Chapter 2 of 6