Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
gane so kake ka raba mu to kayi kadan domin kaunarta nake small ya kwashe da dariya sannu mai sahiba,BANA KAUNAR KA!!! 17 wahida in ce dai ta san kana yi? bari kaji in da ake soyayyar gaskiya ya dauko waya hadda sa handfree hello my dear kina lafiya? lafiya amma ba lau ba what? me ke damunki? ciwon rashin ganinka ina sister ta saku? wani zancan sister ki tana nan lafiya to ka gaisar min da ita kafin nazo okey zata ji yanzu me kike yi? tunaninka da son ganinka okey zan zo anjima me kake so in tanadar maka? nafi so ki akan komai na gode Allah ya kara mana son juna amin my sweety i love you so much gaba daya suka sumbaci wayar small ya kalli shahid ka gani kuma kaji da kunnanka shahid yace tsaya kaji nima ai tana sona tsabar ajine amma bari kaji ya kira wahida cikin sassanyar muryarta tace salamu alaikum amin wa'alaikaikumus-salam kana lafiya?yai murmushi farin ciki ni kaina saida naji sautin murmushin me kike yine? ina kwance ko wani abu zan maka? a,a kawai dai ina son jin ya kike ne? to na gode my brother a,a ban yadda ba to my shahed tabbas yaji dadin yadda ta furta a tunaninsa tunda aka rada masa sunan bai taba jin wanda ya fadu sunan yai masa dadi ba sai wahida yai murmushi yace ban yadda ba to my bom ke! ke! ke! please i am sorry my lovely tank u very much tsalle ya dinga yi yana adungure small ya rike baki anya ba allurar shahid bace ta motsa? small yace anya brother ko dai allurar ce ta motsa dariya kawai yayi,da rana bayan an gama girki ina kwance dakin da aka ware min ina wasa da waya wato game wayar tai kara hello sister ya kike? yadda kike mon,abba sahibina suna nan lafiya? nace baki tambaye naki shahibin bane? ai yanzu muka gama gaisawa sannunku uwayen soyayya,kefe ke ni soyayya bata gabana karatu nasa a gaba to anry wahida daga karatu sai me- ke ki daina ce min anty to me zan ce miki? usaina wayyo kin cuce ni ki ce min autar mom da abba da ya al'amin kin san ko yanxu mom ta haihu kin tashi daga auta? me zai sa mom ta haihu ai daga kaina aka rufe fayil din'BANA KAUNAR KA!!! 18 to autar bom boy ai kuwa bom boy na gaishe ki ince dai yanzu kuna son juna haba dai mahida kina wasa dani wato kin mantani kenan kin sanni in nace in so to fa ina so in kuma bana so bana so na fada miki yanzu bani da lokacin soyayya karatu ne a gabana.....to uwar biro da takarda ya ishe ni ke kuma uwar soyayya fadi ki kara wallahi sai Aliyu haidar, da ya yamma ina kwance ya amin yayo waya salamu alaikum ya Al'amin ka tashi lafiya? lafiya my sister yaushe zaki dawo? kai yaushe zaka zo in ganka? in kinga shahid ai kamar kin ganni tunda kin ce muna kama koya kika ce? a'ah kai daban shi daban wai yaya su small sun girme ku? ke kin yadda? na dan yadda kadan amma to shi kenan ki tambaye shi kwana nawa ya bamu to ya ka gaisarmin da mom me zai hana ki buga ki gaishe ta? wayar tawa ce bbu kudi a ciki okey ki jira zan turo miki,godiya mara iyaka.minti ashirin ba'a yi ba naji karar text message ina budewa kuwa na shigar da lambobin #3000 ya sako min naji dadi sosai hello "na"am auta ya kike? "normal mom" auta ya gida yasu small? "suna lafiya mom ina nan zan zo "to sai kin zo mu kai sallama. SHAHID tsungune gaban anti,tace wai ina za a tura ku shahid?"anti addu'a kawai zakiyi min domin tafiyar tanada........kai k sanar da su baka da lafiya ba zaka ba shahid bana son rasa ka bana son aikin sojannan anti ni dai addu'ar nake muradi shi kenan ki sanar da Dad dinku dadditunkan lokacin na sanar dashi okey Allah ya taimaka, amin mom ta dauko wani littafin addu'o'i ta dauko ta mika masa ya amsa yasa aljihu sannan ya mika mata hannunsa ta sumbace shi,yaso ganin wahida sai dai bata nan domin ta tafi gidansu lokacin haka ya tafi amma ba don yaso ba yaso ganinta suyi sallama! bayan sati biyu muna zaune a falo "hello mom wahida kin wuni lafiya? lafiya lau mom kice mahida ta kawo min kayan ke me zai hana ki fada mata mom kin santa raina ni ina fada mata cewa zatayi ba zata kawo min ba leda ita waye ya raina wani? mom ita ta fara raini nike da ita wacece babba? mom ita ta girme ni da kadan amma ashe dai ta girme ki zan sa ta kawo miki insha Allah to mom na gode sai anjima. yaya faruq hello yayana ina jinki yace ince dai lafiya oh yaya kaga abin da yake hadani da kai ba ko ka tambayi lafiyata kace ya nake bana son jin yadda kai ken mun kai dai wallahi baka da sakin fuska kai dai me ganin fara'arka daga mahida sai sahibarka anty mamy,to ya ranki?BANA KAUNAR KA!!! 19 fari sol tunda ina da wanda zai min inji sanyi da ace bani da shi sai inyi kuka da samunka a matsayin yayana ke wahida Allah in na fito sai na zane ki Allah sarki duka don Allah in zaka fito ka taho da tabarya ko bindiga,na kashe wayar ina dariya a can gida kuwa,a fusace faruq ya fito hannunsa rike da belt kai tsaya yai dakinsu wahida mahida kwance ta takarkare tana waya yana shiga ya soma laftarta wayyo me nai maka ina wahida me za kai mata billahillazi in baki nuna min ita ba sai na zane ki mahida ta dinga dariya tace, wallahi wahida bata nan domin tana gidan anty yanzy fa ta yo min waya ta kare min rashin kunya dakin mom ya shiga mom ina wahida? wahida kwananka biyu da tafiya itama ta tafi gidan sister khadija ya juya yana gunguni dakinsa ya koma ya dauko waya bugu daya ta dauka hello kin san Allah in nazo gidannan sai na lahira ya fiki jin dadi banzamara kunya,Allah ya faruq kasan fa masoyina soja ne ni nasan in kazo gidannan ka taba ni sai ya harbe ka in kuma ka musa to kazo ni kuma zan masa waya ince ga wani yazo zai taba lafiyata kasan yana sona zai iya komai a kaina oho dai dadin abin ba sonsa kike ba la! da ka sani yanxu muna tsananin son juna na kashe wayar ina dariya.faruq ya cika da mamaki dama wahida na son shahid in kuwa haka ne gaskiya bom boy yayi dacan big girl kuma beautiful gentel girl dakin Al'amin ya shiga yake fada masa Al'amin yace kana mamakine? haba dole in yi mamaki ko dan ganin irin tsantsar kiyayyar da wahida ke nunawa shahid wallahi ka bar mamaki domin ka san bom boy dan soyayga ne tabbas zai iya lankwasa wahida san ransa. ina zaune ina karanta wani littafi da ya shahid ya siyo min mahida day amin da ya faruq wayyo dadi ihu na sak na kankame mahida cike da tsatsan farin ciki kicin na shiga na hado musu abin motsa baki sannan na zauna ya Al'amin ina wuni sister ya gida? lafiya lau na lalli ya faruq koda ba gaishe shi kallon arziki bai min ba,anty ta fito tace a'ah lalle yau ina da manyan baki wahida me kika bawa ya"yan nawa? nai murmushi su ya amin suka gaishe ta na kalli mahida mahida ince ko kin taho min da kayana? ai zuwa muka yi mu tafi dake lalle ma keni ba yanzu ba Allah ko sai yaushe? na mike na koma kusa da ya faruq nace ke ni bar ni mu gaisa da yayana,na dafa cinyoyinsa ina tsungune kan gwiyoyiwa nace yaya faruq don Allah kayi hakuri wai ma me nai maka? na kwantar da kaina kan cinyarsa please ya faruq im sorry baki fada kunya Allah in baki bani guri ba zan yo boll dake,stupid girl,mahida ta taso kai don Aah yaya kar kasa ta kuka,ina laifi data baka hakuri,to ban hakura ba wato ke me yar uwa to kamo ni taso kinji anty wahida dadin ta ma ba Abba bane nice ke ma ba zan wani bashi hakuri ba muka koma kusa da yaya Al'amin muka ci gaba da hirar mu.BANA KAUNAR KA!! 20 Muna nan zaune bom boy yai sallama a,a kace muna da manyan baki hadda mahida a gidan? mahida tace Allah yata muna zuwa kaine dai ba a samu ka ga yanxu ma tun dazu muka zo ba don Allah yayi zamu gana ba har sai mu tafi ba ka nan,ni sister ma ce min tayi kwata kwata baka kasar tabbas jiya cikin dare muka iso ku bani ten minuti in yi wanka sai daya soma duba anty sannan ya shiga dakinsa nace yauwa ya amin ga bom boy muna so ju fada mana cikinku waye babba? mahida tai caraf la! baki sani ba ai tsiransu kwana biyu shi yasa ma aka hada sunansu akayi rana daya ke ni dai ban yadda ba duk......bom boy ne yai sallama idona har cikin nasa yai min kyau yana sanye da fakistan ruwan madara karasowa yayi kusa dani cikin rada yace gimbiya me zan samu rabona da abinci har na manta na mike na shiga kicin dama tuni nai masa tanadi na musamman gaba daya na hado musu dasu ya amin can lambu na koma i na zaune ya amin ya shigo ya zauna ya kalleni yace ince dai yanzu soyayar tayi karfi murmushi nai kawai domin nasan babu wata soyayya.bayan isha'i suka tafi mahida taso kwana nina hana ta domin inta kwana bbu mai taimakawa mom wajen shirya abinci duk illahirin yan aikin gidanmu sam mom bata bari suyi mata girki ita take yi duk da kullum sai an fita da abinci masallaci komin yawansa ni zan taya ta ko kuma niyi ni daya sam koka dan mahida bata son aiki aikinta kwanciya game,kallo,karatun littafi,Allah ya sani sam bana son halin mahida domin ya mace ko ba komai aure za ai mata san a rayuwTa bbu abin dana tsana irin kazanta muddin ina gida in kin ganni zaune da dalili shi yasa duk irin fadan da muke da ya faruq ko kadan baya so ya budi ido yaga bana gidan domin in ina nan dakunansu kullum ne saina gyara musu nice wanke musu toilet gyaran gado hatta yan aikinmu su kanyi missing dina. ina zaune dakina small ya shigo wahida bom boy na kira na kalle shi nace yana in ne? yana dakinsa na mike nasa hijabina na fita nai sallama yana kwance ya kalle ni cikin lumshe ido wahida nai masa shiru donni tsoro ya bani ma tunani ko wani abin yasha domin idanunsa sunyi jajir WAHEEDAH ya kara furtawa na'am na ce cikin sauri wahida bani da lafiya me yake damunka kece wahida kece ya kamo hannuna,hannunsa zafi kamar garwashi ba tausaya masa ainun amma don kar in kyale ya samu damar sai na fisge hannuna na ce bana son iskan....kafin na karasa ya fizgo ni ya rungume ni waye dan iskan? gabana ya shiga faduwa, ma don kar in nuna naji tsoro ya samu wata sabuwar damar sai na dake nace kaine dan.......yasa hannu ya doke bakina ya murde min lips ina wayyoahna! kafa yasa yayo ball dani sai gani a kofar daki da gudu na fita nayi sa'a falon ba kowa daki na shiga na kulle nai kuka mai isata. maheedah zaune tana game Al'amin ya siga dakin mahida ya kira sunanta ba tare data bar abin da take ba tace na"am kanna dawo ki shiga dakina ki gyara min kin ga yayi kura sosai to sai ka dawo nai taci gaba da harkar gabana sai kusan magariba ta tuna tai saurin shiga dakin ta burbura sharar minti biyar tana fitowa ya amin ya shigo kai tsaye yai dakinsa ai bai karasa shiga ba ya kwala mata kira mahida da sauri tazo me na saki?BANA KAUNAR KA!!! 21 Yaya ai na share maka ya kalli dakin cike da takaici ko tsarar da tai bata kwashe va a kofar dakin ta barta sannan dakin buzu buzu faruq yace ayya kadan daga cikin aikin mahida,Al'amin ai tayi maka mai kyau ni dana sata gaba daya karkashi gado ta tura min sharar ka ganta nan bbu abin da ta iya sai kallo sai soyayya Al'amin ya hau salati da kin san baki iya ba kice min to kanwar kanwarki ta fiki iya abin duniya,mahida kuka ta saka ai kun san tuni ya ba kuka sani al'amin dan haushin bai karasa magana ba lallai ya shiga tattare sharar. kwalliya nayi sosai na shirya cikkin wani ratsatten less,leshin ya amshe ni nayi kyau ainun na rataya jakata na sa karamin hijabi dakin dubai anty na tafi to wahida ki gaida mom amma fa kar ki kwana to anty a wacce mota zanje? ta mike ta dauko min mullin nace la! anty motar yaya shahid umh ni dai tsoro nake kin san motarsa da sunansa kar inje aka mani,antu tai ta dariya bbu me kama ki kallo daya za,ai miki a san ke kanwarsa ce,bbu me kamaki na juya na salube kai gaskiya notar akwai kyau, mota ce wadda ta amsa sunanta rantsattsiya kirar zamani gaban motar kawai zaki kalla kinsan waye me motar da manyan baki aka rubuta BOM BOY sai dana gama karewa motar kallo sannan na bude na shiga wayyo sanyi da kanshin me motar yaso rudata na shiga lumshe ido kwance nai cikin luntsumemiyar kujerar motar jina soma gyangyadi nai kirgil hoton me motar dake jiyawa gaban motar na zubawa ido yana murmushi yayi kyau ainun hannu nasa na shafi a fuskarsa tare da fadin i love you so much yayana,wannan shine rashin sani wanda yafi dare duhu,ashe duk abinnan da nakeyi bom boy na bayan motar yana kallona,ohi sam ban sani ba koda na hau titi nayi mamakin irin yadda mutane da dama suka dinga daga min hannu kasancewar glass din motar mai duhu ne bbu wanda ya ganni gaskiya kan naje gida na kara tabbatarwa shahid mutumin kirki ne mai jama'a. ina fitowa mai gadi yace sannu da zuwa yauwa baba tsoho ya gida? lafiya lau ina shiga sister ta fito da gudu muka rungume juna dakin Abba muka karasa abba sannu,yauwa sister wahida abba ina kwana? lafiya lau wahida,ya kika baro yar uwar tawa tana nan lafita ta mace in gaishe ku muna amsawa da sauri na mike da gudu nai dakin yaya faruq hello yayana na fada jikinsa ya dago fuskata sister amma kin dawo kenan? la! anty wata in dawo anya anty ba zata bar man keba,umh ai nafi son can saboda me? can sunfi sona basa dukuna da sauri na fita hello ya amin hello ya amin dina na dawo na rungume yayana yace yaushe kika zo sister yanzu nazo amma kin zo kenan munyi kewarki,BANA KAUNAR KA!!! 22 Gaskiyaba zaki koma ba yaya naga dakin ka duk ya canza shima ai yayi missing dinki bebinmu maza huta ki gyara mana dakinmu dakin abban kuma mun sha hira da abba sai da abba ya fiti na shiga dakin yaya faruq na wanko masa toilet sannan na ciro zanin gadon na shimfida masa wani lallausan bargo na goggoge na share na kunna turaran wuta dakin yaya amin shima ba gyara fes na janyo dakin na kulle dakinmu na koma ba zan iya fasalta muku irin yadda dakin ya koma bana dai gyara shina hada kayan wanki na bayar saida na kammala girki dare na gyara kicin din sannan na koma dakin nai wanka har lokacin su yaya basu dawo ba nai wasu mom sallama na tafi. faruq na dawowa dakinsa ya tura haba sanyin a.c da kamshin turaran wuta dan maiduguri ya buga shi kujera ya zaina tare da fadin thank you sister ya zare kayan jikinsa ya shigo toilet shima sai kamshi yake gaskita faruq yaji dadi sosai haka zalika al'amin ya gode wa wahida. iba zuwa gida ya shahid zaune a falo nai salama ya amsa min ciki ciji dakin anty na wuce nai sallama tana zaune ta amsa da fara'arta zama nai kusa da ita tace sannu da zuwa nace anty ya gida lafiya lau ya kika baro su mahida suna nan lafiya lafiyansu klau dakina na shiga wayata ta shiga ringing ya faruq sunansa ya bayyana akan screen din wayar cikin sanyin murya na amsa "hello wai a tunanina laifi nai masa me yasa kika ki bari mu dawo mu kawo ki gida? umh gani nai yamma tayi,okey naga dakina yai fes na gode fa dariya kawao nai. Wahegari na tashi da matsanaicin ciwon kai da kyar na iya fitowa dakin anty naje na gaishe ta sannan dakin daddy sannan dakin small kamar in shiga dakin shahid wata zuciyar tace kawai in share shi daki na koma na cire hijabina sanye nake da wata yar bingilar shimi shara-shara domin kawai na kirjina a bayyane yake kasancewar bbu mai shigo min daki kwanciya nai anty ta shigo min da break fast din da magani ina zaune ina shan tea sun hadu gurin breakfast bom boy yace anty ina yar takine bata jin dadi ya mike me ke damunta bai maji amsar da antin ta bashi ba domin sam hankalinsa baya jikinsa ina zaune ina shan tea yai sallama zama ya yi a gabana ya zuba min ido oho ni na manta ya shahid ina kwance jin shiru nace au good morning domin in ance masa ina kwana ya kan ce mene kuma ina kwana? ikon Allah ganin yadda ya shagalta da sauri na kalli kaina wa iyazubillahi gaba yai mumunan faduwa shi kenan ya gama kalloba inalillahi nai waurin janyo hijabina na rufe jikina nakalle shi cikin bacin rai nace wallahi ka kalli haram ban yafe maka.....yasa hannu ya doke min baki uban wa yace ki zauna a haka to wa ya ce ka shigo min dakina na fada cikin kuka ya mike ya fice nasa kafa nai boll da tea din na shiga birgima shi kenan ya gama kallon abin da zai kalla ni ya cuce ni ya cuci masoyina mahida ta fado dakin ke kuma me kike wa kuka na shiga bata labari na ciro hijabina kin ga fa rigar toke me yasa ba kya son sa bireziyyaBANA KAUNAR KA!!! 23 Allah ya kiyaye ni bana son biriziyya to ai gashi nan ya kalli bati ai kuwa har Allah ya isa nai masa oho ke zata bi. bom boy ya shigo shi da small boy na mike na bar musu falon domin ni haushinsa nake ji sai bayan la'asar mahida ta tafi na zauna ina kallo dakin anty yai sallama yayi shiri na kalli agogo lokacin fitarsa yaya sai kuma gobe da safe na mike na fice ya kalli anty,anty zan tafi sai da safe anty ta janyo wani galan ta dauko glass cup ta cika masa shi da rubutu ya amsa yai bismillah ya shanye tace ka shirya kaje katsina malam baba yana son ganinka to anty yaushe zani kin san fa bani da lokaci ka daure dai kaje ko wuni kayi to anti kaci abinci ya shafa cikinsa rabonsa da abinci tun karin safe ya kalli anti yaga tana kallonsa yace yanzu nasa wahida ta kawo min okey miko min zam zam din can ya mike ya dauko ta juyo a cup tai masa tofi a ciki ta bashi ya sha tai masa nasiha irin tasu ta manya daga nan yai mata sallma har ya fita ya dawo anty ina small, small ya tafi katsin can zai kwana me yasa bai fada min ba kayi hakuri ya fada min in sanar maka mantawa nayi okey Allah ya dawo dashi lafiya amin dakin wahida ya shiga tana zaune tana zuba abinci ya zauna ta mike ta bar masa abincin yai murmushi tare da riko hannunta dan girman Allah ki zauna billahillazi rabona da abinci tun karin safe please help me ta koma tare da cigaba da zuba mana tare muka ci yana min hirar irin nasarar da suka samu a tafiyar da suka yi,muna gamawa ya min sallama ya tafi na mike nai alwala nai sallah sannan na kwanta.bakin dare misalin karfe biyu na shiga toilet na fito ne ina shirin kwanciya sai naji kamar ana dirowa dif!! dif!! dif!! tuni kafafuna suka soma karkarwa jikina ya dauki rawa karar bindiga ita ta dawo dani hayyacina tuni na shiga laluban wayata na shiga danne danne har n nemo ya shahid layinsa na celtel a kulle tumi na tafi glo cikin sa,a ya shiga,hello yaya kana ina? gida a rude nake sosai nutsu ki fada min me ya faru? yaya ka fito barayi sun shigo mana gida barayi wahida to gani nan zuwa har ya kashe y bigo,wahida ki kulle dakinki ki zare key din kar ki fito har sai na dawo cikin kuka na ce to kayo sauri yaya daina kuka yanzu zan dawo shiru ba yaya haba tuni na fita da gudu nai dakin ya shahid na dinga dukan kofar ina kiran sunansa na koma dakin small nan ma a kulle wayyo nai dakin anty anan na gansu dukkaninsu sun wani nannade kansu da fuskarsu nan da nan nayo kansu ina dukansu ina ihu wani daga ciki ya daka min tsawa ke ina zaki? ban sani ba shegu tsinannu,la"anannu ogansu ya haska ni da toch light sanye nake da rigar bacci iya gwiwa wata mahaukaciyar dariya ya saka yace cool down beb ya kalle su ku karasa bari mu daidaita da baby yes sir,cak ya dauke ni na shiga dukansa har da cizonsa ina zaginsa amma bai dire ni ko ina ba sai bedroom dina runi ya raba ni da rigar jikina da gani sai pant ya shiga murzata san ransa,inallilah i wa inna ilaihi rajiun Allahumma ajirni fi musibatin wa aklifi khairin minha,la haula wala kuwata illa billahi aliyul azim,wala haula wala kuwata illah billah aliyul azim,wala haula wala kuwwata illah billahi.....sai kawai ya....to me kake /kike tunani iyeh!! iyayen gulma toh baza kuji baBANA KAUNAR KA!!! 24 bom boy sadaf! sadaf! ya shigo saboda haka bbu wanda ya ganshi kai tsaye dakin wahida ya shiga ganin dakin a bude ya razana shi yana danna kai ya soma jin ihun wahidar ogan yana rike da ita gaba daya ya gama fita a hayyacinsa bbu abin da yafi buri irin ya cimma burinsa,ta baya bom boy ya anyo ransa ya gama baci hankalinsa a tashe gaba daya ya birkice shi kuwa oga tuni ya mance da abin da ya kawo shi wuka bom boy ya soka masa a kirji ina kuka na mike da gudu na kankame shi ya daga aina muka gama ido ban taba ganin shahid cikin irin wannan yanayin ba cikin kakkausar murya yace bai taba kiba ko? cikin kuka nace eh maza ki sa kayanki ki kulle dakinki tuni na rike shi ina kuka to saka kayanki in kai ki dakina ki kulle nasa hijabina ya kaini dakinsa na kulle yace kar ki fito kin ji nace to dakin anty ya nufa gaba daya y tasar musu kasancewar yana da wani sirri wanda shi kadai ya sanyar wa kansa sani don haka cikin kankanin lokaci ya dama dasy ya shiga dakin kwance ya ganta cikin jini inna lillahi wa inna ilaihi rajiun dagowar da yayi ido hudu da wasu suna shirin guduwa yai amfani da piston ya harharbe su ta bude idonta da kyar take magana kaje dakin wahida da mahaifinka da sauri ya mike ya nufi dakin mahaifinsa a kulle ya ganshi cikin jini harbi biyu daya a kai daya a kirji kadan ya hana shahid zautuwa sai dai albarkacin kalmar da yake ta maimaitawa yasa nutsuwa tazo masa ga abinda yake cewa, innalillahi wa inna ilaihi rahiun Allahumma a jirni fi musibatin wa aklifli khairan minha Allahumma la sahla illah maja alhu sahla wa anta taj alul hazna iza shi ita sahla.koda naji shiru bbu alamar motsi sai na fito da gudu nai dakin anty na dinga tsallake su ina wucewa caraf wani ya damko min kafa tuni na shiga ihu wayyo shahid kaxo zai balla min kafa wayyo da hanzari ya fito ya duba dakinsa bai ganni ba a dakin anty ya ganni tsawaya doke min ke wacce irin yarinya ce waya ce ki fito ba yi magana ba na ci gaba da kukana ina nan ina kuka naga sojaji sunata shigowa bayan sun gama shigo wa daya daga cikinsu ya kalli shahid cikin harshen turan ci yace ma akai min ina ji yaya na masa bayani kafa yasa ya doki hannun da gudu nai dakin anty bbu wanda suka taba ko? shahid ya daga rinanim idanunsa aya ce sun harbi dady har guri biyu dad dina Allah ya amahi abinsa sannan sun harbi anty a kirji gaba daya suka sa salati amma musulman cikinsu daga nan yai musu jagora dakin mahaifinsa sun kwace shi sun shimfidar dashi a gadonsa tuni likita ya shiga aiki.BANA KAUNAR KA!!! 25. ina shiga na kankame ta ina kuka hannu ta daga da kyar ta shafa kaina wahida ba dai abin sa sukai miki ko? a daran yaya shahid dani muka kai anty wani babban asibiti kudi basu yi wata-wata ba suka shiga da ita emergency likitoci sunyi nasarar cire mata bulet din ina zaune na hada kaina da gwiwa ya shigo taso mu tafi yace min na mike na bishi muna isa muka tarar su abba mom atu baba rabiu duk sun zo har anyiwa daddyn wanka kukan da nake yine yasa abba yayi min magana tashi ki koma daki ina kallo shahid na kwararawa mahaifinsa addu'a waya naiwa haidar cewa maza ya taho gida bbu lafiya kan kice meye wannan gidan ya cika da mutane tashin hankali, haidar ya iso ya tadda ana shirin fita da mahaifinsa daga dakinsa lokaci daya ya birkice da kyar aka shawo kansa yaiwa mahifin nasu addua,amma sumansa uku koda za,a dauke shi kukan kura yai ya rike makarar ya dinga duka masu rike da ita,shahid shi ya dauki haidar yasa shi a daki ya kulle sannan aka samu damar fita da mahaifin nasa a asibiti kuwa sunce basa bukatar dan jinya sai dai anti da kanta ta roki a bata wahida saboda haka wahida ce a gurinta.bayan sati daya ba laifin jikin antin yana sauki ranar shahid da haidar abba da baba rabiu anty ta soma yi musu magiya hadda kukanta su fada mata gaskiya ina mijinta yana raye ko kuma ya rasu kukanta ya daga hankalinmu ainun,haidar yace anty sai dai hakuri amma maganar gaskiya daddy ya rasu yaune kwanansa bakwai gaskiya ta girgiza domin bbu wanda ya ankara sai ganinta akai wanwar a kasa ta fadi tuni jini ya balle haidar ne ya kira likita,likitoci sukai hanzarin dauke ta wani likita ne ya dinga fada kun gani kun wargaza mana aiki shi yasa muka fada muku bamu.....kan ya karasar bom boy ne cikin fushi ya dakatar dashi ya dinga yiwa likitan bala'i da kyar abba ya ja shi suka tafi.tsakad dare ina zaune kan abin sallah tace wahida ban ruwa insha na mike na dauko robar swan na tsiyayo a cup na dago kanta na bata tasha sosai har tace ya ishe ta na maida ita ba kwantar tace sannu wahida nace yauwa wahida Allah yai miki albarka ubangiji Allah ya raba ki da sharrin makiyanki amin,wahida ki taimaka ki bawa dan uwanki ishassun hadin kai shahid yana tsananin sonki anty ba wai bana sonsa bane ina son karatu ne to wahida Allah ya taimaka ameen,ta koma ta kwata ina jin ta tana ta jero kalmar shahada koda inda saboda yace na saba jin irin wannan saboda koda yaushe sannan duk irin baccin da anty take yi muddin akayi kiran sallah ta kan ce in taimaka mata tayi alwala tai sallah yau ma ina zaune har akayi sallar asuba sai dai nayi mamakin yadda har aka idar anti

Chapter 3 of 6