Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Da sauri ya shigo dakin yana kiranta ...ganin tana toilet ne ya sashi tsayawa bakin toilet din .. "Hudah .....menene ? Kokarin kunna heater take ta kasa sae uban ihu take tana tsalle ... "Na shigo Hudah? ....ya fada a hankali ...jin ihun nata yayi yawa ... bata bashi amsa ba ta cigaba da ihunta ....tura toilet din yayi ya shiga da sauri ....kwalbar miskin ya gani da cotton din da ta dangwalo ...ita kuma tana gefe sae uban ihu take ... Ko baa fada mashi ba ya san abunda takewa ihun ....duk da ta bashi tausayi amma dariya yake mata ....bai ga wanda ya sakata ba kilbibi ne irin nata ..... Cikin kuluwa da dariyar da yake mata ta juyo tana hararanshi tare da watsa mashi ruwan sanyin da ke cikin bucket .... "Ba komae kije da zafinki .....see ..naga wani abu irin wannan a gurin wata mata idan na fita zan sayo maki sae ki kara sakawa ..tunda naga kin girma da yawa ....!!! ...ya fada yana dariya ... Da sauri ta juya ta hade kanta da bango cike da kunya ...ga azabar take ji ...Allah ya isa kuwa ta jawa Lubna yafi cikin kwando ..... Kamar yarda barister shehu ya fada ...haka ta faru ...gidan da suke ciki ya sayar a tunaninshi nan da shekara daya idan ya samu ya maida masu gidansu ...da marece ya kawo mata kudin ....ba tare da sanin kowa ba ta rabasu uku ...kashi daya ta kai gidan marayu akan Allah ya kai ladar kabarin Yaya Saa ....sannan gudan ne ta kaiwa Aunty hanne tace ta boye mata ....sauran gudan kuwa ...babban masallacin garin ta kai tace a gyara shi sannan a sayi duk abunda zaa bukata ....ta sadaukarwa Yaya sa'a da mamanta sae babanta . .. ••°°•• Barister Shehu ne ke fada mata dad dinshi baya lafiya ...45%t fever ...ga diarrhea sossae ......"Allah ya sawake ta fada ."...!! °°••°° *FEEDOHM💞* 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS...._ *_72 to 73_* Tun daga ranar da uncle ya kamata tana matsi bata kuma bari suka hada ido ba ...tana kwance tana chat dinta ...ya shigo tare da tsaya bakin kofar ya zuba mata ido ...rigar dake jikinta cottonsilk orange ta bi mata jiki sannan iyakarta guiwa ....cinyoyinta sun fito kamar irin na turawan nan ..sae gashinta data hade shi ta daure baya .... Bude hanci take tana shakar kamshin uncle a tunanunta daga dakinshi kamshi ke fitowa ... Pictures dinshi ta nuno tare da rungume wayar tana fadin..." I miss you uncle ...matsalanka ka fiye gano abunda yafi karfinka ... Wa yace yafi karfina ....? Da sauri ta juyo tana waro ido kafin ta boye kanta cikin pillow .... dan murmushi yayi kasa kasa yace .."ki tashi ki shirya zaki rakani unguwa ".. ba tare da ya jira amsarta ba ya wuce abunshi ....dakin hanne ya shiga yace ta shirya zasu tafi ....wata uwar harara ta watsa mashi don tun dukan da ya masu over 6month take rike dashi .... "Bana zuwa " ...ta fada tare da gyara kwanciyarta .... Ba tare da yace komae ba ya juya ...amma a zahirin gaskia baya kaunar mutun mai riko .. wacce yama dukan ma ita da kanta ta nemeshi tare da ba shi hakuri duk da shi ya dace ya bata din .... Dan karamin tsoki ya sake dae dae lokacin da Hudah ta fito daga dakinta sanye da gown red .... a tunaninta da ita yake tayi saurin kallonshi tana fadin ..."Uncle sorry wallahi gyalen na rasa inda yake "... Dan murmushi yayi yace "Baki man komae ba Hudah ....kinyi kyau sossae ....amma bara ki fita a haka ba ...." komawa yayi dakin ...cikin kayanta ya dauko mata bakar hijab mai hannu tare da mika mata ta sanya tana murmushi .... A mota ma duk sec sae sun kalli juna tare da sake murmushi ... "Zaki zauna da Auntyn kine koko kinfi so na ajeki GRA ke kadae" ...ya fada tare da dan kallonta ... Shiru ta masa ba tare da tace komae ba ...juyowa yayi yana kallonta yaga gaba daya hankalinta ba ga motocin dake kokarin wucesu ....hannunta ya janyo tare da kura mata ido .... "Bakya jine ".....ya fada dae dae kunnenta ... "Me kace Uncle ? ....ta fada tare da zame hannunta daga nashi ... Kafarda ya janyo yana kokarin rungumeta .."may be idan kina jikina kya fi fahimtar abunda nake fada ...." "Wallahi uncle naji ..ka sakeni please !!.. Hararanta yayi sannan yace .."bana jin kinji abunda na fada tunda baki bani amsa ba !! ...ya fada tare da kokarin hade bakinta ... cikin sauri tace .." Uncle please ka daena ....da Aunty hanne zan zauna "...ta fada tana kallonshi da idanuwanta ta suka koma kalar kuka ... Dariya yayi kasa kasa tare da sakinta yana kallonta ...turo baki tayi tana fadin ... "Saukeni na tafi a napep ni dae !! "A da kenan Hudah lokacin da nake tsoron na tabaki ba yanzu ba da kika zama tawa ...kina iya yin duk kalar abunda kika so ..am ready na bi da ke yarda kike so ...duk da dama kin shirya don har ...!!. Hannunta ta sa abakinshi tayi rau rau da ido .." ".Uncle Dan Allah kabar fada ...wallahi lubna ta bani ....!! wani fitinannen kallo ya watsa mata tayi saurin maida kanta kasa tare da zame hannunta daga bakinshi ... Central market ya nufa da ita ...wani katon shago suka shiga ....Wasu kayane gefe guda ...gurin suka nufa ... "Ki duba abun da bai maki ba ...gobe zai koma dubai din sae ya sako maki wasu ..." ..ya fada yana kokarin daga mata kayan Wani fitinannen kallo ta sake mashi tare da juyawa ta fita daga shagon ta koma mota ta zauna .... Kallonshi tayi cikin natsuwa lokacin da yake kokarin kunna motar tace "Uncle idan zaka hada man lefe har sae kazo dani na gani ...? ..Uncle zan iya aurenka ko babu lefe kuma na rayu dakai kamar baiwa..Ka mani komai a rayuwata uncle bansan dame zan saka maka ba ...!! So yake ya kashe maganar yace "Lubna ta cigaba da baki abunda take baki ke kuma ...!! Kuka ta sake da karfi tana kokarin bude motar ta fita ...hannunta ya rike yana dariya ...ita kuma sae neman kwacewa take ... "Sorry Hudallah na daina kinji ko !! ...ya fada dae dae kunnenta ... Kallonshi tayi tana turo baki ...sannan tace "promise" ...a hankali ... Lumshe idonshi yayi tare da daga mata kai ......kafin ya budesu tar ya zuba mata cikin salon soyayya ...juyar da kai tayi tana kallon waje dauke da murmushi ... *FEEDOHM💞* 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS.._ *_74 to 75_* *_3 month ..._* Shirye shiryen biki ake sossae ..hanne ta zage sae gyara Hudah dun bata mata kallon kishiya sae yar 'uwa duk da akwae dan kishin kadan a ranta ..amma ta tabbata idan har ta fiyo dashi to batawa Mahmoud adalci ba ...tun da har ya jure zama da ita tsawon shekaru ba tare da cin mutunci ba... "Aunty Hanne Dan Allah bara naje na dawo ...Lubna tashi muje !!!! Hanne tace ..".ina zaki Hudah ..so kike mutane su zargeni ...duka gobe fa daurin aurenki kuma zaki fita ...aa gaskia !! Hudah ta riko da hannunta ..."Please aunty hanne...wallahi daga yau baran sake irin wannan fitar ba ...dan Allah ....kinji auntyna ...!. " To Hudah ...ki kula amma kinji ko !!! "Yauwa" ....ta fizgi hannun Lubna suka fice ....Motar Mahmoud din suka shiga ... "Ina za mujene ? ...lubna ta tambayeta ... Hararanta tayi ..Gidansu Shehu ...! "Amma Damsel baki da imani ..bayan kinki aureshi kuma har da zuwa gidansu ki masa me ....? Bata ce mata komar ba tayi parking kofar gidan ...tare da fito da wayarta ta kira Shehun ...ta tambayeshi "yana gida ..".ce mata yayi. " eh yanzu ya dawo shi da dad asibiti suka karbo magani ..." Lubna ta kalli .."fito muje" ...ta fada tare da yin gaba abunta... Ba tare da tayi sallama ba ta hankade labulen falon ....cikin saa su duka ukun na zaune sae safina dake gefe guda tana wasa ... Zumbur Dad da shehu suka mike ....Dad yace ..."Pretty"...kafin ya rufe baki Shehu yace "Sa'adah ",....sannan suka kalli juna tare .... Yar dariya ta sake ..kafin tace .. "Sa'adah ..damsel Pretty.. ..amma asalin sunan Hudallah Ibrahim _!!! ... "Hudallah .".su duka duka maimata har da hajiya data mike lokacin .. "Kwarae amma ba farat daya karamar kwalwarku zata fahimta ba ...Soyayya ......da uba da dansa ....!! " Damsel ..".barister shehu ya fada tare da matsowa kusa da ita ..."Ban fahimceki ba ..." "Yanzu kam zan maka yarda zaka fahimta dakai da jakin ubanka har da ma tunkiyar uwarka ...!! "Ke mara mutunci ....uban me kike nufi ? ..hajiya ta matso a fusace ... Dad da yayi mutuwar tsaye yace ..".karki kuma zaginta hajiya ...dan Allah Pretty ki zauna muyi magana ...wallahi har yanzu ina mutuwar sonki .!!...ya fada cikin kyarma .... Shehu yace ..."Dad Sa'adah tawace kabar fadin haka mana ...ka lallasheta kar tace bata sona dan Allah ...!! "Ashe kun san Allah ....? ..Yaushe kuka sanshi ..ku fada man ...!! ...ta karashe maganar cikik tsawa ... " A gaida jakin malamin da ya tsaya fadarwa Shehu da ubansa fadin suna Allah a baki don basu sanshi a zuciya ba ....!! " Sa'adah "....shehu ya fada tare da yin kneel down a gabanta ..."Dan Allah karki man Haka wallahi ina mutuwar kaunarki ...na tabbata idan ban sameki mutawa zanyi ...!! "Aiko ya kamata uwarka ta tafi neman likafani tun yanzu ....!! Lubna tace ..."haba Hudah karki yi haka ba ...karki zama mara imani ...komae suka maki bai kamata kiyi haka ba .....!! Cikin tsawa tace ..."Kinsan Wacece Yaya Sa'a ? .... Ba Shehu kadae ba Hatta Lubna sae da ta tsorata .... "Yaya Sa'a ...tana iya kwana biyu bata ci abinci ba amma bata taba barin Hudarta da yunwa ko da seconds 2 ....takan kwana tana wahala duk saboda Farincikin Hudah ....Wadannan munafukan Lubna su sukayi sanadin barata da duniya ke har da ummana .... _*A DALILIN YAYATA*_ Nayi komae lubna ba wae don kowa ba sannan nayi soyayya daku !!... "Shehu na tabbata baka manta wacece Ya ya Sa'adatu ba ...mumina saliha daka tarwatsa mata rayuwarta ....to Hudah ce kanwarta ...!! "Wallahi nasan ban kyauta ba amma dan Allah ki gafarceni ...ki tsaya muyi magana wallahi na tuba na gyara duka halina Hudah ...duk saboda ke ...dan Allah karki barni ...na tabbata dad zai bar manke ...,!!! " Mtsee ....gobe kamar yanzu na zama matar barister Mahmoud mutumin da kukayi forcing yazo gidanmu ashe ma haske kuka kawo mana ...!! bata rufe baki ba ya fadi kasa yana tari ...dad da hajiyar sukayi kanshi ...dad ke fadin ... "Karkiyi haka Hudah ...na bar masa ke wallahi na hakura ...!! Harara ta watsa mashi ... Tana fadin... ..."Sweetheart ayi maza aje gwajin kanjamau don na tabbata akwaeta a jikinka ...don ina tunanin har da jakar matarka ma ta kwasa ...a lisaafina Yau 6month kenan da cutar ta shiga jikinka na tabbata tayi kwarin da barata fita ba .....bye!!! ..ta juya ta tafi .. Juyowa tayi da sauri tana fadin .. "Oh na manta ...Shehu ya sayar da wannan gidan akan Naira million 19..idan ya tashi ku tambayeshi ..wawan bai sani ba nina sayi gidan sannan ya maido man da kudin a matsayin kyauta ...so nan da wata daya a tattara komatsae a fita!! ...... Ta fizgi hannun Lubna suka fita ....ita kam lubna binta take da kallon kamar tv ...gani take kamar ba Hudah da ta sani bace .. Da daddare Uncle Mahmoud ya kaisu ita da Lubna da Farida kawarsu da tazo.. gidan liman .... Bayan su Lubna sun fita daga motar ne ya riketa ....yana shafa kunshin da aka mata na zallah bakin lalle ... *FEEDOHM💞* 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS..._ _GWS.....SWEERY ...ALLAH YASA ZAKKAR JIKINE .....PLEASE IDAN AN TARA KANKANA CIKIN KAYAN DUBIYA KI AKE MAN KIN JI KO .....😘😘_ *_76 to 78_* Kallonsa tayi a shagwabe tana fadin ...Uncle suna jirana please ...!! Glass din gurinshi ya rage tare da kwalawa su lubna kira da suke gefe suna jiranta ... Suka matso Lubna na fadin "Uncle gani " ... Lumshe ido yayi yana murza hannjnta ..."Ku shiga ciki Lubna zamu shigo yanzu ..." "Uncle "....ta fada kamar zatayi kuka ... Kallon da ya bita dashi ya sata yin shiru tare da maida kanta kasa ....a hankali take mashi guguni tare da turo baki tana hararanshi ta kasa ... Idonshi na lumshe duk yana jin abunda take fada ...bata tare da ta shirya ba ya rungumota kirjinsa tare da hade bakinsu guri guda yana tsotsa ... kokarin kwace kanta take tana yarfe hannu ...kin sakinta yayi ya cigaba da bata dpkiss ....sae ya ji ta fara kuka ne sannan ya saketa a wahale ... "Maimaita abunda kikace !!...ya fada kasan makoshi.. kwallan daya fito ne ta saka bayan hannu tana gogewa tare da turo baki ta masa banza .... A hankali ya bude ido yana kallonta sannan ya saka hannu da niyar rikota ...tayi saurin ja da baya tana fadin .... "Yi hakuri zan fada maka uncle" ...ta fada tare da goge kwalla ... Maida kanshi yayi saman sitiyari yana jiranta ...jin taki cewa komae yasashi dagowa .yana kallonta .....tayi saurin ja da baya .. "Cewa nayi kamar baka taba aure ba !!!....ta fada a hankali ... "Umhuh ...ina jinki ..sae kika ce mae...kuma bayan wannan? " Shikenan fa abunda nace ."...ta fada tare da janye hannuta cikin nashi.. Dan murmushi yayi tare da rungumota yana niyar kissing dinta ... "Zan fada wallahi ......!! sakinta yayi tare da zuba mata ido ..... A ha kali tace .."sae kuma nace..huh...kayi hakuri Dan Allah Uncle" ...ta fada tare da kallonshi .. "May be dama kina bukatar na cigaba da kissing dinki shi yasa baki so ki fadi abunda na tambayeki .!!..ya dago fuskarta da hannunshi na dama .. Da sauri tace " aa wallahi uncle ..cewa nayi ka cika jaraba ....!!..ta karashe maganar tare da sanya kanta cikin cinyoyinta ... Murmushi yayi kasa kasa tare da bude motar ya fita ya zagaya ya bude mata ...ba tare da ta kalleshi ba ta fito tare da rugawa cikin gidan da gudu ... Binta yayi da kallo tare da lumshe ido ya jingima da motar tsawon wani lokaci .... _Karfe 11:30_ Dae dae lokacin aka daura auren Barister Mahmoud da Hudallah Ibrahim ...wanda liman ya daura ...tare da halattar dunbin mutane daga garuruwa da dama .... Duk yarda barister Mahmoud yaso ayi party ...liman hanawa yayi ...yace ... "Indae kuna son aurenku yayi albarka Mahmoud to dole ku kauracewa duk wata bidi'a ...ban hanaku idan an kai maka matarka ba ...ku shirya walima cikin gidanku domin mutane su tayaku da Addu'a ...!! Godiya sossae Mahmoud yayi sannan ya tashi suka tafi .... Bayan magrib ne ...motocin da zasu dauki amarya suka iso ...kanwar maman Mahmoud ne ta amso amarya an nadeta cikin Saree yellow colour tun daga kanta har kafarta ..... Rungumota tayi tare da sakata cikin Clinto yellow colour ..sannan ta rufeta ta koma cikin wata motar.. aka barta ita kadae .... Duk da baa gaban iyayenta take ba ...amma ranar mutuwarsu ta dawo mata sabowa...ta tabbata da yaya saa na raye babu abunda zai hanata zama gefenta a yanzu ...tayi kwadayin taga farincikin da zata gani a idon yayar tata ... .... *FEEDOHM💞* 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home pf expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS.._ *_79 to 80_* Wani sabon kuka ya zo mata ..yayin da ta sa hannu tana kokarin rufe bakinta gudun kada drivern yaji ta .... Ji tayi an janyota tare da kwantar da ita ...kamshin da tajine ya hanata firgita don har ga Allah bata dauka akwae wani a cikin motar ba bayan driver ... A kan kirjinsa ya kwantar da ita tare da bubbuga bayanta a hankali alamun lallashi ...ba tare da yace komae ba .... Lafewa tayi tana kuka kasa kasa ....Hannunshi ya kai tare da lalubar bakinta ya tura yatsunshi a ciki yana wasa dasu a bakinta .... Kukan ya tsaya cak sae dae ajiyar zuciya da take saki tare da kananan kwallah ...... Jin zaa bude motar ne ya sata tashi daga jikinshi tana gyara Saree dita .... Bude motar akayi tare da fito ta ...sannan Aunty hanne ta matso ta kama hannunta ...Uncle Mahmoud dinne ya zagayo tare da rike gudan hannun nata .... Pictures aka dinga dauka kala kala ....ga dandazon mutanen da sukazo taran amarya ...Ba gidan barister Mahmoud din bane aka kaita ...gidan iyayenshine ....zuwa gobe idan anyi walima su wuce gida .... Tare suka jera su duka ukun har tsakiyar babban falon Gidan ...sannan aka zaunar da Hudah din a kasan tuntu ...Shima barister Mahmoud din zama yayi gefenta ...har lokacin fuskarta na nannade da Saree .... Falon ya dauki haske ta ko 'ina ....yana zagaye da dangin Abba da kuma na mamanshi sae su biyu a tsakiya ... Yayar Mamanshi ce _Aunty Husy_ ta taso tare da aje yan kunne da sakar gold wanda ya kai naira million 15 ...kusa da Mahmoud ...na sayan fuskar amarya ... Gurin ya dauki tafi ganin Mahmoud din ya tura mata sarkar yana girgiza kai ...alamun bai sayar da fuskar Hudah haka ba ... Wata kanwar mamanshi _Aunty Zuby_ ta taso tare da cire tata sarkar da yan kunne ta hada mashi ta tura ...still tura masu yayi yana girgiza kai ...alamun bai yarda ba ... Gurin ya kara daukar tafi lokacin da mamanshi ta taso ta cire tata sakar da yan kunne ta daura mashi a saman tasu ... Sannan ya saka hannu ya dafa sarkokin tare da fara bude Fuskar Hudah Ahankali ..har sae ya kusa budewa sannan ya kalli kanwar mamanshi yana fadin "Gaskia Aunty Zuby ku karo wani abu tukun ..." Aunty Husy ta mashi dakuwa tare da watsa mashi harara .. Sannan ya bude fuskar duka yana murmushi ..... Kanta na a kasa tana kallon carpet din gurin .... "Masha Allah ...tubarakallah ..Alhamdulillah amarya ta hadu ta ko'ina ....fatan mu Allah ya bada Zaman lafiya!! ....Babbar yayar mamanshi ta fada tare da daukar su photo ....kamar an bude gidan photo haka flash light ke tashi gurin .... Sae da aka gama photo sannan gurin ya sake yin shiru ...Mahmoud dinne ya saka hannunshi na dama tare da dago fuskarta ...sannan ya goga hancinsa a lips dinsa yana lumshe ido ....duk uwayen mutanen dake zagaye da falon.. "Mahmoud baka da kunya ni wallahi ban ma san haka kake ba dae yau .."..kanwar Mamanshi ta fada tare da jehoshi da pillow ....Hudah kuwa yarda kasan ta nutse gurin haka take ji .. .. Murmushi yayi kasa kasa sannan kama hannun Hudah ..tare da rarrafawa kusa da kafar Mamanshi ... "Hudallah ki gaishe da Mama "...ya fada dae dae saitin fuskarta ... Dukawa tayi kusa da kafar maman ba tare da ta iya cewa komae ba ...bayanta maman ta dafa ..tana fadin .. "Allah ya maki Albarka Hudah ....! Kowa na falon sae da suka rarrafa ya na rike da hannunta yana fada mata sunanshi tare da matsayinshi ....ita kuma tana dukar da kanta a hankali ...suna sa mata albarka sannan suka dawo inda suke zaune ...duk abunda ake idon hudah na kasa bata dago ta kalli kowa ba ..... Bayan sun zauna ne babbar yayar mamanshi _Aunty Husy_ ta kama hannunta tare da kaita part din hajiya ta zaunar da ita saman gado ta fita .... kamar jira Mahmoud yake ta fita ya fado dakin tare da saka key kamar munafuki _nidae feedohm nace munafuncinne man_...ya zauna kusa da ita ya janyo ta jikinshi yana fadin ... "Hudah sun man bakinciki wae anan zaki kwana ....dan kada ace nayi rashi kunya wallahi dana saceki mun koma gida ko ? ... Banza ta mashi tare da sakin kuka ....kanta ya dago yana lallashinta tayi shiru amma sam taki yin shiru ....sae da ya fara kokarin cire mata Saree da aka lillibuta dashi sannan tayi shiru ... *FEEDOHM💞* 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of Expert & Perfect Writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS.._ *_81 to 82_* "Uncle ka fita dan Allah !!....ta fada tana kokarin tsayar da kuka ... Cikin sauri yace .."Idan na fita zaki bar kukan Hudah ...? Daga mashi kai tayi tare da sadda kanta kasa ....dan kiss ya mata a lips tare da jan hancinta sannan ya fita yana waigenta .....duk da yayan mamarshi tace anan zata kwana hakan bai hana Mahmoud ja mata Allah ya isa ba ... Allah ya soshi ba wanda ya ganshi lokacin sa yake fitowa don suna can suns kokarin hada mata abincin da zata ci wanda zai kara mata lafiya ... Su biyu suka shigo da abinci tare da zame malullubinta ...Aunty Husy ce ta bata abincin a baki ...tare da daura fuska ...don farko cewa tayi bara taci ba ...sae da ta daure mata fuska sannan ta amsa ... Bayan ta gama cin abunci yayar mamanshi ta hada mata ruwan wanka masu uban kamshi tace ta shiga tayi ...tana fitowa ta bata less red tare da head baki tace ta sanya ...da katuwar sakar gold ...sannan ta saka mata takalma hills bakake ...ta rufa mata bakin mayafi a kai ..tare da kama hannunta ..suka shiga part din Abbah ...yana zaune sanye fa farin glass suna shigowa ya mike dauke da fara'a yana fadin ... "Marhaban Hudallah" ....hannunta Abbah ya karba daga hannun Aunty Husy ya zaunar da ita bisa tuntu .... Aunty Husy ta miko mashi plate dauke da saubatussamina .......kadan ya diba a hannunshi sannan ya saka mata a baki...ta daukesu photo ....Fita tayi ta ta barsu su biyu .... Wa'azi ya mata mai ratsa jiki wanda ta tattaba ko mahaifinta na nan iya abunda zai mata kenan ...bata da abun ce masu shi da liman sae dae fatan Allah ya saka masu da alkhairi .. 12:30 .. Masu decoration suka iso ....kujeru suka fara fitowa suna jerawa a harabar gidan ... .sannan suka fara decorating din da yadi blue da fari ....gurin yayi masifar kyau kamar baa cikin gida ba .... Tana zaune Aunty hanne suka shigo ita da Aunty Husy suka bata Saree blue colour ....kaf jikinta sae da aka nannade idanuwanta kawai ake iya hanguwa ..... Fita da ita akayi falo ...acan taji muryar Uncle Mahmoud yana mayarwa da abokan wasanshi magana ..."wae duk family dinsu babu mai kyaun amaryarshi ......!! Gabanta ya fadi lokacin da taji tattausan hannunshi cikin nata ....babu kunya ya daga Sareen yana kallon fuskarta tare da fadin .... " Gaskia na iya zabe ...Tubarakallah ...Aunty Husy da an gama walimar zan tafi da matata.. ..ku dan rufe idonku for some minutes ....!!. Aunty Husy ta kai masa duka ..".Gidanku Mahmoud ....ka rike hannunta ku fita bawae ka ma rashi kunya ..!!.. Dariya yayi tare da kissing dinta a hannu sannan ya jata suka fita harabar gidan ... Sun nuna mata kauna sossae ... _kamar yarda exclusive suka kaunaci feedohm_ ....sabon lefe suka hada mata wae kayan karbar amarya .... Agaban mutane ango ya ciyar da amaryarshi har ta koshi ....sannan aka ce itama ta ciyar dashi ...kasawa tayi ..ta nuna alamun zata yi kuka ...

Chapter 8 of 10