Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS..._ *_51 to 52_* Sanin ta dade ne ya sakata bude kofar falon a hankali ...Tana sanda ....Mahmoud din ta gani zaune bisa doguwar kujera idonshi a lumshe ...san sadawa tayi a hankali zata shigr daki ... "Hudah ....ya kira sunan can kasan makoshi ... Juyowa tayi tana murmushin rashin gaskia tare da fadan ..."Uncle Allah mamansu lubna ta tsayar dani ..." "Su waye suka fita a motar lubna yanzu ? ...ya jeho mata tambaya.. "Uncle aikenmu tayi central market muka sawo mata salad...Allah kuwa" ... Bai kuma ce mata komae ba ...ya maida idonshi ya rufe ...ta dade a tsaye kafin ta shige dakinta ta canza kaya sannan ta fito ta wuce dakin Hanne ...isketa tayi tana gyaran gado ... "Aunty Hanne na dawo ".... "Ina kika je ne " .... Sae da ta kalli kofa sannan ta matsa kusa da ita tare da rada mata a kunne !! Dariya hanne tayi sannan ta daga mata hannu alamun jinjina tana fadin ..."Ki dae kular mana da kanki " .. Hararan wasa Hudah ta mata kafin tace .."Me zaa dafa yanzu ",.. "Ki dafa komae ...bara na ida gyaran dakin sae na fito nima "... Kitchen ta shiga ....ta bude fridge ta fito da kaza ta aje ..sannan ta dauko markadaddun kaya miya da sukayi kankara ta aje gefe guda ....electric gas ta kunna tare da a daura tukunya ta zuba man gyada tare da albasa sannan ta juye kayan miyan ...garlic ta bare ta saka tare da dakakkiyar citta da kanunfari .....ta rufe tukunyar ... Wata tukunyar ta daura ta saka kazan ciki da dan ruwa kadan tare da albasa da citta da spices ta rufe ....cabbage ta dauko ta yanka da carrot ....tukunyar da kayan miyan suke ta koma ...lokacin ruwan cikin kayan miyan sun tsane ..ta kara mai kadan tare da spices ...bata zuba gishiri ba don yana da site effect bare ma na buhu ...bayan mintina kadan kitchen din ya dauki kamshi ....stv fish ta dauko ta gyara sannan ta zuba cikin miyar tare da cabbage da carrot din da ta yanka...ta rage wutan ta koma gurin kazanta ...tana zuwa taga ta dahu sossae ...da yake kazan yana da mai ...ta zuba kuli kulinta a kai tana motsawa a hankali tare da albasa ...sae da kuli kulin ya bi kazar sossae sanna ta sauke ta juye a foodflask ....ruwa ta zuba ta dafa spaghetti tare da peas zallah ....komawa gurin miyar tayi ta sauketa tare da juyewa a flask ... Carrots ta wanke sossae tare da gurje bayanshi ..sannan ta yankashi kanana ta zuba a blender ta markadata ta tace sannan ta zuba sugar kadan tare da madara peak ta ruwa ...ta zuba vanilla ginger ...ta hada ...ta saka a fridge ta rufe ... Daki ta koma still Hanne na wanka ....Itama wankan ta yi ta shirya cikin pakistan riga da wando red ta fito ... Ganin Uncle Mahmoud baya falon ya sakata jera komae a dining sannan ta shiga ta ma hanne magana suka fito ... Hannen ta shiga dakin Mahmoud din ta iske ya fito daga wanka yana shiryawa ... "Looking good yaya"...ta fada tana murmushi ... Shima murmushin yayi kafin su fito falon tare ...lokacin Huda na zaune tana jiransu ...kujeran kusa sa Huda yaja ya zauna ba tare da ya kalleta ba .... Serving Huda ta masu sannan suka fara ci ....shi kanshi so yake ya kalleta amma baya so ta fahimci wani abu ...ga kamshin turarenta ya gama cika mashi hanci ....Kadan kadan Hanne da Hudah suke taba fira ... Abinci yaci sossae kafin ya mike ya barsu gurin ...site din da Hudah take ya juya lokacin da yake kokarin tashi ....itama shi take kallo ....Murmushi suka saki lokaci guda kafin tayi saurin dauke idonta a kanshi ....kadan ya dan taka kafarta ..sannan ya juya yacigaba da tafiyar ... ••°°•• twenty missed call ....ta fada tare da waro ido ... New Number ne ...ko baa fada mata ba tasan me ita ...tana kokarin aje wayan aka sake kira .... Sae da ta kusa katsewa sannan ta dauka tare da langwashe murya tayi sallama ... Tana jin lokacin da ya sake ajiyar zuciya sannan yace .."Haba damsel kin san yarda Hankalina yayi masifar tashi tun dazu nake kira bakya dauka ...dan Darajar Allah ki taimaka man ki bani lokacinki ...wallahi tun bayan tafiyarki na kasa samun natsuwa ..harta matata wallahi kallonta nake maki " ... "Ayya bana kusa da wayan ne.. sorry baby " ...ta fada cikin Husky voice dinta.... "Ya zanyi Damsel ? .. .lokaci guda kin tafi da tunani ...gaskia ke me sa'a ce *_SA'ADAH_*...Lokaci guda kin tafi da zuciyar barister shehu ...baki sanni bane da kin tabbata da you're luckiest person a duniyar nan .. Murmushi tayi ..a ranta tace "na sanka shehu sanin da kai kanka wawan baka yiwa kanka ba " .. Amma azahiri shiru ta masa ..cigaba yayi da amayo mata *_Sirrin zuci_* ...yake ba tare da wani shamaki ba ...Sun kusa 1hour suna wayar har sae da tace zata kwanta ..sannan ya mata sallama ba don yaso ba !! ... Tun da uwar asubaha ya kirata ....dan karamin tsoki ta ja kafin ta dauki Awayar ... "Good morning my damsel ",...ya fada ahankali ... "Babyna ka tashi lafiya " ...ta fada kamar mai rada ... "Ina fa lafiya na kasa bacci Sa'adah!! ..please ki taimaka man ki bani address din gidanku na zo yanzu na ganki dan Allah " .... Maryam taji tana bala'in wae ya raina mata hankali suna kwance yana waya da wata banza ... Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS..._ *_53 to 54_* Tana jin lokacin da ya wanka mata mari tare da fadin uwarta ce banza ... Cikin Shagwaba Hudah tace .."Wae baby hayaniyar me nake ji haka ...bye ...anjima munyi magana bana son hayaniya please " .. "Yi hakuri Sa'adah .. .bara na bar gurin ...kinga wallahi nama tashi ...karki katse wayar dan Allah ...." ya fada cikin sauri .... Duk da sanyin da ake ...can cikin garden ya je ga rakube gurin flowers yana k'yarman sanyi gudun kar wani ma yazo ya masa magana ta kashe wayan .... ••°°•• A rana barister Shehu sae ya kirata yafi sau 50 ...duk ta gama rikita mashi kwakwala ...kullun nacin ta bashi address din gidansu yake amma sam taki yarda ta bashi ...duk da itama tana so su hadun ...don akwae plan din da ta Tana Zaune barister shehu ya kirata ..sae uwar waya take tana dariya ....Uncle Mahmoud dake tsaye kusan 30mints ya saurarenta bata sani ba .... Yar dariya ta sake mai daukar hankalu tare da fadin "Everything nawa naka ne babyna ...just fell free wit me ...ni kaina yanzu ji nake kamar ace muna da aure ...da sae kace baka taba aure ba a rayuwarka ...zan jiyar da kai soyayyar da matarka bata baka ba before ... Shiru tayi kafin ta saki dariya tana fadin ... "just ka sa time ...zan turo maka address dina babyna ...you know how much i love you kuwa ???... "Jikina da duk wani abunda na mallaka is for you baby ...i reall... Ji tayi an fizge wayar da karfi tare da jefar da ita kasa ...a firgice ta juyo tana kallonshi ...hatta jijiyar dake kanshi ta fito sossae ... " Uncle "...ta fada a firgice .. Tsawa ya daka mata "Da uban wa kike waya " .. Dukar da kanta tayi kasa ..bara ta iya jin zata fada mashi gaskia ba yanzu koda zaya daketa ne kuwa ... Wani uban mari ya bata yana fadi "For how long kika mallaka mishi komae naki ...Uban wa yace ke ta shi ke ..? "Uncle ...!! "Shut up !!! ...ashe abunda yasa kike nacin ki ci gaba da karatu kenan ...soyayya Hudah as your age 18 years fa .!!....girgiza kanshi yayi idanunshi suka ciko da kwallah ...first time kenan da ya taba kai hannunshi jikin hmHudah ba da niyar ya lallasheta ba sae don duka ...juyawa yayi da sauri zaya shige dakinshi... Hannunsa ta riko tare da dukawa saman guiwarta Cikin kuka tace .."Na tuba uncle ..baran sake ba wallahi ...i promise baran yi soyayyar gaskia da kowa ba wallahi ..please Uncle for morethan 6 years kana tare dani ba ...baka taba sakani kuka ba ...sae ni uncle ?sae nice Hudah zan saka fitar hawaye a idon mutumin da yafi kaunata a duniya ...please uncle ka yafe man dan Allah ..!!! ... Juyowa yayi a hankali yana kallonta kafin ya saka hannu ya dagota tare da share mata hawayen da suka bata mata fuska ...sannan ya hade ta da jikinshi .... "Bana so Hudah it really hurts ...."...ya fada a hankali Daga mashi kai tayi...tare da lafewa jikinshi ... ••°°•• Barister Shehu na zaune maryam ta fito rike da keys din mota .. ta matse cikin riga da wando ...binta yayi da kallo ...ta gabanshi ta wuce zata fita ... "ina zaki haka ? ...bakya da hankaline baki ga yarda kike ba ? ...ya tambayeta tare da mikewa tsaye ... Wani kallon ta watsa mashi ..."In da nafi wayau zan koma ..don na lura angulu ma ta koma gidanta na gaskia !!! " Me kike nufi?...kina nufin a haka zaki fita wae ? . "Kana mamakine? ...Shehu kenan ...to zan fita sana 'ane ...oh na manta baka san me nake ba kafin ka aureni ko ...? Kallon mamaki ya jefa mata !! "Haba meye na wannan kallon ...karfa ka manta akan karuwarka ka mareni da safe ....nima kuma naga nawa karuwan suka can suna jirana ..shine naga ya kamata na kai masu ziyara ....!!! Ficewa tayi ta barsa tsaye sake da baki ...ga uwar sha'awarta da ta taso mashi ....safina ta fito daga daki da gudu tana kiran ... "Mah!! ..Mah ....zan bi ki "....itama fita tayi waje ta barshi ..... ganin ta saba fitane ta shiga part din hajiya ya sashi kyaleta tare da komawa daki ya hade kai da guiwa .. Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS.._ *_55 to 56_* Maganganun Maryam suka fara mashi yawo ....wae karuwanta ...tabbas ba tun yau ya kamata ya gane maryam yar iska bace ...tunawa yayi da first night dinsu ....ba cikakkiyar mace ya sameta ba ...amma salon da ta dinga mashi shi ya hanashi mata magana ....sae yanzu yake tuno wasu abubuwa wanda bariki irinta maryam ta hanashi gane komae ... Wayar Hudah ya fara nema ....Switch off ...yayi kira yafi dari a take amma bata shiga ...kanshi ya fara mashi ciwo ya rasa inda zai saka kanshi yaji dadi ...bama maryam tafi damunshi ba yanxu ...aa Damsel dinshi ...gashi bata turo mashi address din ta ba bare ya je gidansu Zazzabi yake neman rufeshi ...amma sae kokarin kiran Hudah yake ya kasa samunta ...jin ihun hajiya ne ya sashi tashi ya fita yana dafa bango .....ko iya bude idonshi baya yi ... A bakin gate ya ga Safina a hannun dad ..hajiya kuwa sae ihu take kamar tababba ...a hankali ya matsa gurin "Lafiya hajiya me ke...."Chak ya tsaya ganin jini a jikin Safinar ... Saurin karbarta yayi a hannun dad din a firgice "Dad me ya faru ...me ya sami safinar ..ku fada man meke faruwa ya naga jini a jikinta ..?...take idonshi ya ciko da kwallah jikinshi sae k'yarma yake .. Dad yace "Fyad'e aka mata Shehu ....an cucemu Allah ya Isa!!!...ya dafe kanshi tare da tokare hannunshi da bango ... Zaman dirshan shehu yayi tare da sakin kuka ...ji yake da zaiga wanda ya lalata mashi diya ba abunda zai hana ya kasheshi .... ••°°•• Hudah na zaune Uncle Mahmoud ya shigo rike da leda .... "Uncle sannu da zuwa" ...ta fada a hankali .. Dan kallonta yayi tare da sakin murmushi sannan ya mika mata ledar ...sabuwar wayace Iphone6 ...tare da mtn sim da recharge card din 5k ... Wanni uban tsalle ta saki tare da rungumeshi tana sake mashi kiss ba tare da ta sani ba ....tureta yayi da karfi ya shige daki yana mayar da numfashi .....Jingina yayi da kofar tare da lumshe ido ... Huda kuwa Dakin Aunty Hanne ta nufa da gudu ta nuna mata ..... "Aunty Uncle ".....ta fada tare da rungumeta .... "Uncle na sonki Hudah!!!! ...hanne ta fada da ma'ana biyu .... Ba tare da ta fahimce ta ba tace ..."Na sani Aunty Hanne ....Ban san dame zan saka mashi ba ...? "Da kanki Hudah 'Zuciyarki ya dace ki bashi Hudah...!! Hanne ta fada tare da iko Hannun Hudah .. Da sauri ta kalli Hannen ..."Aunty amma da wasa kike ko ? ...ta tambaya a hankali "Ba wasa nake ba Hudah ....!!!..ta bata amsa kai tsaya " Aunty ki daina wannan maganar please ...Uncle bara ya iya sona ba ..kawae yana tausayina "...ta mike tare da fita daga daki ... Tana komawa dakinta ...ta hada wayar ...Number barister shehu tayi dialing ...har ta kusa yankewa sannan ya dauka ...yana jin maganarta duk ya rude yana tambayarta lafiya ....Ce mashi tayi bata garin ne taje maiguri grandynta bata lafiya ..... Bai yarda ta kashe wayar ba sae da ta bashi full adress dinta sannan .....ce mata yayi da marece zaya shigo yau ... Tun wajen karfe 3 ta fara nacin uncle Mahmoud ya barta taje gidansu lubna ....hanata yayi daga farko ..sae da ta fara mashi kuka sannan ya barta ta fita da zunbuleliyar Hijab dinta ..... Karfe 4 ya kirata yace yazo kofar gidan ...suna zaune da lubna alokacin ...ta dan kalleta kafin tace .."ya jira zata aiko yaro ya shigo dashi ...". " Lubna yazo !! ...ta fada hade da sauke ajiyar zuciya.. Fahad Lubna ta kwalawa kira tace "yaje ya shigo da bako yana bakin gate ...sannan ya kaishi falon baki "....yaron ya amsa da "to" ya fita da sauri Mintina kadan yaron ya dawo yace ya kaishi ...Huda tayi murmushi sannan ta ciro 1k tace yaje ya sawo chocolate ...kin karba yayi ya koma ciki da gudu Lubna ta sake mata harara ..."Damsel karki fita da wadannan kayan daukar Alhakin zaiyi yawa ...ko fa rana baa sa maku ba !! "Da waye ...? ..Hudah ta fada tana kallon cikin idonta "Barister mana ...sae ki rikitashi wallahi ..." Yar dariya ta sake mai sauti tace "Kina tunanin aurenshi zanyi ke !!! Da sauri Lubna ta kalleta ... Amma kafin ta bata amsa ta fice daga dakin da sauri ... *FEEDOHM💞* 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & Perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS..._ *_57 to 58_* Cikin takun jan hankali ta shiga falon dauke da murmushi a kyakykyawar fuskarta ....duka jikinta juyawa yake ...da yake riga da siket ne na atampha holland kuma dinki ya amsheta sossae da yake atamphar ash ce da orange a jiki... Zumbur Barister Shehu ya mike ...ji yake kamar ya je ya rungumeta amma sam ba da shashanci yake son Sa'adah ba ...so yake ya aureta ya adanata gidanshi ...don yanzu sam shida maryam sae kallo gashi ya kasa tabuka abun kirki a kanta .... Katse mashi tunani tayi ta hanyar hure mashi ido ...kamshin mint din bakinta ya sashi lumshe ido ..ya koma ya zauna kamar wani sakarai... "Damsel" ...ya kira sunanta tare da zuba mata ido ... "Why ? ...me yasa kike wahalar dani ...2weeks bama waya wallahi kamar nayi hauka ....bak'ya tausayina Sa'adah....!! . Kallonshi tayi ...a zahiri ya rame ...amma wannan ba shine matsalarta ba "Ayyah sorry baby ..na fada maka naje maiduguri gurin grandy ta da bata lafiya ..amma ai yanzu gani na dawo kuma ina gabanka ..meye na bata rai ...kaga bani phone dinka dear na tura maka pic dina kaima na tura naka yarda ko bama kusa da ka gansu zaka ji dadi ko .....ta karashe maganar tare da langwabe kai ... Cikin sauri ya bata wayar yana murmushi tare da fada mata pin din.. ... Janshi ta dinga yi da fira ba tare da ya lura da abunda take ba ...har sae da ta dauki abunda take so sannan ta tura mashi pic dinta guda biyu .... . Suna firan tana duba agogo ..... ••°°•• Ihun da ta saki ne yasa daga Hanne har Uncle Mahmoud din shiga kitchen da sauri .... Tana rike da hannu sae hawaye ke zuba a idonta ....da sauri ya rike hannun yana kallonta ....yar yankar da tayi karamace amma duk ta cika gidan da ihu.. Dan karamin tsoki Hanne tayi ta juya tana fadin "Kin daiji kunya wallahi ..kamar ba mace ba ".... _Su hanne mata!!!_ Uncle Mahmoud din ta kalla da idonta da har yanzu ke fitar da hawaye ...shima ita yake kallo ...sun fi minti 10 suna kallon juna wanda ke cike da sako kala kala ....ganin baya da niyar daina kalllonta ga jinin da ke kara tada mata hankali ya sata fara bugun kirjin shi a hankali alamun ya mata wani abu ... . "Uncle please do som...!!!.bata karasa ba ya saka hannun a bakinshi yana tsotse hannun ido a lumshe .... Bude ido tayi tana kallon kyakykyawar fuskarshi ...zata iya rantsuwar tun da take bata taba ganin mutun mai kyau kamar Uncle dinta ba .... A hankali ta janye hannunta a bakinshi ba tare da ta daina kallonshi ba ....... Idonshi na lumshe ya janyota jikinshi tare da zagayeta da hannu ...!! Idan har hakan zai saka uncle dinta jin dadi zata iya tsayuwa a hakan har Allah ya karbi Rayuwarta.....ta fada aranta bata san ya fito fili ba... Ji ta yi ya sake da sauri tare da girgiza kai ...." Bana fatan Allah ya karbi rayuwarki a haka ba Hudah In Sha Allahu .....!! Binshi tayi da kallo har ya bar kitchen din..sannan ta jingina da drawers din tare da lumshe ido ... ••°°•• Sae da ta kwanta sannan ta bude wayarta ...text din Barister Shehu ta gani kusa 6 ...ko daya bata bude ba sae ma tabe baki da tayi sannan ta bude Imo dinta .... Hannunta da dungule tare da dagashi sama cikin jin dadi ... Number da tayi saving da Kwad'o tayi dialing thrgh video call... *Feedohm💞* 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITER'S..._ *_59 to 60_* Cikin Saa yana online ya dauka ...Rufe idonta tayi tana fadin "Uncle nayi fushi kuma baran bude idona ba sae kace man sorry ...na canza phone da kyar na yi recalling numberka amma kai ko ka tuna dani haba uncle na .....oya kace man sorry sannan na kalleka .".. Ta fada cikin wata irin murya tare da murmushi a fuskarta ...wanda ya dada fitowa da ainahin kyawunta ... " double sorry pretty".. Ya fada cikin sanyin murya ..duk da yana tunanin mistaken number tayi ba shi bane ...amma da yake ido ga mata sae yaga bara ya iya barin wannan pretty din ba ta wuceshi ... Ta bude idon da sauri tare da waro ido _wanda ta tabbata ko uncle tayi wa irinshi sae yafi minti talatin kafin yabude idonshi ya kura mata ido ..barewa wannan karen ...wanda take tunanin ko jakka aka daurawa zani sae ya bita !!!!_ Haka kuwa ya faru ..don baisan lokacin da ya rungume wayar ba ..sae alamun zanen shaddah da ta gani ... Dariya tayi mara sauti sannan ta datse kiran tare da aje wayar gefe guda ... Kasa hakura yayi ya kirata ..Tana jin alamun ana kiranta amma ta share wayar ...sae da yayi mata missed call kusa 5 bata dauka ba ... Imo din ta koma ta tura mashi text _"am sorry mistake din number nayi..a digit din karshe instead nasa 6 sae nasa 9 "_ kafin ta fira har ya fara typing ... " _Nasan prety ...amma babu ta inda Allah baya hada mutane_ !!! "Ashe kunsa Allah ? ...ta fada a fili sannan ta maida mashi da " " _Ok"..._ Kiranta yayi a video call ...har sae da ta kusa tsinkewa sannan ta dauka ba kunya ya tasa karamar yarinyar cikinshi gaba yana mata sabbatu . .... Kallonshi kawae take tana murmushi kafin tace .. "kayi hakuri na fada mata mistaken number nayi please...!! At long last ma cewa yayi ta bashi adress din garin da take da gidansu ... " ba bukata "...ta fada a hankali .."domin gaskia kai saan ubana ne kaga bara ya yiyu nayi soyayya da kai ba !!! "So baya tsufa pretty" ....ya fada cikin sauri ... . Datse wayarta tayi gaba daya sannan ta kashe ..... Dad din shehu kuwa cigaba yayi da kiranta amma yaji ta rufe ...daran ranar kasa bacci yayi ...bai taba haduwa da yarinyar da ta tafi da imanin shi ba irin yau .... tana bude wayarta kamar rige kiran dad din Shehu na shigowa ..yana katsewa na shehun na shigowa ...bata dauki ko daya ba ta shige tayo wanka ...dama tun da daddare mama ta ce da safe Mahmoud ya kawota zata tayata zama saboda Abba zaiyi tafiya .... Bayan ta shirya suka shiga mota ita da Uncle Mahmoud .. Sun dauki hanya sossae ba wanda ya tankawa wani tsakani ...sae dae lokaci lokaci suna kallon juna ...shiru ya mata yawa gani take kamar baya lafiyane ...tana so ta tambayeshi meke damunshi amma ta kasa ...da ky'ar ta bude baki tace .. "Uncle baka lafiyane ? ...tana kallonshi ... juyowa yayi a wahale yana kallonta ..wani murmushi ta sake mashi da ya sashi ta taka birki da sauri ya kauce hanya ... tsoranta da tayi yasa ta fada jikinshi tare da zagaye hannunta jikinshi ...sauke ajiyar zuciya yayi sannan ya zagaya da hannunshi bayanshi ya riko hannuwanta tare da zameta jikinshi yana kallon idonta ... Bata fuska yayi .."Kin san me kikayi kuwa? .. *Feedohm💞* 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSO💡_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *Na Feedohm💞* *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS.._ *_61 to 62_* "Uncle me nayi "...ta fada hade da fito ido waje ....yarda tayi tunani haka ta faru ..domin lumshe ido yayi na tsawon mintina ... "Da kin kashemu da kin huta",....ya fada still idonshi a rufe ... Rufe bakinta tayi tana fadin ."Uncle daga murmushi ... Harara ya sake mata ...ta kwashe da dariya ...ita kanta yarda take dariyan so yake ya zame mashi matsala ... Tada motar yayi yana fadin "please Hudallah".. ...sauran maganar ya makale a makoshi .... Dariyan ta cigaba dayi cikin salo tana kallonshi tare da fadin ..."Uncle ...!!! Tare da Jan sunan Motar ya kashe ba tare da ya kalleta ba ya fita ...napep ya tsayar ya zagayo ya bude mata kofar ... 1k ya daura mata saman cinyarta yana fadin ..."zo ki wuce Hudah mun hadu acan please " ... "Uncle .."..ta fada a shagwabe ... "Please Hudah .!!..ya hade hannayenshi guri guda yana Nuna mata napep Ba haushi ya bata ba ...sae dariyar da ta masa ta hau napep din tana waigeshi ...sae da sukayi nisa sannan ya tada motar ya tafi gidan shima Sae da ya rigasu zuwa gidansu...yana zaune falo

Chapter 6 of 10