Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta fada kitchen itama ... ••°°•• Maman Huda na tsaye tana goge goge .. Barister Shehu ya fito daga daki fuska daure ....ya zauna bisa kujeran da take kallonta ... Malama ...daga yau karki kuma zuwa aiki nan gidan an sallameki !!!!...ya fada tare da daukar remote yana latsawa .. Maman Huda tayi sararo tana kallonshi cike da mamaki kafin ta danyi murmushi tace .,." Lauya wani abu ya faru kuma ?... Lokacin da nace kizo ki dinga taimakawa Hajiya kin tambayeni dalili? ...ya bata amsa yana kallonta ... "To ....Me yayi zafi Haka lauya ? ..."bara na samu Hajiyar idan wani abu nayi mata sae na bata Hakuri "... Ba sai kinzo ba ...!!..gani nan fitowa ....hajiya ta fada lokacin da take fitowa da part dinta ... Sannan ta ci gaba ..." Da kike son zuwa gurina ...dama ni daukeki aikin ? ...ina jin Shehu ne .. kuma yace ya sallameki to meye na sauran magana ? ... Maman Huda tayi tsaye rike da tsumma tana kallonsu ...a iya saninta babu wani abun da ta aikata ba dae dae ba ...ta ko don Saadatu ta daina zuwa ne? ...ta tambayi kanta arai... Tace "Kuyi Hakuri Hajiya idan dan saadatu ne wallahi har ga Allah bani na hanata zuwa ba ..!! ... Wake maganar sakaran yarinyarki yar iska...!!! ...Hajiya ta katseta tare da zabga mata uwar harara ... Yar iska ....?...ta fada lokacin da idonta ya ciko da kwalla ... Eh Yar 'iska matsiyata ...barister Shehu ya bata amsa ... Wallahi diyata ba yar'iska bace sae dae kaine dan iska ...arziki da talauci duk na Allah ne ...!!!ta basu amsa a fusace ... Bata rufe baki ba Hajiya ta dauketa da Mari tana fadin .."Allah ya mana katanga da talauci ...fice mana daga gida tun kafin na saka a futa dake ...bara kizo har gida ba kina kiran dana dan'iska na zuba maki ido ba ....kama hanyar akurkunki tun kafin na sakashi ya maki shegen duka gurinnan... Allah ya baku Hakuri ...Abunda ta fada kenan tare da fitowa daga gidan ....ko gabanta bata gani sossae har ta isa gida ... Ganin yanayinta ya saka Yaya Saa tayi saurin kamota tana tambayarta lafiya.. Lafiya mama ...me ya faru ?..me suka maki..?...ta tambaya a rude ... bata boye mata komae ba ta fada mata duk irin wulakancin da Barister Shehu da hajiyarshi suka mata ...daga saa har Maman kuka suke kamar ransu zai fita .. Huda dake tsaye jikin kofa tana jinsu ....ta fita da gudu .. Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITERS ASSOCIATION💡_* Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS..._ *_23 to 24_* Ta fitaa da gudu daga gidan ... ..bata tsaya ko'ina ba sae kofar gidansu Barister Shehu ...Wai dadi taji ganin ba maigadi a kofar gate din.. ...ta kutsa kai ta shige cikin har tsakiyar falon ...babu kowa a cikin ...katuwar Plasma dake falonsu ita ta nufa ta fito da duwatsun dake cikin jikkarta ta makaranta ...ta dinga bugawa da karfi ...kafin me plasmar duk ta farfashe ...sannan duk wani abunda tasan na glass ne sae da ta fasa shi..harta windows din dake cikin falon sae da ta fasa...! Jin karar Glass yasa Hajiyar fitowa da sauri daga sink din wanka. ..ta daura towel ...don duk tunaninta daga waje karar ke fitowa sae da taji tabbas daga falon take fitowa Sannan ta fito daga toilet ....tana fadin .. "Waye anan ? ..."nace wane shegene ya shigo yake mana barna...? ...cak ta tsaya ganin karamar yarinya rike da duwatsu duk ta farfasha masu kayan dake falon ...!! Nice nan Hudalliya ....ta fada tare da runtumawa da gudu ta fita daga falon ...hajiya ta bita da gudu tana fadin .. Bala rike man wannan shegiyar yarinyar karka bari ta fita ...!!!...ganin babu maigadi ya saka Huda sake juyowa tare da jifar Hajiya da wani dutsin sannan ta fice da gudu ...!! Da sauri hajiyar ta dafe gefen idonta da dutsin ya sameta ..kafin zafin ya saketa Huda ta bace mata da tunani ...!! "Wace Shegiyar yarinya ce wannan ? ..take tambayar Kanta ..yar gidan wane shege ce ? ...me muka mata dan ubanta ?..."Hurul ..aa Hudiya...mts ...aa ba haka tace sunan ba" ...ta fada tare da dafe kanta tana son tuno sunan ...Da yake bata san Huda ba ...don duk da suke zuwa Huda bata taba biyo Yaya Saa ko Mama ba ... Barister Shehu ya shigo rike da friut din da Hajiyar ta aikeshi sawowa tun bayan fitar Maman Huda ....turus yayi yana kallon hajiyar da ta zabga uban tagumi zaune tsakiyar falon ... "Yan Fashine suka zo Hajiya? ...ya tambaya a rude ... "Yan fashi ko shegiyar yarinya Shehu ?...ta bashi amsa tare da mikewa tsaye..." wallahi wata shedaniyar yarinya ce ta shigo duk ta mana wannan barna ...ban san ko yar gidan uban wa cece ba ...amma tace ko Hurus ...wallahi sunan ya shige man ...amma zan saka a nemo man ita cikin unguwar nan ..." da Sauri yace ..."ko Hudallah? ... "Ba Hudallah ba Shehu ...na manta sunan ...amma wallahi duk randa na kamo ta taja wa ubanta bala'i dan baran kyaleta ba ...har da ni fa tayiwa ruwan duwatsu Shehu ji binan Yar da idona ya kumbura"..to meye hadinmu da ita ..?.. "Hajiya kinga yi man kwatancen yarda yarinyar take ...na tabbata Huda ce wallahi "... "To wacece ita Huda? ..."na fada maka ba haka sunan yake ba" ..."itama da Hu din sunanta ya fara amma nata sunan ban taba jinshi ba .".. "Huda diyar mamansu Saadatu ce wadda aka kora yau ...kuma nasan yarinyar sarai bata da mutunci ...bara yanzu zanje idan ma itace ta sake jawa uwarta bala'i ....!!! Ya fita da sauri ...ko mota bai dauka ba ya taka kasa ....baiyi Sallama ba ya fada gidan a fusace ...Mama na tsugunne ta rafka uban tagumi ...Yaya Saa tana wanke kwanukan da suka ci abincin safe dasu ... Su duka suka mike tsaye ganinshi ... ya Nuna Mama da hannu yana fadin ..."Ina shedaniyar diyarki ? .... Ran mama idan yayi dubu ya baci ta kalleshi a fusace zata yi magana yaya saa ta rigata ... "Bamu da Shedaniya a gidannan ....amma akwaita a gidanku mai dattin da kwali sabon shigan arziki ...banza maciya amana jahilai ...!!! ...ta fada tare da rushewa da kuka ... "Rufe man baki Shedaniya ...akwae shedan irinki mai bin maza ....shegiya karuwa..!!! Mama ta daukeshi da mari ..."Karya kake Shehu har yanzu ban haifi Karuwa ba Wallahi kuma baran taba haihuwarta ba " ..!! Ni kika mara ? ...ko da yake ba komae bane tunda har na kwanta da diyarki !!..zafin ba wani bane da zai dameni ....don ko kadan bai kai zafin da zakiji ba alokacin da kika fahimci diyarki karuwar Shehu ce ..!! ..don bana tunanin ban bar maku yaron da zaku raina ba na Shehu ..ko a tunaninku mutuncin da nake maku sonku nake ..? mtsee Jahilai ...to Sha'awar diyarki nake kuma fine ta kawon budurcinta har gadona ....!! ...ba wani shegen da iyasa ya tsaya maku ..matsiyatan banza!! Wani wawan mari yaya saa ta dauke shi dashi ..tare da sakin kuka ...bata sauke hannunta ba ..Mama ta dauketa da mari itama tana kallonta cike da tuhuma ....!! Sulalewa Yaya Saar tayi bisa guiwarta tana fitar da wani irin gujin kuka ....!! Dariya Barister shehu yayi tare da fita daga gidan ya barsu cirko cirko ...yaya Saa na tsugunne Mama na tsaye tana hawaye ... A zaure yazo fita sukayi karo da Huda ...wani mugun kallo ya aika mata ....itama ta sake mashi nata ...sannan tayi cikin gidan da gudu jin kukan yaya Saa .... Yaya Sa 'a ....dukanki ki ya kuma ?....ta fada tare da dukawa kusa da ita ... Mama ta saka hannu a fusace ta janye Hudar Gefe guda tare da dauke yaya Saa da mari ta janyo kwalar rigarta ta dago kanta ....! "Fada man Sa'adatu' ...fadan man gaskia abunda Lauya ya fada hakane ?..ko karya ya maki Sa'adatu?..ta fada tana kuka ... "Wallahi karya ya mata Mama!! ...Huda ta fada ba tare da tasan abunda ake magana akai ba kawae ta tsinci maganar ne... "Yi man shiru Huda dan Ubanki ...!!!..mama ta kwasa mata tsawa ....firgitar da tayi ya sakata fadawa jikin yaya Saa tare da sakin kuka ..."Fada man Saadatu "...shin na haifi karuwar Shehu kamar yarda ya fada?.. koko sharri ne .!!... Cikin Kuka Yaya Saa tace .."wallahi Mama baki Haifi karuwa ..ba laifina bane Fyad'e yayi man mama ...!! Wani uban duka ta kai mata tana kuka da karfi ....Huda ta rike mata hannu tana kuka ... "Wallahi Mama Hard'e yayi mata ".....ta leka fuskar yaya Saa tana tambayarta ...Yaya Saa Hard'e kika ce ko? ... Fizge Huda tayi daga jikinta tana dukanta ba tare da tasan inda take duka ba ...su duka ukun kuka suke kamar ransu zai fita... "Dan Allah Mama ki kyaleta na rantse maki da Allah Hard'e yayi mata ..!! .mama wallahi agabana yayi mata ...har cewa nayi karka yi mata Hard'e amma yaki saurarena !!! ...kuma wallahi Yayata bata Amai kullun!!!. ....Mamarmu dan Allah ki bar dukanta ..bana so ..!!.....ta karashe maganar tare da rike hannun mamar tana kuka... Wani Uban Mari Mamar ta bata ' ..kafin ta hankadata gefe guda ta cigaba da dukan yaya sa'a ...amma Huda dawowa tayi jikin yaya Sa'ar mama ta ci gaba da dukansu a tare ... Jikin Mama har ky'arma yake ...jin zata fadi kasa ya sakata jingina da bango tana kuka ....sannan taja jikinta ta shige daki ta barsu tsakar gida !! Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡_* Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITER'S..._ *_25 to 26_* Da marece Mahmoud yazo kofar gidansu Huda ya aje motarshi ...jingina yayi yana jiran ko Huda zata fito ...don so yake yau yayi magana da mamanta .... Cikin saa ta fito idanunta jawur tayi kuka har ta gaji ....bisa dakalin gidan ta zauna tare da hade kanta da guiwa .... A hankali ya tako ya iso gurin ya zauna gefenta ..yana kallonta.. " Hudallah".... dagowa tayi tana kallonshi kafin ta kalli motarshi ta sake maida kanta gurinshi ba tare da ta amsa ba ... a hankali yace "Me aka maki Huda? ....wani abu kike so ? .. Kai ta girgiza mashi a hankali tana goge idonta .... "To fada man mana ' ...ko mamanki ta dukeki? ... nan ma kan ta girgiza mashi tare da kura mashi ido ... "To Yaya sa'arki aka batawa rai? ...yauwa Hudallah goge hawayen kinji ki fada man ...oya Yaya Sa'a ce? ..ya fada cikin sigar lallashi .. Daga kai tayi tana fadin ..." Ba lauya bane ya cuci Yaya Sa'a yayi mata hard'e ...kuma sae da nace kar yayi mata ...amma yaki jina!! ..gashi yanzu ya saka mamanmu sae dukanta take ...tana kuka ..." Hard'e ? ...mene haka Huda?....! Harara ta balla mashi tana fadin " karka maidani yarinya mana ...kato da kai baka san Hard'e ba ....wanda idan akayiwa mutanen gidansu suyita kuka??? ..ko baa taba maka bane?.. Shiru yayi yana tunanin me take nufi ...zuwa can yayi saurin kallonta yana fadin ko dae Raping kike nufi ? Ba tare da tace mashi komae ba ta mike zata shige gida ...yayi saurin riko hannunta yana fadin ..." Tsaya man Huda kinji ....please idan kin shiga gidan kice ina son magana da mama ...!! " amma kai mugune ...!! ..baka ga irin marin da ta man ba yau" kake aikeni na mata magana ...so kake ta sake marina kenan. ? kamar yana tsoronta yace " Please Huda ki taimaka kinji ko "... "Idan ta dakeni ' kanka zan rama wallahi " Da sauri yace " Na yarda Hudallah " Shiga tayi ciki zuwa can ta fito tace mashi Idon mamar a rufe yake ....ta mata ...magana taki budewa .....ce mata yayi taje tacewa Yaya Sa'a dan Allah yana son magana da ita .. Kafin ta bashi amsa yaya sa'a ta fito daga gidan da gudu tana kuka ...tare suka shiga gidan har da Mahmoud din... Mama na kwance bata motsi daukarta yayi da sauri ya sakata mota sannan yaya saa da huda suka shiga ciki suna kuka sannan yaja da gudu suka fita daga lungun ... Direct asibiti ya nufa da ita ...cikin gaggawa aka amsheta ....bayan an dubata ne aka tabbatar masu da tana raye ..hawan jini yayi attacking dinta sossae ... Bp dinta 210 ... Daga Hudar har Yaha Saa kuka suke ...Barister Mahmoud kuwa tsaye yayi yana kallonsu ..shi ya biya kudin komae ...aka hada mata magunguna .. Har isha'i yana asibitin ...sae da ta daeo normal sannan likita yace zaa sallameta su tafi gida ..... Barister Mahmoud ya dauko su ya kawo su gida ...da zaya tafine ya fitk da 20k ya bawa mama yace su sayi abinci kafin ya dawo .. Sam Mama taki karba ...tace wanda ya mata bata sani ba ta gode amma wannan bara ta karba ba don yanzu bata bukatar taimakon duk wani mutun Taimakon Allah kawae take so ...Babu irin rantsuwar da bai mata ba ...amma taki karba ... Ganin yafi damuwa da Huda ne ya saka Yaya Sa'a saurin janyo huda jikinta tana hawaye ...don bata kaunar wani namiji ya kula Huda yanzu .....a iya saninta zata iya kashe duk wanda yayi kokarin batawa Huda rayuwa ... ganin kamar basu bukatar shi ya sakashi tashi ya tafi ...zuciyarshi cike da tunanin maganar huda ..."wae Hard'e"...what does she means? ...haka yayi ta sake sake har ya isa gida ... Yana Shiga Mama tace ya dauki matarshi ya tafi da ita ...don wallahi ta gaji da Hanne ....!!!... Ba dan yaso ba ya shiga dakin Hanne tana kwance sae barcinta take hankali kwance ....pillown da ta daura kanta ya dan buga kadan ta mike ba salati tana fadin ..."wane banzane mutun na bacci yake tadashi ? Ba tare da yace mata komae ba ya juya zai fita ..."sam hanne ba da'a" ...abunda ya fada kenan a ranshi ... hannunshi ta riko "Ohhhh ...Yaya ne ....Yi hakuri bansan kai bane yasin" ....ta fada tana dariya ba tare da ya juyo ba yace " ki iskeni falo zamu tafi gidan yau" ... Ihun dadi ta sake tana fadin " Haba yanzu naji magana amma an kunshe mutun cikin gidan sirikai ba damar ya sake sae shegen sa ido "... Ko nuna alamun yaji me take fada baiyi ba ...ya fice daga dakin ...kafin ya zauna har ta fito janye da uwar jikkar ... Mamanshi yayi wa bankwana tare da Abba ...sannan suka tafi ..da yake bai ci komae ba ..ya tsaya wani karamun restaurant zai sayi abinci ... Hanne tace " haba yaya me zaka saya a wannan karamin gurin dan Allah? wallahi ba girmanka bane ...!! Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡_* Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITER'S..._ *_27 to 28_* Dan juyo yayi kadan yana kallonta cike da mamaki kafin yace " banda wani girma Hanne ..sae dae ke nake tunanin girmanki yakai diyar sarki a babban kauyenku !!! tasan magana ya fada mata sae ta kulle bakinta tayi gum ....har suka isa gida bata kara magana ba ..bareshi da ba kowa yake kulawa ba ... Gidan ya dan nunnuna mata sannan ya shige dakinshi ya barta hangame da baki ... ••°°•• Da kyar Yaya Sa'a tayiwa Mama bayani ta yarda ...ranar tace su tashi suje gidansu Barister Shehu ta fada ubanshi wata kila shi ya sauresu a bi masu Hakkinsu .... Da Mama da Yaya Sa'a sae Huda suka tafi ...cikin saa a harabar gidan suka iske su duka ukun tsaye da alama wani guri zasu ....sae sojojin dake tsaye cirko cirko Hajiyar na ganinsu ta daure fuska tare da kallon Shehu ....Mama ta iso ta gaida Alhajin ...tun yarda ya amsa mata gaisuwar jikinta yayi sanyi ... Tace " Alhaji nazo na sanar dakai abunda ya faru ." .. A wulakance yace "ina saurarenki" . tace " Alhaji mu talakawa bamu da komae sae Allah ...ni da diyata muna zuwa aiki anan gidan ...sae Shehu ya haye mata har ya mata fyad'e ...shine nazo na fada maka ko akwae matakin da zaka sauka " "Bullshit kauyawan banza da wofi!! ....matsayita!! sae uban me dan yayi Raping dinta ....kanta aka fara raping koko kanta aka kare ....? ..Kai Shehu ko yanzu kake bukatar Yarinyar nan ...na yarje maka kayi abunda kake so da ita ....gidan ubanka suka shigo ., ..basu isa su wulakanta me ba har gida...!!! "Dat my dady "....ya fada yana aika masu wani irin matsiyacin kallo ...!! Dad din yace ..".Guard !!....ku fitar man da wadannan matsiyatan ku bar waccen ...!!! ya nuna yaya Sa'a ... Da saurin Mama ta rugumeta tare da janta da gudu zasu fita daga gidan ...amma kafin su fita wani daga cikinsu ya fizge yaya Saa tare da tura mama da karfi waje ....haka ya dauki Hudar ya wurgota waje tana ihu tare da turje turje ..... Mama kuwa kwanciya tayi kasa tana birgima lokaci guda numfashinta ya fara sarke mata ....sam Huda bata lura da halin da mama take ciki ba ...tana jikin Gate din tana kuka tare da buga kanta jikin karfen kamar ranta zai fita ... Yaya Saa kuwa ba shehu kadae ba harda guard din dake sae da yace duk mai bukata idan shehu ya gama ...ya bashi dama ....kadan daga cikinsu ne basu taba yaya Saa ba .....numfashinta har daukewa yake don azaba ... sae da suka gama wulakanta ta sannan aka bude gate din aka jeho da ita kamar kayan wanki ....Huda tayi kanta ganin jikinta duk jini ..tana kuka tare da jijjigata ...... ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Huda ....fuskarta kamas babu alamun hawaye sae dae kurawa Huda ido da take tana kuka .....Inda mama take yashe ta kalla ....kafin ta ja jikinta ta isa gurin tana kallon fuskarta ... Ba tare da tace komae ba ta koma ta zauna kar ba mutun ba .... Huda ta cakumo Yaya Saa tana fadin .." Yaya saa me suka maki ? ....me suka yanka jikinki duk jini?....Me yasa bakya kuka ? ... Ba tare da tace mata komae ta nuna mata mama dake kwance a kasa ......gurinta ta nufa tana kiran sunanta ... Mama !!!...ga Yaya Sa'ar sun maido mana. ...ki tashi ki ganta mama duk jini jikinta ban San me suka yanka ba a jikinta......ki tashi dan Allah ta dawo fa Mama ....!!! girgiza take tana kuka ...amma mama ko motsi bata yi ... Liman din unguwar yazo wucewa ta gurin ya gansu haka ....yace " Subhanallah Huda Me ya sami mamar kwance a kasa ..." "ban sani ba ...taki tashine ...kazo ka mata magana ...yaya saa ki taso don Allah ...!!! Da sauri ya iso gurin ...ya leka fuskarta tare da ja da baya ....."inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un "...yake nanatawa ...sannan ya tafi da sauri... Jimawa kadan sae gashi da mutane ....ina suka dauki Mamar suna fadin wae ta rasu ....duk abunnan da ake Yaya Sa'a na zaune idonta na kallonsu ...har sae da aka dauki mamar sannan Huda ta jata tana kuka suka tafi ... Kafin me ...gidan ya cika tab da yan gaisuwa ....huda ke ta uban ihu amma yaya saa kukan ma yaki fitowa ....ita kanta so take tayi kukan amma ba dama Feedohm💞 💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_* 🍁 *_HASKE WRITERS ASSOCIATION💡_* ( _Home of Expert and perfect writers_ ) Na Feedohm💞 *_DEDICATED TO_* _EXCLUSIVE WRITERS..._ *_Main mera dil aurtum ho yana phir kyun ho palken ..👌🏻..jhuka yein wahan ..😘 Haske writers ..Ummy Aisha ..Hajja ..Asmy ..Ayusher ..Fatee ..Khaleesalat hydar ..Billy ..Nana diso ..Asy ..HOENPW😘_* *_29 to 30_* Bayan sati daya ne barister Mahmoud yazo ganin jikin mamar ....Yana zuwa yaga ana addu'ar bakwae kofar gidan .. ...tambaya yayi me akeyi ...wani ya ce mashi Maman su Huda ce Allah yayiwa rasuwa sati daya kenan... turus yayi ya kasa koda daga Kafa da k'yar ya samu ya dafa bango ya zauna a dakalin tare da tallabe kanshi da hannu biyu... Yaya Saa kuwa ta bar magana da kowa ....Sannan duk wani namiji da yazo masu gaisuwa bata karba ...sae ma ta janyo Huda jikinta ta hanata koda motsawa ....!! ••°°••• Barister Mahmoud yana kokarin kawo masu taimako amma sam yaya Saa bata karba ....da taga yana kallon Huda zata fara kuka tare da rokanshi ya fitar masu daga gida dan Allah ...!!! Cikin dan lokaci abunda zasu ci ma ya fara gagaransu ....ganin basu da madafa yasa yaya saa fara wanki da guga da kuma dakau idan ta samu ...duk kokarinta na nemawa Huda kudin makaranta da abinci ...zata iya kwana biyu bata ci abinci ba ...amma bata barin Huda da yunwa ko ta mintu Biyu....duk wani aikin wahala da zatayi bata kashe ko sisi a jikinta sae dae ta kashewa Huda .....duk wani gurinta na duniya yana ga Huda !!.....ta dauki son duniya ta kara daura mata ... Lokacin da cikinta ya fara girma sae ta fara fuskantar wulakanci gurin yaran Unguwa ..da Huda ta fita sae yaran su dinga tsokanarta wae yayarya tayi cikin shege ...!! Haka itama yaya saa da ta fita an dinga zind'enta ana gulmarta ....sae ma ta daina fita kwata kwata ....duk tayi bak'i ta rame ...don Ma Huda ba kanwar lasa bace ...duk wanda ya taba yaya saa bata kyaleshi sae ta bishi har bayan uwarshi ta duka ...idan matar aurece bata kyaleta .. kan yaranta kanana take fanshewa don da sun fito waje zata kamasu ta doka ..yaran basu kara sukuni har sae matar ta zo har gida ta bawa yaya Sa'a hakuri..... Ranar da Huda akayi masu hutu ta dawo daga makaranta ta iske yaya saa kwance bata lafiya ... " Yaya Sa 'a ki tashi muje asibiti kinji ko ...sannu ..ki ta masu Allah ya isa har su mutu ....!!! Ganin ciwon ya dameta ne ya sakata tashi ta shirya suka tafi asibiti ... Bayan sunje ne aka mata aune aune sannan aka ce su jira result ...suna zaune sae uban surutu Huda keyi ..nurse ta fito da result din tare da kiran yaya Saa office din ... banda "Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un" babu abunda yaya Saa ke furtawa ...wae HIV ni Sa'a .... ....Juyar da kanta take ta rasa inda zata sakashi ... tun likitan na kokarin mata bayani har ya fuskanci sam bata cikin hayyacinta ...Huda ta fado office din da gudu ...tana fadin .. "Yaya Sa'a ki fito mu tafi mana ....kin zauna sae surutu suke maki wae Har da fadin kina da HIV ..dan Allah ba sae ki godewa Allah ba ...ni da ko ABC ban dashi ya to zanyi ...ki tashi mutafi ...dan Allah" .. Zuba mata ido doctor din yayi tare da fadin "Sister baraka ...ki fita da wannan yarinyar mu karasa maganar tukun"... Yaya Sa'a tace " kubarta ...itace rayuwa duk abunda ya sameni tare muke bakinciki ...na sani ko batayi yanzu ba gaba sae tayi bakincikin da yafi wanda nayi yanzu...ku kyale ta ...ku kyale man Hudata ...!! ...idonta ya ciko da kwallah .. Da sauri Huda ta kalli doctor din tare da zabga mashi harara tana fadin .." ku mazan nan mugayene ..me yayata ta maku da duk lokacin da ta ganku sae tayi kuka ...ba ku sonta ne? ....tashi muje Yaya sa'a ki bar kuka kinji ko .. Ni kadae ke sonki yayata kuma duk wanda ya cuceki baran taba kyaleshi idan na girma ...!!! ..hannu ta saka ta share mata hawayen tana kallon likitan ... Hannu Yaya Sa'a ta fizga da karfi suka bar office din ...yarda take jan Yaya Sa'a sae ka dauka itace yayarta .... Yaya Sa'a in tsaida mana Okoda mu hau ?... Cikin Kuka tace ..Huda banda kudi okoda.. ....kin gaji da tafiyar ne ? ... Daga kafarta tayi tare da nunawa Yaya sa'a tana fadin.. " lokacin da kika shiga gurin likita na taka kwalba ...ban iya tafiya Sossae Yaya Sa'ata ... kanta

Chapter 3 of 10