Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma, amma ba a irin wannan lokacin ya dace ba, dan abubuwa da yawan gaske na zuwarmin a zuciya game da al'amarin nan, sai dai banason furta komai nafison matsayin Jawaad na jami'in tsaro shi yay wannan tunani, zuwan Umm-Anum da Anuwar ba shine abu mai muhimmanci ba a yanzu ƙwarai da gaske, dan komai ma zai iya faruwa inhar azzaluman da suka ƙulla al'amarin suna tare dasu ne, kai koma nesa da su suke suna bibiyar al'amarin komai dan nima nayi makamancin wannan rayuwar nasan sarƙaƙiyar cikinta, amma kai Jawaad minene a ranka?”.
Zama Jawaad ya gyara cike da kaifin basirar da ALLAH ya azurtashi da ita shima yace, “Na gamsu da duk abinda kuka faɗa, dan nima a kwanakin nan sune suka zama abin nazarina, rashin tambaya ta komai da Ummuna batai ba yafi komai tsayawa a raina sosai, ni a yanzu shirina na farko shine lallaɓata naji waɗanda sukai rayuwa dasu kamar ma'aikatan gidan da sauransu”.
“Tunani mai ƙyau” cewar Takawa da Abu-Siddiq. Jawaad ya cigaba da faɗin, “Sai abokai makusanta da Abbah ya rayu da su kafin shigarsa siyasa da hawansa mulki, abu na uku ne bamu da dama a kansa, dan a wajen Ummuna ne kawai zamu iya jin wasu sirrika game da rayuwar Abba da ƴan uwansa a lokacin da yake mulki, dan haka wannan na ajiyesa gefe zanyi anfani da waɗancan damar guda biyu mugani ko za'a dace, amma nima na gamsu da basai sun bimu ɗinba kam yanzun”.
“ALLAH yay maka albarka” cewar Abbu yana dafa kafaɗar Jawaad dake a kusa da shi. A tare suka amsa da amin. Abbu ya cigaba da faɗin, “Nima nanda sati guda zan biyo bayanku dan inason ganawa da Abba (Alhaji Babba). Kai Jawaad ya jinjina masa yana ɗan murmushi da faɗin, “ALLAH ya tabbatar Abbu”. Da Amin duk suka amsa..
Akan wannan shawarar taron ya tsashi, shi dai Anuwar badan yasoba ya haƙura akan binsu Jawaad, dan yay masifar ƙwallafa ransa da zumuɗin son ganin ahalinsu.
★★★★★★★★
Cikin hikima Abbu ya samo sunayen ma'aikatan da su Umm-Anum sukai rayuwa dasu a gidan gwamnati da kafin hakan, harma da sunayen abokan Abban Jawaad ɗin data iya tunawa da ƙyar.
Sai kuma ta nema tada hankalinta akan komawar su Jawaad ɗin, ta kafe akan ita bazata barsu su koma ko inaba sunzo kenan. Duk yanda Jawaad dake cikin damuwa shima yake ƙoƙarin mata bayani akan aikinsu da buƙatarsu da akeyi taƙi fahimta, tamaƙi sauraren komai, saima ta saka masa kuka daga ƙarshe. Wannan abu ya sake tada hankalin Jawaad sosai, dama dauriya kawai yakeyi. Da ƙyar aka shawo kanta da lallashi akan Jawaad da Bilkisu zasuje su ajiye aikinsu ne su dawo nan da zama gaba ɗaya wajenta.
Wannan batu ya sakata yarda, amma sunsha gargaɗi akan karsu daɗe basu dawo ba, dan da farko ma catai Jawaad yaje shi kaɗai yabar bilkisu ita anan, sai da Abbu ya sake wata sabuwar dabarar ya lallaɓata sannan tadai barsu suje ɗin, sukuma dawo akan lokaci kamar yanda ta faɗa, inba hakaba zata aika a ɗakkosu koda basu gama shiryawaba.
Da wannan yarjejeniya daba tabbatacciya ba muka baro ƙasar saudia cike da kewa ni da boss. su Ummu kam can muka barosu dansu sati biyu zasuyi.
Saukar yamma mukayi ƙasarmu ta haihuwa, inda muka iske Sadiq yazo tarbarmu, dan shikaɗai yasan da dawowar tamu, dama tunda muka tafi boss bai yarda munyi waya da kowaba bayan su oga Aliyu, su Ummah duk yaƙi yarda yay waya da su, dan baiso suji komai da wuri harsu kasa daurewa su sanarma Alhaji babba, a yanzunma da muka dawo bazai faɗa musu komaiba gudun matsala.............✍



Asha sauran weekend lafiya🤒😣🚶🏻🚴🏼



ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[1/17, 7:26 PM] HASNA✍🏻: Amina Wada:
ƘWAI cikin ƘAYA!! - 51 - Wattpad

Turƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...


*_Shin kina ko kana sa sha'awar koyon ilimin ICT?_*

*_Ko kuna da sha'awar yadda ake hada cartoon?_*

*_Ko kana da sha'awar yadda zaka bunqasa kasuwancinka ta hanyar online?_*

*_Matsalarki ko matsalarka rashin makarantun da zasu koyar dake/kai ilimin computer ta fannnin larabci?_*

*ALBISHIRINKU KANAWA*

*_Kukanku ya qare,matsalarku tazo qarshe,shahararren kantin nan na yanar gizo wato RAHAMALLS yazo muku da makarantar koyon sarrafa computer a sauqaqe wato RAHA COMPUTER INSTITUTE(RACI)_*

_Sun tanadarmuku qwararrun malamai wanda zasu koyar daku bisa tsarin da kuma cikakkiyar qwarewa ta yadda zaki fahimta fiye da yadda kuke zato_

*ga masu buqatar aji na musamman har cikin gidajensu,makarantar ta shirya tsaf don baku darussa har cikin gida*

*sannan akwai tsarin ajujuwa na musamman bisa yanar gizo wato(online classes)*

*kaidai maza garxaya ka tuntubesu akan wanannan lambar waya*

08033990209

*_akwai ragin kaso hamsin cikin dari na kudin registration ga kowanne dalibi_*👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽


..................Gidan duk ya ajiye ƙananun ƙura, duk da ko'ina a rufe yake, haka na daure naɗan gyara ɗakinsa dan mu samu inda zamu kwanta, kafin a kira sallar magriba na kammala, shikam wanka ma yayi ya fita tun fara aikin nawa. Bai dawo gidanba har saida akai sallar isha'i, kusan tara sai gashi ya dawo mana da abinda zamuci. Gaba ɗaya banajin daɗin yanayinsa, ya koma min Boss ɗin dana sani a office mara walwala da yawan magana, komai nake sai dai yayta bina da ido kawai, abincinma da ƙyar na samu yaɗan ci yace ya ishesa, nima cire hannuna nai a ciki na ɗauke kaina gefe. “Miye hakan?”. Ya faɗa muryarsa can ƙasan maƙoshi. Ƙoƙarin miƙewa nai tsaye nace, “Na ƙoshi nima...” kafinma na gama rufe bakina naji caraf ya cafko hannuna ya maidoni ya zaunar, kallonsa nai ina kumbura fuska, ya zabgamin harara tamakar idanunsa zasu faɗo ƙasa, “Ina wasa da ke ko?”. Ƙasa nai da kaina dan bazan juri kallon nasaba, “ALLAH nima na ƙoshi to”. Banza yaymin bai tanka ba, ya ɗebo ya kawo bakina, zan ɗauke kaina yay saurin faɗin, “Kinsan ALLAH idan baki shiga hankalinki ba sai na sauya miki kamanin wannan fuskar taki, malama haa”. Idanuna cike da ƙwala na buɗe bakin, ya ko zubamin yana sake zabgamin harara da yin ƙwafa, inaji ina gani yaymin ɗurar dole, shiko yaƙi ya ci, sai yogurt yaɗan sha, hakanne yasa naɗan samu kwanciyar hankali. Kasancewar a gajiye muke ga mai gayya mai aikin baya tare da walwala, gashi zamu koma aiki gobe idan ALLAH ya kaimu sai mukai kwanciyarmu da wuri.

WASHE GARI

           Tun kiran sallar farko na tashi, cikin sanɗa na fita daga ɗakin nasa, kasancewar barcin da muka kwanta da wuri sai na tashi jikina babu nauyi sosai, da wannan damar na fara rage aiki. Koda ya fito zai tafi massallaci ya ga ina aikin gyaran babban falo baice dani komaiba ya fice abinsa, ajiyewa nai nima na koma ɗaki nai salla, ina idarwa ban hutaba na sake fitowa na cigaba, ana idar da salla shima bayan wasu ƴan mintuna sai gashi ya dawo, bayan mun gaisa shima sai ya cire jallabiyar jikinsa ya shiga tayani aikin. Duk da na roƙesa ya bari zan ƙarasa tunda na kusa bai saurareni ba, sai da yaga ya rage bedroom ɗina kawai sannan ya barni na ƙarasa.
          Ƙurar dana gani tasa nake sharo har ƙarƙashin gado kamar yanda nayi a ɗakinsa da ƙarƙashin kujerun falo ma, abu na sharo a ƙarƙashin gadon, wanda ya sakani dakatawa da sharan nasaka hannu na ida jawosa dan naga minene, wallet ce ƴar karama dan bata kai girman normal wallet dana sani ba, kamar zan buɗe sai kuma na ajiye da tunanin ko tashice, saman mirror na ɗaurata na cigaba da sharan harna kammala komai, ganin lokaci yaja na shiga bayi dan yin wanka sauri-sauri, ban wani ɓata lokaciba na fito.

Idanuna ne suka sake sauka akan wallet ɗin nan, duk yanda naso na share a yanzun sai na kasa hakan, na matsa gaban mirror ɗin ina goge fuskata da ƙaramin towel dake a hannuna da hannun haggu, na damar kuma sai na fara ƙoƙarin buɗe wallet ɗin, ɗan ƙaramin hoton dana fara cin karo da shine ya sakani shiga mamaki, na fara fiddo abubuwan cikin wallet ɗin gaba ɗaya, ƙirjina sai wani irin mahaukacin bugawa ya keyi, banma san lokacin dana saki towel ɗin hannun nawa ba jiki na rawa, harda zufa ta fara tararmin a goshi, nagama zazzage komai a ciki, abubuwane masu muhimmanci da daraja dana san maisu bazai taɓa sakaci dasu ba da har zan gansu anan, to wama ya kawosu? Ni dai babu wanda ya taɓa zuwamin nan gidan a kaf mutanen gidan balle nace a mistake wani yazo da su. A fili nace, “To kodai boss ne ya kawo?”. Wannan tambaya na yitane badan zuciyata ta gamsu da ita ba, Duk da sallamarsa da naji a bayana ban iya na waiga ba.
       Ƙarasowa yay yana ɓata fuska ganin bama ta shirya ba, ya ajiye ƙaramin tiren da ya ɗoro musu tea a saman table kafin ya ƙaraso inda take yana jan tsaki. Ganin ko motsi bataiba har yanzu tanata juya abu a hannu sai kansa ya sake ɗaurewa, “Wai kina kallon agogo kuwa Miemaa!?”. Ya faɗa a ƙausashe. Ɗagowa nai ina kallonsa, cikin rawar baki da fargabar amsar dazan iya samu nace, “Dan ALLAH kaine ka kawo wallet ɗin nan ɗakin nan?”.
        Baice komaiba ya tako gabana tare da riƙo hannuna duka biyu yana kallon abinda ke ciki, cards ne masu muhimmancin gaske, ga sunan maisu kuma ɓaro-ɓaro a jiki da hotunan sa, “Ina kika ganta ke?”. Gado na nuna masa batare da nayi magana ba, ya kafe hannayena da nake sake jujjuya cards ɗin ƙo ƙyaftawa bayayi, nikam ƙirjina sake bugawa ya keyi da sauri-sauri, jira kawai nakeyi yace wani abu, amma yaƙi cewar. Hawaye suka sulalomin ina mai fatan kar abinda keta zomin arai ya kasance hakane, kai banama fatan hakan, sai dai idan anason min yawo da hankaline dan a ɓata masa suna. Muryata na rawar kuka nace, “Kace wani abu dan ALLAH boss”. Kansa kawai ya girgizamin yana mai cije leɓensa na ƙasa, ya saka hannu ya amshi komai dake hannuna ya maida a wallet ɗin ya sakata aljihu, taimakamin yay na shirya ina hawaye, wata gigitacciyar tsawa data nema haukatani ya dakamin, “Ke komai kuku! kuka!! kuka!!!, komai abin kukane a gareki, ya isheni haka banason ji kuma, malama ki sharemin waɗanan banzayen hawayen kafin nai miki bugun kayan wanki wlhy a gidan nan!!!”. Na matuƙar tsorata da yanayinsa, na koma jikin madubi na maƙure ina ƙoƙarin haɗiye kukan, gaba ɗaya kamanninsa sun masifar sauyawa, idanunsa sun kaɗa sunyi jajur, baice dani komaiba ya juya ya fice daga ɗakin. Sake fashewa nai da kuka ina faɗin, “Ya ALLAH ka bani haske akan wannan al'amarin”. ƙarar takunsa dana jiyo ya sakani saurin goge hawayen na juya ina saurin ɗaukar soson hoda nahau shafawa. Bayana yazo ya tsaya yace, “Agogon wanene wannan?”. Da sauri na juyo gabana na faɗuwa na zubama hannunsa idanu, kusan mintuna biyu na ɗago na kallesa, Kaina na girgiza masa alamar ban sani ba. “Kin tabbata?”. Na ƙara ɗaga masa kaina. Bai sake cewa komai ba ya koma bakin gado ya zauna tare da ɗaukar kofin tea ɗaya ya fara sha yana cigaba da kallon agogon kafin ya ajiyesa gefensa. Ganin ya kafeni da idanu nai sourin ƙarasa kimtsawa zuciyata nata kaikawo da tunane-tunane kala-kala waɗanda gaba ɗaya sake zurma zuciyata suke a firgici. Tea ɗin ya ɗauka ya miƙamin, babu musu na amsa dan a yanda yake ɗinnan zai iya mammakeni idan nai masa gardama. Ni nafara fita daga ɗakin nakai kofunan kicin na ɗauraye da sauri-sauri na fito, a falo na iskesa jikkata na gefensa ajiye. Ɗauka nai tare da briefcase ɗinsa, baice dani komaiba nai gaba ya bini a baya, shine ya kulle ƙofar sannan muka ƙarisa inda Sadiq ya goge motar ƙal yana jiran fitowarmu shi da maigadi, mun gaisa dasu cike da girmamawa, suka buɗe mana motar muka shiga bayan kowannenmu ya karanto addu'ar fita daga gida.

Story continues below

             Tunda muka fice daga gidan hankalinsa nakan wayarsa, yayin da ni kuma na afka kogin ruɗaɗen tunanin da gaba ɗaya kwanyar kaina ta gaza ɗauka. Jinai kawai an riƙo hannuna, na juyo na kallesa, baice dani komaiba ya matsoni jikinsa tare da aza kaina bisa damtsen hannunsa yana shafa bayana. Shiru nai ina haɗiyar zuciya da hawayen dake taho mani.
        Tunda Sadiq ya tsaida motar muke ta yima station ɗin kallon mamaki, duk da dai safiyace sosai baici ace babu mutane haka ba, sai securitys da keta kai kawo, Sadiq ya buɗe masa ya fita, kafinma ya zagayo ta wajena nidai na buɗe da kaina. Na ƙara ɗan wawwaigawa na kalli ko ina, station ɗin tsit kamar babu kowa a ciki.
       Shima kansa kallon ko ina yake da mamaki, amma baice komaiba, ganin bai amsa jikkarsa ba nasan so ya ke saina kai har office ɗinsa kenan? Tare muka jera, baya bari ya tseremin da ko step ɗaya. Shine ya buɗe ƙofar, muna shiga kawai sai mukaji abu kanmu ana mana wanka da shi. Saurin ƙoƙarin fara share fuskkokinmu mukayi, amma abin yaƙi daina zubowa, sai ma ihun ma'aikatanmu da tafi daya karaɗe wajen. A sannan ne abun ya daina zubowa, muka share na fuskarmu sannan muka kalli juna kafin mu maida ga kallansu. A take kunya ta kamani kuma, dan gaba ɗayansu sukayo mana caa a ka da kalmar “Muna tayaku murnar aure!”.
      Murmushi Jawaad ya daure ya saki duk da iya fuskarsa ne, kafin ya maida dubansa ga Bilkisu datai ƙas da kanta, ya kamo hannunta cikin nasa yana faɗin, “Mun gode sosai, ALLAH yabar zuminci”. Ya ƙare maganar da kai hannun Bilkisu saitin bakinsa ya  sumbata. tafi aka sakeyi, sannan kowa ya nufosu da ƙyautar dake hannunsa, tun jay na amsa har hannunsa ya cika bilkisu ma ta fara amsa, jabeer ne ya matso ya taimaka musu aka tarasu waje guda ya sake musu godiya itama bilkisu tai musu ranta fal mamaki.
        Gaban ƙaton cake ɗin da akai da hotonsu aka jasu, daga bilkisu har jawaad ɗin dai murmushine shinfiɗe a fuskarsu, bazaka taɓa gane sunada damuwa ba, bily ta fara ɗaura hannun ta saman wuƙar kafin Jay ya ɗaura nasa saman nata suka yanka. Ita ta fara cirar ɗan guntu ta saka masa a baki, yay mata murmushi mai sanyi ya ciro kaɗan itama ya saka mata yana jawota jikinsa ya rungume, saboda ganin yanda Rose take musu wani irin mugun kallo mai cike da tsana da takaici yay hakan, da farko baiyi niyyar bama Bilkisu cake ɗinba, amma saboda Rose yayi dan yana lure da ita ko kalma ɗaya bata togaba na tayasu murna, hakama wasu daga cikin matan gurin sai baƙin rai suke da bankama bilkisu harara..
     Nanma tafin akayi, kafin Sir Ahmad ya farayin jawabin taya murna a garesu kasancewarsa head of department nasu, daga nan sauranma suka sake tayasu murna da fatan alkairi da bama Jay hannu suna musabaha, matan kuwa Bilkisu suke bama hannu itama suna mata, shikam Jay sai dai su ɗaga masa dan sunsan ƙa'idarsa ce baya hannu da mace ko wacece ita a station ɗin nan ko tana a gaba da shi kuwa sai dai a kuskure. Suma mazan duk da Bilkisu na ƙasansu hakan bai hanasu mata murna ba, tanata amsawa a kunyace dan wasuma ko magana ita bai taɓa haɗata da suba sai yau.
          Sai da aka gama ɗan kace nace sannan suka wuce office ɗinsa, ƙyaututtukan da suka samu kuwa tuni Jabeer ya saka an kaisu ciki dama.
              Jikkarsa na ajiye masa saman table ɗinsa na ɗan kallesa, ganin hankalinsa nakan files ɗin saman table ɗin ya ɗauki ɗaya yana dubawa saina ce “Sai anjima” kawai na juya zan fita. Caraf naji an riƙoni, kafinma na juyo ya maidoni baya ya jingina da table ɗin, kallonsa nai da mamaki, ya ɗan harareni batare da yace komaiba naji saukar laɓɓansa kawai saman nawa babu zato.
       Idanuna na lumshe kawai ban masa wani musuba ko sau ɗaya, dan inhar zai huce ta hakan to Alhmdllh, rabonsa dako kissing ɗina tun randa mukaje Saudia. Ganin da gaske yake sai kawai na shiga bashi gunmawa, nidai fatana ya samu nutsuwa wannan fushin da fusatar dana gani tattare dashi ya gushe.

lokacin da matsalarnan taku ta faru, saboda ina sonshi na haƙura na mance da komai kamar bai faruba, yazo suka rabu da matansa muka tafi U.S ɗin nan, babu roƙon da ban masaba muyi aure a lokacin tunda dai ai baida mata, amma ya dinga shareni da zancen har muka dawo, yanzu duk ƙoƙarin nan da nai masa bai ganiba sai daga ƙarshe ya auri wannan yarinyar da tazo jiya-jiya cikinmu, bakuga yanda ya yarfani a gabanta ba yanzun, mi take da shi da har zai wulaƙantani a kanta?”.
       Kasa magana duk sukai, dan wannan faɗan kam dai yafi ƙarfinsu, duk da sunsan komai, amma ita rose banda haukarta ai ba lallaine ka SO a SOKA ba ko? Su shaida ne boss bai taɓa cewa yana sonta ba, sannan bai taɓa wulaƙantata ba. Hafiz ya taɓe baki cikin takaici yace, “Ikon ALLAH, so kike ya wulaƙanta matarsa a kanki kenan komi? Mtsoww! Lallai aiki ya sameki, kuka kuwa yanzu kika fara s.....” hannunsa Aliyu ya riƙe da sauri yana murmushi, yasan hafiz da iya yaɓowa mutum zafafan magana, yanzu sai ya sake birkitata. Duk da hakan kuwa sai da Rose ta hayayyaƙo ma Hafiz akan dama ta lura ita tuni ya tsaneta.
       Da sauri Jay ya bugi tebirinsa, cikin tsananin ɓacin rai ya nuna mata ƙofa yana faɗin, “Rose fitarmin a office!!”. Rose ta nuna kanta tana faɗin, “boss ni ka.......” cikin ƙaraji ya katseta ta hanyar sake doka tebir ɗin, “Nace! Ki fitarmin daga Office”. Yanda taga idanunsa sun masifar kaɗawa ya sakata firgita, tasan shi tasan shiɗin wanene idan yay fushi, ta kuma san abinda zai iya aikatawa bayan hakan, ta kalli su Jabeer ta sake kallonsa.
     Tashi Jabeer yay ya kama hannunta ya fitar da ita dan ya tabbata wlhy idan har ta sake wasu mintuna bata fitaba komai yazo masa rai zai aikata mata, sai da ya kaita har waje sannan yace, “Rose miyasa kikai haka? Kinfa san wanene boss?”. Zatai magana yace, “Kinga kije zanzo na sameki muyi magana, amma Please ki daina masa haka babu ƙyau, wlhy na tabbatar yana ɗaga miki ƙafane darajar kina cikinmu, kinsan fa yana gaba dake, sannan boss bayason raini, kije zanzo ni da Aliyu mu sameki”.
     Badan taso ba ta tafi tana sharar hawaye da kissima irin tashin hankalin da zata saka Bilkisu a station ɗin nan.

Turƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...

(🤔Rose mi kike ƙullawa kuma?).

★★★★★★★

         Tana fita Jawaad ya daki kujerarsa daya tashi akai yana faɗin, “Wlhy yarinyar can saita bar aiki a cikinmu, kai ama station ɗin nan gaba ɗayansa”. Da sauri Aliyu ya taso yana faɗin, “Please Boss! calm down, don't waste your time for her, ba yanzu ya kamata ai wannan ba”. Hafiz yace, “Gaskiyane maganar Aliyu boss, micece rose da har haukarta zai dameka, nifa dama can bataimin ba, duk da tana da ƙwazo tana da siffofin mutane masu bala'in son kansu, ka barta saita gama shagala bazaka ɗauki matakin komai a kanta ba sannan ka ɗauka. Amma idan aka maida mata murtani a yanzu anma damu da ita kenan, abinda kawai za'ai mata shine winning, ayi bala'i bala'in winning ɗinta akan Mami, idan tace zata shigar mata hanci kacimin ubanta iyakar iyawa”.
        Ƴar dariya Jabeer da ya shigo yayi jin furucin Hafiz ɗin, ya zauna yana faɗin, “ALLAH kai mugune Hafeez”. Zama duk sukayi suma, Hafiz yace, “ALLAH kuwa jabeer haukar yarinyar baimin ba, haka ake so ne banda hauka?, ni dama ni tace tana so ALLAH kuwa ko, hummm”. ya ƙare maganar da cije leɓe irin na tsantsar mugunta. Basu Jabeer ba hatta Jay sai da ya murmusa yana mai girgiza kansa, dan yasan Hafiz shegen kansane a iya mugunta.
     Ya sauke ajiyar zuya da jan guntun tsaki. Aliyu yace, “Kayi haƙuri boss, mu munzo musha labarin Honeymoon shashashar ta wargaza komai”. Harara ya balla musu, dan haka suka kwashe da dariya suna tafawa. Jabeer yace, “Wlhy Jay kayi wani ɓul-ɓul da kai fa, ka kuma ƙara haske”. “Kana baƙin ciki ne ɗan sa ido?”. Jay ya faɗa yana jefa masa biron hannunsa. Dariya suka sake kwashewa da ita.

Burrum aka turo ƙofa babu ko neman izini, ƙoƙarin janye kaina nayi amma ya hanani kowacce dama, saima sake turani jikinsa yayi sosai da sake sauya salon sumbatar, ƙamshin turaren rose da naji ya sakani nima canja salo dan ta bani haushi ɗazun, dan batamin magana ba sam, nakuma gaisheta taƙi amsamin. Jin ta fita da gudu tana kuka ya janye kansa da ƙyar yana jan tsaki da harar ƙofar. Kallonsa ya maido gareni yana hararata, hakan ya sakani sakin murmushi dan harga ALLAH dariya ya bani, to ni miye laifina kuma?.
      Kaina ya dunguremin da faɗin, “Idan kika cigaba da wannan noƙe-noƙen da sanyi saita cigaba da raina miki ai, ki kwana da shirin cewar ke matar Jay ce a station ɗin nan yanzun ba budurwarsa ba”. Ya ƙare maganar a hankali cikin kunnene kamar mai raɗa. Lumshe idanuna nayi ina murmushi, bance komaiba na ɗauka jikkata nasa a kafaɗa sannan na kallesa, shima kallona yake, murmushi na sake sakar masa da ɗaga masa yatsun hannuna biyu alamar bye-bye. Kafin ya samu damar cewa wani abu harna fice abina daga office ɗin.
          A jikin ƙarfen lifter na iske Rose tsaye sai cika take da batsewa, kallo ɗaya nai mata na ɗauke kaina, “K!!” ta faɗa a daƙile, banza nai mata tamkar banjiba na haye lifter ɗin abuna, wani tsalle tayi zata cakumoni naji muryarsa a bazata kanmu, “Koda kuskure karki sake wlhy hannunki ya taɓamin mata”. Ya faɗa a kausashe. Murmushi nayi da ɗage masa gira na ɗauke kaina, banajin amsar da take bashi dan nayi nisa da su, ina sauka kuma na sake ɗaga masa yatsun hannuna, shima ɗagomin yay, nai gaba abina na barsu bansan yaya suka kwashe ba.

Turƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...

        Bily na ɓacema ganinsa ya juya office batare da ya sake ko kallon inda rose take ba, ta cika tayi fam da baƙin ciki tamkar zatai bindiga a wajen. Ganin zai shige sai tabi bayansa a guje. Tana shiga office ɗin yana zama a kujerarsa, tsabar wulaƙanci sai yay kamar baisan ta shigo ba ya fara ƙoƙarin haɗa Computer ɗin saman table ɗinsa.
     Kuka maicin rai Rose ta fashe da shi tana dafe tebirin da hannu biyu, “Boss! Ni zaka wulaƙanta akan yarinyar da tazo station ɗin nan jiya-jiya? Ni zakaci amana ka yaudara saboda waccan ƴar tatsitsiyar yarinyar da bata wuce ɗiyar cikinka ba?, ko kunya bakaji kake iya nuna ƙaramar yarinya matsayin matarka wai?”.
          Jawaad ya ɗan lumshe ido yana buɗewa akan Computer ɗin da ya kunna, jikkarsa da bily ta ajiye masa ya ɗauka ya buɗe batare da yama rose ko kallo ɗaya bama balle tai tunanin samun amsa.
       Rose dake binsa da kallo ta sake fashewa da kuka tana faɗin, “Yanzu nan boss ina maka magana kana sakemin wani wulaƙancin?”. Sake yimata banza yay yama fara aikin gabansa. A wannan yanayin su Jabeer suka shigo office ɗin dan sunyi knocking har kusan uku yanaji ya share, shigowar tasuma baisa ya ɗago ya kallesu ɗin ba, su dai suka zauna a

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

1 year ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment