Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dasu Hafiz, Jabeer, Aliyu, sai Bilkisu. Sojojin da sukai musu rakkiya da Baba ƙaura sun wuce tun bayan da aka dawo daga binnesa. Rose ma lokacin da su Sir Ahmad zasu tafi dasu Alhaji babba bayan sallar la'asar Jay yace ta bisu. Bilkisu kuwa tana ciki tare da matar Gimba, batasan yaya akai sukasan ita matar Jawaad baceba, sai kawai ganitai anata nunata da faɗin itace matar ogan marigayi Gimba. Haka zasuyita jera mata addu'a da yabon halin Jawaad bisa ɗawainiya da taimakon da ƙauyen yake samu daga Jawaad ɗin ta dalilin gimba. Haka sukaita mata komai a girmame tamkar tafi kowa. Ita harma kunya ta komaji akan yanda suke matan.

         Wajen ƙarfe shida saƙo ya iso mata akan ta fito inji boss zasu wuce. Haka ta tashi ta kimtsa jiki a saɓule dan ta amshi hijjab ɗin matar gimba ta saka tun ɗazun saɓanin da da take da baby hijjab kawai. Sunata mata godiya da addu'a, ƙannensa suka rakota har waje inda motar da zasu tafi take.
       Sau ɗaya na kalli Boss na ɗauke idanuna saboda wani irin tausayi yake bani, na ƙaraso inda yake tsaye na gaishesu tare da sake musu gaisuwa, murya cike da damuwa ya amsa mani yana min nuni dana shiga motar daya buɗemin. Ni da shi da Jabeer ne a baya, ina jikin ƙofa yana tsakkiya Jabeer kuma a ƙarshe, sai Aliyu da zai ja motar Hafiz na gefensa. Haka muka wuce sunata mana addu'oin sauka gida lafiya.
            Sosai Aliyu ke sharara gudu kasancewar garin yay wani irin ɗaurewar hadarin farkon damina mai cike da iska a ciki, babu mai magana a motar sai zancen zuci, cikin awa ɗaya da mintunan da bazasu gaza ashirin da bakwaiba  muka iso cikin gari, zuwa lokacin garin ya sake yin duhu, gana hadari gana magriba, anata salloli a masallatai. Nayi zaton masarauta zasu kaini, sai naga an nufi gidansu Boss, koda mukazo gate sai yace basai Aliyu ya shiga da motarba bara mu sauka anan su wuce kar hadarinan ya riskesu..................✍


(Dolene koda zai halaka da izinin ALLAH sai ya gano suwaye suka kashe ɗan fir'auna, miyasa suka kasheshi?, minene a binne da rayuwarsa da ɗan-fir'auna yaso sanar masa, yanaji a jikinsa kisan ɗan fir'auna nada nasaba da abinda ya shafesa, minene shi? Wannan ne bai saniba.)
dolene jiya kushiga ruɗani akan mutuwar ɗan fir'auna bayan farkon page na nuna bai mutuba, nima sai a Comments ɗinku na fahimci kuskuren danayi na koma na duba page ɗin, wlhy hankalina sam bai kaiba ko'a wajen editing, rayuwace abubuwa sunma ƙwaƙwale yawa, kana gabas tunaninka na yamma, amin afuwa ɗan fir'auna bai mutuba🤦🏻. anahin abinda naso sakawa a

wajen shine (Dolene koda zai halaka da izinin ALLAH sai ya gano suwaye suka so kashe ɗan fir'auna, miyasa sukaso kasheshi?, minene a binne da rayuwarsa da ɗan-fir'auna yaso sanar masa, yanaji a jikinsa masu son kisan ɗan fir'auna nada nasaba da abinda ya shafesa, minene shi? Wannan ne bai saniba).🤗🙏🏻





ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[12/18/2020, 3:57 PM] HASNA✍🏻: +234 909 304 4460:
Page 31

...............“Muje”. Ya faɗa a hankali. Babu shiri nai azamar ɗago idanuna na kallesa, duk da ni yake kallo ban janyeba, cikin harɗewar harshe nace, “Anan zan... zan kwana?”. Tamkar baiji abinda naceba ya ɗauke kansa, dubansa yakai ga sararin samaniya daketa sake caƙuɗewa da duhu, batare da yace min uffanba ya raɓani ya nufi gate. Hawayen da nake maƙalewa suka silalomin a kumatu, a fili nace, ‘Dan ALLAH kar kaimin haka nidai’. Kamar yasan mi nake faɗe ya juyo yayinda ya buɗe ƙofar gate ɗin zai shige, “Karki bari na dawo na sameki a nan gurin”. Yafaɗa yana nunoni da ɗanyatsa alamar gargaɗi. Hannu nasa na share hawayen fuskar tawa kafin na taka nima zuwa gate ɗin. Maigadine kawai ke bin jam'i a bakin gate ɗin da yake anaji daga cikin gida. Ganin yayi tsaye yana kallon maigadin ne yasa nima naja na tsaya, sai da aka sallame sallar da dama zaman tahiyar ƙarshe suke. Kamar jira, ana yin sallama maigadi na miƙewa ya nufosa. Fuska a haɗe Jay ke kallon maigadi, baiko amsa gaisuwar da yake masaba da sannu dazuwa yace, “Ka bautama UBANGIJI tamkar kana ganinsa, dan idan kai baka ganinsa shi yana ganinka, MANZON ALLAH ya horemu da zuwa masallaci muyi sallah cikin jam'i, miyasa kai kafi zaɓar yinta kai kaɗai a cikin gida? Shin tsaron gate dan kar wani ya shigo yafi maka muhimmanci akan zuwa ka samo cikakkiyar ladar da mahaliccinka kaɗai ke badata? Daga yau ina mai baka shawara a kowanne lokacin salla ka kulle gate ɗin nan idan yazama dole saika zama mai tsaron mutanen cikin gidan kaje kai sallah cikin jam'i”. Kan maigadi a ƙasa yace, “Nagode sosai Alhaji, ALLAH ya saka da alkairi ya kareka kaima, ya ƙarin haƙuri?”. Cikin lumshe ido Jay yace, “Alhmdllh, abokinku ya tafi ya barmu”. Hawayene suka ziraro a fuskar maigadi, hakan yasa Jay yin gaba shima yana haɗiye abinda ya tokare maƙoshinsa.
         Jiki a saɓule nabi bayansa mukabar maigadi na kuka, sai naji nima hawayen nawa na sake gangarowa, dukda bawani sanin gimba nai sosai ba mutuwarsa ta taɓani ainun, mutum mai fara'a dason mutane. 
       Yana gama buɗe ƙofar da keys ɗin daya ciro a aljihu iskar na tasowa, hakan yasa muka shige da sauri saboda irin mai ƙasarnan ce sosai, da sauri na maida ƙofar na rufe na jingina jikinta ina sauke numfashi da share fuskata da hijjab ɗin gudun kar wadda ta hau ta shigarmin ido.
     Boss kam ya kunna fitilar falon saboda an kunna Gen..., a take haske ya gauraye ko ina, baice dani komaiba ya nufi sama abinsa. Tafiyarsa kawai zaka kalla zaka fuskanci yana cikin damuwa, dan a sanyaye yakeyinta. da kallo na bisa har saida ya ɓacemin, na sauke ajiyar zuciya ina lumshe idanuna, a ƙasan raina addu'a nake ALLAH yasa idan iskarnan ta lafa yace zai maidani Masarauta.
            Tunda ya shiga bedroom ɗin sai ya shiga yatsina fuska, shaf yama manta ko gadonsa bai samu arziƙin gyaraba yau, duk yanda yake jinsa a matuƙar gajiye haka ya daure ya shiga kakkaɓe gadon, ya gyarashi tsaf kamar ba yanzu za'a kwanta a kansaba, fitowa yay ɗaukar tsintsiya, duk da sarai yaga Bilkisu dake tsaye jikin ƙofa har yanzu yay tamkar bai gantaba yaje ya ɗakko kwandon da kayan sharan ke ciki yazo ya sake hayewa sama.

          Da kallo na bisa, haka kawai sai naga kamar bai daceba, dan da alama shara zaiyi da kansa, bayansa nabi jikina duk a saɓule, ga kaina namin wani irin ciwo ƙasa-ƙasa, ga yunwa dan rabona da abincin kirki tun breakfast ɗin safe, a garinsu marigayi fura kawai nasha rabin kofi itama sai da aka takuramin. Duk da sallamar da nayi bai ɗago daga abinda yakeba, nasan salon amsa sallamarsa a ciki-cikine hakan yasan ban damuba dan nasan dai ya amsani, nace, “Bara in share”. Kamar bazai kulani ba, sai kuma ya miƙamin tsintsiyar ya fice.
       Ajiyar zuciya na sauke na cigaba da sharan a sake ganin ya fita saini kaɗai. Tsaf na kammala sannan na nufi toilet, shima dai yana buƙatar wankin dukda bawani datti yayba na tashin hankali, tsaf na gyarashi cike da ƙarfin hali. Ina fitowa daga bayin shima yana shigowa ɗakin, saurin ɗauke kaina nayi daga garesa saboda ganinsa a tuɓe babu riga sai dogon wando kawai da farar singlet yana waya, ya zauna a bakin gado

n yana cigaba da wayarsa, kusan mintuna biyu ya juyo inda nake tsaye, yatsunsa biyu ya murza sukai ƙara, hakan yasa na ɗago kaina garesa, alamar nazo yaymin. Ahankali na taka zuwa garesa, ya miƙamin wayar batare da yace komaiba ya bar wajen. Duk da bansan ko waneneba haka nai sallama, muryar Ummah naji ta amsamin, hakan yasa na gaisheta cike da girmamawa, itama daga can da kulawa ta amsamin tare da min ta'aziyya. Nai mata godiya Nabeelah ma ta amsa muka gaisa, sai aunty Batool itama, daga nan mukai sallama. Wayar na ajiye masa bakin gado na fita falo, Zama nai a kujera ina jiran ya fito naji hanlin da nake ciki, harga ALLAH bana fatan kwana a gidannan. Nai zurfi a tunani da jiran fitowarsa kira ya shigo wayata, gyara zama nai na cirota a aljihu, Amaturrahman ce, dan haka na ɗaga muka gaisa, daga can tace, “Mun jiki shirune, ca muke tun biyar zaki dawo?”. Ɗan murmushin ƙarfin hali nayi, kafin nai mata bayanin yanda zata iya fahimta, nakuma nuna mata cewar bamu dawoba muna ƙauyen su gimban sai dai gamu nan a hanyar dawowa”  addu'ar isowa lafiya tai mana kafin mu yanke wayar. Na faɗama Amaturrahman hakane da tunanin idan boss ya fito zaiji tausayina ya maidani can a daren nan.

      Jawaad daya samu yay wanka da ruwa mai ɗumi sosai sai yaɗanji daɗi da sauƙin nauyin jikinsa sai dai na zuciya, yay alwala ya fito, ƴan dube-dube ya hauyi sai dai babu ko alamarta a ɗakin, guntun tsaki yaja yana lumshe idanunsa, dan shi kaɗai yasan ya yakeji, ga yunwa ga gajiya ga damuwa, dan shi babuma abinda ya sakama cikin nasa bayan coffee da yasha a office sai ruwa da yayta sha a garin su Gimba. ita kanta tausayinta yakeji gashi bawani ƙarfine da itaba ta tashi daga ciwo shekaranjiya jiya. Wadrobe ɗinsa ya buɗe ya ɗauki jallabiya fara tas ya saka mata turare sannan yasa a jiki, harya shinfiɗa abin salla sai kuma ya kalli ƙofa, koya kirata bazai yuwu tajiba saboda iskar da ake a waje abun babu sauƙi, tamƙar zata ɗauke rufin kwano, danma duk Windows ɗin sashen a rufe suke shiyyasa sukejinta da sauƙi su.
       “Ki taso kiyi wanka”. Ya faɗa kawai daga ƙofar ɗaki ya juya abinsa dan yasan zata iya jinsa daga inda take. Ba ƙaramin wintsilawa kayan cikina sukaiba lokacin da furucinsa ya isomin cikin dodon kunne, sai dai koda na ɗago tuni ya juya sai ƙamshinsa daya barmin. Rasama wane tunani zanyi nai, mi yake nufi da nazo nai wanka? ‘A toilet ɗinsa?’ na faɗa a fili kamar zanyi kuka. saukar ruwan sama babu zato ya sakani miƙewa zumbur dan naji tsoro wlhy, gashi da ƙarfi ya sauka dukda p.o.p hakan bai hanani jin ƙararsaba akan rufin, to nidai dama can akwai tsoro idan ana ruwa, nafi buƙatar naga mutane a kusa dani hankalina yafi kwanciya, balle wannan da ruwan ya kasance kaso biyu a cikin uku iskace ma, wani wal garin yayi na walƙiya, labulen Window'n da ba'a sakiba sai glass ɗin kawai aka rufe yasa naga tamkar inuwar mutum a wajen, jikina har rawa yake na tashi na nufi ɗakin boss da ɗan gudu-gudu sauri-sauri har ina neman faɗuwa, wayatama anan na barta saman kujera. Na maida ƙofar da ƙarfi na rufe ina rumtse idanu da sakin nishi mai ƙarfi, har yanzu ƙirjina sai wani ɓal-ɓal yake badawa.
        Shidai Jay salla yake, amm duk da haka ya jiyo yanda Bilkisu ta rufe ƙofa da ƙarfi, koda ya idar bai juyi ya kalleta ba, ya miƙe domin kawo isha'i da yaga lokacinta yayi. “Sallarce bazakiyi ba komi kike nufi?”. Da sauri na buɗe ido ina kallon bayansa daya juyamin. Murya a raunane nace, “Ai idan naje gida duk zanyi fa?”. Cikin takaici Jay yace, “Ainan ɗin jejine ko? Karki bari na ɓata miki rai a darenan Miemaa, ƙyaƙy! tom”. Daga haka ya kabbara sallarsa.
         Jin yanda yay maganar a kausashe na tabbar zai aikata duk abinda ya faɗa ɗin, haka na nufi toilet ɗin ina ƙunƙuni a raina, wannan wane irin abune haka, miyasa tunda anga hadarin baza'a kaini inda nakeba sai a wuto dani nan, nidai komai dare saina bar gidanan ehe. Da wannan ƙunƙunan a cikin rai na shiga bayin, ruwa mai zafi na haɗa dan jikina bala'in ciwo yakemin sosai, banga wani soso ba bayan nasa a bayin, haka na ɗauka nai wankan da shi ina maijin daɗin ruwan, sai da na kammala nai alwala sai kuma

naji ƙyanƙyamin maida kayan dana cire, to amma idan ba su ɗinba mizan saka? Nida bazan fita da tawul ba gaskiya, to idanma na ɗaura tawul inada kayan dazan saka ɗinne a ɗakin.........?
            Wata irin ƙara na saki jikina na masifar rawa saboda ɗaga kan da zanyi  idanuna sukai tozali da wata iriyar mummunar halitta baƙa ƙirin da jajayen idanu, jikinta dai zam maciji, amma kan bana maciji baneba...
        A rikice Jawaad dake addu'a ya miƙe saboda jiyo ƙarar Bilkisu dake bayi, ALLAH ya sosa bata kulle ƙofarba, ya tura da ƙarfi babu ko neman izini ya shige, dai-dai bily tai baya zata faɗi saboda numfashinta daya ɗauke dan firgici, tallafota yay ta faɗo jikinsa, yayinda idanunsa kebin halittar dake silalawa ta Window zata fice da kallo. Sai da ta gama ficewa tsaf sannan ya maido kallonsa kan Bilkisu, saurin kauda idanunsa yayi dan babu komai a jikinta, ya jawo tawul dake ciƙin ƴar drawern glass na toilet ɗin  ya yafa mata sanann ya ɗaukata cak batare da yace komaiba ya fita da ita. Saman gadonsa ya shimfiɗeta, dukda ya yafa mata tawul sai da ya sake jan bargo ya rufa mata har saman ƙirjinta, tsaye yay yana ƙarema fuskarta kallo tamkar maison gano amsar tambayoyin zuciyarsa akan fuskartata, tsahon mintuna kusan goma kafin yabar wajen ya koma toilet ɗin yana dube-dube, babu komai kam, sannan a mamakinsa Windown kaɗan ya ɗaga, hanyar da yabi baikai faɗin da halittarnan zata iya shiga da fitaba, ‘mikenan?’ ya tambayi kansa, dagacan gefen zuciyarsa ta bashi amsa da (Aljanu). “Aljanu!” ya maimaita akan laɓɓansa har sau biyu. “Hummm!” ya sake faɗa a fili yana ɗibar ruwa kaɗan a ƴar roba dake toilet ɗin ya fita. Iskar hadarin ta fara lafawa, sai ruwa da ake yaf-yaf na farkon damuna, dan daya fara da ƙarfi sai kuma ya koma ɗaf, sai kuma ɗan yaf-yaf, sai dai walƙiya da aketa faman yi harda cida mai ƙarfi lokaci-lokaci. Zama yay a gefen gadon kusa da cikin bilkisu tare da ajiye robar ruwan a ƙasa batare da ya shafa mataba ya faɗa tunani. Abinda ya faru a jeji ɗazun, kalaman baba ƙaura, kalaman abokan ɗan fir'auna, ainahin abinda Gimba ya gani har yazo ya faɗa masa a randa aka shirya juya ɗaurin auren Qaseem da bilkisu zuwa Azeema da Qaseem bilkisu da ɗan fir'auna, Accident ɗin ɗan-fir'auna, mafarkinsa, sai abinda ya gani yanzu wanda ya firgita bily. Ya shiga saƙa waɗanan abubuwan dake gogayya da juna daki-daki a muhalli guda. Yay murmushi mai ciwo saboda amsar data zo masa a zuciya lokaci ɗaya. Cikin zafin nama ya miƙe, Ranƙwafawa yay kan bilkisu ya shafa mata ruwan daya dumtso a hannu, a take ta kawo numfashi mai ƙarfi.
       A hankali na buɗe idanuna, sai kawai a bazata naci karo da fuskar boss dake ranƙwafe kaina daf da tawa, dan har inajin saukar numfashinsa akan tawa fuskar, gabana ya faɗi, nai saurin fara waige-waige danson kauda fuskata. Saukar tattausan tafin hannunsa naji saman fuskar ya sake juyo dani garesa. Duk yanda naso janye idanuna da suka shige cikin nasa na kasa, kallon ido cikin ido mukema juna karon farko, wani irin abu mai wuyar fassara ke fitowa daga ƙwayoyin idanunsa masu girma da sirkin jaa suna shiga cikin nawa, atake naji tsigar jikina na tashi, ƙofofin gashina na buɗewa gashin na miƙewa, jinina dukya tsinke lokaci guda yana wani irin gudu a cikin jijiyoyi, sai kawai na saki kuka a hankali.
      Jawaad da har yanzu idanunsa ke kafe a cikin na bilkisu yaɗan murza babban yatsansa daga jikin hancinta har zuwa ƙasan idonta ya kwashe hawayen dake fitowar ya maida yatsan baya jikin ƴan uwansa, dan har yanzun tafin hannunsa na tallafe da kuncinta na haggu. Ahankali ya furta, “Tabbas ƙaddararki da tawa a haɗe take Miemaa, zan bada ƙarfina da lokacina wajen binciko abinda ya ƙullemu ƙarƙashin inuwa ɗaya insha ALLAH”. Yana gama faɗar hakan ya saka ɗayan hannunma a gefen kumatuna na haggu ya ɗauke duk hawayen dake zuba a idanuna guda biyu, sannan yaja baya tare da miƙewa tsaye yabar wajen.
       Lumshe idanuna nai a hankali kalamansa namin kaikawo tsakanin zuciya da ƙwaƙwalwa, a hankali nima kalaman baba ƙaura da abinda ya faru yau a jejin suka shiga dawomin daki-daki. Jin an ruƙo hannuna nai saurin buɗe ida

nuna, boss ne riƙe da riga a hannu, batare da yayimin maganaba ya ɗaga kaina a hankali ya ziramin wuyan, sannan ya kamo hannuna ya taimakamin na saka, ɗayanma haka. Juyawa yay yana faɗin, “Ki tashi kiyi alwala ki sauke nauyin sallolin dake kanki”. Daga haka ya fice a ɗakin. Dukda tsoron dake a raina haka na miƙe dan nima rashin yin sallar cizon raina yake sosai, sauka nai daga gadon, rigarsa ce t-shirt mai guntun hannu, dukda a ido bata da girma sai gashi takai min har kusan quarter ɗin cinyata, na ɗauki wandon dana gani gefena, a raina nake raya ‘Ni balki, nice kuma da saka kayan boss yau?’.  Sauƙina wandon irin mai taushin nanne da roba acan ƙasansa, sannan a sama ma  robace harda zariya. zariyar naa ɗaure sannan a tsoro-tsoro na nufi bayin ina addu'a a cikin raina, saida na leƙa na tabbatar babu komai sannan na shiga batare dana rufeba na ɗauro alwalar na fito. Nayi namakin ganin hijjab a ajiye, da alama tun ɗazunma ya ajiyeshi, haka na ɗauka na saka na fara sallolin da suka shigemin.

      Jawaad kam koda ya fita sashen Uncle Nasir ya nufa, a falo ya iske yaran harda mamansu suna kallo, duk gaidashi suka shigayi da masa ta'aziyyar Gimba, ya gaisa da Ammi ma, sannan ya zubama Ameera harara da faɗin, “Wannan banzar shigan fa? Ko ɗan kwali babu kanki”. Cike da taoro Ameera ta miƙe tana faɗin, “Dan ALLAH kayi haƙuri Yah Jay”. Bai sake tanka mataba, amma kallon da yake mata ya isheta shiga uku, da gudu tai ɗakinsu domin suturta jikinta, dan dama ya hanasu shigar banza tun yana zaune a sashen (karku manta bayan rasuwar mama Maryam Uncle Nasir shine ya cigaba da riƙon Jay har yay aure). Baya musu wasa idan yaga kan mutum yana rawa, shiyyasa suke masifar shakkarsa, gashi dama baya shiga shirgin ƴammatan gidan saboda gudun raini, samarinma kansu ba kowa ke ganin fuska daga garesa ba sai sa'anninsa dana sama dashi, suma ɗin bai maida kansa sakarai a garesuba ana dai mutunta juna. Raihana da itama ta nutsu waje guda ya kalla, “Tashi ki samo min abincin mutum biyu”. Tashi tai da sauri ta nufi kitchen, itadai Ammi batace komaiba, dan macece mai mutunci da sanin ya kamata, yanda Jawaad ke tsaye kan ƴaƴansu ita daɗi yake mata, dan shakkarsa na hanasu aikata abubuwa masu yawan gaske, har ranta kuma ƙaunar Jay take dan ita dai halayyarsa birgeta yake sosai.
    Suna ɗan taɓa hira da Ammi akan rasuwar gimba Raihana ta fito ɗauke da ƙaramin basket na kaba mai ƙyau a hannu, tace, “Yah Jay gashi, ko nakai can?”. Batare da ya bata amsaba ya miƙa mata hannu alamar ta bashi, kawo masa tayi tana godema ALLAH a ranta, dan dama bason kaiwar takeba kar taje can ya sakata wani aikin kuma, dan hankalinta nakan film ɗin da suke kallo. Yana amsa ya miƙe yayma Ammi sallama ya fita.

        Bayan na kammala sallolin sai kawai na ɗauki Alƙur'anin dana gani a ɗakin na shiga karatu cikin sanyin murya da rauni, dan inayi hawaye na zirara tamkar an buɗe fanfo.
         Wani irin sanyi Jay yaji a ransa, ya ƙaraso cikin ɗakin sautin muryar bilkisu na ratsa zuciyarsa, sai yaji wata nutsuwa mai daɗi na saukar masa har cikin gaɓɓai. Bai dakatar da itaba ya ajiye basket ɗin ya fita, mintuna kaɗan ya dawo ɗauke da kifuna biyu sunata turiri alamar tea ya haɗo musu. Motsinsa ya sani rufe alkur'anin saboda nakai inda zan iya tsayawa, sonake na roƙesa ya maidani masarauta tunda har yanzu da sauran dare, ƙarfe goma da mintuna Uku.
       Ido muka haɗa dan shima kallona yake, na maida kaina ƙasa ina juya abinda zan faɗaɗin da lanƙwasa yatsun hannuna madaidaita, “Dan ALLAH Yayah dare baiyiba, tunda ruwan ya ɗauke ka kaini can koka kaini gidan Dad na kwana”. Jin shiru bai tanka minba na saci kallonsa, shayinsa ma yake sha tamkar bai jiniba, kuma tsabar wulaƙanci kallona yakeyi. Kusan mintuna uku yace, “Taso kici abinci”.
        ‘Yah ALLAH, wai da wane yare zan fahimtar dashi ya fahimtane?’. Na faɗa a zuciya idanuna na cika da ƙwalla, Ban karaya ba dai, duk dan ya barni nafi nabi umarninsa, babu musu na miƙe zuwa garesa, batare dana cire hijjab ɗinba nai yunƙurin zama ƙasa. Gadon ya nunamin da hannu yana sake tamke fuska. Yanzunma dai Umarni nabi na zauna dukda ba ha

ka nasoba, ya miƙomin kofin shayi kawai. Ƙananun kofunane dan basu wuci rabin kofi ba, tea ɗin ma kuma bai cikaba, cikin dauriya da fatan maidani masarauta na hau sha, sosai yayi daɗi abin mamaki, bansan na shanyeba balle dama yunwa nakeji.
         Kofin da yasha nashi tea ɗin ya ajiye, ya buɗe kular dake cikin basket ɗin ya ɗiba abinci dai-dai misali, nidai kallonsa nake ƙasa-ƙasa, tashi yay ɗauke da filet ɗin a hannu ya koma saman kujerar ɗakin, “Ga abinci nan” yay maganar batare da ya kalleniba. Duk da inajin kunyarsa yunwa nakeji sosai, idanma nace bazanciba zan cutar da kaina matuƙa. Kofin na ajiye na ɗiba dai-dai misali. Koda wasa ban ɗago kainaba harna kammala, na miƙe na tattare har filet ɗin daya gama shima na fita dasu duk da a tsorace nake.
           Jay ya bita da kallo harta fice, a ransa yake faɗin, ‘Ahaka sai ka ganta kamar wata saliha, sai dai shegen taurin kaine da ita da tsoro ko farar kura ta shafa mata lafiya’. (Jay a rage sa ido dai. Lol😂).

          Babu jimawa na dawo ɗakin, zuciyata na sake tunzurani akan na sake roƙonsa dai. Yana zaune inda na barsa ya baza takardu a table ɗin gaban kujerar yanata rubutu, na ƙaraso bakina ɗauke da addu'ar neman nasara a kansa, jikin hannun kujerar na duƙa ina mai narke murya dan yaji tausayina. “Amaturrahman ta kirani akan sunga ban dawoba, ni kuma na sanar mata muna hanyar dawowa, kuma zan koma masarauta, nasan sunacan suna jirana”. Aikin gabansa kawai yake kamar bai jiniba, na kuma raunana murya da faɗin, “Boss Please, idan na kwana a gidannan da safe wace amsa zanba mutanen gidan dasu Amaturrahman ɗin?”.
            Karon farko Jawaad ya saki lallausan murmushin da har haƙoransa suka bayyana, dukda yana cikin halin damuwa da alhinin rasuwar gimba sai ta bashi dariya, fuskarsa ɗauke da murmushin har yanzun ya ɗago yana kallonta.
        Wani irin daɗi naji ganin yana murmushi, a tunanina naci nasara, sai gani nai ya ɗauke kansa ya maida ga abinda yakeyi batare da yace komaiba, “In faɗa miki amsar da zaki basu idan sun ganki kin kwana anan da safe?”. Ya faɗa tamkar bashine yay maganarba. Ganin bance komaiba ya ɗago yana kallona, “Ko bakiso na riƙe kayata? Dan ƙyautace, idan ta ƙara wasu mintuna zata zama ta kuɗi”. Baki na tura masa dan haushi, nace, “Inaso”.
        Jay dake kallonta har yanzu yakai yatsansa dab da bakinta ya ɗallah yana faɗin, “K kullum bazaki daina bani ciwon kaiba yarinyarnan?”.
    Saurin ɗaura hannuna nai saman bakina dan zafi, idanuna har sun cika da ƙwalla, saurin rufesu nayi dan karsu zubo, boss mugune yasin, ina tausayinsa ashe bama abin tausayi baneba........
      Ture takardun gabansa yay ya miƙe, a gaban bily dake durƙushe jikin kujerar da yake zaune yaje yay wani ɗan dirƙuso da kowa yasan maza da iya salonsa, da sauri-sauri zuciyarsa ke gudu, lumsassun idanunsa nakan fuskarta datai fayau saboda ramar da taɗanyi.
       Saukar numfashinsa a saman

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

1 year ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment