Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

    Kasancewar su Alhaji baba a hanya suke lokacin da Jay ya kira sai gasu babu jimawa sun iso, gais

uwa sukai da dattijon da babu wanda yasan daga ina yake sai Alhaji baba, da ido yayma Jawaad nuni dasu jirashi. Jawaad ya ɗaga kansa alamar amsawa. Shikuma yabi bayansu Uncle Sulaiman ciki domin duba Bilkisu.
     Dole su Ummah suka fito waje suka bama su Alhaji baba ɗakin dan yamusu kaɗan, Safah da Marwah kaɗai aka bari tare da Bilkisu daketa faman gaishesu kanta a duƙe, dan bata yarda ta kalli kowaba sai da Dad yake matsawa kusa da ita ya ɗago fuskarta yana duba kumburin daya fara sauka da jera mata kalamun ban haƙuri tamkar zai ari baki sannan ne ta ɗago tana ɗan murmushi. “Dan ALLAH Dad kabar damuwa, wlhy ni kawai na ɗauki hakan matsayin ƙaddara da kuskure kawai, kuma nama yafe musu”. Babu wanda bily bata birgeba da kalamanta, wata irin faɗuwar gabace ta riski Alhaji baba lokacin da yay tozali da fuskar Bilkisu, ya kafeta da ido ko ƙyaftawa bayayi, dukda kuwa a kumbure take kaɗan ta gefen haggu saboda duka hakan bai hanashi hango wani abu tattare da itaba. Sam yama daina fahimtar sauran maganar data biyo baya tsakanin Bily dasu Dad, haka kawai ya tafi wani bahagon tunani da shi kansa yasan akwai kuskure a cikinsa. Saurin ture abin yay a ransa suka fito, saida ya kuma waiwayawa ya kalli Bilkisu da batasan yanayiba sannan ya fice.
         Dad wajen likita ya nufa dan yaji yaya ake ciki? Su Uncle Sulaiman kuma suka fita domin tafiya gida, a wajen su Jawaad suka bar Alhaji baba shima.
       Takardar Jay ya bama Alhaji baba, bayan ya karanta ya kalli dattijon, “Ƙanina zance ko ɗana yaushene akesan ganin nasa?”. Dattijo yay murmuahi da faɗin, “Baba yanzuma zamu iya tafiya, dan zanbar yaran anan muje mu dawo”. Kallon Jay baba yayi, yace, “Shikenan kabisa Muhammad”. Jawaad ya kaɗa kansa da faɗin, “To baba, amma zan koma gida na canja kaya tukunna”. Alhaji baba yace, “Ato ai maganinku kenan, ƙiri-ƙiri kun ajiye suturar mutunci kun biyema ta yahudu, saboda irin haka muke muku faɗa akan kuna tunawa da naku suturar kuma, dan sune kayan da zakuje gaban ko wanene batare da kunji nauyin hakanba”. Shidai Jawaad baice komaiba, sai dattijon masarautane keta murmushi da faɗin, “Wannan gaskiyane baba”.

★★★★★★

               Sosai nake a cikin ruɗani da neman mai min ƙarin bayani akan wannan rikiɗaɗɗen al'amari, ina Yah Qaseem ɗina ya shiga da har ake jinginani matsayin matar boss?, shin wai mike faruwa hakane ni bilkisu? Mizaisa aitamin magana a curkuɗe?, a rasa maimin bayanin dazan fahimta. Koda su Oga Hafiz ma sukazo dubani harda matansu, matan sai faman yimin addu'ar fatan alkairi suke da faɗin, wai boss ya dace da matar da suka dace da juna, hakama da Ummie ta dawo tare da ƴan gidansu Momynta da Dady sunata min addu'ar ALLAH yasa hakan shine mafi alkairi, musamman ma Daddyn Ummie danaga tsantsar farin cikin hakan a garesa har suka tafi. Amina ma da Yayansu sunzo sunyi nasu kalar farin cikin, hakama Ummah ƙarama da naji suna faɗi da yaranta da tazo, sai murna suke da kasancewata wai matar ɗan uwansu. ‘Oh ALLAH! wannn wane irin ruɗanine haka?; Ina ƴan gidanmu suke? Dad kawai na gani, amma ko Yah Qaseem ban ganiba, shin ina ya shigane??. Haka naita juya wannan tunanin a raina, yawan jama'a da keta shiga da fici ya hanani sakat ɗin dazan samu na tambaya. A gefe kuma inajin daɗin ganin nima ashe mai mutanece? Ashe inada gatan dazan kwanta ciwo har mutane irin haka suyita tururuwar dubani?. ban sake ganin boss ba har sai bayan sallar zuhur.

★★★★★★

 
              A ɓangaren Jawaad kam kamar yanda ya roƙa alfarma ga dattijo saida suka biya ta gida ya shiga ya sauya kayansa da ɗanyar shadda fara tas da tasha ɗinkin zamani, yaukam hardasu hularsa zannah ainahin nutsatstsiyar saƙar barnawa ta asali sai ƙyalli take, duk wanda ya gansa yaga sabon ango dukda bai shiga daga cikiba😂, shi kansa dattijon tunda Jawaad yafito daga gate ɗin gidan kasa ɗauke ido yay daga kallonsa, a fili ya furta ‘Masha ALLAH ’. Drivern dake jan motarma bai iya ɗauke idanunsaba har Jawaad ya shigo.
                    Sun isa katafariyar masarauta mai daɗaɗɗen tarihi da gininta na ɗaya daga cikin manyan gine-ginen da ake lissafasu a sahun farko na yankin masarau

tun afirika baki ɗaya saboda ƙawatuwarsa da gini mai nagarta data samu, gashi a koda yaushe cikin sake fidda masa wasu tsare-tsaren akeyi masu matuƙar sake ƙawatata. Wannan shine zuwa na biyu da Jawaad yayi cikinta, dan sun taɓa zuwa gaisuwar salla wa sarki Sameer tare da tawagar Gwamna a shekaru uku kenan da suka shuɗe. Sai dai a wannan karon sosai yaga sabbin tsare-tsare da tarin cigaban da yafi na wancan lokacin, bayi sai zubewa suke suna gaisuwa a garesu saboda wanda suke tare, shi kansa Jawaad ɗin kallon wani jinin sarauta suke masa saboda kama yake dasu ta siffofi da dama.
       Jawaad mutumne shi mai nutsuwa da aji, sanan yanada tsari, bai damu da abinda babu ruwansaba komai ƙawarsa da abubuwan kallon cikinsa, wannan halin nasa na yima abu kallon ko in kula yasa sam bai zama ya rikice wajen kalle-jalleba a masarautar dukda ta cancanci a tsaya ƙare mata kallo harda son yin hotunama a cikinta. Tafiyarsa yake kai tsaye tamkar ko yaushe a kuma ko ina ya tainci kansa, bajinta, nutsuwa, da tarin ƙasaita kawai zaka hanga a takun nasa, waɗanda basu da fahimta akan halayyarsa harma zasu iya haɗawa da Izza da girman kai, sai dai kuma sam ba haka baneba, tun asali haka ALLAH yayisa tamkar wani jinin mulki wajen girmama nutsuwa a dukkanin al'amuransa koda akwai ruɗarwa a cikinsu kuwa.
           An saukesa a katafaren falo mai cike da abubuwan ƙawa da birgewa, cikin mintuna ƙalilan aka cika masa gabansa da kayan ciye-ciye da har yake tsogumi a ransa wai ‘Kamar wani mai cikin zani’ (😂kujifa daga abun arziƙi. Lol🤣)
           Bai taɓa komaiba bayan ruwa a kayan da aka jibge masa, dan shi ba ko ina yake sakin jiki yaci abuba (Yau naga mai irin halin babana a iya fulako😍, ALLAH ya gafarta maka baba😥🙏🏻). Cikin nutsuwa yake ɗanbin falon da kallo da jinjina daular dake ciki tamkar babu talaka mai buƙatar abinci da rigar sawa da kuɗin magani a duniya, yaɗan taɓe baki yana gyara zamansa, sam shi fariyya bata birgesa, dukda kasancewarsa mutum mai tarin dukiya bai taɓa sha'awar yin abinda ya fice hankaliba a hidimar rayuwarsa, dai-dai da motar hawansa guda biyuce kacal a duniya, hakama suturar sakawarsa akwai adadin da yake ajiyewa, ya gwammace duk sanda zai ɗinka wasu kayan ko ya saya to ya fidda tsoffin ya bada kafin ya ajiye wasu, baya sha'awar tsube sutura a drawer harya mance randa ya sake maimaita wata.........
       Tunaninsane ya katse saboda sallamar da akayi a ƙofar falon, ya amsa yana gyara zama da tsumewa cike da kame kai. Hadimai mata guda biyune suka shigo, cikin girmama suka gaidashi kafin su sanar masa zai iya tasowa gimbiya ta fito.
     Kansa kawai ya iya jinjina musu, ya miƙe tare da jefa wayarsa cikin aljihu yabi bayansu. Ƙaramin falone madaidaici, sai daifa ya haɗu harma ya gaji da haɗuwar, Hamshaƙiyar mace mai cike da tarin kamala da kwarjini da bazata gaza shekaru arba'in da biyar ba a duniya tana zaune, sai ƙamshi da walwali take cikin alƙyabbar da kallo ɗaya zakai mata kasan an sayeta da kuɗaɗe masu daraja. Gimbiya Munaya Awwal fharok kenan, sarauniyar gagara badau mai lokaci da amfani da damarta tana damawa yanda ya kamata, matar sarki Sameer saifudden Abubakar adalin sarki mai mulkin dake tafiya da koyarwar addinin islama da zamani, cikakken sarki mai iko da ƙasaita, adali mai tarin ilimin addini dana zamani, wanda yasha gwagwarmayar rayuwa tunkan rayuwar tagama sanin shiɗin wanene.
         Da hannu gimbiya munaya taima matashin saurayi Jawaad nuni da wajen zama, bata haifi kamarsaba, amma kuma ta girmesa a shekarun haihuwa. Cike da nutsuwarsa ya zauna, kafin ya risina cikin girmamawa ya shiga gaidata. Gimbiya munaya tai murmushi mai ƙayatarwa dan Jawaad ya birgeta ainun, daganinsa zakasan yajiƙu da tarbiyya tsaftatacciya. Cike da ƙasaita tace, “Kana lafiya?”.
       Jawaad ya amsa da “Alhmdllh ranki ya daɗe”. Murmushin ta sakeyi, kafin ta cigaba da faɗin, “Kana tare da Uwargidan Sakin gagara badau Sameer Saifudden, nasan kana cikin ɗunbin mamakin kiran gaggawa da nai maka wanda ni kaina bansan dalilin hakanba, kawai dai ina danganta lamarinne da tsantsar ƙaunar danaga gudan jinina tanama wadda banmm

a taɓa ganiba mai suna Bilkisu da a jiya nake samun labarin an ɗaura maka aure da ita, hakan kuma yazo da rikicin da ita Bilkisun ke buƙatar taimako”.
      Jin tayi shiru Jawaad ya jinjina mata kai, cike da girmamawa yace, “Hakane ranki ya daɗe”. “Idan ban shiga hurumin daba nawaba inasonjin wani abu koda zan iya bada gudunmawa ta, dan a yanda yarana suka bani labarin abinda ya faru da Bilkisu hakan ya matuƙar tsayamin a zuciya a daren jiya”.
       Murmushi Jawaad yayi, dan haka kawai yaji ƙaunar gimbiya munaya har cikin ransa, batare da tunanin komaiba ya buɗe mata cikinsa gameda abinda ya faru akan auren nashi da Bilkisu. Shiru gimbiya munaya tai tana nazarin maganganun nasa kafin ta sauke numfashi, cike da ƙasaitarta tace, “Jawaad!, a ɗan guntun hangena na fahimci akwai matsala babba dai dake a ƙasa wadda kaima kanka kakeson bincikowa? Hakan ya birgeni, dan inason jarumin namiji mara tsoro mai ƙwazo tamkar mai martaba na, zan baka gudunmawa akan dukkanin shirinka ɗari bisa ɗari, dan bansan mi UBANGIJI ke nufi da wannan haɗin namuba ta dalilin Safah da kullum bakinta bai gajiyawa da ambaton Aunty B”.
        “Godiya muke ranki ya daɗe da wannan karamci, ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani”. Murmushi gimbaya Munaya tai tana maijin daɗin karamarwar Jawaad a gareta, sannan ɗabi'unsa sunyi matuƙar birgeta, idan badan ya faɗaba babu yanda za'ai kai tunanin yafitone daga tsatson tsohon shugaban ƙasa Marigayi Abdul-aziz yusif tafida, adalin shugaba da su kansu masarautarsu tayi ƙyaƙyƙyawar alaƙa dashi a lokacin mulkinsa na shekara huɗu a gwamna ɗaya a shugaban ƙasa, a yanzu haka kuma dukkan kayan itatuwa da kaji dawasu abubuwan da suka shafi gona ana kawomusu shine daga gidan gonarsa......... Kauda tunanin nata tai Tace, “Shikenan Jawaad, yanzu mataki na farko da zamu farabi shine ina buƙatar Bilkisu ta dawo masarauta da zama, dan komawarta gidansu bazai haifar da ɗa mai idoba kodan dalilin ita tsohuwar matar taka da tsohon saurayinta da kuma mahaifiyarsu, zata zaunane na gajeran lokaci daganan zuwa bayan sallar kamar yanda kuka tsaida tarewarta, dan itama tana buƙatar ai mata auren gata tamkar kowane mace mai iyaye kodan hakan yazama izina ga masu irin halin Gwaggonka dake tunanin su kaɗaine a sama babu mai taddosu, inason susan babu wani bawa ƙasƙantacce sai wanda ya ƙasƙantar da kansa ga barin bautar ALLAH saboda son zuciya..............✍

Ina godiya gareku akan addu'oin da akaita zubami harda masu kira da masu turo saƙo, naji sauƙi Alhmdllh sai dai inajinran manyan ledojin kayan dubiya😆😋.


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
[12/11/2020, 3:18 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:
*_WATTPAD:_* _BilynAbdull_

*_TELEGRAM:_* https://t.me/joinchat/TIsXYRvhtri2kQ9E4x7w6g

Page 26


BARKA DA JUMA'A


..............Jawaad da yay ɗan jim fuskarsa ɗauke da murmushi yana juya maganar gimbiya ta ƙarshe a ransa, koba komai ya sakejin kimarta, domin ta nuna tanada ƙyaƙyƙyawan tsari da tausayi akan talakawa. yace, “Shikenan ranki ya daɗe, ke uwace, kinada damar yanke duk hukunci daya dace a kanmu koda babu saninmu, sai dai ina neman alfarmar zuwa na sanarma kakana da kuma ƙannen mahaifiyata, zuwa gobe insha ALLAH zan dawo na sanar miki yanda mukayi”.
            “Wannan tunanin naka shine ƙyaƙyƙyawan tunani da yakamata ya fito daga bakin jajirtaccen ɗa mai riƙo da tarbiyyar magabatansa, kaje ka sanar musu ɗin babu damuwa, sai dai zan baka shawarar koda likita yace zai sallami bilkisu kace ya jinkirta zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, dan nafison da an sallameta kawai nan za'a wuto da ita”.
        Kansa ya jinjina mata. Ta ɗauki ɗaya daga cikin wayoyinta masu azabar ƙyau ta miƙa masa, “Kasaka Number ka anan, saika ɗauki tawa yanda idan sun amince ɗin zakai kirana ka sanarmin basai kayi wahalar zuwa ka koma kawomin bilkisu ba kuma”.
     Tasowa jay yay ya amshi wayar, Number sa ta musamman da wanda ya yarda kawai kuma yakeda kusanci dashi matuƙa kawaine ke da ita ya saka mata, sanan yay kira yaga tata, saving yay mata da Jawaad A yusif ya maida mata yana godiya.

_______________________________

          Tare Jawaad suka dawo da dattijon nan dan zai juya dasu Amaturrahman masarauta.
         Shi kaɗai ya shigo ɗakin da sallama ciki-ciki kamar yanda ɗabi'arsa take ta rashin son hayaniya, babu kowa a ɗakin, Safah kaɗaice kwance tana barci a gadon da Bilkisu ke jiyya, mamaki ya kamashi da tunanin ina suke har ita Bilyn?. kafin yay yunƙurin yin wani abu aka buɗe ƙofar toilet, Bilkisu ce ta fito ɗaure da zani, ta yafa ƙaramin towel a kafaɗarta da alama wanka tayo saboda yanda ruwa ke jiƙe da fuskarta, duk tsefaffen gashinta ya kwanto goshinta da gefen kumatu.
       Wani faɗuwa gabana yayi dan banyi tunanin iske kowaba tunda su Nabeelah sunce zasuje sallah, Mama kuma tunda ta gasamin jiki ta fita akan zata ɗauraye kwankikan da akaci abinci, bawani ƙwarin jikin nakejiba dama, dan dukan da sukaimin yasa jikina yin tsami ko ina ciwo yakemin, wai danma Doctor ya bani maganin ciwon jiki nasha. Nakasa koda ɗaga ƙafata da sunan juyawa baya, sai kawai na duƙe a wajen inaji tamkar ƙasa ta tsage na shiga ciki dan matsananciyar kunyar data riskeni, nice yau tsaye gaban boss babu riga? Dagani sai zani da ƙaramin towel ɗin dana yafo a kafaɗa, kaina sanye da hular wanka, dukda nasan fuskata kawai zai iya gani da hannayena zuwa gwiwa, sai ƙafafuna suma iya rabin ƙwairi dan zanin ya sauka min ƙasa sosai duk da ɗaurin ƙirji nai dashi, hakan ba ƙaramin abun kunya bane a gareni.
          Ɗauke kai Jawaad yay daga kallon daya kafeta dashi yana mai lumshe idanu a hankali da furzar da sassanyar iska daga bakinsa, baice da ita komaiba ya juya ya fita zuciyarsa na gudu da sauri-sauri.
          Hawaye nake kashirɓan da bansan dalilinsuba sam, dukda naji ƙarar buɗe ƙofa da rufewa alamar ya fita na kasa miƙewa tsaye bare na tashi. “Bilkisu lafiya kuwa? Ko jiri kike ganine?”. Muryar mama ta dawo dani hankalina. Saurin ɗago kaina nai ina share hawayen da suka jiƙen fuska, ganin dagani sai ita a ɗakin yasani sauke numfashi ina mai ɗaga mata kai alamar juwarce. Kwanikan hannunta ta ajiye tazo ta taimakamin na tashi tsaye, da taimakonta muka ƙarisa bakin hadon dan a gaske yanzun saima nakejin tamkar juwarce tazomin, ita ta taimakamin na shirya, ina kammala shiryawa su Nabeelah da Amaturrahman da Marwah na shigowa. Sannu suka yimin kafin Amaturrahman ta shiga tada Safah tana faɗin Su zasu wuce gida, jinai kamar nace su zauna, amma banda wannan ikon, ga Safah ta sanya kukan shagwaɓa akan itafa anan zata zauna tare dani. Ina mamakin wannan irin ƙauna da Safah ke nunamin.
      Kafin kowa yace wani Abu boss ya shigo ɗakin da sallama. Nidai ƙasa nai da kaina ban yarda nako saci kallonsaba, tambayar da yakema Safah akan mitakema kuka kawai naji, Na

beelah ce ta bashi amsa da cewar tace bazata tafiba anan zata zauna wajena. Banji ya bata amsaba, sai saukar hannunsa naji akan nawa dake riƙe dana Safah, a take tsigar jikina ta tashi, gashi har yanzu akwai damshin ruwa jikina dama, ya cire hannunta batare da yace uffan ba, binsu da kallo nai ta ƙasan ido har sukaje gab da ƙofa. Ranƙwafawa yay yaymata maganar da duk bamujiba a cikin kunne, ta ƙyalƙyale da dariya tana tsalle, shima wani shegen murmushi ya saki maiban mamaki, Safah tace, “Amma Yayanmu (Yanda taji Nabeelah na faɗa) kafin goben zaka rama mata dukanta ko? Inba hakaba saina saka Abbu ya turo sarkin tsabga na masarauta ya musu dukan mutuwa da dorinarsa”.
      Janyeta yay daga jikinsa da take neman shigewa yana lumshe idanu, a hankali yace, “Karki damu zan rama mata da kaina”. Sosai ta shiga daka tsallen murna Nabeelah da Mama na dariya harma da Amaturrahman, Marwah ce dai tai murmushi kawai tana rakuɓewa a jikina, juyowa yay muka haɗa ido nai saurin janye nawa, da hannu ya yafito Marwah alamar taje itama. Da sauri kam ta nufesa cike da ɗoki harda murmushin daya bama kowa mamaki, dan tunda tazo taƙi sakin jiki da kowa. Hannunsu ya kam suka fita, Amaturrahman taimin sallama tabi bayansu tare da Nabeelah da zatai musu rakkiya, mama kuma ta bisu da kalaman godiya dana addu'a. Nima haka godiyar nake musu har suka fice.

            Bayan wucewar su Amaturrahman Jawaad bai koma cikiba, mota ya shiga yabar asibitin. Kai tsaye gidan Alhaji baba ya nufa, harya zauna kusa da Alhaji baba baisan ya shigoba, saida Jawaad ya kwanta tare da ɗora kansa a cinyar kakan nasa sannan ya kawo numfashi. Cike da mamaki jay yace, “Tunanin mikake haka da zurfi sofo?.”
       Shafa kan Jawaad yay cikin ƙoƙarin danne damuwarsa yace, “Kaima zaka tsufan wataran ai, ango mai rinton mata, yaya kukayi dasu a masarautan?”.
          Dariya Jay ya ƙyalƙyale da ita yana faɗin, “Ashe dai ni jarumine tunda gashi na ƙwace kuma dole a barmin. Ka fara gayamin damuwarka Baba sai na faɗa maka nima”. Jay yay maganar cike da kulawa ga kakan nasa abin ƙaunarsa. Sosai Alhaji babba ya sake danne halin da yake ciki ya nunama Jawaad bashi da wata damuwa, badan Jawaad ya aminceba ya haƙura, sannan ya zayyane masa duk yanda sukai da gimbiya Munaya. Alhaji babba yace, “Banƙi ta tataba, sai dai kuma kai kana ganin babu damuwa?”.
     Zaune Jawaad ya tashi sosai, yace, “Amincewarka ni itace kawai tawa baba, dan kaine zaka hangomin abinda ya dace da wanda yake kuskure saboda kana gaba dani, dalilan data kawo na komawarta gidan Dad abin dubawane, nikuma gashima ban shiryama maganar tarewar tataba saboda akwai ayyukan da gidan da zan ajiyeta yake buƙata, tunanin da nake dai bai wuce dama ta koma gidan Ummah babba ba, dan dama ni ban tsara zata koma can gidanba saboda haɗarin dake tattare da hakan koda Qaseem da Hudah da Momynsu.
        Alhaji baba yace, “Lallai kayi tunani mai ƙyau, yanzu dai ka bata dama, dan kowa yanama Uwargidan sarki ƙyaƙyƙyawan sheda akan adalci da shiga matsalar talakawa da ƙarfinta da dukiyarta, to akanku wannan ba sabon abu bane, bakuma yauta faraba, shiyyasa banajin wani ɗar balle tunanin akwai wani manufa a lamarinata”
          Jawaad yace, “Shikenan Alhajin ALLAH zanyi yanda kace”. Daga haka hira sukaɗan taɓa zuwa sallar la'asar, daga nan Jawaad yay masa sallama ya wuce gida, dan a matuƙar gajiye yake, rabonsa daya huta tun daren alhamis ranar laraba kenan, gabaɗaya bai hutaba, a hankali ya furta, ‘Dukta cinyemin lokaci ta gajiyar dani’ ya ƙare maganar daɗan lumshe idanu ya buɗe akan titi.
            iske gidan nasu yay kaca-kaca anata hayaniya, dai-dai sashensa yay fakin inda ya saba, ya fito fuska ɗaure batare da ya kalli kowaba a cikinsu ya shige abinsa, dan ya fahimci cecekucen maganar aurence suke har yanzu, shikam a tsarinsa duk abinda ya gama da matsalarsa to yagama kenan baya sake waiwayensa sai dai kuma sabo idan ya taso.
       Yanda suka ganshi a tsume yasa aka rasa mai tunkararsa da magana dukda kuwa shigowar tasa suke jira dama, Hatta da Momy da Shahudah duk suna gidan sunzo saboda mama Atika data buƙaci ganin Momy, ga k

ukan da Shahudah keta dirja tunda Jawaad ya baro gidan. (Kaike musu yanda kaso ace ɓarnar motace, inba kaiba saiwa ɗan Abdul'aziz😂, kaikeyi kayi kuma kamar bakaiba dole a ganka a ƙyale🤣🤣).
      Yana shiga falonsa ya dannama ƙofar key yana jan wani wawan tsaki, a kwanakinnan ko shara sashen baya samu saboda yaraba hankalinsa biyu, ga matsalar aiki ga matsalar cikin gida, duk ƙura ta kwanta bisa kayayyakin falon, haka ya tsallake yanzunma ya haye sama, canɗinma dai yay ƙurar sosai, bai kulaba ya ƙarasa bedroom, shi daɗan sauƙi saboda ana zama, gadonma a gyare yake, ga mayen ƙamshinsa daya kama ɗakin na nan, kayan jikinsa kawai ya rage, dagashi sai boxer ya haye gadonsa yana lullumshe idanu. Cikin ƙanƙanin lokaci barci mai nauyi yay awon gaba dashi (Barcin bayan la'asar baida ƙyau Jay🤦🏻). A hankali numfashin Jawaad ya ƙara nauyi alamar barcinsa yayi nisa, mafarki mai sarƙaƙiya, wanda a cikinsa aka sake maimaita masa kalmar “(Ƙaddarar haɗuwar Jini a cikin jini da zai zama jini a yanzu ta zama tabbatacciyar alaƙa da zata zama sanadin buɗe ma'anar jini a cikin jini, takuma warware sirrin ɓoye, Kuzama masu addu'a, dan lokacin da ƙullalliyar sarƙaƙiya mai cike dacin amana zai bayyana yayi, dolene maciya amana, amana tacisu suma, dolene waɗanda sukai shuka su girbe abarsu dai-dai da abinda suka shukaɗin tun a duniya kafin aje babbar kotu kowa ya amshi sakamakonsa, dolene gorar da azzalumai suka fafe dan tafiya ta buɗe a yanzun da suke gab da kaiwa ƙarshen tafiyar tasu, ɗan zaki ya girma, kaine jagoran fidda ƘWAI CIKIN ƘAYA, karkuyi wasa da addu'a!! dan itace babban takobinku na yaƙar wata riundina ta azzalumai masu son zuciya, gaggawarku zaizama sanadin tonuwar wasu jinane da aka kwarayar. wannan itace ƙaddararku, ƙaddara mai sarƙaƙiyar data saƙa jini a cikin jini, karku manta! Addu'a!! Karku manta!! Karku manta!!)”. Cike da firgici Jawaad ya farka, ya jiƙe sharkaf da gumi dukda kasancewar yammace mai cike da ni'ima canjawar iskar farkon damuna, ɗan zafi-zafin dake garin bashida gallazawar da zatakai mutum da irin wannan zufar da yakeyi, gaba ɗaya jiyay ɗakin na juya masa tamkar hajijiya, ya dafe kansa da hannu yana karanto addu'oin da duk sukazo masa kan harshe. Ya ɗauki tsahon mintuna zaune kafin yaji ɗakin ya tsaya dai-dai, ya sauke hannunsa yana furzar da iska zazzafa, idanunsa sunyi wani irin kaɗawa sunyi jazur, wannan wane irin mafarkine haka? miyasa yaketa maimaita kansa garesa? Akan wa ake masa wannan nunin?; ‘Ya ALLAH ka warwaremin abinda banida ilimin saninsa, ka haskamin abinda ya kasance duhu a gareni, ka jagoranci tunanina akan abinda kakemin ishara dashi acikin barcina’. Idanunsa ya sauke akan wayarsa dake haske, kamar zai share sai kuma dai ya ɗauka, ashe yayi barci mai tsaho, ga magrib harta gabatoma, saƙon da'aka turo masa ya buɗe, sanin muhimmancin wanda ya turo masa saƙonne yasashi nutsuwa ya karanta abida ya rubuto.
         “Oga na shirya faɗa maka komai a yanda yake, ina kuma buƙatar a bani matata itama, amma akan farashin kuɗaɗe, kabani address ɗin inda zamu haɗu, sannan kazo da naira miliyan hamsin, nikuma zan baka labari mai matuƙar tsada akan kai kanka bayan nata itama”.  
          Naka ɗan fir'auna.
Ƙaramin tsaki Jawaad yaja yana mai dafe goshinsa da hannun damarsa tare da murzashi da ƙarfi, da ace ya iya kuka akan komai da a yau zama zai kawai yayta kuka har sai ya ƙoshi dan kansa yay shiru, to amma a tsarin wannan harƙallar kuka a garesa kasawace. Miyasa ɗan fir'auna yace yanada labari a kansa? Kenan shima su.... Ya haɗiye abunda ke neman toshe masa numfashi da sauri yana girgiza kai da faɗim, ‘No...’ bazai kasance hakaba. Komawa yay baya ya sake zubewa a gadon, ƴar ƙarar da agogon ɗakin yayce ta sakashi miƙewa kuma zumbur. Toilet ya nufa, ya sakarma kansa ruwa na tsahon lokaci kafin yay wanka ya fito ɗaure da alwala yay gaggawar shiryawa ya fita.

_____________________________

         Ganin mutane sun sassauta zuwa dagani sai Mama a ɗakin da Ummie yasa

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

1 year ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment