Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 5
tafi gida, ni na zo miki da maganin da za ki warke daga wannan cizo da gaggawa. Bayan jimawa muka tashi ina cikin gayar tunani da tsannin tsoro har muka iso zuwa gida. Ban dade da dawowa ba, sai ga mijina ya shigo, ya na duban fuskata sai ya ce da ni, me ya ji miki ciwo a kundukukinki, wuri mani’imci? Na ce da shi, ya yin da muka fita zuwa kasuwa, mun hadu da rakuma akan hanya, an yiwo mata laftu na itace, garin in kauce in bata hanya, itacen ya karce ni a kundukuki har ya ji mini ciwo. Mijina ya ce, babu shakka gobe in yi karar mai rakumar nan ga alkali, a daure shi kuma a rataye wanda ya dauko wa itacen ko wane ne a cikin birnin nan. Na ce da shi, na roke ka don Allah kada ka ga laifin kowa. Ni jaka na hau sai ta yi tutsu da ni, na fadi kasa, dutse ya ji mini ciwo. Ya ce, gobe kuwa na tafi gun Sarkin Musulmi, in hakaita masa da wannan hikaya, a kashe duk mai jakin da ke cikin birnin nan. Na ce, yanzu kai ka sa a kashe mutane duka saboda ni? Wannan al’amari ne da Allah ya gudanar bisa ga ikonsa da hukuncinsa, me za ka yi? Ya ce, babu makawa ga haka. Ya zabura ya mike tsaye cikin fushi, ya yi kururuwa, kururuwa mai tsanani. Kofa ta bude, babbakun bayi guda uku suka fito ta kofan nan, suka jawo ni daga shimfidata, suka yashe ni tsakar gida. Ya umurci bawa daya daga cikinsu da ya rike kafadata ya zauna bisa ga kaina. Ya umurci na biyu da ya zauna bisa gwiwowina, shi danne kafafuna. Na uku ya zo da takobi ga hannunsa, ya ce, ya shugabana in sare kanta da takobin nan, ko in raba ta gida biyu kowa ya dauki daya? Mijina ya ce, sare ta gida biyu, kowa ya dauki daya ku jefa ta cikin kogin Dujillati, kifi ya cinye ta, wannan shi ne sakamakon wanda ya yi ha’inci ga rantsuwar masoyi. AA Misau Ke magana Zan dakata anan Sai Allah yakaimu gobe Suleiman Zidane Kd 015. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA . . Copied AA Misau Ke magana . Labarin Yarinya Mai Jiran Kofa . (2) Yarinya ta ci gaba da labarinta da cewa: Lokacin da mijina ya ji jawabina, ya zabura ya mike tsaye cikin fushi, ya yi kururuwa, kururuwa mai tsanani. Sai na ga kofa ta bude, bayi guda uku, bakake suka fito daga cikinta, suka jawo ni daga kan shimfidata, suka yasar da ni tsakar gida. Ya umurci bawa daya da ya danne kaina, ya umurci na biyu ya danne kafafuna. Bawa na uku ya zo da takobi a hannunsa ya ce, ya shugabana in sare kanta ko in raba ta biyu kowa ya dauki rabonsa. Mijina ya ce, raba ta gida biyu da takobinka, kowa ya dauki daya, ku tafi ku jefa ta a cikin kogin Dujillati kifi ya cinye ta, wannan shi ne sakamakon mai yin ha’inci ga rantsuwar masoyi. Sannan sai ya waka wadan nan baitoci: “Idan abokin tarayya ya kasance ga masoyiyata, na haramtawa kaina son ta. Ya raina mutuwata ita ta fi alheri, ga son da ya kasance akwai kishiya a cikinsa” Bayan ya gama wannan waka, ya dubi bawan nan ya ce, raba ta biyu ya Sa’adu! Bawa ya tsiraita takobi, ya daga ta sama, sannan ya dube ni ya ce, ki na da sauran bukata? Ki na da wata wasiyya da za ki yi? Wannan shi ne lokacin rayuwarki na karshe a duniya. Yayin nan na daga kaina, na dubi halin da na ke ciki. Na tuna da da daukakar da na ke da ita, yau ga shi na zamanto makaskanciya, na tuna irin dukiyar da na ke da ita, da matsayina, sai hawaye ya zubo daga idona, shar shar shar. Na waka wadan nan baitoci: “Na zaunad da zuciyata cikin so, ta zauna. Na hana idona barci, suka hanu. Na saukad da ku cikin zuciyata, ta karbe ku. Kun yi mini alkawarin zama cikin so, amma da kuka mallaki zuciyata sai kuka warware. Ba kwa jin tausayin bakin cikina a gare ku? Shin kun amince da juyawar zamani ne? Shin ba ku yarda da kaddara ba ne? To ina rokon ku, domin Allah da Manzonsa, idan na mutu ku rubuta a kan allon kabarina, wannan mai bege ce, ta sadaukar da ranta ga abin da ta ke so, kuma ta mutu a kan soyayya.” Yayin da mijina ya ji wannan waka, sai fushinsa ya karu a kan fushi, sai ya yi wannan waka ya na cewa: “Kin bar abin son zuciyarki, kika so abin zargi, kika nado zunubi wanda ya halasta kisanki. Kika nufi abokin tarayya cikin tsarkakakken son da ke tsakanimmu. Gaskiya ni zuciyata ba ta yarda da abokin tarayya a cikin soyayya.” Yayin da ya gama waka tasa, na yi kuka, na rarrashe shi, na ce shi yafe mini daga kisa, ya dauki dukkan dukiyata ta zama fansar laifin da na yi masa. Na kuma ce da shi, da girmanka idan ka bar ni, ba ka kashe ni ba, Allah zai hukunta tsakaninmu, hukunci tsarkakakke. Ka daukaka mini nauyin bege, ni na gajiya daga daukar riga biyu in ribanya. Ba na al’ajabin tallafar raina, amma ina al’ajabin ina za ka da alhakina? Da ya ji wannan magana tawa, sai ya shure ni, ya zage ni, sannan ya yi wannan waka ya na cewa: “Kun shagala da mu, kuka so wanimmu. Kun bayyana kaurace mana, ba tare da mun yi muku laifi ba. Tilas mu bar ku, tun da kuka bar nufinmu. Mu hakura da barinku, tamkar da kuka bar mu.” Yayin da ya gama wannan waka, ya daka wa bawan nan tsawa ya ce, raba ta gida biyu, ba ta da wani amfani a gare mu. Lokacin da bawa ya gabata, ya daga takobinsa sama zai sare ni, na sakankance da mutuwa, na debe kauna daga rayuwa, na bar al’amarina ga Allah, Madaukakin Sarki. Na yi kalmar shahada, na rufe idona ina jiran na ji saukar takobi a jikina. Daga nan sai ga tsohuwa ta shigo. Ko da ta gan ni cikin wannan yanayi, sai ta fahimci abin da ya faru. Nan take ta fadi gaban mijina, karkashin kafafunsa, ta na sumbatarsu. Ta ce, ya saurayi, don martabar goyon da na yi ma ka, ka yafi wannan yarinya, ita ba ta aikata wani zunubi da wannan hukunci ya wajabta gare ta ba. Kai yaro ne karami, ina ji maka tsoro daga addu’a tata, domin addu’ar wanda aka zalunta abar karba ce ga Ubangijin talikkai. Yayin nan tsohuwa ta fashe da kuka. Tsohuwa ba ta gushe ba tana rarrashin mijina, tana kuka tana buga kanta ga kafafunsa, har ya ce da ita, tashi na yafe mata, amma babu makawa in aikata mata tabo mabayyani a jikinta tsawon rayuwarta. Ya umurci bayi suka tube ni daga tufafina, aka hallaro masa da tsumagiyar giginya, ya saukar mini da duka a jikina, duka mai tsanani. Bai gushe ba yana duka na, bisa ga bayana da hakarkarina, har na suma na faku ga barin duniya domin tsananin bugu. Ya umurci bawa daya da ya dauke ni, idan dare yayi, ya jefar da ni a cikin gidana. Lokacin da na farka, na gan ni a yashe cikin gidana, na yi godiya ga Allah da ya kubutar da raina. Na yi ta jiyyar wannan duka da mijina ya yi mini, har na warke sarai. Amma wannan tabo na bugu yana nan tamkar da gan shi a jikina, ya Sarkin musulmi. Bayan na warke, na dawo gidan mijina, sai na tarar da gidan nan a rushe daga farkonsa har karshe, na yi mamaki a kan faruwar wannan abu. Daga nan sai na ziyarci wannan ‘yar uwa tawa a gidanta. Na same ta tare da wadan nan karnuka, ta labarta mini abin da ya faru duka, gare ta da kuma yan uwanta. Na debo dukiyata na dawo gidanta muka ci gaba da zama tare. Muna zaune a cikin gidan nan, sai ga wannan yar uwa tamu, wacce ta kasance ita ce karamarmu, muka dauke ta a matsayin Jekadiyarmu, wadda ke zuwa kasuwa tana sawo mana kayan abinci da na marmari. Muka zauna a wannan gida babu ruwanmu da maza, saboda abin da ya faru da mu a baya, na daga maza. Na kasance duk lokacin da na ji wakar soyayya, tsikar jikina ta kan tashi, hankalina ya kan gushe har na suma, saboda wannan abu da ya faru da ni. Wannan shi ne labarina da kuma dalilin tabon bugu da ke jikina, ya Sarkin Musulmi. Halifa ya yi matukar mamaki da al’ajabin labarun wadan nan yan mata. Ya yi umurni da a rubuta wadan nan hikayoyi na yan mata da kuma na samari masu ido daya-daya a littafi, a ajiye su a dakin adana littattafai, domin na baya su karanta su amfana da darussan da ke cikin wadan nan hikayoyi. Sannan ya juya ga yarinya shugabar yan mata, ya ce, yalla ko kin san inda aljanar da ta sihirce yan uwanki ta ke? Yarinya ta ce, a’a, amma ta ba ni wani yanki na gashin kanta, ta ce duk lokacin da na ke son ganinta, na kona sili daya za ta bayyana da gaggawa, ko da kuwa tana bayan dutsen kaf. Halifa ya sa yarinya ta kawo gashi daya na aljana, ya sa aka hada garwashin wuta, ya jefa gashin a ciki. Lokacin da hayaki ya tashi, iska ta kada shi ko’ina, sai suka ji kasa na girgiza, kamar za ta tsage. Wata irin tsawa da hargowa ta cika fadar. Jim kadan sai ga aljana ta bayyana, cikin kyakkyawar shiga ta musulunci, da ma Allah ya yi ta musulma ce. Tana bayyana, sai ta gabatar da sallam ga Halifa da cewa, amincin Allah ya tabbata a gare ka, ya Sarkin Muminai. Halifa ya amsa mata da cewa, amincin Allah ya tabbata a gare ki. Sannan ta ce, ka sani ya Halifa, wannan yarinya ta yi mini taimakon da ba zan manta da shi ba har duniya ta nade, domin ita ce ta kashe mini babban makiyina a duniya. Domin in saka mata da wannan alheri da ta yi mini, na sihirce wadan nan miyagun yan uwa nata, wadan da suka yi niyyar halaka ta, zuwa karnuka. Da na yi niyyar in kashe su ne, sai na lura da cewa za ta damu da hakan, shi ya sa ban kashe su ba. Amma bisa ga girmamawarka da yardar yarinya, ya Sarkin Musulmi, idan kuna so in mayar da su ga siffarsu ta asali, to zan mayar da su, na kasance musulma mai biyayya ga shugabanni. Halifa ya ce, na roke ki tare da yardar yarinya da ki mayar da su ga siffarsu ta asali. Bayan wannan sai mu binciki al’amarin wannan yarinya da aka yi wa duka, mu nemo wanda ya zalunce ta, mu fitar mata da hakkinta. Aljana ta ce, na ji na karba. Yanzun nan zan mayar da su ga siffarsu ta asali. Amma wanda ya doki yarinyar nan, mutum ne makusanci da kai, karewa ma, a cikin iyalinka ya ke. Ta ce a kawo mata tasa da ruwa. Da aka kawo mata, ta yi wani zance ta tofa a cikin ruwan. Sannan ta yayyafa wa karnukan nan ruwan, ta ce, ku fita daga cikin wannan siffar, ku komo ga siffarku ta mutane. Nan take karnukan nan suka juye zuwa kyawawan yan mata, son kowa kin wanda ya rasa, tamkar yadda suke a da. Tsarki ya tabbata ga mahaliccin wadan nan yan mata. Bayan aljana ta mayar da yan matan nan ga siffarsu ta asali sai ta ce da Halifa, ya Sarkin Musulmi, ka sani cewa ba kowa ne yayi wa yarinyar nan duka ba face danka Aminu. Shi ne ya ji labarinta, da kyawonta. Ya nemi yardarta suka yi aure. Aljana ta kwashe labari duka ta fada wa Halifa, tamkar dai yadda yarinya ta fada masa. Da Halifa ya ji haka, ya ce, tsarki ya tabbata ga Allah, wanda ta sanadiyyata ne wadan nan yan mata, da suka shafe lokaci mai tsawo suna cikin siffar karnuka da azabtarwa, suka sami yancinsu. Sannan ya sa aka nemo masa dansa Aminu. Ya sa shi ya biya yarinya diyyar tabon da yayi mata a jiki. Da yake kuma suna son juna, ya sa aka mayar da aurensu. Ya sa aka gina musu wani gida mai kyau, fiye da wancan da ya ruguje. Ya aurad da yarinya shugabar yan mata, da yan uwanta biyu da aka kubutar daga siffar karnuka, ga samarin nan uku masu ido daya-daya, da ma ‘ya’yan sarakuna ne. Ya nada samarin nan hakimai, ya sa su a cikin mulkinsa. Ita kuma yarinya jekadiya, Halifa ya aure ta, ta zama matarsa, ya kebe mata shiyarta dabam, ya ba ta kuyangi masu yawa, wadan da za su rika yi mata hidima. Suka zauna cikin jin dadi da more rayuwa, har mai rabawa ta zo ta raba. TAMMAT. Anan hikayar tazo karshe AA Misau Ke magana Suleiman Zidane kd Domin samun wasun sabbin Littafi 08161272634 An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 5 of 5