Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
cikin rumfar, na zauna ina saye ina sayarwa.Amma 'yan uwana sai suka sayi haja mai yawa, suka dauki ijarar jirgin ruwa suka nufi wurin fatauci cikin duniya nesa da garinmu. Na yi musu addu'a, 'Allah ka yi musu budi, ni kam na fi so in zauna gida lafiya. Tsiya da kwanciyar hankali ya fi arziki da tashin hankali.' Na zauna tsawon shekara guda cikin rumfata, tsawon wannan lokaci kuwa Allah ya bude mini kofofin arziki, na sami riba ninkin-ba-ninkin, na tara dukiya kamar yadda mahaifinmu ya bar mana.Wata rana da hunturu, ana zazzaga sanyi, ina zaune cikin rumfata, na sanya riguna biyu, na gashi mai taushi, masu tamanin gaske, sai ga 'yan uwana sun zo gare ni. Kowane daga cikinsu na sanye da tsummar riga, duk ta kekkece har ana ganin fatar jikinsu. Ga lebbansu sun yi fari fat sun bushe, jikinsu sai makyarkyata yakeyi saboda sanyin da ke bugun su.... Admin AA Misau Ke Magana Suleiman Zidane Kd HIKAYAR DAKO DA YAN MATA.. 004. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA . Copied AA Misau Ke Magana . Labarin Saurayi Na Farko Mai Ido Daya (2) . Saurayi na farko, mai ido daya, ya ci gaba da ba da labarinsa da cewa: “Lokacin da na gaya wa bappana abin da ya faru da dansa, sai ya ce in kai shi gidan da na bisne dan nasa tare da matar nan, ko Allah ya datar da mu da gane bigiren da na rufe su. Muka tashi muka je gidan. Muna zuwa, da dubawa haka, sai na shaida wurin da kabarin nan yake, muka yi farin ciki mai yawa. Muka samu magirbi, muka tone kasar, sai ga rufi ya bayyana, muka cire shi sai ga tsani ya sauka kasan ramin. Na tattaka tsani na sauka kasa, gwargwadon tsawon ramin nan zira’i hamsin, bappana ya biyo ni daga baya. Yayin da muka riski karshen tsani, muka sauka kasa, sai ga wani hayaki ya bayyana bisa garemu, sai na ji bappana ya fadi kalmar nan da mafadinta ba shi tsorata, ita ce, Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un! Muka ci gaba da tafiya, sai ga mu a cikin daki cikakke da abinci da kayan marmari, da ruwan sha. Mun gani a cikin dakin babban gado mai labule, muka samu dan bappana kwance a kan gado tare da matar nan da suka shiga da ita cikin wannan rami, sun zama bakin gawayi , suna rungume da juna, ka ce su an jefa su cikin rijiyar wuta. Yayin da mahaifinsa ya ga haka, fuska tasa ta sake, ya ce, “Haka ya kamata da kai, ya kai daddauda, wannan azabar duniya ce, saura azabar lahira, ita ce mafi tsanani, mafi wanzuwa.” Yayin nan saurayi mai ido daya, ya ce wa yarinya da sauran jama’ar da ke sauraren labarinsa, “Kuna jin zancena! Yayin nan bappana ya shuri dansa da takalmi. Na ce da shi, abin da suke ciki bai ishe ka ba har sai ka shure shi da takalmi?” Ya ce, “Ya dan dan uwana, wannan da nawa, ya kasance a lokacin kurciyarsa mai tsananin son yar uwarsa, wannan da suke uwarsa, wannan da suke kwance tare, na hane shi gare ta, ina cewa a cikin raina don su yara ne, yayin da suka girma barna za ta auku a tsakaninsu. Na tsaya bisa ga haka. Na tsawace su, tsawa mai tsanani, a kan su rabu da son juna don babu aure a tsakaninsu. Na tsare shi daga gare ta, na tsare ta daga gare shi. Ita kuma ta kasance ta na sonsa, so mai tsanani. Shaidan ya tabbata tsakaninsu. Shi ya yi wannan gidan karkashin kasa a boye, ya tara abinci a ciki, tamkar da ka gani, duk lokacin da ya ga na shagala da wani abu, ko na fita zuwa ga farauta, sai ya zo shi da wannan yar uwa tasa, su boye suna aikata abin da ransu ya kawata musu. Yayin nan ya yi kuka, muka yi kuka tare da shi. Ya ce da ni, “Kai ne da na maimakonsa!” Yayin nan na yi tunani kadan na duniya da zantuttukanta da al’amurranta, masu faruwa, na tuna Waziri da yadda ya kashe ubana, ya riki matsayinsa, ya cire mini idaniya da gangan, da wannan dan bappah nawa, da abin da ya same shi na konewa shi da yar uwarsa. Sannan muka hawo tsani, muka mai da rufi, muka mayar da kasa, muka aikata kabari tamkar yadda shi ke, muka komo zuwa ga gidanmu. Tun ba mu gama zaunawa ba, sai muka ji bugun tambari, da ganguna da algaitu, muka hangi masu da takubban mayaka su na walkiya a cikin rana. Duniya ta cika da kura, karar kofatan dawaki da kukansu ya gauraye ko’ina, hankulanmu su ka kada, ba mu da labari. Sarki ya tambayi labari, su waye haka? Aka ce da shi, Wazirin dan uwanka ne, ya tara askar da runduna don shi abka maka da yaki, ya ci birninka ba tare da kun shirya ba. Domin shi yana jin tsoron ka sami labarin ya kashe dan uwanka, ka abka masa da yaki. Koda na ji haka, sai na ji tsoro, na ce a cikin raina, idan na sake na sake fadawa hannun Waziri ba shakka zai halaka ni. Bakin ciki ya rufe ni, na tuna abubuwan da suka faru, na daga musibu da suka abka wa mahaifina, da dan bappana, na rasa yadda zan yi. Na tabbata idan mutanen Waziri suka gan ni, za su shaida ni, su kama ni su kai ni gabansa, ba ni samun daya da zan tsira daga hannunsa. Sai na aske gemuna, na sake tufafina, na fice daga birnin na nufo wannan birni. Wassalam, wannan shi ne labarina. Yalla ko wani ya kai ni ga Sarkin Musulmi Halifa, in labarta masa da wannan hikaya tawa, da abin da ya gudana gare ni. Na shigo wannan birni a cikin wannan dare, na tsaya, ina madimauci, ban san inda zan nufa ba, sai ga wannan mai ido daya yana tsaye. Na yi masa sallama, na ce da shi ni bako ne! Ya ce da ni, ni ma bako ne! Mu na cikin haka sai ga wannan abokin namu, na uku ya zo mana, ya yi sallama a garemu, ya ce ni bako ne! Mu ka ce da shi mu ma baki ne. Muna tafiya duhu ya yi mana, kaddara ta koro mu zuwa nan gidanku, muka nemi masauki, kuka saukar da mu, har abin da ya faru yanzu ya faru. Wannan shi ne dalilin rasa idaniyata ta hagu, da aske gemuna da na yi.” Suka yi mamakin zancensa, Halifa ya kaikaici yan mata ya ce da Ja’afaru, “Da dai ban taba jin tamkar abin da ya gudana ga wannan saurayi ba.” Yarinya Shugabar yam mata ta ce, “Tube kanka daga igiya, ka kubutad da ranka. Maza ka kama tafarkinka.” Ya ce da ita “Ba ni tafiya, sai na ji labarin wadan nan sauran mutane.” Yayin nan saurayi na biyu, mai ido daya, ya gabata gaban yam mata, ya yi gaisuwa ga shugabarsu, ya ce “Ni ba a haife ni da ido daya ba, akwai abin mamaki mai yawa ga hikayata wanda ya fi na wannan aboki nawa da ya gama bayar da labarinsa.” Ya fara bayar da labarinsa kamar haka: Zan dakata anan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba Admin AA Misau Ke Magana WHATSAPP 08161272634 005. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA . Copied AA Misau Ke Magana . Labarin Saurayi Na Biyu Mai Ido Daya (1) . Saurayi na biyu mai ido daya ya gabata, ya yi gaisuwa ga yarinya shugabar yam mata sannan ya ce, “Ya shugabata, ni ba a haifeni da ido daya ba, akwai abin mamaki mai yawa ga labarina. Da za a rubuta shi da tsinin allura, a duba da kaifin ido, da ya zama abin lura ga masu hankali. Da farko dai ni Dan Sarki ne jikan Sarki. Na karanta Alkur’ani bisa ga ruwaya bakwai, na karanta littattafai ga masu su, sannan wakoki, na yi kokari a cikin dukkan saninsu, har na tserewa mutanen zamanina, na wuce su. Sunana ya watsu, labarina ya isa ga dukkan Sarakuna na yankinmu. Sarkin Hindu ya ji labarina, ya aika wa ubana cewa yana son in tafi kasarsa in kai masa ziyara, yalla ko sa karu da wani yanki na daga tarin ilimina. Ubana ya amince da wannan bukata ta Sarkin Hindu, ya shirya mana jirage shida cike da guzuri. Muka kama hanya cikin bahar har tsawon wata shida cikakku sannan muka isa bisa tudu. Muka sauke kayanmu daga cikin jirgi, muka labtawa rakuma, muka tafi kadan- kadan. Daga nan, sai muka hangi kura ta daukaka, ta tokare sararin samaniya. Da aka jima, sa’a guda, sai ga mahaya sittin sun bayyana a gabanmu, duka zakokin fada ne. Muka lura muka ishe su duka Larabawa ne, mafasa tafarki. Yayin da suka iso wurinmu, ga mu, mu jama’a kadan, muna dauke da kaya niki-niki, sai suka abka mana. Muka yi musu ishara da cewa, mu manzanni ne zuwa ga Sarkin Hindu, kada ku cuce mu. Suka ce, mu ba mu kasance karkashin hukuncinsa ba, ballantana mu ji tsoronsa. Suka kashe wasu daga cikinmu, mu kuma saura muka yi ta kammu, kowa ya kama gabansa, muka bar wa ‘yan fashi kayan. Na kasance ban san inda zan nufa ba, da ina Dan sarki madaukaki amma yanzu cikin sa’a guda na komo wulakantacce. Na tafi har na iso kan wani dutse, na shiga cikin wani kogo na kwanta na huta. Da rana ta fito, na ci gaba da tafiya har na iso wani Birni rayayye, cikakke da alheri, lokacin tsananin dari ne, sai ka ce damina domin ni’ima tasa da kamshinsa, na yi farin ciki da isowata wannan Birni. Saboda tsananin gajiya da tafiya da bakin cikin abin da ya same ni da kurar hanya, duka suka hadu suka canja mini kama, idan an gan ni sai a dauka wani miskini ne. Bayan na iso Birnin, ban san inda zan nufa ba, sai na karkata zuwa ga gefensa, na ga madinki cikin rumfa, na yi sallama gare shi, ya mayad da sallama gare ni. Ya yi mini shimfida. Ya tambaye ni labarina. Na labarta masa duka abin da ya faru gare mu na daga mafasa. Bayan ya ji labarina, ya tausaya mini a kan abin da ya faru, sannan ya ce da ni, samari kada ka bayyana wa kowa wannan labari naka, domin ina ji maka tsoro ya kai ga kunnen Sarkin wannan Birni, domin kuwa shi ne babban abokin gabar mahaifinka, akwai wata fansa da ya ke so ya dauka ga mahaifinka, da kasarku da wannan kasa ba a ga-maciji da juna. Madinki ya halarta mini abinci da abin sha, muka ci tare da shi, muka zauna muna zance har dare ya yi. Ya gyara mini wani wuri kusa da turakarsa, ya kawo mini abin da nake bukata duka na daga shimfida da abin rufa. Na zauna tare da shi kwana uku, yayin nan ya ce da ni, ba ka san wani aiki da za ka fara yi ba a matsayin sana’a domin samun abinci? Na ce masa, ni almajiri ne, bayan karatu ban san wata sana’a ba. Ya ce, aikinka a cikin Birninmu baya da martaba, babu wanda ya san rubutu haka nan karatu, kowa dukiya kawai ya sani. Amma zan gaya maka wata sana’a idan za ka iya yi. Na ce, wace sana’a ce? Ya ce, ka tashi, ka riki gatari da igiya, ka tafi itace cikin daji, kaga da wannan sana’a, mutane da yawa sun yi arziki a cikin wannan Birni. Na amince da wannan zabi na madinki. Ya hada ni da wasu masu yin wannan sana’a, sannan ya yi mini wasicci da kada in gaya wa kowa labarina ko asalina. Na fita tare da su, na yiwo itace, na komo da kaya bisa ga kaina, na sayar da su rabin dinari, na ci rabi na ajiye rabi. Na dauwama bisa ga wannan hali har tsawon shekara guda. Wata rana na fita zuwa yin itace, na zurfafa cikin daji ban sani ba, sai na samu wata matacciyar itaciya da itace da yawa a kanta. Na shiga karkashinta, na ga tamkar shuri mai zuma, na tona gefensa na gusad da kasar kewayensa, na gan shi tamkar katanga, na sara gatari bisa ga kansa. Na ga rufi na farin karfe, na share kasar daga nan sai ga rufi na itace, na yaye shi, tsani ya bayyana a karkashinsa, na sauka zuwa ga kasan tsanin sai ga kofa, na shiga cikinta. Na ga soro mai kyakkyawan gini da zane da lailaya. Na ishe yarinya cikinsa, kai ka ce an gina ta da lu’ulu’u, tana sanyaya zuciyar mai bakin ciki, tana tsarkaka tunanin mai bacin zuciya. Yayin da na dubeta, na yi sujuda ga mahaliccinta domin abin da ya bayar gare ta na daga kyawo da cikar halitta. Ta yi duba zuwa gare ni ta ce, yalla kai mutum ne ko aljani? Na ce da ita, ni mutum ne! Ta ce da ni, wa ya sadar da kai ga wannan bigiren da ni ke cikinsa shekara goma sha daya ban ga kowa na daga bil Adam ba? Yayin da na ji zancenta, na ji dadi a cikin raina na ce, ya shugabata Allah ne ya kawo ni zuwa ga wannan wuri, mai yiwuwa ya yi nufin gusad da abin da ke tare da ni na daga bakin cikin rayuwa. Na labarta ma ta hikayata tun daga farko har karshe. Kafin na gama ba ta labarina, tuni idanunta sun cika da hawaye, saboda tausayi. Ta ce da ni, lalle ka gamu da jarabawar rayuwa kwatankwacin irin tawa. Yarinya ta ci gaba da cewa, ni kuwa labarina shi ne, ni yar Sarkin Hindu ce, mahaifina ya aurar da ni ga dan bappah na, ina ‘yar shekara goma sha biyu. Daren amarcina, Ifiritu ya sace ni, sunansa Jarjarisu dan Rajimusu dan Ibilisa, ya kawo ni cikin wannan wuri. Ya tara mini dukkan abin da nake bukata na daga tufafi da kayan ado da na shimfida, da na kayan abinci da abin sha. A cikin kowane kwana goma, ya kan zo ya kwana gare ni, kwana daya. Amma idan ina son ganinsa kafin lokacin, ya ce in taba wadan nan sharuddan rubutu na bisa kubba da hannuna, yayin da na shafa rubutun kafin in dauke hannuna, ya bayyana. Yau kwanansa hudu da tafiya, sai ga ka na gani. Ko za ka amince ka kwana biyar gare ni kafin ya sake dawowa, ka debe mini kewar rashin ganin dan Adam na tsawon shekara goma sha daya da ban yi ba? Zan dakata anan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba Admin AA Misau Ke Magana Suleiman Zidane Kd 006. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA . Copied AA Misau Ke Magana . Labarin Saurayi Na Biyu Mai Ido Daya (2) . Saurayi na biyu, mai ido daya, ya ci gaba da labarinsa da cewa: “Sai na amince da bukatar yarinya, ‘yar Sarkin Hindu wadda Ifiritu ya sace ta ya boye a wannan wuri da na same ta. Zan kwana biyar a gare ta, sannan in kama gabana kafin zuwan Ifiritu. Ta gabatar mini da abinci da abinsha, muka ci, muka sha tare da ita. Muka dade muna zance, tana mai matukar farin ciki da kasancewata a gare ta. Bayan mun gama zance, ta ce da ni ka kwanta ka huta ya shugabana, ka kasance mai aikin wahala ne. Ta kai ni wani daki, ta nuna mini gado, na hau na kwanta. Ban san lokacin da barci ya dauke ni ba saboda tsananin gajiya. Can da na farka daga barci, sai na ishe yarinya tana yi mini tausa ga kafafu, na kiraye ta da kyakkyawan suna, na gode mata, na yi mata addu’a a kan wannan karimci da take nuna mini. Ta ce, Wallahi ni na kasance mai kunkuntar kirji da zama wannan wuri ni kadai, cikin karkashin kasa, ba ni da abokin zance tsawon shekaru. Na gode Allahn da ya kawo ka gare ni. Na kara yi mata godiya, sai kuma na ji sonta ya tabbata cikin zuciyata, fushina da bacin raina, na daga abin da ya same ni, ya yaye. Muka zauna muna zance, tsawon dare, daren da babu tamkarsa cikin raina. Muka wayi gari muna masu farin ciki. Na ce da ita lalle ne sai na fitar da ita cikin wannan wuri, in hutar da ita da wannan aljani. Ta yi dariya, ta ce, “Ya shugabana, ka rufa wa kanka asiri, mu yi zamam mu a haka, cikin kwana goma kana da tara Ifiritu yana da daya, wannan ma ai ya ishe mu. Amma ina ji maka tsoron ka ce za ka fitar da ni daga wannan wuri.” Da yake sonta ya riga ya mamaye zuciyata, sai na ce da ita, “Ki shafa rubutun kubbar nan, ki kirayi Ifiritu ya zo, ni kuwa na sare kansa da takobin nan in kubutar da ke daga gareshi, ni na saba da kisan Ifiritai.” Koda yarinya ta ji zance na, sai ta yi waka ta na cewa, “Ya mai neman rabuwa, ka jinkirta da hilarka, ganinka ya ishe ni bege, hilarka, ganinka ya ishe ni bege, ka hakura, karshen haduwa rabuwakarshen haduwa rabuwa.” Koda na ji wannan waka tata, ban waiwaya zuwa ga zancenta ba. Ban san lokacin da na shuri kubbar nan ba, shuri mai karfi. Da yarinya ta ga haka, sai ta rikice, ta fashe da kuka ta ce, “Wallahi ka cuce ni, amma ka yi gaggawa ka tserad da ranka, ka fita ta wurin da ka shigo, babu makawa tunda aka bugi kubbar nan, yanzu Ifiritu zai bayyana, ya ko halaka ka, ya halaka ni.” Don tsananin tsoro, ya shugabata, na manta takalmi na da gatari na a cikin ramin nan. Yayin da na hau mataka ta biyu, na waiwaya don in duba, na ga kasa ta kece, Ifiritu ya fito mai mummunar magana. Na ji ya ce, me ya same ki, ki ka yi kira na a wannan lokaci? Ta ce, wani abu bai same ni ba face zuciyata ta kuntata, ina so in sha abin shan da zai sanyaya zuciyata. Na tashi domin dauko abinsha, sai na fadi bisa ga kubbar. Ifiritu ya ce da ita, karya ki ke, fajira! Ya duba cikin soron sai ya ga gatarina da takalmi, ya ce da ita, wannan ba kayan mutum ba, bil Adama. Wa ya zo miki da su? Yarinya ta ce, ni ban gan su ba face yanzu da ka shigo nan, wata kila kai ne ka shigo da su, suna a jikinka ba tare da ka sani ba. Ya ce, karya ki ke, wannan zancen banza ne, ba shi yiwuwa gareni in shigo da wadan nan kaya ba tare da na sani ba. Amma da sannu zan kamo wanda ya shigo da su nan in zo miki da shi. Sannan ya tsiraita ta, ya daure ta bisa ga shisshinai hudu. Ya zama yana azabtar da ita domin ta fada masa gaskiya, amma bai ji kukanta ba. Ta yi kurum. Na fito ta bisa ga tsanin ina firgitacce, jikina na rawa. Yayin da na taka doron kasa, na mayar da rufin ramin kamar yadda yake. Na yi nadama bisa ga abin da na aikata, gayar nadama. Na tuna yarinya da kyawunta, da yadda wannan la’anannen ke azabtar da ita bayan ta kasance tare da shi tsawon shekaru masu yawa bai azabta ta ba, sai ta sanadiyyar zuwana gare ta. Na tuna ubana da mulkinsa, da yadda na zama mai sai da itace, sai na waka wannan baiti na ce: “Idan zamani ya zo ma ka da musiba wata rana, wata rana ka ga sauki, wata rana ka ga tsanani.” Na tafi har na zo ga abokina madinki, na same shi yana hura wuta a gaban rumfarsa, ya fito waje yana duban hanyata. Da ya gan ni, ya yi murna ya ce, “Ni na kwana jiya ina tunaninka ina jin tsoron ko ka hadu da miyagun namun daji ko wani hatsari. Na gode Allah da ya maido ka lafiya.” Na gode masa bisa ga tausayinsa da kulawarsa a gare ni. Na shiga cikin rumfata, na zauna ina tunanin abin da ya gudana gare ni, ina zargin kaina bisa ga shurin kubbar nan da na yi. Daga nan sai ga abokina madinki ya shigo gare ni ya ce, “Wani mutum, Ajami, ya zo yana neman ka, da gatarinka a gare shi da takalminka. Ya ce abokanka ne, masu saran icce suka yiwo masa kwatance da kai, bayan ya tsinci gatarinka da takalmi a daji, shi ne yanzu ya kawo maka. Yana nan zaune cikin rumfata yana jiranka.” Yayin da na ji wannan zance, nan take kamata ta sake, hankalina ya tashi, domin na gane ko wane ne Ajamin nan, ba kowa ba ne face Ifiritu, ya rikida mutum domin ya zo ya tafi da ni ya hallaka ni. Ko kafin na bayyana wa madinki halin da na ke ciki, sai kasa ta tsage a gabanmu, Ifiritu ya fito ya sure ni, ya yi sama da ni, bayan wani dan lokaci kankane, ya komo kasa da ni, sai ga mu a cikin ramin nan, inda na tarar da yarinya. Koda na duba haka, sai na ga yarinya a daure, tsirara, jini na gudana daga gefenta. Idanuna suka kada, hawaye ya zubo mini. Ifiritu ya rike ta, ya ce da ita, “Ya munafuka, ba wannan ne abin begenki ba?” Ta dubo zuwa gare ni ta ce da shi, “Ban san shi ba, ban taba ganin sa ba cikin raina, bai halatta ba gare ni in yi masa karya.” Ifiritu ya ce, “Idan gaskiya ne maganar da kike fada, dauki takobi ki sare kansa.” Ta dauki takobi, ta tsaya bisa ga kaina, na yi mata ishara da kundukuki na, hawaye na gudu. Ta yi mini ishara da cewa kai ne ka aikata wannan duka gare mu, da ba ka shuri kubbar ba, da yanzu muna nan hankalinmu kwance. Ta daga takobi sama za ta sare mini kai. Ta jefar da ita gefe, ta fadi kasa ta na kuka. Yayin nan Ifiritu ya dauko takobi ya mika mini, ya ce da ni ka sare wuyanta ka kubutar da kanka, in sake ka, in dauke ka im mayar da kai ga ubanka, domin ni, na san labarinka duka. Na riki takobi, na gabata ga yarinya. Na daga takobi sama zan sare kanta, sai na ga hawaye na gudana a idanunta, sai takobi ya subuce daga hannuna, ya fadi kasa. Na dubi Ifiritu na ce, “Ya kai Ifiritu, mai girma, sadaukin shugaba, idan har wannan yarinya, mai karamin hankali da tunani, ta kasa sare mini kai, ta yaya ni da hankalina zan sare wuyanta ba tare da laifin kome ba? Yadda bai halatta gareta ta sare wuyana ba, haka ba ya halatta gare ni in sare nata. Ba ni aikata haka har abada.” Ifiritu ya yi fushi, fushi mai tsanani, kamarsa ta juya, ya yi mana tsawa har sai da kasa ta girgiza, ya ce, “Kaiconku ya fajirai! Ya tabbata ke nan da so a tsakaninku, hakika sai na yi muku azaba, azaba mai tsanani wadda za ku gwammace da daya ya kashe daya daga cikinku. Zan dakata anan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba Admin AA Misau Ke Magana 08161272634 007. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA . Copied AA Misau Ke Magana . Labarin Saurayi Na Biyu Mai Ido Daya (3) . Saurayi na biyu, mai ido daya, ya ci gaba da labarta wa yarinya, shugabar yam mata, da sauran jama’a hikayarsa, da dalilin da ya sa ya rasa idaniyarsa daya. Ya ce, “Kuna jin zance na? Ya yin da Ifiritu ya ga babu wanda zai iya kashe wani, tsakanin ni da yarinya, sai ya ce, kaiconku! Cewa tsakaninku da so! Ya dauki takobi ya sare hannun yarinya na dama, ya kuma sare na hagu, sannan ya sare kafarta ta dama, ya kuma sare ta hagu. Ni ko ina gani da idona. Na sakankance da mutuwata, na dubi yarinya, ta yi ishara gare ni da idonta, Ifiritu ya gan ta. Ya ce da ita, kin yi zina da idonki! Ya sa takobi ya fille kanta. Ya waiwayo zuwa gare ni, ya ce, ya kai mutum, mu, ga shari’armu, idan mace ta yi zina, kisanta ya halatta gare mu. Wannan yarinya na zaro ta cikin daren amarcinta, ta na ‘yar shekara goma sha biyu ba ta san kowa ba, face ni. Na kasance ina zuwa gareta sau daya cikin kwanaki goma, na kan zo mata ne a siffar mutum, Ba’ajamata ne a siffar mutum, Ba’ajami. Yanzu na sakankance ta ha’ince ni, shi ya sa na kasheta, amma kai bai kamata ka ha’ince ni game da ita ba. Amma babu makawa in wofinta ka, in rabu da kai lafiya, amma ba ni kashe ka. Ifiritu ya tambaye ni, wace irin cuta na ke so ya cuce ni? Na yi farin ciki da murna mai yawa, na yi tsammani ko zai yafe mini. Na ce da shi me zan roke ka, ka yi mini? Ya ce, ka tambaye ni, wace sura, cikin halittu, ka ke so im mayar da kai? Ko kare, ko jaki, ko biri, ko kuma wata sura dabam? Na ce da shi, ina tsammani za ka yafe ni, ya kai shugaban aljannu, sai Allah shi jikan ka. Na marairaita gare shi gayar marairaita, ina rokonsa yafuwa. Ya ce da ni, kada ka tsawaita mini magana, amma kada ka ji tsoron kisa, don ba zan kashe ka ba, amma ba ni yafe maka har abada. Babu makawa in sihirce ka. Ya dauke ni, ya kada da ni zuwa ga bisa, har na ga duniya daga karkashina, ka ce ita kwaryar ruwa ce. Yayin nan ya sauko kasa da ni, ya ajiye ni bisa ga dutse, ya debo ruwa kadan, ya gama da kasar bisa dutsen, ya karanta wani zance, wanda ban fahimta ba, cikin ruwan, ya watsa mini shi, ya ce, fita daga wannan sura zuwa ga surar biri a cikin wannan lokaci! Nan take na rikide, na zama biri, mai shekara dari. Lokacin da na ga kaina cikin wannan mummunar sura, na yi kuka bisa ga raina, na hakura bisa ga karkatar zamani, na sani zamani bai bar kowa ba. Na gangaro daga saman dutsen zuwa ga karkashinsa, na yi tafiya wata guda cur, sannan na iso bakin gabar Baharal Maliha, na tsaya sa’a guda, sai na hango jirgi a tsakiyar Bahar, iska ta yi masa kyawo, ya nufo tudu. Bayan jirgin ya dangana jikinsa da kasa, sai na lababo na shige ciki. Da mutanen ciki suka gan ni, sai daya daga cikinsu ya ce, mu fitad da wannan shu’umi daga jirgimmu. Wani ya ce, mu kashe shi! Wani kuma ya ce, tsaya in kashe shi da wannan takobi! Ya zaro takobi. Na yi kuka har hawayena ya gudana. Babbansu ya ji tausayina, ya ce, ya fatake, ku sani, wannan biri ya nemi ceto gare ni, don haka na cece shi, ku bar shi cikin kuyangi na, kada kowa ya cuce shi. Yayin nan uban tafiya ya kasance yana kyautata mini, komai na fada masa yakan fahimta, ina biya masa bukatarsa zuwa ko ina. Ina bauta masa cikin jirgi. Jirgi ya dace da yanayin Bahar mai dadi, bayan kwana hamsin, muka isa wani Birni mai girma da yawan jama’a, babu mai sanin adadinsu face Allah, Madaukakin Sarki. Da muka iso, muka tsayar da jirgimmu, sai ga masinjojin Sarkin garin. Suka shiga cikin jirgi suna yi wa mutane maraba da zuwa, sannan kuma suka ce, Sarki ya aiko mu zuwa gare ku da wadan nan takardu, ko wanne dayanku shi rubuta shadara na jawabin kayansa. Na tashi, ina cikin surar biri, na karbi takardu a hannunsu, suka ji tsoron kada in yayyaga su, in zuba cikin ruwa, suka hanani, suka nemi su kashe ni. Na yi musu ishara da cewa, ni ma zan rubuta. Uban tafiyar mu ya ce, ku barshi, shi rubuta! In ya yayyaga takardun, ko ya bata rubutun, mu kore shi daga gare mu, in ya kyauta mu rike shi. Yalla ni, ban taba ganin biri mai fahimta irin tasa ba. Aka ba ni takarda, na riki alkalami na sa a cikin taddawa, na rubuta shadara, na tsara wannan waka ina cewa, “Hakika Allah ya rabanta ni, zamani ya hukunta alherinsa gare ni bayan mugunta tasa. Ya uban tafiya, alherinka gareni ba ya kidayuwa, Allah ba ya maraita talikkai idan kana nan, cewa kai, alherinka ya mayi mamayin uba.” Sannan kuma na rubuta, “Idan an bude taddawar daukaka da ni’ima, ka tsoma alkalaminka na daga baiwa da karimci, ka rubuta alheri, in ka kasance mai iko, da haka nan ake daukaka madaukakiyar daraja.” Bayan na gama rubutu, na mika musu takarda. Masinjoji suka tattara takardu, suka tafi da su zuwa ga Sarki. Lokacin da Sarki ya karanta abinda ke cikin dukkan takardun nan, rubutun kowa bai kayatar da shi ba face rubutuna. Sarki ya ce da masinjojinsa, ku tafi ga wanda ya yi wannan rubutu, ku tufasassheshi wannan riga, ku hawar da shi bisa ga alfadara, ku zo da shi da kida, ku hallaro shi gabana. Ko da masinjoji suka ji zancen Sarki, sai suka yi murmushi. Da Sarki ya ga haka, sai yayi fushi, ya ce, yaya zan umurce ku da umurni na daga bakina, ku yi mini dariya? Suka ce, ya Sarki, ba mu yi dariya ga zancenka ba, face da cewa, wanda ya rubuta wannan takarda ba mutum ba ne, biri ne, yana tare da shugaban masu jirgin. Sarki yayi al’ajabin zancensu, ya yi nishadi da farin ciki, ya

Chapter 2 of 5