Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
rumfata. Bayan shekara hudu, mazajen yan uwannan nawa suka banzatar da dukiyar yan uwana suka wulakanta su sannan suka kore su. Yan uwana suka zo wurina, da farko ban gane su ba domin duka wahala ta tsufar da su. Yayin da na shaida su na ce, ya yan uwana me ya faru da ku bayan aurenku? Suka ce, ya yar uwar mu, zance ba shi da amfani a halin yanzu, bakin alkalami ya riga ya bushe, abin da Allah ya hukunta ba shi canjawa, cewa mu kaddara ta fada mana na daga asarar dukiyarmu, yanzu ba mu mallaki ko dirhami ba. Koda na ji haka sai na kwantar musu da hankali, na ce haka Allah ya kaddara, babu mai ikon juyad da ita. Na aika da su gidana, na tufatar da su tufafi masu tamani. Sannan na ce da su, ya yan uwana kune manya ni kuma ni ce karama daga cikin ku, don haka yanzu ku ne a matsayin iyayena. Rabon da na samu na gadon kudin mahaifinmu, Allah ya sa albarka a cikinsa, na juya shi ta hanyar kasuwanci, na kuma sami riba mai yawa don haka ya ishe mu, ni da ku, mu raba shi daidai. Ya Halifa, na kyautatawa yan uwan nan nawa, gayar kyautatawa, mu ka zauna tare muna kasuwanci tsawon shekara guda, suka zama masu arziki da dukiyata. Wata rana sai suka ce da ni, suna son su koma ga mazajensu. Na ce da su, ya yan uwana ku sani cewa kyawawan maza masu amana kadan ne a wannan zamani, za su karbe dukiyarku ne su wulakanta ku, su kore ku daga wurinsu, shin kun manta abinda ya faru da ku a baya? Suka ce, su dai za su koma. Na yi na yi da su, suka ki. Na barsu suka koma gun mazajensu. A cikin sa’a kadan da komawarsu, mazajen suka rude su, suka karbe dukiyarsu suka tafi suka bar su. Suka komo zuwa gareni suna matsiraita, suna mai kawo mini hanzari cewa, ya yar uwarmu, kada ki rike mu da laifimmu, ke ce karama daga gare mu amma kin fi mu hankali, cewa mu ba za mu sake yarda da maza ba har abada. Na ce, maraba da ku ya yan uwana, ba ni da tamkar ku a duniya, ta yaya zan juya muku baya. Na sumbace su, na dada musu karimci. Muka zauna tare da su tsawon shekara cikakkiya, na yi nufin zuwa fatuci birnin Bisira. Na shirya babban jirgi, na cika shi da kayan fatauci da guzurim ma su jirgi. Na ce da yan uwana, ko za ku zauna a gida har in tafi Bisira in komo, ko kuna da sha’awar mu tafi tare? Suka ce, za mu tafi tare, mu ba mu iya rabuwa da ke. Na raba dukiyata, ta kudi, kashi biyu, na boye daya a gida na riki daya domin ban sani ba kila wata kaddara ta asara ta fada mana a can. Idan mun koma ma samu abinda zai amfane mu. Bayan mun gama shiri, muka shiga jirgi muka tsunduma cikin bahar. Muka yi ta tafiya, dare da rana babu tsayawa. Muka yi kwanaki muna tafiya, ashe ba mu sani ba mai jirgi ya bata hanya, muka shiga wani bahar wanda ba mu sani ba. Bayan tsawon wani zamani, sai muka hangi wani birni daga nesa. Muka nufe shi har muka isa kan tudu. Muka tambayi mai jirgi sunan wannan birni. Ya ce, Wallahi ban sani ba, ni ban taba ganin wannan birni ba, ban taba zuwa gareshi ba. Ku sani cewa mun bace hanya, amma al’amari yayi mana kyau tunda mun samai wannan birni. Ku fitar da kayan ku, ku shiga cikinsa ku yi ciniki. Amma ku bari na shiga cikin garin na duba yanayinsa da yanayin mutanensa. Mai jirgi ya shiga cikin birni ya jima, bayan wani lokaci ya dawo garemu. Ya ce, ku tashi mu shiga cikin wannan birni ku yi al’ajabin ikon Allah don ku nemi tsari daga fushinsa. Ku bar kayan ku a cikin jirgi. Muka shiga cikin birni. Muka iske dukan halitta mai rai da ke cikinsa an shafeta ta koma siffar bakin dutse. Muka yi mamakin ganin wannan abu. Muka shiga cikin kasuwa muka ga kayayyaki, zinariya da azurfa, zube ga rumfunan sayar da su. Ga mutane, wasu a tsaye, wasu a zaune, wasu suna ciniki, wasu suna gaisawa, wasu na cin abinci, amma duk an shafe su zuwa siffar dutse. Sai kayayyakin siyarwa ke kyalkyali a cikin rumfuna. Muka yi mamakin wannan abu, muka ce watakila wani babban al’amari ya gudana ga jama’ar wannan birni. Muka fita daga cikin kasuwa muka rarrabu cikin kwararo kwararo na wannan birni, ko wanne dayanmu ya manta da abokinsa domin dimbin dukiyar da ke cikin wannan birni. Kowane kwararo akwai mutane da dabbobi, amma dun sun zama bakaken duwatsu. Amma ni na hangi wani babban gida, na shiga cikinsa. Na same shi abin gajiyarwa ga ido gun kallo, ashe nan ne fada. Na shiga cikin soro, na sami dukan koran da ke ciki an yi su ne da zinariya da azurfa. Yayin nan na ga Sarki zaune akan karagar mulki, hakimai da fadawa sun zagaye shi, suna sanye da tufafi wadanda ke dimauta wanda ya gansu. Yayin da na kusata da Sarki, na gan shi akan karaga abar aikatawa da lu’ulu’u da jauhari, ko wace fuska ta na haske tamkar taurari. Da tufafi a jikin Sarki zanannu da zinariya, da wasu dakaru mutum uku, daya a kowane gefe da kuma daya a bayansa, kowanensu na rike da zararren takobi, duka suna cikin siffar duwatsu. Yayin da na ga haka hankali na ya tashi da ikon Allah. Na shiga cikin gida, na iske sarauniya da adon lu’ulu’u mai yawa a jikinta, ta saka hula a kanta wacce aka yi wa ado da zinariya da jauhari, da wata babbar sarka ta zinariya a wuyanta. Ga kuyangi, kowace da dangin kayan ado dabam a jikinta, suna masu yin hidima ga sarauniya, duka an shafesu bakaken duwatsu. Na shiga wata budaddiyar kofa na ga matakai masu hawa zuwa sama, na tattaka su na hau sama. Na samu wuri shimfidadde da shimfidun darduma mai tasuhi, da gado na marmar an yi masa ado da zinariya da azurfa, da katifa akan gadon. Na ga wani haske yana tashi daga wani bangare na wannan daki, na iske jauhara tamkar kwan jimina, ita ce mai hasken. Na yi al’ajabi, matukar al’ajabi, na dukiyar da ke cikin wannan gida. Na ga fitilu a kunne cikin wani daki, na shiga ban ga kowa a ciki ba, na ce a raina, babu makawa wani mai rai ne ya kunna wadan nan fitilu. Na zama ina bincike cikin wannan gida, na dulmiya cikin tunani har dare yayi. Na yi nufin fita in koma inda jirgimmu, na kasa gane kofar fita. Na juya ga dakin da na ga gado a ciki, na haye kan gado na rufa da mayafi domin inyi barci, na kasa. Can zuwa tsakiyar dare, ina kwance na kasa barci, sai na ji am fara karatun Alkur’ani da wata murya mai dadi. Na sauko daga kan gado, na fito, sai na ji karatun na fitowa ne daga dakin da na samu fitilu a kunne. Na zo a hankali na leka cikin dakin, sai na ga saurayi a zaune kan shimfida, mai kyakkyawar magana, da Alkur’ani a gabansa yana karantawa. Na yi mamaki da ya kubuta daga sauran jama’ar wannan birni da aka mayar da su duwatsu. Hm Zan Dakata An an Saikuma Allah Ya kaimu Gobe Zamu Cigaba Admin AA Misau Ke Magana Guyson Kenan Suleiman Zidane Kd 012. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA . Copied AA Misau Ke Magana Guyson Kenan . Labarin Yarinya Shugabar Yan Mata (2) . Yarinya shugabar yan mata, ta ci gaba da labarinta da cewa: Bayan na gama kallon abin mamaki, da ikon Allah, a cikin gidan nan, sai na yi nufin fita domin in koma inda yan uwana. Na nemi hanya na rasa, sai na koma dakin da na ga gado da shimfida. Na haye gado na yi kwance, da nufin in yi barci, amma ya gagara. Can zuwa tsakar dare, sai na ji karatun Alkur’ani na fitowa, daga cikin dakin da na ga fitilu a kunne, da wata irin murya mai dadi. Na tashi na nufi wannan daki, sai na ga wani saurayi ne yake wannan karatu. Na yi mamakin ganin cewa shi kadai ne ya tsira a cikin wannan birni, ba a mayar da shi dutse ba. Na shiga na yi masa sallama. Ya dakatar da karatunsa, ya juyo ya dube ni, sannan ya mayar mini da sallama. Na ce da shi, na roke ka, don girman wannan littafi da kake karantawa, ka yi mini bayani a kan tambayar da zan yi maka. Ya yi murmushi ya ce: Ki labarta mini dalilin zuwan ki wannan gari namu, har kika shigo wannan gida, sannan in labarta miki duk wani jawabi da za ki tambaya gare ni. Na ba shi labarina, da na yan’uwana, da kuma niyyarmu ta zuwa birnin Bisira wurin fatauci, da yadda muka bace hanya har muka iso wannan birni. Ya yi al’ajabi, gayar al’ajabi. Yayin nan ni kuma na tambaye shi bayanin wannan birni, da abin da ya sa aka shafe su zuwa duwatsu, da kuma dalilin da ya sa shi ba a shafe shi dutse ba. Ya ce: Ki jinkirta mini. Ya nade takardu, ya saka su a cikin jikka ta hadalashi, ya zaunar da ni a gefensa. Na yi duba izuwa fuskarsa, na gan shi tamkar farin wata, mai kyawawan siffofi, da tattausan lafazi, mai kwarjini ga magana, madaidaicin tsayuwa, matsakaicin kundukuki. Na yi duba zuwa gare shi, dubar da ta azabtar da zuciyata, son shi ya huru, tamkar wuta, a cikin zuciyata. Na yi burin ina ma ya zamanto mijina. Na ce da shi, ya shugabana, ka yi mini bayani a kan abin da na tambaye ka. Ya ce: Na ji, na dauka. Sannan ya fara ba ni labari kamar haka: Ki sani, wannan alkarya birnin ubana ce, shi ne wanda ki ka gani a cikin wannan fada, da dukkan jama’ar da ke cikinta, da dimbin dukiyar da Allah ya ba su. Kuma Sarauniyar nan da ki ka gani, ita ce uwata. Jama’ar wannan gari, da Sarkinsu duka, sun kasance majusawa ne. Suna bauta wa wuta, suna barin bauta wa Allah Mai iko. Sun kasance suna rantsuwa da wuta, da haskenta, da inuwarta mai kuna. Ubana ya kasance ba shi da da tsawon lokaci, sai Allah ya arzuta shi da ni. Bayan na fara girma, ya bayar da ni ga wata tsohuwa mai reno, ya ce: Ki rike shi, ki rene shi, ki koyar da shi dabarun addinimmu. Tsohuwar nan ta kasance mai yawan shekaru ce, ta san ilimi na taurari, da na zaman duniya, da dukkan ilimomi. Ta kasance musulma ce, ta bayar da gaskiya ga Allah da Manzonsa a boye. Tana shiryar da mutane addinin musulunci ba tare da sanin Sarki ba. Ta rike ni, tana koyar da ni addinin Islama, maimakon addinin bautar wuta. A wurin ta na koyi tsarki, da farillar alwala, da salla. Ta koyar da ni karatun Alkur’ani. Yayin da ajalinta ya yi, ta ce da ni: Ya dana, ka boye wannan al’amari ga ubanka, kada ka sanar da shi, ya kashe ka. Bayan tsohuwa ta mutu, na ci gaba da bauta wa Allah a boye. Mutanen gari kuwa suka kara kafircinsu, da butulcinsu, suka kara zurfafa a cikin sabon Ubangiji. Suna nan cikin wanan hali, sai wata rana, daga cikin ranaku, suka ji mai kira yana kira da madaukakin sauti, tamkar tsawar aradu. Na nesa da na kusa duka sun ji wannan murya tana cewa: Ya mazauna wannan birni! Ku juya zuwa ga barin bautar wuta! Ku bauta wa Sarki Mai iko, wanda yake saukar muku da ruwa daga sama, ya ba ku dukiya da abinci! Mutane duka suka tsorata da jin wannan murya, da gargadin da ta yi musu. Suka tafi wurin ubana, Sarki, suka ce da shi: Ya Sarki, mene ne wannan sauti, mai tsanani, da muka ji ya tsoratar da mu? Ya ce: Kada jin wannan sauti ya tsorata ku, kada ku juya ga barin addininku na bautar wuta. Mutane suka dauki maganar ubana, suka ci gaba da bautar wuta. Basu gushe ba suna ci gaba da bauta wa wuta, da yin butulci ga Allah Madaukakin Sarki, tsawon shekara guda da jin sautin nan na gargadi. Aka kara gargadin su da barin bautar wuta, ba su bari ba. An yi musu wannan gargadi sau uku, kowace shekara sukan ji wannan murya mai gargadi, har shekara uku, amma ba su bar bautar wuta ba. Ba su gushe ba suna madurkusa, wurin bautar wutarsu har masifa ta saukar musu. Abin ya faru ne wata rana bayan hudowar alfijir, aka shafe su zuwa babbakun duwatsu, haka nan dabbobinsu, wani bai kubuta daga mazauna wannan birni ba, face ni. Daga ranar da wannan abu ya faru, ina bisa ga wannan hali, na karatun Alkur’ani. Na tabbata a kan haka, har zuwa wannan lokaci da kika same ni. Yarinya ta ci gaba da ba Halifa da sauran jama’a labarinta, ta ce: Ya Sarkin musulmi, lokacin da na ji labarin saurayi, da dalilin da ya sa aka mayar da mazauna wannan birni duwatsu, na yi mamaki, matukar mamaki. Sannan na tambayi saurayi, na ce da shi: Ya shugabana, yalla ko za ka bi ni zuwa garimmu, ka hadu da masana, ka karu da iliminsu, ni kuma in zama kuyangarka? Ina da jirage madaukaka da ake zuwa mini fatauci, da dukiya mai tarin yawa. Watakila Allah ya turo mu wannan birni ne naku domin mu tafi da kai zuwa garimmu. Na yi ta lallashin sa dai, har ya yarda zai tafi tare da mu. Bayan gari ya waye, muka tashi, ni da saurayi, muka shiga cikin taskoki, muka debo daga dukiya, abubuwa masu saukin dauka amma masu tsada. Muka fito daga gidan, muka kama hanyar zuwa inda jirgimmu ya ke, a bakin bahar na garin. Muka hadu da bayina, da mai jirgi suna nema na. Yayin da suka gane ni, suka yi farin ciki. Suka tambaye ni inda na shiga, tun jiya suna nema na. Na labarta musu da abin da na gani, da kuma kissar mutanen wannan birni, da kuma dalilin da yasa aka shafe su. Suka yi mamaki. Yayin da yan’uwana suka ga wannan saurayi, da irin kyawon da Allah ya yi masa, sai suka yi kishi na, suka hassade ni, suka kulla makirci a cikin zuciyarsu, amma ni ban san nufinsu ba. Muka shiga cikin jirgi. Muka zauna muna jiran iska, har ta yi mana dadi. Muka saki jirgi, muka nausa cikin bahar, muka tasamma jahar da birnin Bisira ya ke. Yan’uwana suka tambaye ni, muna cikin zance, suka ce da ni: Ya yar’uwarmu, me kike nufi da wannan kyakkyawan saurayi? Na ce da su, Ina so in aure shi, ya zamanto mijina, kuma in damka masa amanar dukiyata, amma sai idan ya yarda. Bamu gushe ba muna tafiya, iska ta yi mana kyau, har muka fita daga bahar abar tsoro, muka shiga bahar mai aminci. Muka tafi kwanaki kadan, har muka kusato Bisira, gine-ginenta suka bayyana a gare mu. Lokacin da dare yayi, muka shiga barci, yan’uwana suka tashi, suka dauke mu, ni da saurayin nan da shimfidummu, suka kunduma mu cikin bahar. . Zan dakata anan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba Admin AA Misau Ke Magana Guyson Kenan Suleiman Zidane Kd 013. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA . Copied AA Misau ke magana Guyson kenan . Labarin Yarinya Shugabar Yan Mata (3) . Yarinya shugabar yan mata ta ci gaba da labarinta da cewa: Muka ci gaba da tafiya a cikin bahar, kwana da kwanaki, har muka fara hango gine-ginen birnin Bisira. Wata rana da dare, jirgimmu na tafiya a cikin bahar, barci ya dauke mu duka, sai matukin jirgin ne kawai ke ta faman tuki. Sai yan uwana suka lallabo, suka dauke mu, ni da saurayi da shimfidummu, suka kunduma a cikin ruwa, jirgi yayi gaba. Allah ya nufa da saurayin nan bai iya ninkaya ba, nan take ya dulmuye a cikin ruwa yayi shahada. Ni kuwa, sai Allah ya koro mini da wani itace, na kama shi na hau, iska ta yi ta tura ni har na zo bakin gabar wani tsibiri, na taka na shiga cikin tsibirin. Ban gushe ba ina tafiya cikin wannan tsibiri har gari ya waye, da na dubi kasa sai na ga sawun kafar dan Adam, amma akwai alamun sawun ya dade. Yayin da rana ta fito, na cire tufafina na shanya su a rana. Ina zaune gindin wata itaciya ina jiran tufafina su bushe, sai na hangi wasu macizai guda biyu, sun nufo inda na ke a guje, daya na biye da daya. Da suka iso wurina, sai na lura da cewa daya macijin ya biyo dayan ne yana neman ya hallaka shi. Wanda aka biyon sai ya nufo inda na ke, ga alama kamar yana neman taimako daga gare ni. Sai na dauki wani babban dutse nan kusa da ni, na dubi macijin da yake neman hallaka dan uwanshi, na kwantsama masa shi a kai. Nan take ya mutu. Macijin da aka biyo kuwa da ya ga na kashe abokin fadansa, sai na ga ya fito da fuka-fukai, ya tashi sama, ya kada cikin sararin Subuhana, har ya bace wa ganin idona. Na cika da al’ajabin wannan abu. Na sa tufafina, na ci gaba da tafiya har rana ta yi zafi. Na kwanta a karkashin wata itaciya domin in dan sarara, sai barci ya dauke ni. Yayin da na farka daga barci, sai na ga wata kyakkyawar yarinya tana yi mini tausa ga kafafuna. Na yi zumbur na tashi zaune, na ce wace ce ke? Yarinya ta ce, haba ya shugabata, amma kin cika mantuwa, yanzu har kin manta ni? Ke ce wadda kika aikata mini alheri, wanda ba zan taba mantawa da shi ba har tsawon rayuwata. Ke ce kika kashe makiyina wanda yayi niyyar ya halaka ni, ba domin kin cece ni daga gare shi ba, da tuni ya kashe ni. Ni ce macijin nan da kika taimaka dazu. Ni aljana ce, macijin nan ma aljani ne, shi makiyina ne, babu wanda ya kubutar da ni daga gare shi, face ke, hatta aljanu yan uwanmu tsoronsa suke ji. Yayin da kika kubutar da ni daga gare shi, na kada cikin iska, na tafi zuwa ga jirgin nan da yan uwanki suka jefar da ke daga cikinsa. Na kwashe dukan abin da ke ciki na dukiya, na kai miki shi gidanki, na dulmiyar da jirgin. Yan uwanki kuwa, na sihirce su karnuka, babbakun karnuka. Ni, na san dukan abinda ya gudana tsakaninki da su, amma saurayinki ya halaka cikin ruwa, na yi nema ko gawarsa ban gani ba, ban san abinda Allah ya nufa da shi ba. Bayan aljana ta gama ba ni labari na abinda ya faru da yan uwana, ta dauke ni tamkar kibtawar ido, ta ajiye ni a cikin gidana. Na samu dukagidana. Na samu dukan dukiyata, ko allaura ba ta bata ba a ciki. Sannan kuma na ga karnuka biyu a daure. Yayin nan aljana, macijiya, ta ce da ni cikin kakkausar muryce da ni cikin kakkausar murya: Da girman rubutun nan da ke jikin zoben Annabi Sulaimanu, idan ba ki bugi kowace daya daga cikinsu, a cikin kowane dare, bulala dari uku ba, babu rangwame, zan zo in yi miki azaba mafi tsanani daga tasu, in maishe ki tamkar su. Na ce, na ji, na dauka! Ban gushe ba, ya Sarkin Musulmi, ina dukan su wannan duka, ina kuma jin tausayinsu bayakuma jin tausayinsu bayan na gama dukan nasu. Wannan gama dukan nasu. Wannan shi ne labarina da wadan nan karnuka, ya Sarkin Musulmi. Halifa da sauran jama’a suka yi mamakin wannan labari na yarinya, mamaki mai yawa. Yayin nan Halifa ya yi umurni da a rubuta wannan labari a ajiye shi domin ya zama abin misali ga al’umma mai zuwa. Sannan ya dubi yarinya mai jiran kofa ya ce, ki labarta mana da abinda Zan dakata anan saikuma Allan ya kaimu gobe zamucigaba Admin AA Misau ke magana Guyson kenan 08161272634 014. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA . Copied AA Misau Ke magana . Labarin Yarinya Mai Jiran Kofa . (1) Bayan yarinya shugabar yan mata ta kare bayar da labarinta, sai Halifa ya dubi yarinya ta biyu, mai jiran kofa, ya ce, ki labarta mana da abinda ya same ki na daga tabon bulala da muka gani a jikinki. Yarinya ta fara bayar da labarinta, da kuma dalilin tabon bulala da ke jikinta, ta ce: Ya Sarkin Musulmi, ubana ya kasance attajiri ne, ya mallaki dukiya mai tarin yawa wadda Allah kadai ya san yawan adadinta. Kuma na kasance ni kadai ce ‘ya tasa. Bayan ya mutu, na gadi dukkan dukiya tasa. Bayan yan shekaru kadan na yi aure. Na auri wani saurayi wanda shi ma ubansa ya mutu ya bar masa gadon dukan dukiyarsa. Bayan aurenmu da shekara guda, sai Allah ya yi masa rasuwa. Na gada daga gare shi dinari dubu tamanin da gidan da mu ke ciki, shari’a ta bar mini. Bayan na gama takabarsa, na sa aka dinka mini riguna guda goma, aka kawata kowace riga da kayan ado kala-kala, a takaice dai kowace riga sai da aka kashe dinari dubu wurin dinka ta. Ina zaune a gidana, wata rana sai ga wata tsohuwa ta shigo, mai daurarriyar fuska, mai nadadden goshi da nitattsun idanu, da wawilon baki, harshenta na rawa, wuyanta karkatacce tamkar da wakar wani mawaki da yake cewa: “Muguwar tsohuwa mai sanar da Ibilis da abin da bai sani ba, a cikin aikinta mafi sauki ta kan dabaibaye alfadara dubu da abawar tautau da aka wadarta. Muguwar tsohuwa mai halasta haram da kaifin zamba da kissarta, da za a auna makircinta da nauyin dutsen Uhudu da ya rinjaye shi.” Yayin da tsohuwa ta shigo wurina, ta yi mini sallama, na amsa mata. Sannan ta durkusa ta gaisheni da girmamawa, ta ce da ni, ‘yata, na zo ne in nemi wata alfarma a gare ki. Yarinya ta kasance a gare ni, yau ne kuma daren amarcinta, ina so ki sami ladarta da tawa, ki hallarci zaman amarcinta, ki zamanto bakuwarta ta musamman, ita mai yawan tunani ce domin rashin gata, ba mu da kowa sai Allah madaukakin Sarki. Yayin nan tsohuwa ta yi kuka, ta sumbaci kafafuna. Tausayinta ya kama ni, na yanke shawara zan karbi goron gayyatarta. Na ce da ita, na ji na dauka. Ta ce da ni, ki shirya da isha’i zan zo mu tafi tare da ke. Yayin nan ta sumbaci hannuna ta fita. Na tashi na yi wanka, na yi kwalliya sosai na shirya jikina tsaf, na debi kudi masu yawa wanda zan ba amarya, na zauna ina jiran isowar tsohuwa. Jim kadan sai ga ta, ta gabato ta ce da ni, ya shugabata tashi mu tafi, jama’a na can duk sun hallara, na shaida musu da zuwanki, sun yi farin ciki da kasancewarki babbar bakuwa ta musamman, suna can suna jiran zuwanki. Na tashi na bi tsohuwa a baya, muna ta tafiya tinkis-tinkis har muka shiga cikin wani kwararo, da shigarmu kwararon na ji wani irin kamshin turare na tashi a cikinsa. Muka nufi kofar wani katafaren gida, muna dada dosar gidan kamshin nan na karuwa, har muka iso kofar gidan. Na gan shi gida ne ginanne na kasa, an adanta bayansa da zane. Muka ishe masu gadin kofa a tsaye. Da suka gan mu sai suka bude mana kofa muka shiga. Muka ishe zaure, an rataye fitulu a kowace kusurwa ta zauren suna ci, suna haske tamkar rana. Muka wuce cikin gidan muka shiga cikin wani soro, muka ishe shi da shimfida ta kilisai masu taushi, ga fitulu ko’ina suna haske tamkar rana. Ga kuma gado na mirmir an yi masa ado da lu’ulu’u da jauhari, an lullube shi da shifida Siniya da hadalashi namusiya. A zaune akan gadon, na ga yarinya cikin sitira, ka ce ita farin wata ce a cikin taurari. Tana gani na, ta sauko daga kan gado ta tare ni da murna da farin ciki tana cewa, maraba, marhabin da ‘yar uwata da ta zo ta debe mini kewa, ta faranta zuciyata. Ta kama hannuna ta zaunar da ni akan gadon nan, sannan ita ma ta zauna kusa da ni, tsohuwa kuwa ta fita ta bar mu. Bayan mun zauna, yarinya ta dube ni ta ce, ya ‘yar uwata, aminiyata, ina da dan uwa wanda ya gan ki wata rana, ban san lokacin ba, ya ji yana son ki da aure. Shi saurayi ne mafi kyawo daga gare ni, zuciyarsa ta so ki, so mai tsanani, ya rasa yadda zai yi ya bayyana miki. Ya ba wannan tsohuwa kudi ta shirya wannan hila a gare ki domin ki yarda ki zo nan gidan dan uwana, shi kuma ya sami damar da zai bayyana miki abun da yake cikin ransa. Dan uwana yana son ya aure ki bisa ga sunnar Ma’aiki, babu aibi ga halal. Ko kin yarda na kira shi domin ku daidaita da juna? Yayin da na ji zancen wannan yarinya, na dubi kaina, na ga na abku a cikin gida, ga masu gadi tsare da kofa, babu hanyar guduwa. Na ce da ita na yarda. Ta yi farin ciki, ta tashi ta bude wata kofa da take boye a cikin soron. Na ga saurayi ya fito daga cikin wani daki. Wannan saurayi da kyau ya ke tamkar wakar wani mawaki da ya ke cewa: “Alheri ya yawaita ga Allah da ya yi baiwa a gare shi, ya halicce shi, ya daidaita shi, ya tara masa dukkan kyawo, ya sa dukkan talikkai su dimauta da ganin kyawonsa. An rubuta kyawo karkashin kundukukinsa, mun shaida babu birbishinsa da kyawo a cikin talikai” Yayin da na dube shi, nan take kibiyar sonsa ta daki zuciyata, na ji babu wanda na ke so kamar shi. Lokacin da ya shigo sai ya sami kujera ya zauna. Ya gabatar mini da bukatarsa ta son aurena, na amince da ita. Bayan an daura mana aure da wannan saurayi, a daren amarcina muna zaune tare da shi, sai ya dube ni ya ce, amaryata ina so ki yi mini wani alkawari, alkawarin kuwa shine, zuciyarki ba za ta taba karkata ga wani na ba, muddin ina raye kuma a matsayin mijinki, domin ni na kasance mai tsananin kishi ne. Na ce da shi na yarda da wannan alkawari ya shugabana. Ya dauko Alkur’ani mai tsarki ya ce in rantse akan wannan alkawari. Na rantse masa da ba zan kula ko wane da namiji ba. Na zauna tare da mijina, cikin jin dadi da annashuwa har tsawon wata guda. Wata rana na nemi izini ga mijina, ina so in tafi kasuwa in siyo wadansu zannuwa, ya yi mini izini da in tafi. Bayan na rufe jikina kaf da tufafi, na riki tsohuwa domin ta raka ni zuwa kasuwa. Muka tafi har muka iso cikin kasuwa. Tsohuwa ta ja ni zuwa rumfar wani yaro tajiri mai sayar da zannuwa na ado. Da muka isa muka yi masa sallama, bayan ya karba muka sheda masa cewa mun zo ne domin sayen zannuwa, na ce ya kawo mana zannuwan da babu irin su wajen kyau a cikin shagonsa, komai tsadarsu. Ya ce, to. Ya kawo mana kujeri muka zauna, shi kuma ya shiga cikin shago domin zabo mana kalar zannuwan da muke so. Bayan saurayin nan ya shiga cikin shago, sai tsohuwar nan ta dinga yabonsa da koda shi a wuri na. Tana cewa ai wannan yaro mutumin kirki ne, yana da ladabi, ubansa ya mutu ya bar masa dukiya mai yawa. Na dube ta na ce, ba na bukatar ki yabe shi a wurina, muradina mu sayi abin da ya kawo mu mu juya zuwa gida. Bayan yaro ya dawo da zannuwa, na zabi wadan da na ke so, na ce su yi ciniki da tsohuwa, suka yi ciniki, na ba tsohuwa kudi na ce ta ba shi. Da ta ba shi kudin sai ya ki karba, ya ce, haba wannan shi ne zuwanku na farko shagona, bai kamata na karbi kudinku ba. Tsohuwa ta ce idan bai karba ba me ya kamata mu yi? Na ce mu mayar masa da zannuwansa, mu tafi wani shago mu siya. Yaro ya dube ni ya ce, wallahi ba na karbar ko daya, dukkan abin da ke cikin shagon nan, sumba daya da zan yi miki ta fi shi. Da za ki amince na sumbace ki, sumba daya, da na ba ki dukkan kayan da ke cikin wannan shago nawa. Na ce, tir da kai! Allah ya kare ni da in ha’inci mijina, shin ko ba ka san cewa ni matar aure ce ba? Tsohuwa ta dube ni ta ce, haba ‘yata! Don dai sumba guda me zai same ki, ki yarda da wannan yaro, hakika ya jarrabu da son ki, ki ji tausayinsa ki biya masa da bukatarsa. Na ce da ita, hala kin manta da cewa ni rantsattsiya ce daga kula wani namiji ba mijina ba? Ta ce da ni, bar shi ya sumbace ki sumba daya, babu abin da zai same ki, ya ‘yata da me sumbatar ki za ta amfane shi? Abin da zai yi cikin yan dakiku ya gama, mu kuwa mu yi tafiyarmu. Tsohuwa ba ta gushe ba tana kyautata mini wannan abu tana gusar da laifin aikata haka har na amince da bukatar yaro. Na rufe fuskata da mayafi, yaro ya zo kusa da ni, ya sumbaci kundukukina ta cikin mayafi. Yayin da ya sumbace ni, sai ya gatsa mini cizo da hakoransa, cizo mai zafi har sai da ya cire fata daga kundukukina. Na fadi kasa somammiya saboda zafin wannan cizo. Yayin da na farka, sai na ga tsohuwa rungume da ni, shago a rufe, babu yaro babu dalilinsa. Tsohuwa ta ce, abin da Allah ya so shi ne mai yiwuwa, wannan yaro ya cuce mu. Ki tashi mu

Chapter 4 of 5