Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 01. BIRNIN DUWATSU: Hikayar Abdullahi dan Falilu da 'yan uwansa Copied AA Misau Ke Magana E-book Suleiman Zidane Kd 08161272634An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ Wata rana Halifa Haruna Rashid na duba harajin da sarakuna da hakimansa suka aiko da shi cikin wannan shekara, sai ya lura cewa Sarkin Basara ne kadai bai aiko da nasa harajin ba. Don haka sai Halifa ya tara 'yan majalisarsa. Da suka taru sai ya ce, "Ina Waziri Ja'afaru?" Waziri Ja'afaru ya zo kusa ga Halifa ya tsaya ya ce, "Ga ni, Allah ya daukaki mulkinka." Halifa ya ce, "Harajin kowane sarki da ke karkashina ya shiga baitulmali, amma babu harajin Basara." Ja'afaru ya dukar da kai ya ce, "Ya Shugaban Muminai, watakila akwai wani babban al'amari da ya faru ga Sarkin Basara da ya sa shi sha'afa da aiko da nasa harajin." Halifa ya ce, "Yau kwana ashirin da gama tattara haraji, idan har wani al'amari ya same shi, mi ya sa bai aiko mana ba, domin mu san halin da yake ciki?" Waziri ya amsa masa, "Allah ya taimake ka, ina ganin mu aika masa da manzo wanda zai dawo mana da labari." Halifa ya ce, "Ka tura Abu Is'haka al-Mausili, daya daga cikin amintattunmu." "Na ji, na amince. Ina mai biyayya ga Allah, ina mai biyayya gare ka, ya Shugaban Muminai." In ji Ja'afaru. Nan da nan sai Ja'afaru ya sa aka kira masa Abu Is'haka zuwa gidansa. Da ya zo sai ya rubuta takarda a madadin Halifa, ya ba shi ya ce, "Karbi wannan takarda ka kai wa Abdullahi dan Falilu, Sarkin Basara. Halifa ya duba dukkan harajin da sarakunansa suka aiko amma bai ga na Sarkin Basara ba. Idan ya tattara harajin ka karbo ka dawo mini da shi, idan kuwa bai tattara ba, to ka zo tare da shi, ya fada wa Halifa da bakinsa abin da ya hana shi aiko da nasa haraji." Abu Is'haka ya ce, "Na ji, na amince." Waziri Ja'afaru ya hada shi da mahaya dubu biyar suka nufi Basara. Yayin da suka yi kusa da birnin Basara sai Abdullahi dan Falilu ya sami labarin zuwansa. Nan take ya fita da runduna ya tarye shi, suka dawo cikin birni tare, har suka isa fada. 'Yan rakiya kuma sai suka kafa tantuna a bayan gari, aka aika musu da dukkan abin da suke bukata na abinci da abin sha da shimfidu. Lokacin da Abdullahi dan Falilu da Abu Is'haka suka shiga fada, sai Abu Is'haka ya zauna bisa karaga, ya zaunar da Abdullahi dan Falilu kusa gare shi. Wazirai da fadawa kowa ya zauna gwargwadon matsayinsa. Da fada ta nutsu, sai Abdullahi dan Falilu ya mike. Bayan ya yi sallama da gaisuwa ga Abu Is'haka sai ya ce, "Ya shugabana, ko akwai wani sako ne da ka zo mana da shi?" Bako ya amsa, "I. Na zo ne domin na karbi harajin kasarka. Kowa ya aika da harajinsa amma Halifa bai ga naka ba, ga shi har lokacin karba ya wuce." Abdullah dan Falilu ya yi murmushi ya ce, "Allah Sarki, an ce rashin sani ya fi dare duhu. Da ka sani da ba ka walar da kanka garin zuwa ba. Haraji na nan na kammala hadawa, da gobe nake niyyar aikawa da shi. Amma tun da ka zo zan damka shi ga hannunka, ka wuce wa Halifa da shi. Yanzu sai ka zauna ka huta zuwa kwana uku, mu shirya maka liyafa ta musamman domin karramawa da kuma girmama Halifa, a kwana na hudu sai na ba ka harajin tare da tsarabar da za ka tafi da ita." Abu Is'haka ya ce, "Babu laifi ga wannan." Daga nan sai Abdullahi dan Falilu ya sallami kowa. Da aka watse sai ya ja bakonsa zuwa wani kayataccen soro da babu kamarsa ga kyawu. Ya sa aka jera akussan abinci domin Abu Is'haka da manyan na hannun damarsa. Suka ci suna raha har suka bankare cikannansu. Da suka koshi sai aka kawar da akussa aka jera gorunan gahawa da abin sha. Suka yi ta sha suna hira, ba su ankara ba har dare ya raba. Aka shirya wa Abu Is'haka shimfida mai taushi bisa gadon zumarrazi da aka shafe da ruwan zinariya mai kyalkyali. Admin AA Misau Ke Magana Suleiman Zidane 02. HIKAYAR BIRNIN DUWATSU: Copied AA Misau Ke Magana . Suka yi ta sha suna hira, ba su ankara ba har dare ya raba. Aka shirya wa Abu Is'haka shimfida mai taushi bisa gadon zumarrazi da aka shafe da ruwan zinariya mai kyalkyali. Abullahi dan Falilu ya kwanta kusa gare shi, amma a nasa gadon daban. Abu Is'haka ya kwanta kamar zai yi barci amma barcin bai dauke shi ba. Sai ya yi ta karatu a cikin zuciyarsa, wani lokaci kuma sai ya rera baitoci a kan sha'anin rayuwa. Da ma shi mutum ne gwanin hikima, ga shi kuma gwanin bayar da labari, shi ya sa Halifa ke son sa kwarai da gaske har ya sanya shi daya daga cikin amintattunsa. Haka ya ci gaba da karatunsa yana rera wakoki har zuwa talatainin dare. Daga nan sai ya ga Abdullahi dan Falilu ya tashi daga kan gadonsa, ya daura damara ga kugunsa, ya bude wani dan akwati ya dauki bulala da shama'a kunnaniya, ya fice daga cikin soron da suke kwance, yana tsammani bakonsa barci yake yi. Yayin da Abu Is'haka ya ga haka sai mamaki ya kama shi, ya ce a cikin ransa, "Ina Abdullahi dan Falilu za ya da bulala cikin dare? Yalla ko yana nufin ya azabta wani. Bari dai na bi shi in ga abin da zai yi cikin wannan tsohon dare." Yayin da Abu Is'haka ya tashi ya bi bayansa yana sanda a hankali yadda ba za a ji tafiyarsa ba. Ya ga Abdullah ya bude taska ya fito da kabaki daga cikinta da tasoshi hudu a gabansa cike da waina da nama, da kasaken ruwa. Ya dauki kabakin ya tafi, Abu Is'haka ya ci gaba da bin sa a hankali, har ya shiga daki. Da Abu Is'haka ya ga ya shiga cikin daki sai ya ja ya tsaya daga bakin kofa, ya zama yana leken cikin dakin. Ya ga dakin mayalwaci, an shimfide shi da shimfidu na alfarma. A tsakiyar dakin an kafa gado na li'aji zananne da zinariya, a jikin gadon an daure karnuka biyu da sarkoki na zinariya. Abdullahi ya ajiye kabaki daga kuryar daki, ya zare damuttsansa, ya kwance kare na farko. Kare ya zama yana wutsilniya yana turmusa hancinsa ga kasa, ka ce shi yana sumbatar kasa ne gaba ga Abdullahi, yana kuka kasa-kasa da murya mai mai ban tausayi. Duk wannan abu da karen nan ke yi, Abdullahi bai kula ba, ya rife shi ya buga ga kasa, ya daure kafafun. Ya zari bulala ya sabkar masa da bugu, bugu mai karfi ba da tausayi ba. Kare ya yi ta wutsilniya yana kuka, kuka mai tsanani, amma Abdullahi bai dakata da bugun sa ba har sai da ya ji ya bar motsi ya suma. Yayin nan ya ja shi kasa ya kai ga gadon nan ya daure shi ga bigirensa. Ya kwance kare na biyu, ya aikata bugu gare shi kamar yadda ya yi wa na fari. Daga nan sai ya ciro adiko ya riga goge musu jikinsu yana ba su hakuri yana cewa, "Kada ku rike ni da wannan abu, ba da son raina na aikata muku shi ba. Allah ya ba ku sauki ya kawo muku mafita." Ya ci gaba da yi wa karnukan nan addu'a yana shafa jikinsu. Duk wannan abu da ke faruwa, Abu Is'haka amintaccen Halifa na make bakin kofa yana leke da idanunsa yana kuma ji da kunnuwansa, yayi mamakin wannan abu matukar mamaki.Bayan karnuka sun farfado, sai Abdullahi ya jawo kabakin nan ya rika ba su abinci da hannunsa suna ci har suka koshi. Ya goge musu bakuna. Ya dauko kaskon ruwaya ya shayar da su. Daga nan sai ya dauki kabaki da bulala ya riki shama'a ya nufi kofar fita. Abu Is'haka ya yi sauri ya koma bisa gadonsa, ba tare da Abdullahi ya gan shi ko ya ji motsinsa ba, ya kwanta kamar yana barci. Abdullahi ya mayar da kabaki da kaskon ruwa a cikin taska, ya dawo cikin soro ya mayar da bulala cikin akwati, ya kwance damara, sa'annan ya kwanta bisa gadonsa. Abu Is'haka kuwa yana kwance ya kasa barci saboda tunanin wannan abu da ya gani, sai mamaki ke cin sa. Ya rika cewa a cikin ransa, "Ina mamakin dalilin wannan abu da na gani." Ba shi ya daina tunani da al'ajabi ba sai da gari ya waye. Yayin nan suka tashi suka sallaci sallar asubahi suka karya kumallo suka sha abin sha, sa'annan suka shirya suka fita fada.Zuciyar Abu Is'haka ta cika da tunanin al'amarin da ya gani mai ban mamaki, har aka yi fadanci aka tashi hankalinsa ba ya tare da shi, kuma bai tambayi Abdullahi dalilin wannan abu ba. A dare na biyu Abu Is'haka ya sake bin Abdullahi a baya, ya ga ya aikata wa karnukan nan abin da ya yi musu a daren jiya. Ya buge su da bulala, yashafe musu jiki yana ba su hakuri, sa'annan ya ba su abinci da abin sha. Hakakuma a dare na uku ya aikata musu. A ranata hudu sai Abdullahi ya kawo haraji ya ba Abu Is'haka tare da tsaraba mai yawa, suka yi ban kwana ya tafi, ba tare da ya tambayi sababin bugun karnuka ba, ya bar abin a cikin ransa.Kwanci tashi har ya iso birnin Bagadaza, ya ba Halifa haraji wanda ya tambayi dalilin jinkirin kawo shi. Abu Is'haka ya amsa masa, "Ya Shugaban Muminai, ko dana isa na tarar da ya gama tattara harajin har ya yi nufin aikowa da shi, da a ce ma na kara kwana daya ban isa ba, da na haduda manzanninsa a hanya. Amma ya Shugaban Muminai, na ga wani abu da ya daure mini kai, ya sanya ni cikin tunani da al'ajabi mai girma, tare da Abdullahi dan Falilu. Ban taba ganin wannan abu ko jin labarinsa ba tun da nake.""Wane abu ne wannan da ka gani mai ban mamaki, ya Abu Is'haka?" Halifa ya tambaya.Abu Is'haka ya amsa, "Na ga abu kaza da kaza." Ya kwashe labarin abin da ya ga Sarkin Basara na aikata wa karnuka cikin dare ya fada masa. Ya kara da cewa, "Hakana ga yana yi tsawon dare uku da na kwana tare da shi. Da farko sai ya bugi karnukan sai sun suma, sa'annan ya rika shafe jikinsu da kyalle yana rarrashi. Idan suka farfado sai ya ciyar da su abinci ya shayar da su ruwa. Ni kuwa ina make dagawajen dakin ina kallonsa, bai taba lura da ni ba."Halifa ya tambaye shi, "Ka tambaye shi dalilin wannan al'amari?"Abu Is'haka ya amsa, "A'a, Allah ya ja zamanin Sarkin Musulmi."Halifa ya cika da mamaki. Ya dubi Abu Is'haka ya ce, "Maza ka koma Basara ka taho mini da Abdullahi dan Falilu da karnukan nan biyu."Abu Is'haka ya sunkuyar da kai kasa ya ce,"Ya shugaban Muminai, ka dora mini aiki mai nauyi. Abdullahi ya girmamani ya kuma yi mini alheri mai yawa lokacin da nasauka gare shi. Wannan abu da na gani sirri ne gare shi da ba ya son kowa ya sani.Yanzu da wace fuska zan tinkare shi har nayi masa maganar karnukan nan duk da irin alherin da ya yi mini, Wallahi ina jin kunyar yin haka. Da zai yiwu, sai Sarkin Musulmi ya aika wani manzo da takarda yana umurtar Abdullahi ya zo tare da karnukan."Halifa ya yi murmushi ya ce, "Idan na aika wani zai iya musantawa ya ce, 'ni ba ni da wasu karnuka,' amma idan kai ka tafi ka ce masa, 'na gan su da idona' ba shi da ikon musantawa. Don haka dole kai za ka tafi kazo mini da shi da karnukan nan, idan kuwa ba haka ba ina yanka ka."Abu Is'haka ya ce, "Na ji, na dauka, ya Sarkin Musulmi, Allah ya agaje mu. Da ma an ce harshe shi ke yanka wuya. Laifina ne da na gaya maka wannan labari, amma inaso ka rubuta mini takarda da hannunka wadda zan ba shi."Halifa ya rubuta takarda ya ba shi, ya karba ya kama hanyar Basara. Yayin da Sarkin Basara ya ga ya komo nan da nan, sai ya ce, "Allah ya sa dai lafiya ka koma haka da wurwuri, ya Abu Is'haka? Ko harajin ne ya yi kadan Halifa ya ki karba?"Abu Is'haka ya dube shi cikin jin kunya ya ce, "Ya Sarki Abdullahi, harajinku ya cika daidai, Halifa ya karba cikin farin ciki. Amma ka gafarce ni saboda na ci amanar bakunta, wannan kuwa sharrin Shaidan ne!"Abdullahi ya tambaye shi cikin mamaki,"Wace amana ka ci tamu?""Ka sani kwana uku da na yi tare da kai, a cikin kowane dare nakan bi bayanka, ba tare da ka sani ba, har zuwa dakin da kake bugun wasu karnuka biyu. Wannan al'amari ya sa ni mamaki matukar mamaki,ni kuma sai na ji kunyar na tambaye ka. Yayin da na koma Bagadaza sai kaikayin baki ya ja ni, na gaya wa Halifa wannan labari. Da na san zai nemi na dawo na tafi da kai tare da karnukan da ban gaya masa labarin ba, to amma kaddara ta riga fata, babu wanda ya isa ya canja kaddarar Ubangiji. Ga takarda Halifa ya ce a ba ka, a ciki yana umurtarka da ka tafi gare shi tare da karnukan nan. Amma don Allah ka yafe mini wannan laifi da na aikata maka." Ya duka ya yi ta ba shi hakuri.Abdullahi ya yi jugum yana tunani, can sai ya ce, "Babu komai da yake kai Halifa ya turo ba zan iya karyata ka ba, domin kai abokina ne. Amma da a ce wani ne ba kai ba, ya fada wa Halifa wannan labari, da na musanta wannan al'amari, na ce wa Halifa karya yake yi, ni ba ni da wasu karnuka. Amma yanzu zan dauki karnukan mu tafi tare ko da hakan zai zama karshen rayuwata."Abu Is'haka ya kama hannun Abdullahi ya sumbata yana cewa, "Allah ya rufa maka asiri kamar yadda ka rufa mini asiri ba ka karyata ni ga Halifa ba."Abdullahi ya shirya tsaraba mai kauri da zai kai wa Halifa, ya dauki karnuka tare da shi, ya aza kowanne bisa rakumi ya daure shi da sarkar zinariya, ya tafi tare da Abu Is'haka har suka isa Bagadaza gaban Halifa. Abdullahi ya dauki kasa a gaban Shugaban Muminai, ya umurce shi ya zauna. Da ya zauna sai ya jawo karnukan nan biyu gaban Haruna Rashid, wanda ya tambaye shi, "Mene ne labarin wadannan karnuka, ya Sarki Abdullahi?" Karnuka kuwa sai sumbatar kasa suke yi gaban Halifa suna kada wutsiya kamar masu kawo kara gare shi.Halifa ya cika da mamaki, ya dubi Abdullahi ya ce, "Gaya mini labarin wadannan karnuka da abin da ya sa kake bugun su kowane dare, sa'annan kuma ka ba su abinci kana rarrashi."Abudllah ya dukar da kansa kasa a gaban Halifa ya ce, "Ya Halifan Allah, wadannan ba karnuka ba ne face samari biyu, ma'abuta kyawu da cikar halitta da kwarjinida daidaito. Su biyun nan duka 'yan uwana ne, uwarmu daya ubanmu daya."...... ...... ...... Admin AA Misau Ke Magana Suleiman Zidane Kd 03. HIKAYAR BIRNIN DUWATSU: . Copied AA Misau Ke Magana . Abdullahi ya dukar da kansa kasa a gaban Halifa ya ce, "Ya Halifan Allah, wadannan ba karnuka ba ne face samari biyu, ma'abuta kyawu da cikar halitta da kwarjini da daidaito. Su biyun nan duka 'yan uwana ne, uwarmu daya ubanmu daya."Halifa ya tambaye shi cikin mamaki, "Yaya dan Adam zai koma siffar kare?"Abdullahi ya amsa, "Ka yi mini izini, ya Shugaban Muminai, in labarta maka da gaskiyar labarinsu"Halifa ya ce, "Fada mini labarinsu, amma na hore ka da ka gaya mini gaskiya domin ita ce jirgin tsirar kowane mutum, ita ce alamar managarta daga cikin mutane."Abdullahi ya ce, "Ya Halifan Allah bisa ga bayan kasa, zan fada maka gaskiya a gaban wadannan karnuka, idan na yi gaskiya za su shaide ni, idan kuma na yi karya za su karyata ni a gabanka."Halifa ya dube shi, "Wadannan ai karnuka ne, ta yaya za su yi magana balle su gasgata ka, ko su karyata ka?"Abdullahi ya dubi karnuka ya ce, "Ya 'yan uwana, idan na fadi karya ku rauda kawunanku kuna kyibta idanu. Idan kuma na fadi gaskiya ku sunkuyar da kawunankukasa kuna lumshe idanu."Daga nan sai Abdullahi dan Falilu ya fara labari ya ce: Ya Halifa, ka sani mu uku muke 'yan uwan juna, uwarmu daya, ubanmu daya. Sunan mahaifinmu Falilu. An rada masa wannan suna ne saboda su biyu uwarsu ta haife su tare, 'yan tagwaye. Daya ya mutu nan take, mahaifinmu ya wanzu. Don haka sai mahaifinsa ya sanya masa suna Falilu, watau wanzajje.Mahaifinsa ya rene shi har zuwa girmansa,ya yi masa aure da mahaifiyarmu, sa'annan ya kwanta ya mutu. Yayin da mahaifiyarmu ta sami ciki sai ta haifi wannan dan uwan nawa na farko, aka sanya masa suna Mansur. Ta sake samun ciki, ta haifi wannan dan uwan nawa na biyu, mahaifinmu ya rada masa suna Nasiru. Da ta sake samun ciki na uku sai aka haife ni, mahaifina ya sanya mini suna Abdullahi. Mahaifinmu ya rene mu tare cikin tsananin kulawa har sai da muka isa munzalin mutane, sai ya kwanta ciwon ajali ya mutu. Ya bar mana gadon gida da rumfarsa ta kasuwa wacce take cike da dukiya ta daga dukkan tufafin Hindu, da na Rum, da na Hurassana, da wadansun wadannan, tare da tsabar kudi har dinari dubu sittin. Muka wanke gawar mahaifinmu, muka yi masa jana'iza, muka kai shi masaukinsa na karshe, muka gina kubba mai girma a wurin domin girmamawa gare shi. Muka gayyaci malamai wurin kabarinsa, suka yi ta sauke Kur'ani mai girma tsawon kwanaki arba'in domin nema masa gafara, da nema masa tsari daga shiga wuta. Bayan an yi sadakar arba'in sai na gayyaci dukkan tajirai da manyan gari na shirya musu walima, aka ci aka sha aka tumbatsa. Da aka gama cin abinci sai na mike na ce musu, "Ya ku mutane, ku sani cewa wannan duniya ba matabbata ba ce, lahira ita ce gidan dawwama. Girma da daukaka sun tabbata ga wannan wanda baya gushewa har abada. Shin ko kun san dalilin da sa ya sa na kira ku nan, a cikin wannan rana mai albarka?"Suka amsa mini, "Allah shi ne masani a dukkan abin da yake boye."Na ce musu, "Mahaifina ya mutu ya bar kudi masu yawa, to ban sani ba ko akwai wanda ke bin sa bashi daga cikinku. Idan akwai mai bin sa bashi sai ya yi magana yace, 'ina bin sa abu kaza da kaza' ni kuwa in biya shi saboda in sauke masa nauyin da ke kansa wanda bai sami saukewa ba."Dukkansu suka amsa mini, "Ya Abdullahi, hakika duniya gidan rudi ce, lahira ita ce gidan tabbata. Wane kinibibi zai sa mu ce muna bin mahaifinka bashi, don dai son abin duniya. Dukkanmu mun san cewa cin dukiyar marayu babban laifi ne. Allah ya ji kan mahaifinka da rahama, ba mu san mai bin sa bashi ba, shi ne ma ke biyar mutane da yawa. Mahaifinka ba abin da ya ke gudu irin cin bashi, sau da yawa mukan ji shi yana addu'a, 'Allah ka tsare da cin bashi, Allah ka da ka dauki raina da bashin mutane ga wuyana.' Dukkanmu shaidu ne, idan ya dauki bashin mutum, nan da nan yake biyansa ba tare da mai kayan ya matsa masa ba. Idan kuwa kayansa aka dauka bashi, to ba ya takura wa wanda ya amshi kayan, idan ma talaka ne sosai sai ya yafe masa. Idan kuma ba talaka ba ne kuma mutumin ya mutu bai biya shi ba sai ya ce, 'na yafe masa, Allah ya yafe masa laifukansa.' Don haka muna da tabbacin babu mai bin sa komai."Yayin da na ji haka sai na ce musu, "Na gode, Allah ya yi muku albarka." Daga nan sai na juya wurin wadannan 'yan uwa nawa na ce musu, "To kun ji, babu mai bin mahaifinmu bashi. Kun dai sani ya bar mana kudi masu yawa da gida da rumfa cike da kaya. Tun da mu uku ne, ke nan za a kasa dukiyar kashi uku kowa ya dauki kashi guda. Me kuka gani yanzu? Mu bar dukiyar yadda take muna juya ta tare, mu ci mu sha tare, ko kuwa a raba kowa ya dauki rabonsa ya shiga juyawa da kansa?"Suka ce mini, "Mun fi so a raba kowa ya dauki kasonsa."Abdull ahi dan Falilu ya dubi karnuka ya ce,"Haka aka yi, ya 'yan uwana?" Suka sunkuyar da kai kasa suka lumshe ido, suna ishara da cewa, "Haka ne."Abdullahi ya ci gaba da labari ya ce, sai na kira wakilin alkali, ya Shugaban Muminai, ya raba mana dukkan dukiyar da mahaifinmu ya bari da kudi. Gida da rumfa suka fada cikin rabona, saboda 'yan uwanasun ce sun fi son tsabar kudi. Dukkanmu muka amince da wannan rabo, 'yan uwana suka kwashi kudi cunkus, ni kuwa aka bar mini gida da rumfa da 'yan kudi kadan, wadanda na sayi kayayyaki na zuba

Chapter 1 of 5