keys dinsa da wayoyinsa ya fice
Ma'u kam ta kasa gaskata sauyin datake gani gun Oga Turawa
A wajen aiki anga sauyi wajen Bature, fuskarsa dauke da annashuwa sabanin yadda ke a hade kamar hadari
Haka Bature ya kasance ranar cikin farin ciki da annashuwa tareda jin dadi
Yanason kiran ma'u yaji ya ta kasance abun haushin shine baida numberta kuma abun ashsha ne ya kira a tura masa, haka yanaji yana kallo ya gagara samunta
Excuse ya dauka ya nufo gida tun lokacin tashinsa baiyiba
Ssai Ma'u tasha tarairaya da tattali gun Bature, a Baturensa yake a fuska amma gangar jikinsa sun bauta mata ssai ya shiga mata hidima
Misalin 9:30 na dare Bature ya gama shirin kwanciyarsa, yaxo ya rumgume Ma'unsa tsam a jikinsa yana shakar kamshinta mai rikita masa tunani, shiru yayi kamar yayi bacci yana shakar kamshin a hankali
Ma'u najin Bature yayi shiru, ita a ganinta bacci yayi ta janye jikinta daga garesa ta sauko a kan bed din a hankali, wai don kada ta tadashi, tayi hanyar barin falon don tana tsoron kada dare yayi dare Bature ya maimaita abunda yayi daxun
Tana gab da kama handle din kofar Bature daya kyaleta yaga iya gudun ruwanta yace
"Xanyi mutukar saba miki idan kika fice daga dakin nan"
Rintse ido Ma'u tayi cike da tsoro ta dawo ta kwanta nesa da Bature
A limshe da ido Bature yace
"Idan kika bari na biki inda kike abunda na miki daxun nafila ne"
Bbu shiri Ma'u ta mirgino ta shige jikinsa xuciarta na dukan uku uku
Bayan Sati Daya
Ssai Zahra ta shirya kanta tayi gyara na musamman ta fito fess
Ana washegari xata koma Abuja aka rangada mata kitso da lalle masu daukar hankali
Gun su Abba taje ta nemi afuwarsu kuma ta sheda musu gobe xata koma dakinta fatan alkhairi suka mata
Dataje gun Ammi kam cewa tayi
"Idan don Allah xaki koma Allah ya hada kanku xaina lfy, idan kuma wani sharrin xai kaiki Allah yasa kaikayi ya koma kan mashekiya"
Gidan Bature
Tun daga ranar da Bature ya kwashi gara, bbu abunda ya sake shiga tsakaninsa da Ma'u sai dai idan ya dibo xafi ya sauke da romance
Ssai Ma'u tanajin dadin kasancewa da Bature don ya gama tsayan xuciarta da xafafan romance dayake mata masu birkita mata lissafi
Sonshi ya mata mugun kamu, har addu'a take kada Allah yasa Zahra ta dawo sai dai kawai a tura mata takardan sakinta (kujimin Ma'u da bushewar ido)
Shiko Goga Bature ya mance da kowa da komai sai som Ma'u dake kara ninkuwa a xuciarsa, ssai yake kokarin koyawa Ma'u sonsa da kuma rage mata tsoronsa, kuma yana ganin ci gaba ssai don yanxu tana iya xama gefenshi ta sake sosai
Half gown ne a jikin Ma'u, ta tufke gashinta tana tsaye a jikin madubi tana ma kanta Murmushi
Da mamaki taje bakin window tana duba wayene yaxo don taji karar tsayuwar mota
Gabantane ya shiga dukan uku uku lokacinda taga Zahra ta fito daga motar tayi wani kyaun ban mamaki
Take Ma'u taji kuka yaxo mata
"Kukan uban me xakiyi? Xuwa xakiyi kisata kuka bawai ki tsaya kina mata kukaba, nuna mata xakiyi kin rigada kin rushe gomnatinta"
Xuciar Ma'u ya sanar da ita
Da sauri Ma'u ta fice xuwa main palo, xama tayi akan cushion kafart daya nakan daya ta dau wayarta ta kara a kunne
Tanajin motsin shigowar Zahra, duk da xuciarta ya tsinke amma ta dake tace
"Baby kenan kasan bbu abunda xan ajje maka sama da abunda kafi so, kaga yadda bakin abun dadinka suka kumbura suna jiranka kaxo ka sotsesu yadda ka saba"
Rashin jin takun Zahra ne yasa ci gaba da bayani don tasan Tarkonta ya kama kucciya
A shagwabe tace
"Amma Sweety a hankali xakayi ko, don wlh ban gama wartsekewa ba da na jiya"
Shiru tayi kamar mai sauraran bayani daga dayan bangare, daga bisani tace
"Toh Honey, bari naje bedroom sai muyi video call din na nuna maka kayan dadinka"
Mikewa Ma'u tayi tana kada jikinta ta nufi Bedroom dinta
Kukan kura Zahra dake tsaye saura kiris xuciarta ta buga don bakin kishi tayi ta nufi kan Ma'u gadan gadan
Ummu Subay'a❤
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻
1⃣9⃣
Jin hucin Zahra da Ma'u tayi a bayanta shi yasata rugawa da gudu ta shige dakinta tayi masa key
Bugun kufar Zahra take da karfi
"Don ubanki ki bude kofar nan, Ashe ke kamar' yar iskace da kin tsaya dana nuna miki yadda ake iskanci, bari Ya Baturen ya dawo yau xai xaba koni ko ke"
Sanda Zahra ta gaji don kanta ta wuce dakinta ta nata bambami
Haye kan bed dinta Ma'u tayi tana daria
"Hoohooohoo ni Ma'u, haka kawai xata sakamin hawan jini gwara na fara saka mata"
8pm Bature ya sauko palon cikin takunsa na katsaita, wuce Zahra dake xaune a falo taci kwalliya na alfarma yayi ya nufi dinning space
Kamar Zahra xatayi kuka ta mike ta bishi dinning space din
Kujera dake kallon nashi taja ta xauna ta marairace fuska tare da kissa tace
"Don Allah Sweety kayi hakuri, nasan ban kyauta ba wlh baxan sakeba"
Ko kallon inda take Bature baiyiba sai ma ci gaba da latsa wayarsa dayaci gaba
Daman tasan xa'a rina kukan kissa tasa
"Pls mana Dear, Allah baxan sake ba"
"Hakurin me kike bani? Me kikamin?"
Bature yayi maganar yana dialing number Ma'u
Ringing biyu yayi ta daga
"Sai naxo na daukoki"
Yana fadar haka ya katse wayar
Kishi ne ya turnuke Zahra
"Na maka laifi mana naki biyoka lokacinda ka nemi na biyoka"
Baki ya tabe yace
" kanki kikawa ba niba, kinga kanki xaki bawa hakuri "
Jin takun Ma'u ne ya hana Zahra magana
Black jeans da red bodyhug Ma'u tasa, sunyi matukar amsarta, daure gashinta tayi da black ribborn, fuskarta bbu wani kwalliya amma tayi kyau ssai
Cikin takun Jan hankali ta iso dinning space din, kujerar dake gefen Bature taja ta xauna
Satan kallon Zahra tayi taga tana mata mugun kallon, murmushi kasa kasa Ma'u tayi tace
"Ashe kin dawo Anty Zahra, Sannu da dawowa"
Mugun harara Zahra ta wurga mata
Baki Ma'u ta tabe ta shiga serving nasu
Wani kasada ta gwadayi na hada abincinta da Bature, addu'a take Allah yasa kada ya kobsata
Zahra ko ido ta xuba tana kallon ikon Allah, ita dai iya saninta tunda take bata taba cin abinci a plate daya da Bature ba, abun bakin ciki sai ga Ma'u xataci plate daya da Bature, kukane yaxo mata mai karfi, dakyar tayi jarumta ta danne kukan
Shima Baturen Mamaki ssai hakan ya bashi, amma da shike shi namijin dunia ne sai ya boye mamakinsa, yana jin jina wayo irin na Ma'u, mace komin kankantarta akwai kisisina da kissa a tare da ita
Karar spoons kawai ke tashi a dinning space din, bbu mai cewa uffan
Zahra dai jagwal gwala abincin kawai take don ta kasa kai ko loma daya bakinta tsabagen kishin dake cinta
Lura da haka da Ma'u tayi tace
"Anty Zahra ya bakya cin abincin, ko kin koshine"
Murmushi tayi tacigaba
"Kodashike ma yadda Ummi ke son kin nan nasan ta cika miki ciki kanki taho"
Ba karamin namijin kokari Zahra tayi ba wajen danne xuciarta kada ta biyewa Ma'u don ta fahimci Ma'u so take tayi double offense, dabara ne ya fado mata ta maidawa Ma'u murmushi tace
"Nadanci abincin ai, banaso naci dayawane na kasa farantawa Sweetyna rai anjima, don kin san ya jima da samun nutsuwa"
Kadan ya rage Ma'u tasa kuka, ita tai maganar kuma ita ya dama don ssai martanin Zahra ya bugeta
Ikon Allah Bature ya tsaya kallo da Ma'u da Zahra duk mamaki suke bashi, kunne kawai ya baxa musu amma idanunshi yana kan plate kamar baisan me suke cewaba
Shiru wajen yayi Ma'u na naxarin wani irin martani xata maidawa Zahra, Sam kishin dake cinta ya hanata tunanin komai haka ta hakura da tafarfasar xucia suka kammala cin abincin
Bature ne ya fara barin dinning space din yana murmushi kasa kasa
Zahra na ganin ya haura ta dubi Ma'u irin kallon gargardin nan tace
"Wlh Ma'u ki fice idona, ke har Yaushe kikasan dadin miji daxaki budi baki kimin fitsara, keda kike matar hadi, idan ma badon kaddara ba ina Ya Bature ina ke, kuma ina mai miki lalbishir daga yau kin bar kwanan dakin Ya Bature idan ma kina kwana"
Ganin Bature baya nan kuma idan ta kuskura ta tanka mugun duka xatasha gun Zahra yasa Ma'u mikewa a hankali ta nufi bedroom dinta, daidai xata shiga bedroom din ta daga murya inda Zahra xata jita tace
"Ma'u batasan dadin mujiba sai dai mijine yasan dadin Ma'u don yadda yake ihu da sambatu ya nuna baya samu wannan dadin gun muna mata sai mace, kuma batun matar hadi inaga kin manta bara na tuna miki, Zahra ma Matar hadice bata soyayya ba, maganar kwanan daki kuma yanxu Ma'u ta fara sula tsiya a turaka"
Bata jira komai ba ta shige bedroom dinta ta banko kofa
Yatsa Zahra ta ciza ta kada kai irin xan kamakin nan ta bar dinning space din itama ta haura
Kwance Bature yake kan gadonsa na alfarma sai murmushi yake don yanada tabbacin wannan salon na matansa zai sanya kusanci ssai tsakaninsa da Ma'u ya samu yadda yake so
A hankali Zahra ta turo kofar ta shigo bedroom din, xuwa tayi ta durkusa gaban bed
"Pls Honey ka taimakamin wlh na gane kuskurena, Allah baxan kara maimaita hakanba"
Kamar mai bacci Bature yayi banxa da ita
Ssai Zahra tayi ta masa magiya hadda kukanta, amma Bature yaki kulata
Daga karshema cewa yayi
"Idan kin gama kije ki kiramin Ma'u mu kwanta"
Ihu Zahra tasa
"Wayyo Allah na shiga ukuna don Allah Sweety ka rufamin asiri ka barni ni kwana a da kin nan wlh ina bukatarka"
Dakyar dai ta shawo kanshi sanda ta hada da maganar rashin haihuwarta kan ya saurareta
"Shikenan Zahra ya wuce, amma kuma ki sani idan kika kuma aikata haka sai dai ki tsinci takaddar sakinki a hannunki"
Share hawayenta Zahra tayi ta haye kan bed dinta ta rumgume Bature
"Nagode ssai Dear, insha Allah baxan kuma hakanba"
Su Bature daman ana hannu take ya baxama duniar Ma'aurata ya shiga sula tsiya
Sam bacci ya kauracewa Ma'u sai juyi take, don tayi mugun sabo da romancing dinta da Bature keyi, kuka tayi ssai dakyar da sudin goshi bacci yayi gaba da ita
Washegari kin fitowa breakfast Ma'u tayi, Babu kuma wadda ya nemeta hakan kuwa ba karamin dadi yama Zahraba don a ganinta ta fara maganin Ma'u
Sai 10 Ma'u ta fito cikin shirinta na fita anguwa tea kawai ta hada tadanyi sipping tayi dialling number Bature
Sanda ya kusan katsewa kan ya dauka
"Ina kwana"
Ta fada a sanyaye
"Lfy"
Ya amsa a takaice
"Daman so nake xanje wajen Anty Falmata"
A dayan bangaren Bature yace
"Na mantama ban sanar dakeba ta haihu yau kwana hudu"
Ido Ma'u ta zare tace
"Meta samu"
"Idan kikaje xaki gani, kuma kada ki jima"
Bai jira cewarta ba ya katse wayar
Bakaramin amfani xuwan Ma'u gidan Falmata yayi mata ba, don taje ta samu 'yan uwan Falmata sunxo daga Maiduguri sun bata lacca ssai baida kayan gyaran jiki data samu
Lokacin dinner ne Bature ya sanar dasu ya raba musu kwana bibbiyu
Bayan kwana biyu
Bbu abunda ke shiga tsakanin Ma'u da Zahra sai harara da habaici tun ba Zahra ba ta dau abin da zafi, ssai take nuna kishinta a fili
Yau Ma'u xata amshi girki, xuwa tayi kitchen ta kori cookernsu, ta xage ta rangada girki mai rai da lfy don cikin laccan hadda yima miji girki aka shaida mata
"Gaskia yau girkin Samuel yayi dadi ssai, Honey ka turashi course ne"
Zahra tayi maganar lokacinda take kokarin kai spoon din meat love rice bakinta
"Ai basai ya tura Samuel course ba tunda ya auro wadda ta iya girki"
Cewar Ma'u tana sipping Ginger juice datayi
Daga Zahra har Bature mamaki ta basu, aina suke lokacinda ta koyi girki har ta iya haka
Harara Zahra ta hurga mata tace
"Kinga Ma'u kada ki kuskura kice xaki raina ni don kaddara ta saki auren mijina, ko bbu komai na girmeki balle kuma idan aka duba dangantakarmu"
Marairaice fuska tayi abin tausayi tace
"Pls Honey ka shiga tsakanina da Ma'u don wlh xan iya babbalata wani sa'in"
Mugun kallo ya jefa musu kowa ya shiga taitayinsa, amma kasa kasa Zahra ke harar Ma'u
Koda lokacin kwanciya yayi, wanka da Humra Ma'u tayi ta nufi turaka
Waya ta samu Bature nayi da Balarabe, gefenshi ta xauna akan bed tana jira ya gama wayar
Katse wayar Bature yayi ya juyo yana duban Ma'u
"Wayayi girkin daxun"
Ya jefa mata tambaya
A shagwabe tace
"Ni nayi"
Shagwabar tata ta burge Bature ssai
Rumgumeta yayi a jikin shi
"Idan kuma na samu bakye kikayiba sai na sassaba miki"
Wasa ta shigayi da gashin dake kwance a kirjinshi tace
"Meyasa baka shaving gashin nan?"
Tayi tambayar cikin salon Jan hankali
Ido Bature ya xuba Mata nadan lokaci yana naxarin yadda batajin tsoronshi yanxu idan har akaxo fagen nan, kanshi ya kada daya tuna jaraba gareta
"Kinaso inyi shaving wajen ne?
Ya tambayeta yana shimshina gashin kanta dayasha gyara ssai ga kamshi
Tura bakinta tayi tace
" banason kayi shaving yafi kyau haka, kaga Babyn Anty Falmata kyakyawa dashi kamar na sato na gudu"
Ta canxa topic din
Daria ta bawa Bature amma sai yayi murmushi yace
" kinason Babyne?"
Kai Ma'u ta kada alamar "eh"
Janyota yayi jikinsa ya fara kissing dinta a kasalance yace
"Insha Allah yau xan miki ajiyar Baby"
Ma'u da babu baki shiru tayi tana karbar sakonni, ssai ta dage wajen mayar mishi da raddi
Jaraba plus jaraba abun ba magana ssai suka mori juna, sai yanxu Bature yasan yayi aure yana gamsu yadda ya kamata ba kamar Zahra yanxu yanxu tace ta gajiba
Asuba ta gari Ma'uBature
Hu6a Mubi LGA Adamawa State
Durkushe Hajiya Turai take itada Ummi da Lubna gaban boka a cikin wani bukka mai duhu
Hajiya Turai ce ta xayyanawa boka bukatarsu, daria bokan ya kece dashi yace
"Hajajo mutan Makkah, kisa ranki a inuwa indai wannan itace kawai bukatan angama, naga yanada mata ita matar ya xa'ayi da ita"
"Ya saketa kawai boka"
Lubna ta fada kaitsaye
Kai Hajiya Turai ta girgixa
"Ai idan ya saketa anci bulus, kada ya saketa ya dai tsaneta yayita gana mata axaba, yadda Ammi ta bakanta mana rai muma sai mun bakanta mata"
Lubna tace
"A'a Anty bakya ganin xai shafi auren Shukrah ko Zahra"
Gyara xama Ummi tayi tace
"Baxai shafi ko dayaba idan ma shafarne Zahra ce kuma xuwa na gaba akan Bature xa'a mana aiki"
Boka dai da ido yake binsu yana murmushi yana kada kai
Sanda ya tabbata sun gama maganarsu ya dauki kullin magani ya bawa Ummi yace
"Wannan a saka mishi a cikin abinci da xarar yaci shikenan aiki ya gama kyau"
Cika boka sukayi da kudi suka mike suka fice
Ransu fari kal
Ummu Subay'a❤
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻
JINJINA
Mahmu Gee
Habiba Mohammed (Sahra)
Afrah Bhai
2⃣0⃣
Yau asabar tun safe Abdallah da Batool dukaxo gida, suna xuwa bai kai minti biyar ba saiga Hisham da Shukrah, duk a falon Ammi suka hada xango bayan sun gaisa da iyayensu
Tunda Ummi taga Abdallah ta shiga kitchen da manta don hada masa favorite dinsa jallof na couscous
Hira suke ssai sai daria suke da shewa abun gwanin ban sha'awa
Ammi tace
"Ja'iri lokacin da aka aura maka ita ba har xaxxabi kayiba"
Batool tayi sauri tace
"To Ammi hada wuri ana xaman lfy xaki bata, xaxxabin ma ai naso ne koh Baby"
Ta karashe maganar tana dagewa Abdallah Gera
Murmushi Abdallah yayi yace
"Ssai kuwa xaxxabin sone"
Baki Ammi ta tabe tace
"Xakuji da gulmarku"
Hisham yasa daria bbu kakkautawa
Duk suka xuba masa ido
Ammi tace
"Kai kuma me haka kamar sabon kamu"
Tsaigaita dariar yayi yace
"Ina tuna yadda al'amura xasu wakana a gidan Ya Baturene, ga Ma'u ga Ya Bature ga kuma Zahra, xanso naga wannan dramar"
Duk daria sukasa Shukrah tace
"Ai kuwa ba karamin drama akayiba, don dukkansu bbu tayan baya"
Kasa kasa da Murya Batool tayi tace
"Sis ya kamar akwai ajiyar Babynmu ne"
Murmushi Shukrah tayi tace
"Kai Sis wlh kin fiya gulma ya akayi kika gane"
Itama Batool murmushi tayi tace
"Nima inadashine shiyasa na gane"
"Haba dai Sis"
Shukrah ta fada da dan karfi
Duk suka juyo suna kallonta
Jan hannunta Batool tayi suka mike suka nufi bedroom din Ammi
Harara Ammi ta bisu dashi tace
"Sai manyance kama uwayen mata"
Daria Hisham da Abdallah sukayi
Warmer mai kyau Ummi ta dauka tasakawa Abdallah abincin a ciki ta barbada garin maganin da boka ya bata a ciki ta juya ssai maganin yabi jikin abincin, ta bari a kitchen ta nufi bedroom dinta tayi wanka kan ta kirasa yaxo yaci
Hira Batool keyi da Shukrah kowa na bada lbrn yadda take xaune da mijinta cikin jin dadi
Wayar Shukrah ne ya hau ringing, Honey ne manne screen din tayi picking cikin sauri
"Assalamu Alaikum Honey"
Amsa sallamar Hisham yayi yace
"Sweery pls samomin abinda xanci kixo kiyi feeding na, part din Mami"
"Toh Honey gani nan tafe"
Ta katse wayar ta mike
"Sis bara na kaiwa Honey na abinci"
Kai kawai Batool ta gyada mata don bacci ya fara Kamata
Direct part din Ummi Shukrah ta nufa, kitchen kai tsaye Shukrah ta nufa
Tana shiga kitchen din idonta ya sauka kan warmer da Ummi tasa abinci, bude warmer tayi taga abunda ke ciki
Murmushi Shukrah tayi ta dauki plate ta dibi abincin, har xata fita taga ya kamata ta kara abincin kada nasu Abbu ne, konawa kitchen din tayi ta bude tukunya ta kara abincin a warmer ta fice
Kamar yadda Hisham ya fada mata a falon Mami ta sameshi takai mishi abincin, take Hisham yaci abincin don shima yanason couscous
Tusa Abdallah a gaba Ummi tayi sai yaci abincin
Plate Abdallah ya dauka ya dibi kadan na sama yaci don ya rigada ya cika cikinsa kan suxo
Gidan Bature
Tun safe Ma'u na kwance a dakinta tana fama da masanancin xaxxabi, ko breakfast bata fita tayiba ga Bature baya gari ya tafi port court
Rashin ganin Ma'u ya damu Zahra amma tana tsoron shiga dakin Ma'u kada wani Kissa ta shirya, shiyasa Zahra tayi xamanta a falo tana jiran dawowar Bature don ranar xai dawo
Dakyar Ma'u ta lallaba ta janyo wayar ta tayi dialling number Bature, hawayene ya shiga bin kuncinta dataji number switch off, tana tsoron kiran Zahra kada ta mata wulakanci
Bature na dawowa Zahra ta karbesa hannu bibbiyu da taimakonsa ya kintsa
Suka fito falo tare, a cushion suka xauna
"Sweety baxaka ci abinci bane"
Zahra ta tambayi Bature cikin kissa
Kwantar da kansa Bature yayi a jikin Zahra ya limshe idonsa, Ma'u kawai yakeson sanyawa a idonsa
"Ma'u fah?"
Yayi tambayar cikin ko in kula
Bata rai Zahra tayi tace
"Tana dakinta"
Ta bashi amsa a takaice cike da kishi
Mikewa Bature yayi ya nufi bedroom din Ma'u
Kuka mara sauti Zahra tasa tanajin tsanar Ma'u ssai
Ssai xaxxabin yaci karfin Ma'u, bugu daya ta fice hayyacinta, tayi amai ssai
Bature na bude kofar dakin idonsa yakai kanta, da gudu ya karasa dakin ya dagota, ya mannata da jikinsa bai damu da Ammi daya bata mata jikiba
"Lfy HUSNA meya sameki"
Duk da Ma'u na cikin matsanancin hali vai hanata jin dadin sunanba
Daukarta yayi ya shige da ita toilet ya mata wanka, shiryata yayi cikin dogon Riga yasa mata hijab ya fice da ita
Zahra na xaune sai kallonsu tayi, mikewa taxo jikinta har rawa yake tace
"Lfy Sweety? Meya sameta?"
Mugun kallo ya hurga mata
"Bani waje na shige, kina gidan nan batada lfy amma kikayi zamanki koki lekata"
Baki Zahra ta bude xatai magana, yadan hankade ya shige
Kamar xatai kuka ta koma ta xauna
Da isarsu Hospital cikin kankanin lokaci aka tabbatarwa Bature Ma'u nada ciki sati biyar
Ssai Bature yayi murna hadda bawa Doctor tukwici, daga bisani kuma tausayin Zahrarsa ya kamasa
Ma'u naji tanada ciki tayi murmushin mugunta a xuciar ta tace
"An bani lasisin sheke ayata yadda ya kamata, Anty Zahra kin bonu"
Tun a hanyarsu ta dawowa Ma'u ta shiga shagwabewa Bature, shi kuma yana biye mata
Fargaban wani Irin hali Zahra xata shiga ya hana Bature sanar da ita Ma'u nada ciki
Fitowa falo ma'u tayi tana chart a WhatsApp
Kujerar dake fuskantar wadda Zahra ke xaune ta xauna, tana murmushi da Batool ta sanar mata tanada ciki kuma take tambayarta idan Anty Jidda ta haihu xataje suna
Voice note Ma'u ta shigawa Batool
"Da wuya naje Sis, kin san Ya Bature bayason nayi nesa dashi, amma xan lallabasa yabarni naje"
Tana gamawa tayi sending
Baki Zahra ta tabe tace
"Makaryaci dai bai ji dadiba wlh"
Murmushin mugunta Ma'u tayi amma bata tanka ba, dialling na number Bature tayi, yana picking a shagwabe tace
"Sweetheart wlh tun daxun miyau na sai tsinkewa yake"
Daga dayan bangaren Bature yace
"Mekikeso Husna"
Sake shagwabewa tayi tace
"Gwaiba nakeso naci"
"To bbu damuwa xan turo akawo miki"
Yayi maganar tare da katse wayar
Mikewa Ma'u tayi tana daria kasa kasa
Shan gabanta Zahra tayi
"Ke rainin sense dinki ya isheni haka, idan kika kuma wlh sai nayi kasa kasa dake"
A tsiwace Ma'u tace
"Da kuwa an daureki har igiya ya saura don wlh Ya Bature baxai barki kimai asarar baby ba yabarki"
Zaro ido Zahra tayi hadeda dafe kirji
"Kina nufin kinada ciki"
Kada kai Ma'u tayi tace
"Confirm, congratulation kin kusa xama yadikko"
Jimamine ya hana Zahra cewa komai ta wuce Ma'u jiki a sanyaye ta haura dakinta
Ganin yanayinta yasa Ma'u tausaya mata tayi danasanin fada mata maganar, itama Ma'u jiki a sanyaye ta wuce bedroom dinta
Banko kofa Zahra tayi ta fada kan bed tasa kuka mai cin rai ta janyo wayarta tayi dialling Number Ummi
Gidan Bature
Waya Ummi take da Hajiya Turai, korafi Hajiya Turai take mata
"Anya Hawwa kin bawa yaron nan maganin nan yaci kuwa"
"Wlh Anty na bashi kuma a idona yaci"
Ummi tayi maganar tana rage muryan Tv
"Gaskia yaci muga result don Zee ta matugar daga min hankali kwanarnan"
Shigowar Shukrah cikin kukane yasa Ummi ba shiri ta katse wayar
"Mexan gani Shukrah? Me aka miki"
Xubewa a jikinta Shukrah tayi tana kuma mai cin rai tace
"Ummi na shiga uku, Ya Hisham xai kasheni, yau da safe shegen duka yamin kuma yace shi Yanxu Zee yakeso"
Wani jirine ya fara dibar Ummi tace
"Ke banason shirma wata zeen yakeso"
"Zeen Anty Turai, hadda daukar numberta a wayata ya kirata"
Hannu Ummi ta dora a ka tasa kuka tace
"Wayyo Allah menakeji haka, don Allah Shukrah kicemin karya kike"
Kara volume na kukanta Shukrah tayi tace
"Wlh gaskia ne Ummi, Ya Hisham ya tsaneni"
Wayar Ummine ya shiga ringing, batayi kukorin daina kukarba ta picking call din
Zuciarta ce ta fara dukan uku uku dataji kukan Zahra
"Wayyo Ummi na shiga Tara, Ma'u nada ciki, pls Ummi kiyi wani abu"
Kuka mai karfi Ummi tasa, tanayi Shukrah nayi ga kuma Zahra itama tanayi abundai babu dadin gani
Da gudu Zee ta sauko daga staircase taxo ta fada kan cinyar Hajiya Turai
"Mom daxun Ya Hisham ya kirani yanatamin xantukan soyayya hadda cemin idan bai aureniba xai iya rasa ransa"
Murmushi Hajia Turai tayi tace
"Kujimin jibebbiya Abdallah ya kiraki ko Hisham"
Gyara kwanciyarta Zee tayi kan cinyar Hajia Turai tace
"A'a Mom Ya Hisham ne Mijin Shukrah"
Da mamaki Hajiya Turai tace
"Hisham kuma garin yaya haka, naga kina murna ina Abdallah kike so"
A shagwabe Zee tace
"Ai da babu gwara ba dadi, kuma ni ina tsoron Batool nan gwara Shukrah xan iya duk yadda naso, bakiga ranar danaje ina yimasa wasaba sai hararata take kamar xata doken, nidai nafison ya Hisham yanxu"
Kada kai Hajiya Turai tace
"Shikenan ni farin cikinki nakeso, tunda Hisham din kikeso hakan xa'ayi"
"To Mom bakya ganin xamu samu matsala da Anty Hawwa"
Baki Hajiya Turai ta tabe
"Idan xaki samu farin ciki ko Mijin Hawwa xaki aura ina bayanki, matsala kuma ita ya shafa"
Rumgumeta Zee tayi tace
"Proudly Mom, love you much"
Daria Hajiya Turai tayi tace
"Love you much more Zee"
Ummu subay'a❤
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻
GODIA DUBU
Pherty Zahra (Jiddatul Musty)
Son so
Ummu Subay'a Fans❤
2⃣1⃣
"Wlh banga mahalukin da zai hana auren Zee da Hisham, tunda tace tanaso, ai ba akanmu aka fara hada 'yan pendoni gida daya"
Cewar Hajiya Turai tana kada jikinta
Salle Ummi tayi ta dire tace
"Billahillaxi baxai yiyuba, karyanki tasha karya Zee baxata tabs auremin Mijin diyaba, tunda Zee tasako kanta cikin familyn mu komai ya dinga tabarbaremin"
Lubna data xuba musu ido tace
"Kinga Anty Hawwa duk fa Abunda ya faru laifinkine, maimakon ki bawa Abdallah magani kikaje kika bawa Hisham"
Harara Ummi ta gallawa Lubna tace
"Zan ci ubanki idan baki rufemin bakiba, na dau asara wancan karon amma wannan karon bbu ni bbu asara ko mutuwa Zee zatayi baxata auri Hisham ba"
Dariar Boss Hajiya Turai tayi tace
"Nima Turai baxan dau asara ba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 12