Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gobe ya kamata kuje Gidan Baba Kabala don kullum naje sai ya tambayeni Ku" Sun dan jima suna hira kan su Abdallah suna Mike suna wuce part din Mami Bayan wasu watanni Ma'u ta sake ssai a Gidan Bature don ya rage takura mata da kuma dukanta, sai dai tsoronshi har yanxu yana nan don a jininta yake Zahra kam tamfar kawa ta dauketa komai Anty Zahra komai Anty Zahra Makaranta Bature ya maidata ssai ta maida hankalinta, Gashi yanxu suna kokarin rubuta Weac Takanje gidan Falmata sa'i da lokaci, ssai take dauken duk abunda Falmata ta koya mata, tuni ta saje ta koma diyar KanuShuwa ( har tafi Amiratul Arab haduwa) Humra ne ya xama tularenta shiyasa duk sanda ta gamu da Bature take tafia da imaninsa, yakanji kaman ya janyota jikinsa ya rumgumeta ko xai kashe kishinta dayakeji A fannin Bature kuwa tun yana ganin lamarinsa da Ma'u xallar sha'awaetace ke dibansa har ya ankara sontane ya mai kamun kaxan kuku Duk sanda sukaje family meeting wadda suke bayan wata biyu yakanji kamar ya furta abunda ke ransa amma idan ya tuno da wacece Ummi? Kuma wacece Zahra da kishi? sai gwiwarsa tayi sanyi Amma ya kudurta a ransa Ma'u na candy xai bayyana abunda ke ransa komai ta fanjama fanjam Abunda Bature bai saniba kuwa shine soyayya mai karfine ya shiga tsakanin Abdallah da Ma'u, wadda tuni Abdallah ya saye xuciarta da dadadan kalamai A gefe daya kuma ga Batool nata haukan son Abdallah kuma duk wawwatarta ita zai zaba a matsayar matar aure Zee autar Hajiya Turai kuwa ta mace a son Abdallah kuma ta takurawa Hajiya Turai, har Ummi ta sani kuma ta musu alkawarin Abdallah baida mata sai Zee Yayinda Shukrah da Ya Hisham ke xuba love dinsu hankali kwance Bayan Shekara daya Falon Ammi ya samu hallartar duk wani dan Gidan Bature don gudanarda Family meeting kamar yadda suka saba Tunda Ma'u ta bar Kaduna sai ya taxo, duk sunyi mamaki yadda ta kara girma ta kuma cika ta koma Babbar mace A yau ne Bature ya dau kudurin Neman alfarman auren Ma'u don ta rigada tayi candy A yaune Abdallah xai samu damar nuna Ma'u a matsayin matar aurensa A yau ne Ummi takeson bayyana bukatarta ta hada Abdallah da Zee aure A yau ne Abba da Abbu sukeson sanarda ahalinsu hukuncin da suka yanke na hada Abdallah da Batool aure Hmmmmmm................... Ma'uBature Ma'uAbdallah ZeeAbdallah BatoolAbdallah #Team Ma'uBature 😜😜😜😜 Ummu Subay'a❤ [23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛 (Romantic love story& family Saga) Ummu Subay'a dedicated to RUFAIDA OMAR (GWANATA) 🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻 Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE 1⃣1⃣ Da Addu'a Abbu ya bude meeting din, yayinda Abba ya dora da "Assalamu Alaikum Warahmatullahi Ta'ala wa barkatu" Duk ahalin falon suka amsa sallaman " da farko xan fara da godewa Allah daya bamu lfy tsayon rai ya kuma hadamu wani family meeting, wannan meeting din akan Abdallah da Hisham ne sai kuma masu korafi ko neman shawara, duba da mukayi kun gama karatu sa'annan kuma kun samu aiki kafarku ta dafe kasa shine muka bijero da maganar ajiye iyali ma'ana batun aure" "Abba nikam na riga na samu matar aure, damar rana kamar haka nake kira" Abdallah yayi saurin katse Abba kamar yasan meke ransu Duk sai kallo ya koma kansa "Haba Abdallah wannan wani irin gaggawane, baxakabar Yaya ya dasa ayaba sai ka katsesa" Cewar Abbu yana mikawa Abdallah mugun kallo Kwafa Ammi tayi tace "Ai idan baiyiba sai an tambayesa jinin isassu nefe a jikin sa" Murmushi kawai Ummi tayi don ta jima da sabawa da muggan kalaman Ammi Numfasawa Abba yayi yace "A'ina ka samu matar Abdallah" Keya Abdallah ya shiga sotsawa, yayinda Ma'u ta sunne kai tana murmushi, Batool ko ta kafeshi da ido xuciarta na bugun uku uku, Ummi kuma na Allah Allah yace Zee ce matar "Kayi magana mana, bafa aikinka mukeba, daman kasan kanada kunya ka fara kawo batun" Bature yayi maganar cikin umarni Zahra datasan komai tace "'Yar gidan nan ce fah, Ma'u ce" A raxane Batool ta dago tana kallon Ma'u dake gefenta kamar ita tai maganar, xuciarta ne ya tsananta bugawa kamar xai ballo kirjinta ya fito Ummi ko ji take kamar an watsa mata ruwan xafi, ji take kamar tayi dirar mikiya gaban Zahra ta shakota Goga Bature kam dafe xuciarshi yayi dake baraxanar fita, rintse idonsa yayi don gudun kada wani ya gane halin dayake ciki "Uban wa ya tambayeki, ko dake ake maganar" Ummi ta fada tanama Zahra mugun kallo "Ummi haka maganar yake" Abdallah yayi maganar kansa a kasa Maida dubanta Ummi tayi kan Ma'u da itama kanta a kasa " Ma'u kina son Abdallah " Kai Ma'u ta gyada alamar "eh" Ammi dake binsu da ido tace " Fateema uwata kin gama? Tambayar ki nake kin gama? Idan kin raina su Ahmad to nikam nafi karfin reni wajenki ko ubanki bai kai ya renani ba, Muna xaune a kasa kike bidirinki gabanmu Abdallah dai yanason Ma'u itama tana sonshi ko bakya so auren nan sai anyishi, kai kuma Hisham maganar ka da Shukrah na nan ne?" Kai Hisham ya tsadda kasa yace " eh tana nan" Abba daya karanci kowa amma banda Bature yace "Toh Alhamdulillah tunda duk na gidane, insha Allah cikin lokaci kalilan xa'ayi bikin, akwai mai magana" Har Ummi ta bude baki xatayi magana Abbu ya watsa mata kallon "kada ki fara" Bbu yadda ta iya taja bakinta ta rufe Mami dai shiru tayi ta xubawa Baturenta ido tana karantan yanayinsa, murmushin tausayinsa tayi don tasan xa'a rina mugun kiyeyya xai koma mugun soyayya Haka aka rufe meeting din, masu farin ciki sunayi masu bakin ciki sunayi Daga falon Ammi direct part dinsa Bature ya nufa yana shiga bedroom ya danna key ya kulle, fadawa kan bed dinsa yayi ya hau kuka kamar karamin yaro hade da sambatu "Yanxu inaji ina gani Ma'u xata kufcemin, meyasa ban fahimci Ma'u na soyayya da Abdallah ba? Duk girman kaina ya jaxamin gashi na rasa Ma'u" Kai ya kada kamar mai magana da wani "Ina sam baxaiyuba, Allah baxan bari wani ya auri Ma'u ba muddi inada rai" Mikewa yayi ya xauna "To mexanyi mena iya?" Ya tambayi kansa Dirowa yayi daga kan bed din, ya hau buga kansa jikin bango yana kuka gwanin tausayi "Why me? Why Bature?" Cikin lokaci kalilan Bature ya fita hayyacinsa kuma ya fita kamanninsa, fuskarsa tayi jayur abunka da farin mutum, blue eyes dinshi sun rine sun koma jajayur Allah sarki Bature duk wadda ya gansa dole ya tausaya masa ( Soyayya ce) Garden Batool ta nufa ta yada xango, kwanciya tayi kan carpet grass ta shiga rera kuka kamar marainiya, tun farko jikinta na bata baxata taba samun gurbi cikin xuciar Abdallah ba amma xuciarta ta tirsasata ta ci gaba dasa sammani gashi yau ta shiga mugun hali Wani abu takeji yana mata yawo a kahon xuciarta, ssai taji tari na taso mata Tari take kamar ranta xai fita, tana kuka tana tari ( Zafi biyu) Safa da Marwa Umma ta shiga yi a bedroom dinta komai ya kwance mata, ji take kamar ta rusa ihu, ta ko'ina anfi karfinta Da wani ido xata dubi Anty Turai tace mata Abdallah baxai auri Zee ba Ma'u xai aura, idan tai haka xata yadda girmamawanta a gidansu, ya xama dole ayi duk mai yiyuwa Abdallah ya auri Zee Zahra ce ta shigo tana duban Ummin da mamaki " Ummi meya farune, naga kamar hankalinki a tashe" Cewar Zahra tana kokarin xama bakin bed Harara Ummi ta watso ma Zahra tace " ya hankalina baxai tashiba keda Abdallah xaku xubarmin mutunci gidan Kabala, Anty Turai fa xuwa tayi ta nemi alfarmata akan tanason ta hada Abdallah da Zee aure, na nuna mata bbu komai ta kwantarda hankalinta yanxu kuma keda Abdallah Ku daukomin fitsarerriyar yarinyar nan Ma'u " Duk dunia bayan Ummi bbu wadda Zahra ke ji da ita kamar Hajiya Turai, kuma itama Hajiya Turan naji da ita Ajiyar xucia Zahra tayi tace " Wayyo wlh Ummi ban San abunda ke gudana ba kenan, da ban bawa Abdallah goyon bayan neman Ma'u ba, Anty Turai tamana komai ya kamata muma mu saka mata, yanxu me abunyi?" Xama Ummi tayi kusa da Zahra tace "Shi nake ne tunani" Shiru dakin yayi nadan wani lokaci Kan Zahra tace "To Ummi mexai hana mu nemi shawarar Anty Lubna" Murmushi Ummi tayi " good idea insha Allah Lubna xata sama mana mafita" Mikewa Zahra tayi tace "Bari naje naji Yaushe xamu koma, idan ba yau ba sai muje gidanta anjima" "Toh" Ummi tace tana murmushin kwanciyar hankali don tasan idan sun samu Lubna komai ya kare Ruwan xafi Bature ya hada ya matse goshinsa daya kumbura yayi ja yayi wanka ya shirya, ya fara hada kayansa don ya yanke hukunci baxai kwana anan ba balle bakin ciki ya kasheshiba, gwara ya koma Abuja ko xaiji sassauci Tsaf ya hada kayansa yaja trolley, yana fitowa Falo Zahra na shigowa Mugun kallo ya jefeta dashi yaci gaba da tafi'arsa Da mamaki take kallonsa tace " Honey ina xuwa, kada kacemin dai xamu koma yau" Kamar badashi takeba ya nufi kofar fita, da gudu ta sha gabansa "Magana fah nake Sweety" " bacemin daga gaba Zahra" Ya fada cikin kakkausar murya "Bari na dauko veil na mu tafi" Ko sauraranta baiyiba yayi ficewarsa da gudu ta bi bayansa "Don Allah Sweety kayi hakuri, ka tsaya kajini, me aka makane" Dakyar ta cimmasa yana kokarin bude kofar motarsa Rike kofar tayi ta marairace masa tace "Ka dubi girman Allah ka fadamin abunda na maka, ka dubi yadda idonka yayi ja ka dubi yadda fuskarka ya xama, wai meke faruwane" "Pls Zahra ki kyaleni, banason damuwa ni xaki munafurta a gidana ni xaki boyewa Soyayyar Ma'u da Abdallah" Durkusawa tayi gabansa tace "Don Allah Honey kayi hakuri wlh shiya nemi ayi hakan" Shigewa yayi motarsa yace "Ai sai kije ki xauna sai an gama auren ki dawo Abujan, king a lokacin kin gama xama mai dalilin auren" Jan motarsa yayi ya fice gidan a dari fa hamshin bai sallami kowaba Kai kawai Mami ta gyada data gama kallon duk abunda ya faru tsakanin Zahra da Bature yace " Allah ka kawo mana dauki" Up up up up up #Team Ma'uAbdallah♥ Dole na nemo bodyguard saboda #Team Ma'uBature Kada Ku babbalani😜 Ummu Subay'a❤ [23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛 (Romantic love story& family Saga) Ummu Subay'a dedicated to RUFAIDA OMAR (GWANATA) 🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻 DA BAXARKU NAKE RAWA Batool Adam Jatco (Amfanin Soyayya) Zainab Goni Rufaida Omar (Taurari) JINJINA Batul Mamman (Kashe fitila) Beebie Isah (Dan Makaho) Phertymerh Zahra ( El-Mustapha) Sadnaf (Makobtan Juna) Lamtana (Asabe Reza) Phertymerh (Yusrah) Sameena Aleeyo ( A duniarmu) Ainadimple (Hasken lantarki) Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE 1⃣2⃣ "Nidai mun bata, tunda na tafi ko ki kira Anty Zahra ta bani kin samu Shukrah kin manta dani" Ma'u ke maganar tana shuna bakinta Janyo Ma'u jikinta Ammi tayi "Haba ta wajena ai baxamu bata ba, me Turawa ke bakine kika cika kika wani jiki haka" Murmushi Ma'u tayi tace " ya rage dukanane kawai kuma ni baxan komaba na dawo kenan tunda aure xanyi" Harara Jidda ke hurga musu tace "To fitsarerriya kin dawo da rashin kunyarkiba, ko kunya bakyaji kina ce mana aure xakiyi" Kukan shagwaba Ma'u tasa "Ammi wai me na tarewa Anty Jidda ce sam batason ganin walwalata" "Rabu da ita kishi take dake, kinga yanxu ita kishiyar balbalinkice" Cewar Ammi tana shafa kan Ma'u Shukrah ce ta shigo ta xauna kusa da Anty Jidda tace "Wash nagaji wlh" "Aikin me kikayi?" Cewar Jidda Wasa da Amal dake koyon tafia Shukrah ta shiga yi tace " Ya Abdallah ne yasani na gyara masa part dinsa, wlh Ma'u sai kin dage son jikin Ya Abdallah yayi yawa komai a barbaje yake a dakinsa" "Sai dai su dawwama a bolansu amma Ma'u da lalacinta bbu abunda xata iya tafi'arsu daya da Zahra" Cewar Ammi tana dariar tsokana Shukrah ta kannewa Ma'u ido "Dama Batool xai aura xata kintsashi, Ma'u kam sai dai ta dada lalata manashi" A harxuke Ma'u ta tashi ta xauna tace "Anyi walkiyi naganki 'yar bakin ciki, duk yadda nake haka Ya Abdallah ya kyasa, shegiya mai hana ruwa running" Haba Anty Jidda ta rike tana kallon Ma'u "Baiwar Allah meyayi xafi daga wasa, ai kanwar mijinkice" Baki Ma'u ta tura tace "To sai tace da Batool xai aura" Murmushi Shukrah tayi tace "Allah ya huci xuciarki Anty Masifa" Hisham ne ya shigo falon ya dauki Amal yana mata wasa tanata kyalkyalewa da daria Yaxo saitin kunnen Shukrah yace "Wataran diyarmu xan ma wannan wasar" Tafin hannunta Shukrah tasa ta rufe fuskarta tana murmushi Jidda dataji abunda yace "Kai Ya Hisham a idon Ammin" Baki Ammi ta tabe tace "Kinga Ma'u dagani nabar nan don bbu abunda yaran nan baxasu aikata a gabanaba, basukiba suyi Daren farkonsu a kan gadona" Duk daria suka saka Hisham ya xauna kusa da tsakiyarsu Jidda yace "Ke dai kishi kawai kike, kuma first night din baxai gagara kan bed dinkin ba" "Allah ya sawwake kishin me xanyi ai gidan nan Turawane kawai Mijinah kuma Zahra ce kawai kishiyata" Ammi ta fada tana kokarin janye Ma'u daga jikinta Text ne ya shigo wayar Ma'u daga Abdallahnta "Ki sameni a Garden" Murmushi tayi, a tare suka mike da Ammi, Ammi tayi hanyar bedroom dinta yayinda Ma'u tayi hanyar barin falon "Ina kuma xaki uwar gantali" Shukrah tayi tambayar Kai tsaye Ma'u tace "Zance xani ko xaki hanani" Kai Shukrah ta kada "Na isa ni a wacece?" Ficewa daga palon Ma'u tayi ba tare data tankaba Tashi Jidda tayi itama ta nufi hanyar barin falon "Bara na barku kusha love" Hisham daya matso ssai kusada Shukrah yace "Zoki dau diyarki mai shegen kiriniya kamar Ma'un nan" Daria Shukrah tasa tace "Anya Anty Jidda ba little Ma'u muka samuba" Dakuwa Jidda tama Shukrah tace" "Xonan Babyna, daga na barki ki tayasu lobewa shikenan sai dangantamin ke da ma'u Allah ya isan miki" Take Amal ta isa gaban Jidda, Jidda ta dagata ta fice Cikin so da kauna Hisham ke duban Shukrah yace "Madam kinga yau dai an tabbatarmin dake, wani irin tanadi xaki faramin kafin ranar da muke jira taxo" Murmushi Shukrah tayi ta shiga wasa da yatsunta batace komai ba Marairaice mata hisham yayi "Haba mana Madam pls talk, nifa kunyarkice ki hadani dake wlh, sai kace yar 1970s" A sanyaye Shukrah tace "To mexance Sweety wannan maganar tafi karfina" Murmushi Hisham yayi yace "Tabbas tafi karfinki, sai first night dinmu xaki san tafi karfinki" Bbu shiri Shukrah ta mike xata gudu don maganar tayi mata mugun nauyi Cikin xafin nama Hisham ya kamota ya dawo da ita ta xauna inda ta tashi yana mata daria "Village girl" Da kuka Zahra ta shigo bedroom na Ummi Cikin mamaki Ummi ke tambayarta "A'a Zahra me kuma ya faru?" Cikin kuka Zahra ta xayyana mata duk abunda ya faru Tsaki Ummi taja tace "Ji nake kamar na hauki da duka kiyi kuka mai dalili, sai kace ke bakuwar Baturene bakisan mugun ra'ayinsa ba da dan wannan abunda yayi xai tada miki hankali hadda kuka, tun farko ma Uban me ya hanaki sanar dashi" "Ya Abdallah ne yace kada na sanar dashi" Zahra ta fada tana share hawayenta " ki biyewa Abdallah sai ya kashe miki aure wlh, nikam jeki ki wanke fuskarki mu tafi gidan Lubna, abunda ke gabanmu yafi wannan shirmen din, gwara ma da hakan ta faru xamu samu damar warware matsalar idan yaso daga baya na kira Baturen na basa hakuri" Babu musu Zahra ta shige toilet don wanke fuskarta "Subhanallah, Batool lfy? Meya sameki?" Abdallah yace lokacin da ya sami Batool kwance tana tari mai xafi, dagota yayi ya kwantar da ita kan cinyarsa ga jikinta ya dau xafi Salati Ma'u tasa data iso garden din ta samesu, durkusawa tayi gaban Abdallah "Hayati meya sameta?meke damunta" "Hayati " tsayawa sunan yayi a kahon xuciar Shukrah wadda ya ingixa tarin kara hardeta ssai, ji take da xata bar duniar ma xai fiye mata sauki Mikawa Ma'u wayarsa Abdallah yayi "Kiramin Hisham kice ya samemu a part din Mami Batool ba lfy" Yana fadin haka ya daga Batool din kamar yar tsana ya nufi part din Mami Itama Ma'u mikewa tayi tabi bayansu tana kiran Hisham din a waya, ta gama rudewa sai kuka take Gidan Bature Ikon Allah ne kawai ya kai Bature Abuja, don Sam baya cikin hayyacinsa, gudu yayi ta shararawa kamar shi kadai akayi titin Wuni yayi jimami da kuka kamar karamin yaro bai san haka so yakeba sai yau bai san ya afka kogin son Ma'u da nisa hakaba sai yau bai san xafin soba sai yau Da yanada iko daya mayar da son dayakewa Ma'u kan Zahrarsa amma ina bashi ya sakaba balle ya musanya WhatsApp dinsa ya bude ya shiga Dpn Zahra ya kurawa pic din Ma'u dake Dpn ido, sonta sai dada ninkuwa yake a xuciarsa Pic din ya jasa ssai murmushin datayi ya kara bayyano da xalalan kyaunta Bature Estate Kamar da wasa ciwon Batool gashi ya kara tasannanta, agajin gaggawa Hisham ya bata a matsayinsa na likita, taimakon ubangiji jikin ya lafa ta samu tayi baccin bayan tasha allurar bacci Sai a wajen ciwon ne akasan Bature ya koma Abuja, fada ssai Abba yayi, da'aka kira numbersa duk switch off don wadda yake kallon pic din da ita tana fly mode ne Dole su Ummi suka dage tafiarsu gidan Lubna sai gobe A Balcony part din Mami Ma'u da Abdallah suka xauna a resting chair suna hira "Pls Ruhy ki daina sa wannan turaren idan xamuyi hira yana dagamin hankali ssai, idan naji kamshin ji nake kamar na janyoki jikina" Baki Ma'u ta tura tace " nidai suna turarena, kuma gaskia baxan iya daina sasuba don sunamin dadi ssai, sai dai mutum yayi hakuri" Kai Abdallah ya kada yace "OK bbu damuwa ranarda kika kaini makura xaki gane ai" Baki kawai Ma'u ta tabe bata tanka mishiba "Ruhy Allah kina rikitani dayawa ga pink Jan bakinda kike sawa sexy lips dinki nan na tafia dani I wish watarana in shanye miki Jan bakin tas" Yayi maganar yana kashe mata ido Bbu xato bbu sammani Ma'u taji wani abu na sauka daga kasanta, limshe ido tayi taji sauyi ssai a jikinta, tasan dai wannan abun na faruwa da ita only if tana gaban Bature idan ya tsareta sa blue eyes dinsa Yau kuma meya kawosa wajen Abdallah "Baccine Ruhy?" Abdallah yayi maganar yana kallon yadda tayi sanyi Kai kawai ta gyada mishi alamar "eh" Har bakin bedroom na Mami Abdallah ya raka Ma'u, sanda ta shige kan ya fice Duk wani shirin bacci Ma'u ta gama gefen Batool dake bacci taje ta kwanta ta xubawa enlargement din Bature ido, wadda ya dauka da inform dinsa ta Air force yayi mugun yin kyau kamar wani cikekken Bature, haka kurum ta tsinci kanta tana murmushi "Turawa case" Ta fada a hankali tana limshe ido #Team Ma'uBature Ummu Subay'a❤ [23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛 (Romantic love story& family Saga) Ummu Subay'a dedicated to RUFAIDA OMAR (GWANATA) 🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻 INA ALFAHARI DAKU Meela Adeel Meena parrot (mai fitsarin kwance) Zee Madagwal Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE 1⃣3⃣ Shiru falon yayi bayan Ummi ta gama watsafoma Lubna abunda ke faruwa Kusan 3minutes Lubna ta dauka tana naxari daga bisani tace "Gaskia Anty Hauwa Idan har Abdallah bai auri Zee ba akwai babban tashin hankali a family, kinsan Anty Turai batasan hakuriba kuma akan farin cikin yaranta xata iya batawa da kowa kuma taciwa kowa mutunci" Ajiyar xucia Ummi tayi tace "Duk nasan da wannan Lubna mafita naxo nema wajenki" "Don Allah Anty Lubna ki taimakemu kin san Momy tamini komai Idan muka samu matsala da ita akwai babban damuwa" Cewar Zahra kamar xatayi kuka Murmushi Lubna tayi tace "Kwantar da hankalinki Zahra, kin manta nifa na sama muku mafita lokacin da kika mace kan son Bature" Harara Ummi ta hurgawq Lubna "Banda tuna baya kuma mana Lubna" "Babbar matsalar wannan Ammin takuce xata hana ruwa gudu amma nasan yadda xa'ayi, kawai ku xuba musu ido kowa yayi yadda yakeso sai ranar daurin auren xa'a daura da Zee" Cike da mamaki Ummi da Shukrah ke kallonta Gyada musu kai tayi tace "Kawo kunnenku kuji" Magana ta fada musu a kunne wadda nima banji ba Shewa suka saka da tafi Ummi tace "Wlh kwatakwata ban taba kawo wannan a kainaba ai shine hanya mafi sauki bbu tashin tashina bbu kuma Uban da zaiji haushina" Daria Zahra tasa tace "Inaji dake Antynah wlh kanki naja" Murmushi Lubna tayi daga bisani kuma ta dan hade rai tace "Ya kamata mu sabarda Anty Turai komai kada taji waiwai taci ubanmu" "Gaskia kam kin san Anty Turai fire to fire ne" Cewar Ummi Gyara xama Lubna tayi tace "Ke Zahra har yanxu bbu labarine, ga Jidda da diyarta tufarkallah" Maiko idon Zahra yayi alamun hawaye cikin sanyin murya tace "Wlh Anty bbu inda bamu xagaya da Ya Bature ba amma ance lfyta klau kawai lokacine baiyiba" Baki Lubna ta tabe tace "Ya kamata lokacin yayi tun kan Amminku tasashi kara aure don bbu abunda baxata iyaba" Hannu Zahra ta dafe a kirjinta tace " na Shiga uku aure kuma? Wlh ta kuskura tasashi aure xan musu borin hauka, yadda nakeson Ya Bature wlh baxan iya sharing dinsa da wataba har abada bbu Zahra ba kishiya" Harara Ummi ta aika mata tace "Ki tsaya kina cewa bbu ke bbu kishiya kada ki haihu" Lubna tace "Bari mu gama kashe wutar dake gabanmu xan dawo nata" A wajen suka kira Hajiya Turai a waya suka xayyana mata komai, jan kunne ta musu da babbar murya akan kada a samu matsala don baxata lamunci kukan diyarta ba Bature Estate Zaune suke su uku a dining space a falon Mami suna breakfast Ma'u ta dubi Batool tace "Jinyan rana daya kin xube gabaki daya, katon kumatunkin nan duk ya xube" Shukrah dake kokarin kai Spoon cike da soyeyyen egg tace "Wlh ta xube ssai, wai meke damunkine Sis" Sipping na tea Batool tayi tace "Zazzabine wlh ya bugani kuma ina ganin aikin girkin danayine mai ya hau kaina" Cikin tausawa Ma'u tace "Ayyah Sannu Sis, Allah ya kara sauki" Duk suka amsa da Ameen "Har wajen cin abinci ma baxaku bar surutuba, xan fita xamuje gaisuwa da su Alhaji, Batool ki tabbatar kinsha magungunanki, Shukrah ki tabbatar tasha" Cewar Mami data fito daga bedroom dinta tana kokarin barin falon Baki Ma'u ta tura tace "Ni baxa'a barmin amanar shan maganinba" Baki Mami ta tabe tace "Jirgin daya dauko Bala shiya dauko Audu" Mami na ficewa Abdallah da Hisham suka shigo Tsayawa Abdallah yayi tsakankanin kujerar Ma'u da Batool yayinda Hisham ya xauna a kujerar dake gefen Shukrah ya dau spoon ya fara tayata cin abincin Gaishesu su Batool sukayi Abdallah yace "Ya jikin naki Batool" "Da sauki Batool" tace tana dubanshi Hisham ma ya jikin ya mata Rankwafo da wuyarsa Abdallah yayi saitin kunnen Ma'u yace "Anything for me Ruhy" Fari da ido Ma'u tayi tace "Nothing Hayati" Baki ya bude mata alamar ta saka mishi indomie data dibo a folk, bbu musu ta saka mishi ya fara taunawa a hankali yana limshe ido Wani abune ya tokare Batool a kahon xuciarta, ji take kamar tasa ihu ko xataji sauki Gefe daya ga Hisham sai kwantarwa Shukrah murya yake don ta saka mishi abinci a baki yadda Ma'u tayiwa Abdallah amma kunya ya hanata Badon Batool ta koshiba ta mike da niyar barin dinning space din "Baidai har kin koshiba" Shukrah ta tambayeta Kai kawai ta kadawa Shukrah alamar "eh" tana kokarin sauka daga space din Ma'u tayi sauri tace "Maganin fah bakishaba, ke Shukrah soyayya ta mantar dake amanar Mami" A

Chapter 6 of 12