Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yayi yace "Saboda Zahrarsa na bashi dukkan hakkinsa kuma tana masa yadda yakeso" Murmushin jin dadi Zahra tayi bata kara wani kalmaba don tasan halin abunta bayason Jan xance Tsab Bature ya karanci Ma'u tanason kallon fina fanan soyayya, duk inda take Zee TV na wajen, idan ana xuba love har wani limshe ido take kamar wata mai Masoyi Ko yanxu ma love ake xubawa a film da ake haskawa a Zee TV limshe idonta tayi hadda wani dan mika duk Bature yana kallonta Dafe kansa yayi da wata xucia tace masa "Kodai ta dau irin Sha'awar kane" Kai ya girgixa "No idan ta dau akwai matsala ai baxata taba iya jurewa ba" " tunanin me kake Sweety" Muryan Zahra ce ta katse mai tunanin dayake, ya sauke ido daga kan Ma'u ya mayar kan Zahra yace "Abunda ya shafi aikine Darling" Bbu wadda ya sake magana har suka kammala break fast Bature dai jefi jefi yana kallon Ma'u After One Month Shakuwace ssai ta shiga tsakanin Ma'u da Zahra ssai sun fahimci juna Ma'u ta fahimci xafin Zahra sai an tabota ne take nuna, ita kuma Ma'u bbu hanyar daxata tabota shiyasa take jin dadin xama da ita Itama Zahra ta fahimci fitinar Ma'u ganin idon Ammi ne don yanxu kamar ba itaba, sai dai son jikin har yanxu yana nan wannan nema kesa wataran ajisu Ma'u da Goga Bature kam bbu yabo bbu fallasa, idan Bature sukayi nisa Muhammad yaxo suna hira da shima tare da Zahra, idan Bature na goshi kuma ko kulasu bayayi A satin ne Bature suke shirye shiryen xuwa England don hallaran yayesu Hisham da Abdullah daga Cambridge University Ana washegari xasu tafi Balarabe da Jidda suka iso Abujan Jidda da Balarabe sunji dadin yadda sukaga Ma'u ta sauya, Jidda hadda wani doronta wai ta iya bada shawara Zaune kan bed Bature yake yana aiki a laptop dinsa yayinda Zahra ke hada musu kaya Bayanta gama ta xauna a bakin bed din tace "Sweety har yanxu banji kayi magana akan inda Ma'u xata xauna kan mu dawo, ko xa'a barta anan ita dasu Tawa" Kamar badashi take maganaba sanda ya gama abunda yake cikin laptop din ya rufe ya ajiye a kan bed side table, ya janyota jikinsa yayi kissing na neck dinta kan yace "Nariga na gama magana da lieutenant Shehu xata xauna a can kan mu dawo" Shigewa ssai Zahra tayi jikinshi tace "Ai kuwa Matarsa Falmata tanada kirki, Ma'u xataji ddin xama wajenta" Bakinshi ya tura cikin nata ya farasha abun mamaki sai xuciarsa na xayyano mass kalar bakin Ma'u dashi yakesha xaifi wannan dadi Rintse idonsa yayi yana kokarin kawarda tunanin a xuciarsa amma ina ya kasa, komai ya taba na Zahra sai ya dinga imaging da nake Ma'u ne dayafi wannan dadi Pls kuyi hakuri da wannan Heart you all fans♥ Ummu Subay'a❤ [23/10, 01:08] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛 (Romantic love story& family Saga) Ummu Subay'a dedicated to RUFAIDA OMAR (GWANATA) 🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻 Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE 0⃣8⃣ Bature Estate Zaman Gidan Bature yayi dadi ssai ga ahalinta, bbu tashin hankali da raba fada ko fargaba kowa jin dadin rayuwarsa yake Hatta 'yan aikin Gidan sun samu sariri don suma Ma'u tasa su a gaba Zaman Ammi da Shukrah gwanin sha'awa bbu uhmm bbu uhm uhm Ita kanta Ammi ta samu kwanciyar hankali har tadanyi kiba, gudun kada a mata daria ne yasa take maganar Ma'u Xaune Shukrah da Batool suke a garden Batool na chatting yayinda Shukrah ke karanta The Still Born na Zainab Alkali Kowa ya maida hankali kan abunda yake Ihu Batool tasa dataci karo da status na Hisham da Abdullah sunyi posting pics na Graduating dinsu " wooow wannan damuwar kyaun fah,Sis dubi yadda Bature Family muka haskaka a England " Karbar wayan Shukrah tayi "Woow kyau kenan, ji yadda Ya Bature ya saje cikin Turawan nan" Karbe wayarta Batool tayi taci gaba da kallon pics din tana yabawa Hade rai Batool tayi ta tura wayarta kan table dake gabansu taja dogon tsaki Da mamaki Shukrah ke kallon Batool tace "Sis meya faru kuma?" Wani tsakin Batool taja tace "Dubi yadda Ya Abdallah ya rumgume yar iskan nan kamar wata matarsa" Daukar wayar Batool Shukrah tayi ta dubi pic din da Batool ke magana Daria Shukrah tasa tace "What's wrong, nidai banga komai anan ba Sis, kodai kina cikine" Harara Batool ta ballawa Shukra tace "Waje nake ba cikiba yar renin sense" Daria Shukrah ta kuma sawa tace "Idan tayi tsami maji" Kwantarda kanta Shukrah tayi kan kujerar datake xaune, ta limshe idonta, a xuciarta tace "Koda son Ya Abdallah xai kasheni baxan bawa kowa damar fahimtar meke cikin raina ba" (Toh fah wata sabuwa) Kuje Barrack Xaman Gidan Shehu yayiwa Ma'u dadi ji take kamar kada su Bature su dawo Falmata irin matanan ne da'ake kira kaitsatattun mata, ta iya komai don janyo hankalin miji Tunda ta dora idonta kan Ma'u jininsu ya hadu jinta take kamar kanwarta uwa daya uba daya Fahimtar wacece Ma'u yasata cin alwashin sai ta xamar da Ma'u katsaitacciyar mace Da dabara Falmata ta fara nunawa Ma'u hanyar xama katsaitacciyar mace Yau kwanar Ma'u biyu a Gidan Shehu Suna kitchen Falmata na kirki Ma'u na kallon komai Falmata ta dubi Ma'u tace " Asma'u ki kalla da kyau inaso idan kin koma gidanku kije kidanga ma Oga Bature" Baki Ma'u ta tabe tace "Sai dai idan nayi aure nama Mijinah amma baxanwa Ya Bature ba, kinga ma can chief Samuel ne keyi" Cike da mamaki Falmata tace "Kina nufin Zahra batawa Oga Bature abinci" Kwafa Ma'u tayi tace "Tab wlh bata girki, bana tsammanin ma ta iya don gidanmu masu aikine ke girki, Mami Umman Ya Bature ce kawai ke girki a Gidan mu" Kai Falmata ta kada tace "Ya kamata ki koyi girki idan kinason ki xama Tauraruwa a wajen mijinki" "Toh ai banda wadda xata koyamin" Cewar Ma'u tana tura bakinta cikin shagwaba Murmushi Falmata tayi tace "Drama Queen shiyasa Babynah yace yanason dramarki, yanxu abunda xa'ayi idan kin koma sai ki dinga xuwa ina koya miki" Wanke hannuwanta Ma'u tayi data gama yanka albasa tace "Ai Ya Bature baxai yardaba" "Xai yarda mana idan na rokeshi" Falmata tayi maganar tana dauko flask don juye kunun gyadar data gama Satinsu Bature daya a England suka tattaro suka dawo Nigeria tare dasu Hisham Gidan Bature Zaune suka a Palo bayan kowannensu ya kintsa kansa Hira suke ssai suna daria banda Bature dayayi kicin kicin da ransa kamar yadda ya saba jefi jefi yake tsoma bakinsa cikin hirar " yaushe xaku gangara Kaduna ne" Jidda ta tambayi su Hisham "Jibi insha Allah xamu gangara" Hisham ya bata amsa Daria Abdallah yasa yace "Ammi ikon Allah" "Ammi dake Kaduna meya hadaka da ita" Balarabe ya jefa masa tambaya Ajiye wayarsa gefensa Abdallah yayi yace " yanxu Shukrah ke isarmin da sakonta wai mu dawwama Gidan Ya Bature kada mu dawo" Duk sukasa daria banda Bature daya tabe baki Hisham yace "Yanxu kuma mutum xai koma ya tararda bakin cikinta da Ma'untan nan" Jidda dake bawa Amal Nono tace " ai kana tare da Ma'u, tuni ta dawo nan" Cike da mamaki Su Abdallah suke kallon Jidda Kai Abdallah ya girgixa yace "Ban amince ba Jidda, na tabbatar da Ma'u na Gidan nan bbu abunda xaisa hanata fitowa" Daria Zahra tasa tace "Ma'u damuwa hadda kuma kun San halinta, tana can anguwa mun bada ajiyarta kan mu dawo" "Allah sarki duk wadda aka kaiwa ajiyar Ma'u an hada da aiki" Hisham yayi maganar yana daria "Silent pls" Cewar Bature lokacin da yake kiran Wayar Shehu Gidan Shehu Daga wanka Ma'u ta fito, shafe jikinta tayi da lotion dinta masu kyau tasa Riga da sikat na atamfa, tana kokarin daura dankwali Falmata ta shigo dakin da sallama Amsawa Ma'u tayi tace "Yawwa Anty pls xoki dauramin Dankwali irin yadda kika daura taki jiya? Murmushi Falmata tayi tace " fuskarki ma yaci make up Drama Queen don kayan yayi matukar amsarki kamar Celebrity " Murmurshi Ma'u tayi taji dadin yabonta da Falmata tayi Rangadawa Ma'u make up Falmata tayi, takuwa yi kyau ssai, dauri mai matukar kyau Falmata tama Ma'u Nan kyaun Ma'u ya bayyana na aslin fulanin Congola Farace Sol Ma'u irin hasken Fulanin Congola, fuskarta dogone mai dan fadi, fararen idanuwantane ya karawa Fuskarta kyau, lips dinta masu dan kauri hadda wani layi layi a jiki masu matukar kyau Baxa'a kirata doguwaba kuma bata cikin gajeru, shape nata 8figure ne wato akwai dukiyar Fulani ga kuma maxaunai tare da hips, cikinta kuma a shafe kamar wadda bata cin komai "Tabarakhallah Mashallah" Cewar Falmata data gama shirya Ma'u tsaf kamar wata Amarya Juyawa Ma'u tayi ta dubi kanta a mirror sai murmusawa take don tasan ta gama kyau, ji take kamar na ita bace "Kinga ina trolleynki, muje driver ya maidake yanxu Babynah ya kira Oga Bature yace a maidake" Kwabe fuska Ma'u tayi kamar xatayi kuka tace "Nidai bbu inda xani kawai su barni nan nafi jin dadin xaman nan" "A'a Drama Queen rufamin asiri kixo muje, ko ni ban goyi bayan xamanki nan ba, kina wannan daukar wankan ai sai Baby yace shidai sai Drama Queen ya korani Maiduguri" Ma'u batasan lokacin da tasa daria ba tace "Na shiga ukuna wlh baxan auri Uncle Shehu ba" "Koma yayane muje nikam" Har bakin Mota Falmata ta raka Ma'u "Wlh xanyi missing naki Drama Queen" Cewar Falmata tana rufe murfin motar "Nima xanyi Missing dinki Antynah" Ma'u ta fada tana maida hawayen dake shirin xubo mata Gidan Bature Cilla Amal Abdallah keyi sama, sai daria yarinyar ke barewa dashi Zahra dake kallonsu tana sha'awa inama diyarta ce tace "Amal batada tsoro Sam kamar Goggonta Ma'u" "Kai Zahra pls daina hada diyata da Ma'u, ai idan Amal ta dauko Ma'u sadakarta xan baku" Jidda tayi maganar tana duban Amal din Tawa ce ta shigo falon da sallama dauke Trolleyn Ma'u Zahra na ganin trolley tace "To Ya Hisham ga mutumiyarka ta iso" Duk duban Tawa sukayi Jidda tace "Ina Ma'un take" "Tana xuwa" Tawa ta bawa Jidda amsa ta wuce Bedroom Jidda Da sallama Ma'u ta shigo falon tana cat walk da Falmata ta koya mata Duk ido suka xuba mata cike da mamaki Bature kam kamar wani mutum mutumi kafe Ma'u da ido yayi wani abu da bai tantance ko meye bane ya shiga yawo a xuciarsa, wani felling na musamman yakeji Hakama wajen Abdallah har wani limshe ido yake yana jin wani bakon yanayi na xiyartarsa, take ya tantance Sone "Mr Bature kana cikine" Balarabe yaxo daidain kunnen Bature ya rada masa Wani mugun kallo Bature ya watsawa Balarabe yace "Allah ya sawwake Zahrata ta isheni, mexanyi da wannan kucakar" Ganin hankalin Zahra na dawowa kansu ne yasa Balarabe Jan bakinsa yayi shiru "Woow Ma'un Ammi kece haka kamar wata celebruti" Cewar Jidda tana murmushin ganin Ma'u tayi fes Itama Ma'u murmushi ta sakar musu, wadda yasa Bature Mutuwar xaune hadda wani limshe idonsa Duk halinda yake cikin Balarabe na lura dashi, murmushi kawai Balarabe yayi yana hasaso budurin daxa'ayi nan gaba Nagode da addu'arku Fans Ummu Subay'a❤ [23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛 (Romantic love story& family Saga) Ummu Subay'a dedicated to RUFAIDA OMAR (GWANATA) 🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻 Ina taya daukacin al'ummar duniya murnar Babban Sallah Allah ya maimata mana ya nuna mana ta badin badada Mahajjatan mu kuma Allah ya karbi ibadunsu ya dawo dasu lfy Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE Fans banida bakin godia da irin addu'o'in da kuka sambadamin Nagode ssai sai dai nace Allah yabar zumuncin Kaina Dirar mikiya nayi a garina BORNO da YOBE, duk da ku bayinane amma jininku dake gudana jikina yasa baxan mantaku ba Yakaru Yakura Yagana Falmata Fanni Hawwa Mrs Zanna Mrs Barma Mrs Indimi Mrs Mandira Mrs Banki Mamin Gana Mamin Ari Ummu Sarki Ummu Maina Ummu Shuwa Amiratul Arab Da duk 'yan kungiyar KANUSHUWA Ina alfahari daku Kuma ina muku BARKA DA SALLAH 0⃣9⃣ Zama kusada Zahra Ma'u tayi a kujerar dake kallon nasu Bature Dan tura bakinta tayi tace "Sannunku da dawowa" Duk suka amsa mata banda Bature dake satan kallonta lokaci xuwa lokaci Kwantarda kanta tayi a jikin Zahra tace "Nayi missing dinki Anty" Shafa bayanta Zahra tayi tace "Nima nayi missing dinki Ma'un Ammi, yaki ka bar Falmata?" "Tana lfy tace tana gaidaki ma" Cewar Ma'u tana kara shigewa jikin Zahra Baki Jidda ta tabe tace "Allah yasa baki mata ta'asa ba" Tura baki Ma'u ta kuma tace "Bbu abunda na mata har cewa take dana xauna amma tana tsoron kada na kwace mata Miji, kamar ance Mata inason mijinta" Duk.sanda ta basu daria, Abdallah yace "Babu ruwanki da Mijinta auren gida xakiyi" "Wannan kam sai Gidan don bbu wadda xai iya xama da ita sai na Gida" Cewar Hisham Shiru Ma'u tayi bata tanka musu ba Kiran Sallah Azahar ne yasasu Bature mikewa don tafia masallaci 8:30pm Bature ya raka Balarabe wajen business partner sa yayinda Abdallah da Hisham suka fita xaga gari don Abba ya kira gobe gobe su dawo Ammi ta daga musu hankali "Ma'u Ma'u Ma'u" Jidda dake shirin Shiga wanka ta kwadawa Ma'u kira Ma'u na kwance kan 3siter tana kallon Turkish series, film din na tafia mata yadda takeso Tanajin kirar da Jidda ke mata taki amsawa "Nikam Ma'u bake Jidda ke kiraba" Cewar Zahra data shigo falon yanxu, bata rai Ma'u tayi tace "Ni banjiba" Daidai nan su Abdallah suka shigo dauke da manyan ledoji a hannunsu A cikin falon suka yada xango Zahra ta musu sannu da dawowa "Ma'u ki kiyaye nifa" Zahra tayi maganar a dan tsawace Tashi Ma'u tayi ta xauna tace "Me kuma nayi" Harara Zahra ta watsa mata tace "Ban saniba, tun ina daki nakejin Jidda na kiranki kuma sarai kinji kika shareta, idan kin samu love story kamar wadda aka bawa aljannah, idan aure kikeso.sai ki fada a miki, ga Yah Abdallah naga kamar yana ciki" Mikewa Ma'u tayi tana gunaguni "Ni banasonshi kuma bazanyi aure yanxuba sai nayi Master's, ita kuma Anty Jidda sai iya kiran mutane axo a dauki Amal tasan baxata iya riketa ba meye na haifarta" Tashige cikin bedroom da Jidda ke ciki Kai Abdallah ya kada yana murmushi yace "Drama Queen nifa yanxu duk abunda take burgeni take" Daria hadda shewa Zahra tayi tace "Ya Abdallah ka fito fili kace kana ciki musha biki, amma dai ka dibo ruwan dafa kanka, mai xama da Ma'u sai ya shirya" Bude ledan dasuka shigo dashi Hashim ya fara yi yace "Ya shiryan kenan tunda ya fara xancen, nidai wlh baxanyi makobtaka dakaiba don ko makobtaka kayi da Ma'u sai kaji jiki" Bugun Bayan Hisham Abdallah yayi yace "Nidai nagani inaso wlh kuma duk yadda take xan xauna da ita macece ai lankwasata bbu wuya" Wani dariar Zahra tasa tace "Badai Ma'u da shegen taurin kantan nan ba, kai dai xakaji jiki mukam namu sannu ne" "Kinga Zahra banason renin sense, nan gaba kadan Antynki ce Ma'u" Abdallah yayi maganar yana dan hade rai Baki Zahra ta kama tace "Ikon God sai looking, Ma'u ce Antyn nawa" Harara Jidda ta watsawa Ma'u data shigo dakin "Sai yanxu kikaga damar xuwa jin kiran nawa?" "Ni bbu abunda naji sai yanxu" Cewar Ma'u tana tuttura bakinta daya xama mata jiki Handle na kofar toilet Jidda ta rike tace " dauki Amal kije da ita ki riketa" Tana fada tayi shigewarta Toilet yayinda Ma'u taje ta dau Amal ta mata rikon ko in kula Kuka Amal tasa don kanta na rinto Daga cikin toilet Jidda tace "Wlh Ma'u idan kika yarmin da diyata xan sassaba miki" Xarewa Amal ido Ma'u tayi "Kimin shiru ko na yaddake a kasa don uwarki, anajin kukanki hadda min kashedi, gaki diyar gold shegiya mai kama da ubanta" Gyara rikon da ta mata tayi ta fice falo Kai tsaye cinyar Zahra ta dire Amal "Gashi inji Anty Jidda wai ki riketa kan ta fito" Xama tayi kusa da Zahra, ganin wani irin kallon da Abdallah ke matane yasata shagwabe fuska tace "Ya Abdallah kallon nan yayi yawa kona maka kama da budurwarkace" "Ai ba kama bane kece Budurwar tawa" Baki Ma'u ta tabe taci gaba da kallon datake Hisham ya mikawa Zahra ledojin da suka shigo dasu yace "Zahra ga tsaraba" Karbar Ledojin Zahra tayi ta musu godia 9 dai dai suka watse a falon har Ma'u tayi bacci, Jidda ta tasheta ta shiga bedroom A gigin bacci Ma'u ta haura bedroom din Bature tayi kwanciyarta Sai 10 Bature suka dawo, Balarabe ya shige bedroom dinsu da Jidda yayinda Bature ya shige Bedroom dinsa Murmushi yayi dayaga mutum kwance kan bed dinsa, duk xatonsa Zahra ce don bayason ya dinga binta bedroom dinta, itako ragwanci ne ke sata kwanciya a Bedroom dinta Sanda ya shirya tsaf ya kashe wutar dakin ya hau kan bed din Tun kan kamshi yaji akwai banbanci don ita Zahra bata amfani da Humra, Ma'u ko wanka da Humra Falmata ta mata Bai damu da banbancin daya keji ba don yasan bbu wadda xata xo dakinsa sai Zahrarsa Ssai yakai kaimi wajen aikawa Ma'u sakonni masu rikitarwa Cikin bacci Ma'u ta dinga jin wani bakon yanayi, ssai ta bude tana karbar sakonnin don duk xatonta mafarkine sai nishi take tana sauke numfashi a hankali Bature kam ya rikirkice don bai taba jin irin haka daga Zahra ba Tsaki Zahra taja don mugun felling takeji sanadiyar Fura da Nonon datasha daxun, kuma tun daxun taji shigowar Bature amma yaki yaxo gareta Saukowa daga bed tayi tana mita " jarabar Sweety ya rabe nima" Kai tsaye bedroom din Bature ta nufa Ummu Subay'a❤ [23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛 (Romantic love story& family Saga) Ummu Subay'a dedicated to RUFAIDA OMAR (GWANATA) 🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻 Kuna Raina Batool Adam Jattko Ummi ontop Maryam Paki Mrs Adam Maman Rufaida Anty Fauxy Zainab Goni Mrs Mansoor Da duk writer's na KAINUWA Da fatan anyi Sallah lfy Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE 1⃣0⃣ Mtssssssssssw Bature yaja dogon tsakin jin ana bugun kofar dakinsa, gashi saura kadan ya fada Duniar Ma'aurata wakeson kawo mishi cikas Jin bugun na kara tsananta yasashi mikewa akan Ma'u ya dau jallabiyarsa ya nufi bakin kofar a harxuke Ma'u ko tanata sharar baccinta kojin bugun ma batayiba don tanada nauyin bacci "Wayene?" Bature ya tambaya cikin baccin rai Shan jinin jikinta Zahra tayi, dagajin muryansa yayi fushi da ita na xuwa dakinta ta kwanta bayan yasha mata korafin bayason ya dinga binta dakinta Cikin sanyin murya tace "Sweety nice" Tashin hankali A raxane Bature ya xaro blue eyes dinshi, idan dai ba karya kunnensa ya masa ba kamar muryan Zahra yaji "Ke wace" Yayi tamvayar in unbelievable voice Murmushi Zahra tayi kasa kasa tace "Kajimin Mutumin nan da rainin sense" Ta dora murya a dage "Zahra ce" "Zahra" Ya maimaita cike da mamaki "Idan Zahra ce a waje wacece a ciki?" Ya tambayi kansa Hannu yasa ya kunna wutar dakin, ya kai dubansa kan bed Da Ma'u yayi toxali tana kwance naked don ya rabata da komai na jikinta Kawar da kansa gefe yayi cike da tsoro "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Kawai yaketa maimaitawa "Tayaya akayi Ma'u taxo dakinsa har kan gadonsa? Akwai banbanci tsakanin Ma'u da Zahra meyasa dayake neman natsuwa da ita bai fahimta ba?" "Pls Honey kayi hakuri baxan sake ba kullum xan dinga xuwa dakinka" Muryan Zahra ya katseshi "Kada ki yadda na fito na sameki a wajen, idan kina son kanki da lfy ki gaggauta barin bakin kofar nan" Yayi maganar cike da bacin rai don duk ita ta jaxamishi komai, idan da tana kwanciya a dakinsa ai Ma'u xata tarar da ita da hakan bai faruba, idan badon Allah ya kiyaye ita Zahrar taxo ba ai sai mai afkuwa ta afku Kamar walkiya Zahra tabar kofar dakin don tasan waye Baturen Kusan 8 minutes Bature na tsaye bakin kofar yana nemawa kansa mafita Komawa kan bed din yayi ya maidawa Ma'u kayanta, a hankali ya dagata kamar 'yar tsana yana Allah Allah Kada ta tashi ko ya gamu da wani a hanyar kaita dakin ta Cikin Sa'a ya kaita har ya dawo bata tashiba bai kuma hadu da kowa ba "Alhamdulillah" Bature yace daya kwanta kan bed dinsa Sai dai sam bacci yaki xuwa mishi sai tunanin abunda ya faru daxun yake Yawo a kwakwalwarsa, yana rufe ido kuma sai Naked surar Ma'u ka masa gixo ga wani mugun felling dake ratsashi ga Hajiya Babba na neman agaji Bbu yadda ya iya haka ya dau wayarsa ya dannawa Zahra kira Tana kwance tana kuka taji ringing din wayarta Murmushi mai hawaye tayi kan ta picking "Kisa in jiraki" Kat ya katse wayar No wasting of time Zahra ta mike ta nufi bedroom dinsa Gangan jikinsa ce kawai ke tare da Zahra amma ruhinsa na wajen Ma'u da tunanin yadda ya dibi ganima a jikinta daxun, duk yadda yakai ya mance komai ya gagara, sai yau ya gane mata suna suka Tara Washegari Balarabe da Jiddarsa suka koma Lagos yayinda Abdallah da Hisham suka wuce Kaduna Bature Estate "Ya kuka samu Ma'uta, nasan ta rame tayi baki tsabagen wahalar da Bature ke bata" Ammi ce ke maganar yayinda su Abdallah suka kewayeta Murmushi Hisham dake xaune kusa da Shukra yayi yace "Don Allah kujimin matarnan maimakon ki fara tambayarmu ya gajiyar hanya angama karatu lfy amma sai ki taremu da wata wai Ma'u" Dakuwa Ammi ta mishi tace "Ma'un tawace wata don kaniyarka, anki tambayarka komai sai Ma'u" Daria Abdallah yasa yace "Ma'unki lfyrta klau sai kinga inda ta kara kyau da kiba tacema a gaisheki" Washe baki Ammi tayi "Ashe Turawan( wataran haka take kiran Bature) an fara hankali" Hiran gundurar Shukrah yayi tace "Ya Abdallah kun gama kenan bbu komawa ai" Kada kai Abdallah yayi yace "Bbu komawa mun dawo kenan sai kuma idan nai aure muje honeymoon da matata" Batool da tunda ta shigo falon take satar kallon Abdallah ta limshe ido, a hankali tace "Ya Allah cikamin burina" "Kayi budurwa kenan Mijinah" Ammi ta hurga mai tambaya "Eh na fidda matar aure dai tafi karfin budurwa" Baki Ammi ta tabe tace "Budurwa dai ai sai ta mana kafin ta xama matar aure" Hisham kwantar da kansa kan hannun kujera yace" Ta gama miki ma don ta gida xaiyi" Xuciar Batool ne ya fara dukan uku uku Shukrah tace "Pls Ya Abdallah wacece?" " sai lokaci yayi xaki Santa don ko itama ban fada mataba" Ajiyar Xucia Batool tayi tana Allah yasa itace Guda Ammi ta rangada "Nasan ko wacece" Hararar wasa Abdallah ya mata yace " wai tsohuwar nan wayo xata mana mu fada mata, to baxamu fada ba" Lami yar aikin Ummi ce ta shigo palon da sallama ta durkusa ta gaidasu "Hajiya ce tace su Abdallah suxo anxo gaidasu" Fuska Abdallah ya hade yace "Su wayene?" "Hajiya Turai ce" Cewar Lami Hisham yace "Kice muna xuwa" Tashi Lami tayi ta fice Kwafa Ammi tayi tace "Isassu an iso, tsabagen takai ma ban kai taxo ta gaidani ba sai dai ta turo kuje" Mikewa Hisham yayi ya tallafawa Abdallah ya mike suka fice Ammi ta dubisu Batool tace "Baxa kuje kuma Ku gaida Turai din ba" "Babu inda xani wlh sai dai ita Shukrah" Cewar Batool tana mike kafarta "Nima bbu inda xani" Shukrah ta fada tana gyara kwanciya akan 3siter Hajiya Turai addar Ummi ce uwarsu daya ubansu daya, itama kamar Ummin take karyar arxiki da son suna, tana auren Senator tana ji da kanta ssai Yaranta Hudu duka Mata biyu sunyi aure sauran biyu Teema da Zee "Nikam wai uwar me suke har yanxu basu karasoba" Cewar Hajiya Turai tana kada kafarta Bata gama rufe bakiba su Abdallah suka shigo Gaisheta sukai ta amsa da sakin fuska "Kai yarana sun girma sauran musha bikin kyece raini, ya hanya? Ya karatu?" "Lfy Klau Alhamdulillah, daman munyi niyar xuwa wajenki a Abuja sai Zahra kice mana kuna nan" Cewar Hisham Abdallah ya dora "Ina su Zee? Koda shike muna gaisawa ma a WhatsApp" Baki Hajiya Turai ta tabe tace "Suna can gidan Baba Kabala" Ummi dake duba materials da Addartan ta kawo mata tace " kuma

Chapter 5 of 12