Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 7
yaiwa *KUYANGA* Ta,aziyya domin yana son Yarinyar aransa domin Nutsuwarta Kwana tayi tana kuka tana tuno fuskar yaronta Aranta kuwa tanajin bazata taba yafewa Wanda yai mata wannan abuba don ancuceta saida akaga tafara kaunar yaron aka rabata dashi UMMAH kuwa ranta fes ta cikawa jakadiya alkawarinta na abubuwan datace zata bata Ammafa agun yarima bata jin ta dadi shiga daya shiga biyu saiya gaya mata magana tamkar ba mahaifiyarsa ba "Kinji dadi kinraba Dan tahaliki da duniya kunji Dadin hakan Kuda Allah kuncuceni kunrabani da farincikina. 😏kunjishifa kaika manta daka sa aka raba bawan Allah da duniya Ashe abun ba dadi Kwana uku da faruwar hakan LAMIDO yazo yi mata gaisuwa Tafito cikin hijab har kasa Yakura mata ido harta iso gareshi tagaidashi ckn ladabi Ya amsa yana kallon Dan karamin bakinta mekamada alawar lollipop Yace " ZEENATU ya hakuri kuma? Ckn sanyin muryarta tace "Da Godiya Yace " Allah yajikansa yabaki hakurin rashinsa Ahankali tace "Amin nagode" Yaso yafurta mata wata kalma saikuma yafasa Yaimata sallama yatafi Yauma binshi tayi da kallo Yanda yake takunsa na kasaita da iya tafiya ta sarakai abin birgewane kokusa Yarima baikamoshi akomai ba Tabbas LAMIDO na daban ne Ayau tayiwa Allah godiya dayasa zata zamo mallakinsa donta farajin wani Abu akansa Abin mamaki ma da dare kasa bacci tayi tayita juyi akatifa tana tuno irin yanda yake maganarsa da tsari da tausasawa ga iya kallo kodon idanunsa Sexy eyes ne gashi da kyau da tausayi Tabbas Samun Namiji irin LAMIDO sai antona Tooo🙄😳fans *KUYANGA* me kuka fuskanta ne a Heart din KUYANGA To kodai ta kamu ne ??? Muje zuwa [8/8, 8:11 PM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA...* 📿 *_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Nabilancy Luv* 💘 (Auntyn S&S) 90-95 FAATU ce A zaune aturakar mai martaba bayan yagama cin abinci yadubeta yace "Kince kinada magana inajinki meke tafe dake akwai damuwane? Ta gyara zama tace "Dama maganar LAMIDO ne Naga tunda har anyi sadakar arbain din jaririn Zeenatu nace to me zai hana atsaida ranar Auransu da LAMIDON ba tunda har ya amince kuma naga kamar yafara sonta Murmushi Sarki yayi yace "To babu komai sai a tsaida Wata daya mai zuwa sai adaura Auran nasu bamusan me Allah ya ajiyeba kuma Inaso aranar da za,a daura Auran ayi bikin dorashi Kan karagar mulki natsufa yakamata nayi murabus nadorashi akai duk abinda nakeyi wanda yakamata yake kaina zai iya sannan ya cancanta don haka zansa ayi shela agari kowa yasanda wannan rana FAATU tace "To amma Takawa kana ganin wannan abun dakayi bazai kawo rabuwar kai atsakaninsa da Dan,uwansa yarima ba mahaifiyar safa ta kudurci dantane zai zama sarki natabbata zataji ba dadi koma tayi bore Sarki yace "Nike da iko da komai daga kan mutan gari da bayi da ku kanku iyalaina da dukuma Sarautar kanta Dan haka babu me canzamin zabin da nayiwa Garina Ckn biyayya FAATU tace " angama ranka ya Dade Allah yaja kwana yakara lfy Yace "Amin Fatima. Inkin futa kituromin LAMIDO tace "To. Bayan futarta tazarce Dakin MAMAH domin takai mata wannan batu sbd duk abinda take ciki saita sanarta kuma bata zartar da komai saida izininta Jakadiya na zaune kusa da MAMAH tana mata hira Shigowar FAATU yasa ta tsahirta tareda gaisata FAATU ta amsa tareda zama kusada MAMAH Ta zayyanewa MAMAH komai na abinda Mai martaba yatsara na bikin LAMIDO da *KUYANGA* Da kuma bikin nada LAMIDO Sarki da za,ayi Jakadiya na qunsa tafuce da rawar jiki ta nufi dakin UMMAH Donkai mata Rahoto UMMAH taga shigowar Jakadiya hankali atashe Ranta yai matuqar baci dajin wannan kalami daga bakin Jakadiya kamar ta Dora hannu aka tayi kuka taji Inama tana da damar da zata hana wannan Nadi Jakadiya tace "Kibar komai ahannuna domin nima bazanso adora Lamido INA gani ba zanso ace Yarima ne zaizama sarkinmu UMMAH ta gyada kanta tana fadin "Nagode jakadiya nasan ke me qaunata CE Jakadiya taxo futa adakin kenan sukai kicibus da Yarima shima yashigo dakin UMMAH Kallon kallo sukaiwa juna ko gaidashi Jakadiya ba tayiba kowa aransa akwai abinda yake ayyanawa akansu Yaxauna akan kushin yana fadin "UMMAH naxo gaya mikine zantafi turai nan da kwana biyu nagaji da zama agarinnan babu masu sona Tace "Kamar yaya babu masu sonka baya gamu nida mahaifinka Yace "Hhhmmm adane kike sona amma ayanzu kam dagake har TAKAWA babu me kaunata kinrabani da gudan jinina kinkuma ki sanyawa Takawa ya yafemin yafaina fushi dani Tace "YARIMA kai kake janyo komai gashi yanzuma zaka tafi kuma kasan bason tafiyarka yakeyiba Danhaka tafiyarka daidai take da karin wani laifin kanka sannan kuma abinda nayi daidaine agunmu nidakai domin inhar Yaron ya girma xai iya tasowa ackn wani yanaya na mugayen halayya ko kuma muzama abin kwatance Inaso kacireshi aranka kafuskanci abinda ke shirin Kasantomu na Nadin Sarauta da mai martaba zaiyi akan kaninka LAMIDO Yarima ya gyara zama da firgici akan fuskarsa yace "Da gaske UMMAH yanzu haka Takawa zaimini SBD yabakanta min rai. Tabbas saina dauki mataki sosai akai Waye ya kawo miki wannan labarin? Tace "JAKADIYA CE yace "shikenan. Yafuta yanufi Dakinsa yadebo kudi masu yawa aljihunsa yafito yanufi sashin da Jakadiya take Cikin ikon Allah Yatararta Ita kadai kuwa Tanaganinsa gabanta yafadi ganin irin kallon da yayi mata dazu tana ganin ko akwai manufarsa ta hakan Yakalleta ba fara,a afuskarsa ya mika mata kudi ahannunsa yace "Karbi wannan ! Jiki na tsuma ta karba Tace "na menene wannan? Yace "Nakine aiki zansaki Tace '"aikin meye hakan? Wannan uban kudi yafi karfina Yace "Yanda kika zama makisiya shine nakeso ki kashemin wani nima Ta zabura "Baxan iya ba walh Yadaka mata tsawa "zaki iya !! Waishinma kinji kowaye? Tace "waxan kashe? Kaitsaye yace mata "LAMIDO!! taji dirar Kalmar akunnenta tadira gefe tana miko masa kudin "karbi kudinka bazan iya kashe LAMIDO ba ka kaiwa wadanda sukai maka aiki akan MAHBUB suyi walh bazan iyaba Yadaka mata harara yace "babu Wanda zansa yayi saike don haka kisani k'in yinki yana daidai da tonuwar asirinki Yana gama fadin haka yajuya yabar ta tsaye atsorace take da wannan lamari ina ita ina iya kashe LAMIDO to yanzu yazatayi gashi tana bukatar kudin sbd yawansu yakai ace tagina kanta da rayuwarta na wasu shekaru toshin yanzu Yaya zatayi ? Rana zafi inuwa Quna!! Mafita ce tazo mata arai gara taraba kudin biyu taje tasami Fadawan da taga yasa su kashe MAHBUB tabasu sutayata aikin ****** Abin Duniya yadami Yarima gashi da gasken Gaske Mai martaba yajuya masa baya ko gaisuwarsa baya amsa masa don hakan ma ya qudiri niyyar kawar da LAMIDO domin yazamo dolen sarki yanad'ashi agaba yakuma Auri *KUYANGA* Shawara ya yanke natafiya Turai tun agobe domin in aka kashe LAMIDO kada adora zargi akansa gara ayi bayanan Da safiyar Lahadi ya daga ko sallama da Mahaifinsa baije yayiba yabarwa UMMAH sallahun tagaya masa Itako dama ranta baiso ba Da kuwa taje ga sarki tagaya masa ko uffan baice mataba shiru yayi mata dole tabar maganar yariman ta tafi Amma ta qudurci yin aikin Asiri atsakaninsu domin janyo soyayyar yariman azuciyar sarkin Yarima Yana dira akasar waje Allah yahadashi da wata bakar fata Ta nuna tana muradinsa azahiri bama tasan shidin Dan sarki bane saida taga alamomi a Dan zaman da sukayi na mintina a Airport Hindu "Yar Minister ce a jahar Kaduna mahaifinta me kudine sananne Alh Khalid Baffanyo "Yar boko ce gata da jijji da kai da dagawa Amma yau sai Allah ya damketa duk yanda take wulakanta samari a garinsu sai gashi ayau Allah yasa mata Soyayyar Saurayin da batasan asalin saba tashi guda Dayake yariman ma na mamajo ne tuni ya afka cikin sonta shima taringa kanainaya da kissa don yasota takuma yi sa,a Har rakiyarta yanema gidansa takuma bishi Saidataje gidansa ta tabbatar shidin Dan babban gidane ta gane dawa take tare Domin tafahimci da alamar Dan gatane kamar yadda take yar gatan babanta Saida suka kadaita sannan yahau tambayarta meya kawota England ? Tace masa tazo Hutu ne gun kawunta Wanda shiya riketa alokacin datayi karatunta acan Takuma gaya masa asalinta da matsayin data taka na aiki domin tana aiki da Ministry of Health itace Director asashen kula da Asibitocin Shiyyar Su Ya jinjina kai yace " Ina sonki zaki Aureni? Da zakuwa tace "Kwarai kuwa inhar da Gaske kake na amince maka amma kada ka yaudareni bani da dadi Yayi dariya yace " nima ba Dadin gareniba. Tayi dariya kawai Aranar ta tayashi kwana agidan sunyi romance amma basu zarta nan ba don ya ayyana aransa ita zai aura takwanta masa Aranar sun tsaida magana zaizo nanda sati biyu Kaduna yagaida iyayanta zai kuma tura magabatansa Tunda suka tsaida magana da Hindu shikenan soyayya ta dinke atsakaninsu akullum suna tare awaya ba dare ba rana Shaquwa sukai sosai in basuji muryar juna ba basajin dadi Tana daga Kaduna amma kowa nata yasan da Fara soyayyarta da yarima Iyayanta harsun San da sunansa domin ta gaya musu tuni Dama ita kadai suka Haifa itace shalele sunaji da ita basa son bacin ranta Yarima yakasa sakat tuni yahado kayansa sai Nigeria Amaimakon yadiro Kano saiya zarce Kaduna Kai tsaye yabi kwatancen d tayi masa Ta aika da mota aka daukoshi aka kaishi gidan Yaji Dadin tarbar da tayi masa da yan gidan Yai mamakin ganin shankwamen gidansu kamar gidan Gwamna ga tarin motoci kamar ana saidasu Akaita kawo masa gaisuwa ma,aikatan gidan aka cika gabansa da kayan ciye ciye A main falour aka saukeshi Mahaifiyarta taje takuma yaba da zabin diyar tata Saida yajira mahaifinta Alh baffanyo yadawo suka gaisa ckn mutunci Dayake mutumne wayyaye tuni yace yabashi ita yakuma bashi sati yaturo magabatansa Yarima yai na,am Sunyi soyayya kafin yatafi da yamma yai mata sallama yabi jirgi yataho Kano Yaringajin kamar karsu rabu tamkar Wanda tayi masa asiri yaringaji Ransa Dari qal yasami Matar Aure yasan yanzu dole maimartaba zai sauko inyaji zaiyi Aure Muje zuwa fans [8/12, 10:51 AM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA* 📿 *_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *HAPPY SALLAH* Eid⁠-Mubarak to all the muslims all around the world. May Allah SWT grant us the ability to make the most of this years. *Nabilancy Luv* 💘 (Auntyn S&S) 95-100 Da Isar yarima gida kai tsaye gun mahaifiyarsa ya nufa Tayi mamakin zuwansa bai sanar mata ba Yana murmushi yace "UMMAH dawowar gaggawace tasameni adalilin Matar Aure dana gamu da ita UMMAH da mamaki tace " Matar Aure kuma yarima ?a INA? Yagyara zama yazayyane mata komai Tahau gyada kai tana jin farin ciki aranta domin jin yarinyar yar masu dashine kuma hakan yayi mata arai tafiso shima yariman yayi Aure kamar yadda LAMIDO zaiyi domin Aure yana karawa mutum martaba da kima a idon Al,umma abin tinkahon tane ace tayi suruka Yar babban gida ba "yar Bayi ba dama Tasawa abin albarka tareda karfafa masa guiwa " na amince maka kayi Aure adaidai wannan lokaci Yarima domin makiya suji kunyar abinda ake shirin maka tunda nasan duk don abakanta maka aka shiryi Auren su balle anga kafito da maitarka karara ka watsar dasu zuwa gaba mushirya kutunguila akansu inhar Aka nada LAMIDO sarautar domin baxamu barsuba Ya gyada kai yace "Nima akwai shirin Dana shirya akan LAMIDON, UMMAH saidai zan ajiye komai agefe sai bayan nayi Auren tukunna amma kiyi kokari Takawa ya karbi abin da muhimmanci ahada ayi tareda na LAMIDON domin iyayan yarinyar da Gaske suke asatinnan zasu Zuba idon ganina UMMAH tace " kada kaji komai Aure fa kamar anyi Angama ****** Koda UMMAH tajewa da Mai martaba wannan zance Murna ma yayi domin yasan yin Auren Yariman kamar wata hanyace zatazo masa ta shiriya don haka saiya nuna amincewarsa da gaggawa tareda tsayar mata da maganar zai tura aje akai kudin Aure tareda tsaida musu rana daidai Dana LAMIDO Taji dadi tayi masa godiya takoma yiwa Yariman Albishir Da farin ciki yakwana jin antsaida masa ranar Aure sati uku masu zuwa Yaiwa Amarya Hindu albishir Ai ihu taringayi Dan dadi da farin cikin data tsinci kanta aciki Tuni ta gayawa iyayanta tamkar suma sungaji da itan saigashi suma suna murnar Ackn Satin kuwa Mai martaba ya Aiko batun nan Aure Galadima ne da Liman Amintattun Sarki sukaje kai kudin Aure Dubu Dari biyar Da kwatance suka sami gidan domin mahaifin Hindu fitaccene babu Wanda baisan Gidan Minista ba a A T/wada Kaduna Anbasu an amince musu nanda sati ukun Dayake kanin mahaifinsa ne da Yayan mahaifin nata da Amininsa suka karbesu agidan Ministan Anbasu tukuici me tsoka tareda karramawa domin da tsaraba aka rakosu da zasu koma Kaji da cake da lemuka da turarika da shaddoji haka aka zubasu a but din motarsu Koda suka koma suka rattabasa sarki abinda suka gano cewar iyayan yarintafa Sunada mutumci da Halin girma Sarki yaji dadi yasawa abin Albarka Zancen Auren yarima da LAMIDO yazagaya gari anata irgen kwanakin dasuka rage sbd irin shagulgulan da aka shiryi yi sbd nad'in da za,aiwa LAMIDO na zama sarki da zaiyi Lefe ma yarima A England yatafi yahado Shiko LAMIDO dayaje gun *KUYANGA* tambayarta yayi "Gimbiya! Takalleshi da murmushi kan fuskarta tana murza zoben hannunta da MAHBUB yabata kafin yarasu Tace ahankali " Harna zama gimbiyar ?ai naga Gimbiya Matar Sarkice wacce yakeso kuma Yayi murmushi dama shidin ma,abocin murmushine yace "Zeenatu kenan ai kamar kinzamane Tunda saura kwanaki daga lokacin da Aka daura mana Aure nima naxama Sarki Kema kinzama Gimbiya tunda aranar za,ai Nadi Ta gyada kai tanajin annashuwa aranta da kuma sonshi ackn zcyrta Shima hakan yakeji aransa agame da itan Yakatse shirun nata dacewa " Awace kasa kikeso ahado miki lefe? Takama baki "Ni na isa? Wacece ni tab ahado anan Yasha mur! Yace " keko kika isa kuma ke me matsayice da kima don haka daga yau kidaina ma daukar kanki maqasqanciya agidannan domin kintashi daga *KUYANGA* kindawo *GIMBIYA ZEENATU* Tayi murmushi ita kanta sunan yayi mata dadi Yaci gaba da fadin"kinaji ko zamuje Sudan ko Dubai inhado miki komai acan nida Abokina Safwan tare mukai karatu dashi acan mahaifinsa ne liman na gidannan tare TAKAWA ya biya mana zaizo kugaisa Takawa yana sonki Zeenatu ki godewa Allah jarabtar da Allah yayi mk arayuwa tazame miki riba da ci gaba domin ayau yakirani yakaramin kudi akan Wanda yabamu na siyayya nida yarima yace ke tadabance inyi miki siyayya mekyau Yakarasa maganar yana kallon kyakykyawar fuskarta yana murmushi Itama murmushin takeyi tana fadin "Naji dadi nagode ayiwa takawa godiya Yace " To ni zankoma Tayi masa yar rakiya da baifi taku biyar ba ta koma tana waigensa LAMIDO ya burgeta tabbas yanada aji ga iya magana da kalami duk macen dayace yanaso dole ta amsa domin shi din abin sone Tana shiga Daki tafada akan gado tana fara,a Zulaihat tabita da kallo tana fadin "Yarinya tashiga kogin soyayya tafito Dafatan kinyo iyo kinkamo kifi? *KUYANGA* tayi murmushi tareda tashi tazauna tana fadin "Zulaihat kifaye ma nakamo ba kifiba tabbas LAMIDO yatafi dani kamar yadda nima natafi dashi Allah nake godewa da yabani wannan baiwar ta zama matarsa gashi Yace Takawa yana sona yakara masa kudi akan Wanda yabasu da yarima na soyayyar lefe Mahaifiyarsa kawai nakeji bansaniba ko itama tana sona kamar yadda Sarkin ke sona? Zulaihat tace "Hhhhmm Zeenatu kenan aike abar soce itama banajin zataki sonki tunda ta tako har gidannan tazo miki barka da gaisuwa Dan haka kigodewa Allah kawai " Allah nagode maka.cewar *KUYANGA* Zulaihat tace "Ga magunguna can inji Iya Sha,awa tace kada kiyi sake da kowanne masu kyaune akwai nasha da nono dakuma nasha da Zuma anjima zata kawo miki na tsugunno *KUYANGA* takama baki " oh maganin mata kuma tun yanzun? Zulaihat tace "Eh aishine daidai hakan kinga abin xaifi kamaki Sosai " Hhhmmm Allah dai yasa ba daci Zulaita tace "koma me gareshi haka zakisha tunda kinsan Halin tsoffin nan insuka bada Abu ba,ashaba fada zasuyi suce suna mana gata muna gocewa *KUYANGA* Tayi murmushi tadauki magungunan tafara hada wa xatasha ****** Yarima yadauki wayarsa yalalubo nambar abokinsa SAHABI da suka Dade basuyi wayaba Acan bangaren SAHABI yana ganin kiran Yariman yayi murmushi yadaga yana fadin" Dama kana da nambata kamance dani Yarima yace "inada ita mana fushi nayi dakai na abinda kayimin amma yanzu na huce Dan haka Ina gayyatarka Aurena karshen wata SAHABI yayi murmushi yace " Allah yasanya Alkairi nima Auren zanyi nanda sati mezuwa kafin nakama Yarima yace "Shegen kaya wato banda nakira bazanjiba kenan ?lallai na yarda karikeni aranka SAHABI SAHABI yace " ba haka bane yarima Aurenne ba Wanda nakeso ba Hadani akai da yarinyar diyar kanin mahaifina ce ita ke sona Dariya yarima yabushe masa yace "sunmin daidai walh domin insun kyaleka " yar talakawa zaka dauko musu banza me sakaran ra,ayi Sahabi yace "kai " yar INA zaka aura? Yarima yabashi labarin Hindu da yanda suka hadu a Airport a England SAHABI yace "Hhhmmm to bagiringirin ba dai tayi mai Yarima yace " oho dai nafika tunda ni Auran Soyayya zamuyi "Nima bawai kinta nakeba tunda yar 'uwa tace Ina Zeenatu naji ance abinda ta Haifa yarasu Yarima yace " Eh, Sunkusa Aure da LAMIDO... SAHABI yakatseshi da sauri "ya akai hakan dama soyayya sukeyi? Nan yarima yazayyane masa komai SAHABI yace " Gud ammafa naji dadi LAMIDO yaburgeni Allah yasanya Alheri Yarima baikulaba yai masa sallama Acan kasan ransa soyayyar Zeenatu na nan baxai mantawa ****** Anata shirye shiryen biki akowane bangaren Shi yarima agidansa na cikin gari zai zauna baiyda ra,ayin zama acikin gidansu wai kada atakura masa shida amaryarsa Shiko LAMIDO sashi guda aka gyara masa agidan me dauke da dakuna agidan gidan yasha gyara babbane dama ba kowa ciki Aka zuba komai na alfarma agidan Lefe yazo daga Dubai akwatuna goma Sha biyu cike fal da kaya tsadaddu Komai dozinne ciki koina acikin gidan da wajen gidan zancen kayan lefensa akeyi domin sunhadu sunburge kowa Saida aka kaiwa takawa yagani yace sunyi yasa albarka kana mata suka hadu suka dauka bayan Su MAMAH DA FAATU sun gani aka kaiwa KUYANGA Tsoffinsu sunsaka albarka sunyaba Angyagije Zeenatu anfiddata kunya dukda sunsan arina Shiko Yarima karya yahada ackn kayan duk don ace nashi sunfi na LAMIDO Harda key din mota yasaka akan lefen mahaifiyarsa ta saka takardun gida duk akan lefen gudummawarta duk don mutane suga na LAMIDO lami ne sannan su burge mutan Kaduna Amarya anata rawar kai anatashan magungunan karin Ni,IMA da tsukewa sbd gurin anshigeshi Tun fara karatunta a Abroad tayi soyayya da wani Anwar yamaisheta tamkar mata ta amince masa daga baya ya yaudareta yana gama karatu yakoma kasarsu yamance da ita Shiyasa data hadu da yarima takasa ta tsare saida taga natsaida lokacin Aure sannan hankalinta yakwanta Duk kashe kudin da akai alefenta baisa sunyi rawar jiki ko an yababa tunda su ba farin shigar komai bane ita kanta motocinta biyu na hawa tanada gidaje kuma Aiko dai yan kawo kaya suka koma jiki asanyaye danma anbasu tukuici me tsoka Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya Allah yakawomu wannan rana Ranar Asabar takama ranar daurin Auren da nadin sarautar Ancika agdn sarki anata kade kade da bushe Bushe da algaita LAMIDO yasha kwalliyar sarakai Yayinda yarima yai tashi ta angwaye daidai misali ba yabo ba fallasa yasha tsadaddiyar shadda babbar Riga d yar ciki Saida akayi nadi LAMIDO yazama sarki sannan aka daura auransa da KUYANGA kana akayi shagulgula sannan wasu suka dunguma da angoma Yarima suka tafi daurin Aurensa Kaduna Andauro Aure antaho da Amarya a ranar domin sai dare suka iso aka ajiyeta a gidansa dake GRA Itako KUYANGA data tashi daga wannan suna daga yau ta tare ackn gidan sarkin A gidan mijinta LAMIDO daya zamo sarki ayau To fans saimu Tara a page din gaba *GIMBIYA ZEENATU* Cigaban KUYANGA Wanda zakuji badaqala da cakwakiya ackn Wanda nake muku zaton yafi wannan Dan haka kada kubari abaku labari Taku har kullum Auntyn Sayyada da Shahida An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7