Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
bangarensu ta zarce bata bari kowa yagabta ba Adakinsu mutum biyune basuyi bacci ba Zulaihat idonta biyu kawarta Da zulaihat taganta kirji ta dafe tana fadin "wa nk gani kamar Zeenatu? Dama yau kuna tafe amma banji sanarwar ackn gidan ba *KUYANGA* Tazauna tana fadin "wash !barni na huta tukunna zulaihat saiki watson tambayar Zulaihat ta janyo jakar da Zeenatun tashigo da ita takaya tace "lallai kyan tafiya dawowa ina yariman ko batare kuka dawo ba? "Idan tare muka dawo zaki ganmu atarene? Zulaihat Tahau murmushi tana fadin "inafa kawai dai tambayace *KUYANGA* tace '"to batni nahuta tukunna sannan kibani labari akan MAHBUB dina. Zulaihat tayi dariya tace "MAHBUB dinki yananan qalau. "To masha Allahu. ****** Gari na wayewa aka aiko kiran *KUYANGA* labari yakaiwa UMMAH anga Zeenatu ta dawo gdn da daddare Saida UMMAH ta tabbatar da lallai Zeenatun ce tunda tazo da gaggawa kiran tadurkusa agabanta UMMAH tace "Meya dawo dake Gida yarima baisaniba? Gaban *KUYANGA* Yafadi take dabara tazo mata "Fita nayi don ganin gari shine na bace har wasu suka tsinceni suka tambayeni inda nake nikuma namanta inda zance musu bansan kwatancen mazaunin yarima shiyasa dasukace zasu dawo dani Nigeria ban musa musuba UMMAH nagama ji tace "kodai yawon iskanci kika tafi Allah yakamaki aka dawo dake gidan?. Da sauri tahau girgixa kai tana hawaye tabudi baki tace "walh ba haka bane waccen maganar danayi ce gaskiya. UMMAH Tace ta tashi tabata guri tayiwa kanta rayuwar jin dadi wasu ma nema suke Tana futa UMMAH takira Yarima tagaya masa komai Yarima yasha mamakin dahar ta iya dawowa ita kadai yacewa UMMAN yana tunanin akwai wanda yataimaka mata ta gudo zaiyi bincike UMMAH Tace "nidai kawai kadawo Yarima domin nafi son zamanka akusa da mahaifinka don inyana ganinka akusa dashi zaifi shakuwa dakai sannan Hakan ne zaisa sarauta ta dawo hannunka ta sauki tunda wancen Sahoramin yatafi Sudan karatu bazai dawo yanzuba Yarima yace "Nima bana jin Zandawo Yanzun UMMAH saikamar nanda wata guda. Tace "To kayi kokarin kadawo awata gudan kada ka kara fa. Yace "angama UMMAH Na baxan karaba. Sukai sallama Saida Labari yakai kunnan sarki wai *KUYANGA* Dasuka tafi Turai da Yarima ta gudo itakadai Mamaki ya ishi sarki domin baisan anyi tafiya da mace ba da bazai bariba balle har ya yarda yabar yarima yatafi da mace Aranar yasaka UMMAH agaba yace ban kanki in aske Yaita mata fada harsaida tayi hawaye Tana fadin "Ayi hkr Takawa ai anrigada anyi kure dahar aka tafi ba.a gaya makanba baza.a karaba Ita kuwa *KUYANGA* tasake ackn "yan'uwanta Bayi bata nuna wata damuwa ba ko Wani abun Haka suma basu gano komai ba saima yabon canxawarta dasuke tayi wai tayi kyau fatarta tayi kyau acan Shiko MAHBUB kallonta yai tayi yana fara,a dajin dadi yana fadin '" kincanza dayawa Zeenah kinyi matuqar kyau fatarki sai sheki takeyi lallai kin huta acan kinbarmu ckn aikin wahal Inafa Hutu tambayemu kasha labarin komai πŸ˜… tayi fari πŸ™„ tace kaima ka kara kyau anya kayi kewata kamar yadda nayi taka kuwa? Yace "sosai kuwa ko nan gurin damuke xama zaishedi hakan dafatan dai soyayyata batayi gibi ba tananan yanda nasanta da yawa? Gibi kaiπŸ˜‰πŸ˜„ Amma injini ita cewa tayi "Saima karuwa tayi ai aduk inda nake dana tafi ina tare da sonka da kaunarka Yace "naji dadi soaai. Dayake wayar da yarima yabata Boyeta tayi sam bazata bari MAHBUB yagani ba balle yayi mata fassara gara Zulaihat ta nuna mata amma tace kada tafada wa kowa Zulaihat hartana tsokanart dacewa "Toko dai SAHABIN nan zaki Aurane komai kice SAHABI mudai kada kiyi mana sakiyar daba ruwa *KUYANGA* tace "Banga abinda zaisa nabar MAHBUB ba kima bar wannan maganar SAHABI abokin shawara ne abokan taka ce atsakaninmu Dariya kawai Zulaihat tayi tare dajan bakinta tayi gum ***** Watan *KUYANGA* D'aya da dawowa yanayinta yacanxa domin wani laulayi taringayi ga yawan Zazzabin dare Da ciwon Ciki da bacci da kasala da kwadayi da take yawan yi Zulaihat itace tajikinta ita tasan matsalarta na rashin lfyr saita samo mata magunguna taita bata na gargajiya tana jikawa tana bata tana sha Kwana biyu tayi akwance MAHBUB yatada hankalinsa ganin ciwo yaki lafawa Kullum cikin Aikawa da Rubutu yake Aranar data gama shanye jikon da Zulaihat tayi mata aranar tayita malelekuwa atsakar daki mararta na ciwo kamar ta mutu Tana ihu tana kiran sunan Allah Jini ne yaringa xuba ajikinta ta kasanta me yawa Zulaihat ta tsorata ainun Da gudu tagayowa manyansu tsoffin Bayin gidan Da sukazo kanta sukaga ikon Allah abin yafi karfinsu sai suka baxama cikin gidan gun matan Sarki aka gayo musu Mamah ta tsakiya da Amaryar Sarki Faatu mahaifiyar Lamido sune suka fara zuwa gunta kafin UMMAH Tazo Likitansu na ckn gidan aka kira macece *DOCTOR HALIMA WASAI* da kayan aikinta tazo taxaci abin karamine Saida tazo taganta tace musu ai bari zatayi da alamar cikine da ita maza atafi da ita asibiti don inya bare ayo mata wankin cikin Hankalin kowa na gidan yatashi ba,a bari sarki yajiba UMMAH taringa fadin "shegiyar yarinya Me sifar munafukai ashe abinda tayo akasar ta gudo kenan lallai asirinki yatonu Yarima bashida Alhaki shiyasa baima saniba ta munafurceshi. MAMAH tace "ai irin wannan ba,a aibunta mutum kuma bamu tabbatar ba likitanma zato takeyi dan haka muyi mata fatan Alkairi tunda D'a nakowane UMMAH ta harari MAMAH dama haushinta takeji ganin ta rungumi FAATU sunhade mata kai UMMAH ta watsowa MAMAH magana me zafi dan taji haushi tace "TO IN D'A NAKOWANE WANI MA YAYI D'AN MANA NAZACI TUN ZUWANKI GIDANNAN KATON KASHI KAWAI KIKEYI KOKIN TABA YIN BARIN MA? MAMAH jarumar mace me tawakkali tayi murmushi tace "Bantabayi ba Amma nagodewa Allah yabani Taqwa da Sanin yakamta kuma ina dada gode masa nasn kuma bai manta daniba, na tabbatar kuma inhar yabani agaba inda yawan rai xanfiki iya yiwa yara tarbiyya....FAATU ce taja hannun MAMAH tana fadin "kibar maganar haka kiyi shiru ga mutane fa bayinku agun baikamata ba. MAMAH da FAATU suka bar gurin Ita UMMAH Data gwaba me zafi aka mayar mata tafi MAMAHn jin xafin maganar ma Yawwa ai gara hakan dama inbaki yafadi son rai aibaisan me za,a mayar masa ba. *Muje zuwa dai Auntyn Sayyadah da Shahidah* πŸ˜…πŸ˜‚πŸ€£πŸ˜€πŸ˜ƒπŸ˜„πŸ˜†πŸ˜‡πŸ˜‰β˜ΊπŸ˜Š [7/28, 9:09 PM] Ummi Tandama: πŸ“Ώ *KUYANGA* πŸ“Ώ *_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *WANNAN PAGE DIN SADAUKARWA CE GA KAWATA TAKAINA REAL UMMEEY ZEEY Marubuciyar "YAMMATA ALKAIRIN ALLAH YAKAI INDA KIKE INA FANS DINA KUNEMI BUK DIN "YAMMATA KADA KUBARI ABAKU LABARI* *Nabilancy Luv* πŸ’˜ (Auntyn S&S) 45-50 ACAN Asibiti Likitoci sunata iya bakin kokarinsu domin Suga jinin dake zuba daga jikinta yatsaya don tafuta ahayyacinta Saida Allah yataimaka jinin yatsaya kana sukai mata allurar bacci sannan aka nemi "yan uwanta domin suzo adebi jininsu akara mata Likitocin kansu sunyi zaton cikin dake jikinta yazube to ajiyar Allah baifita ba sai wuya datasha Iya Yabi wata tsohuwa cikin wadanda suka kawota tace musu su taimaka su karasa fitar da cikin ba Aurene da itaba Abin kunya taja musu Dr Halima tace mata "Gaskiya bama zubda ciki domin inmunyi hakan tamkar munyiwa ubangiji shishshigine domin bamusan nufinsa dayasa tasamu cikin ba alokacin da bai dace tasamu ba Iya tace "Amma dai da kuntaimaka sbd idan labarin yaje kunnan sarki baxataji ta dadiba dan korarta ma zaiyi agidan kuma gashi bamusan cikin wayeba gata marainiya Dr halima tace "koma dai meye ne iya saidai kuyi hkr mufa bama Abotion a asibitinnan sannan kusani wannan ciki bame futa bane inhar kuma kukayi kokarin yi masa dole to tabbas zaku iya rasa ranta awajen zubarwa Iya Yabi ta tsorata matuqa gaya jiki na rawa tace "to abar maganar Allah yabata lfy yarufa Asiri Acan gida Da labarin neman jini yazowa kowa sai akaita nokewa MAHBUB kuwa da rawar jiki yanufi asibitin sbd yabada jininsa ga masoyiyarsa Shi atunaninsa ko wata lalaurar ce tadaban take wahalar da ita ********* Dayake aranar LAMIDO yadawo yanufi daga SUDAN yagama karatunsa wanda yayi na shekara 5 Rangadi suka futa shida maimartaba domin Sarki yana son LAMIDO kwarai. can bayan gari yajashi wai suyi hirar yaushe gamo anitse kada atakura musu LAMIDO yaji dadin wannan zaman da mahaifin nasa domin sunsa hira tun da sukazo wajen sha daya nasafe sai yamma suka fara haramar komawa gida dayake dirar sassafe yayi Nigeriyar Jakadiya tana gaban UMMAH tana fadin "Ranki yadade naje cikin azama fada domin insanarwa sarki labarin irin abin kunyar da *KUYANGA* ta hada mana ayau sainatarar bayanan natambayi Dogari wai yafuta shida LAMIDO dakuma fadawa Rangadi Lallai nayarda Sarki yana son LAMIDO domin namanta rabon dana ganshi yafuta ran gadi balle bai taba zuwa da YARIMA ba anya kuwa ranki yadade ba asiri Matar can tayiwa Sarki da Yarima ba kuwa? UMMAH ta hau gyada kai ckn takaici tana fadin "Ai walh jakadiya matar can burinta ackn gidan nan baxai taba cikaba domin D'ana shine sarkin gobe da yardar Allah kuma Duk me binsa Da sharri sai nayi maganinsa muxuba mugani Har dare da Sarki yadawo shida LAMIDO labari baije kunnan saba Sai da Sassafe Jakadiya ta bazama taje takai gaisuwa tagurfana agabansa don takware a munafurci da gulma Saida tagama banbadan cinta dayi masa kirari kana ta zayyano masa komai duk abinda tasani daya faru Sarki yayi Shiru kirjinsa na dukan uku uku dan fargaba Yanzu cikin KUYANGUNsa akaiwa 1 ciki?me hankalin ciki da yasanta farin sani sbd yawan Ayyukanta ackn gidanba da ladabinta Yadafe kai yai tsahon minti biyar ahakan kana yadago ya kalli jakadiya yace "maza kije ki kira min matan gidannan su ukun Su UMMAH Da FAATU Da MAMAH yake nufi Dakin fulani tafara isa tagaya mata kana tawuce dakin MAMAH Bayan tasanarta kiran sarki saita wuce Dakin FAATU Tana shiga ta tararta da LAMIDO Suna hira tadurkusa takai gaisuwarta garesu kana ta isar da sako tafuta Koda suka hadu gaban Sarki UMMAH tafisu faduwar gaba sbd tasan kaf dinsu itace me laifi tunda itace silar samuwar cikin *KUYANGA* dan dabata turata kasar wajeba da yarimanba da batasa samuba Bayan Shiru na wasu mintina Sarki yayi gyaran murya kana yakallesu d'aya bayan d'aya yace "Kunada masaniyar Abinda yake faruwa agidannan? Suka hau gyada kai Yace "to ya akai har hakan tafaru ?ya akai *KUYANGA* Tasami ciki a ina akai hakan meyasa kukai wannan saken...? MAMAH ta budi baki ahankali ckn ladabi tace "Ranka yadade Takawa banida laifi ciki FATUU ma tace "Nima dai banida laifi… UMMAH ckn jin haushinsu tace "to tunda bakuda laifi ciki saiku gaya masa me laifin naga alamar dai so kuke kununa masa karara nice da laifi ack Mai martaba yadaga mata hannu yace "ya isa bana son daga murya domin zcy ta tafasa takeyi raina abace yake tambaya kawai nayi ba neman jin fitina ba ya akai hakan tafaru agayamin. MAMAH Tace "Ranka yadade cikin nanfa tun daga turai aka sameshi domin da alamar dashi ta dawo domin YARIMAN ma da suka tafi dashi can tabaroshi baisaniba ta dawo. Sarki Abdallah ya furgita da jin wannan maganar yace "TURAI!? ya akai har *KUYANGA* taje turai batareda sanina ba meyasa yarima yatafi da ita ba,a gayamin ba tabbas FULANI kece da laifi tunda kinsan da tafiyar tasu kika boyemin kinkuma san halina akan in aka munafurceni a abu UMMAH tayi kasa da kanta Yaci gaba da cewa "To shi yariman ne yayi mata cikin ko wa? Da sauri tadago tana fadin "ba cikin yarima bane baima san ta taho ba Yace min ta dade bata gidansa tun zuwanta kasar idonta yabude take bin maza farkan natane yasata ajirgi ta taho ahalin yanzuma yarima baisan tanada cikiba Mai Martaba yace "Koma dai menene laifin na yarima ne ko ba cikinsa bane to kune sila sannan Alhakin yana kanku meyasa Da hankalinki xaki hada mace da namiji suje su zauna agida daya ba matar saba bakomai ba Alhalin kinsan halayyar d'anKi munada masaniyar yana bin matan turawan nan acan Maimartaba yaja ajiyar zuciya yace "Yarima baidauko halin kirki na gidan sarauta ba domin babu me munin halinsa adangina banyi fasikanci ba banyi shaye shaye ba amma gashi Allah yajarabceni da yaron dakeyi Allah nagode maka Allah kashirya minshi UMMAH tahau zubda hawaye tana fadin "Amma dai kasan akwai mahassada na agun baidace karinga aibunta min Da suna gunba., Tsawa yadaka mata "yimin shiru fulani ko ranki yabaci banasan zancen banza wadannan abokan zaman kine ba mahassadan kiba Kuma ki gaggauta kiran yarima awaya kigaya masa maza injini yadawo gida Tahau gyada kai tana goge hawaye Yace duk sutashi sutafi Sun mike kenan zasu futa saiga Jakadiya ta shigo da sauri tadurkusa tace "Anzo da babban batu daga asibitin da aka kwantar da *KUYANGA* Ana bukatar jini ackn gidannan za,a kara mata domin tana cikin wani hali. UMMAH taharari Jakadiya Yayinda FAATU taji wani tausayin *KUYANGAR* Yashigeta tace da jakadiya "Maza Ki kiramin Ladimo A bangarensa kisanar masa yafito yaje asibitin adebi nasa.… Mai martaba najin tafadi hakan yai mata magana "akan wane dalili zaki bashi wannan umarnin Alhalin jiya-jiya yadawo baigama hutawa ba zaki sashi wahala babu nasiyane da baxamu siyaba.? FAATU tace "Ranka yadade dazu muna hira dashi yagama fadamin an auna jininsa anga Group O" ne yace kuma yana son yaga yabaiwa mai bukata domin yasami lada natabbata kuma inyaji ackn gidannan ne zaije da gaggawa Mai martaba yagyada kansa yace "To ace masa yabayar din nima na Amince tunda ladan yake nema. Jakadiya tace "angama zanje yanzu ko ingaya masa. Duka suka fucedaga Turakar Sarkin Koda jakadiya tajewa da Lamido wannan magana ta umarnin yaje yabadajini inji mahaifiyarsa bashiri yahau shiryawa zuwa Asibitin Direbansa na gidan da aka ware masa yanema yace maza yakaishi Asibitin da suke ganin likitansu Zuwansu keda wuya suka tarar ana Auna jinin MAHBUB Likitan daya gama awon jinin yadawo yatarar dasu duka azaune yace "jinin MAHBUB baiyiba damar diba shima yana bukata sannan yanada Typhoid Nan LAMIDO yamike yace da likitan shi aje a debi nasa yanada tabbacin nasa zaiyi tunda group O ' Ne dashi zai iya baiwa kowa jini Likitan daya Auna yagani yatabbatar saiyace da LAMIDO "jininka yayi saidai ba leda daya take bukata ba adebi biyun ba matsala ko adebi daya su sai dayan? LAMIDO yace "Debi biyun na amince lada nake nema bawani abuba Take yakwanta aka debi leda biyu Saida yahuta agadon sannan yafuta daga asibitin ko *KUYANGAR* bai nemi inda takeba don hankalinsa ba,a gunta yakeba bukatarsa dai ta biya yataimaka mata don baiwaye taba ma. Koda yakoma gida mahaifiyarsa taringa masa godiya da addu,a gareshi takuma bashi labarin yarinyar da abinda yafaru da ita LAMIDO yadade yanajin ciwon abin aransa meyasa akaiwa baiwar Allah haka meyasa don anga batada gata aka danne mata hakki? Dayake shi mutum ne mejinkai da tausan bayi sannan gashi da ilimin Addinin domin acan din dayaje karatu Islamic yakaranta yanada sani sosai Yadago da kansa ckn Qunar rai yace da Mahaifiyarsa "Amma sam abinda yarima yakeyi baya kyautawa kodayake UMMAH ta daure masa gindi kuma inada tabbacin shine ma zaiyi cikin Sharri kawai za.ayi mata FAATU tace "Muma tunanin mu kenan Amma dai koma meye ai dole asiri zai tonu tunda Inta futo daga Asibitin zata fadi ko cikin waye kuma Takawa yace agayawa yarima yadawo da gaggawa LAMIDO Yace "Insha Allahu saina taimaka mata Da jikina da abin hannuna. FAATU tayi murmushi tace "Allah yabaka iko D'an Albarka ACAN asibiti kuwa MAHBUB ne Shida Zulaihat suka kebe yana tambayarta shin abinda yaji ackn gidan sarki gaskene? Zulaihat tarintse ido tana futarda kwallah tace "MAHBUB duk abinda kaji gaskiyane Likitocin sun tabbatar Zeenatu cikine da ita na Daya da satittika wanda yaso ya bare Allah baiyiba rabon dai ta wahala ne Nayi kuka sosai danaji hakan dama kuma nafara fahimtar hakan kafin rashin lfyr tata. MAHBUB yarintse idanuwa yana hawaye kirjinsa zafi yake masa meyasa Zeenatu taci amanarsa?meyasa Zeenatu tacanza hali? Meyasa tabiyewa sharrin Shaidan da Namiji ta Amince da wani Alhalin Sunyi Alkawarin Aure ……? Muje zuwa fans [7/30, 2:25 PM] Ummi Tandama: πŸ“Ώ *KUYANGA...* πŸ“Ώ *_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Nabilancy Luv* πŸ’˜ (Auntyn S&S) 50-55 Jakadiya ce Zaune agaban UMMAH tagama kawo mata tsegumin Matan Sarki wai da alamar sun hade mata kai sunaso asirinta yatonu agidan abata mata d'a UMMAH ta furzar da iska abakinta kana tace "jakadiya nadade da sanin abinda suke ciki nasan basa sona dani da yarima Kuma walh sainayi maganinsu agidan nan daya bayan daya cikinsu Jakadiya tace " nibakomai nakeji ba sai *KUYANGA* Kada tacewa sarki cikin na Yarima ne domin zata iya k'ak'aba masa don tagaji abin arxiki na gdn Sarauta UMMAH ta quta kana tace "zankuwayi maganinta domin nagama yanke shawarar abinda zansaka kiyi mata Wanda inhar kikayi zanbaki makudan kudi da zinare da gida agefen gari ckn gidajen Yarima Jakadiya tahau murmushi tace " fadi ko meye kikeso inyi zanyishi uwar dakina "yr sarki jikar sarki me babban daki uwar gidan Sarki Fulani uwar Yarima Wanda zaihaye karaga da yardar Allah UMMAH tayi murmushi najin Dadin kambamawa tace " So nake dazarar ansallamo *KUYANGA* daga asibiti yazamo tadawo karkashin kulawarki koda ace ta fadi ckn Yarima ne ko bama nashin bane yazama tana tare dake kullum zansa ta dawo dakinki inyaso kafin ta haihu kisa mata guba a abinci ko kishaqeta da filo ta mutu kawai Zabura jakadiya tayi kana tace "Ranki ya Dade bazai yiyu akasheta da gaggawa ba za.a fassara mu kokuma azo ayi nadama gara dai inta haihu inbi dare inkashe abinda ta Haifa UMMAH tayi murmushi tace " Dakyau jakadiya kinada hangen nesa tabbas zama dake akwai riba hakan ma da kika tsara yayi don haka kizama ckn shiri Koda jakadiya ta futa daga dakin UMMAH saita nufi Dakin MAMAH domin kai mata tsegumin UMMAN tayi sa,a kuwa ta tarar da FAATU atare da MAMAHn suna hira Jakadiya takai gaisuwa garesu kana ta xauna gefe bakinta na motsawa irin na munafukai sunso tsegumin MAMAH tace "ya akai jakadiya akwai wani abun ne? Jakadiya tahau shafa hab'a tana fadin 'Dama wani Abu najiyo dayake damuna tunda naji nakasa fada muku FAATU tace 'ikon Allah mene wannan Abu fadi muji shi Jakadiya tayi kasa da murya tace " Ranki ya Dade Gimbiya FAATU zancen ma dai akan d'an kine domin FULANI tananan tana hakon tayi masa mugun Abu domin kada yagaji sarautar mahaifinsa kada ma yaji yanaso aransa sannan inada tabbacin Yarima ne yayiwa *KUYANGA* cikin nan amma naga tanaso adanne mata hakkinta don haka yakamata kuyi wani Abu akai MAMAH Da FAATU suka kama baki suna mamaki domin kuwa basu zataba duk da sun Dora zarginsu akai MAMAH tace "lallai jakadiya mungode munyarda ke me kaunarmuce don haka munbaki izini akan kiringa bibiyar lamarin don kar hakanta yacimma ruwa Jakadiya tace " Angama ranki ya Dade Amaryar Sarki Dangwale shalele agun maimartaba Uwar Lamido me jiran gado Koda jakadiya tafuta sai FAATU tacewa MAMAH "Nifa shiyasa bantabajin inason LAMIDO yahau kankaragar nan ba in maimartaba yayi murabus haka shima LAMIDON bashida ra,ayi Sam mulkin baya gabansa balle yadorawa ransa MAAMAH tace " to duk da hakan dai saiki tashi tsaye kiringa addu.a ba dare ba rana kirage bacci kigayawa Allah akan yakawo muku agaji kada aje a cutar miki dashi Nan dai MAMAH tayita bata addu,o,in na kariya domin sunfurgita da zancen da sukaji abakin Jakadiya ********** A can Asibiti kuwa anbaiwa *KUYANGA* kulawa daidai gwargwado harta samu kanta Zulaihat CE agunta kafin arubuta musu sallama Domin sai data kwana daya a asibitin kana aka bata sallama Suka dawo gida Zulai ita ta gaya mata duk abinda yafaru da ita tunda a sume aka debeta xuwa asibiti batasan me akai mata ba tundaga Karin jini da daukar jininta aka auna aka gano tanada shigar cikin Hannu ta Dora aka taringa kuka tana fadin "Nashiga uku na cuci kaina da tun farko na aminta dakai ban bujire makaba.biyayya batayimin ranaba wayyo Rayuwata ta gurbata Allah kadauki Raina kona hu.... Zulaihat tayi saurin toshe mata baki " kada kice haka Zeenatu Allah yajarabceki da hakan babu tsimi babu dabara sannan Ni bana zarginki sai tausayinki "Inke bakya zargina Zulaihat MAHBUB fa ? Nasan kome zance baxai yardaba Allah ne kadai zaifutar ni ko a gidannan. Zulaihat tace " Waye yayi miki cikin? *KUYANGA* Tace "wakuwa zaimin inba Yarima ba cikin sane bantaba sanin wani namiji ba inba shiba harta dole yakemin....nan tahau baiwa zulaihat labarin yanda rayuwarta ta gudana a Turai tareda Yarima bata rage mata komai ba har taimakonta Da SAHABI yayi Zulaihat tashare hawayen tausayin zeenatu tace " Zeenatu Yarima yacuce ki domin ayanda nafuskanci MAHBUB yaji ciwon abun yakuma zaci ko kinyi cikinne abisa sonki har kuka yayi yace yayi nadamar fara kaunarki yace kincuceshi yayi kuka sosai a asibiti Kuka takara fashewa dashi jin yanda MAHBUB yadauki lamarin Shikenan tafaru ta kare tasan ko a agidan bakowa zai yarda ba sai Wanda yasan halayyar Yariman Zulaihat ita tayi ta dannarta tana bata baki Dan kwantar mata da zcy Kwana tayi kuka duk tafuta hayyacinta ta rame Ko futa dainawa tayi saidai Zulaihat ta karbo mata abincinta in an gama abangaren nasu dayake dakinsu daya da zulaihat din Tayi zaton ko MAHBUB zaizo yadubata amma saitajishi shiru na wasu kwanaki baizoba Sannan takara tabbatarwa lallai yadau zafi da ita Sati Daya da maganar cikin da *KUYANGA* Tazo dashi daga turai YARIMA yadawo Magana ta yada ko ina na cikin gidan sarki Wasu suna yarda na yarimane wasu kuma suna ganin bazai zama nashiba tunda ance yawonta take da maza dataje turan KARSHEN TIKA TIKI TIK!! Dawowar yYarima yasa kowa agidan yashiga murna domin ansan tunda yadawo kasar za,a samo matsaya akan cikin *KUYANGA* Tana Zaune adaki tana tunanin data sabayi Zulaihat ta shigo da Sauri tace mata "Zeenatu yi sauri kidauko hijabi muje an aiko sanarwa daga Fada Sarki nabukatarki agun Yarima yana can fadar da Kaf Ahalin Gidan za,ayi Zubeben kwarya... Gabantane yafadi tareda dafe kirji take hawaye suka hau zarya akuncinta Zulaihat tajata jiki tace mata "daina kuka kwantar da hankalinki me gaskiya yana tare da Allah Abinda kika Sani shi zaki fada kada kiji tsoro kada kuma kirage komai *KUYANGA* Tahau gyada kanta taredajin karfin guiwa ajikinta Zulaihat tace " muje inrakaki fadar...... πŸƒπŸΌβ€β™€πŸƒπŸΌπŸ‘­πŸšΆπŸΌβ€β™€πŸšΆπŸΌπŸ•΄πŸ½πŸ‘ͺπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©πŸ‘¨β€β€β€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€β€πŸ‘© fans kutaho rakiya mana Duk masoyin *KUYANGA* kada yasake abarshi abaya ataho arakata Fadar *SARKI ABDALLAH* MUJE ZUWA FANSπŸ˜… [7/31, 11:29 AM] Ummi Tandama: πŸ“Ώ *KUYANGA...* πŸ“Ώ *_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *Nabilancy Luv* πŸ’˜ (Auntyn S&S) 55-60 CARBI ne ahannun *KUYANGA* datake ja ackn burmemen hijabin dayake jikinta Addua kawai takeyi Akan Allah yabata Nasara yashige mata gaba yakuma dorata akan maimartaba Gaban tane yafadi ganin yanda fada ta cika da ahalin gidan daga matansa da yaransa YARIMA da LAMIDO da kuma fadawa da Galadima da sauran masu mukaman gidan Bayi ne kawai basa gurin Kowa ita yake kallo itako kanta akasa tasami guri anesa dasu tazauna Zulaihat ma ta xauna kusa da ita Maimartaba yana ganin shigowarta yayi Gyaran murya ganin tazauna nesa da mutane duk aka nutsu ana kallonsa Yace " *KUYANGA ZEENATU* Ke muke jira kuma adalilinki muka taru anan Dan haka kidawo tsakiyar mutane kizauna domin ki amsa tambayoyi daga bakina Tayi saurin tashi tabi umarni takoma tsakiyarsu inda fadawa suka bata guri akusa da Yarima dayake kusada Sarki LAMIDO na gefen yariman Wanda tunshigowar *KUYANGA* Yazuba mata idanu yana kare mata kallo Bayan ta zauna Mai martaba yawatso mata tambayar data rikita mata kwanya "Dawa kike tarayyar fasikanci a kasar waje ??? Ahankali tace " Bakowa, Yace "To waye yayi miki ciki? Hawaye na zuba a idonta tace " cikin jikina bana kowa bane illah na YARIMA! fadawa suka hau salati Yayinda Sarki ya rintse idanu jin yasami jika Dan gaba da fatiha a ckn gida Suko matan kirji suka dafe alamun mamaki Yarima kuwa fuskar sace ta nuna bacin rai tsababa ji yake tamkar yashaqeta ta mutu akan wannan tonon sililin datayi masa LAMIDO kuwa girgiza kai kawai yk yi na al,ajab sannan yana mamakin yayan nasa da wannan hali UMMAH mahaifiyar Yarima Ta dakawa *KUYANGA* Tsawa "karya takeyi munafuka saikin nemo Wanda yayi miki inma ackn turawan da kika barosu kika gudo Sarki ne yatsawatar mata akan tayi shiru Yajuya kan Yarima yace masa " YARIMA ya abin yake? kanada tabbacin naka ne ko ba nakaba? Yarima yaji sassanyar Tambaya sai yahau gyada kai yana fadin "Ranka ya Dade bansan da maganar ba baninayi mata cikiba Sarki

Chapter 4 of 7