Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shi kuwa bunayya da sauri ya bi bayan d'aya daga cikin likitocin yana tambayarsa ,yanayin jikin umminsa ,suna tafiya doctor na yi Masa bayani ,har suka shiga cikin office dinsa, ya dan juyo yana dafa kafadar bunayya "ka kwantar da hankalinka inshallahu zata samu sauki, ka dinga had'awa da addua zamuyi mata allurar yanzu dan ta samu relief, bunayya yayi jugun hawaye na kwarara akan kuncinsa , da kyar yayi karfin halin juyawa batare da ya cewa likitan komai ba, ya bar office din kai tsaye d'akin d'a'a kwantar da ummi ya nufa ,yana shiga ta bud'e idanunta tana ganin shine, ta d'auke kanta zuwa wani bangare tare da cewa "kace masa kar ya k'araso gareni banason ganinsa ,ya bar d'akin nan bana son ganina acikin idanuna , karaf maganarta ta shiga cikin kunnuwanshi . tun kafin Wanda aka bawa sakon ya fad'a masa , ya tsaya daga inda yake yana duban ummi da har lokacin kuka take .. "Ummi .... Ba..bana son jin komai daga bakinka ta k'arasa maganar tana sauke numfashi da kyar " Hannu abi ya d'aga masa al'amun ya tafi kawa .. Ahankali ya juya jikinsa a matukar sanyaye ya fice ya nufi harabar hospital din yana jin wani irin kuna acikin zuciyarsa , kai tsaye bayan mota ya bud'e ya shiga ya zauna yana jin wani irin bakinciki ,batare da bata lokacin ba direba ya yiwa motar key ,suka bar hospital, zaune kawai yake a bayan motar amman shi kad'ai yasan abinda yake ji ,shi kad'ai zai iya misalta halin tashin hankali da yake ciki. da fari baiyi tunani zai damu a dalilin cikin jikin muwaddat ba domin ganinsa haka shine sakamakon masu hali irin na iyayensa ,sai yanzu ya fahimci abun ba haka bane, suna shigowa gidan ,ya nufi part din umm domin ganin halin da muwaddah take ciki ,can karshen gadon ummi ya iske kwance tana jujjuya Kai had'e da rike kasan mararta ,ya k'arasa gareta da sauri yana k'ok'arin kamota jikinsa ta goce "karka ta 'bani ... kana ta yunkura ta mike tsaye ta soma tafiya. Da kyar take takawa ta fito tana layi hakan yasa ya biyo bayanta da sauri yana Kiran sunanta "muwaddat Ina zaki cikin wannan hali ? Ta juya ahankali domin fad'a Masa bakar magana jiri ya kwasheta tayi kasa zata fad'i cikin rud'ewa ya kamota jikinsa ya d'auke cak dan ganin jini a bin kafafunta , part dinsa yayi daita , da kyar ya samu jinin daya soma bin cinyoyinta ya tsaya amman ya Sha wuya sosai, yanzu wani irin son cikin ne ya dawo masa sabo fil .... Allurar bacci yayi mata domin tasamu natsuwar zuciya, amman ta burkice masa tana zuba masa ruwan bala'i .. Duk yadda yayi k'ok'arin ya shawo kanta ta fahimceshi amman abin yafi karfinsa, sai faman had'ashi da Allah take ya rabata da ciki ,gabad'aya ya sake shiga rudu .. yana kallonta ta fice daga bangarensa shima ya biyo bayanta anan suka ci karo da idanun baba mai gadi kallo daya yayi masu ya kawar da kansa yana Allah wadai da masu hali irin su "da al'amun uwarsu bata da lafiya, amman hakan bai saka sun hakura da juna ba, wannan wace irin maseefa ce haka? yayi maganar a kasan ransa " ko yake zuwa yanzu ya daina ganin laifin su sakacin iyayensu ne .. Binta bunayya ya shiga yi har ya karaso inda take bai tsaya wata wata ba ya d'auketa ya sabata a kafad'arsa yayi d'akinta daita ,ya kwantar yana mata sannu , sannan ya koma cikin part dinsa, har kusan magariba yana d'akinsa kwance bai tashi ba tunani Kashi da Kashi ke dawainiyya dashi, jifa jifa ya kan Kiran abi ya tambayi yanayin jikin ummi ,sannan haka ya dinga zariya tsakanin part dinsa zuwa na ummi domin duba lafiyar muwaddat.. Karfe biyun dare muwaddat ta farka daga baccin daya d'auke ta ,yana zaune akusa daita ya zuba mata ido, hannushi cikin nata jin motsin datayi ne yasa ya gane ta farka da sauri ya mike yana Kiran sunanta muwaddat, sai ma ta rufe idanunta wasu zafafa hawaye na zubo Mata babu irin maganar da bai mata ba amman ta shareshi band'aki ya shiga ya had'a mata ruwan mai d'an dumi zuwa yayi zai d'auketa duk da Jikinta babu kwari sai data fixge tana zabga masa uwar harara "bana son jin hannunka ajikina na tsaneka ka rabu dani .. Kuka ne yaci karfinta, jin kukan nan yake har cikin zuciyarsa ya kasa ce mata komai " Can kusan minti goma yace "plz muwaddat kina bukatar kulawa da taimakona a daidai wannan lokacin .. "Banason ko wani iri taimako ne daga gareka ka barni na mutu na huta da wannan bakinci ," komawa tayi tayi kwanciyarta, har kusan asuba yana fama daita tana jin Fitarsa matsalaci .... Koda ya dawo ma kusa daita ya tsaya ,ban da hawaye babu abinda idanuwanta ke zubarwa cikin sanyayyiyar muryarsa yace "Dan Allah muwaddat na rokeki ki bar kukan nan haka kada yayi miki illa " "Yaya kuke son nayi, gaki tashin hankali gurinki ,ga matsalar ummi ,Ina bukatar kowane daga ciknku arayuwata ,bana son ba rasaki "kiyi hakuri muwaddat ki d'auka kaddararmu ce tazo haka ... Gefe ta juyar da kanta "ka rabani cikin Nan ni banaso ....... Shiru yayi kawai had'e da kafeta da tsumammun idanunsa ,yau tazo Masa da abubuwa dayawa tashin hankali da rudani , gabad'aya duniya ta cakud'e mashi waje d'aya ba ta bangarenta ba, bata bangaren umminsa ba ,bai ta'ba sanin haka tashin hankali irin wannan daya ke ciki yake da ciwo ba , "ya zai yi da kaddara data afka masa? " d'an da zai fara samu a duniya shine yazo ta wannan hanyar ...." Cike da muryar kuka tace "dan Allah ka rabani da cikin tun kafin ummi ta dawo ,na had'aka da Allah ka ci .... "Dan Allah dan annabi malama ya isheki " "enough muwadda " " Wai ma me kika d'auke ni ne ? "Mahaukaci ko me ? "Nasan na aikata zina dake na tsawon lokaci har ga sakamakon nan ajikinki ,amman wallahil azim bazan iya zubar da wannan ciki ba .... "Bazan iya d'aukar wannan zunubin ba ... "bazan iya kashe kiyashi ba ,bare gudan jini ...... I can't muwaddat Yana gama fad'ar haka ya juya fuuuuuuuuuu cikin tashin hankali... Mmn sudais MUWADDAT PAGE 39 page 39 dan baka hanzarta zubar min da cikin nan ba ,zan gudu, dan kuwa zaku nemi gabad'aya ku rasa, bai tsaya ba, yace"ki fi ruwa gudu, idan kin tashi gudun ki tafi lahira karewarta kenan, ciki ne dai ni muhammed auwal bazan zubar ba,ba kuma zan saka hanunana ba,na dai d'auki zunubin aikata zina ,amman batu na zubda ciki bai k'arasa maganarsa ba ya k'arasa ficewa daga d'akin, aiko ta sake rushewa da kuka.. Kai tsaye bakin get ya nufa inda yana zuwa ya tsaya ,a kan baba mai gadi ,yana bashi umarni "baba ka tsaya kan aikinka sosai ,acikin gidan akwai muwaddat kamar yadda kasani ,duk lokacin dana nemeta na rasa abakacin Aikinka, kuma wallahi tallahi kaji na rantse kotu ce zata rabumu .. . yana gama fad'ar haka ya juya ya nufi inda motar ummi take parke Bakin baba mai gadi na rawa yace " Ina ai bama za'a yi i haka ba ,ai tunda ka fad'i haka, an gama. aranshi kuwa cewa yayi tsinanun ya'ya kawai Allah yasa karku kashe iyayenku da fitinarku, yana nan tsaye har sanda bunayya ya tadda mota,shi kuma ya bud'e mashi get ya fita, sannan ya samu guri ya zauna akan farar kunerarsa ya kunna radio ya soma sauraron labarai .. Ahankali yake tuki yana zance zuci ,har sanda ya kawo hospital inda mutanen da suka san shi d'an madam ne suka shiga yi masa, ya mai jiki,shi kuma yana basu amsa da alhamdullahi, adaidai bakin Coridon da zai Kai ka dakin da ummi take, suka had'u da abi wanda ya dawowarsa kenan daga massalaci .gaishe shi yayi had'e da tambayarsa jikin ummi ? Alhamdullahi ka godewa Allah jikin umminka yayi sauki sosai ,zuwa anjima nan zamu dawo gida yaya muwaddat din take, hope babu wani Abu da ya sameta jiya? "Lafiyar nan dai da sauki abi ,tare suka k'arasa cikin d'akin abi nayi masa nasiha koda suka isa d'akin ,sun iske ummi ta idar da sallah tana k'ok'arin mikewa da kyar ,sai dai har lokacin kallo d'aya zaka mata kasan tana cikin tashin hankali da damuwa mara misaltuwa ,kallo d'aya tayi masa ta d'auke kanta daga garesa ta koma kan gado ta zauna ya k'araso gareta yana kok'arin yi mata sannu cikin sanyayyiyar muryarsa ,amman Sam taki amsa masa illa ma sake tamkar wace aka aikowa da sakon mutuwa ,abi ne ma ya d'an bashi kulawa, amman shi ba wannan kulawar yake so ba shi yafi son ummi ta amsa masa, bazai iya jurar fushin umminsa ba ... haka ya cigaba da tsayauwa agurin yana bata hakuri har karfe takwas ta bugu ganin ta mike tayi kwanciyarta akan gadon marasa lafiya ya juya ya tafi . had'e rai datayi Har yaje asibitin ya dawo damuwa ce cike da zuciyarsa ,duk wanda ya gansa yasan yana cikin matsanancin 'bacin rai bai sake neman inda muwaddat take ba yayi zamansa a bangarensa ,baba mai gadi kuwa ya kasa ya tsare abakin get. Bayan sallar azahar yaji hon din shigowar mota, haka nan jikinsa ya bashi abi ne suka dawo ,dan haka ya tashi ahankali ya isa jikin window tare da yaye labule yana lekewa, tabbas shi din ne ya hango har da umminsa gabansa ne yayi wani irin mugun fad'uwa da karfin gaske. ya dawo ya canza kaya zuwa jallabiyar brown colour sa'banin d'azu da yake sanye da vest da boxer, ya fito yana taku cike da sanyin jiki ,koda ya fito har sun shiga cikin gidan shima yasanya Kai ,inda ya iske binta mai aiki sai faman jerawa ummi sannu take tana amsawa da kyar shima sannun yashiga yi mata .. Ganin binta tsaye ne yasa ummi taki korar bunayya,da binta zata tafi ummi tace "ina muwaddat? "Ina ganin tana d'akinta" "Je ki kice mata tazo yanzu"binta tace "tam had'e juyawa ta bar parlour'n. binta na barin bangaren ummi tashiga Zuwa bunayya ruwan bala'i ta inda take shiga bata Nan take fita ba abun har yaso bawa abi mamaki dan shi tunda yake bai taba sanin mukaramarsa na da irin wannan halin ba sai wannan lokaci "ishaq ka fad'awa d'anka...ka fad'a masa banason ganinsa arayuwata da duk inda nake ,har ya gama iya rayuwarsu kar ya kusanto inda nake bani bashi .. "Wallahi matukar baka bukatar nayi wani mummunar furuci akansa ya fad'a masa kiyayi zuwa inda nake ,ta k'arasa maganar tana hakki sama sama... Alama abi yayiwa bunayya ,daya bin umarninta yasan duk wannan abun datake na wani lokaci,da kuma bacin rai ,bacin rai kuwa babu abinda baya sawa Bunayya wanda idanunsa suka rikid'e sukayi ja tsabar tashin hankali da yake ciki, ya juya da kyar yake daga kafafunsa ya fice daga parlour'n. Yana fita ummi ta fashewa da wani sabon kuka. Jiki a matukar sanyaye muwaddat ta shigo parlour'n tamkar gazar da kwai ya fashewa aciki ,kanta sunkuye a kasa ,dan bazata iya duban idanun ummi, ba haka ma abi ,ummi ta d'ago ta dubeta cike da tsantsar 'bacin rai da nadamar rikonta datayi arayuwa ,datasani kam tayi shi babu adadi ,data san haka zata zamo mata arayuwa wallahi da batayi ganganci d'aukota ba, ta barta tare da iyayenta ganinta yanzu yasa kukanta ya tsananta saboda wannan tashin hankali yasa tayi wata irin katuwar rama wanda yasa kallo d'aya zaka mata kasan tana d'auke da ciki ,muryar ummi a sarke tace "yanzu saboda Allah da annabi kun kyauta min kenan, barin ke muwaddat da kika biye masa, ke fa macece.. ? "da girmanki da hankalinki da tunaninki kika biye kaninki suka aikata zina.. Abi yayi saurin runtse idanunsa kana ya bud'e su yana nunawa muwaddat gurin zama saboda ganin yadda jikinta ya soma "mai yasa kika biyewa kaninki kuka aikata mana haka muwaddat? "mai yasa muwaddat? "ko kin manta matsayinki ahalin yanzu kin tsaida mijin aure ,har ma da sa ranarsa akanki? "wai a ina ma kuka yi wannan cikin na tsawon wata biyar bamu sani ba? ummi ta mike tayo kanta gadan gadan abi ya tsaidaita ta hanyar rikota .. "ka barni nayiwa wannan shegiyar yarinya dukan mutuwa ,da girmanki muwaddat da hankalinki da tunaninki idan bunayya yaro ne ke yarinya ce ? "'shekara ashirin da biyar zuwa da shida amman kika biye masa kika ruguza tarbiyar dana baki na tsawon shekaru, "yanxu me kike son duniya tace akaina? ta k'arasa mgnr tana kuka tana nunata da yatsan hannuta "hakika kun cuceni kun cuceni.. kunci amanata ,kun yaudareni yanzu ni na cancaci wannan tozarci muwaddat, na amince dake, na baki dukkanin yardata, ban taba tunanin zakiyi min haka ba "why muwaddat? why why why!!! kika biye wa son zuciyar auwal? "wayyo Allah ni mukarama, yau ni tawa ta sameni mai zancewa d'anuwana ya fahimceni..? abi ya kamota ya zaunar daita agefenshi "kiyi hkr mukarama ,kinsa Baki da lafiya zuciyarki na bukatar natsuwa ki d'auka haka tamu kaddaro tazo, babu yadda zamuyi bamu isa mu gujewa kaddararmu ba lahaula wala kuuwata illa billah, babu tsimi babu dabara duk abinda Allah ya tsarawa bawa to babu tantama sai abun ya sane shi ki yawaita furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun acikin zuciyarki... muwaddat ta taso daga inda take zaune jikinta na rawa, ahankali take d'aga kafafunta har ta K'araso ta durkushe agabansu' abi dan girman Allah ka bar ummi ta zarta da duk wani hukunci data gadama akaina,na cancaci fiyye da duka agurin ummi akan abinda nayi, tayi min duk abinda zatayi koda kuwa ta kama ta kasheni ne, ka barta matsawar zata huce takaicin abinda nayi mata. ta juya ta fuskanci ummi idanunta taf da ruwan hawaye suna zuba akan kuncinta umminah kiyi hkr dan girman allah ki yafe mana,duk da ba ke ce kika kawoni duniya ba amman idan kika tsine min sai tsunuwarki tayi tasiri akaina, dan Allah ummi ki taimaka ki taimaki rayuwata ki rabani da wannan ciki koda kuwa mutuwa zanyi na gwan wannan cikin shegen dake jikina... haka akan dai na haifi daga ummi har abi saurin runtse idanuwansu sukayi da saboda d'acin kalmar data fad'a, "first jikan da zasu samu a duniya shine yazo mata ta wannan hanyar da bata dace ba, ita kuwa wani irin kuskure ta tafka arayuwrta? "ummi wallahi nayi danasani arayuwata. abi dan Allah kabawa ummina hakuri kace ta yafe min wallahi sharrin sheidan dana zuciya, wallahi bazan sake ba na tuba abi ta k'arasa maganr cikin kuka tana had'e hannunwanta duka .. shiru ne ya biyo baya sai sheshekan kukan ummi da nata dake tashi ahankali "baza'a zubar da cikin jikinki ba muwaddat ,za dai musan abinyi tashi ki shiga d'akinki abi ya fadi hkn yana kallonta... ta yunkura da kyar ta tashi tashiga jan kafafunta da suka mata nauyi ta nufi d'akinta tana kuka, tana shiga ta ta fad'a kan gadon tana sake fashewa da wani kukan "na cutar da kaina,na cuci rayuwarta yau nice d'auke da cikin shege" wayyo Allah ni muwaddat ina zan kai wannan kayan abun kunyar.. . ..? zumbur ummi ta mike tashiga zagaye parlour'n tana zance zuci" dan dole tasan abunyi kafin kunnuwan mutane gari dana danuwanta suji wannan abun kunyar da aka aikata acikin gidanta ,dan dole ta nemawa kanta mafuta, "to mai zanyi ? 'mai zanyi akan wannan cikin..? Ta tambayi kanta. "dole na samo mafurtar abinyi, shiru tayi sannan ta nufi d'akin cikin sauri abi yabi bayanta shima atare suka Shiga d'akin "mukarama yanzu Yaya zamuyi? ta tako ta fad'a kirjinsa tana wani irin kuka mai ban tausayi •ban sani ba ishaq. bansan abinda zamuyi ba. amman nafi tunanin mu zubar da cikin nan kawai shine kwanciyar hankalinmu. "wannan ba shine mafuta ba mukarama , illa zunubi da zamu d'aukarwa kanmu, muyi hakuri mu rungumi kaddararmu data samemu wannan abun daya faru duk laifinmu ne,kuskurenmu ne mukarama, tunda yaron nan tun farko ya nuna mana aure yake so, ya bini ya biki yayi iyakacib kokarinsa amman muka kekashe kasa muka ki yarda •mu kace karatu 'yanzu ga illar abinda son zuciyarmu ya jawo Mana, da'ace mun barsa tun farko yayi aurensa da duk haka bata faru damu bae kalu bali ga iyaye masu hali irin namu ,mukarama ni dake muka tsunduma yaranmu cikin wannan mummunar rayuwar _ •wa man kaddarallahu haqqa kadarihi* ki yarda da wannan kaddarar data samemu mikaram daman duk muslimi dole ne yayi imani da kaddara mai kyau ko akasinta, ni dai na yarda da kaddara data fada mana kuma na amsheta da hannu biyu biyu wannan shine sakamakon iyaye irinmu masu biye son zuciyarsu zare jikinta tayi a jikinsa ta koma ta kwanta akan katifa, numfashi take saukewa ahankali ahankali kana ta runtse idanunta gam ta dinga jin wannan bakon aliamarin dake faruwa daita tamkar a almara ko wani shirin film, itace zatayi jika ta wannan hanyar? "anya zata iya wannan hakuri ta bar cikin nah kuwa? "kai dole tasan abunyi, Cire cikin zatayi alabashi daga baya ,sai a yi musu aure , Udata bar wannan abun kunyar azo ana zaginta a gari wallahi gara ta Cire mata . koda a boye ne batare da sanin daci da radadi tana jin bazata iya jure wannan abun kunyar data aikata da kaninta ba, tana jin tamkar tattara inata inata tabi uwa duniya. ko ta kashe kanta "karki kashe kanki ki mutu kafira ga zunubi zinar da kika aikata ga na kisan kai, gara ki Shiga uwa duniya take ta amince da wannan shawarar da zuciyarta ta bata"cikin sauri ta karasa inda jerin akwananta suke ta dauko karamar ciki ta isa gaban wardrobe dinta tashiga dibar kayanta da abubuwan amfaninta tana zubawa aciki.. can bangaren ummi dake kwance akan gadonta tana faman joyi daga karshe ta yunkura ta mike jikinta tmkr ba nata ba, ta zauna tana sake goge hawayen daya gagara tsayawa a idanunta Ita isa bakin bayi da niyyar Shiga ta dauro alwala .cak ta tsaya kirjinta na wani irin harbawa can kuma tasoma jiyo motsin haka nan zuciyarta lace ta leke taga me ke faruwa . cikin sanda ta fito ahankali tana taka step. gabanta yayi wani irin mahaukaci bugawa da karfln gaske sakamakon abinda idanunta yacin karo dashi , muwaddat ce ke kiciniyar bude kofar babban parlour'n da niyyar fita. Wata uwar razananniyar Kara ta Saki hade da jero sallati ,wanda janyo hankalin abi ya fito daga d'akinsa a firgice Yana dubansu muwddat kuwa wani irin tsalle tayi hade da jifa da akwatin hannuta ,jikinta ya kama rawa take kuma dan cikinta yasoma motsi sosai abinda bata ta'ba ji ba kenan a tun samuwarsa.. •me nake shirin gani yau ni mukarama? "me kike Shirin aikatawa muwaddat "ina zaki da akwati? muwaddat ta rushe da kuka jikinta na rawa . •tambayarki nake nace ina zaki ? "Kar dai guduwa zakiyi muwaddat ki barni cikin wannan tashin hankalin? tasoma taka step biyu biyu ko ganin gabanta batayi har ta k'araso gabanta tace •guduwa zakiyi ki barni ko me? jin tayi shiru taki amsa mata tambayoyunta yasa tashiga yaryarfa mata mari •guduwa fa kike shirun yi muwaddat? "yanzu daman zaki iya barin? "zaki iya guduwa ki barni cikin damuwa ? " idan kin gudu ina zaki eye? Ki fada mun ina zaki tana tambayar ta tana yarfa Mata wasu marurukan daga karshe ta rufe ta da duka "Gara na kashe ki da hannu na binne gangar jikin ki akan ki gudu ki Shiga k' wannan shine kare na farkO da ta SMaya hannunta aiikin a tun ,duka tayi mata har sai da abi ya tsaidaita tukLJnM1 kasa tana kuka •guduwa take Son yi ta barni ishaq Cikin tashin hankali " miki daga • kike k Ok'arin kinsa jurar rashinki ba, tasorna gindi Z•JWa inda di take durkushe gwiwaWinta tana ta ajikinta •karki barni dan Allah karki barn. 'dan kika barni Zu•ciyata buga Zan mutu 10kacina baiyi zatayi tsanani da muni ta kama fuskarta da hannuwanta duka tana kallon Cikin •mai baki min kina bunayya ba? •wallahil dana San kina Son Shi haka da tuni na barku kun aure akanki San zaki hake, bansa adalilin Son iya mallaka masa jikinki makauniyar SOyayya kadai Ce Zata Sa ki jikinki bashi baki nuna kOda kina Shi rnuwaddat ta runt* idanunta Wasu zafafan zafl Shiga tana girgizawa ummi •yi min Shiru farkO sake tafka babban kuskuren aray•uwata da har na matu bazar' daina danasani be, kika gudu kika har Zan dangwama Cikin karki sake tunanin barin muwaddat tana kwakwameta aiikinta• na da kaddara imani h awaye Cicciko a idanuta abi Sun bashi Zaka masu ka tabbatar da suna Cikin taghin hankali barin muwaddat daya Gama karanta dake dentin duk halin da zuciya ke ciki fuska Ce ke kaf'n baki ya yanayinta gabacfaya jikin ummi ya game yin tSanyi ta tuba mata tams-a Ce dina •kingani ko daga ni sai ke abi (nuke cikin hankali tSaWOn daren nan gagara ratsuna bumnaya ke can Yana sharar baccinsa shi nmi ba kunya b.a, mai kika biye •kiyi hkr wallahi nayi dan Allah ki yafe min Zan jin radadin abinda nake ji Zuciyata, ta Shiga Shata bayanta tana kuka ko ba muwaddat na da tsananifi biyayya tana dadin yadda take Santa Ahankali mikar daita tsare ta rabata aiikinta cfakina karki kZra barinmu duk runtse rnuna tare kinji gudawa abar a sanadin yin Ciki bash. da arnfani Yana da dayawa ga idan kin gudu kika san hannun Zaki facia? har guka Shiga dZkin dukkaninsu kuka ummi ta kwantar daita akan gadon ta kwanta kinji nima na hakura kema ki dawwalawa Allah lamarinki , taje ta kulle kofar har da zare key dan jin tsoron karta gudu tazo tashiga bayi.. muwaddat ta runtse idanunta "batasan wani irin so ummi take mata ba ? shi kuwa abi zubewa yayi acikin d'aya daga cikin kujerun dake parlour'n ya goge hawayen dake k'ok'arin fitowa daga cikin kwarnin idanunsa "gabad'aya a halin yanzu baya ganin laifin yaran yafi d'aura laifin komai akansu bangaren bunayya shima ranar haka ya kwana Yana tunanin , wani sain Yaja tsaki wani lokacin yayi murmushin jin dadi.. wayarsa dake gefensa ne tayi ringing alamun ana kiransa duba Wayar yayi ganin wacce ke kiran ne yasa shi jan dogon tsaki kafin daga baya ya d'auka, yayi shiru Yana jiran yaji abinda zata fad'a, yasamu damar cin ubanta da tushe a bangaren faiza kuwa dadi ne yakamata saboda ta yita kiran layinsa na London bai Shiga daga baya tayi tunanin ta kira na Nigeria taso tasoma jin sanyayyiyar muryarsa mai sata jin kasala a sansar jikinta, amnan yaki yin mgn sai hucin numfashinsa, a sanyaye tace "'hello Yaya auwal.." "lafiya kika kirani ya fad'i hkn a takaice? duk da yadda ya amsa mata hakan bai sa taji zata fasa maganar datayi niwa ba . tace 'Yaya auwal daman nace... "kika ce uban me da uwar me ? "faiza! faiza!! faiza!!! sau nawa na kiraki? muryarta a sanyaye tace "sau uku •na rantse da girman allah na haramta gareki koda kuwa banyi nasarar samun muwaddat ba, bariji gabad'aya a tsarina bana son mace irinki mara aji da kamun kai ,duk da kasancewarki yarinya amman wallahi gara na auri irin muwaddat sau hudu saboda bana sonki, kuma bazan taba sonki ba har abada ,saboda xuciyarta yayarki take so koda kuwa tafi yadda take shekaru Yana gama fad'ar haka ya katse kiran ya koma ya kwanta Yana fidda numfashi sama sama.. Mmn sudais ce MUWADDAT ~NA *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ _AUNTY SALAMATU AYYUBA_ _(UMMIN KADUNA )_ bismillahirrahmanirrahim page 40 ....shiru ne ya ratsa gidan tun sanda su ummi suka baro parlour'n , abi dake zaune akan kujera mai zaman mutun d'aya ya rafka uban tagumi, gabad'aya abun duniya ya dameshi ,ya kasa tashi daga zaunen da yake, mafuta kawai yake nema da tunanin wanda zai tautauna matsalarsa dashi akan bakon lamarin daya samesu . a qalla ya kusan minti talatin zaune agurin yana tunanin mafuta , mutun na farko da zuciyarsa ta bashi umarnin ya nema ,shine d'an'uwansa umar ,batare da 'bata lokaci ba, abi ya mike cikin hanzari ya nufi d'akinsa yasoma neman layinsa . Bugu d'aya biyu uncle umar ya d'auki wayar bakinsa d'auke da sallama byn sun gaisa ne abi ya shiga sanar masa abinda dake faruwa a gidansa , take zuciyar uncle umar ta tsaya na wunci gadi , a tsaye uncle umar yake amman bai san sanda ya Kai zaune rike da wayar ba tsabar firgici da tashin hankali , har gumi na karyo masa tsabar rud'anin da buguwar zuciyar d'aya tsinci kansa alokaci ,d'aya byn d'aya yake sauraron bayanan abi "abinda ya gudar musu kenan tun farko shiyasa ya d'auke bunayya zuwa wata uwa duniya da sunan karatu ,amnan duk da haka basu tsira ba ... "Wannan wace irin maseefar rayuwa ce haka ? "Wasu irin yara ne haka da nacin tsiya ? ya yiwa kansa tambayar yana mai dafe gaban gashinsa, Yana sake tuno abubuwan da idanunsa suka ci karo dashi a wancan lokacin ,abi bai boye masa komai ba tun daga farko har kan maganar zuwan iyayen al'ameen da ummi ta tilastashi akan lallai sai ya amshi kayan aurensu, "ni duk cikin lamarin babu abinda ke bani mamaki kmr yadda alhji Mahmud yayi min bakan da zance kmr bai san abinda ake ciki ba ,kwata kwata yayi min shiru da batun auren al'ameen da muwaddat , haka zalika nasan dole yana da masaniyya akan zuwan iyayen yaron amman har yanzu bai ce min komai ba .... "umar bazan boye maka ba naji haushin wannan shirun da alhj muhmud yayi min ,saboda nasan babu yadda za'ayi ace bai san komai dake tafiya ba ,duk nayi iya tunanina ban gano ta inda ake irin haka ba, ta yaya ma za'a ce... "Kayi hakuri yaya ,uncle umar ya katse shi ta hanyar fad'ar hk "kayi mashi uziri , ka daina ganin laifinsa, shima wata killa yana jin yadda kake ji din ne azuciyarsa ,shiyasa bai maka maganar ba ,tunda Kai ma akaidance yakamata ka nemeshi akan batun zuwan iyayen yaron

Chapter 34 of 40