Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 4
ba a garin nan. Koda bayan an daura auren dole ne a nemo ta, dole ne a gano inda ta shiga." . "Haba Alhaji, to amma saboda Allah yaya za a ce an daura mana aure ba amarya? Kai ma ka san cewa wannan ba karamin tonon asiri ba ne a gare ni. Ya kamata dai a san abinda ake ciki kawai." . Siririn mutumin ya share zufa de ke kan dokin wuyansa. "Wallah ni kaina ban san me yake damun wannan yarinyar ba. To ka san bai yiwuwa ka haifi yaro sannan kuma ka haifi halinsa, wannan hali nata ni ban san inda ta samo shi ba, domin kuwa daga ni har uwarta duk mutanen kirki ne wallahi." . Gali ya harari mutumin a fakaice, a zuciyarsa ya ce "Kana matsayin mutumin kirki amma ka damfare ni kusan miliyan guda, don kawai za ka ba ni 'yarka?" To amma dai a zahiri cewa ya yi da shi, "Ni dai ka ji bayanina Alhaji, in dai har ba a gano mini amaryata ba, to ina jin mu duka sai kawai mu yi hakuri da maganar. Domin kuwa jiya aka daura auren abokina, muna so ne mu hada bukukuwanmu rana daya da aurenmu, amma kuma ni a ce wai ba a ga tawa amaryar ba. Wannan ai tonon silili ne ake nema kawai a yi mini." . dan motsattsen mutumin ya yi ajiyar zuciya, jikinshi ya soma kyarma domin kuwa a yadda ya lura da kwayoyin idanun saurayin ya san cewar abubuwan da yake fada har cikin zuciyarsa abinda yake nufi kenan. . "To ni yanzu don Allah me kake son in yi maka? Ai'sha dai ni na haife ta, kuma ta kwashe kayanta ta gudu ta bar gidan nan, me kake so yanzun in yi maka, tunda ka ce ba ka yarda ba?" . Saurayin ya sake hade fuska sannan ya ce da shi. "Ai ba wani abu ba ne mai wahala, ina ganin Alhaji, in dai ban takura maka ba, ai ina gani ban yi laifi ba idan na ce ka shiga cikin gida ka tattaro min kudadena da na kashe tun farkon soyayyata da 'yarka A'isha. Domin kuwa idan har za ka iya tunawa ka amshi manyan kudade a wajena, kuma kai ma ka san dai ai ba kyauta na ba ka su ba, domin kuwa inda a ce ni talaka ne ba ni da kumbar susa, na tabbata daidai da rana daya ba za ka taba barina in zo kofar gidanka har in furta ina neman 'yarka ba . Don haka ni ma na rika ba ka kudaden da kake bukata, na san dai ba ka mance ba da su ba." Saurayin ya dan yi murmushin takaici sannan ya ci gaba da shaidawa ramammen tsohon . "Tun fara neman auren A'isha na fara lissafin abubuwan da nake kashewa a dalilinta, kai hatta man da nake zubawa a motata in zo wurinta, da kuma kudin da nake baiwa yara su kira min ita, duk ina rubutawa. A halin yanzu lissafi ya yi kauri, domin kuwa kullum sai na ciro doguwar takardata ta lissafi, na yi bitar kudaden da ke cikin akawun dina da wurinka . Don haka na ba ka awowi goma ka tattaro min kudadena. In ba haka ba, ka ji na rantse maka da Allah, sai na dankara ma ka harsashin bindiga, tsohon banza makwadaici kawai macuci!" . Gali ya bude kofar motar a fusace ya shiga ya tashe ta. Ya juyo ya dubi motsattsen mutumin, wanda a halin yanzu ko'ina a jikinsa kyarma yake yi hatta fuskarsa da ke dakon faskeken tabaron ita ma kyarma take yi, duk da uban kayan da aka jibga mata, . "Kada ka damu Baba, na ga ka rude, ai kudin ba wasu masu yawa ba ne, miliyan daya da dubu dari bakwai da hamsin kawai, sai naira dari uku da talatin da biyar." Ya fizgi motar ya fice a guje daga kofar gidan . Motsattsen mutumin ya bi kurar motar da kallo. A daidai lokacin ne faskeken tabaron ya kubuce daga 'yar mitsitsiyar fuskar tasa, ya fadi kasa. Tuni har ya fara tsammanin hawan jini. . ___________ Shuraih 99% Iyaye ayi hattara da amsar kudi ko wani abu a hannun siriki kafin Aure . Duniya ta lalace da cin hanci wai har MALAMAN ADDINI suna RASHAWA ._____________ AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 11 . ____________ Tsawon mintuna biyar mafadaciyar matar na ta faman yiwa mijin nata banbami. Yana tsaye kawai yana duban ta, sai zufa ke ta faman kwararo masa, tana wanke masa fuska, kamar ana yi masa sakiya . Ya rasa da me zai ji tsakanin masifar da kuma gargadin da surukinsa ya zo ya yi masa. Ya san cewar wannan saurayin dan bindiga-dadi ba hankali ya cika ba, kamar yadda da ma ya dade yana jin ana cewa ba duk soja ne ke da cikakken hankali ba . Hakika yana iya aikata duk abubuwan da ya fada, ga shi kuma yanzu Juma ta tuso shi a gaba da tata masifar. . Duk ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. "Kawai aikin banza Malam, ka jawo min 'yata kwalli kwal da nake alfahari da ita a duniya ta tattara kayanta ta gudu, da ma haka kake so sai ka zuba ruwa a kasa ka sha, burinka ya cika." . Alhaji Dage ya yi shiru, bai ce da ita kala ba, domin kuwa ya san cewa yanzu ba lokacin tankawarsa ba ce, don kuwa har ga Allah matar tasa ta tunzura. Ya san cewa idan ya biye mata, tana iya kama shi da kokawa, kuma ba ya kokwanto ya san cewa shi za ta kayar . Shi ya sa ya rufawa kansa asiri ya rabu da ita, in ta yi ta gaji dai ai dole ne ta bari. Juma ta sake cewa da motsattsen mutumin cikin kwarmato kamar za ta hadiye shi. . "Wai me kake nufi ne Alhaji, ba ka ce komai ba. Ko kuwa kana nufin shi kenan, kai ka cinyewa mutane kudi, ni kuma ka bar ni da asarar 'yata. To ai sai ka sake tunani, don kuwa ba kyale ka zan yi ba, duk inda 'yata ta shiga sai ka je ka kwakulo min ita, in dai kana son zaman lafiya a duniyar nan, to wallahi ka nemo min A'isha domin kuwa duk kai ka jawo mana wannan masifar." . Ramammen mutumin ya yi ajiyar zuciya, a karo na farko ya ga cewar ya kamata dai ya dan ce wani abu. Don kada ta ga ya ki tabuka komai, ta sake haye masa yadda ta ga dama. . "Ba na son rashin albarka, Juma." Ya ce da ita, "Ni kike yi wa wannan tsagerancin ko kuwa kin fi ni son 'yar tawa ce, da kike fada min wadannan maganganun? Ko kuwa ni ne zance ta gudu ta bar gidan? Wannan tsinanniyar yarinya ina amafaninta, duk ba halinki ta kwaso ba? Ke din a da can me ye ba ki yi ba? Ba don yanzu an mance, ba a tone- tone, shi ne har kin samu bakin magana. Kada in sake jin muryarki a kan maganar nan Juma." . Ya zazzaro mata idanunsa da ke cikin fasasshen tabarau, a tsammaninsa watakila ta dan ji tsoro ta lafa. To amma kuma cikin rashin sa'a sai ya ga ta yi shewa, sannan ta yi tafi ji kake fas, ta ce da shi. . "Lallai yau da tone-tone a gidan nan. Au kai nan har gori zaka yi min? Ka mance da abubuwan tsiyar da ka kuntuka a baya? Haka fa kawai nake zaman hakuri da kai. . Shi ne yanzu har ka samu bakin da za ka yi tonon silili. To ai sai mu fara a ji ni da kai wa ya fi wani mugun tabo, ba tsoron ka nake ji ba Alhaji, mu yiyar tonon asiri." . Alhaji Dage yayi saurin tsayar da ita, da ya ga ta sake hayewa. "Duk wannan ba ta taso ba, ni dai gaya miki na yi dama don maganar da ya dace ki rika fada, ai ba cewa na yi za mu yi wani tone- tone ba, don kuwa mu dai ba yara ba ne, ya isa a ce mun mallaki hankalinmu a halin yanzu." . Juma ta yi guda sannan ta ce da shi. "Ashe ka ji tsoro mai gida. Ai na so mu jarraba tonon silili da kai wallahi da ka ga dan biki da cika yau a gidan nan. In ana fadin abin kunya kai har ma ka sa baki a gidan nan. In ba abin kunya ba mene ne amfanin karbarwa mutane dukiya don za su auri yarka? Haka fa ka yi ta yi wa ragowar yayan danginka da ka rika a gidan nan. Ka aurar da yan mata sama da biyar duk a bisa zalunci. Yanzu suna can dakunan mazajensu suna shan wahala ana yi musu gori da wulakanci, tunda dai ka saida musu da mutunci. To ni ba mai yi wa yata A'isha wannan mulkin mallakar, mu zuba ni da kai a gidan nan tun da kai ba ka gudun abin kunya." . Mutumin ya yi ajiyar zuciya, ba shi da ta cewa domin kuwa duk abin da matar ta fada gaskiya ne duk ya aikata. Yana jin ta ta ci gaba da cewa da shi. . "Duk wanda ya sa ranshi a kwadayin abin duniya dole ne ya ga wulakanci mai gida, amma ina amfanin a ce a matsayinka na babban mutum wanda zai yiwa wani nasiha a ce kana rigima kai da surukanka kana amsar musu dukiya? Yanzu ga abin da ka jawo mana, wannan mutunci ne?" . Ramammen mutumin ya girgiza kan shi kamar uwa na wa danta fada "To ai laifin yarinyar ne ni wannan tsinaniyar yarinyar wallahi ta cuce ni.." . "Ka da ka tsinewa yata a banza domin kuwa ba ta da laifi, kai ka jawo mana wannan rigimar muna zaman zamanmu lafiya. Ka san cewar A'isha ba ta kaunar yaron nan ka nace a kan maganar nan don ka gan shi da kumbar susa, ga shi yanzu kana jin tsoron fita waje ka da surukinka ya harbe ka . Ina na taba jin irin wannan abin tsiya ma a duniya, ni Juma." Alhaji Dage cikin nadama ya ce. . "Kin ga laifina ne a banza Juma, amma a matsayina na magidanci saboda Allah ba ni da yanci zabarwa yata mijin da na ga ya fi dacewa da ita? Wani zamani dai Allah ya kawo mu inda yara ke kangarewa su fi karfin iyayensu. . Mu a zamaninmu wane yaro ya isa ya ce shi zai yiwa kansa zabi sai wanda ya ke so, mu kuma mutane sai mu bar abu ya lalace da kanmu, mu ce ai zamani ne, da gangan ake kyale yara suna wannan iya shegen da fitsarar ana kallon su." . "Ba haka ba ne maigida" Juma ta ce da shi "Ko ka ki ko ka so al'amura suna canzawa, kuma zamani ya kan zo da abubuwa iri-iri dole kuma mutum ya bi abinda zamani ya zo da shi matsawar bai sabawa shari'a ba. Ai ba haramun ba ne don yaro ya zabi wanda ya ce yana so ya aura. Kuma da ka ce a naka zamanin ba haka ake yi ba, kai zamaninka ka sani, ba ka damu da zamanin yayanka ba. A zamanin naka ai bante ake daurawa ba sutura ba, me ya sa ba za ka cigaba da daura bante a wannan zamanin ba, tun da ka ce ba ka amince da canjin zamani ba, sai ka koma tafiya tsirara da bante, don kuwa shi ake daurawa zamaninka na baya." . "Yanzu dai mu bar wannan maganar" ya ce da ita abin da ya faru dai ya riga ya faru, dole ne in sanar da jami'an tsaro su shiga cikin maganar don a kawo karshen wannan rigima, kafin abin ya kai mu ga kashe-kashe don na ga alamar abin da wannan mahaukacin sojan ke nufi kenan, in ya so daga baya sai in sayar da gidana na sabuwar unguwa in biya shi kudadensa, ita kuma A'isha sai a nemo ta a bata wanda take so." . Juma ta dan saki ranta ta ce da shi. "To yanzu da ka yi haka kai kanka ba ka fi jin dadi a ranka ba? Ai wannan shi ne datattako maigida, yanzu to ka nemi a zauna lafiya." Kamar aikin budar idanu cikin yan tsararun mintuna mafadanta ma'auratan biyu suka dawo cikin raha kamar ba su ba. Shekaru sama da talatin kenan, suna wannan halayya, an ce a cikin minti daya sai su hautsine da fada, kafin kiftawa da bismillah sai kuma a ga sun dawo suna dariya. . To sai dai kuma a wannan karon da sun san cewar akwai wani shu'umin saurayin da ya cika bindigarsa da harsashi, sannan kuma ya saya musu likkafani jana'iza da ba su sake yin wata raha ko dariya ba. _____________ A'isha ta dubi angonta Nazifi cikin farin ciki sannan ta ce da shi "Nazifi 'darling' yau dai Allah ya cika mana burinmu, mun zama mata da miji. Duk duniya babu mai raba mu ni da kai masoyina." . Nazifi ya dube ta shi ma duba na so da kauna yana kwance a kan doguwar kujerun da ke cikin tsararren dakin da suke ciki, ya ce. "Ai ni A'isha ba ma abinda zan iya cewa sai dai kawai in godewa Allah da kuma wannan abokin nawa domin kuwa wallahi ni dai ya gama yanto ni, ya yi min komai na alheri." A'isha da ke zaune a kusa da shi ta ce cikin mamaki "Wai da gaske bayan ya ba ka rabin miliyan har kuma wannan gidan duk shi ya ba ka, Nazifi?" . "To ga zahiri ma kin gani A'isha tun da har ga shi kuma na shigo da ke kin tare a ciki, ko kuwa ke a da kin ga na yi miki kama da wanda zai iya mallakar wannan tsantsareren gidan?" . A'isha ta yi dariya farin ciki. "Mun gode masa wallahi. Don Allah sai yaushe zai zo don in gan shi mu yi masa godiya ta musamman akan wannan abin alheri da ya yi mana?" . Nazifi yace da ita "An jima nan kadan za ki ji ya zo ya kwankwasa mana kofa domin kuwa shi ma yau ake daura aurensa da wata yarinya a nan garin kuma mun yi da shi zai biyo min ya dauke ni mu wuce wurin daurin aure tare." . A'isha ta sake lumshe idanu cikin murna ta ce. "Mun gode wallahi, Allah ya bar zumunci tsakanin mu da shi. Yaya sunan tasa amaryar Nazifi?" . Nazifi yayi farat ya ce. "Ai abin namu ni da shi ya zo daya domin kuwa saboda tsabar shakuwa da muka yi da shi, har ankon sunan amare muka yi, cikin sa'a ita matar tasa sunanta A'isha." . Suka yi dariya, A'isha ta ce. "Lallai abin yayi min dadi Nazifi, ka ce kun samar min kawa kenan ni ma" Suka ci gaba da dariya abin gwanin ban sha'awa. Suka fito da naman kaza suka tasa a gaba, dama tun tarewa su gidan a daren jiya Nazifi ya sawo dakwalen kaji soyayyu har guda uku. Tun a jiya suka cikye biyu saura ragowar daya wacce suka baje a halin yanzu. . Ba abin da ya dame su, kudine dai sun samu abin kamar daga sama, dole ne su godewa wannan abokinsu mai farar aniya. A daidai wannan lokaci ne Gali ya karaso kofar gidan fuskarsa a murtuke kamar wanda aka yiwa albishir da mutuwa. Lokaci-lokaci yakan kai hannusa cikin aljihu ya shafi bindigarsa. Kamar yadda ya tsara a ransa, . daga nan idan ya gama gaisawa da ango da amarya, to farauta zai wuce abinsa. Ba farautar namun daji zai fita ba, farautar amaryarsa A'isha zai fita da kuma saurayin da aka ce ya sace masa ita sun gudu. Kuma ya sha alwashin muddin ya yi ido biyu da A'isha da wannan saurayi da ya sace ta, to ba wani bata lokaci duk aikawa da su zai yi barzahu . Gali ya yi murmushin mugunta sannan ya sake mika hannu ya shafo bindigarsa wacce ke boye a cikin aljihu. Ya daga hannu ya kwankwasa kofar gidan a sanyaye. A'isha da Nazifi da ke cikin gidan suna baiwa juna naman kaza a baki, suka dubi juna cikin farin ciki a dai dai lokacin da suka jiyo sautin bugun kofar "Kin ji dan halak!" . Nazifi ya ce "Shi ne yake kwankwasa kofa, Gali ne abokina. Je maza ki bude masa kofa ki rako shi, A'isha." . Amayar ta ce da angonta a sanyaye. "Wata kila ma wasu miliyoyin kudin ya sake kawo mana 'darling'." Nazifi ya ce "Babu mamaki, A'isha ai na fada miki abokin nan nawa yana bala'in sona, ke dai je ki bude masa kofa, ki tarbo shi ya shigo." . ___________ YAU KAM RIGIMA ZATaYI KISA . Ya kuke ganin zata kaya Ku biyoni Shuraih 99% a littafin AJALI Nazifi ya ce "Babu mamaki, A'isha ai na fada miki abokin nan nawa yana bala'in sona, ke dai je ki bude masa kofa, ki tarbo shi ya shigo." . A'isha ta mike cikin farin cikin tana rangwada ta nufi kofar gidan. Hakika sun yi dace ita da angonta Nazifi, Allah ya hada ta da mai sonta kuma ita ma take kaunarsa. Ya raba ta da wannan wahalallen da a da ya nace mata, A'isha ta ce a zuciyarta tana murmushin farin ciki. . Ta kama kofar gidan da hannayenta biyu, ba tare da wani fargaba ko zullumi ba TA BUDE MASA kOFAR! ****====****** Dankareren kayataccen gidan ne da ya kai matuka wajen tsaruwa. Jama'a da dama kan dakata don yiwa kyakkyawan gidan kallon tsaf! saboda ginuwarsa. Mutane da dama kan tuna da kayataccen gidan saurauniyar ingila dake "BUCKINGHAM PALACE" a duk lokacin da suka dubi tsararren gidan. Wani dadin abin da ke matukar jan hankalin jama'a ga hadadden gidan shi ne daddadan kamshin furanni dake gewaye da gidan. dan tsamurmurin dattijon maigadin da ke zaune akan bencin a gefen katotuwar kullalliyar kofar gidan mai fasalin fuka-fukan dawisu, ya dan yamutsa fuska gami da gyara rikon jaridar da ke hannusa tamkar mai tsammanin shekowar wani a guje ya wafce ta, cikin zakuwa ya soma bude shafukan cikin ta, a shafi na biyar ya yi ido hudu da labarin da yayi matukar jan hankalinsa mai taken KADDARA KO FANSA! . A hanzarce ya muskuta gami da gyara zama, kana ya sake kafa kwala- kwalan idanunsa akan hotunan gawarwakin wasu mutane biyu mace da namiji da ke gefen rubutun, cikin zakuwa ya soma karantawa. . A safiyar jiya ne yan sanda suka tsinci gawar wani saurayi Nazifi tare da masoyiyarsa A'isha. . An tsinci gawarwakin ne yashe a cikin wani sabon gida bayan an harbe su da bindiga har lahira. Tuni jami'an tsaro sun cafke wanda ake zargi da aiwatar da kisan gillar wanda ya kasance wani matashin soja wanda shima yake kaunar budurwar, wanda kuma har an sa ranar bikin su da ita amma kuma ita ba ta kaunarsa. . Mahaifin yarinyar mai suna Alhaji Dage ya yi nadamar afkuwar mummunan al'amarin sannan kuma ya tabbatarwa da wakilinmu cewar dukkan wannan al'amari da ya afku laifinsa ne sakamakon tilastawa diyar tasa da ya yi a kan sai ta auri wanda ita ba shi take so ba. A karshe ya yi kira ga iyaye a kan su dinga mayar da hankali a kan dukkan abin da `ya`yansu ke bukata matsawar dai hakan bai sabawa addini ba. . Sannan kuma ya yi doguwar addu'a gami da bayyana matukar alhininsa ga mamatan . Don jin yadda zata kaya mu hadu a cigaban littafin nan mai suna A’ISHA don jin karshen sarkakiyar sarkakakken labarin. Na gode, naku Shafi’u Dauda Giwa. ......................... Anan kuma ayau muka kawo karashen littafin AJALI amma da yardar Allah daga nan zuwa wani lokaci zan saka maku cigabansa . AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing Shuraih Usman 99% .... JINJINA GA Shafukan Shuraih 99% Zauran labarai Home of Littatafan yaki and Hausa novels . Ina mika sakon gaisuwata ga ahalin kungiyar TSANGAYAR MARUBUTA TASKAR GIDAN LITTAFI ..... Nine naku a kullum da ko yaushe Shuraih Usman 99% Ku tareni a littafin A'ISHA AJALI Marubucin littafin Shafi'u Dauda Giwa Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4