Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
yawan lokuta samarin unguwar suna bakin ciki da wannan al'ada tasa, ta zama a waje, domin yana matukar takura masu wajen ganawa da 'yar kyakkyawar yarinya A'isha. . Bayan A'isha ta gama waigen kowanne bangare na harabar, sai ta hango Nazifi a can rakabe a jikin wata bishiyar dorawar turawa da ke kusa da babbar kofar shigowa cikin gidan. Yana tsaye a jikin bishiyar, ya jingine akwalar kekensa a gefe guda. Hannayensa a harde a kan kirjinsa, ya sako wani farin yadi boyel, wanda ya dan fara zazzagawa . A'isha ta isa gare shi tana murmushi. Tun daga nesa da ya hango ta shi ma yake murmushi, har ta kawo inda yake. "Wallahi har na cire tsammanin zuwanka, Nazifi." . Soyayya da dadi jama'a Saide daga karshe....... Its shuraih 99% AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 5 . "Wallahi har na cire tsammanin zuwanka, Nazifi." Ya ci gaba da murmushi, ya ce da ita. "Haba A'isha, ai ke ma kin san cewar tunda dai har na daukar maki alkawarin cewar zan zo, ai ba zan karya ba." . Suka sake yi wa juna wadansu sabbin murmushi. "Gaskiya na ji dadi wallahi Nazifi, ka san yadda soyayyar ta koma yanzu. Wani lokacin sai ka ga an kulla alkawura sama da dari, amma da wahala ka ga an cika ko da goma ne a cikin darin. Kai dai ka san cewar da a ce yadda ake kulla alkawarin soyayya a duniyar nan, haka ake cikawa, to da yanzu babu sauran wani mutum wanda ba shi da masoyinsa." . Nazifi ya yi dariya. "Duk da haka dai A'isha, ai dole ne a samu nagari, kin san ba zai yiwu a ce duk an zama daya ba, duk da lalacewar da soyayya ta yi za a samu mutane nagari da ke cika alkawarinsu." "To za ki fara ke ma ko...?" Ta yi dariya. "Ba haka ba ne, wannan ai gaskiya ce Nazifi, domin kuwa ba wani zolaya don ka fadi halayen masoyinka nagari." . Suka sake tuntsirewa da dariya a lokaci guda. Nazifi ya fara cewa bayan sun gama dariyar. "A'isha akwai abun da ke tattare da zuciyata, wanda duk na kosa da ma in zo in amayar maki da shi. Wallahi A'isha jiya ban yi wani barcin kirki ba, domin kuwa ina komawa gida, tunaninki ya dabaibaye mini zuciya, sannan kuma ko da na samu damar yin barcin, mafarkinki ne ya buwayi kyakkyawan barcin nawa. Don haka nake so idan ba za ki damu ba, ina son mu yi maganar aure in dai har da gaske ne kina so na." . A'isha ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce da Nazifi, "Na ji duk bayaninka Nazifi kuma na matukar farin ciki, to amma ina son ka yarda har zuciyarka. Nazifi wallahi ni ma duk duniyar nan babu wanda nake so sai kai. To amma da akwai wata 'yar matsala guda daya da ke tattare da ni. Ina son idan na fada maka kada ka karaya, domin kuwa wannan matsala ba za ta hana mu gudanar da soyayyarmu ba. Ta dan saurara sannan ta ce da shi. . "Nazifi saura kwana takwas kenan a daura aurena." Saurayin ya rike numfashinsa cikin kaduwa, sannan ya dafe kirjinsa, "Aurenki!! A'isha...ban fahimce ki ba." . Ta girgiza kanta "kwarai kuwa aurena Nazifi. To amma ina son ka sha kuruminka, domin kuwa ni da ma ba na son saurayin da za a daura mana aure da shi, kawai mahaifina ne ya takura min a kan al'amarin. To amma a halin yanzu, tunda har Allah ya hada soyayyarmu da kai, wannan zancen aure babu shi, ya lalace, in Allah ya so kai ne mijina Nazifi." . Nazifi ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce da ita. "To amma kuma iyayenki kuma fa A'isha, kina jin za su amince?" "Sun riga sun san komai Nazifi, domin kuwa na fadawa mahaifiyata gaskiyar abinda ke zuciyata, to amma ban samu goyon baya ba. Domin kuwa a dalilin na ce ina kaunar ka Nazifi sai da ta lakada min dukan tsaiya, da kyar mahaifina ya yi mata magana ta rabu da ni." . Suka kurawa juna idanu cikin jimami. Nazifi ya ce "To amma kuma A'isha kina jin al'amarin nan zai yiwu? Tun yanzun fa kenan har kin fara fuskantar matsaloli, to ina kuma a ce tafiya ta yi nisa a tsakanina da ke?" "Me zai hana al'amarin yiwuwa Nazifi?" A'isha ta ce da shi. . "Ni dai na daukar maka alkawari, duk rigimar da za a yi ba zan amince a daura mini aure da wannan wahalallen ba, don haka na riga na gama tunanin komai a halin yanzu, kai kawai nake jira, don in ji ta bakinka. In kana jin za ka iya jurewa, kamar yadda ni ma zan jure, komai wahala mu rike juna." . Nazifi ya sake yin doguwar ajiyar zuciya, sannna ya ce da ita, "Kada ki damu A'isha, na daukar maki alkawari, komai wahala ni ma ina nan tare da ke, sai dai mutuwa za raba mu." . A daidai wannan lokacin ne da suke ta wannan doguwar hirar tasu ta masoya, kamar an jeho shi, sai Alhaji Dage ya fito daga cikin gida. Tun dazu yake zaman jira, yana tsammanin jin sautin dankareriyar mota ta yi fakin a kofar gidan, domin kuwa shi har yanzu tsammani yake yi, sabon saurayin da A'isha ta ce ta sake, wani hamshakin attajiri ne wanda ya rude ta da zunzurutun kudi. Fitowarsa ke da wuya, ya kai ganinsa inda A'isha ke tsaye tare da saurayin a gindin bishiyar. Alhaji Dage ya yi raunanannen murmushi da ya hango wanda ke tare da ita, domin kuwa ya dauka cewar masinjan masoyin 'yar tasa ne, ya zo fadawa 'yarsa A'isha cewar Alhajin ba zai samu zuwa ba. . Alhaji Dage ya nufi inda suke a tsaye. Ya hango tsohuwar akwalar keken saurayin a jingine da bishiyar, kamar dokin kara, nan da nan sai ya ji tausayin saurayin ya kama shi, domin kuwa yana matukar takaicin yadda attajirai da manyan ma'aikata ba sa kulawa da masinjojinsu, haka dai ya iske su suna cikin hirar . Nazifi ya rage tsawo ya gaishe da Alhaji Dage. Ya amsa cikin fara'a-fara'a akaici-takaici, kana ya ce da saurayin. "Allah sarki! Kai ya turo kenan, bai samu zuwa ba. In ka je ka ce da shi na yi zaman jiransa, domin ina son mu yi wata 'yar ganawa da shi a kan lamarin 'yata A'isha da ya ce yana so" . dan saurayin da 'yar budurwar suka kalli juna cikin tsananin mamaki. Ba su san me siririn mutumin yake nufi ba, to amma shi bai damu ba, sai ma ya ci gaba da zancensa kai- tsaye. "Idan ka gama fada mata sakon da ya aiko ka, don Allah ka yi saurin janye akwalar keken ka tafi malam, domin ina jin tsoron kada ka tsorata mini agwagi da dawisu da wannan tsohon keken mai shegen rakin tsiya." A'isha ta dubi mahaifinta cikin damuwa, ta ce da shi cike da kaduwa. . "Baba shi ne, ba aiko shi aka yi ba." "Ban fahimta ba, shi ne wa?" Ya zazzaro kwala-kwalan idanunsa da ke boye a cikin kwafcecen-tabaron. . A'isha ta ce da shi cikin ladabi. "Baba shi ne ai saurayin da nake so dama, shi ne masoyin nawa." Tuni jikinta ya soma kyarmar kaduwa. . Alhaji Dage ya kai hannu cikin razana, ya ciccibo katon tabaronsa kaya guda, ya rike a hannusa, ya kalli saurayin sama da kasa sannan ya ce a sanyaye. . "Lallai A'isha tubarkalla na ga saurayin, ya sunanka malam?" Nazifi ya sunkuyar da kansa kasa, domin kuwa ya tabbatar akwai matsala babba da ke shirin faruwa. To amma dai duk da haka, sai ya kokarta ya bude baki ya baiwa mutumin amsa. "Sunana Nazifi" Alhaji Dage ya dubi A'isha ya daka mata tsawa. "Shige cikin gida kafin in zo in same ki `yar banzar yarinya kawai" . A'isha ta juya cikin tsananin karaya, ta nufi cikin gidan. lokaci-lokaci ta kan waigo don ganin abin da zai wakana ga masoyinta. Nan da nan ta soma addu'ar Allah ya sa dai kada mafadacin baban nata ya buge shi, domin kuwa ta san shi wajen saurin hannu. . Wannan na daga cikin abin da ya sa shi yin kaurin suna a unguwar, domin kuwa ya sha marin samarin da ke zuwa wurin `ya`yansa, musamman ma idan a kasa mutum ya zo ba a mota ba . Shigewar A'isha ke da wuya, sai ya tattara hankalinsa gaba daya ya ce da dan saurayi Nazifi. "Ina son in yi maka gargadi na farko, kuma na karshe, wannan yarinya `yata ce, ni na haife ta, kuma saura kwana takwas kenan a daura aurenta, ka rufawa kanka asiri ka fita daga cikin harkokinta, domin kuwa A'isha a halin yanzu ko kai aka sayar ba za ka biya abinda za kai aurenta ba. Domin kuwa na san dai ba za ka kai naira miliyan guda ba, don haka kar ka jawo wa kanka bala'i dan saurayi." . Nazifi ya girgiza kai cikin gamsuwa bayan da ya ji mafadacin mutumin ya kai aya. Ya jawo akwalar kekensa cikin hanzari domin kuwa in ma tsautsayi ya ratsa ya ga alamar cewar jiki zai yi tsami, to ba zai bar akwalar keken a wurin ba, wacce ita kadai ya mallaka a duniya . Malam Nazifi abun tausayi Talakan masoyi ya hadu da ma kwadaicin siriki Its shuraih 99%AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 6 . Nazifi ya girgiza kai cikin gamsuwa bayan da ya ji mafadacin mutumin ya kai aya. Ya jawo akwalar kekensa cikin hanzari domin kuwa in ma tsautsayi ya ratsa ya ga alamar cewar jiki zai yi tsami, to ba zai bar akwalar keken a wurin ba, wacce ita kadai ya mallaka, a duniya. . Alhaji Dage ya sake cewa da shi a fusace,kafin ya tafi. "Ka rike a zuciyarka dan saurayi ba na magana biyu, haduwar mu da kai ta biyu babu dadin gani. Idan na sake ganin ko da inuwarka a nan gidan,kai ko sawunka na gani wallahi sai na aika polisteshan, an kulle min kai, shege beran masallaci." ________________________________ Wata dankareriyar mota mai tudun baya, ta garzayo a guje kamar kibiya, tana sheki a cikin hasken kwaleliyar ranar wacce ke ta faman gasa naman bil'adam. Jama'ar da ke zazzaune a bakin titin, suka bi motar da kallo, domin kuwa lokaci-lokaci sukan ga motar ta shigo cikin unguwar tasu, to amma kuma har yanzu babu wanda ya san takamaiman abin da ke kawo motar a kai- akai ba . Kamar kullum sai motar ta rage gudu sannan ta fara sigina, cikin abin da bai fi dakika biyar ba,har ta tsallako titi. . Saurayin da ke tuka motar ya daga musu hannu, wannan al'adarsa ce koda yaushe, da ma ya kan dago musu hannu in ya same su a zazzaune. Yawanci idan haka ta faru, su mutanen ba sa wani kula shi, ko a yanzun ma da ya dago hannu da kyar aka sami mutane uku da suka kula da shi, su ma kuma ba hannu suka daga masa ba, kai kawai suka gyada masa kamar kadangaru. . Me yiwuwa idan aka tona zuciyar mutanen unguwar watakila suna da gaskiya, domin kuwa tun ganin farko da suka yi wa saurayin ya shigo unguwarsu, duk da yake a cikin mota yake, ta gilashi suke hango shi, a matsayin suna kwararrun zauna gari-banza, sannan kuma masana akan ilimin sa-ido, sun fahimci cewar wannan saurayi duk inda ya fito ba mutumin kirki ba ne . Akwai wani mutum da ya taba cewa ma da ganin saurayin ya san cewar dan fashi da makami ne, shi yasa da zarar ya shigo unguwar suke hade masa fuska, kamar sun ga mutuwa. . Saurayin bai taba kula ta tasu ba, don kuwa ya san cewar wata rana ma ba za su sake ganinsa ba, neman aure ya jawo mishi shigowa wannan unguwar mai cike `yan sa-ido, dazarar an yi aure kuma ta kare . Saurayin ya yi murmushi da ya tuno cewa nan da kwanaki hudu za a daura auren sa da A'isha rabin ransa, Aisharsa da ya mace a kan kauna tsawon lokaci. . Ko da ya tsallaka titi sai ya shiga layin gidan su masoyiyarsa A'isha wacce yake ta faman ambatar sunanta sai kace mai bitar darasi. Ya ci gaba da murmushinsa sannan ya daki sintiyarin motar cikin farin ciki, . hakika komai yana da iyaka, ya ce a zuciyarsa. Ya dauki dogon lokaci yana nunawa A'isha soyayya, amma ta ki ta gane kullum sai dai kawai shi yake kidansa sannan kuma yake rawarsa, amma ita ba ma ta tasa ta ke ba. To amma dai yanzu ai wulakanci ya kare tunda dai ta kusa zama matarsa, ko da a ce ba ta kaunarsa, ai ya zame mata dole ne ta zauna da shi tunda dai ya saye iyayenta. . Saurayin ya ci gaba da murmushinsa na samun nasara, ya ce a zuciyarsa, "Hakika kudi suna da matukar amfani a rayuwa," domin ya san cewar da bai mallake su ba to da shi da A'isha kyakkyawa sai dai hange daga nesa. Da yawa daga cikin abokansa sun sha damun shi da surutai a kan wannan soyayya da ya ke yi wa A'isha domin kuwa ta sha ta kwabsa shi ko a gaban wanene ko da kuwa yana tare da abokansa ne . Akwai wani lokaci da wani abokinsa ya ce da shi. "Don Allah Gali ka rabu da yarinyar nan tun da dai ba ta kaunar ka, wai kai ina ma ka taba jin inda aka yi soyayyar dole ne? Ya kamata ka canza sheka haka nan, domin kuwa akwai `yan mata kyawawa a garin nan, ba A'isha ba ce kadai kyakkyawa" Gali ya yi murmushin ya ce da shi . "Abokina kada ka ga laifina don na likewa yarinyar nan, wani lokaci ni kaina nakan yi kokarin ganin cewar na cire son ta a zuciyata, don in huta wa rayuwata domin kuwa A'isha ta zame mini kamar maruru ko sartse a cikin zuciya, ba na minti daya a duniya ban yi tunaninta ba sannna kuma ba na iya daina son ta a zuciya ta." . Tun daga wannan rana mafi yawa daga cikin abokan Gali suka shafa masa lafiya, wadansu kuma suka ma bata da shi domin kuwa su a ganinsu ya ba da sojoji, ba haka aka san zuciyar soja ba. To amma kuma abin da ba su sani ba game da lamarin soyayya shi ne, ta kansa mutum ya makance ya dukufa akan son wani abu, wanda sauran jama'a ko da kudi aka hada su ba za su so wannan abu ba, . domin kuwa idan ba haka ba, babu abinda zai sa babban ba'askare a cikin sojoji, wanda ya shiga har kasashen turai, amma ya dishe da kaunar wata yarinya `yar cikin gida ba kirar waje ba, har kuma ta zo tana wulakanta shi, lallai abin dai kam akwai takaici. . Gali ya yi ajiyar zuciya da ya tuno walhalun da ya sha a baya na kaunar wannan yarinya A'isha, ya ce a bayyane cikin rada-rada. "Kin ba ni wahala A'isha amma ba komai na kusa ramawa" A daidai wannan lokaci ne ya karaso kofar gidan, ya yi fakin din dunkulalliyar motarsa mai tudun baya, ya fito yana sanye da dogayen kayan shudiyar shadda, dinkin ta- zarce, dogo ne kakkaura baki, yadda yake haka zuciyarsa take bakikkirin domin kuwa da ran mutum da na kiyashi duk daya suke a wurinsa. . Shekarunsa za su kai talatin da biyar koma fiye a duniya. Ya shiga zagayen gidan kai tsaye, ya tsaya a cikin harabar inda shuke- shuken alfarmar suke. Bai dade ba a wurin wata karamar yarinya ta shigo cikin gidan, ya tsayar da ita, ya ce da ita. . "Kice wa Ai'isha Gali yana jiran ta a waje" Ba a jima ba yarinyar ta fito ta ce da shi. "Ta ce tana zuwa" Ya zaro wazobiya sabuwa fil ya mikawa yarinyar. Ta amsa cikin doki ta fice a guje. . Gali ya yi ajiyar zuciya ya fara nazarin harabar gidan. dawisu da agwagin ruwa da suka fi komai ba shi sha'awa suna ta yawace- yawace, da kuma koke-koke abinsu. Ya yi mamakin yadda mahaifin A'isha rabin ransa ke matukar kulawa da wadannan halittu. Ba a jima ba A'isha ta fito. Tun daga nesa ta murtuke fuskarta da ta hango Gali tsaye kamar gunki . Ta ce a ranta "Wannan wahalallen banzan kuma yaushe ya dawo?" Ta karaso wurin da yake ta tsaya, ko sallama ba ta yi masa ba, ballantana kuma ta dube shi, to amma shi da yake ya saba da wannan dabi'a tata, bai damu ba sai kawai ya fara aikinsa na surutu. . "Ai'sha ya kamata yau dai rana daya ki saki fuskarki a gareni, domin kuwa ni da ke mun zama daya, kin ga fa yau saura kwanaki hudu kenan a daura mana aure . Bai kamata a ce mu yi aure kuma ya kasance ba wata kwakkwarar jituwa a tsakaninmu ba. A'isha ya kamata ki hakura haka nan, bakin alkalami ya riga ya bushe." . Ta juyo cikin izgili ta dube shi a yatsine ta ce da shi. "Kai da wacce kuma za a daura muku aure?" Gali ya dube ta cikin kaduwa. . Ku jira part 7 _________ Yan mata kudaina wulakanta samari Domin kuwa zai iya yiwuwa su zaku Aura Izan ya kasance Saurayin da ki ka wulakanta wajen neman aurenki ya zama mijinki sannan ki ka kamu da ciwon sonsa a yayin da shi kuma ya fara Rama wulakancin da ki ka masa . Mutane masu tsananin fushi, masu rike abu a zuciya, basa taba manta wulakanci . Wani mawaki yace = in aka furta so gareka sai kai na'am a zuciya karka zagi Kauna, = Masoyi yana da rana = Masoyi yana da Rana . Sai mun hadu gobe Its shuraih 99% AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 7 . "Kai da wacce kuma za a daura muku aure?" Gali ya dube ta cikin kaduwa. . "A'ah! ni da ke mana A'isha, ko ba ki gane ni ba ne? Ni ne Gali masoyinki." . A'isha ta yi murmushi, amma ko da ganin murmushin ka san cewar a boye a bayan sa akwai abubuwa marasa dadin ji bila'adadin. . "Wani lokacin ka kan ba ni mamaki Gal wai kai don Allah wanne irin mutum ne a duniyar nan? Ba tun yau ba na nuna maka a zahiri, na furta maka baki da baki ba na sonka, ba zan taba sonka ba kuma, to amma kai ka like mini. Yanzu kai saboda Allah har sha'awa kake yi ka auri matar da ba ta kaunarka a duniya?" . Saurayin ya yi ajiyar zuciya ya ce da ita cikin damuwa "A'isha kin dade kina wulakanta ni a lokacin da ni kuma nake ganiyar nuna miki tsantsar soyayya tagari. To amma kuma ke mene ne dalilin da za ki ce ba kya kauna ta? . Dole ne ma ki so ni A'isha, don kuwa babu dalilin da zaki ki so na. Me kike bukata ki mallaka a duniya wanda ba ni da shi? Ke kanki kin san cewar ina da abinda za ki so ni a duniya.." . Aisha ta tsayar da shi ta hanyar jifan shi da wani busashshen murmushi "Lallai ba ka da hankali Gali kuma ba ka san soyayya ba, tunda har ka iya bude baki ka ce wai kana da abin da zan so ka da shi dole . Na san cewar ba wani abu kake takama da shi ba face dukiyarka, to bari in fada maka ni ba dukiyarka ba ce a gaba na? Kai a haukanka shi kenan don kana da kudi dole ne mace ta soka wannan ba gaskiya ba ne ka sake tunani, domin kuwa kai ka mallaki kudi amma kuma ni ba na sonka. Ka ga kenan ashe ko wannan ma ya ishe ka darasi, don ka fahimci cewar kudi ba sa iya sayen soyayya." . Gali ya dubi `yar budurwar cikin harzuka, tunda suke ba ta taba kule shi irin wannan karon ba. Ya ce da ita a fusace "To ya isa hakan nan mu bar wannan zancen, yanzu mene ne shirye-shiryenki game da auren mu? Na san dai ba za ki rasa bukatar wani abu ba." . Tace da shi "Ina bukatar abubuwa da dama amma kuma ba wurinka ba. Ina da bukatar ne a wajen mijina da zan aura, ko ba ka san cewar wani zan aura ba ne Gali?" . Ya dube ta a tsorace "Wai me kike nufi ne? A'isha ni fa ban gane ba, duk kin ruda ni wallahi." . Ta ci gaba da murmushinta sannan ta ce da shi. "Abin da nake nufi shi ne saura kwanaki hudu a daura aurena da wani saurayi da nake kauna a zuciyata, amma ba kai ba." . Gali ya ce da ita cikin rudani. "To ai ni ma saura kwanaki hudu kenan mahaifinki ya daura aurenki da ni, kuma har ma na fara raba katin gaiyata, A'isha." . "Wannan matsalarka ce Gali, ni dai kasancewar ban taba cewa in kaunarka ba kuma ban taba amsar komai naka ba don haka idan an daura aure sai a kai maka wata amayar amma ba dai ni ba." . Tana gama furta kalaman sai ta juya ta shige gida tan kunkunai hade da yin tsaki. Saurayin ya bi ta da kallo har ta bace, maganganunta na ta faman amsa kuwa da kururuwa a kwakwalwarsa. Tuni har ya fara lissafo mutanen da ke bukatar a sai musu likkafani a cikin jerin wadanda zai aika barzahu, indai har ba a kai masa amaryarsa daki nan da kwanaki hudu masu zuwa ba _____________ BABI NA UKU . Ba kasafai Nazifi yake barcin rana ba, domin kuwa ko ba inda yake da bukatar zuwa, da wahala ka same shi a kwance da rana tsaka kai ko rashin lafiya yake yi bai cika kwanciya a daki da rana ba, . bar shi dai ya fito kofar gida ya zauna a dakali ya karanta mujallun fina- finai ko kuma littafan soyayya. To amma kuma sabanin wannan halayya tasa da aka san shi da ita shekara da shekaru, kwanaki biyu kenan Nazifi yana wuni a gida a kwance, ko lekowa waje ba ya yi . Mahaifiyarsa Tabawa ta yi iyakar kokarinta don ya fada mata dalilin canjin wannan halayya tasa amma kuma abin ya faskara, ya ki ya fada mata, sannan kuma babban abin da ya fi ba ta mamaki shi ne wai a cewarsa lafiyarsa kalau, ba inda ke yi masa ciwo. A cikin kwanakin biyun nan ko wurin sana'arsa ta kafinta bai leka ba, . wanda abu ne mai wahala ko ma kuwa menene dalilin a ce Nazifi ya ketare rana daya bai je wurin wannan sana'a tasa ba. To amma kuma abinda ya tsorata Tabawa shi ne, wani lokacin idan yana kwance yana barci idan ta leka dakinsa , sai taji yana ta sambatu a cikin barci, yana fadar sunan wata yarinya wai ita A'isha. Sannan kuma wani lokaci sai ta same shi yana ta murmushi . Ko da Tabawa ta lura da wannna bakon al'amari da ya sami danta Nazifi sai ta ce da shi a fusace a wuni na biyu . "Haba ai ni dama na san a rina ai ga irin ta nan kullum kwanan duniya yaron nan sai na yi fama da kai ka rika shan maganin miyagu da kuma na mutanen boye, amma taurin kan tsiyarku na `yan zamani ya hana ka Nazifi, ga shi nan ai ka yi gamo da aljana za ta sabautar da kai a banza." . Tun daga wannan lokaci Tabawa ta fara shirye-shiryen kaiwa bokanyarta ziyara, domin kuwa ta san cewar wannan aljana da ta cafi danta guda daya da take alfahari da shi a duniya, duk tsiyar aljanar in dai har ta kai ta wajen kwararriyar bokanyarta Iya mai dogari, to ko ba ta shirya ba sai ta fice daga jikin danta Nazifi . To amma kuma shi Nazifi ya san cewar ko sarakan bori na duniya ne suka taru a kan shi ba za su iya maganin wannan matsala tashi ba, domin kuwa duk kwarewarsu akan wannnan sana'a ba za su iya mallaka masa masoyiyarsa da ya kamu da ciwon so ba, wacce saura kwanaki biyu kacal a daura aurenta da wani saurayin can daban .... CIWON SO kenan ___________ MASOYA AKIYAYE Izan zaka so mutum to ka soshi daidai wa daida Haka nan yan mata kada ku dauki son duniya ku daurawa saurayi/budurwa, daga karshe kuma ku rasasu, rayuwarku ta fada cikin garari . Its shuraih 99% AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 8 . Kamar kullum a cikin kwanaki biyu yana kwance sai mahaifiyarsa ta shigo cikin dakin. Ya yi tsammanin zancen neman maganin ta zo yi masa, to amma sabanin haka sai ta ce da shi. . "Wata yarinya ce wai ta zo tana son ganin ka, shi ne na ce bari in zo in sanar da kai." . Nazifi ya mike zumbur cikin mamaki, domin kuwa inda haka nan ne banza sai a wuni ana fama da shi ba zai tashi ba, kai a cikin kwanaki biyun nan har lokacin sallah sai ya zo ya wuce yana kwance ba zai yi ba. . Amma yanzu daga jin an ce wata ta zo nemansa, duk da dai bai san ko wace ce ba, amma a can cikin zuciyarsa sai ya ji ya dokanta da ya fita din. . Ya tashi da sauri kamar ba shi ne ke wuni a nannade a gado ba, kamar wanda ake yiwa karin ruwa. Lallai dai sha'anin yaran zamani sai dai a bar su, Tabawa ta fada a zuciyarta, ita ma ta fice daga dakin. . Fitar sa ke da wuya ya cikaro da ita a tsakar gida tana sanye da atamfa shudiya da kuma dan fingilin gyale. Hakika zatonsa ya zama gaskiya domin kuwa wacce yake tsammani ce ya gani. Suka yiwa juna murmushi, Nazifi ne ya fara yi mata magana. . "A'isha da ma ashe ke ce...?" Ta jefe shi da murmushin Allah kashe ni don dadi, sannan ta ce da shi. "Kai da wa kake tsammani?" "Ban yi tsammanin ki ba, domin kuwa na dauka cewar tuni kin mance da ni A'isha." Ta sake jifan shi da wani murmushi. . "In ban da abinka Nazifi ka taba ganin inda mace ta mance da mijinta? Ko ba ka san cewar ni a matsayin mijina nake daukarka ba, ko ka mance da alkawarin da na daukar maka ne in dai ina da miji a duniya ai kai ne Nazifi." . Ya lumshe idanu don farin ciki, a zuciyarsa ya ce Allah ya sa haka ya zama gaskiya A'ishata, sannan ya ce da ita. . "Zo mu shiga daga ciki A'isha nan ba wurin da za mu tattauna matsalolinmu ba ne." Suka shiga cikin dakinsa, rufin kwano doron zabuwa amma kuma babu silin babu komai a ciki idan aka tsame dan tsurkun gadonsa na katako mai kama da makara da kuma wata kujera daya ita ma ta katako mai kafa uku da rabi. A'isha ta yi wa kujerar kallon nutsuwa kafin ta sami mazauni a kanta, domin kuwa tunda suka shigo cikin dakin ta dubi rubabbiyar kujerar ta fara zullumin cewar da wahala kujerar ta iya daukar nauyin mutum dukansa . To amma kuma cikin sa'a sai kuma ta dauke ta gaba daya, duk da yake dai takan nemi ta turgude a dalilin nakasar da ta yi na gutsurewar rabin kafa guda. Nazifi ya fada kan

Chapter 2 of 4