Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
gadon katako . Da farko A'isha ta yi tsammanin gadon zai baje a kasa, to amma abin mamaki sai ta ga shi ma gadon taurin rai gare shi irin kujerar, bai yi komai ba sai dai burari da raki domin kuwa ko'ina a jikinsa ihu yake yi da zarar an motsa. . Saurayin da budurwar suka kalli juna cikin nutsuwa, Nazifi ya fara magana "A'isha ina fatan ba ki samu wata babbar matsala ba a wurin mahaifinki, domin kuwa ransa ya baci sosai a dalilin ganina da ya yi tare dake." . Ta ce da shi "Kai zan yiwa wannan tambayar ka riga ni Nazifi, domin kuwa tun rabuwarmu nake faman zullumin ina fatan bai doke ka ba Nazifi." Ya yi ajiyar zuciya. . "Bai doke ni ba amma kuma gara ma a ce duka na ya yi da abin da ya sanar da ni. Ya gargade ni kada in sake kusantar inda kike A'isha. Wannan kalami da ya yi ya sosa zuciyata, a dalilin haka ne na sami kaina a cikin wani hali mawuyaci. Tun wannan lokaci ban sake fita ko waje ba kullum ina nan a daki ina jimamin rabuwata da ke domin ni ban ma yi tsammanin zan sake ganin ki ba har abada, A'isha." . Ta yi murmushin karfin hali. "Duk wannan bai kamata a ce sun sa ka tsorata ba, domin ni kaina ya sha yi mini wannan barazanar, don haka ka kwantar da hankalinka Nazifi, aski ya riga ya zo gaban goshi." . Ya dube ta cikin rashin fahimta, "Kamar yaya ban gane ba?" Ta sake yin murmushin. "Abin da nake nufi shine wahalar mu ta zo karshe in dai ka shirya, kuma da gaske kana kauna ta har cikin zuciyarka kamar yadda ni ma nake kaunarka" Ta dan saurara sannan ta ce da shi a sanyaye. ''Nazifi ka shirya gobe mu je a daura mana aure.'' . Saurayin ya ji gabanshi ya fadi ras da kalaman suka dira a cikin dodon kunnen shi a bazata, kadan ya rage ya fado kasa don tsananin razana. . ''A`isha aure fa kika ce?'' Ta dube shi har cikin idanunsa ta ce da shi. ''Aure mana Nazifi ko ba ka shirya ba ne, dama yaudarata kawai kake son yi ban sani ba." . Saurayin ya dubi kwayoyin idanin `yar budurwar da ke zaune akan kujera ta sa shi a gaba, ya tabbatar lafiyar ta kalau ba tabin hankali ta samu ba, ya ce da ita cikin mamaki. . "A'isha kin taba ganin inda saurayi da budurwa kawai suka ware kansu suka aurar da kansu ba wasu shaidu ko waliyyai, sannan kuma ya za a yi a ce gobe-gobe ba wani shirye-shiryen komai." . `Yar budurwar ta ce da shi "Ni ba cewa na yi ka sayo min akwatuna ba, sadaki kawai nake so a wurinka, shi ma don ya zama dole ne, da ba zan bukaci komai a wurin ka ba kuma shi din ma sai abinda ka kawo ka ba ni. Malamin da zai daura mana aure da shaidu, kai ko ma mene ne ake bukata ba za mu sha wahalar samu ba. . Wannan alhakin ka ne ka nemo mana malami wanda zai daura mana aure cikin sirri daga mu sai mu sai shi. Daga nan kuma sai ka samar mana wurin zama na sirri . Duk wadannan abubuwan ne da ya kamata a ce ka shirya su a gobe domin kuwa idan abin ya wuce gobe, to mun rasa juna kenan har a bada." . Shiru bai ce da ita komai ba domin kuwa maganganun da take fada duk sun gama sa shi tsurewa. Zuwa can sai ya ce da ita cikin in- ina "To ai ni a gaskiya A'isha wallahi abin ne ya zo mini duk a kurarren lokaci, kuma bayan haka kin dai gani da idanunki wallahi ba wani wadata ne da ni ba kuma ba wata kwakkwarar sana'a nake yi ba. sannan...." , Ta katse shi cikin damuwa. . "Duk da haka dai na tabbatar a matsayinka na namiji indai har ka yi niyya duk wadannan abubuwan ba za su gagare ka ba, in dai har kana sona da gaske to bai ma kamata ka tsaya ka kawo mini wadanan matsalolin ba, kasancewar dai ko rance ka nema a wurin abokan sana'arka ba za ka rasa samu ba. Ba wasu kudin ba ne masu yawa za ka tanada ba Nazifi, sadaki kawai fa na ce ina bukata, daga nan kuma sai 'yan kudin da za a baiwa limamin da zai daura auren, don mu rufe bakinsa kada ya tona mana asiri. Haba Nazifi ka yi tunani fa ka gani, akwai wanda ya kashe miliyoyin kudi a kaina, amma na ce ba na kaunar shi sai kai Nazifi, amma kuma kana nema ka ba ni kunya, ka kware mini baya." . Ya yi saurin cewa da ita "Ba haka ba ne A'isha, ke kina ganin kamar ba na son al'amarin ne, wallahi ina so. To amma matsalolin da ke tattare da al'amarin nake hangowa. Idan fa muka yi auren nan a boye, muka nemi wurin zama dole ne a yi bincike don a gano inda kike a garin nan, kuma abin duniya ba ya boyuwa, dole ne asirin mu ya tonu wata rana, don aure ba abin wasa ba ne." . "To sai me don an gane daga baya in dai mun yi auren? Ai shi kenan, ka san dai duk duniyar nan idan an taru ba mai raba mu, tunda muna son juna. Kuma wai kai tsoron me ma kake ji? Sai ka ce ba namiji ba. Rigima wa ta kashe a duniya? Mu yi auren nan shi ne mai wahala, komai zai biyo baya ya ma biyo. Ni fa mace ce Nazifi amma har in ce na ji na gani a kan soyayyar mu, amma kai kana namiji ka tsaya kana fargaba. Ni wallahi ka fara ba ni kunya Nazifi." . Ta kura mishi idanu a yayin da ya yi shiru yana mis-mis da baki, yana kokarin fitar da tunani daya tsakanin amincewa da kuma sabanin haka, daga nan sai ta cigaba da ta ga bai ce komai ba. . "Idan kuma kana ganin ba zai yiwu ba, shi kenan ba matsala sai in tashi in yi tafiyata, ka nuna mini kenan da ma ba kauna ta kake yi ba, sai in je in rungumi kaddara in auri wancan saurayin da ba na kauna a zuciyata, wanda shi kuma yake sona kamar ya hadiye ni. Ba komai Nazifi, dama an ce son maso wani koshin wahala."Ta mike daga kan musakar kujerar da niyyar ficewa. Nazifi ya yi farat ya ce da ita, bakin sa na rawa. . "Ki gafarce ni A'isha, abin bai kai mu ga haka ba. In dai don wannan maganar ce kina bukatar komawa ki zauna, na amince zan yi duk abin da kika ce da ni. Ni dai a halin yanzu ko sisi ba ni da shi a aljihuna, to amma kuma tunda kin ce da ni rigima ba ta kashe uban kowa, to ni ma zan jarraba yin ta, don na san ba za ta kashe ni ba. Domin kuwa ba karamar rigima ba ce mutum ya tunkari aure awoyi ashirin da hudu masu zuwa sannan ya nemi gidan haya, da kuma kudaden limamin daurin aure duk kwana daya kacal, amma kuma bai tanadi ko ahu a aljihunsa ba, ke ma kin san wannan katuwar rigima ce, A'isha." . ___________ Tab malam Nazifi kwarankwasa maganarka dutse ce, Don da rigima na kisa, da wannan typing din bai zo gareku ba sakamakon rigimar dana jajibo ma kaina shekaran jiya, sai de dakyar na sha yayin da fuskata ta suntuma suntum, idanuwa na sukai luhu luhu, sakamakon dukan da na ci wajen ......... Kaga su o'o da o'o an kasa kunne don jin tsurku to na fasa bada labarin, its shuraih 99% . Part 9 is loading AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 9 . Washegarin ranar tun da sassafe misalin karfe bakwai, Nazifi ya fara zirga-zirga a cikin garin yana fafutukar nemo rancen isasssun kudin da zai rike , kafin nan da wadansu awoyi in dare ya yi, domin kuwa a yadda suka rabu da 'yar budurwar ta ce da daddare za ta zo ta same shi su wuce wurin daurin aure. . To amma kuma tun a jiya din bayan sun rabu yake ta faman cuku-cukun inda zai sami kudin da yake bukata, amma kuma shi dai a iyaka kokarin sa bai san inda zai samo wadannan kudi ba. . Sannan kuma bugu da kari ba shi da wata tsohuwar ajiya ko kuma wadansu kadarori ballantana ya daga su ya makar don ya sami kudaden da yake bukata. Ya san cewa in dai ba tsohon kekensa ba to da wahala ya sami wani abu da zai sayar, wanda kudinsa za su kai dubu daya, ko suturunsa ya daga ya sayar ya san cewar ba za su samar masa kudin ba. . Don haka ya kasance cikin rashin kwanciyar hankali ko wani barcin kirki bai yi ba. Duk mutanen da Nazifi yake tsammanin zai sami kudi a wurinsu, da kuma abokansa duk ya bi su daya bayan daya amma kuma Allah bai sa ya dace ba . Da rana ta take misalin karfe sha biyu sai Nazifi ya zauna a makarin wata kwalbti dake bakin titi, yana tunanin inda zai sake dosa kuma gashi lokaci kara kurewa yake yi. . Nazifi yayi ajiyar zuciya, sannan ya mayar da hankalin shi kan motocin da ke wucewa ta gabashi ya yiwa kansa murmushi, da ya yi tunanin cewar wai saura bai fi awoyi takwas masu zuwa ba ya zama ango, amma kuma babu ko ahu a aljihunsa, . gashi kuma wata azababbiyar yunwa ma yake ji, ko abin da zai sa a cikin shi bai mallaka ba amma kuma wai a yau ne zai tare da sabuwar amarya, wacce wani ya kashewa kusan miliyan guda don a mallake ta, lallai wannan shi ne daukar dala ba gammo. . To wai shin me zai sa ma in dami kaina ne? Nazifi ya tambayi kanshi lallai fa bai kamata ba ma ya tsaya yana damun kanshi, domin kuwa ita ta ce ta ji ta gani, ko ba shi da ko sisi, ya san cewar za ta san inda za ta samo masa kudaden tun da dai ta riga ta mutu akan kaunarsa. . Ya sake yiwa kansa murmushi sannan ya ce a bayyane. "Kada ka damu Nazifi, ko baka da ko sisi yau sai ka zama ango a duniyar nan, kuma sai ka tare a dakin kyakkyawar amarya, wacce farashinta ya zo daidai da naira miliyan..." . Bai gama tunanin ba ya ji dirar zukekiyar motar a gabanshi, ya dawo hayyacinsa cikin kaduwa a lokacin har gilashin motar ya sauka kasa , suka dubi juna shi da dogon saurayin dake cikin motar, shi kadai sanye da bakar kwat, yana murmushi. Da farko Nazifi bai gane shi ba, domin kuwa rabon da a ce sun hadu da wannan saurayi tun a makarantar sakandire, inda suka gama tare, to amma a halin yanzu ya kara girma da kiba da ba don tun a wancan lokaci sun shaku ba, to har ga Allah da Nazifi bai gane babban abokinsa Gali ba. . "Nazifi me kake yi a nan zaune, lafiya" Nazifi ya mike ya dafa tagar motar ya ce dashi cikin mamaki "Gali ashe dama kana duniyar nan" Saurayin ya yi dariya. . "Ina nan a raye Nazifi, ina nan a garin wallahi" Samarin biyu suka gaisa cikin farin ciki nan suka tuna da tsohuwar abotarsu tun suna makaranta. . "Wallahi Gali na cire tsammanin za mu sake haduwa, domin kuwa tun shekara da shekaru na neme ka har na gaji." Amma kuwa har yanzu tunanin awoyin da suka rage ta zo ta same shi ne zuciyarsa. Gali ya ce da Nazifi ya bude bangaren mai zaman banza ya zauna suka sake gaisawa da Gali babban aminisa. Gali ya ce da shi. . "Na san cewar dole ne ka yi mamakin bacewar da na yi shekara da shekaru Nazifi, ba na kasar ne domin kuwa tun bayan gama makaranta ni ban ci gaba da karatu ba, sai na shiga aikin soja, aka turani kudancin kasar nan, daga baya kuma da za a je sasanta rigimar kasar Saliyo aka diba har da ni. . Tun wancan tsawon lokacin muna can sai bara aka dawo da mu, shi ne na dawo gida a halin yanzu don in yi aure, domin kuwa wallahi abokina mun sami alheri sosai a dalilin wannan yaki da muka je." . Nazifi ya ce da shi cikin yake-yake, dariya- dariya. "Ai na ga alama wallahi mutumina ka sami hutu, mu muna nan har yanzu a rabe muna ta `yan buge-buge, amma ba wani canzawa kullum muna guri guda." . "Tun bayan gama makarantarmu me ka yi Nazifi?" Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce da shi. . "Ba na aikin komai Gali, kawai dai ina dan taba sana'ar kafinta wacce nake dan samun na batarwa a cikinta" . Gali ya dan nuna damuwarsa a fuska sannan ya ce da shi. . "Rayuwa kenan Nazifi sai hakuri, ka san cewar kowa rabon shi yake samu a duniya mutum bai wuce rabon shi Nazifi." . Nazifi ya yi murmushi a zuciyarsa yace "Ni kuwa na san haka tunda gashi ba ni da ko ahu amma zan auri kyakkyawa wacce wani miloniyan ke burin ya aura a duniya." . "Yanzu zaman me kake yi a nan kai kadai cikin rana, Nazifi?" Ya sake yin ajiyar zuciya, "Wallahi wannan zaman da ka ga na yi Gali ina cikin wata katuwar matsala ce wacce ta fi karfina." . Gali ya yi masa murmushi ya ce da shi. "Ni kuwa ban yi tsammani cewar a wannan halin da nake ciki har akwai wanda zai ce ya fi ni shiga matsala ba, matsalarka ba ta kai ko rabin wacce nake ciki ba" . Nazifi ya ce dashi. "Haka dai ka ce Gali amma da a ce za ka ji matsalata, kai da kanka za ka san cewar ta fi taka matsalar" fada min matsalar taka na ji ni kuma zan fada maka tawa matsalar." Nazifi ya kurawa gilashin motar idanu ko kiftawa ba ya yi sannan ya ce da abokin nasa . "A halin yanzun da ka ganni a nan Gali, yau ne za a daura aure na kuma a yau ne zan nemi gidan da za mu zauna ni da amarya, amma kuma ko sisin kwabo ba ni da shi a aljihuna . Ka san cewar ina cikin matsala maigirma, Gali" Gali ya tuntsire da dariya. . "To kai Nazifi ya aka yi ka daukowa kanka wannan rigimar, ka san cewa ba ka da ko sisi? sai ka ce za ka auro `yar tsana ba mutum ba?" . Nazifi ya dube shi sosai ya ce. "Wallahi rigima ce kawai Gali, bari ka ji yadda abin ya faru. Tun farko yarinyar ce ta like mini na rasa yadda zan yi da ita shi ne ta ba ni zabi ko dai in nemo kudi a daura auren a yau din nan ko kuma mu yi hannun riga ma'ana mu rabu , to ni kuma ina bala'in son yarinyar nan Gali, kullum tana raina, shi ne na yi mata karya zan nemi kudin amma har yanzu da ka same ni a nan ko kwabo bai zo hannuna ba, kuma anjima za a daura aurenda daddare" . Gali ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce. "Eh, to kai ma kana cikin matsala Nazifi, to amma kuma dai har yanzu ina jin matsalata ta fi taka domin kuwa ni ma gobe ne za a daura aurena da wata yarinya, na kashe kudi sun kusa miliyan daya a kan wannan yarinya, . to amma kuma ba ta kauna ta ko nan da can. Ko jiya da na je wurinta da zage-zage muka rabu amma kuma gobe ne za a daura mana aure domin kuwa tuni har na gama rarraba katin gayyata, Nazifi." . Nazifi ya ce da shi "Ina ban da abinka Gali me ya ja maka yin wannan tabargaza? Yaya za a yi bayan kasancewar yarinyar ba ta kaunar ka amma kuma ka kashe mata wadannan uban kudade sai ka ce za ka auri `yar zinariya, ba wacce take da jini irinka ba?" . "Wallahi Nazifi ni ma dai rigima ce kawai ta sa ni yin wannan aika-aikar domin kuwa irin ciwon son yarinyar nan da nake shi ya sa na turawa iyayenta wadannan makudan kudade, domin kuwa na san cewar duk tsiyarsu dai ko ba sa so dole ne su ba ni yarinyar, tunda dai ba za su iya biyana kudin da na kashe ba." . Abokan biyu suka tuntsire da dariya a lokaci guda hade da tafa hannuwa. Nazifi ya ce da abokin nasa. . "Kai rigima dai ba ta karewa a wannan duniyar Gali, in kana duniya ka ga tsiya iri-iri, wato in da za ka san cewar ni dan tsiya ne, bani da kirki abokina, wani miloniya ne fa ke son yarinyar nan tawa amma kada ka ga yadda take kwabsa shi . An ce wai da motoci yake zuwa wurin ta zuka-zuka, amma kuma na kwace mishi ita." Suka sake fashewa da dariya Gali ya ce . "Ai ni har yanzu ban ma gano nawa abokin karawar ba, wallahi na rasa dan iska da ke hurewa tawa budurwar kunne a garin nan. To amma ina nan ina zuba idanu sai na gano dan banza." . Ya rage fara'a sannan ya ce da abokin nasa. "Ka san abin da zan yi masa kuwa Nazifi?" Nazifi ya girgiza kai cikin rashin fahimta. Gali ya dan yi busasshen murmushin mugunta sannan ya ce da shi. . "Harbe shi zan yi da `yar kaunar bindigata." Suka sake yin dariya a lokaci guda, amma shi Nazifi yake-yake yi ba dariya ba, domin kuwa bai taba tsammanin irin wannan tunani na kashe mutum a zuciyar abokin nasa ba. . To amma kuma abin da bai sani ba, shi ne abokin nasa yafi jin tausayin kashe kiyashi fiye da kashe mutum. Gali ya tattara hankalinshi wuri guda sannan ya ce da Nazifi. . "Kada ka damu Nazifi zan magance maka matsalarka gaba dayanta, daga nan kuma sai mu dawo ni ma ka taya ni don mu magance tawa matsalar. . Yanzu dai da farko zan ba ka gida da zaka zauna kai da amaryarka domin kuwa ina da sababbin gidaje har guda uku a garin nan duk gaba daya na ginasu, sannan kuma zan ba ka isassun kudin da za ka yi hidimar komai da komai na wannan aure." . Nazifi ya ji numfashinsa ya dauke, don tsananin murna, "Na gode sosai Gali, wallahi ka yi bala'in `yanto ni mutumina" . Gali ya jawo wata bakar jaka da ke bayan motar, ya dorata a kan cinyar Nazifi, sannan ya danna wani kwado murfin jakar ya bude. Nazifi ya some a zaune, jakar dankare take da 'yan dari biyar-biyar sabbi fil da su, suna ta daukar idanu. Gali ya dafa kafadarsa cikin tsokana sannan yace da shi. . "Kai banza na ga duk ka bi ka wani rude sai ka ce ka ga wasu kudin arziki Ka da ka damu Nazifi ba su da yawa rabin miliyan ne, da ma yanzu na je banki na amso su, Allah ya sa rabonka ne, ka je ka yi hidimar aurenka da su." . Nazifi ya dubi abokin nasa a rude ya ce da shi cikin kidimawa "Duka ka bar mini Gali? Rabin miliyan fa ka ce...?" Gali ya daga masa girar idanunsa sannan ya ce da shi. . "Eh, rabin miliyan ne Nazifi, ko sun yi maka kadan ne in kara maka kamarsu su zama miliyan guda?" . Nazifi bai gasgata kunnuwansa ba. ________ Hehe Rikici bata kisa amma da alama zata fara takan Nazifi SOJA GALI yayi tabargaza, shin meye tunaninku alokacin daya gano budurwarsa daya rage saura kwana biyu a daura masu aurene, Nazifi zai aura, kuma zasu zauna cikin gidansa, me zai faru . GWARAMA KENAN Its shuraih 99% ________________ BABI NA HUDU| . Dogon malamin wanda ke sanye da dogayen kaya farare rike da dogon carbi a hannunsa ya gyara zaman katon nadinsa, wanda ya mike tsawon bayan sa ya kwanta, kamar wutsiyar doki, ya dubi saurayin da budurwar, wadanda ke zaune a gaban shi suna sauraronsa kamar wadanda ke daukar darasu ya ce dasu cikin girmamawa, . "Yara me yake tafe daku?" Nazifi da A'isha suka dubi juna a sannan lokaci guda suka yi ajiyar zuciya, domin kuwa shi dai Nazifi tun kafin su zo wurin malamin da ma yana shakkar da wahala idan za su yi nasara, to amma dai a yadda ya ji ana kishin- kishin tabbas ya ji an ce wai wannan malami dan tsubbu ne shi ya sa ya zabi su zo wurin sa, domin kuwa ya san cewar zai dan fi saukin kai in dai suka nuna mishi makudan da ke hannusu . Nazifi ya dan yi masa murmushi sannan ya ce da shi. "Mhm. da ma malam wata `yar matsala ce ke tafe da mu zuwa wurinka." . Malamin ya sake gyara zaman a kan tafkeken buzu, sannan ya gyara zaman nadinsa mai kama da mushen jimina, domin kuwa tun zuwan wadannan yara biyu saurayi da budurwa, ya ji kansa yana dan sarawa kamar zai yi ciwo, domin kuwa duk ya rasa kansa kamar ba mutane ba. . "Ni fa a gaskiya ban gane abin da kuke nufi ba, ban san me yake tafe da ku ba. Ina jin da za ku fito fili ku fada mini matsalarku da zan fi son haka, amma kuna ta wasa da hankalina sai ka ce wani karamin yaro." . Nazifi ya sunkuyar da kan shi cikin ladabi ya ce da malamin. "Ka yi hakuri malam lamarin ne yana da dan wahala shi ya sa ka ji muna fargabar fada maka." . Malamin ya shafi dogon gemunsa ya ce da su "Duk da haka dai tun da kun rigaya kun zo ai sai ku fada mini in ji domin kuwa ina da aiki da yawa a gabana, kun ga yanzu dare ne lokaci ne da muke aiki da rauhanai, ba lokacin tsayawa wasa ba ne." Wannan karon yana magana yayin da yake dan zazzare ido don barazana. . Saurayin da budurwar suka sake kallon juna. `Yar budurwar tana sanye da burmemen hijabi, tana sauraron diramar da ake yi tsakanin saurayinta da kuma malamin mai kama da rauhani, domin kuwa ya mafi kama da rauhanin fiye da mutane. Nazifi ya ce da shi kai tsaye.. . "Alagafarta malam ka gafarce mu, ba wani abu ya sa muka zo wurinka ba ni da wannan masoyiya tawa sai kawai don wata `yar bukata wacce muke son ka share mana hawaye a kan ta." . Nazifi ya dan saurara sannan ya cigaba. "Alagafarta malam mun zo gurinka ne don ka daura mana aure a boye, ma'ana ba ma son kowa ya san da faruwar wannan al'amari." , Dogon malamin ya zaro idanunsa cikin rudani kana ya yi saurin dafe kan shi. A wannan karo ji yake kamar zai rabe gida biyu domin kuwa duk shekarun da ya dauka yana wannan sana'a ta tsubbu ya hadu da attajirai da talakawa, `yan kasuwa, da kuma `yan siyasa, kai har da `yan fashi da makamai, amma ko sau daya bai taba jin wani ya zo masa da tatsuniya irin wannan ba, sai a wannan karon. . Ya gyara zamansa sannan ya muskuta baya kamar yana tsammanin za su haushi da duka a cikin dan tsurkun dakin nasa na ganawa da baki. . "Ku gafarce ni yara a gaskiya ba ni jin zan iya wannan aikin, ina jin sai dai ku lalubi wani malamin amma dai ni ba na irin wannnan aika-aikar." . Nazifi ya dubeshi cikin damuwa. "Ka taimake mu malam, wannan ba wai abin assha ba ne domin kuwa kai ma za ka samu lada, tun da dai raya sunnar fiyayyen halitta ce." . Malamin ya ce "Ba wai taimakon naku ne bana son yi ba, to amma shi aure ba haka nan ake yin sa kawai ba wani bincike ba, domin kuwa ni yanzu ba zan iya sani ba ko da aure a tsakaninku ko babu ba, tunda dai ban taba ganinku ba. Sannan kuma ban san da wacce manufa za ku yi auren ba." . Nazifi ya sake marairaicewa. "Wallahi malam ba wata manufa, muna so ne kawai mu yi aure, wadansu matsaloli ne suka sa za mu yi a boye." . "To me ya sa ba za ku sa iyayenku a gaba su wakilci maganar ba? Ko ba ku da iyaye ne a nan garin?" . Masoyan biyu suka sake duban juna, kana saurayin ya ce, "Muna da iyaye Malam, to amma dai wannan wani sirri ne a tsakaninmu da kai. Mun wakilta ka ka zama iyayenmu, sannan kuma ka zama waliyi a tsakaninmu duka, kuma kai ne shaida." . Malam ya tattara carbinsa wuri guda kamar `ya`yan goriba sannan ya dubi masoyan biyu ya ce da su. "Aure irin wannan ba shi da kyau, ko kuma in ce yana da matsala domin kuwa babu mamaki ma kun sha nono daya." . Nazifi ya ce a marairace. "Wallahi malam ba mu sha nono daya ba, masoyiyata ce ba kanwata ba ce." Malam ya sake hade fuska duk ya yi zufa sharkaf ya ce da su "Kai ni fa ban taba yin wannan aika-aikar ba, a gaskiya sai dai ku gafarce ni ba zan aikata wannan tabargazar ba, domin kuwa shi aure ba haka kawai ake..." . Maganar ta makale a makogwaronsa, bai samu damar karashewa ba sakamakon abinda ya hango a hannun saurayin. Sababbin `yan dari biyar ne dami guda suna daukar idanu. Saurayin ya ajiye kudin a gaban malamin sannan ya ce da shi . "Amincewarka muke bukata ba wa'azinka ba Malam, domin kuwa ba haka nan za mu barka ba. Idan ka amince ka dauki wannan duk naka ne ladan aiki. Idan kuma ba ka amince ba shi kenan sai mu dauke kudinmu muje gaba wani malamin ya daura mana auren. To amma dai me ka gani?" . Malamin ya sake gyara zama kamar wanda yake zaune a kan kunama, ya sake duban kudin a halin yanzu bayan ciwon kan da yake ji har wani abu kuma yake ji yana tsikarar hakarkarinsa da cikin zuciyarsa. Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce da saurayin. . "Kada ku damu yara zan dan yi shawara. Mu gani, ni dai a gaskiya ban taba irin wannan ba, to amma dai tunda kun ce a taimaka muku ai dole ne a taimaka muku din. Ina ganin ba wata matsala ta yanka maka sadaki ka biya, yanzu nan ma sai a daura muku auren, ku yi tafiyarku." . Yana gama fada ya warce damin kudin, ya bankada karkashin tafkeken buzunsa ya watsa su ciki. Duk fa wa'azin da ya yi musu a baya duk ya mance. . _____________________________________ Shuraih 99% . "Ku yi hakuri Gali, wallahi ni kaina ban ji dadin faruwar wannan mummunan al'amari ba. To ka san zamani ya canza. Wallahi ni kaina ban san lokacin da yarinyar nan ta lalace haka ba, ban taba tsammanin zata iya guduwa ta bar gida a kan wannan maganar ba." . Gali da ke sauraron Alhaji Dage ya hade fuskar shi. ''Agaskiya Alhaji ba zan yarda da duk abinda za ka fada mini a kan wannan al`amari ba. Ta yaya ma za a ce in gama raba katin gayyata, anjima nan jama`a fa za su fara zuwa kofar gidan nan don daurin aurena da yarinyar nan, amma ka ce da ni wai tun daren jiya ba a san ma inda take ba . Dole ne a nemo mini matata, in dai ana son zaman lafiya.'' Alhaji Dage ya gyara zaman faskeken tabaronsa, wanda ya fi fuskarsa sai ka ce wazirin akun magana jari. "Bai kamata a ce ka yi saurin fushi haka ba Gali, domin kuwa wannan yarinyar dai ba za ta bata

Chapter 3 of 4