Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels AJALI Marubucin littafin Shafi'u Dauda Giwa Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 1 . BABI NA FARKO . "A gaskiya Nazifi sai dai ka yi haquri da abinda zan fada maka ni dai shawarar da zan ba ka ita ce, ka yi haquri ka manta da al'amarin wannan yarinyar domin kuwa a gaskiya ba abokiyar tafiya ba ce" . Nazifi ya dubi abokin hirar tashi cikin mamaki da kaduwa, "Kamar yaya in yi haquri Jamilu, ban gane abinda kake nufi ba." Jamilu ya muskuta a kan dogon bencin da suke zaune, "Ka gane ko Nazifi, ba wai ina nufin yarinyar ba ta da kyawawan halaye ba ne, a'a tana da halaye nagari. To amma, ni dai halayen babanta nake hango maka Nazifi. Na san halin mutumin domin kuwa tunda ka yi mini kwatancen yarinyar, na fara zulumin ka yi zaben tumun dare." . Nazifi ya sake duban sa cikin rudani. "Haba Jamilu wannan wace irin magana ce? Yaya ma za a ce in ga yarinya jiya-jiyan nan, sannan kuma in ji ina son ta a raina, har mu gama tattaunawa mu yi alqawari ni da ita, amma kuma ina fada maka ka ce da ni in rabu da ita. Kai ma kanka ka san cewa wannan magana taka Jamilu ba mai amsuwa ba ce." . "Ba ina qoqarin raba ka da yarinyar ba ne Nazifi. Abinda nake qoqarin nuna maka a nan shi ne wannan yarinyar ba baquwa ba ce a wurina. Na san gidansu domin kuwa mun taba zama a unguwar. Hakan shi ya sa na fahimci cewar ba za ka iya jurewa da halayen mahaifinta ba." . Samarin biyu suka qurawa juna idanu. Nazifi ya ce da shi, " To ai ni ban gane matsalar da kake so ka nuna mini na rabuwa da ita din ba ne, kuma ka qi ka sanar da ko wane ne mahaifinta, domin kuwa ni gidansu kawai ta kwatanta mini ba ta fada mini sunan mahaifinta ba." . Jamilu ya dan saurara sannan ya ce da shi, "Mahaifinta ba wai voyayye ba ne, sunansa Alhaji Dage, wataqila ma dai ba za ka rasa jin labarinsa ba." "Ban san shi ba, Jamilu, to amma dai tunda ka sanar da ni a halin yanzu, ina ganin kana iya ba ni taqaitaccen bayani game da halayen nasa don in fahimci irin matsalolinsa da kake magana a kai." . Jamilu ya kai ganinsa dama da hagun harabar qofar gidan, ya tabbatar babu wanda yake sauraron hirar tasu, sannan ne to ya dawo da hankalinsa kan Nazifi, wanda ya yi fakare yana sauraronsa. . "Ka gafarce ni Nazifi, zan fada maka halayensa gaba daya. A gaskiya Alhaji Dage ba ya baiwa talaka auren `ya`yansa, domin kuwa ya aurar da `ya`yansa aqalla guda biyar, amma kuma na ji an ce duk a cikin wadannan `ya`yan nasa, babu wacce ta auri talaka irinka Nazifi. Kuma a wata majiyar ma an ce wai idan har ka auri 'yar gidan Alhaji Dage, dole ne ka riqa samar masa da albashi kowanne wata. Ka ga dai kai talaka ne Nazifi, don Allah ka yi wa kanka qiyamul laili, kada ka jawowa kanka abin tsiya kana zaune lafiya. Kawai ka mance da zancenta, ka nemi wata budurwar daidai qarfinka." . Nazifi ya yi shiru yana tunanin maganar, zuwa can sai ya ce, "Amma fa al'amarin nan ya daure min kai Jamilu, domin kuwa jiya a wurin fatin nan kada ka so ka ga yadda yarinyar nan ta manne mini, duk inda na nufa tana liqe da ni kamar cingam. Kuma har ma mun yi alqawari da ita cewar zan kai mata ziyara a yau din nan." . Jamilu ya fashe da dariya. "To daga haduwar fari kuma kawai sai ka tsaya kana damun kanka Nazifi? Sai ka ce za ta kai ka qara idan ka ce ka fasa yin soyayyar? Ni dai ka ji shawarar da zan ba ka. Idan ka dauka ta yi maka amfani. Idan kuma ka yi kunnen uwar shegu da wannan shawara tawa, to wannan kuma ya rage naka. Ni dai na fita haqqinka a matsayina na abokinka, tunda dai ka tambaye ni gaskiya na gaya maka." . Koda ya kammala sanar da shi sai ya juyar da fuskarsa wani bangaren don ba shi damar yin tunanin maganganun. . Nazifi ya yi tagumi yana tunanin wadannan maganganu na wannan aboki nasa Jamilu. Sannan ya sake dawo da farkon haduwarsu da yarinyar a daren jiya sanda ake fatin wani abokinsa. . Tana daya daga cikin manyan qawayen amarya. Tana sanye da shudin gwaggwaro. dan saurayin ya yafito ta tun daga nesa cikin qwarewa da sabo da kiran kyawawan 'yan mata a wurin fati na yau da kullum. . Kyakkyawar yarinyar ta taso daga cikin qawayenta ta same shi, suka dan kebe, sauran jama'a kowa nata harkarsa. "Idan ba za ki damu ba 'yan mata, zan so ki ba ni 'yan mintuna koda biyar ne haka, domin kuwa ina da wata 'yar magana da ke." . Yarinyar ta yi masa fari, ga alamar wayayyiya ce, ta ce "In ban da abinka malam, ka taba ganin wanda zai damu da sauraron baqon shi? Ba komai kai dai yi bayaninka ina sauraron ka." . Nazifi ya yi mata murmushin farin ciki. "Na yi farin ciki da kika nuna mini yarda kuma na ji dadi sasai da sakin fuskar da kika nuna mini." . Ya dan saurara sannan ya ci gaba da cewa da ita. "Ni dai sunana Nazifi kuma dan asalin garin nan ne ni, domin kuwa iyayena ma a nan aka haife su. A zahirin gaskiya ni ba wani mai wadata ba ne, domin kuwa sana'ar kafinta nake yi, a nan nake ci in sha, sannan kuma in yin wasu 'yan buqatuna. Wannan shi ne dan taqaitaccen tarihina da zan sanar da ke. Na fada miki ne don ki san ko ni wane ne kafin ki ba ni amsar tambayoyin da zan yi miki." . "Wacce tambaya ce Malam Nazifi?" Ya yi mata murmushi, "Mhm! Tambayar ba wata boyayyiya ba ce. Da ma so nake yi na ji ko kina so na, sannan kuma za ki iya aure na? Ni dai gaskiya ina masifar qaunar ki malama, domin kuwa ba ki lura ba ne tunda aka fara wannan fati ke nake ta kallo?" . Zan cigaba Abokai AJALI Marubuci Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by Shuraih 99% @shuraih 99% Page 2 . Ta yi dariya, "Na ji bayaninka Malam Nazifi kuma ina yi maka albishir da cewar ka sami karbuwa a zuciyata, domin kuwa ni kaina ina matuqar sha'awar namiji irinka mai ban dariya." . Suka tintsire da dariya a lokaci guda. "Kada kuma ki ziga ni mana, in riqa fasa kaina a wurin 'yan mata." "Ba maganar ziga Nazifi, gaskiya nake fada." Ya sunkuyar da kansa sannan ya ce da ita yana murmushi. . "Ban san iyakar godiyar da zan yi miki ba wallahi, ga shi kuma ban san sunanki ba." Ta dan yi farin cikin kissa, sanna ta ce da shi. . "Kada ka damu Nazifi, kana iya kira na da A'isha." "Mhm! sunan naki akwai dadi wallahi, da ma wata rana na tava mafarkin zan auri wata kyakkyawar mace mai suna A'isha." . Suka sake yin dariya, ta ce da shi. "Kai dai Malam ba ka rabo da abin dariya wallahi." Abu kamar wasa a cikin 'yan mintoci biyar din da suka yi suka saba da juna sai ka ce sun shekara biyar da fara soyayya. Bayan ta yi masa kwatancen gidansu, shi ma ya sanar da ita inda gidansu yake. Sai ya ce da ita. . "Ina fatan dai daga wannan bikin ba mun rabu kenan ba, A'isha?" Ta sake duban shi ta ce. "Ni dai a bangarena ba mu rabu ba, amma idan kai ma haka abin yake a zuciyarka, me zai hana kai ka fara kawo min ziyara don in tabbatar da gaske kake yi." . Nazifi ya ce da ita. "Yaushe to zan zo in same ki, A'isha?" Ta jefe shi da wani sabon murmushin. "Ko gobe ma kana iya zuwa Nazifi, kowanne lokaci ina nan a gida ba inda nake zuwa." "Ki saurare ni da yamma A'isha, in Allah ya so za ki ganni." . Ta sake cewa da shi. "Don Allah ka zo Nazifi, wallahi ka shiga raina. Ba na gajiya da sauraron maganarka, kamar kada mu rabu." Suka yi dariya cikin farin ciki . Wannnan shi ne mafarin wannan al'amari. Har aka tashi fatin ya koma gida, bai daina tunanin 'yar budurwar ba. Duk ya qosa gari ya waye don yamma ta yi ya je ya same ta. . To amma ko a cikin ranshi, dama ya yi alqawarin kafin ya je wurinta sai ya shaida wa abokin sana'arsa Jamilu. Domin kuwa har suka bar wurin fatin a daren jiya bai sanar da shi abinda ya wakana a tsakaninsa da yarinyar ba . Tunanin Nazifi ya katse a yayin da ya ji Jamilu ya girgiza kafadarshi. Ya dube shi cikin tsananin kidimewa. . "Wanne irin tunani ne wannan Nazifi? Daga na dan ba ka mintoci biyu ka yi nazari amma ka share wajen mintoci goma?" . Nazifi ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ce da shi. "Wallahi tunaninta nake yi Jamilu." "Tunanin wacce kuma?" Jamilu ya tambaye shi. "Maganar me muke yi da kai, Jamilu? Tunanin masoyiyata A'isha mana, ko ka mance ne" . Jamilu ya dube shi cikin rudani. "Au Wai da ma duk shawarar da na ba ka, ba ka dauka ba Nazifi? Ai ni na yi tsammanin ka mance da al'amarin. Ni wallahi da na ga ka yi shiru na dauka tunanin wani abun kuma kake." . Nazifi ya kawar da kansa cikin wani yanayi mai kama da damuwa, sannan ya dubi abokinsa Jamilu. . "A gaskiya ba zan boye maka ba Jamilu, ba na jin zan iya rabuwa da A'isha, tunda dai tana so na. Na san dai duk tsiyar baban nata ba dai zai kashe ni ba don na ce ina son 'yarsa." ************* Ya fito daga cikin dakinsa, a lokacin da ya ji Burarin 'yarsa A'isha, riqe da jarida a hannunsa, sanye da qaton farin tabarau a kan ramammiyar fuskarsa. A daidai wannan lokaci ne mafadaciyar matar ta ci wa kyakkyawar yarinyar kwalar riga ta girgiza da Karfi, sannan ta daka mata tsawa. "Don ubanki wane ne saurayin da kika canza, fada min?" . Yarinyar ta sake fashewa da kuka, ta dora hannayenta bisa kanta. "Lallai A'isha kin zama 'yar iska, ni zaki dubi tsabar idanuna ki sanar da ni cewar wai ba kya son Gali, kin samu wani sabon saurayin To ki fada mini ko dan gidan uban wane ne a garin nan ko in ci ubanki." . Ta sake cukuikuyarta ta kayar da ita a kan lallausan kujerun da ke zagaye da tsararren falon. , "Ya isa haka nan." Tsamurarren mutumin ya fada a sanyaye. Babu alamar damuwa ko farin ciki a fuskarsa. To amma dai da ganin guru-gurun idanunsa da ke cikin faskeken tabaran ka san cewar ba a son ranshi matarsa take dukan 'yar tasa Kwallin kwal da ya fi kauna a duniya ba, duk da yake dai bai san laifin da yarinyar ta yi ba. . Matar tasa mai suna Juma ta dago kai ta dube shi tana numfashi sama-sama kamar ranta zai fita, kwata-kwata ba ma ta san lokacin da Alhaji Dage ya shigo falon ba, sai dai kawai maganarsa da ta ji. "Laifin me ta yi miki kuma Juma, kike yi mata irin wannan mahaukacin duka? Irin wannan in tsautsayi ya ratsa ai sai ki karya ta a banza." . Ta sakar mata wuyan riga, A'isha ta miqe tana sharbar kuka. Ta nufi dakinta da gudu-gudu. Alhaji Dage ya bi ta da kallo, duk da yake idan yana sanye da farin tabaronsa ba kasafai mutum zai iya karanto wani yanayi a fuskarsa ba, to amma dai a wannan karon duk da wannan uban tabaron da ya tsare harabar kusan ramammiyar fuskarsa gaba dayanta, hakan bai hana bayyanar da alamomin damuwa ba a kan fuskar tasa. . "Wai laifin me ta yi miki ne, iye?" Juma ta dube shi cikin tsananin damuwa. "Ba ka ji magana da muke ba ne da ita a lokacin da ka shigo?" "Ba wannan na tambaye ki ba. Ko na ji ko ban ji wannan ni ta shafa, ke dai ki fada mini abinda na tambaye ki." Mafadaciyar matar ta sake numfasawa, duk fuskarta ta yi sharkaf da zufa sai ka ce ta ci uban aiki. . "Wai Alhaji, wannan 'yar banzar yarinyar saura kwana takwas kenan fa a daura aurensu da Gali, shi ne don rashin albarka ta same ni har daki ta shaida mini cewar wai ba ta son shi, ta samu wano sabon saurayi wanda take so." . Alhaji Dage ya cire qaton tabaron cikin tsananin kaduwa da jin zancen matarsa Juma, saura qiris jaridar ta sullube daga hannunsa ta fadi qasa. Ya tambaye ta a tsorace. "Ta canza wani saurayi fa kika ce...? "Qwarai kuwa, idan kuma ka tababa sai in kira maka ita ka tambaye ta ta fada maka kai ma ka ji." . Ramammen mutumin ya ja doguwar ajiyar zuciya. Abu na farko da ya fara darsuwa a zuciyarsa shi ne, yanzu dai idan wannan 'ya tasa ta bijire har maganar auren nan ta lalace, a ina zai lalubo dubbban daruruwan kudin da suka cinye wa wannan saurayi da zai aure ta? wanda akalla ba akasara ba, in dai lissafi za a yi dalla-dalla to sun ci wa saurayin kudi ya kai miliyan guda, duk don kawai za su aurar masa da 'yarsu daya, sai kace 'yar zinare. Shi kuma da yake Allah ya jarrabe shi da son ta, haka nan yake ta bayarwa, tunda dai ya san in dai aka riga aka yi auren duk masifa dai kuma ba za a ce ya riqa ba da albashi duk wata ba. . "Amma fa wannan yarinyar tana neman dama mana lissafi, domin kuwa idan zancen auren nan ya lalace ban san yadda zan yi da wannan yaro ba." . Ya yi ta sambatu shi kadai matar tana tsaye tana kallon sa. . Abokai kuyi mani afuwa kwana biyu ina skul shi yasa kuka jini shiru Shuraih usman AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 3 . Duk da yake da ita ma irinsa ce, ba wai auki gare ta ba, to amma dai ta fi shi cika fuska, domin kuwa duk da tambarin da sunanshi ya yi a gari, wajen masifa da rashin hakuri, to idan ya dawo cikin gidansa kuma sai ya yi lagwaf kamar tsumma. . Domin kuwa matarsa Juma ta fi shi masifa nesa ba kusa ba. Kuma ko tsiyar tasu ta taso shi da ita, ba ya wani cin riba, don kuwa ta fi shi baki. Shi ya sa yake lallaba ta tunda dai ya san cewar jiya ba yau ba ce. . Da ace sanda yake da dukiya ne, kafin ya samu karayar arziki, ai itama ta san cewar ba abokiyar takawarsa ba ce. To amma tunda ta ga cewar dan abinda yake takamar ya kare, sai dai 'yan dabaru a gari, ita ma ta daina raga masa a cikin gida . "To wai a ina ma ta samu wani saurayin, kuma ma dan gidan wane ne a garin nan?" Alhaji Dage ya tambaye ta cikin karaya. . Juma ta turo baki a fusace ta ce da shi. "Ni fa ba ta fada mini ko wane ne ba. ta dai ce da ni ba za ta auri Gali ba. Kuma ni ina tsammanin duk yadda aka yi a wajen wannan tsinannen fatin bikin kawarta da ta je jiya, ta hadu da saurayin domin kuwa ba ta dawo nan gidan ba sai da talatanin dare." . Alhaji Dage ya warware jaridar ya soma fifita, domin kuwa a halin yanzu shi ma zufa- zufa yake ji. . "To in ban da abinki Juma me ya sa kike barin yarinyar nan tana zuwa wani fati? Kin san fa yanzu zamani ya canza. A wurin wannan fate-faten na alatsine, a nan 'yan mata suke lalacewa, su kangare a yi ta fama da su, ko kuma ma su je su kunsowa mutane abin kunya." . "To yanzu dai aikin gama ya gama." Juma ta ce da shi. "In dai kangarewar ne ita dai A'isha ta riga ta yi tunda har ta dube ni ido da ido ta ce a canza mijin aure, don haka yanzu ya rage namu mu nemi mafita, amma wannan cacar bakin da muke yi ba za ta fisshe mu ba." . Alhaji Dage ya sake jan doguwar zuciya, sannan ya ce da matar tasa. "Eh to ke ma a nan kin kawo shawara mai kyau Juma, domin kuwa ko da a ce al'amura sun lalace ita yarinyar ba ruwanta, mu za a tsare don haka lallai dabara ta rage tamu." . Ya sake numfasawa, zuwa can ya tattara hankalinsa wuri guda, ya ce da matar tasa a sanyaye. "Ina ganin abinda za mu yi shi ne mu zuba idanu mu ga sabon saurayin nan, babu mamaki yana da maiko-maiko. Idan zai iya ba mu naira miliyan guda mu biya Gali kudadensa da ya kashe, ina jin ai ba wata matsala ba ce, miliyan guda kawai zai ba mu sai a sallami Gali a daura auren da shi." ********** . Ta sami kimanin awa daya cur a kwance a dakinta, tana ta faman sharbar kuka ita kadai. Tunda take a duniya ba ta taba samun kanta a cikin matsanancin halin damuwa irin wannan ba. . (Shuraih 99% daga hausaebooks.cf) A'isha ta tsayar da kukan, ta mike ta zauna a kan gadonta, ta kurawa bangon dakin idanu, ko kiftawa ba ta yi. To amma a zahiri ba bangon dakin take nazari ba, hankalinta da kuma wani tunaninta kai gaba dayan zuciyarta ma ba ta kan komai sai a kan wannan dan saurayin da suka hadu a wurin fatin kawarta a daren jiya . Tun rabuwarsu bayan ta dawo gida, ta yanke shawarar ko dafa ta za a yi a tukunya ba za ta taba yarda a yi wannan aure nata da wannan saurayi mai suna Gali ba. . Domin kuwa har ga Allah matsa mata ake yi, amma ba ta kaunar sa ko miskala zarratin, to amma a yanzu tunda dai har Allah ya hada ta da Nazifi, to ta kwana gidan sauki. . A'isha ta dade da sanin wannan al'ada ta mahaifinta, domin kuwa ba akana ta ya fara yiwa `ya`yansa auren dole da, attajirai masu hannu da shuni ba. Duk yayyenta da aka aurar su kimanin biyar duk auran dole akayi musu, to amma ita lallai akwai alamar daga kanta za`ayita ta kare, . domin kuwa komai tsiya baza ta bada goyon baya ba, duk da yake kuwa ta san mahaifinta ya ciwa saurayin makudan kudi, duk kuwa da cewa saurayin nata Gali soja ne, da shi aka je kasar Saliyo. . Ita kanta wannan dukiyar da yake facaka ita, a dalilin wannan yaki ya same ta, domin kuwa an ce gwamnati ta basu miliyoyin kudi, wadansu kuma suna cewa daga can kasar ya samo wannan dukiya. To amma dai koma mene ne sanin kowa ne cewar saurayin ya samu kudi, , wadanda kuma ba su yi masa amfani wajen mallakar masa zuciyar `yar budurwa A`isha ba, domin kuwa ko da wurinta ya zo sai dai ya kari surutunsa shi kadai, amma ba za ta ce masa ci kanka ba . To amma kuma duk da wannan durama da suke yi wai a zahiri saura kwanaki kalilan a daura musu aurensu. A`isha ta share hawayen da ke gangarowa daga cikin idanunta, sannan ta yunkura gwuiwoyinta babu karfi . Ta sauka daga kan gadon, domin kuwa ta san cewar a kowane lokaci bayan yanzu, Nazifi zai iya zuwa ya same ta a cikin wannan hali. Don haka gara ta gaggauta ta kimtsa kafin ya zo. Nan da nan ta nufi bandaki, . ta yi wanka ta fito fes kamar babu wani abu da yake damun ta. Ta fiddo kayan kwalliyarta ta soma caba ado. Har kawo wannan lokaci zuciyarta ba ta daina tunanin masoyinta Nazifi ba. . Ta yi tunanin cewar duk don saboda ta ce tana kaunarsa aka lallasa mata shegen duka, ta yi wa kanta murmushi sannan ta ce a bayyane. "Ka da ki damu A`isha ba ki fadi kasa ba, in dai don soyayya za a yi miki wannan uban duka na kawo wuka. Ba ki fadi a banza ba A'isha, 'yar autar mata, soyayya ai ta fi gaban wasa." . Ta kammala shiryawa, ta dubi madubi, ta gamsu da abinda ta gani. Ta yi wa kanta murmushi domin kuwa ta san cewar wannan kwalliyar za ta biya kudin sabulu, tunda dai masoyinta na gaskiya ne zai ga kwalliyar. . Dadai a ce wannan wahalallen ne zai zo, to ba za ta tsaya bata lokacin inganta wata kwalliya ba. Domin kuwa ita da a ce ma akwai abinda za ta shafa, ko ta sanya a jiki, ya gani ya daina kaunar ta, to da tuni ma ta aikata sun rabu, don ta hutawa rayuwarta da wannan naci nasa. . Haryanzu dai kuna tare da Shuraih 99% cikin littafin AJALI na shafi'u dauda giwa Muje zuwa AJALI Na Shafi'u Dauda Giwa Typing by Shuraih Usman Post by shuraih 99% @shuraih 99% Page 4 . Tunda take ba ta taba ganin mutum da shegen nacin tsiya irin wannan saurayi da aka sa ranar bikinta da shi ba . Babu irin cin mutuncin da ba ta yi masa ba, amma kullum yana nan like da ita don tsabar masifar naci. . Don ma ta yi sa'a ne a halin yanzu ba ya nan,ya yi tafiya kafin ranar daurin aure ta zo Amma ba don haka ba da tuni har ya zo ya dame ta da surutun tsiya. . Tunanin A'isha ya yanke a yayin data ji sallamar wani karamin yaro, ta amsa sallamar yayin da yaron ya turo kofar dakin ya shigo . "Wani mutum ne ya ce in kira masa ke, yana can waje." A'isha ta ji gabanta ya fadi, ta ce da yaron. "Bai fada maka sunansa ba?" Yaron ya dan yi jim, sannan ya ce da ita. "Ya fada min, ya ce in fada maki Nazifi ne ke son ganin ki." A'isha ta rike numfashinta, ta yi murmushi sannan ta ce da yaron. "Don Allah ka je ka ce da shi ga ni nan zuwa yanzun nan." "To." Yaron ya fada cikin ladabi, ya fita. Ficewarsa ke da wuya ta bazama zuwa inda kayan sawanta suke, ta zabo wani uban leshi mai ruwan hoda, ta fara hanzarin sanyawa. . Duk Allah-Allah take yi ta je ta same shi, domin kuwa da tunaninsa ta kwana a zuciyarta . To sai dai kuma abinda 'yar budurwar ba ta sani ba shi ne ba ita kadai ce ke murna da zuwan saurayin ba, bayan ita hatta mahaifinta ma shi ma yana matukar murna da ganin saurayin, domin kuwa ya yi bakam a daki, . duk ya kosa su yi magana da sabon saurayin ya shaida masa kaulinsa na zunzurutun kudi naira miliyan daya, idan yana son a aurar masa da kyakkyawar A'isha. . BABI NA BIYU Ta fito daga cikin gida fuskarta wasai, sai sheki take yi, tana murmushin farin ciki. Kai da gani ka san cewar a boye, a bayan wannan kyakkyawar fuskar tata, akwai wani muhimmin albishir, wanda ga dukkan alamu kuma idan har ta furta shi daga bakinta, . To dole ne ma ya dadada wa wanda take shaidawa, tabbas zai dadada zuciyarsa. A'isha ta tsaya wuri guda, tana waige-waigen inda ya tsaya a cikin harabar gidan, wadda ke cike da shuke-shuke na alfarma da kuma tsirarun dawisu dake zirga-zirga nan da can $ jikinsu sai kyalkyali yake yi, a cikin dan abinda ya yi saura na hasken ranar da ke kokarin isa ga mafadarta. Duk da karayar arzikin da mahaifinta ya yi, da ganin dankareren gidansa, ka san cewar a wani zamani da ya wuce an yi tabara da naira. . Ba kasafai za ka samu wani mahaluki a harabar gidan ba, kullum wurin yana nan tsit kamar makabarta. Wani lokacin kuma idan Alhaji Dage ya bushi iska, yakan fito da kujera wajen harabar ya zauna ya yi ta karanta jarida. Mafi

Chapter 1 of 4